ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya zan iya kwana a Wakin nan? Ta faWa tana zare hijjabin jikinta dan zafi take ji. Garin zare hijjabin hular kanta ta biyo hijjab Win ta ma™ale a ciki.

"Shi dai kallon ta yake yi yana mamakin abinda ya kawo ta, tunda ta shigo yake jin ™hamshinta, lokacin da ta cire hijjabin sai ya kasa daina kallonta tun daga gashin kanta har ™afarta da take sanye da room slippers mai kamar safa. ˜are mata kallo yake yi cikin jajayen kayan da suka yi mata kyau, sun karSeta duk da basu kama jikinta ba amma surarta ta bayyana a cikin kayan musamman ™irjinta."

"Ido ya lumshe jin zuciyarsa na bugawa sosai, ya haWWiyi yawu ya sake buWe ido yana kallon gashin kanta da ta Waure shi a tsakiyar kanta. Ya ji me take cewa yana mamakin kenan Didi ce ta turo ta tazo ta kwana tare dashi, lallai Didi ta raina shi da yawa, sai ya taka mata burki ya ga ta za™e da yawa a lamarinsa."

"Kamar ance Nayla ta kalli gefenta ta ganshi a zaune yana kallonta, ta firgita tare da faWin,  Innalillahi!. Hijjab"

"Win ta mayar da sauri jikinta har yana rawa ta ce,  Dama& Dama& ..Didi ce& .dama& .tace& .wai nazo na kwana a nan ta faWa a rarrabe tana kallonsa. Mugun haushin abinda ta aikata yake ji shiyasa bata samu zarafin magana daga gare shi ba. Ya Wauke kai yana cigaba da kaWa ™afarsa as usual."

"Nayla ganin haka gabanta ya cigaba da faWuwa ta yi ™asa da kai ta ce,  YaMar Didi ce ta turo ni, na ce bazan zo ba ta ce sai na zo, ka yi ha™uri. Wani iri yake ji a zuciyarsa duk sanda zata faWi sunan nan, bai san me yake ji ba amma bai taSa jin abinda yake ji ba tunda ya zo duniya. Yana jin sunan ya soki zuciyarsa kamar allura, dan wani lokacin har sai ya runtse ido saboda sukar da yake ji, yana jin sunan har cikin jininsa."

"Yana jinta tana magana nan ma banza ya yi mata bai tanka ba,amma a zuciyarsa yana tunanin irin matakin da"

zai Wauka akan Didi.

"Tana tsaye yana zaune babu wanda ya sake cewa komai, ita tsoro take ji kar ta zauna tayi laifi shi kuma bazai ce"

mata komai ba. Ta gaji da tsayuwa tunda ta daWe a tsaye kafin ta shigo shiyasa ™afar ta ta Wan ri™e kaWan.

"Tsam ya tashi tsaye da niyar zuwa ya samu Didi ya tako zuwa kusa da inda Nayla take tunda tana kusa da ™ofar Wakin. Kanta na ™asa bata san ya zo inda take ba sai motsisa ta ji, tayi saurin matsawa shi kuma ya ja handle W in ™ofar. Abin mamaki ™ofar a kulle take alamun an kulle su ta waje. Murmushin takaici ya yi yana cize baki dan ya san aikin Didi ne. A bayyane ya ce,  Didi ta gama raina ni. Nayla ta kasa kallonsa tunda ta fahimci ™ ananun kaya ne a jikinsa ta kasa kallon koda ina yake tsaye. Tana mamakin kenan Didi kulle su tayi tunda gashi ya ja ™ofar a kulle, ita kanta mamakin Didi take yi balle shi."

"Ta gaji da tsayuwar gashi bata son yin laifi daman ta san haushinta yake ji, shi kuma ya koma inda ya tashi ya"

"zauna. Kallon kujerun Wakin tayi ganin ™arama ce ta zaman mutum Waya, duk da tana da faWi amma baza ta iya kwanciya a kai ba. A hankali ta taka ta zauna a kan kujarar ko inda yake ta kasa kallo."

Shi bai ce komai ba itama bata ce komai ba amma ta gaji bacci take ji. Kallon inda yake tayi ta ga idanunsa a

"kulle suke kamar bai san ma tana Wakin ba. Sai da ta tattaro nutsuwarta sannan ta ce,  YaMar bacci nake ji. A firgice ya kalle ta kamar daman jira yake tayi magana ya ce,  jira ki ke na zama gado ki kwanta!?. Yadda ya yi maganar a fusace ya saka ta kawar da kai dan idanunsa ma sun yi ja. Mi™ewa tayi da ™arfin guiwa ta ™arasa kan gadon tana tunanin kwanciya, a hankali ta zauna kamar mai ciwo kafin tayi salatin annabi ta kwanta ko hijjab Win bata cire ba."

"Hasken Wakin ya dame ta, amma tana tsoron kar ta kashe tayi laifi hakan ya saka ta cure hijjabinta Wora akan fuskarta dan ta daina ganin hasken. Yana daga zaune ya kalli inda take yana mamakin wai shine zai kwana Waki Waya da wata mace a rayuwarsa, tunda ya yi hankali bai taSa zaman awa daya da ko wacce mace ba balle kwana a Waki sai ba yau. GabaWaya wani iri yake ji yana ganin kamar akwai raini a cikin lamarin. Duk yana kallon ta har ta kwanta da yadda ta Wora hijjab akan fuskarta duk yana ganin ta."

"Shi kansa hasken ya dame shi, hakan ya saka ya mi™e ya kashe ya koma inda ya tashi ya zauna. Nayla jin an kashe hasken ta cire hijjabin tana ajiyar zuciya tana kallo shadow Winsa daga inda take kwance tana ta salati tana fatan bacci ya dau™e ta. A haka bacci ya kwashe ta ba tare da ta ga ya motsa daga inda yake ba.KRB3P019 Arewabook@nanahaleema11."

"Omar yana kallon ta har ta yi bacci a kan idanunsa, ya rasa ta yadda zai fara iya kwnaciya da mace a waje Waya shiyasa ya yi kamar bacci yake yi har ta kwanta tayi bacci. Tashi zaune ya yi sosai yana kallonta ya furzar da iska yana kallon ™ofa yana mamakin wannan ™arfa-™arfa na Didi. Yanzu in fitar gaggawa ta same shi fa? Ta rufe ™ ofa ta baya ta bar su a cikin kamar yan prison."

"Ajiyar zuciya ya sake yi gabaWaya ™hamshin Nayla ya mamaye Wakin, ™hamshin sai ya bada kala biyu da ™ hamshin turarensa da ™hamshin nata turaren, sai hakan ya bada wani ™hamshi mai bala'in daWi da kwnatar da hankali. Shi dai ya san bazai iya kwnaciya da Nayla a waje Waya ba, kuma bai san a inda zai kwanta ba tunda Didi ta rufe ™ofar balle ya ce zai fita zuwa falo ko ya fita daga gidan."

"Tashi ya yi ya dawo kan cousion ya zauna, ya Wora ™afarsa akan table ya jingina da kujerar yana lumshe ido. Hoton Naylan ne ya gifta masa a lokacin da ta zame hijjabi ta gashin kanta ya bayyana, ya buWe ido ya kalleta duk da baya ganin ta sosai amma tayi bacci. Tashi ya sake yi ya Wauko waya ya dawo ya zauna ya shiga page W insu na Instagram ya duba sai ya ga gabaWaya an goge video Nayla kamar yadda ya ce."

"Ajiyar zuciya ya yi ya kifa wayar a ™irjinsa yana jin zafi-zafi a ™irjinsa ba tare da ya san dalilin hakan ba. Shi dai ya san bai taSa jin abinda yake ji akan kowa ba sai ita Win, bai san me hakan yake nufi ba, amma yafi danganta hakan da yadda aka bashi ita baya so. Da wannan tunanin ya yi bacci a kan cousion ba tare da ya sani ba."

Haka ya dinga yin baccin yana farkawa saboda ya takura dan shi ya saba kwanciya a waje mai girma. Bai samu

"wani baccin kirki ba har asuba tayi, ya tashi zaune yana ri™e wuya saboda yadda ya ri™e masa yana Wan juya kansa kaWan. Kallon ta ya yi a lokacin ta motsa itama da alama ta ji kiran sallar a zuciyarta."

"Ajiyar zuciya ya yi ya mi™e ya shiga banWaki, yana fitowa ya saka doguwar riga da slippers ya taka zuwa kofar W akin, yana jan ™ofar yaji ta buWe. Dariya ya yi mai sauti a ransa yana girmama makircin Didi. Har zai fita sai ya kalleta ya ga bata tashi ba sai ya ja ™ofar kawai ya fita."

"Da ya dawo bai duba inda Didin ta ke ba Wakin ya shiga kai tsaye ya samu Nayla akan sallaya. Kallon sa ta yi ta ce, ""Ina kwana."" Maimakon ya amsa sai ya zauna sannan ya ce, ""Lafiya."" Daga nan ya ja bakinsa ya yi shiru"

amma yana so ya tambayeta ciwon kan da ta kwana dashi amma izza da aji bazai bashi dama ba. Sai kuma ya

sake tashi zai fita ya ake ji a kulle ™ofar.

"Dariya ya yi mai sauti a bayyane ya ce, ""Didi makira ce."" ˜aramin tsaki ya yi ya dawo ya zauna amma har lokacin fuskarsa da annuri sosai. Nayla saboda ciwon kan bata tsawaita zaman ba ta mi™e ta koma inda ta kwanta ta zauna, sai take jin yanyinta gabaWaya babu daWi. Hasken take son kashewa amma tsoron faWansa take yi shiyasa ta ha™ura ta sake kwanciya kamar jiya."

Shi dai Omar bai motsa ba yana dai kallon ta tana satar kallonsa a tsorace. GabaWaya ta rufe jikinta har fuskarta saboda hasken ya dame ta ga kanta da yake ciwo. Ya jima a haka kafin ya tashi ya kashe hasken Wakin ya koma ya zauna.

"Bai saba bacci bayan asuba sosai ba amma sai gashi ya kai har tara na safe a zaune yana bacci. A hankali ya buW e ido Wakin babu haske sosai saboda labulayen a sake suke kuma an kashe hasken Wakin. Wayarsa ya taSa ya ga safiya tayi sosai, ya juya kansa da jijiyar wuyan ta ri™e ya kalli inda Nayla take ya ganta luf bacci take yi. Hamdala ya yi da bata riga shi tashi ba, ya mi™e da™yar saboda ri™ewar ™afarsa da wuyansa ya yo ya shiga ban Waki."

"Ruwan zafi ba wani damunsa ya yi ba hakan ya saka bai kunna water heater ba ya kunna ruwan fanfo banWakin ya yi wanka. Har ya fito ya shirya Nayla ko motsi bata yi ba, shi kuma hakan ya yi masa daWi sosai ya samu ya shirya yadda yake so. Bai buWe ™ofar ya fita ba sai goma na safe sannan ya fito zuwa falon."

"Motsin Didi ya ji a kitchen ya shiga kitchen Win a karo na farko a rayuwar zaman gidan, yana shiga suka haWa ido da ita sai tayi dariya kafin ta yi magana ya ce, ""ina kwana."" Maimakon ta amsa sai ta ce, ""Angon Nayla, yau kaine har goma kana bacci? Lallai bacci ya yi maka daWi."""

"""Hmmm"" shine abinda ya furta kawai ba tare da ya ce komai ba. Didi ta kalle shi cike da tsokana ta ce, ""har"

"wani kyau na ga ka ™ara yau, sai ™hamshi ka ke yi ka fito a sak ango."" Nan ma bai tanka mata ba ya ma Wauke kai daga kallonta kamar ko yaushe fuskar babu fara'a."

"Didi ta ce, ""Don Allah kai kanka baka ji daWi a ranka ba? Ai ko babu komai na saka ka kwana Waki Waya da matarka."""

"""Shiyasa ki ka kulle ™ofar kenan?."""

"""Na san hali ne ai, tsaf zaka zo kana yi min wannan hargitsin na ka shiyasa nayi maganin ka."""

"Omar ya shafa fuskarsa ya kalle ta ya ce, ""da ki ka yi hakan wacce riba ki ka samu?."" Didi ta ce, ""riba da yawa"

"na same ta, ciki harda rashin tashin ka da wuri."""

"""Hmm Didi kenan. Kina ™o™arin ganin yarinyar nan ta raina ni, kina yi min abinda ki ke so a kanta."" ""Babu zancen raini, matar ka ce ta sunna. Nan gaba ma haihuwa zaku yi tare."""

"Kallon ™asan idanu ya yi mata kamar zai yi magana sai ya share ta yi dariya ta ce, ""ka yi magana mana, ka faWa kar ta kashe ka."" Banza ya yi mata bai kuma cewa komai ba ta gyara tsayuwa ta ce, ""Omar wai kana siyo ΄an kaya haka na gidan nan matsayinka na mai gida? Kamar su bread haka da safe, kuWin kayan miya, kuWin masu wanki, kuWin guga, da sauran kayan amfani na yau da kullum, kana yi?."""

"Ya kalle ta bai ce komai ba sai ta sassauta murya ta ce, ""Omar ka san ha™™in aure, ka san duk responsibilities W in yarinyar nan yanzu a kan ka yake. Ka duba saboda tsoronka da take ji ko Wakinka bata taSa shiga balle ace ta kwana, balle kuma ace ka sauke mata ha™™in da Allah ya Wora maka a kanta. Baka san rashin lafiyarta ba balle ka siya mata magani, baka san me take so ba balle ka siya mata. Duk da iyayenta sun kawo ta da gara akwai ™ anunun abubuwa da in ka bata fuska zata faWa maka tana da bu™atar su. Tana da mai aiki da take taimaka mata da aikin gidan nan itama ita take biyanta, duk da "" Katse Didi ya yi ya ce,"

"""Au har mai aiki ce da ita?."""

"""Ba ma ka sani ba kenan?."""

"""An faWa min? Wai gaibu na sani ne da zan dinga sanin abubuwa ba tare da an sanar dani ba Didi?."""

"""Baka san gaibu ba, amma in ka tambaya za a faWa maka. Kai ka san yarinyar nan ΄ar gata ce baza ta iya aikin gidan nan ita kaWai ba, wannan dalilin ya saka mai aiki take zuwa da yamma in ta dawo daga wajan aiki ta Wan yi mata gyara-gyare ta koma. Duk da mai aikin ta gidan kakarta ce amma ha™™in biyanta a wuyan ka yake. Har kuWin wanki ita take biya, duk da akwai washing machine a banWakin Wakinka da nata amma baza ta iya wanki da kanta ba, ta san a gidansu ba itace take yi ba yi mata ake yi. Omar kar ha™™inta ya kama ka fa."""

"Omar ya ce, ""Didi duk abinda ki ka lissafa ban sani ba, ko kina so ki ce zan san abu ne ba tare da an faWa min ba?."""

"""Baza ka sani ba Omar, amma in ka tambaya zaka sani."""

"""Ki kai ™arshen maganar ki sauri nake yi"" ya faWa yana sake tamke fuskarsa."

"Didi ta ce, ""ni dai ina faWa maka gaskiya, don Allah gyara saboda gaba."" TaSe baki ya yi ya ce, ""Didi ba auren nan nake so ba, auren ya zo ne a lokacin da ban shirya ba. Bana so kamar yadda itama bata so, wani dalilin iyayenta ya saka suka aura mata ni a matsayin hukunci saboda ga mai munin hali na duniya gabaWaya. Har gobe Ina zama a nan ne saboda ke, ba dan ke ba da yanzu ta jima da yin wani auren ma."""

"Didi ta ji haushin abinda ya ce, tana mamakin yadda yake faWar baya sonta kai tsaye ko nauyi bata ji, ta ce, ""baka yi saboda ni Win ba ai, da kayi saboda ni da ka karSi auren nan hannu biyu kun yi rayuwa kamar ko wanne ma'aurata."""

"""Uhum in da ban yi dan ke Win ba da yanzu ba wannan zanem ake yi ba. Zan bayar a kawo miki bread Win"" ya faWa yana niyar fita."

"""Ka bar shi bana ci, Kuma ka tsaya ka ci abinci."""

"""Babu abinda zan yi a duk abinda ki ka ce"" ya faWa yana fita ya bata waje. Ajiyar zuciya tayi ta tsaya kawai tana tunanin yadda zata yi da Omar, lamarinsa gaba yake in ta biye tashi sai su kai shekara a wannan rayuwar. Ita kuma Nayla take tausayi, in ba dan ita ba Ina ruwanta da rayuwarsa?."

"""Didi Ina kwana."" Didi jin muryar Nayla sai ta juya da fara'a tana kallonta ita kuma sai wani sunkuyar da kai ta"

"ke yi. Dariya ta bawa Didi ta ce, ""Kin tashi lafiya amaryar Omar?."" Nayla ta kalle ta cikin shagwaSa ta ce, ""Didi shine jiya harda kulle ™ofa."""

"""Ya jikin ki?."""

"""Da sau™i, ban tashi da ciwon ba. Don Allah Ddi ki fito daga kitchen Win nan, bara na je nayi wanka nazo nayi breakfast Win."""

"Didi ta ce, ""kina can wajan mijinki ba dole na tashi na dafa miki abinci kafin ki fito ba? Kar ki damu ni na gama"

"komai ke nake jira."" Nayla kunya ta kamata, duk da ba wani abun ne ya faru ba amma sai ta ji nauyin Didi. Ta ce, ""Gaskiya ban ji daWi ba wallahi, ya zaki yi girki da kan ki?."" Didi ta ce, ""kar ki damu, ni ai ba ba™uwa ba ce. Jeki ki yi wankan ki dawo."" ˜arasowa tayi ta kunna gas ta Wora ruwan zafi ta ce, ""YaMar ya shigo nan ne?."""

"Didi ta ce, ""eh, bai jima sosai da fita ba."" Girgiza kai tayi ta ce, ""naji ™hamshinsa, for the first time ya shigo kitchen Win nan"" ta faWa tana murmushi. Bata jima ba ta kashe gas Win ta Wauki tukunyar gabaWaya ta tafi da ita. Didi ta bita da kallo ta ce, ""in sha Allah komai ya kusa ™arewa Nayla.""KRB3P020"

"Ranar ma haka suka yini suna hira, Omar tunda ya fita bai dawo ba babu wanda ya damu da ya dawo ko ya"

"zauna. Ranar Nayla ce da kanta ta gyara Wakinsa, ta canja bedsheet Win duk da taga alamun an taSa wanke shi, ta yiwa Wakin turaren wuta sai ™hamshi ya ke yi. Tayi mamakin tsaftar sa domin Wakin tsaf ko kayan nan da"

"maza suke tarawa shi babu, komai neat har da ™aramin dustbin a gefe da kuma tsintsiyaa ajjiye. Toilet Win ma haka yake komai yana mahallinsa hatta towel da bathrobe suna ajjiye a inda aka ajjiye su."

"Bayan ta gama aikin Didi ta dinga tsokanarta ita kuma kunya take ji. Da yamma ta shirya cikin abaya ba™a wacce ta haskata matu™a ta fito falo ta kalli Didi ta ce, ""Didi bara na je wannan store Win na baya, akwai abinda zan siyo zan je dashi aiki gobe."""

"Didi ta ce, ""ma sha Allah Nayla, wannan kyau haka? Wanda bai sanki ba sai ya sauka bakya jin hausa ai."" Dariya"

"tayi sosai ta ce, ""kai Didi, kamar wata ke."""

"""Amma dai kin fadWawa mijin na ki zaki fita ko?."" Nayla ta ce, ""ya bani damar zuwa ko ina ai, tunda ya ce naje duk inda nake so kar na sake tambayarsa."" Didi ta ce, ""haka ne. Sai kin dawo."""

"""Yanzu zan dawo Didi, da ™afa ma zan je bazan hau mota ba. Ina so ma na bada motar car wash zan kira Bashir ya kai ta"" ta faWa tana fita daga falon."

"Wajan mintina talatin da fitar sai gashi ya shigo ko sallama bai yi ba. Didi ta Wauka Nayla ce sai da ta juyo ta ganshi ta ce, ""A'a sai yanzu?."" Ya kalle ta kamar zai yi magana sai ya yi shiru amma bai daina kallonta ba. Didi da mamaki ta ce, ""meye na kallon?."""

"Girgiza kai ya yi ya Wauke idonsa daga kanta, ya sake juyowa ya ya kalli Didi ya ce, ""ki faWawa wannan yarinyar kar ta sake fita koda ™ofar gidan nan ne."" Didi da mamaki ta ce, ""wacce yarinya kenan?."" Wani irin kallo ya yiwa Didi na kin san wacce make nufi ai, sai ta ce, ""To baka faWi suna ba ta ya zan gane ta ne?."" Ya ce, ""koma dai wacece, ki sanar da ita kar na sake ganin ta fita."""

"Didi ta ce, ""Wai Nayla ka ke nufi? To akan me zaka hana ta fita?."" A lokacin Nayla ta buWe ™ofar ta shigo tana cewa, ""Didi har na dawo, shiyasa na tafi key Win gate saboda kar na tashe ki buWe gate."""

"Kallon ta ya yi ya ce, ""ke! Kar na sake ganin ko da wasa kin fita daga gidan nan."" Nayla ta bishi da kallon"

"mamaki kafin tayi magana Didi ta ce, ""ba kai ka ce ta dinga zuwa duk inda zata je ba?."" ""Ai ban ce ta dinga yawo a kan titi ba!."""

"""To in bata yi yawo a kan titi ba a kan me zata yi yawo? Wai me take damunka ne Omar don Allah?. Kai ka bata damar fita kace ta fita duk lokacin da take so, dan ta fita sai ya zama fitina kenan?."""

"Nayla a sanyaye ta ce, ""kai ka ce na je ko ina babu ruwan ka."" Wara idanu ya yi akanta kamar tayi masa allura"

"ya ce, ""yi min shiru a wajan nan!."" Didi ta ce, ""ba gaskiya ta faWa ba? Ba haka ka ce Win ba?."""

"Omar a fusace ya ce, ""To yanzu na canja, na canja yanzu!. Kuma dole abi abinda na ce in ba haka ba baza a ga"

"daidai ba wallahi!. Kar na sake ganin ta fita"" ya juyo ya kalle ta ya ce, ""kar na sake gani kin fita, na soke maganar da nayi a baya, duk inda zaki je ki tabbatar kin sanar dani, in ba haka ba ranki in ya kai guda dubu W aya bayan Waya sai na Sata su wallahi."" Didi ta ce, ""Ikon Allah, me ya kawo wannan canjin kuma?."" ˜aramin tsaki ya yi ya ce, ""oho kuma"" Ya kalli Nayla da idanunsa bai ce komai ba kawai ya fita."

"Sai da ta tabbatar ya fita sannan ta ce, ""ni dai bana taSa yi masa daidai a rayuwa."" Didi ta ce, ""me ya faru a wajan ne?."""

"""Babu fa Didi, kawai yana so ya dinga yi min faWa ne shine kawai."""

"BuWe ™ofar aka sake yi duk zaton su shine ya dawo sai suka ga Tk da leda a hannunsa, ya gaishe su ya ce, ""gashi in ji Tiger."" Didi ta kalle shi ta ce, ""me ya Satawa Damisar na ku rai haka? Ya shigo yana ta bala'i shi kaW ai."" Tk yayi ΄ar dariya ya ce, ""Babbar Yaya ai wani ne yanzu ya riga Antynmu ™arasowa gidan nan, ya zo ya samu Damisa a tsaye yake faWa masa shi dai yana sonta. Ana haka sai gata tana tahowa, shine ran maza ya S aci. In kinga faWan da yake yi yanzu da ya fita sai ya baki tsoro"" ya ™arashe faWa yana dariya."

"Didi ta murmusa ta ce, ""fushi yake yi mai hujja."" Tk dariya ya yi ya fita bai sake magana ba. Ita dai Nayla tana"

"tsaye har lokacin bata zauna ba, Didi ta jawo hannunta ta zauna ta ce, ""Ke ashe kasuwa ki ka yi shiyasa ran mijin naki ya Saci har ya soke fitar ki ko na."""

"Nayla a sanyaye ta ce, ""wallahi Didi ban san shi ba."" Didi ta ce, ""haba meye na wallahi Nayla?. Kawai ya ganki yaji kin yi masa bai Wauka kina da aure ba shine kawai."""

"Nayla ta ce, ""kuma Didi ai bana saka kaya half niked ko?."" Didi ta ce, ""bakya sakawa Nayla, kina shigar mutunci"

"irin ta masu mutunci."""

"""Da na sani ma ban fita ba, abinda na je nema ma ban samu ba."""

"Ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Didi ta ce, ""na ce miki Omar kishin ki yake yi kin ce ba haka ba, yanzu"

"meye wannan in ba kishi ba?."" Nayla ta Wago ta taSe baki ta ce, ""yadda baya sona baya so wani ma ya so ni, shine kawai dalilinsa."" Didi ta yi murmushi ta ce, ""na gaji da musu dake, mu je a hakan."" Nayla ta ce, ""Amma Didi ya ce kar na sake fita, kuma zan je aiki gobe."""

"""Kar ki damu, ki jira ya shigo zuwa dare sai ki sanar dashi, yanzu a dokin fushin ya ke."" Nayla ta girgiza kai suka cigaba da hira da Didi bata bari wani zancen kishi ya yi tasiri a ranta ba."

"Yau ma kamar jiya Didi ta yiwa Nayla dole na zuwa Wakin Omar, babu yadda bata yi ba amma Didi ta ce sam sai ta tafi, kamar zata yi kuka saboda ciwon da kanta yake yi mata, amma Didi ta ce ta sha magani in ta je can tayi bacci kan zai daina ciwo. Ita tsoro ma take ji kar ta je ya

Please Login or Register in order to submit comment