ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce, ""Senator daman akwai maganar da zamu yi da kai."" Sen ya ce, ""Ina"

"ji."" Abiy ya ce, ""Akwai wani yaro Omar da ka kama ya je Abuja gidan ka haka ne?."""

"Sen ya Waure fuska yanayin sa ya canja lokaci guda ya ce, ""Haka ne."" Abiy ya ce, ""Ina neman alfarma ka taimaka ka bani shi."" Sen ya kalli Abiy ya ce, ""ka san abinda ya aikata min kuwa? Narma fa ya je har gida ya ce yana so yana kallo na ina kallon sa."" Abiy ya ce, ""na sani, naji labarin komai. Ya yi tsaurin ido sosai bai kuma kyauta ba, amma kaima matsayin ka na babban Wan siyasa ajjiye a wani waje ana azabtar dashi hakan bai kamace ka ba."""

"Sen ya ce, ""Babu yadda na iya ne, ina so a koya masa hankali shiyasa na aikata hakan. Na so na tura shi prison"

"kawai na ™yale shi ne."""

"""Amma abinda kayi a yanzu zai iya taSa maka siyasarka, da zarar maganar ta fita shikenan za a dinga yaWawa ana faWar ™arya da gaskiya. Ka fini sanin meye siyasa, ka san yadda ™aramin abu yake zama babba, ka san yadda ™aramar magana take zama babba a gare ku."""

"Sen ya yi ajiyar zuciya ya kalli sauran ya basu labarin Omar kaf har zuwan Narma Kano da komai ya faWa musu, kana ya ce, ""in ban saka an killace shi an wula™anta shi ba ta ya zai fahimci ya yi kuskure?."""

"Mai girma gwamnan jahar Katsina kuma mahaifi ga Ashraf ya ce, ""hakan ya yi, amma da ka sani baka saka ana"

"wahalar da shi ba gaskiya, kai ka faWa mana tasiri da ya yi maka a lokacin zaSe, baka ganin zai zama tasiri nan gaba wajan lalata komai?."" Senator ya yi shiru yana tunani kafin ya ce, ""shiyasa zan san abinda zan yi a kai shi kotu a yanke masa hukuncin da bazai fito ba har abada."""

"""Wannan ba shawara ce mai kyau ba, kafi kowa sanin meye siyasa da yadda harkokinta suke gudana"" Abiy ya faWa yana kallon sa."

"Senator ya ce, ""asiri ya yi mata, in ba haka ba tana matu™ar son Ashraf, rana tsaka ta daina wai shi take so."" Abiy ya yi dariya ya ce, ""babu wani zancen asiri ni a ganina gaskiya, kawai tasirin soyayyar ne ba komai ba. Kuma yanzu ai komai ya wuce tunda ka tura ta london, a shawarata kawai ka aura mata Ashraf Win ya bita can su zauna a hankali zata manta dasahi."""

"Mahaifin Ashraf ya ce, ""Abinda zan ce kenan, tunda ka ce ka tura ta Londan ayi auren au sai Ashraf Win ya bita can. Su samu good one year basa ™asar nan, in suka dawo sai ayi biki tunda babu wanda ya san ma sun yi aure. Amma barin sa a kulle ana wahalar dashi zai iya taSa ka nan gaba wallahi. In ΄an uwansa suka shiga gidajen ya Wa labarai suna cewa dan ya ce yana ΄arka ka yi masa haka ka yi tunanin maganar da zaka jawo."" Wajan ya rabu biyu, Abiy da mahaifin Ashraf suna ganin ri™e omar bai kamata, ba sauran suna ganin hakan shine daidai."

"Senator ya kalli Abiy ya ce, ""A ina ka san shi?."" Abiy ya ce, ""Unguwar su a nan kakar Nayla take mahaifiyar"

"Bilkisu matata da ta rasu. Shekaru kusan goma baya an taSa yun™urin yiwa Nayla fyaWe, shine ya kuSutar da ita har aka yi ™o™arin kai shi prison saboda ya zubarwa da yaron jini aka ce ya Wauki doka a hannunsa, ni na san yadda akayi dai bai je prison ba. Yayarsa sun saba da Nayla sosai, halin da take ciki shine ya tashi hankalin Nayla tazo tana yi min kuka, kuma ko bata zo ba nayi niyar bin maganar saboda na rama alkhairin da ya yi min da alkhairi. Ina neman alfarma ayi masa afuwa bazai sake wannan gangancin ba."""

"Sen ya yi ajiyar zuciya ya kalli Abiy ya ce, ""kuma ka tabbatar itama ba asirin ya yi mata ba?."" Abiy ya yi dariya"

"mai sauti ya ce, ""babu asirin da ya yiwa Narma ma balle Nayla ta shigo ciki, Babu abinda ya yi musu. Kuma ni dan ina bibiyar good background da good manners a aure ne, da ace yana dasu tsaf zan ce ka bawa Narma shi Win. Ai kana da arzu™in da zaka iya sakawa ya tashi daga nobody to somebody."""

"Sen ya taSe fuska ya ce, ""Allah ya kiyaye, Jahili ne fa ko secondary school bai gama ba. Ina zai iya kaiwa a rayuwa babu ilimi?."" Abiy ya ce , ""ni dai ayi min alfarma a bani shi."" Sen ya yi shiru yana tunani, bazai iya ™in yiwa Abiy alfarma ba saboda mutuncin da yake tsakanin su. Amma in ya tuna wula™ancin da Omar ya yi masa"

sai yaji bazai iya bada shi ba.

"Senator ya ce, ""Shikenan, za a ™yale shi gobe. Amma saboda kai ne kawai babu yadda zan yi maka, amma wallahi da sai ya ™are rayuwarsa haka."" Abiy ya yi dariya ya ce, ""godiya nake mai girma Senator kuma sirikin Gov, future Kano state gov in sha Allah."" Dariya suka yi aka share zancen suka cigaba da hira har bayan sallar la'asar kafin kowa ya watse."

"Kasancewar ranar ne dinner Win Shayida su Nayla suna gida su ukun a falo suna ta jan Nayla da hira amma ta kasa sakewa. Abiy ne ya shigo falon duk suka mi™e tsaye ya kalle su da murmushi suka gaishe shi ya amsa kafin ya kalli Nayla ya ce, ""Mamana kina lafiya kuwa?."" Nayla ta ce, ""lafiya lau Abiy, ciwon kai ne tun na jiya har yanzu."""

"""Kwana biyu ciwon kai yana damunki sosai, ki je asibiti mana."""

"""Wallahi stress ne aiki na kawai Abiy, da nayi bacci na tashi sai na dawo daidai."""

"Abiy ya yi dariya ya ce, ""kaga sabuwar ma'aikaciya."" Tayi dariya Abiy ya zauna yana cewa, ""™arfe nawa zaku tafi Kaduna gobe? Ni sai jibi monday zan dawo in sha Allah ."" Nayla ta ce, ""Duk lokacin ka ce Abiy."""

"""Saboda aikinki dole a koma gobe gaskiya, zamu gani zuwa azahar sai ku tafi in Allah ya kaimu."""

"Bata yi magana ba ya kalle ta ya ce, ""Maganar Wan daban yaron nan."" Ai da sauri ta Wago tana kallonsa a lokacin Mama tazo ta zauna a wajan. Abiy ya ce, ""Mun yi magana da Senator..."" ya faWa yana duba waya wacce sa™on text ya shigo. Shiru ya yi bai yi magana ba yana duba wayar. Nayla ji take kamar ta ™wace wayar daga hannunsa saboda ya kai ga faWa mata abinda zai ce."

"Abiy ya ajjiye wayar ya ce, ""mun yi magana ya kuma amince zai ™yale shi, gobe ma ya ce zai sake shi ya dawo gida in sha Allah."" Wata irin ajiyar doguwar zuciya Nayla tayi, ta lumshe idanu tana jin wani irin daWi na ratsa zuciyarta. Abiy ya bita da kallon mamaki ganin yadda farin ciki ya bayyana a tare da ita kamar itace Yayar ta sa. A hankali ta buWe ido suka haWa ido da Abiy da yake kallonta, da sauri ta sunkuyar da kai amma murmushi take yi. Abiy ya ce, ""ko dai kema ™anwarsa ce ne Nayla? Wannan ajiyar zuciya haka kamar Jawad aka kama za a saki?."""

"Murmushin ya™e tayi ta ce, ""Abiy kawai Ina murna ne in na tuna yadda Didi zata yi murna."" Abiy ya zuba mata ido yana binta da kallon tuhuma kafin ya ce, ""kin tabbata?."" Sai taji tsoro ya shige ta da tunanin Allah yasa bai gane wani abun ba. Ta sake sunkuyar da kai tace, ""Eh Abiy."""

"""To ya yi. Ki sanar mata gobe zai dawo in sha Allah."" Da farin ciki ta amsa shi kuma ya tashi ya shiga ciki Mama"

"ma tabi bayansa. Nayla na shiga Waki sai gata ta fito da key Win motar Mama, Salma da Jidda suka kalle ta kafin su magana ta ce, ""Gidan Hajja zan je, in zaku je kuzo mu tafi."" Salma ta karSi key Win hannunta tace, ""bani baza ki sake ™o™arin kashe mu ba."" Bata ma ji ba tayi gaba burinta kawai taje ta faWawa Didi. Salma ce ta ja motar suka tafi gidan Hajja."

"Nayla na shiga ta tarar da Didi ita da AbdulHamid suna tsaye da alama sallama yake yi mata. A guje ta faWa jikin Didi ta ce, ""Didi Abiy ya yi magana da Senator ya tabbatar masa da gobe zai dawo, gobe zai dawo Didi"" ta faWa da murna sosai. Didi cikin farin ciki ta ce, ""da gaske ki ke? Da gaske ki ke Nayla?."""

"""Da gaske nake Didi."" Didi ta ce, ""Alhamdulillah! Allah na gode maka, Allah na gode maka"" ta faWa tana sake rungume Nayla da take dara saboda murna."

"""Na gode Nayla, na gode Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya baki miji na gari."" Ciki suka shiga dan Didi ta"

"manta da AbdulHamid da yake wajan. Sai da suka shiga falon Hajja Salma ta ce, ""Amin Didi. Dan wallahi itace jiya ta samu Abiy tana kuka kamar zata mutu saboda a fito da Omar, yadda muka bar gidan nan jiya baki ga gudun da ta dinga yi damu a mota ba saboda kawai take ta samu Abiy. Cikin ikon Allah tana faWawa masa ya kira shi a waya ya Wauka, yau suka haWu ya yi masa maganar ya kuma amince"" Salma ta faWa tana kallon Didin"

da ta san aikin Nayla ne yadda ko Omar Win ya fito ya san ita tayi masa hanya ya fito.

"Didi ta sake ri™e Nayla tana godiya tana hawaye tana cewa, ""na gode Nayla, Allah ya bani abinda zan saka miki Nayla. Na gode sosai."" Hajja ta ce, ""itama ai ta saka alkhairin da ya yi mata ne Aisha, kin manta abinda ya yi mata?."" Didi ta ce, ""ban manta ba Hajja, amma wannan taimakon da tayi min ai baza ki haWa shi da wancan ba. Ta ceci rayuwata ta ceci ta Omar, bani da abinda zan saka mata saka addu'a."""

"Hajja tayi dariya dan ko ita ta ji daWin labarin dawowar Omar. Didi ta ce, ""Nayla mu je na yiwa Abiy godiya, mu je yanzu in yana gida."" Hajja ta ce, ""A'a Aisha, ki bari ya dawo sai ku je ku same shi tare."" Didi ta ce, ""Amma ya kamata na je yanzu kafin ya dawo ko?."" Nayla ta ce, ""to sai mu je in anjima, ko kuma ki yi masa waya."""

"A nan suka baje ana ta hira da nishaWi Didi ji take kamar ta mayar da Nayla ciki saboda son da take yi mata. Sai bayan i'sha suka tafi saboda dinner da zasu je, tare da Didi aka je ta yiwa Abiy godiya ya ce babu komai. Drivern Hajja ne ya dawo da Didi su kuma suka fara shirin dinner. Ko a wajan dinner kowa ya lura da walwalar da Nayla take yi, su dai su Salma fatan samun sasssuci akan abinda yake damunta suke yi mata."

"Washe gari ranar lahadi ™arfe goma na safe ta fita daga gida zuwa gidan Hajja. Ta samu Didi ma bata nan ta shiga gida tana aikace-aikace Saboda dawowar Omaar. Salma ce ta shigo tana cewa, ""shine ko ki jira ni kika taho bayan kin san Jidda tana gidan ta."" Nayla ta ce, ""to ba gashi kin zo ba. Matsa min naje gidan Didi."" Salma ta ce, ""ba da wuri Abiy ya ce zaku koma ba ne? Yana ta faWa ya ce kin san zaku tafi Kaduna ki ka fito yawo."" ""Kin ga Ina zuwa"" ta faWa tana fita ta shiga gidan Didi Salma na biye da ita."

"Lokacin da suka shiga Didi share Wakin Omar take yi, jin sallamar Nayla ya saka Didi ta ce, ""Nayla gani nan, shigo."" Nayla gabanta ya faWi matu™a, ta kalli Salma da take tsaye sai Salma tayi tsaki ta shiga Wakin."

"Nayla ta shiga Wakin a sanyaye da sallama gabanta yana faWuwa, Waki ne babba mai girma dan yafi na Didi girma. Babu tarkace a Wakin babbar katifa ce mai girma da tudu, sai wardrobe mai guda shida a gefe, sai mirror mai irin wardrobe Win a gefe wanda abubuwan da suke kansa basu wuce guda biyar ba."

"Didi ganin Nayla sai ta yi murmushi ta ce, ""Nayla har kin fito?."""

"""Wallahi na fito Didi. Kin san fa yau zamu wuce Kaduna."" Didi ta ce, ""wallahi duk sanda ki ka zo bana so ki dinga zancen zaki koma Kaduna Win nan, bana jin daWi ko kaWan.."" Nayla tayi dariya tana cigaba da kallon W akin da sai ™hamshi turare yake yi mai sanyi."

"Didi ta ce, ""Ina gyara Wakin mutumin naki, in ba haka ba in yazo da faWa zamu fara kin san baya ™aunar ™ura ko kaWan. Zai iya zama wajan da aka zubar da kaya amma bazai iya zama a waje mai ™ura ba. Shiyasa yake gyara Wakinsa ko yaushe, dan shi baya jin gyaran Waki."" Salma ta girgiza kai ta ce, ""Ga Wakin nan tsaf dashi kamar ba na maza ba, har so nake na shigo dan naga ™azantar da take ciki ashe Wan gayu ne."""

"Didi ta yi dariya ta ce, ""Ai baya shiri da waje kaca-kaca, kinga tsintsiyarsa a ajjiye ga dustbin"""

"Didi ta faWa tana nunawa Salma amma Nayla ce ke gani. Salma ta ce, ""shikenan ya huta, ko ya yi aure babu ruwansa da sai an gyara masa Waki."""

Nayla sai murmushi take yi tana kallon Wakin tana jin farin ciki a zuciyarta. Fita suka yi zuwa falon Didi bayan ta gama gyarawa har da fesa airfreshner. A falon suka zauna suna ta hira Nayla sai kallon ™ofa take yi amma babu alamun Omar ko kaWan.

"Duk ta damu ga rana tana yi lokacin tafiyar su yana gabatowa. Suna zaune har azahar tayi Omaar bai dawo ba,"

"a lokacin kiran Abiy ya shigo wayarta tana Wauka bai jima yana magana ba ya kashe, Nayla ta kalli Salma da Didi ta ce, ""Didi zan je gida zan haWa kayana zan wuce, sai dai na ce sai na dawo wani lokaci. Wata™ila ma sai bikinki"" ta faWa tana kallon Didi."

"Didi ta ce, ""tafiyar ta tashi?."""

"""Wallahi Abiy yace na zo zamu tafi."""

"""Na so kun haWu da Omar kafin ki tafi gashi bai dawo ba har yanzu. Amma zamu zo Kaduna tare dashi mu sake yiwa Abiy godiya sha Allah."" Nayla ta yi murmushi ya ce, ""Allah ya kawo ku. Salma zo mu je"" tare suka fito Didi tana ta yi mata godiya har sai da Nayla ya nuna bata so sannan ta daina suka shiga gidan Hajja. A harabar gidan Hajja ta kalli Salma ta ce, ""Salma don Allah ki zauna da Didi in ya dawo ki yi min video ki tura min kin ji?."""

"Yadda tayi maganar sai ta bawa Salma tausayi a sanyaye ta ce, ""in sha Allah zan yi miki, kar ki damu."""

"""Na gode ΄ar uwa."" Daga haka suka shiga wajan Hajja tayi mata sallama a gaggaucs saboda kiran Abiy da yake shigowa wayarta. Ta Wauki motar da ta zo da ita ta bar unguwar zuciyarta duk babu daWin rashin ganin masoyinta.KRB2P008"

Arewabooks@nanahaleema11.

Didi da Salma tun suna zaman jiran dawowa Omar har suka gaji da zama suka koma gidan Hajja. A can suke

"zaune har akayi sallar magriba babu alamun Omar. Didi a lokacin ta yi ajiyar zuciya a sanyaye ta ce, ""wata™ila bai amince ya sake shi ba ne, wata™ila kuma Omar Win ne ya yi taurin kai ko ya faWi wata magana mara daWi."" Hajja ta ce, ""ki ta addu'a zai dawo, tunda Abdullahi ya ce zai dawo na tabbatar zai dawo kar ki damu."""

"""Assalamu alaikum!"" aka faWa a ciki ba tare da sallamar ta fito sosai ba tare da shigowa cikin falon. GabaWaya suka juya ga wanda ya shigo suna kallon sa."

"Didi wara idanu tayi ganin Oamar Winta a tsaye yana kallonta, sai ta zabura ta mi™e ta ™arasa inda yake ta ri™e hannunsa ta ce, ""Omar kai ne?."" Kai ya Waga mata ya ce, ""eh Didi, ni ne."" Ajiyar zuciya ta yi ta ce, ""Alhamdu lillah! Allah na gode maka, Allah na gode maka da ka dawo min da Omar cikin ™oshin lafiya."""

"Duk ta ruWe tana addu'a kamar wacce bata cikin hankalinta, ganin hakan sai ya dafa kafaWarta muryarsa a sha™ e ya ce, ""Didi ki nutsu mana."" Didi ta ce, ""na kasa nutsuwa Omar, na kasa. Farin cikin dawowarka ba zai bar ni na nutsuwa ba."" Sai a sannan ya kalli Hajja da take kallonsa ya ce, ""Ina yini."""

"Hajja ta ce, ""daga nan? Baza ka shigo ka zauna ba?."" Didi ta ri™o hannunsa zuwa cikin falon ya tako da™yar dan baya jin daWi gabaWaya. Zama ya yi Hajja ta kalle shi ta ce, ""Barka Omar, Ina fatan komai lafiya ko?."" Kai ya W aga kawai bai ce komai ba dan maganar ma wahala take masa, ya kalli Didi da take kuka ya ce, ""meye na kukan kuma Didi? Ba dai gani na dawo ba? In kina kuka bazan ji daWi ba."""

"Saurin goge ido tayi ta ce, ""na daina Omar, farin cikin ganin ka ne ya saka haka nake kuka amma na daina."""

"Hajja ta yi murmushi tana kallon sa, abinda ya bata mamaki tsaf dashi baza ka ce ya fito daga wahala ba. Duk da ya rame sosai fuskar sa ta Wan yi duhu amma shigarsa da yanayinsa gabaWaya bai nuna haka ba. Yadda ta ce gashin fuskarsa ya taru yanzu duk an rage sai wanda ya saba bari abin ya bawa Hajja mamaki."

"Didi ta kalle shi ta ce, ""Ka yiwa Hajja godiya, ta silar Hajja da Nayla ka dawo gida yau. Mahaifin Nayla shine ya"

"saka aka dawo da kai gida."" Hajja ta katse ta ta ce, ""Aisha ki bar shi ya huta tukunna, yana bu™atar hutu sosai. Ku je gida ya huta maganar ta biyo baya."" Kamar jira yake ya mi™e dan daman bai so shigowa ba, kawai dan Bashir ya ce masa tana ciki ne ya saka shi ya shiga. Hajja ya kalla ya ce, ""Sai da safe."""

"""Allah ya tashe mu lafiya Omar"" ta faWa da murmushi tana kallon sa."

"Fita ya yi Didi ta dawo kusa da Hajja ta ce, ""na gode Hajja, na gode Allah ya biya ki da aljanna. Duk ta dalilinki"

"Omar ya fito, ta dalilinki ne Hajja. Allah ya sa aljanna ce makomarki."" Hajja da Salma suka amsa da amin Hajja ta ce, ""kar ki damu Aisha ai a riga an zama Waya, kallon jikata nake yi miki kamar Nayla da su Salma, Kar ki damu ki kwantar da hankalinki. Ki shiga kitchen ki Wauki abinci a nan ki kai masa ya ci ya huta, in zai je ganin likita ma aje a duba shi ya dawo hankalinsa kamar da."""

"Didi ta ce, ""to Hajja. Amma na so Nayla tana nan ya dawo, ban san dame zan sakawa Nayla abinda tayi min ba"

"Hajja."" Hajja tayi murmushi ta ce, ""kin san bashi da uwa sai ke Aisha, ki tashi ki je ki bashi abinci ya huta sai mu yi magan."" Da to ta amsa ta tashi taje ta Wauki abinci a kitchen Win Hajja, ta Wauki hijjabi da wayarta ta fita daga gidan cikin farin ciki."

"Hajja tayi murmushi bayan ta fita ta ce, ""Allah sarki Hauwa'u sarki tausayi, sai da ta san yadda tayi mahaifinta"

"ya fito da Omaar. Allah ya biyata."" Salma ta amsa da amin tana kallon video da ta yi a zuwan Omar tana tunanin ta tura mata ko ta share ta kawai. Kiran Nayla ne ya saka shigowa wayarta, daga tafiyarta zuwa yanzu sau goma sha bakwai kenan tana kiranta, Salma"

tayi tsaki ta mi™e ta shiga Waki.

"Didi da ta fita a tsaye a ™ofar gidan ta ga Omar shida mutane sa, da hanzari ta ™arasa ta buWe gidan ta manta a rufe gidan ya ke. Sai da ta Wan jima da shiga sannan ya shigo falon tana kallon sa har ya ™araso. Ta ce, ""™anina ga abinci kazo ka ci sai ka kwanta ka huta ko?."" Omar ya zauna ya ce, ""na ™oshi Didi, na ci abinci magani kawai zan sha na kwanta."""

"""Sannu"" ta furta a sanyaye tana kallon sa. Kawai ya Waga kawai bai ce komai ba."

"Didi ta ce, ""na ganka tsaf ba kamar lokacin da naje na same ka ba."" Omar ya ce, ""ban shigo cikin gari ba sai da"

"na tabbatar na dawo nutsuwata. Da aka bani wayata sai na kira su Bash suka same ni a wajan gari, har asibiti mun je a ™ara min ruwa an kuma bani magani. Wannan dalilin ne ya saka na jima ban shigo ba sai yanzu."" Didi ta ce, ""gwara da ka yi hakan ko dan saboda ΄an gulma. Amma ka rame sosai Omar, kuma ka yi duhu."" Bai ce komai ba ta sake kallon sa ta ce, ""to ka sha maganin kafin kwanta sai ka fi jin daWin bacci."""

"Kallon ta ya yi da kulawa ya ce, ""kema kin rame Didi, baki da lafiya ne?."""

"""Lafiya lau nake Omaar, rashin ka ne kawai ya kawo hakan."" Šan murmushi ya yi ya ce, ""Sai ka ce in ina na nan Win ba faWa muke yi ba."" Didi ta yi ΄ar dariya ta ce, ""Ko doke-doke muke yi ™arewar faWa ba."" Murmushi ya sake yi ya ce, ""Kar ki damu yanzu na dawo ai."""

"Kafin ta yi magana ya ce, ""an ce a gidan Hajja ki ke kwana ko?."""

"""Eh Omar, hana ni kwana anan tayi ta ce na koma gidan ta saboda mutane."" Kai ya girgiza da yayi masa nauyi bai sake magana ba. Dauriya kawai yake yi yana magana saboda ita, amma kansa ciwo yake yi sosai."

"Mi™ewa ya yi sai ya yi kamar zai fadi ta zabura ta mi™e tana kallonsa, Omar ganin yadda ta zabura sai ya dake ya ce, ""kar ki damu ba wani abun bane, kaina ne yake ciwo kaWan."" Har Waki sai da ta raka shi ta tabbatar yana cikin ™oshin lafiya sannan ta fito ta shiga nata Wakin tana tunanin dame ya kamata ta sakawa Nayla alkhairin da tayi mata?."

Washe gari.

"Ya ji sau™in jikinsa babu laifi ya daure bai kwanta ba saboda kar hankalin Didi ya tashi, hakan ya saka shi ya fito ya samu tana ta aikace-aikace kamar kullum. Tana ganinsa ta dakata ta ce, ""ka fito? Ya jikin na ka?."" Šan lumshe ido ya yi ya buWe, da zai iya faWa mata gaskiya da ya ce mata babu sau™i dan ciwon kan bai rabu dashi ba, ga jikinsa gabaWaya babu ™arfi, ga ciwo da duk gaSoSin jikinsa suke masa. Amma da yake baya so ya sakata a damuwa sai ya ce, ""na ji sau™i. Kawai bana jin ™arfi ne sosai."""

"Didi ta ce, ""Sannu. Zauna na kawo maka shayi ka sha zaka ji daWi."" Zaman ya yi kamar yadda ta ce ta kawo masa shayi ya karSa tana yi mata sannu. Zama tayi a nesa dashi tana kallon sa ta ce, ""sannu Omar."" Kai ya Wan Waga kaWan yana shan shayin a hankali ba dan yana jin daWinsa ba sai dan saboda ita Win."

"Shiru ya ratsa tsakani, tayi shiru shima ya yi shiru yana shan tea a hankali yana kallon wani wajan daban. Didi"

"ta ce, ""in ka warware ina so zamu je Kaduna gidan mahaifin Nayla mu yi masa godiya. Shi ne ya yi magana da"

"Sen ya rabu da kai Omar, ΄arsa Nayla ce taje tana kuka ta ce don Allah ya yi wani abun ka fito."" Omar ya kalle ta ya ce, ""to"" ya amsa a ta™aice dan baya son doguwar magana."

Ido ta ga ya lumshe ya ajjiye kofin hannunsa ta bishi da kallo kafin ta mi™e ta ™yale shi

Please Login or Register in order to submit comment