ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake damunki. Jiya Maman ki ta ce min harda ciwon ™irji ko?."" Kai ta Waga alamun eh har lokacin idanunta a lumshe yake kafin ya ce, ""Jawad gobe zai kai ki wajan likita, na lura kece bakya son zuwa."""

"""Hajiya Nayla"" Salma ta furta tana kallon ta. Da sauri ta buWe ido tana kallon mutanen da suke zaune a falon. Dam! Gabanta ya buga haWa ido da suka yi da Omar da yake zaune daga gefe ya Wago kenan suka haWa ido. Wara idanu tayi ta kalli Abiy ta sake kallon su Salma ta ce, ""Salma, Didi?."" Didi tayi murmushi ta ce, ""Na'am Nayla."" Sai kuwa tayi ihu ta tashi a guje ta koma kusa da Didi ta ce, ""Didi yaushe ku ka zo? Shine ba a faWa min ba?. Wai ko mafarki nake yi ne?."""

"Didi ta ce, ""ba mafarki ki ke yi ba Nayla, ni ce yau a Kaduna."" Nayla ta ce, ""ikon Allah. Kuma Mama bata faWa min ba fa, ta ce min kawai Abiy yana nemana, ashe ku ne kuka zo. Sannu da zuwa."""

"""Yauwa Nayla, ya jikin na ki?."""

"""Da sau™i"" ta faWa tana sauke da ido ™asa farin ciki yana mamaye zuciya ta ganin masoyin ta a zaune a falon gidan su."

"Abiy da yake kallon ta yana murmushi ya ce, ""ki tashi ki je ki saka a haWa musu breakfast sun yi tafiya mai nisa."" Mama ce ta shigo falon da sallama ta ™araso ta zauna suka sake gaisawa da Didi shi dai Omar bai iya kallon ta ba sun gaisa kawai dan in akwai abinda ya tsana bai wuce gaisuwa ba."

"Abiy ya kalli Mama ya ce, ""wannan shine wanda ya taSa taimakon Nayla a Kano shekarun baya. Kin tuna?."""

"Mama ta ce, ""Allah sarki na gane shi."" Didi ta bawa Mama abinda ta taho musu dashi Abiy ya ce, ""harda wahala? Ku da ku ka yi tafiya mai nisa har sai an yi tsaraba?."" Didi murmushi ta ke yi ta ce, ""Babu komai Abiy."" Abiy ya ce, ""mun gode sosai, Allah ya bar zumunci."""

"Didi ta amsa da amin tana murmushi, ta ji daWin yadda Abiy ya karSe su wallahi, ta kuma fuskanci gadon kirki Nayla tayi daga wajansa. Mama ta kalli Nayla da ta kwantar da kanta a kafaWar Didi tana kallon Omar ta gefen idanu ta ce, ""Nayla ki je ki saka a haWa musu abinci su ci ko?."" Nayla ta Wago a sanyaye ta ce, ""To Mama."" Abiy ya ce, ""Mamana jikin ne?."" Ta girgiza kai ta ce, ""A'a Abiy, murnar ganin Didi ce kawai."""

"""To maza ki je a haWa musu abinci, sun yi doguwar tafiya."""

"Bata mi™e ba gani take in ta tafi bazata cigaba da kallon Omar ba, shi kam ko kallon inda take ma bai yi ba balle ya yi magana. Abiy ya ce, ""amma dai sai gobe zaku koma?."" Didi ta wara idanuta ce, ""A'a, anjima kaWan zamu koma in sha Allah."" Abiy ya ce, ""Toh, ai na Wauka zaku kwana ku huta gajiya ai. Shikenan ni daga nan zance ya kiyaye hanya, zan shiga Zaria bazan dawo na zame ku ba gaskiya. Allah ya kiyaye hanya na gode da girmamawa."" Omar ne ya buWe baki kamar mai koyan magana ya ce, ""Amin. Mun gode sosai, Allah ya ™ara girma."""

Lumshe ido Nayla tayi jin kalaman Omaar idanunta suna cika da hawaye saboda tsantsar bugawar da zuciyarta

"take yi. Salma na lura da ita haka Mama duk motsin ta akan idanunta take yi. Abiy ya ce, ""amin Omar, Na gode"

"sosai. Mamana ki raka su falo su huta."" Nayla ta amsa ta mi™e ta ce, ""Didi ku zo mu je"" ta faWa a sanyaye. Didi ta mi™e Salma ma ta mi™e Abiy ya ce, ""Omar ku je tare, Jawad raka shi zai fi sakewa."" Jawad ya amsa yana mi™ ewa shima suka shiga ciki."

"˜aramin falon ba™i aka shigar dasu mai kyau madaidaici. Nayla ta kunna a.c bayan ta kunna hasken falon ta fita daga falon ita da Salma. A kitchen Salma take ce mata, ""Nayla don Allah ki nutsu, sai rawar jiki ki ke yi kina bayyana feeling Winki a fili."" Sai kawai ta rungume Salma ta fashe da kuka tana cewa, ""Salma Omar ne a gidan mu, Omar ne a zaune shaida Abina suna magana. Salma na kasa tantance adadin farin cikin da nake ji, ji nake kamar zuciyata zata buga saboda murna Salma. Omar Wina yana nan lafiya, Allah na gode maka, Allah na gode maka"" ta faWa cikin kuka sosai."

"Salma ta ce, ""to ki yi ha™uri ki bar kuka mu kai musu abincin in ya so sai mu yi magana."" Nayla ta Wago daga jikin Salma tana share hawaye ta ce, ""Salma ki yi addu'a Allah kar ya Wora miki soyayya irin wacce ya Wora min, akwai azaba ba kaWan ba Salma. Na kasa yin lafiya cikin kwanakin nan kuma duk saboda tunaninsa."" Tausayi ta bawa Salma matu™a, idon Salma ya kawo ruwa amma bata yi kuka ba ta daure ta yi mata shiru bata tanka mata ba."

"A haka suka zuba abincin a flaks, doya ce da ™wai da sauce sai dankalin turawa soyayaye da kuma soyayyen ™ wai. Ga farfesun naman rago da aka yi shi mai ruwa, sai shayi da manyan slice bread da gwangwanin madara da na milo da sugar."

A kan table suka ajjiye sannan Salma ta koma ta kawo ruwa da lemo masu shegen sanyi ta ajjiye. Didi ta kalli

"Nayla da take tsaye kana ganin ta ka san tayi kuka ta ce, ""Nayla jikin ne?."" Nayla ta kalli Didi ta ce, ""A'a Didi, kaina ne yake ciwo shiyasa."""

"""Sannu, Allah ya ™ara lafiya. Ki je asibiti a duba ki."" Kai kawai ta Waga dan ™irjinta ya yi mata mugun nauyi, ga Omar dai tana kallonsa amma kewarsa take ji kamar ta je ta rungume shi haka take ji."

"Shi kuwa Omar yana jin su amma baya Wagowa waya yake dubawa ba tare da yana yin wani abun a wayar ba. Fitar Salma da Nayla ya saka Didi ta ce, ""kai kuwa Omar ko sannu ai ka ce mata ko? Itace silar fitowar ka daga hannun Sen na faWa maka. Ko ya jiki ai ya kamata ka ce mata zata ji daWi."" Shiru ya yi bai ce komai ba, gabaWaya a takure yake jin kansa cikin jin nauyi wanda bai san dalilin faWuwar hakan ba."

"Salma da Nayla sun jima basu dawo ba har kusan mintina talatin kafin su dawo, Didi ce kawai ta sha tea amma shi ruwa kaWai ya sha bayan nan bai sake Waukar komai ba."

"Nayla ta kalli Didi ta ce, ""Didi har kin ci?."" Didi ta ce, ""na sha tea Nayla, in zan yi tafiya bana son cin abinci"

"wallahi."" Nayla tayi murmushi tana satar kallon Omar da ya ajjiye ruwan da ya sha a lokacin."

"""Yaushe zaki zo mana Kano?."" Nayla ta kalli Didi ta ce, ""ai sai bikinki, aiki ya saka ni a gaba ya hana ni zuwa ko ina. Ni dana sanin ma fara aikin nake yi wallahi."""

"Didi tayi dariya ta ce, ""Allah ya kaimu, ya taimaka miki."" Ta amsa da amin wajan ya yi shiru babu mai magana."

"Didi ce ta sake cewa, ""Salma an kaiwa driver abincin?."" Salma ta ce, ""na tabbatar ma ya cinye yanzu."" Didi ta yi murmushi suka sake yin shiru. ˜arar wayar Nayla ce ta katse shiru ta kalla ta ga Abbas ne ta kalli Salma ta ce, ""Yayanki ne."" Salma tayi dariya ta ce, ""yayan mu dai, kema ai yayanki ne. Baza ki Wauka ba?."" Nayla ta ce, ""ana babbakar giwa waye zai je ™aure zomo?."""

"Salma ta murmusa cikin tausayin ΄ar uwarta ta ce, ""Gaskiya ne."" Didi ta kalli Nayla ta ce, ""Nayla zan shiga ban Waki."" Salma ta ce, ""mu je na raka ki."" Didi ta mi™e ta fita ita da Salma aka bar Omar kawai da Nayla a zaune. Wani irin yarrr Nayla take ji a jikinta, gashi dai kamar bai san tana zaune ba amma wani irin suka zuciyar take yi ga farin ciki da yake mamaye zuciyarta. Ganin ba ita yake kallo ba kawai sai ta zuba masa ido tana kallon sa cikin shau™i ko ™ifta ido bata yi."

"Waya ta Wauka kamar tana dubawa tana yi masa video ta yadda bazai fahimta ba. Omar kuwa shi kansa wani iri yake ji, ya na kallon su har fitar su Didi ya kuma san tana zaune ita a falon. Wani iri yake ji a jikinsa kamar taS a zama da mace shi da ita kawai ba. Duk da dai akan Narma kawai ya faru amma sai yake jin wannan daban kamar bai taSa shiga irin yanayin da yake ji ba."

"Hannunsa ta kalla ta kuwa yi farin gani, domin azurfar da ta bashi tana sanye a Wan yatsansa na biyun ™arshe a hannun haggu. ""Wayyo Allah!."" Ta furta bata san ta ce ba saboda farin cikin da ya sake mamayeta. Jin abinda ta furta sai ya Wago ido yana kallonta a lokacin ta rufe ido ita kuma saboda tsananin farin ciki. Šauke kai ya yi ita kuma ta buWe ido, gabaWaya ta kasa sarrafa kanta ™iris take jira ta fita daga hankalinta"

"Didi da Salma ne suka dawo Didi ta kalle ta ganin sai murmushi take yi ita kaWai sai ta kalle shi taga babu alamun ma sun yi magana da ta san hali. Mamakin murmushin Nayla take yi saboda ta san tsoron Omar take ji, amma yanzu gashi an bar su su biyu tana ta murmushi mai kyau."

"Nayla ta kalle ta ta ce, ""Didi mu je Wakina ki kwanta ki huta."" Didi tayi dariya ta ce, ""Sallar azahar kawai zamu yi mu juya, kwanciyar me zanyi gashi har sha biyu da rabi tayi?."" Nayla ta ce, ""kai Didi, ni na Wauka sai yamma."" ""Gwara mu shiga Kano kafin duhu ya yi Nayla."" Nayla ta girgiza kai tana ta murmushi abin ta kamar sabon kamu. Omar dai baya magana Didi sai girmama hali irin na sa take yi, yazo har gidan su yarinya amma ya kasa ce mata ya jiki bayan a gabansa aka ce bata da lafiya."

"Salma ta ce, ""Didi mu je Wakin Nayla ki yi alwala ki yi sallah."" Didi ta amsa da to Nayla dai bata son tafita amma haka ta mi™e a lokacin Jawad ya shigo ya zauna yana Wan jan Omar da hira duk da bai sake ba. Nayla bata so barin wajan ba, haka suka shiga babban falon suka hau sama har Wakin Nayla."

"Didi girmama gata irin na Nayla take yi, musamman yadda Abiy ya ruWe akan ciwon ta ga kuma girman Waki kamar baza tayi aure ba. A nan suka yi sallar azahar suna ta hira da Didi, duk da ta lura Nayla bata cikin walwala dawowar su Wakin amma bata tambaya ba."

"Bayan an idar da sallama suka sakko suka haWu sa Mama ta bawa Didi kaya a leda sannan ta bata kuWi ta ce in ji Abiy ya ce su yi kuWin mai. Ta dinga yi mata godiya sosai, Nayla ta ri™e mata kayan ita da Salma suka fito har bakin motar."

"A tsaye suka tarar da Omar shida driver da alama su suke jira. Didi ta buWe motar sannan ta kalli Nayla ta ce, ""Nayla ba™o zai yi halin sa, Mun gode da karrmawa Allah ya bar zumunci."" Nayla ido ya ciki da hawaye ta ce, ""Amin Didi. Allah ya kiyaye hanya."" Salma ta ri™e hannunta tace, ""Nayla meye na kukan?."" Sai ga hawaye shar ya sakko mata, ta juya da sauri ta rungume Didi ta ce, ""bana so ku tafi Didi, don Allah ku kwana."" Omar da yake jin me cewa ya kalle ta yana mamaita su kwana, Lallai ma yarinyar bata da hankali."

"Didi ta ce, ""Nayla banda abin ki meye na kuka kuma? Ki yi ha™uri wata ran ai zan dawo in sha Allah."" Nayla ta"

"Wago daga jikinta ta ce, ""to Didi. Wallahi bana so ku tafi, ji nake kamar na bi ku."""

"""Ki yi ha™uri kin ji? Ai zaki zo Kano Win ko?."" Ta Waga kai kamar yarinyar ™arama Didi ta ce, ""to kin gani, ki yi ha™uri kar ki saka ni kuka nima."" Nayla ta goge ido ta ce, ""Allah ya sauke ku lafiya."""

"""Amin Nayla. Allah ya baki lafiya, ji ke ki ga likita gabaWaya kin canja kin rame kamar ba ke ba."""

"Nayla ta ce, ""to Didi zan je in sha Allah."" Didi ta shiga mota Salma ta ri™e Nayla ta ce, ""ki yi ha™uri ki ta addu'a, canji zai zo daga wajan Allah."""

"""Ina yi Salma, kema ki dinga yi min."""

"""Ina yi miki kullum Nayla, Allah ya sassauta miki. Ba dan ban cewa Daddy zan kwana ba ai da nayi zamana na W"

"ebe miki kewa. Amma zan dawo."" Ta Waga kai kawai tana kallo Salma ta shiga motar."

Kallon inda Omar yake tayi suka haWa ido dan kallon ta ya ke yi yana tunanin meyasa yake yawan ganinta tana

"kuka, shagwaSa ce ko sangarta ko rashin hankali?. Ganin sun haWa ido sai tayi murmushi idonta duk hawaye ta ce, ""Allah ya kiyaye hanya& .Yaya Omar!.."" Wani iri yaji a zuciyarsa, mace ta farko da ta taSa ce masa Yaya kenan a rayuwarsa. Sai yaji wani irin rauni da bugun zuciya, har lokacin kallon ta yake yi hawaye suna sakko mata daga idonta."

"Samun kansa ya yi da yin murmushi ya Waga kai ya ce, ""Amin, Mun gode"" daga haka ya buWe motar ya shiga. Ai Nayla suman tsaye tayi a wajan saboda gigicewa. Na farko murmushin da ya yi mata, na biyu maganar da ya yi, na uku godiyar da ya yi mata sai take ji kamar an yi mata babban albishir."

"Horn Win motar ne ya saka ta dawo hankalinta, ta share hawaye tana dariya tana kuka ta Waga musu hannu suka fita daga gidan ita kuma ta juya a sanyaye ta koma cikin gida.KRB2P012"

Arewabooks@nanahaleema11.

"Sai la'asar suka shiga Kano, Didi sai da ta shiga wajan Hajja ta bata labarin duk abinda ya faru har kayan da"

"Mama ta bata da kuma kuWin da Abiy ya bayar ta nuna mata. Hajja ta dinga murmushi dan ta san daman baza ta ji kunya ba dan Didi ta je gidan su Nayla ba, saboda kirkin Abiy da matar gidan. Dubu hamsin ta lissafa a dubu Wari biyun da Abiy ya bayar ta bawa Salma ta ce, ""Salma ga na saka data."" Salma tayi dariya ta ce, ""Haba Didi, wallahi bazan karSa ba, na gode sosai."""

"Didi da mamaki ta ce, ""Meyasa baza ki karSa ba?."""

"""Haba Didi, dan na raka ki sai kin bani kuWi? Wallahi bazan karSa ba."" Didi ta ce, ""to ki bawa Sayyadi driver Hajja ya saka kati."" Salma ta karSa ta ce, ""zan bashi in sha Allah."" Didi ta dinga godiya sannan ta tashi ta shiga gidan su."

Sallar la'asar tayi tare da yin wanka sannan ta dawo falo ta zauna. Yunwa take ji amma bata tunanin zata iya

"girki a gajiye take sosai. Baccin gajiya ne ya Wauketa sai kiran sallar magriba ne ya tashe ta. Mi™ewa tayi tana salati ta yi alwala ta dawo ta tayar da sallah, bayan ta idar ne ta iya tashi ta dafa musu indomie ta zuba a plate kenan ta fito falon ya shigo da sallama."

"Amsawa tayi sai ta bashi plate Win hannunta ta ce, ""tun Wazu na so nayi mana girki sai nayi baccin gajiya."" Kar Sa ya yi ya zauna ta koma ta Wauko ragowar da ta ajjiye masa ta dawo ta zauna ta fara ci kamar yadda yake ci shima. Sai da ta kusa cinyewa sannan ta tura masa ragowar kuWin da Abiy ya bayar ta ce, ""Mahaifin Nayla ya bada dubu Wari biyu ya ce mu zauna mai a mota, na bawa Salman Hajja dubu hamsin ta™i karSa, amma na ce ta bawa driver da ya kaimu shima ya siyi kati. Ga ragowar nan, ga kuma kayan da Mamanta ta bani. Lace ne da atampa sababbi da turaren wuta, humra da mayafi"" ta faWa tana nuna masa kayan akan kujera."

"Bai ce komai ba sai da ya kusa cinye indomie Win sannan ya ajjiye plate Win ya kalle ta ya ce, ""Didi baki kyauta min ba, abinda kin ka yi min sam ban ji daWi ba."" Didi da mamaki ta ce, ""me nayi maka?."""

"""Meyasa baki faWa min in za a ce waje irin wannan ana siyan abu a kai ba? Sai gani nayi kawai kin bada tsaraba ba tare kin faWa min ba. Shiyasa ake cewa ke ce kike Waukar Wawainiya ta bana yi miki komai."" Didi da mamaki ta ce, ""Omar da girman ka da komai sai na faWa maka? Baka san ya kamata ba dai?."""

"""Didi ban sani ba, ban sani ba. Bani da mahaifiyar da zata faWa min abinda ya kamata da wanda bai kamata ba. Ban ji a raina ya kamata ace na siyi wani abu na kai ba saboda ban saba zuwa ba, ban taSa yiwa wani godiya a duniya ba daga shi sai Hajja. Da nake zaune a gabansa ji nake kamar ana Waure ni, ban taSa jin nauyi da girman mutum a idanuna kamar yadda na ji na shi ba. Na ji na kasa haWa ido dashi balle na yi magana, a karo na farko a rayuwata da naji girma da nauyin wani mutum, duk na Wauki hakan a rashin sabo saboda ban taSa zuwa wajan wani da sunan godiya ba. Meyesa kafin mu tafi baki faWa min ana siyan abu a kai ba?."""

"Didi kallon sa take yi har ya kai ™arshe ganin da gaske yake maganar sannan ta ce, ""shikenan naji laifina ne ban"

"faWa maka ba, nan gaba sai ka aikata ba tare da an faWa maka ba. Kuma in na siya kamar ka siya ne ai."" Omar ya ce, ""ni dai ban ji daWi ba, da kin faWa min da ko wani abun an siya an haWa an ka. Da kin faWa min da ni zan bada kuWin abinda zaki yi."" Didi ta ce, ""shikenan ai ya wuce."""

"Ajiyar zuciya ya yi ya ce, ""Nawa ki ka kashe?."""

"""Gurasa ce fa ta dubu goma ba wani abun ba."" Hannu ya saka a aljihu ya Wauko dubu bakwai ya ajjiye mata ya ce, ""ga kuWin da ki ka kashe. Sannan ki haWa da wannan ma ki ri™e hidima ce a gabanki"" ya faWa yana nuna mata wanda ta turo masa kusa dashi. Didi tayi murmushi ta ce, ""to na gode."""

"Wayar Didi ce ta katse masa maganar da ta yi niyar yi, ta duba taga Nayla ce sai ta saka a speaker daga can S angaren Nayla ta ce, ""Didi ina fatan kin sauka lafiya, Ina ta kiran ki Wazu baki Wauka ba."" Didi ta ce, ""mun sauka lafiya lau Nayla. Bacci nayi shiyasa baki same ni ba. Ya jikin naki?."""

"""Jiki da sau™i Didi."""

"""Kin daina kukan?."" Nayla ta Wan murmushi ta ce, ""Didi na daina"" ta faWa a sanyaye. Didi ta ce, ""ai gwara da ki ka daina, gabaWaya duk na damu wallahi:"""

"³ar dariya tayi ta ce, ""An gode Didi, na ji daWin zuwan ku sosai."" Didi ta ce, ""mu ne da godiya Nayla. Yadda aka karSe mu a gidan ku wallahi ya fi min komai daWi."""

"""Babu komai Didi. A gaishe da Yaya Omar"" ta faWa a rabe muryarta har rawa take yi. Didi tayi murmushi ta"

"kalli Omar da yake suraren su ta ce, ""Yaya Omar yana jinki."" Nayla tayi murmushi ta ce, ""na san bazai yi magana ba, amma ki ce ina yi masa bangajiya mun gode sosai."""

"Didi ta ce, ""to Nayla, mun gode da tarba mai kyau Allah ya ™arawa Abiy tsahon rai."" Nayla ta amsa da amin tayi shiru ko Omar zai yi magana amma bai ce komai ba dole ta yanke wayar. Murmushi Didi tayi bayan ta kashe wayar ta ce, ""Wai Yaya Omar, Nayla akwai ta da bin dariya. Ko yaushe ya zama Yaya Win oho mata."""

"""Ban cancanci ace min Yayan bane shiyasa har sunan ya baki dariya?."" Da mamaki ta kalle shi dan bata Wauka zai yi magana ba, sanin halin sa ba tankawa zai yi ba musamman Nayla da yake yawan faWar haushinta yake ji."

"Didi ta sake yin dariya ta ce, ""A'a ni ban ce ba Malam Omar, meye nawa na cewa baka cancanta ba? Kawai na"

"san haushinta ka ke ji ne."" Bai yi magana ba ya share ta Didi ta ce, ""anyi kiran sallar i'sha, sallah zan yi"" ta faWa tana tashi ta shiga ciki ya bita da kallo."

"Yaya Omar Win da Nayla ta faWa a lokacin da zasu bar gidan su da yadda hawaye yake zuba a idonta kawai ya tuna, ajiyar zuciya ya yi ya rufe ido sai kuma Narma ta faWo zuciyarsa itama lokacin da take kuka lokacin da ta je wajansa. Tashi ya yi ya bar falon zuciyarsa cike da tunani kala-kala."

Bayan Kwana biyu.

"Bikin Didi ya matso sosai an kai lefe gidan Kawu akwatina goma sha huWu kaya masu yawa sosai. Baba Adamu kamar yadda ya ce an gama zuba komai na gidan Didi, hatta kayan kitchen ya zuba sai abinda Didi ta siya ta ajjiye aka kai can. Gida ne babba da falo biyu da bedroom uku, sai dai unguwar babu jama'a sosai amma gida kan ya yi kyau sosai."

"Didi ana ta yi mata gyaran jiki duk da ita kaWai take yi komai, sai Hajja da Salma da suke taimaka mata dan bata da wani dangi da yake taimakon ta tunda ba sabawa suka yi sosai ba. Har gwara Umma Sarood ™anwar mahaifiyarta ta kawo mata turaren wuta irin nasu na mutanen Chad, har kayan gyaran jiki ta haWo ta kawo mata. Mama Zainab Yayar mahaifiyarta ita kuma ta Wau™i nauyin zuba turaren wutar gidan, ta ce duk wani abu indai na ™hamshi ne ita zata yi amma bata so Omar ya sani. Didi ta ji daWi sosai har ta nuna musu, kuma suna yawan kiranta su ji shirin biki, zuwa ne dai basa yi saboda haWuwa da Omar baya zama alkhairi. Duk wani shiri ita da Hajja ake yi sai Salma da ta kasance tana tare da Hajja ko yaushe."

"angaren Omar ya watsar da duk wani abu da yake yi a baya, duk da daman ya jima da watsarwa amma yanzu yana ™o™arin ganin ko cikin ΄an uwansa ΄an daba na baya ya daina shiga. Ya tattara kayan sana'ar da yake so ya fara kawai yake yi, shida yaran sa su uku gabaWaya sun bashi haWin kai wajan yin sana'ar da suke fatan zata kai su inda basu yi tunani ba. Duk abinda ake saka shi a ciki a Sangaren daba yanzu an daina, ko an zo masa da maganar zai ce babu ruwansa a kai maganar gaban hukuma. Duk da hakan dai ba a kawo masa wargi saboda lasar yaji baya hana gyaWa yin garWi, duk da haka akwai sauran tsoro da kwarjinin da yake dashi a wajan mutanen gari. Halayyarsa baby abinda ya canja, baya shiga harkar kowa kuma baya sauraren kowa, fuskarsa kullum a haWe magana ma ba ya yi."

"Lamarin Narma ya ajjiye a gefe, duk da yana tunawa musmaman yadda abubuwa suka faru a gidan su, kuma"

"yana matu™ar tausayinta in yaga tarin messages da kiran da take yi masa baya Wauka. Wani messages Win ya karanta kamar ya yi mata kuka haka yake ji dalilin da ya saka ya daina buWewa gabaWaya, dan in yana buWewa

Please Login or Register in order to submit comment