You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
sai da yaji tsigan jikinshi na tashi, sufwan kam babu abinda yake mamaki sai yanda he's having the same feeling for the second time shima habib da sufwan same thing sukeji, basusan suna Jin exactly yanda dabba keji idan yaga mahauci ba, duk Dan Adam daya taba cin naman mutum one look you will have a strange. my friends when ever you look at someone and feel strange there's something wrong with the person, so be careful and be warned, bayan kaman minti daya aka shigo da tray din abinci Mai raI da lafiya aka jera a dining,
"Ku tashi kuci abinci..." Ya umarce su, duk daga Kai sukayi suka sake kalli junansu suka sadda Kai kasa, dariya alhaji yayi Sannan yace
"Aa wannan Abu haka kaman ba maza ba?... Kar dai kuyi disappointing Dina...Don kallon Maza nayi maku shiyasa nakeson Baku chance...in kuma ba mazan bane the tou in hakura..." Bai karasa ba suka Mike da sauri kaman wasu yara, dariya ya zauna yana yi cikin ranshi yana in tunanin if This guys are capable of what he have in mind for them, zama sukayi zuciyar su na dar dar suka fara zuba Abincin da tunda suke basu taba ganin abinci Mai kyau a face kaman shi ba Sannan kamshinta ma is making them salivating,
"Ku saki jiki kuci ku koshi..." Alhaji idris Yafada masu, daya daga cikin masu aiki ta dauko plate ta zuba masu white rice sai ta bi da miyan dayasha Nama followed by coslow sai a wata karamar bowl ta zubawa kowannensu chicken pepper sauce, cup ya dauko ta zubawa kowannensu juice Sannan ta ajiye robar ruwa Mai sanyi da cup gefe, fita tayi ya bar falon shima alhaji idris ya mike yana cewa
"Bari in watsa ruwa...and remember to feel at home Don Yanzu mun zama daya..." Yafada yana Kama hanyar daya daga cikin kofofin dake nan falon, yana barin dakin suka fara waigawa Sannan habib yace
"Ni Wallahi kamshin Abincin nan ya cika min ciki..." Yafada in form of whisper,
"Amma mutane suna hutawa mu kuma we're struggling for survival.." Sufwan yafada yana kallon pepper soup dake gabanshi yana tururi,
"Ai Wallahi ko daga yau bazan Kara samun irin wannan Abincin ba sai na cinye tas..." Inji usman dake daukan spoon,
"Yanzu hankalina ya fara kwantawa compared to before..." Inji habib
"Nima tunda na fara ganin mutane a gidan naji saurki...sai dai the feeling..." Sufwan bai karasa ba usman ya Dora mashi hannu a baki yana cewa
"He might be listening...kunsan irin wannan gidan have lots of securities..kilan ma da akwai camera kan dining din nan bamu sani ba..." Usman ya fada cikin rada, da sauri suka fara kallon dining dake salki
"You may be right..." Habib ya fada. Sannan ya Kara da cewa
"Eat in silence..." Yafada yana daukan spoon din, coslow dake saman Abincin ya maida gefe yana cewa
" am not going to eat this..." Yafada yana dariya kasa kasa, sufwan kallon shi yay yace
"Wallahi dukda ban taba ci ba ban barin komai...ai da koyo ake zama perfect..." Yafada yana deban rice da coslow, yana kaiwa baki ya tauna yana sauraron taste din, idanuwa ya lumshe yana cewa
"Kai Alhamdulillah...dadi yayi Wallahi..." Yafada cikin santi, dariya sukayi duk Wanda ya Kai Abincin nan baki sai ya saki santi Jin abinda bai taba ji ba, ahaka suka cinye Abincin tas,kowannensu jingina yayi da kujeran dining yana lumshe idanuwa kaman zasuyi bacci, ya sanyi ac dake ratsa su.
Alhaji idris na shiga dakinshi ya saki dariya, dariya Wanda bansan meaning dinshi ba, bakin gado ya zauna yana lumshe idanuwa yana tunani, he's thoughts are so hard to read, sai da ya gama tunanin da yake ya Mike ya shiga bathroom yayi wanka ya fito daure da towel, kwantawa yayi kan gado ya cigaba da tunani,
"There's nothing to regret about it...no regrets no going backwards..." Yafada yana Shafa zoben dake hannunshi, kwantawa yayi still saying
"No regrets no going backwards..." Ya sake chanting kaman yanda sukeyi a chan cult. Sai da ya tabbatar sun cinye sun huta ya Mike ya saka jallabiya ya fito falo, tun daga nesa yaga duk sun Dora Kai a table din dining da alaman zasuyi bacci ko sun fara bacci, sallama yayi in a calm manner sukayi saurin daga Kai, idanuwansu da suka Chanza kala ya kalla ya Dan saki dariya yace
"Da alaman bacci zakuyi..." Mikewa sukayi tsaye sufwan yace
"No sir..." Bai karasa ba alhaji yace
"No you're free in zakuyi bacci da akwai wurin da za'a kaiku ku huta Ai..."
"Aa sir...we're alright..." Habib ya fada mashi cikn biyayya, zama alhaji yayi suma suka dawo falon suka zauna kasar dakin a gabanshi,
"Alhaji mungode...Allah ya biyaka..." Usman Yafada mashi, hannu alhaji ya daga mashi Sannan yace
"Haba Banda godiya pls...now inason ku bani tarihin rayuwar ku..." Ya tambaye su, sufwan né ya fara da bashi labarin rayuwar shi bai boye mashi komai ba, ahankali alhaji ya girgiza Kai cikin ban tausayi Sannan ya juya ga habib shima habib ya bashi nashi tarihin in details shima he sai da alhaji ya tausaya mashi Sannan ya koma ga usman Shima ya bada nashi in details sai da ya Kai aya Sannan alhaji yace
"Kungani haka rayuwar take...babu Mai taimakonka sai ka tashi ka taimaki kanka...ko ni nan inda ban taimaki Kaina ba da kilan Ina cikin masu yawon maula...mutane Yanzu basu taimakon kowa sai kansu...one have to be strong and strong heartened before you can make it...ni Yanzu tambayan da zanyi maku shine how ready are you to make it?.." Ya tambayesu idanuwanshi kansu..."
"Very ready..." Usman Yafada Sannan sufwan da habib suka ce
"We're ready to make it sir..." Cikin Jin dadi ya kada Kai tare dacewa
"What lengths are you ready to go to be rich?.. Nasan kunsan yanda talaucin yake so kun shirya yin kudi beyond your imagination?.." Ya sake tambayan su, da sauri suka daga mashi Kai cikin Jin dadi,
"Inason Inji kunce we're not ready..." Yafada masu cikin Karin karfin gwiwa
"We're ready sir..." Suka amsa mashi gabaki dayansu,
"Are you ready to say bye bye to poverty?.." Ya sake tambayan su cikin karfi
"Yes sir..." Suka amsa mashi da karfi,
"That's the spirit...tunda kunason kudi you will make it...za'a ji sunanku koina...zaku fita daga cikin kunshin talauci...zaku maida kasar wajen tamkar bathroom dinku...zaku hadu da duk Wanda kukaso gani without delay or obstacles...kome kukeso zaku samu...you will have money at your fingertips...kawai I want to ask if you will do anything to get all I just said..." Su sufwan da already sun fara hangan kansu cikin arziki suka cewa
"Yes sir..." Suka fada in chorus saboda yanda alhaji idris ke maganar kudi makes them wants to have it all, they don't want to know what's involved, su dai kawai a nuna masu hanyar da zasu samu kudi, kowannensu tunanin da suke shine ya zasuyi rayuwa when the money has arrived, sufwan is thinking of ya tada alhaji Ibrahim daga unguwar ya sa a fashe gidasshi ya ginawa mahaifiyar shi makeken mansion Sannan ya auri yarshi yaci ubanta son ranshi kuma ubanta yay magana yasa a zane shi, Sannan ya bude wurin tallafawa talakawa mussanman matasa da basu da abunyi, shi kuma habib kawai babu tunanin dayake sai yanda sai maida mahaifiyar shi gimbiyar mata idan yayi kudi, zai gida mata gida babba da maaikata kala kala har da masu yi mata massage, shi kam usman babu inda yake hangan kanshi sai a different countries irin Paris, London da sauran su, kawai yana hango kanshi da wata classy elegant lady a biggest shopping mall in the world suna shopping, idanuwa suka lumshe duk komai yayi disappearing tunda kudin basu zo ba
"Sir pls a bamu aikin..." Sufwan yafada cikin rawar jiki, dariya alhaji idris yay yace
"Relax sons..ai tunda Allah yasa you're willing then kun gama kudi...kilan ma if you're smarter than me kuzo kufini kudi tunda ku matasa né...zaku iya kawo more income fiye Dani..."
"Wallahi sir zamuyi aiki fiye da yanda kake tunani..Wallahi we will make you proud...you will never regret knowing us..." Habib Yafada cikin excitement, Don Yanzu babu fargaba ko daya a kanshi, all he want is the wealth, he never thought of being so rich sai Yanzu, kawai gani yake he's willing yayi komai just to be filthy rich,
"I know you will make proud...kawai Ina ganin ku naga ambitious guys...guys that have suffered a lot and that are ready to make it...you guys are lucky..." Shuru sukayi suna kallon shi, kawai suna tunanin in ya gama maganar da zaiyi masu zai fada masu aikin da zasuyi Wanda zai sa suyi kudi sosai, mikewa yay ya shiga ciki yau fito da kudi kaman na jiya kallon shi suka dingayi har ya dawo ya zauna, na farko ya makiwa sufwan, da rarrafe sufwan yaje ya amsa tare dayi mashi godiya, daya ya mikawa habib shima ya amsa yayi godiya Sannan ya bawa usman shima yayi godiya,
"Yanzu kuje ku fara Shan shagalinku..." Yafada masu sounding like the real man that he is, surprise look né kwance kan face dinsu,
"Sir yau she zamu fara aikin?.." Sufwan tambayeshi cikin girmamawa, Dan murmushi Alhaji ya saki saboda bashi da right da zai fada masu exactly abinda zasuyi sai dai grandmaster Yafada masu da kanshi Sannan basu da daman ganinshi sai karshen wani watan,
"Sai karshen wata zai kaiku inda za'a Baku aikin...kawai alkwari daya nakeson kuyi min..kuyi min alkwarin you will do anything to send away the poverty in your life..." Da sauri sukace
"Munyi maka alkwari sir,,."
"Very good,,,one day you will thank me...Sannan billions of guys out there will do anything to be lucky as you...Don haka kuje amma every week ku dinga zuwa kuna amsar up keep money..." Yafada masu cikin farin ciki, da sauri suka durkusa suna yi mashi godiya, nuna masu yayi kawai su godewa Allah da ya basu saa suka hadu dashi, mikewa sukayi suka fita shi kuma yayi relaxing yana cewa
"Grandmaster...am fulfilling your dreams...you asked for more people from the north...am giving mine..." Yafada cike da farin ciki.
Su habib na fita suka kalli masu roko dake cike da Kofar gidan, baisu ce komai ba har suka bar wajen,
"Nikam am still surprised..wai haka yake bawa mutane Kodai mu kadai ya bawa?.." Habib ya fada sounding so inquisitive
"Wai Kai what's your problem?.. Bakaji yace we're lucky ba?.. Sannan bakaji yace he's looking for guys that have suffered life that are willing to do anything ba?.." Usman ya fada cike da Jin haushin habib, tsayawa sufwan yayi yace
"Wai meye anything da yake magana...anything like what?.." Sufwan yafada yana tsaye rike da waist dinshi,
"Dan Allah can you guys allow us to enjoy this moment...ai daga nan ka fito Yanzu...da sai ka tambayeshi...after all in kunyi hakuri zamuga aikin da zamuyi ..." Usman Yafada ya sake amsawa sufwan cikin fushi, basu Kara cewa komai ba har suka bar unguwar suka, suna dab da fita daga cikin unguwar sukaga wannan motar yanmatan gidan alhaji idris sun dawo,
"Wallahi inayin kudi sai na auri daya daga cikin wannan yan biyun..." Usman Yafada yana lumshe idanuwa, kallon shi sufwan da habib sukayi suka kwace da dariya
"Kana kallon kanka kuwa?.." Sufwan yafada cikin dariya, harara usman ya watsa mashi Sannan yace
"Ai ba Yanzu nace ba...cewa nayi in nayi kudi..." Yafada cikin Jin haushin shi, dariya suka sukeyi Sannan sufwan yace
"Banga laifinka ba Wallahi..Don ko ni ina da nawa plans din..." Yafada atakaice
"What is yours?.." Habib ya tambayeshi cikin sanyinmurya,
"It comes with revenge on alhaji Ibrahim's family..."
"Hmm Kai dai babu ruwanka dashi...ko iyalanshi..." Inji habib, habib bai Karasa ba sufwan yace
"Nikam ke da ruwa dashi...ai he's my neighbor...kasan duk halin da muka fada yau Mutumin nan yana da nashi kason?.. Remember yana da halin da zai taimaka mana amma kememe Mutumin nan yaki...he's so greedy...kuma you know greedy people always pay for their greedy attitude..." Sufwan ya fada cikin bacin rai kaman he knows something big is about to happen in their lives,
"Ai kuma he's not the only rich man da bai taimaka mana ba.., remember ba shi kadai bane wurin Wanda mukaje néman taimako ya hanamu...your own uncle refused the o helps us...balle wani neighbors.." Habib Bai karasa ba sufwan yace
"Shi kuma kawu musa must pay dearly ..ni banason maganar shi saboda it always reminds me of my late young sisters....ya zaayi in mance da daukan fansa kan Wanda yana ji yana gani yaki taimaka mana da kudin hospital din sick sisters Dina?..hmmm kawai a bar maganar..." Sufwan yafada cikin tsananin bacin rai,
"Kawai dai Allah yasa mu samu aikin tukun...I pray he shouldn't change his mind..." Usman Yafada,
"Kuma Allah yasa aikin ya zama alkhairi a garemu...in kam ba alkhairi bane Allah yasa fasa..." Inji habib, dariya usman yayi yace
"Ka taba ganin aikin da ba alkhairi bane?.. Nadai San ba sata zai samu ba..."
"Kudai kuce ameen..." Habib Yafada mashi atakaice,
"Ameen.." Suka amsa kaman basu son magana.
"Nidai Yanzu ga shawara..me sai Hana Yanzu mu shiga gari mu Dan fantama?.. Mu samo new clothes da yanmata?.. At least mun samu wajen zuwa Zance...." Inji usman
"Great idea..." Habib ya fada, adaidaita suka tsaida sai cikin kasuwa. Shopping sukayi Don sai da kowannensu ya kashewa kanshi wajen 30k, Sannan suka sayi turmin atampa guda biyar each Don su Kai gida ga iyayen su, shi kam usman shadda guda biyu ya sayawa dad dinshi, suna kan hanyar su tadawowa gida suka hadu da uncle din sufwan wato elder brother din babanshi, gaidashi sukayi yayi saurin kauda Kai kaman bai gansu ba.
A gida kam mahaifiyar habib is still inquisitive about inda habib ke samu kudi Don zaunar dashi tayi kaman wani small boy Tana interrogating dinshi. Shi kuma ya nuna mata ta kwantar da hankalinta it's their time to shine, ba Don taso ba ta amshi Kayan, nan take ya bata kudi yace ta Kai a dinka mata uku sisters dinshi su kuma a dinka masu biyun.
A gidansu sufwan kuma mahaifiyar shi bata wani damu da source of money din ba...kawai it should keep coming ko ya wace hanya ce, babu nuna godiya babu adua, all she's thinking shine yau cigaba da kawowa Sannan Tana ganin ya samu aiki baison fada mata gaskiya ita kuma since she's not the kind of mother that will call her son down and aske the truth she don't care, all she knows is itace mahaifiyar shi and she right and total control over him.
A week later nana ta fara registration a school, kudi dad dinta ya bata ta sayi abubuwan da take bukata ta ge ta sayi Kayan gayu, though basu da tsada amma suna da kyau in their own way, kawarta Maryam sai mamakin irin halin nana kawai take, she's thinking anya karatu zatayi?, saboda nana itama Maryam ta nemi ta zauna hostel saboda komai nasu tare sukeyi.
Su habib kuma yau suka sake komawa gidan alhaji idris kaman yanda yace su dawo su amshi kudi, yauma same talks about readiness and will ya dinga fada masu, one thing about him shine in yana fada maka maganar kudi you will want to jump and get it by fire by force saboda he will show you money si the only joy and happiness in life,
"Ku yi duk abinda kukeso Sannan babu Mai hanaku even the filthy hukuma will be at your beck and call, ..."Yafada masu sai da yaga yana Jan raayinsu sosai ya sake dauko kudi ya basu, yauma 100k ya bawa each of them, godiya sukayi mashi as usual suka tafi.
, abinka da Wanda yake ganin kudi in two weeks suka fara chnazawa, some of their peer group suna wondering abinda ke faruwa, saboda the change was becoming rapid, mahaifiyar habib Sam bata da kwanciyar hankali saboda yanda habib ke shiga da fita cikin kudi, but mahaifiyar safwan never asked for once were the goodies are coming from. Ita kawai ya kawo ta amshe.Ahaka dai wata daya yayi alhaji idris ya kirasu gidanshi ya shaida masu su shirya zasuyi tafiya gobe. Cikin farin ciki suka Mike saboda they can't wait for o start working because they want the real cash.
Nan na kawo karshen free pages dina, for those that are interested should pay 200 through 0024878383 stanbic and show their screenshot to 08106102727 via whatsapp or ku tura card na 250 to 08106102727 via whatsapp, abinda yasa nace card 250 is that masu bank transfer Ana charging dinsu over 50 naira. And pls in har kika turo kudinki then kin dauki amanar bazakiyi sharing ba, in kuma kinsan baki iya rike amana then pls don't send because the moment you send it means you accept. And remember every reasonable person know that 200 or 250 ba kudin sayan novel bane, you should know that kudin da zaki biya it's just for reading, pls don't share my novel because if you do na Barki da Allah. Inda hakkina kanki Allah zai bimin. Nagode da irin hadin Kai da kuka bani a baya, when others were busy saying all sorts of things ku kuma were busy showing me love, Allah yayi maku fiye da yanda kuka yi min. Nagode.
Plsssss share.6❤💜💙💛💚
Sirrin wasu gayun
💜💛💙❤💚
® zuwairat (ummumaryam)
6⃣
Don't read if you didn't pay
Dedicated to my anty...bani da bakin gode maki sai dai ince rabbi ya biya bukata.w
Cikin farin ciki suka isa unguwar su, kowa gida ya nufa babu tunanin da suke sai Allah ya kaisu gobe su fara aiki, sallama sufwan yayi a Kofar shiga gida Inna dake zaune tsakar gida tana kulla manja ta amsa mashi kaman batason magana, wurin ta ya karaso ya durkusa ya gaidata, amsawa tayi bata daga Kai ba,
"Inna..." Ya kirata
"Naam..." Ta amsa mashi concentrating on what she's doing,
" Inna gobe zamuyi tafiya da alhaji..." Ya fada mata cikin natsuwa, ahankali Ta daga Kai ta kalleshi Sannan tace
"Zuwa Ina?.." Ta tambayeshi Tana gyara Kayan Sanaar ta saboda ya sun she's doing good business a cikn gida da kudin da safwan ya kawo
" Inna Nima ban sani ba..amma aiki zamu fara..." Yafada mata yana durkushe nan kan kafarshi,
"Tou shikenan...amma in kana da sauran kudi ka kawo saboda ban san ranar dawowar ka ba..." Tafada cikin natsuwa babu fada, ahankali ya saka hannu cikin aljihunshi in a fiddo wasu mint din 1k guda talatin making 30k daga cikin sauran na last week da alhaji idris ya basu ya mika mata, tsaya kallon kudin tayi kaman kashi Sannan tace
"Gaskiya wannan yayi kadan,..rai kusan nawa ke da akwai gidan nan?.. Ko ya kudin sanaar kake son in fara tabawa...ka Karo..." Tafada Tana maida mashi na hannunta, hannu ya sake sawa ya Karo 5k ya mika mata, fixgewa tayi Tana cewa
"Lallai Dan nan...Kai dai mugun marowaci zaayi...kudin tinjim a jikinka amma sai na roka ka bani...duk wahalal Dana sha da Kai ka mance...shine zakayi min rowa..." Ahankali ya lumshe idanuwa tare dacewa
"Inna Wallahi ba rowa nake maki ba...kinga sauran kudin" Yafada yana fiddo Wanda basu wushe 8k ba Sannan yace
"Kinga Inna tafiya zamuyi...ban San inda wurin zai kasance ba...shiyasa na adana...amma kiyi hakuri...in sauran kikeso gasu..." Yafada yana mika mata sauran kudin, to he's surprised sai yaga ta amshesu Tana cewa
"Nasan kana da sauran kudi...kawai Raina min hankali zakayi...Kai Wallahi nasan in Kayi aure bazan ci moriyarka ba..." Tafada cikin matsanacin fada, safwan zama yayi yana kallon ta, he can't believe she just collect all he has on him,
"Yanzu Inna bazaki bani komai ba?.." Ya fada gwanin ban tausayi, daga Kai tayi is a watsa mashi harara Sannan tace
"Dalla rufemin baki...nasan kana da sauran kudi da yawa..."
"Wallahi Inna bani da ko sisi..sauransu kenan..." Yafada kaman zaiyi mata kuka, asiyace ta fito daga cikin kitchen tace
"Inna ki bash mana...shifa ya nemo kudin...Don ka kinyi saa yana baki?.." Aikam Bata karasa ba ta dauki shoe dinta ta wulla mata Tana cewa
"Kinci ubanki?.. Dan ubanki kinzo néman wani Abu wajena kiga yanda zan gurguri burouban ki...Dan ubanki in banyi tsaye kanshi ba kina ganin ko na abinci zamu samu?.." Inna ta fada cikin tsananin fada, ahankali safwan ya Mike ya je wajen sister dinshi dake tsaye Tana Shafa inda Inna ta jefa yace
"Ba komai sister..zan samu kudi wajen su habib..." Yafada yana rike shoulder dinta, yarinyar turo baki tayi without saying a word,
"Munafuki..." Inna ta fada Tana kallon shi, ahankali ya dawo ya sake durkusawa gabanta Sannan yace
"Nidai Inna pls inda abinda nayi maki ki fadamin...a da Ina tunanin Don ban kawo komai gida né kike Jin haushi na..amma Yanzu na Lura ba haka bane...Dan Allah Inna ki fadamin laifina da ko sau daya bazaki bude baki kiyi min adua ba..." Wani irin kallon Inna ta watsa mashi Sannan tace
"Lallai ma yaron nan...ni zaka bude baki ka fadawa wannan maganar...ni zaka fadawa ban yu maka adua?... Ni da na durkusa na haifeka kake cewa inayi maka ba daidai ba?.." Da sauri safwan yace
"Inna kiyi hakuri,...ba haka nake nufi ba...naga kullum maman habib cikin yi mashi adua take ko a gaban mu...amma ke ba kiyi min...ko da dagani sai ke ban taba Jin kinyi min adua ba...Ni kuma Inna inason Jin kina yi min adua..." Tsoki Inna taja tace
"In Banda abinda Ai wasu basu da alkunya...in ba haka ba meye na tisa yaro gaba ka nayi mashi adua?.. " safwan kallon ta yayi yana wondering why she's like this yaji Tana cewa
"In da banyi maka adua zaka kawo Yanzu?..ko so kka ince zo nan zanyi maka adua?.." Ahankali safwan ya girgiza Kai Sannan yace
"Kiyi hakuri..." Yafada yana mikewa, banza Inna tayi dashi bata ce komai ba alaman she's still angry with him. Fita yayi daga gidan ya koma dakinshi da Yanzu ya Chanza katifa da curtains, kwanciya yayi yana tunanin rayuwa, he don't know abinda zaiyi Don ya farantawa mahaifiyar shi, komai ya samu jikinshi rawa yaje ya Kai mata amma ko good word bata bashi balle tayi binciken inda yake samo kudi, kullum yana Jin dadin yanda mahaifiyar habib ke maida duk hankalinta kan alamranshi kaman shi kadai ta Haifa, tunda alhaji idris ya fara basu kudi duk sanda ya shiga gidan sai ta kirashi Ta tambayeshi dalilin dayasa ake basu kudi. Amma mom dinshi bata damu ba. He's sure ko yau ya mutu she won't miss him.
Shi kam habib daya fadawa mom dinshi zasuyi tafiya ta rufe Ido tace batasan zancen ba,
"Babu inda zakaje..." Mamanmu tafadawa habib sounding so frank.
"Haba mamanmu...ai ba wani waje zanje ba...aiki zamu fara..ko kina son in cigaba da yawon néman aiki kaman yanda nayi a baya?.." Bai karasa ba ta girgiza mashi Kai tare dacewa
"Sam ba haka bane modibbo...kawai ni banson tafiyar..Sam hankalina bai kwanta da shi ba...gaskiya ko kadan hankalina bai kwanta da aikin ba...Kai ni in son sanuna né kar ka Kara zuwa wajen wannan Mutumin Mai Baku kudi...Sam banaso..." Tafada babu wasa, ajiyan zuciya shi habib ya saki Don shi kanshi bai son zuwa but something still keep pushing him, yasan ba komai ke pushing dinshi ba illah the way he suffered for survival, ko kadan bai son komawa gidan jiya, when no body is willing to help, when they will trek for miles with dusty legs, when they slept with hunger...shi ya Riga ya ga muguntar mutane na rashin taimakon talakawa, he don't want to go back there ever again, shiyasa yake suppressing duk feeling da yake samu game da alhaji idris yake dannewa kaman bai damu ba
"Mamanmu Ai aiki zamuyi...Sannan nay Mai alkwarin bazanyi abinda bakiso ba...kindai San bazamu abinda ya sabawa irin tarbiyar da kika bani ba...bazan taba yin abinda zai munana maki ba..pls mamanmu ki fahimce ni..." Yafada mata kaman zaiyi kuka, ahankali mahaifiyar shi ta girgiza Kai Tana cewa
"Ba haka bane...nidai kawai jikina baiyi min dadi...Wallahi ban taba Jin abinda nakeji kwanan nan ba...inayin adua amma kuma wannan damuwar yaki gushewa...inajin kaman wani Abu zai faruwa ..." Da sauri habib yace
"Mamanmu kina kashe min jiki...in kuma bakinso nayi aiki shikenan...bazan je ba tunda kinson in dinga maula..babu matsala zan dinga samun kudi wajen su safwan da usman..." Yafada yana jingina da bango,
"Aa ba haka bane...ni bazan zama uwa Mai bakin ciki da samuwar danda ta haifa ba...kaje...Allah ya tsare min ka...Allah ya bada saa..." Dan murmushi ya saki
Book Chapters
Chapter 5
Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500