You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ya fiddo ya bude yana kallon girmanta, waje ya fito ya rike waist yana kallon mutane dake wucewa, yana nan tsaye ya hango yar Wata neighborhood dinsu ta taho, yarinyar zatayi 14, yasan she will still be a virgin, kiranta yayi tazo da sauri saboda Tana girmama shi,
"Habiba dan Allah ki amso min madara shagon shamsu, in kin zo ki ajiyemin cikin daki..." Ya fada mata, babu musu yarinyar ta amshi Dari biyar dake hannunshi tace
"Yaya na nawa?.." Ta tambayeshi
"Ki sayo na Dari..." Ya amsa mata yayi kaman ya shige cikin gida, yarinyar da sauri ta bar wajen saboda itama aikenta akayi a gida, yana ganin ta bar wajen yayi ya dawo ya shiga dakinshi ya dauko yadin ya tsaya bayan Kofar, bayan kaman minti goma yarinyar ta dawo ta tsaya bakin Kofar tayi sallama taji shuru, idanuwa yayi rolling yana cewa
"I said step Inside..." Ya fada cikin ranshi, yarinyar kaman taji ta Dan leka dakin ta ajiye madara da chanzi ta daga Kai ta ga mutum tsaye, zata bude baki tayi magana safwan ya yarfa mata yadin from head to toe, ban karewa yarinyar tayi for like 1 minute Sannan ta cire yadin daga kanta da hannunta ta fita daga dakin tayi hanyar gidansu, babu Wanda yaga both shigarta da fitarta, har ta isa gidansu bata ce komai ba, ta hadu da wasu friends dinta sunyi mata magana amma no response, safwan saurin nade yadin yayi ya maida cikin bag dinshi ya fito yana kalle kalle, duk Wanda ya ganshi yasan bai da gaskiya, sai zaro idanuwa kawai yake gabanshi na mugun faduwa, leka dakin yayi ko zai ga kudi yaga babu komai. Tsayawa yayi dukda Dan iskar dake busawa he was sweating.
Yarinyar kam yana shiga gidansu ta samu waje ta zauna, idanuwanta bude sun Chanza yanayi, mahaifiyar yarinyar fitowa tayi daga daki dayake duk suna ciki suna kallon film
"Wai habiba yaushe zakiyi hankali?..' Na aikeki kinzo kin zauna babu magana kuma kin shigo babu sallama..." Matar ta fada cikin bacin rai, yarinyar na zaune yanda take bata ko motsa ba, tureta mahaifiyar ta tayi Tana cewa
"Habiba dake nake fa?.." Matar ta fada Tana turata sai taga yarinya tayi baya ta fadi kasa, nan ta saki salati tare da ihu Tana kiran a taimaka mata, before you know it har gidan ya chika da mutane, wata tsohuwar mata ta amsheta a hannunta Tana kallon yanda idanuwa habiba that ita Kadai tasan what she's seeing and going through because she's battling for her life,
"Ku taimaka min..." uwar habiba Tafada cikin matsanacin kuka, tambayanta akayi abinda ya sameta amma habiba batayi magana ba kuma she's breathing normal saidai idanuwanta da suka kafe waje daya da kuma Chanza kala, uwar yarinyar sai kuka take Tana fada masu abinda ya faru wai ta aiketa da sauransu, nan mutanen da suka ganta suka dinga cewa
"Ai Yanzu nan muka ganta..." Ai sai wasu suka dinga cewa gamo tayi, safwan dake zaune waje yasan something is happening saboda yaga yanda mutane ke shiga gidan, zama yayi yana zufa sosai saboda fargaba, bai mintuna goma bai leka dakin ba ko zai ga kudi amma nothing, Kofar ya jawo ya rufe ya nufi gidansu Usman yana bashi labarin yayi daya amma har Yanzu shuru,
"Ita yarinyar fa?.." Usman ya tambayeshi,
"Oho...naji uwar Tana ihu...I think something is happening to her..." Yafada babu tausayi or tsoro, suna nan zaune har kusan goman dare suna planning rayuwar su, ita kuma she battled for her life har zuwa goma da rabi tace ga garinku nan, safwan na dawowa gida ya bude dakinshi zai shiga, irin kudin da ya gani yasa yayi saurin komawa baya yaja kofar ya kulle.
Thanks.10💙💜💛💚❤️
Sirrin wasu gayun
💛❤️💙💜💚
® zuwairat (ummumaryam)
1️⃣0️⃣
Don't read if you didn't pay because if you do you owe me🙅🏿
Dedicated to my anty...wish you all the best in here and hereafter. Bani da bakin godi
Chest dinshi ya dafa yana sakin ajiyan zuciya da karfi, he can't believe this is how easy it is, kukan da yake ji a neighborhood dinsu bai dameshi ba, all he's thinking about is wannan makudan kudin da ya gani, it scares him, bai taba ganin kudi ko a film Mai yawan wAnda ya gani a dakin shi ba, sai da ya gama surprise breathing Sannan ya sake lekawa cikin dakin, sai gani yayi kudin yayi multiplying, idanuwa ya zaro kaman zasu fito waje saboda yanda gabanshi ke faduwa, this time shiga dakin da babu wajen saka kafa yayi Don ko Ina dakin kudine, da sauri ya maida Kofar ya rufe, yana nan tsaye kudi ya Kara appearing, ihu ya saki yana cewa
"Money..." Da karfi sai kuma yayi saurin rufe bakinshi kar ajishi, Allah ya taimaka da akwai hasken nepa so he can see clearly, zama yayi gabanshi na faduwa, sai kallon kudin da ke multiplying kawai yake, the money is too much, jiki na rawa ya dauki wayarshi ya kira number usman, ringing biyu usman dake chan yana tunanin who he's first victim will be yayi piçking,
"Usman nayi kudi...kudi everywhere..usman zo kaga ainahin kudi...original money..." Safwan Yafada kaman sabon shigan mad person,
"Am coming..." Usman Yafada atakaice Sannan ya katse wayar, safwan zama yayi kan kudin yana debo da both hands dinshi,
"Welcome to the world of classy people...na shigo gari...na shigo gari...you better watch your back..." Yafada yana zufa, more money was still coming, after kaman minti biyar yaji murya from nowhere ance
"Your sacrifice is accepted...welcome to the world of fame..." Yaji maganar kaman daga sama, ko kadan bai wani razana ba, some of the money is not Nigeria currency, ya dai San dollars but sauran bai San ko na wanne countries bane, da akwai at least 5 different currencies wajen, sai ware idanuwa kawai yake yana ganin he's a rich man already, duk bag dinshi ya dauko ya bude su, kudin ya fara kwasa yana zubawa amma more is still coming, har ya gama deban dukkan kudin ya cika two bags din amma still da akwai sauran kudi and still wasu da appearing, a sauri ya Mike ya fita zai shiga cikin gida sai suka hade da Inna, kallon yanda jikinshi ke rawa tayi amma she didn't ask what's wrong with him,
"Inna Ina zuwa haka?..' Ya tambayeta gabanshi na faduwa Don he was thinking she heard he's screaming about money, kallon banza ta watsa mashi not minding yanda yake zufa and the guilt that is written all over him tace
,"bakaji anyi rasuwa nan makota ba?..." Tafada Tana wuceshi fuuu kaman zata tashi sama, Dan tsayawa yayi ya bi Bayanta da kallo har ta bace mashi saboda yana tsoron kar ta shige dakinshi, sai da ta sha corner Sannan yayi saurin shiga cikin gida ya wuce inda Inna take ajiyan buhunna ya dauko Kato guda daya ya, yana kokarin komawa sister dinshi itama. Ta fito, kallon shi tayi from head to toe taga yanda yake zufa then jikinshi na rawa tace
"yaya..lafiya..." Tafada Tana noticing abinda mahaifiyar su ta kasa ganewa saboda rashin lura, Dan murmushi ya saki yana goge face dinshi yace
"Me kika gani?.." Ya tambayeta, kura mashi Ido tayi taga he's scaring her son dukda he's her brother and she loves him she can smell something fishy,
"Nima bansani ba.,amma duk naga ka firgice..." Wani irin kallo yau watsa mata before saying
"Ni mate dinki né da zakice na firgice...wai ubanme kike baki kwanta ba..." Ya tambayeta sounding so harsh,
"Rasuwa akayi Ai...yaya habiba ta rAsu...." Tafada mash kaman zatayi kuka, bai Kara cewa komai ba ya fice daga gidan rike da buhu sister dinshi tabi bayanshi da kallo yana mamakin abinda yasa ya koma haka kaman wani sabon shigar mahaukaci, safwan na fita usman na zuwa, lokacin shadaya saura amma saboda rasuwa da akayi da akwai mutane saboda duk mutuwar yarinyar ya tada masu hankali sosai, inda mutane zasu maida hankali ga safwan da usman da nan take za'a gane something fishy is happening Don while some people where busy discussing abinda ya samu yarinyar su kuma suna ciki sun rufe kowa sai kus kus suke,
"Wai ance yarinyar ta rasu..that means duk wacce mukayi amfani daita will not survive..." Inji usman, safwan ko sauraron shi baiyi ba sai kwace kudi yake yana zubawa a buhu, a ranar duk unguwar basuyi bacci ba sai very few da basu da human feelings, uwar yarinyar kam sai suma take Tana farfadowa because she can't believe her daughter is gone, safwan na tashi da asuba dukda sai 4 bacci ya saceshi yayi saurin duba buhun kudinshi da kuma bags yaga it's not a dream it's real, fita yayi yaga rana ta fito duk an shimfida mats Kofar mahaifin yarinyar, da sauri ya fita ya shiga cikin gida, Inna na zaune tsakar gida ta bishi da harara har ya shige bathroom Tana hararanshi, yau ko irin gaisuwa daya sabayi mata Ta amsa a wulakance bai yi mata ba, fitowa yayi da bucket zai debi ruwa tayi saurin cewa
,"kull...kar ka kuskura ka debi wannan ruwan...yaushe rabo daka debo ruwa gidan nan?.. Kai Yanzu ka girma Ai..." Tsoki yaja ya ajiye bucket din, Inna ta bude baki tace
"Ni kake jawa tsoki?.." Ta fada afusace Tana kokarin mikewa, da sauri ya bar compound din Don yasan in har ya tsaya he can strangle her to death, da yana fushi amma na Yanzu ya linka na da, he easily get angry and in yayi fushi sai yaji he's becoming uncontrollable,
"Da ka tsaya inci uwarka shege matsiyaci..." Tafada, yana jinta ya sake Jan tsoki yana cewa
"Let's see..." Yafada yana shigewa dakinshi, wayarshi ya dauka ya Kira alhaji idris ya Sanar mashi abinda ke faruwa,
"Zan aiko da mota anjuma a daukeka da kudin,ka samu waje kayi counting sai a samu gida ka saya yauyau din nan..." Ya fada mashi
"Ok..amma za'a yi janaizar yarinyar...in an gama sai in kiraka..." Safwan ya fada mashi yana zufa,
"Ok babu matsalar..." Ya amsa mashi, Kaya safwan ya dauka ya saka ya fito waje, bayan kaman minti ashirin da zamanshi aka fito da yarinyar tare dashi aka sallaceta aka kaita makwancinta, yana zaune wurin amsar gaisuwa yana Jin yanda mutane suka dinga cewa
"Ai gamo tayi.,shiyasa babu kyau aiken yara mussanman mata bayan magrub..." Yaji suna ta maida yanda aka yi..
Yau bayan nana ta shirya in a sexy gown Wanda bai wuce 3k ba tayi rolling kanta ta zauna ta tsara makeup dinta da kanta ta fito tayi kyau sosai, bag dinta ta dauka ta fito Don daman Maryam ta dade da tafiya lecture kuma daman tunda suka dawo hostel basu taba tafiya school area tare ba saboda yanda nana ke behaving yana damun Maryam sosai amma ko advice ta bata sai ta datsa mata magana Wai Ina ruwanta, jiya ma haka bayan ta gama lecture ta dawo hostel ta dau wanka ta fita da Maryam ta tambayeta inda zata sai tace iska zata sha, haka ta tafi sanye da Kayan that's almost nothing, kawai ita gurin ta taci kwalliyarta ko Allah yasa ta hadu da wani big boy, she's so much in love with fairytale life, she thinks kawai good looking, handsome, hot guy will come from nowhere and just marry her, or date her, yanda take yi a hostel Baka taba tunanin yar civil servant ce because ta kashe kudin upkeep dinta for wears. Tana fita ta kulle kofarsu, daya daga cikin matan da suka taba maganar ta nufota Tana cewa
"Excuse me..." Ahankali nana ta juyo ta kalleta,
"Hi.." Itama Ta amsa mata sounding nice, karasowa matar tayi tace
"Yanmata ya kike?.."
"Lafiya lau..." Nana ta amsa mata Tana ajiye keys a bag dinta,
"Kawai I want to tell you tunda kika dawo hostel din nan I like you swag...dukda ke ba mate dina bace I will want us to be friends..." Matar ta fada, murmushi nana tayi Wanda ya sake bayyana beauty dinta
"Amma anty nagode...na gode sosai..." Tafada Tana murmushi,
"Yauwa..." Matar dake sanye sa jeans Wanda ya matse ta sosai Sannan Tana sanye da just singlet kuma da ganinta kasan first class bitch ce, amma nana bata damu da yanda take ba, asalima she loves people with class da effizy,
"Pls can I have your number? " Inji matar,
"Eh mana..why not..." Ta amsa mata, hannu mata ta saka bayan Jean dinta ya dauko iPhone x da ke cikin aljihunta saka number nana Sannan Tayi mata flashing, yar small phone din nana yafara ringing ta Fiddo ta,
"Wannan itace wayarka ko kina da wata?.." Matar ta tambayeta,
"Itace wayata..." Nana ta fada mata Tana kokarin storing number gira daya ta daga Sannan tace
,"store my name with big mama..." Inji matar, babu gardama tayi storing Sannan tace
"Anty zan tafi...lokacin lecture ya kusa..." Nana Tafada mata,
"Ok ba matsala.....zan kiraki bayan lecture...hope zakizo dakinmu?.."
"Eh mana..." Inji nana,
"Good...ayi karatu lafiya..." Big mama Ta fada mata Sannan ta juya itama nana ta tafi cikin ranta sai dadi take ji she's coming close to classy people, San ajinta ba ga Maza kawai ya tsaya ba , har mata indai suna da class tanason su.
Habib né zaune da safe suna Shan koko da kosai da aka kawo masu daga gidan abban Fatima, ya Lura har Yanzu he's mother is disturbed Don she don't talk much Sannan breakfast din ma Don ya matsa mata yasa takeci, grandmother dinshi ce ta fito da sanda Ta taka ahankali tazo ta zauna kusa dasu, sisters dinshi mikewa sukayi suka basu wajen
" hindatu meye matsalarki..,na Lura tun jiya da kuka dawo ko maganar kirki bakiyi...kodai bakisan zama Dani?.." Tsohuwar Ta fada, da sauri mamanmu Ta girgiza Kai Tana cewa
" aa ba haka bane...kawai banajin dadi né, ..shiyasa..." Ta amsa mata wearing a smile,
"Tou Allah baki lafiya...modibbo Kai kuma tunda Allah yasa ka dawo gida sai kayi hanzari kayi aure...bamuson matasa suna zama babu aure...duk saaninka suna da yara da mata fiye da daya..." Tafada babu wasa, rufe fuska habib yayi kaman mace alaman yaji kunyar maganar da grandma dinshi tayi m cikin ranshi yana tunanin he wish yana iya aure in few days yasan ya rayuwar aure take kafin ya bar duniya, sallama akayi Fatima ta shigo, daga Kai yayi ya kalleta, dariya tayi mashi ta durkusa ta gaishesu, just that moment sai yayi tunanin inama zaa bashi Fatima, sai kuma yayi tunanin she's too young,
"Yaya baba yace kazo..." Fatima ta fada mashi, sauran kosai a saka a baki ya Mike yana biye daita har suka isa Kofar inda abban Fatima ke tsaye, durkusawa yayi ya gaisheshi yau amsa Sannan yace
"Ka gama kalaci mu Dan leka gona?.."
"Eh na gama..." Habib ya amsa mashi,
"Tou ka tashi mu tafi...zan nuna maka gona kaine..." Ya fada mashi, ahankali habib ya Mike suka dinga tafiya, sai da suka kusa hour guda suna tafiya Sannan suka isa gaton gona,
"Wannan gonar na mahaifin mu né wato kakarka,...duk shekara Ina bada hayarta Ana noma amma tunda Allah yasa ka dawo gida sai ka dinga nomata..." Idanuwa Habib ya zaro saboda farin ciki yace
"Kawu kai fa...ai wannan wajen yayi mani girma..." Habib Yafada wishing that he will be alive to stay with those happy people,
"Kar ka samu damuwa...ai da akwai gonakai da dama...kadai in kana da karfin noma kayi mu gani..." Yafada cikin zolaya, dariya habib yayi sai kuma yayi shuru kaman Wanda ya tuna wani Abu,
"Menene matsalar modibbo..naga yanayin ka ya Chanza..." Ya tambayeshi, ajiya zuciya Habib ya saki Sannan yace
"Kawu Dan Allah ko ban nan ka kula da mamanmu...shiyasa na maido maka su..." Yafada cikin sanyinmurya, ahankali abban Fatima ya kalleshi yace
"Bangane ba..Ina zaka?.." Ya tambayeshi sounding very confused,
"Aa babu inda zani kawu...amma Dan Allah ko da tafiya tazo na gaggawa ka taimaka min ka kula dasu...nasan Kai adaline kuma duk inda nake nasan zaka kula dasu sosai...nidai kawu Dan Allah Dan annabin rahama kar ka bar mamanmu ta sha wahala, nasan su Aliya matanesu aure zasuyi..." Abban Fatima sakin baki yayi yana kallon shi saboda yanda yake magana har tsoro ya fara bashi,
"Nifa ban gane ba..Ina zaka?.. Ko ma inane Ai tunda Baka dade da zuwa ba ka Bari ka huta tukunna..."ya fada mashi,
"Kawu..." Habib ya sake kiranhi kaman zaiy kuka, ahankali abban Fatima ya daga Kai ya kalleshi tare da amsawa
"Dan Allah kawu da gaske nake..ka kula da mamanmu..." Ya fada hawaye na taruwa idonshi,
"Ikon Allah..tou naji....mu koma gida...ka fara bani tsoro..." Inji abban Fatima,
"Kawu...Dan Allah ... " habib Bai karasa ba abban Fatima yace
"Ya isa...YaNzu mu koma gida..." Yafada mashi atakaice, ajiyan zuciya habib ya saki Sannan ya biyoshi tunani yake ko ya fadawa kawunshi ya saida gidansu kuma yanda yana da kusan 420k amma yana tsoron kar ya nemi kudi ciki, kawai tunani yake kawai zai bawa mamanmu kudin ta rike wajenta if anything happens to him she should use it to take care if herself and his siblings, suna Dan taba hira suka isa gida, lokacin an gamawa Fatima awara sun fito ita da abokan Sanaar ta su habib suka dawo,
"Fatima talla zaki?.." Ya tambayeta while shi dad dinta ya shige cikin gida, murmushi ta saki da innocent face dinta tace
"Eh yaya modibbo...ko in Baka kaci..." Ta tambayeshi Tana dauke robar, ahankali ya girgiza Kai yana cewa
"Ai ban dade da cin kalaci ba...kawai adawo lafiya..." Ya fada idanuwanshi cikin nata sai dai ita bata kura mashi ido for a long time
"Yaya kaci kaji in yayi dadi..." Tafada mashi Tana ajiye robar, abokan tafiyar ta tsayawa sukayi suna kallon habib saboda dukda in town shi talakane yafi mazansu na nan haduwa nesa ba kusa ba, he's cute daman and ga height he's complexion is not too dark and not too bright,
"Allah Fatima ki barshi...zaki dade baki dawo ba?.." Ya tambayeta sounding concern,
"Aa..bayan laasar zan dawo..." Tana zuba manyan awarar cikin Leda,
"Ina kuke zuwa talla?.." Ya sake tambayan ta yana kallon hannunta dake cikin robar awarar ta,
"Tashan marabar kano..." Wata daga cikin yanmatan ta amsa mashi, sai lokacin ya tuna da akwai wasu wajen, murmushi ya sakarwa wacce Ta amsa mashi, mikewa Fatima tayi ta mika mashi awara Tana cewa
"Yaya gashi..." Ahankali ya girgiza mata Kai yace
"Wannan yayi yawa...ki rage..guda uku kawai yaisa..." Ya fada mata, Dan turo baki tayi Wanda yasa habib Dan kallon ta sosai, tunda yake bai taba yi mata kallon minti daya ba sai yau, she's such an angel in disguise,
"Yaya Ai ba kai kadai bane a cikin gida...kawai ka tafi dashi..." Tafada Tana mika mashi, yanda ya kura mata Ido yasa tayi saurin dauke kanta, su kuma kawayenta sai kallon shi suke, mika mashi tayi kanta kasa ya mika hannun ya amsa ya hada da hannunta tayi saurin janyewa, yar jikinta na rawa ta dauki robar awarar suka tafi, sake juyowa yayi yana kallon ta, itama juyawa tayi Tana he's still standing staring at her back, murmushi ya sakar mata tayi saurin dauke kanta.
"What are you doing..you have few days to die kuma kayi tsaye kana kallon mace..." Zuciyar shi Ta fada mashi, ajiyan zuciya ya saki yace
"Oh Allah...one more chance pls...kar ka Bari mushirikai su samu galaba Kaina oh Allah...rabbi saboda tsoron ka naki bin hanyarsu ta banza...rabbi stand for me where I have nobody, be my Guadian...protect me from their evil eyes...ya rabbi don't lead my friends astry...." Yafada yana tafiya rike da ledar awarar da Fatima ta bashi, cikin kakarsu da suke ya shiga rike da ledar, sallama yayi mamanmu ake zaune tayi tagumi Ta amsa mashi, siblings dinshi na zaune kusa daita duk faces dinsu babu walwala da alaman duk wurin baiyi masu ba, ahankali ya zo ya zauna ya ajiye masu ledar awarar sisters dinshi suka dauka suka bude suna ci,
"Ku dan bamu waje..." Habib ya fada masu, mikewa sukayi suka shiga dakin da kayanshi suke.
"Mamanmu..." Habib ya Kira mahaifiyar shi tare da Kama mata hannu, ahankali ta daga Kai ta kalleshi,
"Mamanmu kiyi hakuri...banason ranki ya baci...Wallahi mamanmu kome nayi Don ke nayi...mamanmu banason in zama danda duniya zasuyi Allah wadarai da haihuwata da kika yi...mamanmu ki saki jikinki Dan Allah..." Yafada mata,
"Modibbo ni ka fadamin abinda ke faruwa...Wallahi hankalina sai fi kwanciya in kin fadamin..." Ahankali ya girgiza Kai yana cewa
"Mamanmu in na fada Maki mutuwa zanyi...mamanmu Dan Allah ki bar tambayata...kawai ki yi min adua kamar yanda kika Saba don ko Yanzu nasan aduar ki ce yasa na dawo gareki lafiya...kinji mamanmu..." Ajiyan zuciya mahaifiyar shi ta saki tace
"Ina kuka je Dan Allah..."
"Mamanmu Dan Allah ki bar tambayata...kiyi min alkawarin bazaki Kara tambayata ba pls..." Yafada yana kokarin kuka,, ahankali ta daga mashi Kai, murmushi ya saki yana goge hawayen da suka taru eyes dinshi yace
"Mamanmu ki saki ranki...kindai San bazan taba yin Abunda zai bata maki ba...mamanmu Dan Allah ki dingayi min adua..."
"Modibbo sai dai in Kara..amma kullum cikn yi maku adua nake...kullum fatana Allah ya tsaremin ku a duk inda kuke..." Tafada Tana rike da hannunshi,
"Nagode mamanmu...inda za'a bani damar dawowa duniya da kuma damar zabar mahaifiya..Wallahi mamanmu bazan zabi kowa ba saike...kin chanchanci yabo mamanmu...nagode mamanmu..." Mamanmu fashewa tayi da kuka Jin yanda habib ke magana, ahankali habib ya daga hannunshi ya Dora kan face dinta yana cewa
"Dan Allah mamanmu kar kiyi hawaye..."
"to ka bar wannan maganar da kake..Wallahi kashe min jiki kake..."
"Tou na daina mamanmu...bazan Kara ba...kawai kiyi min aduar kar wani Abu ya same ni Dan Allah..." Yafada yana hawaye, mamanmu sumbatar hannunshi tayi tace
,"modibbo indai a wannan cikin nan nawa ka zauna wata tara...tou babu abinda zai sameka sai da yardar Allah ....babu Wanda yaisa ya cutarmin da Kai muddin Allah na amsar rokon bayinsa....yanda bana cikakken bacci saboda yarana babu wani azzalumi da zai cutar dakai...kaji kou ka kwantar da hankalinka..." Tafada still shedding tears, rungume ta yayi yana kuka, he's feeling nobody will step into inda yaje ya rayu without doing what they wanted him to do,
"Mamanmu Ina sonki da yawa...banason rabuwa dake..." Ya fada cikin matsanacin kuka,
"Ba zamu rabu ba sai lokacin da Allah ya kaddara...Sannan bana fatan binne da sai dai da ya binne ni..." Tafada Tana Shafa bayan kanshi, saida yayi kuka ya koshi Sannan ya daga Kai daga shoulder dinta yana goge swollen and red eyes dinshi, mikewa yayi ya shiga dakin da yake, yana shiga ya cikaro da wannan same yard da zoben kan mat daya kwana, afirgice ya koma gefe daya but did not come outside Don kar ya sake tadawa mom dinshi hankali, aduar ya farayi, sai da ya Kai karshen aduar ya tofa kan Kayan nan take sukayi disappearing, kan tabarman ya zauna yana tsinewa alhji idris daya saka a wannan matsalar, ajiyan zuciya ya saki yana aduar Allah ya kare su safwan Don shi duk ya da yake tsoron kar su kasheshi hankalinshi yafi tashi in tuna da su safwan, yasan in har sun yi yanda suka sasu rayuwar su will be one of misery, bag dinshi ya dauko ya bude ya dauki sauran kudin ya fito, wajen mamanmu ya dawo ya Kama hannunta Sannan ya Dora sauran kudin cikin hannunta tare dacewa
"Mamanmu...ga sauran kudin...nasan kin iya Sanaa...ki..." Bai karasa ba ta watsa mashi harara tare dacewa
"Kana hauka né?.. Ya zaayi ka dauki kudi ka bani alhalin kaine tamkar uba ga yanuwanka?.....ni me zanyi da kudi in har kana fita ka kawo?.. Dan Allah ka rike su ka juya Allah ya sa masu albarka..." Mamanmu Ta fada Tana maida mashi kudin, idanuwa ya lumshe hawaye na taruwa yace
"Mamanmu naji...amma ki rike wajen ki har nan da sati biyu sai ki bani..." Yafada hawaye na gangarowa daga idanuwanshi,
"Aa Kai dai ka rikesu..." Tafada Tana mamakin why he's like this,
"Mamanmu Dan Allah ki rikesu...nan da sati biyu kin bani..sai in nemi abinda zanyi dasu..." Yafada cikin kuka,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...modibbo Dan Allah meye haka?... Meke faruwa Dan Allah?.."
"Mamanmu kinyi min alkawarin bazaki sake tambayata ba...nidai kawai ki rikesu .zan amsa in lokacin danace maki yayi..Ina and tsoron in kashe su..." Yafada yana goge face dinshi,
"Modibbo nasan Baka da kashe kudi...amma tunda ka nace in rikesu kawo.." Ta fada Sannan Ta amshe kudin daga hannunshi,
Yanzu ya zaayi muci abunci...tunda dai kasan ba kullum zasu cigaba
Book Chapters
Chapter 9
Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500