ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da an gama aikin nan a daren nan, kar wanda ya biyo ni."" Goje ya ce, ""Amma Damisa zuwan mu yana da mahimmaci."""

"""Kar wanda ya biyo ni!"" ya faWa yana nuna su da yatsa tare fita kai tsaye ya nufi gidan."

"Nayla tana kwance a Waki ta ji wata ™ara mai ™arfi da hanzari ta mi™e zaune tana raba idanu, ta sake jin ™a™ar alamun ana ™o™arin buWe gate Win gidan da ™arfin gaske. Gabanta ya faWi ta dafe ™irji ta ce, ""Lafiya ake dukan gate Win nan haka? Kai ashe na manta ban kulle ba"" ta faWa tana mi™ewa da™yar saboda ciwon kai ta fito a hankali kamar munafuka."

"Tana zuwa falon aka sake dukan ™ofar da ™arfin har lock Win ya cire tunda iya shi kaWai ne a jiki bata saka key ta kulle ba. Shigowar mutane take ji ana cewa, ""Wallahi yau ko shi ko matarsa sai Waya ya ba™unci lahira. Ya yi silar zuwa mu prison shi ya zo yana zaune ya ma yi aure yana jin daWin rayuwa, na rantse da Allah bai isa ba yau sai ya ba™unci lahira."" Nayla ta zaro ido gabanta ya faWi jikinta ya hau rawa a lokacin ta ji ana taSa ™ofar falon. Tsalle tayi ta koma da baya cikin matu™ar tsoro ta gudu ciki ta shiga Waki ta shige can ™arshe jikinta na matu™ar rawa tana hawaye."

Motsi da ta ji a Wakin ne ya saka ta Wagowa a razane ™irjinta ya buga ta sake zabura cikin tsananin tsoro kamar wacce ta zauce.KRB3P011

"Nayla a gigice take matu™a hakan ya saka suna haWa ido da Omar da ya shigo Wakin a karo na farko ta diro daga kan gadon a hanzarce, cikin sacannin da bai wuce biyu ba ta zo inda yake ta ri™e shi jikinta na rawa tana faWin,  Tsoro nake ji, tsoro nake ji ka taimaka min zasu kashe ni. Yadda jikinta yake rawa zai tabbatar da gaske a tsorace take bata cikin nutsuwarta. Ta ri™e masa riga gam hannunta sai rawa yake yi sosai."

"A karo na farko da hannunta yazo jikinsa shima na sa hannun ya je jikinta, duk da shima baya cikin nutsuwa"

"hankalinsa a tashe yake yana tunanin ko wani abun ya same ta ya dawo gidan, sai da yaji haWuwar hannunsu a waje Waya a jikinsa da zuciyarsa, duk da hannun nata rawa yake yi amma hakan bai hana shi jin ba™on yanayi a tare dashi ba."

" Babu abinda zai same ki, ki nutsu ya furta a tausashe yana kallon yadda take kuka sosai kanta ko Wankwali"

"babu. Gashin ta yana cure a tsakiyar kanta ta Waure shi da ribbon. Kamar ma bata ji me yake faWa ba har lokacin bata cikin nutsuwarta saboda tashin hankalin da taji yana ™o™arin tunkaro ta, kasheta fa taji ana zancen za a yi, to ba dole hankalin ta ya bar jikinta na wani lokaci ba."

"Nayla har lokacin hawaye ta ke yi tana ri™e dashi ta ce,  Tsoro nake ji, zasu kashe ni. Sun Salla gate sun shigo, Ka taimaka min ta sake faWa a tsorace sosai tana ri™e hannayensa duka biyun tana waige-waige. Abinda ya ji ya ratsa hannunsa mai kama da jan wuta shine ya saka shi yi mata tsawa ya ce,  ba na ce ki nutsu ba! Ki saurara da wannan shirmen! Ya faWa da ™arfi ba tare da ya sani ba saboda shock Win da ya ji ya ratsa hannayensa ya shiga har cikin jininsa ya zaga sa™on ya tafi har ™wa™walwarsa lokaci guda."

Firgigit Nayla tayi ta tsaya cak tana kallonsa har lokacin jikinta bai daina rawa ba amma ta saki hannunsa babu

"shiri. Kallon ta yake yi kamar yadda take kallon sa tana share hawaye ya ce,  babu abinda zai same ki, ki nutsu ki daina yi min shirme ya faWa yana fita ya bar ta a wajan jiki na karkarwa."

"A gefen gadon ta zauna tana ajiyar zuciya, tsoron da take ji ya ragu ganin Omar Win yana nan amma har lokacin a tsorace take ta kasa sakewa gani take kamar zasu dawo su kashe ta Win."

"Shi kuwa harabar gidan ya fita zuciyarsa na yi masa zafi akan abinda aka yi masa, yana fitowa harabar gidan ya"

"tarar da Bash da Goje da Tk suna jiran fitowarsa. Yana ganin su ya ce,  bana ce ku zauna kar ku fito ba?. Goje ya ce,  Haba Damisa, an shigo har gonar mu kuma mu zauna muna kallo?. Tsaki ya yi ya ce,  to da ku ka zo me zaku yi?. "

" Umarnin ka mu ke jira, wallahi yau baza su kwana lafiya ba. Azumin gobe sai dai su yi shi a kabari. "

"Hayaniya yake jiyo daga waje ya ce,  su waye a waje?. Bash ya ce,  masoya ne, sun Webo kayan aiki suna jira ka ce wani abun. "

"Tsaki ya sake yi ya fita zuwa wajan dan ganin abinda yake faruwa, yana fitowa ya ga matasa da makamai an"

"taru ana jira ya fito, yana fitowa suka fara hayaniya wannan yace wannan wancan ya ce wannan. GabWaya baya fahimtar abinda ake faWa hakan ya saka ciki cikin tsawa ya ce,  ya isa! Ya isa!. "

"Duk suka yi shiru ya kalle su ya ce,  ban ce kowa ya yi wani abun ba, ban ce kowa ya aikata wani abun ba. Kar"

"wanda ya yi musu komai, a bari hukuma tayi aikin ta. Ina sake maimaitawa, kar wanda ya Wauki doka a hannunsa. Šaya daga cikin matasan ya ce,  Madugu har gida fa, har gida suka zo aka yi mana ba daidai ba kuma ka ce mu bari?. Kaima wasa ka ke yi baza mu ™yale su ba wallahi. Ranmu fansa ne a gare ka Damisa, zamu iya Satawa da kowa mu shirya da kai wallahi. "

"Omar ya ce,  ni dai na ce kar wanda ya yiwa kowa wani abun, in kuma ba haka ba duk wanda ya aikata saS"

"anin abinda na ce zai haWu da fushina mai yawa. Kowa ya wuce ya tafi ya yi alwala ya tafi masallaci ya yi sallah. Wani zai sake magana cikin tsawa ya ce,  Na ce ku bar nan ko!. Dukkan su barin wajan suka yi ya kalli su Bash ya ce,  ban ce kowa ya aikata wani abun ba, haka zalika ban bawa kowa umarnin tura wasu su yi wani abun ba, ku ™yale ni ni nasan matakin da zan Wauka. "

"Tk ya ce,  Amma Damisa& . "

 Shiru! Na ce a ™yale ni ya faWa a tsawace yana kallon sa dole ya yi shiru suka fita shi kuma ya koma ciki. Kamar ya shiga Wakin ya duba ta amma sai ya fasa ya yi zaman sa yana kaWa ™afa cikin Sacin rai mai yawa.

"Wai shi za a zo har gida aka yiwa wannan wula™ancin, in ba dan kura tayi lafiya ba ai da gobe garin Kano an wayi gari jini ya Sata ko Ina, azumin gobe jama ar Kano da jini zasu sha ruwa. Babbar sa ar da suka yi Omar W in dah dana yanzu akwai banbanci, in ba dan haka ba da duk sai dai iyayensu su haifi wasu, koda bai Wauki mataki da kansa ba za a Waukar masa. A bayyane ya ce,  ko ya ya kayi ™o™arin zama mutumin kirki sai an yi abinda za a saka ka koma na banza. "

Tsaki ya yi ya fita yana kallon gate Win ya mayar ya rufe dan ba Salla shi suka yi duka suka yi masa har lock Win ya zare. Ko key bai saka ba ya dawo ya zauna a kan kujera yana kaWa ™afa yana tunanin irin hukuncin da ya kamata ya yi musu. Yana wanna tunanin ya ga ™arfe uku na dare ta yi ko ina sallah ake yi. Kawai sai ya tashi ya yi alwala shima ya tayar da ta sa sallar.

"Nayla kuwa baccin wahala ta yi alarm Win wayar ta ne ya tashi ta, ta tashi da nauyin jiki da ciwon kai daman dashi ta kwanta gashi tayi kuka kuma bata samu baccin kirki ba, alawala tayi ta tayar da sallar tahajjud."

"Washe gari sai ™arfe goma na safe ya tashi, kasanacewar juma a ce manyan kaya ya saka ya fita, kai tsaye police station Win da ya saka kai yaran ya wuce. Da yake Dpo da suka saba ne suka tattauna ya ce masa za a W auki mataki mai ™arfi, zuwa ranar monday za a tura su kotu bisa tuhumar tayar da faWa har cikin gida al™ali yanke musu hukunci."

Omar ya san za a yi hakan shiyasa bai damu ba ya wuce zuwa shago. Kowa mamakin ganin sa yake yi kuma ba

"a ji wani tashin hankali ya sake faruwa ba, kowa mamaki yake yi da labari bai zagaye gari ana cewa Tiger ya"

mayarwa da kura a niyar ta ba. Duk inda ya wuce kallon sa ake yi yana kuma sane da kallon da ake masa kawai babu wanda ya isa ya tunkare shi da maganar ne sai dai kallon kawai.

"Nayla ranar bata je aiki ba ita da aiki sai ranar monday, tana zaune kiran Didi ya shigo wayar ta tana Wauka a gigice Didi ta ce,  Nayla lafiya ki ke dai ko? Na ji labarin abinda ya faru jiya. Ina fatan dai kina lafiya?. Nayla a kasalance ta ce,  Lafiya lau Didi, Amma a tsorace nake sosai. "

 Ina Omar Win?.

 Ni ban sani ba ta faWa murya na rawa sosai.

" Ki nutsu Nayla, babu abinda zai same ki. Bara na kira Omar Win naji abinda yake faruwa ta faWa tana yanke"

wayar. Nayla tayi ajiyar zuciya har lokacin zuciyarta bugawa take yi dan bata taSa ji ana cewa za a yi kisa a zahiri ba sai dai a film.

Abu na social media nan da na labari ya zaga ko Ina da ko wanne gari. Arewa bloggers suna ta rubuta an kaiwa

Omar Tiger babban Wan daba mai murabus hari har cikin gidan sa ana yi yun™urin kashe matarsa.

A can Madina a lokacin Mama tana zaune bayan sun dawo daga sallar juma a suna zaune ita da Abiy sai ga

yaran nasu gabaWaya sun shigo Wakin Abiy gashe shi. Suna zaune ana hira Mama ta Wauki waya tana dubawa.

"Mama ta ce,  Innalillahi wa inna ilaihir raji un! A tare duka suka kalle ta a gigice jin salatin da tayi Abiy ya"

"ce,  lafiya?. Mama ta kalle shi ta kalli wayar ta ce,  Jiya da daddare an kaiwa babban Wan daba na jahar Kano mai suna Tiger hari har cikin gidansa, an yi yun™urin kashe matarsa Allah ya ta™aita Mama ta faWa cikin sigar karanto musu abinda yake da rubuta."

"Jidda ta ce,  Innalillahi wa inna ilaihir raji un! Mama Twinny! Ta faWa a gigice tana wara idanu waje. Mama"

"a ruWe ta ce,  ku kira mana wayar ta da hanzari don Allah. Yaya J da Yaya Ahmad da Jidda har rige-rigen kiran wayar Nayla ake yi cikin tsananin tashin hankali."

"Abin haushin gabaWaya basa samunta sai kira ake yi amma bata shiga. Yaya J yayi tsaki ya ce,  Ba a samun ta a"

"waya. Abiy ya bisu da kallo ganin duk sun ruWe su ga masu ΄ar uwa, ya yi dariya ya ce,  meye duk ku ka tashi hankalin ku haka? Abinda ta aura kenan daman, kuma kun san haka zata iya faruwa ko yaushe, to meye na Waga hankali kuna salati haka?. "

"Yaya ya ce,  Abiy batun kisa ake yi fa, kisa fa. Abiy ya Wauke kai bai ce komai ba. A lokacin Jidda ta same ta"

"WhatsApp call tana Wauka ta saka a speaker ta ce,  Twiny lafiya ki ke dai ko? Yanzu mu ka ga abinda ya faru jiya a social media, kina lafiya?. "

"Nayla a sanyaye ta ce,  Lafiya lau nake Twiny, babu abinda ya same ni. "

 Kin tabbatar? Ya na ji maganar ki haka kamar kin yi kuka?.

" Bani da lafiya Twimy, stress na aiki ya saka ni a gaba ga azumi, kullum a wahale nake yini saboda gajiya ga ciwon kai. Ina Abiyna? In kin je Wakinsa ki ce ina gaishe shi ina yi masa barka da juma a. Na yi masa missed call bai Wauka ba. "

"Jidda ta kalli Abiy da ya duba wayarsa bayan ya ji abinda Nayla ta ce sannan Jidda ta ce,  Yana jin ki, muna"

"tare gabaWaya Mama ta ga abinda ya faru. Kuma babu wanda ya kula a cikin mu sai yanzu, da wani abun ya same ki tun a jiyan da sai yanzu zamu sani. Yaya J ne ya ce,  Nayla kin tabbatar lafiya lau ki ke ko?. Nayla ta ce,  Lafiya lau Yaya J, Ina Yaya?. Yaya Ahmad ya ce,  Nayla gani nan, gaskiya baki da lafiya Nayla? Gaba Waya voice Winki ya canja, sannu kin ji, ki samu ki je asibiti a baki magani. "

" Yaya Strees ne kawai wallahi, yau kuma da yake ban je aikin ba ma Ina gida bana ji daWin jikina. "

" To sannu, Allah ya ™ara lafiya, Allah ya kiyaye gaba. Ki yi magana da mijin na ki gaskiya a san matakin da za a"

"Wauka, bazai yu shi da aikata laifi hukunci da ™o™arin shafar ki ba. "

"Nayla ta ce,  to Yaya. Ina Anty Halisa da Amma?. "

" Sun shiga masallaci ita da Jalila, Amma kuma gata nan a wajena. "

" To Yaya a gaishe su, a gaishe da Mama da Abiy. Mama sai a lokacin ta ce,  Nayla kina lafiya dai ko?. Tayi murmushi ta ce,  eh Mama lafiya ta lau, ki gaishe min da Abiy. "

"Abiy jin tana ta ambatar sunansa sai ya ji zuciyarsa tayi rauni ya ce,  Mamana ya ibada?. Nayla jin muryar"

"Abiy da hanzari sai ta ce,  Abiy barka da Juma a, ya ibada?.  Alhamdu lillah Mamana, yanzu na ga kiran ki na je masallaci.  To Abiy. Allah ya amsa ibada. "

" Amin ya fita daga nan bai sake cewa komai ba. Jidda suka yi sallama ta kashe wayar. Kafin wani ya sake magana a cikin su Abiy ya ce,  Ku bani waje zan huta kafin lokacin sallah. "

"Duk suka mi™e suka fita tare da jan ™ofar,bayan sun fita ya kalli Mama da take hawaye ya ce,  lafiya?. Ta goge ido ta ce, Irin zargin da ake yi min akan auren Nayla da abinda ake faWa a kaina ne yake karya min zuciya. Yanzu tsakani da Allah meye amfanin auren irin wannan mutumin? Gashi tun auren bai je ko ina ba an fara neman rayuwarta akan abinda bata san ma anyi ba. Ni ban san Nayla wacce irin yarinya ba ce da ta nace akan wannan banzan mutumin ba wallahi, ka duba yanzu tambayarta ake yi amma sai maimaita lafiya lau take yi, kar ma ta ce ba lafiya ba ace za a raba su kenan ko?. "

"Abiy ya ce,  to waye ya ce zai raba su?. "

" A yanayin Yaya da Jawad tsaf zasu iya raba auren nan in wani abun ya same ta. Shine take ta maimaita lafiya lau take, Ina jin wannan takaicin abin har zuciyata, ina jin zafin abin nan har ™ohon zuciyata. A haka ma bata samu shiga a wajansa ba har yanzu, har yanzu ko kallon arzu™i bata ishe shi ba, har yanzu baya kallon ta matsayin matarsa ya jingine ta a gefe kamar wacce aka kai masa ita ajiya, amma sai wani lafiya lau take maimaitwa. Nayla kamar ba ni na raine ta ba, ka duba Jidda da mijinta suna nan suna ibada, gabaWaya dangi ana nan ana ibada amma ita banda ita, kuma hakan bai dame ta ba. Allah wadaran naka ya lalace Mama ta faWa tana kuka."

"Abiy ya murmusa akwai bai ce komai ba ya tashi ya fita daga Waki. Mama ta goge hawayenta da ta tabbatar ya shiga ta ce,  Nayla zama da Omar ai ko bakya so. Allah na tuba ka yafe min ina ™asa mai tsarki ina ™arya ta faWa tana tashi tayi alwala ta saka babban hijjabi ta fita itama."

"Nayla kuwa bayan sun gama waya Abba ne ya kira ta, shima tambayar da yayi mata kenan ta amsa da"

"lafiya lau. Bayan ta kashe Maman Kano ™anwar Abiy ta kira ta, bayan ta gama da ita Mama Sa adatu, bayan ta gama Baba. Har Daddy da suke tare da su Hajja a saudia sai da ya kira ta amsar da ta bawa su Jidda ita yake basu."

"Ajiyar zuciya tayi bayan ta gama amsa wayar ta ce, Nayla ΄ar gatan dangi, kowa kirana yake ya ji lafiyata. ˜ wan™wasa gate Win ta ji ana yi a tsorace ta tashi ta saka hajjisbi ta je ta buWe."

"Mama Sa adatu ta gani ta rungume cikin murna ta ce,  Mama sannu da zuwa. Mama ta bita da kallo ta ce,  Duk da mun yi waya hankalina ya kasa kwanciya wallahi, kina lafiya?. Nayla tayi dariya ta ce,  lafiya lau nake Mama ta faWa tana kulle gate Win suka shiga ciki."

"Mama ta bita da kallo ta ce,  Amma yanayin ki bai gwada lafiya ki ke ba, kalle ki fa. Nayla ta zauna kusa da"

"ita ta ce,  Mama tun jiya daman bani da lafiya, stress na aiki ga azumi ya saka min zazzaSi. "

" Ayya sannu, amma dai babu abinda ya same ki ko? Mun yi waya da su Yaya ya ce na taso nazo na duba ki. Da"

"Abbas zan turo sai na ce bara na zo da kaina, ni kaina hankalina ya kasa kwanciya duk da mun yi waya sai nake ji kamar ba lafiya ki ke ba. Nayla ta ce,  lafiya ta lau wallahi Mama. Mama ta ce,  na ga alama. Amma ya aka yi abin ya faru jiya? Su waye haka suke son cutar dake har gida?. "

 Wallahi Mama ban sani ba.

 Shi bai faWa miki ba?.  Tunda ya fita ma bai dawo ba.

" Amma naga an ce ya kai su gaban hukuma an za a hukunta su, hakan da yayi daidai ne da bai Wauki hukunci a hannaunsa ba. Nayla tayi shiru bata ce komai ba."

"Mama ta ce,  yanzu me ki ke so?. Nayla ta kwanta a kafaWarta ta ce,  Babu komai Mama. Mama ta ri"

"™e ta tana shafa kanta a hankali cikin tausayinta da ™auna. Ita kuma Nayla ji take kamar ta kanta a jikin mahaifiyarta yake, shafa kanta da Mama take yi ya saka bacci ya Wauke Nayla."

"Motsawa Mama tayi sai Nayla ta buWe ido Mama ta ce,  kwanta ki huta zan tafi gida, gobe ki zo mu sha ruwa"

gabaWaya. Idanunta a lumshe Mama ta tashi fita amma zuciyarta babu daWi bata so ta tafi ta barta.

"Nayla ta jima tana bacci har biyar na yamma, sai da ta farka tayi sallar la asar ta fara lazumi saboda lokacin"

amsa addu a na ranar juma a.

"(Lokacin amsar addu a na bayan sallar la asar a duk ranar juma a, lokaci ne mai matu™ar falala kuma addu a bata da hijjabi a wajan Allah. Duk abinda aka ro™a a wannan lokaci Allah ya amsa sai dai a jira lokaci. Lolacon amsa addu ar yana farawa ne bayan sallar la asar zuwa magriba, babu wanda ya san ta™amaiman ™arfe nawa lokacin yake shiga, abinda malamai suka sanar damu bayan sallar la asar zuwa magriba a tsakanin haka lokacin yake farawa. Allah ya bamu iko ya amsa mana bu™atar mu amin.)"

Tashi tayi ta dafa tea kamar ko yaushe tana tunanin bayan tea me zata dafa ta ci? Ita in tana azumi bata iya cin

"abu mai nauyi shiyasa sai ta rasa abinda zata ci. Irsh ta gyara ta soya,"

ta soya ™wai duk ta ajjiye. Dawowa tayi ta zauna ta cigaba da addu a a wajan har aka yi sallar magriba sannan ta yi sallah ta ci abinci ta sha magani.

"Kamar ko yaushe bai shigo ba sai bayan sallar tarawee, ta shigar da kaya kitchen ta fito kenan ya shigo. Kallon"

"ta yayi ya Wauke kai ita kuma ta ce,  an sha ruwa lafiya. "

" Lafiya. Ba zato taji ya amsa hakan ya saka ta kalle shi sai taji ya ce,  jiya na ce ki rufe ™ofa, meyasa baki rufe ba?. Nayla ta ce,  kaina ne yake ciwo shiyasa na manta ban rufe ba. "

" Kar ki sake kuskuren barin gidan nan a buWe, duk da babu wanda zai sake shigowa. "

"Nayla jin yana yi mata magana a tausashe ssi ta damu damar shagwaSa kamar zata yi kuka ta ce,  Don Allah"

"ka daina tafiya ka barni ni kaWai, tsoro nake ji wallahi. Šago ido yayi ya kalle ta jin yadda take magana kamar zata yi masa kuka. Share batun yayi bayan ya Wan murza goshinsa kamar yadda ya saba ya ce,  Ya ciwon kan?. Nayla wara ido tayi jin abinda ya tambaya ta kasa bashi amsa sai kallon sa da take yi dan bata yi zaton zai tambaya ba."

"Ganin irin kallon da take masa na mamaki sai ya Wauke kai ya wuce ta. Motsawar da yayi zai bar wajan ya saka Nayla ta dawo daga duniyar mamaki ta ce,  na ji sau™i. Bai ce komai ba ya shiga Waki ba tare da ya kalle ta ba. Nayla daWi kamar ya kashe ta, ko babu komai yana damuwa da lamarin ta tunda gashi bai manta tana ciwon kai ba, lallai ana samun cigaba ta tabbatar addu ar da take yi ce Allah ya amsa mata.KRB3P012 Arewabooks@nanahaleema11."

"A yadda take kwance kallo Waya zaka yi mata ka san bata da lafiya, idanunta a kulle yake sai juya kai take cikin ciwon kan da ya fi komai damunta a yanayin da take ciki. Ashraf ne ya shigo ganin yanayin da take ciki ya ce,  Baki da lafiya, dole mu je asibiti, Ta so mu je ya faWa yana Wago ta daga kwance."

" Jikinki ya yi zafi sosai. Cikin muryar marasa lafiya ta ce,  ka ™yale ni kawai, bana son zuwa ko Ina.  Sai kin je, bazai yu ki dinga zama da ciwo ba. Ina son lafiyarki ko dan na samu abinda nake so. Mi™ar da

Please Login or Register in order to submit comment