ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce,  kawai sai na karSi abinci a gidan wani Wan uwa, haka akwai dan mutuwar zuciya?. Ba halina bane, ko a gidanki bazan karSa ba balle wani. "

"Didi ta yi murmushi kaWan ta ce,  yanzu dai me zaka ci yau?. Ya marairaice fuska yana lumshe idanu cikin jin"

"daWin ganinta ya ce,  kema kin sani ai Didi.  An gama. "

 Me kika fito yi ne?.

" Ganin ka mana, tunda kai baka je inda nake ba ai ni nazo inda kake. Kullum cikin tunanin ka nake, sai da na fito nazo na samu nutsuwa. Omar ya shafa kansa yana murmushi cike da ™aunarta ya ce,  naso nazo kuma fa, zan zo dai ba yanzu ba. Bata ce komai ba tayi murmushi kawai."

"Kallon ta ya kuma yi fuskarsa a sake kamar zai yi magana sai ya fasa. Ta Waga kai ta ce,  FaWi abinda yake"

bakin ka.

"Yayi ΄ar dariya ya ce,  a dai yi shiru kawai, amma naji daWin ganinki. Murmushi ta kuma yi ta ce,  na shiga wajan Hajja ta ce min kwana biyu bata ganin ka, shine nace Omaar kai kuwa baka shiga ku gaisa?. "

"Ya wara idanu ya ce,  Wai Hajjan nan wacece tawa? Uwata ce ko kakata?. Babu dangi uwa da uba ki dinga"

"saka ni zuwa wajan ta?. Didi ta ce,  babu Waya, amma ta wani Sangaren tafi dangin uwa da uban, saboda"

"tayi mana abinda si basu yi mana ba a lokacin da muke bu™atar taimako. Bani da wacce nake kallon matsayin uwa da Kaka sai ita, in kai baka kallonta a haka ni a haka nake kallonta. "

 Ke ki ka ga zaki iya ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba.

"Didi tayi dariya tana girgiza kai ta ce,  oh halin ka dai na zafin kai yana nan, Allah ya sauke maka shi ka huta. "

"Bai ce komai ba sai leda da ya Wauko a gefen sa yana fito da takalma daga ciki. Didi ta ce,  kai ma sha Allah! Omaar wannan design Winku ne?. Bai yi magana ba ta sake duba takalmin, daga can ™arshen takalmin wajan dunduniya akwai wani ™aramin sign da aka rubuta tiger cikin wani rubutu da yake a kwance sai ka kula zaka fahimta."

"Didi tayi murmushi ta ce,  kai amma yayi kyau takalmin nan Omar, kamar ba hannu ne yayi shi ba. Ya kalle"

"ta ya ce, na ki ne, gana mijinki. Ban san size Winsa ba ban sani ba ko zai masa ya faWa yana bata. Iri Waya ne takalmin banbancin design na maza da mata, amma iri Waya ne sak komai da komai. Didi ta ce,  kai amma mun gode. Kuma kaga zaku iya fara siyar da wannan couple design Win wallahi za a yi ciniki. "

" Ana yi sosai ma, sai dai ki cigaba da taya mu addu a ya faWa tana kallon ta."

" In sha Allah Omar, addu a kullum cikin yi maka ita nake. Yanzu ma tunanin sadakar azumi nake yi, ban san ya za a yi ba. Can unguwar mu babu wasu jama a sosai sannan ban san kowa ba tukunna, nan kuma kai kaWai ne da ace kayi aure ne sai matarka cigaba da yi, amma zan san abinda zan yi. Yadda Allah ya dafa mana ana cinikin nan dole mu dage da sadaka, Allah ya cigaba da ri™o da hannun mu ya gafartawa iyayen mu. "

"Ya amsa da amin kana ya ce, Ki dai faWa min in za ayi kar naji kin bayar da kuWin da kanki, sadakata ce daman"

"ai. Tayi dariya ta ce,  tamu dai, ai tare muke yi ba kai kaWai ba. "

"Omar dai bai tanka mata ba ta sake juya takalmin da yayi kyau sosai ta ce,  Amma kuna Wora a social media"

"ko?. Omar ya ce,  eh to bana ce ba, ana yi amma ba a mayar da hankali sosai a kai ba, amma za ayi.  Ya dai kamata wallahi, daman kai alhajin danne-danne in baka Wora kana talla ba ai danna wayarka bai yi rana ba. Nima a turo min hotuna zan saka a status da kuma Instagram page Wina. Customers dina na abinci in sun gani zasu siya sosai ma kuwa. "

 To. Bashir ne mai yin hotuna ya iya Waukar hoto sosai. Zan tura miki.

" Wanne suna za a sakawa company?.  Ni wallahi ban sani ba, zaSi. "

" Ga tiger na gani a rubuce, mai zai hana ba za a sakawa company suna Exclusive Footwear by Tiger ba, sannan sai ya zama logo Win takalman da hoton Tiger a jiki, amma a canja wannan na jiki. "

"Kai ya Waga ya ce,  za a yi hakan. "

" Ai gwara, ta yadda duk inda aka ga takalman a san na mu ne. Tunda dai wannan suna na Tiger ya shiga jininka, gwara ma a saka shi yadda kowa zai san naka ne yanzu ka bar rayuwar baya. "

"Kai ya Waga mata kafin ya ce,  za a yi, amma fa sabon kashe kuWk ne ni duk na talauce ya ™arasa faWa yana murmushi. Dariya tayi ta ce,  da rarrafe yaro yake fara tafiya, wata ran sai kuWin sunzo ka rasa me ma zaka yi dasu. Allah ya taimaka ya bada nasara ™anina. Murmushi yayi ya ce,  Amin Didi. In sha Allah sai na saka ki farin cikin da baki taSa yi ba a rayuwarki, zan cika miki dukkan burinki na duniya indai ina da rai. "

"DaWi ya mamaye zuciyar Didi ta ce,  Allah Amin. Ya rabbil alamin ka cikawa ™anina burinsa, ka bashi ikon neman halak ta hanyar halak. Murmushi ya sake yi ya amsa da amin bai ce komai ba amma a zuciyarsa yaji daWin ganinta ya kuma ji daWin addu ar da take yi masa."

"Kallon falon tayi ta ce,  WaWi da kai baka da lalata waje, sannan kana da ™o™arin gyara. Babu laifi dai kawai zance, amma gidan da ΄ar ™ura kaWan, kalli fa tv can. Omar ya kalli inda ta nuna ya ce,  tunda ki ka bar gidan nan ban taSa ta ba, kin san bana ™ura ko wajan ma bana kallo. "

"Murmushi tayi daman ta san kallo bai dame shi ba, shi dai barshi da ya zauna kawai shi kaWai hakan yafi masa komai daWi. Tana ta yabon takalmin kafin tashi ta shiga kitchen tana ji a zuciyarta sana ar nan da Omaar ya fara zata kai shi inda bai yi tunani ba.KRB2P017"

"Didi tana kitchen tana ta yi amsa mita ya bar ™wai sun lalace shi dai yana zaune dan shi bai ma duba ba balle ya san akwai wani ™wai a kitchen Win. Gajiya yayi da ya bar wannan, ya lalata wancan da take ta faWa ya fita. Wayarsa ce tayi ™ara a lokacin ya duba sai ya ga DPO da suka saba dashi ne. Šauka yayi suka gaisa yake sanar dashi in yana da dama da lokaci yana son ganinsa, ya amsa masa da zan zo in ya fito daga nan suka yi sallama ya kashe wayar."

"Wajan Didi ya koma a lokacin ta fito daga kitchen ta ce, ""Komai na kitchen Win nan ya la'ance Omar, gas Win duk ya yi ba™i saboda baka gyarawa."" Ya kalle ta ya ce, ""to aikina ne? Ina iya abinda zan iya na bar sauran."" ""Yanzu dai ka bayar a siyo kayan miya nayi maka girki."""

"""To zan aiko dashi, zan fita yanzu amma ba zan jima ba dawo."""

"""Kar ka manta dai ka bayar a kawo."" Da kai ya amsa mata ya fita ita kuma ta koma ciki."

"Bashir ya kira a waya yazo ya Wauke shi a machine suka tafi police station Win. Har offfice Win dpo suka shiga suka gaisa Omar ya zauna shima Bashir ya zauna yana kallon sa. Dpo ya ce, ""Damisa daman na kira ne akan yaran da suka dame mu da faWace-faWacen nan na daba da ™wacen waya da sace-sace. Mutanen gari suna cewa ΄an sanda basa yin komai wajan kama irin waWanna mutanen, gwamtani ta matsa mana lamba akan mu kawo ire-iren waWannan Sata gari da ake nema. Wannan dalilin ya saka na kira ka dan ka taimaka min wajan kama su."""

"Omar ya ce, ""amma kwanaki ka kira ni na tabbatar maka da duk abinda ya shafi wannan Sangare na fita a ciki, aikin ku ne kama mai laifi ba ni ba, na yi iya abinda zan yi muku a baya amma yanzu babu ruwana a cikin wannan lamari."""

"""Na sani Damisa, taimako nake so ka yi min wajan bani list na waWanan Sata garin da ka sani dan a taimaki al'ummma."" Omar ya kalle shi ya ce, ""dole sai an haWa kai da mutanen gari da masu unguwa sannan za a kawo ™arshen wannan faWan na cikin unguwa. Ko wacce unguwa a san su waye Sarayin sun kuma san masu tayar da fitina, wani lokacin masu faWace-faWace daban masu sata da ™wace waya daban, amma da yake su masu faWan su ake gani da makami duk abinda ya faru kawai su ne. Kowa na unguwa ya san waye Sarawon unguwa ya san mai faWan daba, kowa ya san har cikin gidan su amma tsoro sai ya hana a faWa. Misali kamar ni a baya, kowa ya san ina daga cikin Sata garin da ku ke nema, amma in zaku kwana kuna tambaya a unguwar babu lallai a faWa muku saboda ana jin tsoro. Kowa ya san ta inda Sarna take Sullowa a unguwanni shiru kawai ake yi, iyayen su kuma in aka zo ana faWa sai suce su ™arya ake yiwa yaran su kuma bayan sun san gaskiya. Wannan abinda kake so nayi maka aikin ΄an unguwar da ka ke nema ne, shugaban unguwar zaka je ka samu ya baka list na mutane da ake zargi a wannan Sangaren."""

"Dpo ya ce, ""Wannan gaskiya ne Damisa, kuma inda ΄an unguwa zasu yi ™ungiya suzo wajan hukuma su faWi suna da inda waWannan mutane suke wallahi da sun rage mana aiki. To kowa ya san Wan iska amma sai a ™i fa Wa, in an faWa an kama iyaye su shiga radio suna cewa an kama musu yara ba tare da laifin komai ba kuma sun san gaskiya. Yanzu ™ananun yara ake samu da wannan Wabi'a, wani yaro da aka kama da laifin ™wacen waya bai fi shekara sha biyar ba. Da aka kama shi mahaifiyarsa zage-zage ta dinga yi mana wai ™arya ake yiwa W anta, da aka tambayi yaron ya amsa a gabanta ya aikata, akace meye dalili ya ce baya cin abinci ya ™oshi shiyasa yake ™wacewa ya siyar dan ya ci abinci. Tsakani da Allah wannan ba laifin iyaye bane?."""

"Omar ya ce, ""shiyasa na faWa maka mafita, kowa ya san na kirki ya san na banza. Manyan unguwa zaka samu a"

"haWa kai dasu a hukunta duk mai laifi."""

"""Kai na san ka sansu, shiyasa ana nemo ka dan ka taimaka min."" Omar yaja numfashi ya kalle shi ya ce, ""ni"

"unguwar da nake babu wannan matsalar gaskiya, sai dai sauran unguwanin."""

"""Su nake so ka bani list na waWanda ka san basa jin magana."" Omar ya girgiza kai kafin ya kalle shi ya ce, ""To ni yanzu bazan iya banbancewa ba saboda kaga na jima da fita harkar nan, kullum samun sabbabin fuska ake yi musamman yaran da ka faWa wanda suke fara ta'addaci saboda babu. Amma idan na tattara zan turo maka koda ta waya ne."" Dpo ya ce, ""na gode sosai Damisa. Samun irin ku masu taimakawa hukuma abin alfahari ne sosai."" Ya kalli Bashir ya ce, ""ma sha Allah! Kaima ka dawo kamar Ogan ka."""

"Bash ya ce, ""duk inda Damisa yake a nan muke."" Murmushi yayi ya ce, ""Gaskiya ne. Gwara hakan, yanzu kowa"

"ya ganku ya ga mutanen kirki. Duk da dai daman Damisar naku bai yi irin kamannin ku ba."" Omar mi™ewa yayi suka sake gaisawa da shi sannan ya fita suka wuce shago kai tsaye."

Ana ta aikin takalma shagon ma ya yi kaWan sai da aka sake karSar wani haya aka haWa biyu saboda Waya ya matse. Ya jima a can sai bayan sallar la'asar sannan suka koma gida Bashir yana sauke shi ya tafi shi kuma ya shiga gida.

"Kallon gidan ya tsaya yi domin an share shi tass babu ™ura ko kaWan sai ™hamshi yake yi, ya yi murmushi dan ya san aikin Didi ne ya shiga falon da sallama. A zaune ya same ta tana waya yana shigowa ta kashe wayar ta ce, ""ina ka shiga tun safe?."" Zama ya yi ya ce, ""na je shago ne. Ni na Wauka kin tafi."""

"""Ban tafi ba, sai zuwa magriba zai zo mu tafi."" Bai amsa ba ta ce, ""da sai na fita na bar gidan a buWe?."" ""Yau aka fara?"" Ya faWa yana kallonta."

"""To kaje dai ka ci abinci."""

"""To Didi, an gode."" Kallon sa dai take yi cikin tausayi dan gabaWaya tausayi yake bata, rashin uwa babban masifa ce a duniya, inda ace mahaifiyarsu tana da rai da Omar bazai yi maraici dan tayi aure ba. Tashi yayi ya shiga kitchen Win sai ga shi ya dawo da abinci a bowl ya zauna yana ci sai aka kira shi a waya ya Wauka yana amsawa duk magana akan sana'ar da ya fara ne kafin ya kashe."

"Kallon sa ya ga tana yi ya Wauke kai bai ce komai ba, ya kuma kallonta ya ga dai kallonsa take yi ya ce, ""Didi ya dai?."""

"""Omar ka daure ka yi aure don Allah."" Ya Wan yi murmushi kaWan ya ce, ""Ikon Allah, wai meye damuwarki akan nayi aure ne?."""

"""Saboda ina so ka fita daga maraicin nan da ka ke ciki."""

"""Wa zan aura?."""

"""Ga mata nan da yawa sai wacce ka zaSa. Ka duba yadda ka koma saboda rashin mai kula dakai."" Šan taSe baki ya yi ya ce, ""to zan yi."""

"""Ko ka bani dama na zaSa maka matar?."" Kallon ta yayi sai ya Waga mata gira alamun eh ta ce, ""da gaske fa nake."""

"""Nima haka"" ya bata amsa yana cigaba da cin abinci dan so yake ya katse zancen auren nan da take yawan yi masa."

Kamar yadda ta ce sai bayan sallar magriba AbdulHamid yazo suka shiga har wajan Hajja suka gaisa sannan

"suka fito, Omar ta kira a gida suka gaisa yana ta tambayar yaushe zai kawo musu ziyara ya ce zai zo. Sallama suka yi suka tafi shi kuma ya koma gida zuciyarsa babu daWi ko kadan."

"Ashraf duk yadda ya kai ga rarrashin Narma abin ya ci tura sai kuka take yi kamar ranta zai fita, hankalinsa ya"

"tashi sosai dan bai Wauka zata yi kuka har haka ba. Ya Wagota jikinsa yaji jikinta akwai zafi alamun zazzaSi ya ce, ""Haba my love! ki daina wannan kukan mana, jikinki yayi zafi sosai."" Narma ta ture hannunsa daga jikinta ta ce, ""ka ™yale ni."""

"""Ta ya zan ™yale ki bayan baki da lafiya? Ki tashi na kai ki asibiti kinji."" Tsaki tayi ta juya ta kwanta tana share hawaywe. Babban ba™in cikinta da Ashraf ya same ta a banza a wofi, ta so tayi tattalin jikinta har ta kai wa Omar masoyinta amma gashi a banza a wofi ya same ta komai ya lalace."

"Shi kuwa Ashraf baya ya koma yana kallonta, sai da ta gaji da kukan dan kanta sannan tayi bacci ya tsaya yana"

"kallonta. Murmushi ya yi yana shafa fuskarsa, tarin sha'awarta da yake ji gabaWaya ta kau sai shau™i da ya ke mamaye masa zuciya. LeSensa yake lashewa a hankali in ya tuna irin abinda ya tarar a jikinta sai yaji tsigar jikinsa na tashi har yana mararin sake kai kansa gare ta."

"Ta jima tana bacci har akayi sallar i'sha sannan ta farka, tunawa da abinda ya faru da ita sai ba™in ciki ya mamaye zuciyarta, tsanar Ashraf ta yi mata dirrar mikiya a zuciyarta. Da™yar ta iya tashi ta kai kanta banWaki ta jima a ciki sannan ta fito. Doguwar riga kawai ta saka ba tare da ta saka komai ba ta saka hijjabi ta tayar da sallah. Jiri taji yana Waukarta a tsaye sai da ta zauna ta iya ™arasa sallar."

"Tana idarwa kiran Mum ya shigo wayarta Wauka murya a dashe ta ce, ""Mum!."" Daga can Sangaren Mum ta ce, ""Subahanallah! Daughter me ya same ki? Kar ki ce min kuka kika yi?."" Narma ta ce, ""Mum bana son zama a nan ni gida zan dawo, bana son zama da Ashraf baya sona ko kaWan."""

"""Me ya faru?."""

"""Mum raping Wina yayi"" ta faWa murya na rawa alamun kukan zata sake yi. Mum da mamaki ta ce, ""raping! Ashraf Win ne yayi raping Winki?."""

"Narma ta ce, ""Eh Mum."" Mum ta ce, ""Narma! he's your husband fa, dan hakan ya faru baza ki kira shi da"

"raping ba."""

"""Amma Mum ai ya faru ne without my consent, ya san bani da lafiya bana cikin nutsuwata amma bai iya ™yale ni ba sai da yayi raping Wina. Ya bari na amince mana, ya bari na samu lafiya mana. Ni na gaji bazan iya zaman nan ba Nigeria zan dawo."""

"Mum ta tausasa murya ta ce, ""i'm sorry, yanzu me kike ji?."" Narma a shagwaSe ta ce, ""my whole body is in pain, I can't event sit properly. Mum I don't think I can stay here anymore"" ta faWa a sanyaye cikin sangarta da shagwaSa. Mum ta ce, ""ki daina kuka, kin sha magani?."""

"""Uhum uhum."" ""Ina Ashraf Win?."" ""I don't know."""

"""Okay, let me call him to take you out to hospital"" Tana faWar haka ta yanke kiran."

"Ba jimawa Ashraf ya shigo ya ™araso ya Wuka a gabanta ya ce, ""i'm sorry my love, I'm sorry. Tun Wazu nace mu je asibiti kika ™i, yanzu ga Mum ta kira ni tace na kai ki asibiti. Please saboda Mum ki tashi mu je kin ji?."" A tausahe yake maganar amma jin maganarsa take yi kamar ta aljanu saboda haushinsa da take ji."

"""Please my love!"" Ya sake faWa yana kallonta tare da Wagota ta mi™e tsaye. Zare hijjabin jikinta ya yi ya ajjiye ya kalle ta ya ce, ""na saka miki kayan?."" Idanunta a kulle yake ya kalli kayan jikinta yaga ana hango komai na jikinta. Wajan kayanta yaje ya duba ya Wauko doguwar riga wacce tafi ta jikin ta kauri sai dai itama roba ce. Bai damu ba ya ™araso ya bata ya ce ta saka."

"Zame ta jikinta tayi ta fara saka wacce ya bata yana tsaye yana kallonta, lumshe ido yayi yana sake ™arewa surarta kallo da take a bayyane babu abinda ya rufeta. Ashe duk abinda yake gani a cikin kaya yana Waukar hankalinsa ba komai bane, yanzu ne yake ganin asalilin sura da abinda ya aura, dan shi kam surarta ya aura dan"

"ba ™aramar sha'awarta yake yi ba. Babu abu mai Waukar hankali a jikinta kamar ™ugunta, hips Winta a cike yake sosai ga wrist Win nata Wan ™arami kuma siriri hakan ya bawa shape Winta damar fita sosai, in ta juya baya boobs Winta ma abin kallo ne."

Da™yar ya iya kawar da kai ta saka kayan amma ta™i motsawa ™arshe sai dau™ota ya yi suka fito harabar gidan. Da yake akwai mota a apartment Win da suke yana fita ya ajjiyeta ya buWe garage ya Wauko mota sannan ya sake fitowa ya Wauketa ya sakata ciki suka tafi. Koda suka je can ma duba ta aka yi aka bata magani aka saka mata drip dan jikinta ya saki. Bacci ta sake yi shi kuma yana tsaye yana kallon ta cikin tsantsar shau™i da son sake kasancewa da ita a karo na biyu.

Da daddare hankalin Nayla sam baya jikinta kasancewar washe gari shine ranar da Abiy ya bata zata

"faWa masa waye zaSinta. Bata cikin kwanciyar hankali dan bata san abinda zata ce masa ba. Tana zaune a falo tana kallon tv amma ba fahimta take yi ba tunanin ta na ga abinda zata cewa Abiy ya amince da ita. Dan ita dai ta san bata son waWannan mutane, in tace ta Wauki Waya wanda zata iya zaman aure dashi ta cuci kanta ne, kuma kamar yadda Mama ta faWa zata dinga kwasarwa kanta zunubi ne kawai."

"Mama ce ta shigo Wakin har ta zauna kusa da ita bata sani ba sai da ta taSata sannan ta kalleta ta ce, ""Nayla tunanin me kike yi haka?."" Nayla ta sauke numfashi tace, ""Mama tunanin gobe nake yi, ban san me zan cewa Abiy akan maganar nan ba."""

"Mama ta ce, ""har yanzu bakya jin zaki iya zama da mutum Waya a cikin su?."" Nayla ta Waga kai ta ce, ""bana ji Mama, wallahi bana ji gabaWaya."" Mama tayi ajiyar zuciya ta ce, ""Kawai zan faWa masa akwai wanda ki ke so."" Nayla ta wara idanu waje tana kallon Mama da firgici ta ce, ""don Allah Mama kar ki faWa masa, in kika faWa masa ya nemi sanin waye shi fa?."""

"""Sai mu faWa masa waye, in ya kuma kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa da kina sona kuma aurensa kike so ki yi."""

"Nayla ta fara girgiza kai cikin tsoro ta ce, ""bazan iya ba Mama, bazan iya ba wallahi."" Mama ta dafata ta ce, ""ni"

"zan iya yi miki faWan Nayla, abinda nake so in ya kira ki ya tambaye ki ki tabbatar masa dake shi kike so kuma shi ki ke son aura. Zaki iya ko baza ki iya ba?."""

"Nayla ta kalli Mama cikin rauni ta ce, ""Mama bazan iya ba, bazan iya kallon Abiy na tabbatar masa Ina son"

"Omar ba, bazan iya ba gaskiya."" Mama ta ce, ""zaki iya, zuciyarki zaki saurara da zarar ya kiraki, kar ki bar harshen ki ya sarrafa kalaman zuciyarki, kai tsaye ki bari su fito daga cikinta ki faWa masa gaskiya, in ba haka ba in ya gano da kansa ransa ne zai Saci sosai."""

"Nayla ta ce, ""Mama gwara ya gano da kansa da ace nice na tabbatar masa."" Mama ta dafata cikin rarrashi ta ce,"

"""Nayla bazan taSa bari naga kina son abu ina da damar baki shi ban baki shi ba, sannan bazan taSa bari naga kina shan wahala akan abinda bai fi ™arfin ki ba kuma na zuba miki idanu. Zan iya yin ko meye wajan ganin na samar miki da farin ciki koda ni zai zama silar ba™in cikina. Dan haka ki bani haWin kai Nayla, na tabbatar miki zanyi abinda mahaifinki zai baki abinda kike so ba tare da tashin hankali ba ko wani abun."""

"Nayla ta kalli Mama cikin gamsuwa da kalamanta ta ce, ""Na sani Mama, amma bakya ganin Abiy zai yi fushi"

"dani?."""

"""Babu fushin da zai yi dake, ki bar komai a hannuna ina tabbatar miki da babu abinda zai faru sai alkhairi."" Nayla ta sauke numfashi ta ce, ""To Mama"" ta faWa a sanyaye tana wasa da hannunta. Mama tayi murmushi ta ce, matar Omar."" Kunya ta bata sai ta rufe fuska da hannunta kafin ta buWe ta ce, ""Mama shi fa bai san Ina sonsa ba, taya zan aure shi?."" Mama ta yi murmushi cikin shigar kwantar da hankali ta ce, ""ke dai ki jira mu gama da Abiy zamu koma kansa."" Kai

Please Login or Register in order to submit comment