You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
da bamu abinci ba..." Mamanmu tayi adding,
"babu matsala..zan amshi dubu goma Inje wajen kawu sai yasa a rakani kasuwa in sayo Kayan abinda zamuci..." Yafada mata, dubu ashirin dake kan kudin ya amsa ya fara counting mamanmu tace
"Dan Allah ka rike wannan koda zaka bukaci wani Abu..., " Ta fada mashi m bai Kara cewa komai ba ya tura cikin aljihunshi, ya Mike ya fice daga yar karamar gidan.
Safwan na dawowa daga inda aka Kai yarinyar makwancinta ya shiga dakinshi ya debo kudi masu uban yawa Sannan ya turasu cikin aljihunshi ya fita daga cikin dakin ya maida kofa ya kulle, cikin gida ya shiga ya tarda Inna na hura wuta while sister dinshi Tana wanke wanke, hannu ya saka cikin aljihunshi ya debo wannan kudin da bai sani ko nawa né ba ya mika mata, da sauri ta daga Kai tace
,"ya uwa Dan albarka...ko kaifa,.." Ta amshi kudin tana mikewa,
"Ki dafa abunci ki Kai gidan rasuwa...zan fita..." Yafada mata, bata fuska tayi tace
,in na dafa abinci cikin wannan kudin ai sun kare,.." Tafada alaman she don't want to cook from the money, idanuwa yayi rolling Sannan ya sake saka hannu cikin aljihunshi ya debo wasu kudin yace
,"ya isa ko a Kara?.." Ya tambayeta Kai tsaye, da sauri ta sake amshe kudin Tana cewa
"Nayi maneji..." Tafada kaman kudin basu isheta ba,
"yaya wannan kudin haka kaman banki?.." Kanwarshi tafada mashi, daure face yayi baice komai ba ya fice daga gidan, bai Kara cewa komai ba ya fice daga cikinshi, what he saw scares the hell out of him, habiba ce ya gani tsaye cikin dakinshi sanye da Kaya fari tas from head to toe ihu ya saki da karfi yana fita daga dakin da gudu.
Shima usman was successful wajen kiran wata cousin dinshi yayi yace tazo zai aiketa, the same thing da safwan yayiwa wannan yarinyar shima yayi mata.11💜💚💛❤️💙
Sirrin wasu gayun
💜💛💙💚❤️
® zuwairat (ummumaryam)
1️⃣1️⃣
Don't read if you didn't pay, if you do you owe me.
Karki karanta baki biya ba Don in kin karanta kin biyoni
Dedicated to my anty. May all the good things comes your way.ameen
Da ihu safwan ya shiga cikin gidansu mutane dake zaune waje kalleshi sukayi amma dayake taki daya yayi ya shiga gida babu Wanda yasan if he's really shouting ko kuma kawai kunnen su né, Inna dake zaune Tana arranging kudin da safwan ya bata Don tasan exact amount din tayi saurin daga Kai ganin mutum da gudu, da sauri itama ta Mike tana cewa
"Biyo ka akayi?.." Ta fada Tana kallon zaure ko zata ga mutum amma ba komai, safwan dake nishi saboda tashin hankali sai leka Kofar waje yake,
"Na shiga uku..." Ya fada cikin tsananin tashin hankali, sister dinshi rikeshi tayi yana tambayar
"Yaya lafiya..." Ta tambayeshi itama Tana kallon waje, Inna ma Tana gama leko zaure taga babu kowa ta juyo gareshi Tana cewa
"Nace ubanwa ya biyo ka?" Ta tambayeshi sounding so angry, nishi kawai safwan yake saboda tunda aka haifeshi he has never been this frightened,
'"Wai Dan ubanka bazaka fadi abinda ke damunka ba?.." Ta daka amshi tsawa, sister dinshi rikeshi tayi Tana cewa
"Inna ki bishi a hankali mana...baki ganin ki magana bai iyawa..." Bata karasa ba Inna ta dungureta a goshi Tana cewa
"Dalla rufemin baki ..." Ta fada Sannan ta sake juyawa ga safwan da har lokacin idanuwanshi Kofar shiga gidan yana ganin kaman zaiga habiba,
"Wai ba da kaineke ba.." Ta daka mashi tsawa, ko jinta baiyi balle ya amsa mata, nishi kawai yake, tsoki Inna taja ta koma baya ta zauna ta inda take in the first place ta cigaba da counting kudi ta hankalinta jwnace, jiki na rawa safwan ya koma ya zauna nan kasa sai sakin ajiyan zuciya kawai yake, yanda ya zaro idanuwa is a thing that calls for concern amma Inna zama tayi Tana gyara kudin Tana counting kaman ba danta bane zaune duk ya fita hayyacinshi, ahankali sister dinshi ta durkusa ta Dora hannu a shoulder dinshi yayi saurin Jan baya yana kallon ta, alaman he's frightened of her touch
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun yaya Dan Allah me ya faru... Gamo kayi?.." Ta tambayeshi cikin kulawa, Inna daga Kai tayi ta kallesu ta saki tsoki ta maida hankali kan abinda takeyi, safwan kallon sister dinshi yayi da red eyes dinshi ya ce
"asiya..." Ya Kira sunan ta kaman bashi ba,
"Naam yaya..." Ta amsa mashi hannunta kan shoulder dinshi,
"Dan Allah dauko min wayata..." Yafada still panting,
"Yana Ina?.." Ta tambayeshi,
"Dakina..." Ya amsa mata atakaice, mikewa yarinyar tayi ta shiga ciki ta dauko hijab dinta daga cikin daki Sannan ta Kama hanyar waje, har ta Kai bakin zaure safwan ya tuna da da kudin dake dakin sai yace
"Minti daya na baki kidawo...wayar Tana kan katifata,...in kin dauko ki kullemin Kofar..." Yafada mata, Inna daga Kai tayi ta kalleshi tace
"Ko ma meke damunka kanka kadai zai kare..." Tafada mashi Tana kallon yanda ya susuce, daure fuska yayi tare da kauda kanshi gefe, bayan kaman minti daya da rabi yajita shuru,
"Asiya!!!" Yafada da karfi kar taje tayi mashi bincike, sake kallon shi Inna tayi ta Galla mashi harara ya dauke kanshi, da sauri asiya ta fito rike da wayar ta kulle Kofar ta shigo cikin gidan
"Dan uwarki me kika tsayayi cikin dakin?" Ya daka mata tsawa
"Kai dai atakaice so kake ka zageni kou?.." Inna ta fada sounding angry, ko kallon inda take baiyi ba yacigaba dacewa
"Baki jina da uwarki?.." Ya sake daka mata tsawa, rawar jiki asiya ta farayi Don tunda take bata taba ganin yayanta haka ba, Inna kam Kama baki tayi Tana salati,
"Yaya mukullin na nema.." Asiya Ta fada jikin cracking voice, harara ya watsa mata tare da Inna Sannan ya mika mata hannu yana cewa
"Kinga kowa dakin?.." Ya tambayeta, sauri ta girgiza mashi Kai Tana takowa ta ajiye wayar da makullin dakin a hannunshi Sannan ta juya, har lokacin bata daina tunanin halin safwan ba, tunda suke dashi bai taba zaginta ba sai yau, Sannan bai yarda ayi zagi a inda yake amma yau sau gashi yana Burma mata zagi, Dan juyowa tayi ta kalleshi suka hada Ido ya zaro mata idanuwa tare dacewa
"What?.." Ya sake daka mata tsawa, bata San yana da manyan idanuwa ba sai yau, yanda ya zaro idanwaun tamkar zasu fito waje, da sauri ta dauke kanta gabanta na faduwa, Inna girgiza Kai tayi Tana watsa mashi kallon haushi da takaici, number alhaji idris yayi dailing yana mikewa domin shiga dakin Inna, yana kaiwa bakin Kofar ta tayi saurin cewa
"Wallahi kar ka sake ka shigar min dakin Dan ubanka..." Ta fada a fusace, baki ya tabe ya juya ya shiga dakin su asiya ya zauna kasa yana jiran alhaji idris yayi piçking calls dinshi, har ta tsinke bai daga ba, tsoki safwan yaja yana cewa
"Dalla banza pick up..you just got me messed up..." Ya fada yana sake dailing number dinshi, saida ta kusa tsinkewa Sannan alhaji idris yayi piçking
"Alhaji I saw the girl I used..." Ya fada voice dinshi na rawa, dariya alhaji idris yayi Sannan yace
"Relax..wannan ba wani Abu bane...dole tayi hunting Dinka..."
"Inna lillahi...you have finished me,,,.you know spirit will hunt me amma you don't bother to tell me...now what am I going to do..." Yafada cikin tsananin tashin hankali Sannan yana maganar a cikin harshen turanci don kar kowa yaji,
"I said you should relax..." Alhaji idris ya fada sufwan bai Bari ya karasa ba ya daka mashi tsawa dacewa
"The hell I should relax...am telling you i saw a ghost and busy telling me to relax..." Yafada cikin ihu Wanda yasa Inna da asiya kallon junansu,
"Kai stop shouting at me...kar ka Kara..." Alhaji idris Yafada sounding angry, idanuwa safwan yayi rolling Sannan yace
"Sorry..am disturbed that why..."
"then ka jira kaji abinda zance maka...she will go away...but if you keep on getting scared you might run mad..." Idanuwa safwan ya zaro Jin an ambaci madness
"You have finished me,,," Safwan Yafada yana kokarin kuka,
"Haba just relax..." Harara safwan ya watsawa wayar yana kokarin maida hawaye dake neman zubo mashi
"Show you don't care about her...It's what will show you're ready to be in the brotherhood,...ba'a bukatar matsoraci..it's meant for real men..so just act as if you don't care about her,..." Inji alhaji idris
"We're talking about ghosts here...how can I be a man with a ghost..." Yafada yana Danasanin yin Abunda yayi
"If you're not scared of her she will go away...remember the enjoyment with money in our possession...remember the classy things you can do with money...and on the other side remember where you will be sleeping if you run mad...so the choice is yours..." Yafada mash yana kokarin katse wayarshi safwan yayi saurin. Cewa
"Anymore surprise?.." Ya tambayeshi
"No...it's only the first one...daga ita no one will hunt you ever again..."
"ok...then when will you send a driver..." Safwan ya tambayeshi
"Later in the night..." Ya amsa mashi atakaice Sannan ya katse wayarshi, safwan lumshe sai hawaye, at a moment sai yaji kaman an cire mashi yanar face dinshi, he was reflecting on abinda yayiwa habiba, then the other second the thinking was over, goge face dinshi yayi yana cewa
"No to poverty..I absolutely no to poverty...i will never again go backwards..." Yafada face dinshi kaman bai taba dariya ba, sai da ya tabbatar ya goge face dinshi, Sannan ya Mike yau fita daga dakin,. A compound kam ko kallon fuskar kowa baiyi ba balle yaga irin kallon da Inna take mashi, Dakinshi ya koma yana faduwar gaba amma he has promised himself never to be scared again with confidence ya bude Kofar ya shiga ciki she was still there, ko faduwar gaba baiyi ba ya dake ya nufi inda daya daga cikin bag daya saka kudi yaje ya dauki daya, spirit din habiba was still standing by wishing she can revenge what he did to her, ficewa yayi daga cikin dakin ya maida Kofa ya kulle, hanyar gidansu usman yaje ya tardashi zaune yayi tagumi yana jiran shima ya fara ganin alert, yana ganin safwan yayi saurin cewa
"Ina zaka..." Ya tambayeshi,
"hutawa..." Ya amsa mashi atakaice,
"Muje tare...nidai nayi da murja tun dazun Ina jira babu alert..." Dariya safwan yayi yace
"Muje tare mana..." Da sauri usman ya Mike ya sake Kaya suka fita daga unguwar.
Habib né zaune gaban kawunshi yana cewa
"Kawu Dan Allah Ina néman inda ake saida Kayan abinci..." Bai karasa ba kawunshi yace
"Ai Ina da hatsi da masara a rumbu...kawai abinda zaku bukata sai yan shinkafa da sauran yan Kayan da ba'a rasa ba..." Abban Fatima ya amsa mashi, idanuwa Habib ya lumshe yana sakin ajiyan zuciya, he feels so relaxed saboda yasan kawunshi bazai bar mamanmu ta wulakanta ba, hannu ya saka cikin aljihunshi ya dauko 5k ya bashi, surprise look kawun yayi mashi Sannan yace
"Wannan na meye?.." Ya tambayeshi
"Ai kawu kyauta ce daga gareni...kawai ka amsa .." Ahankali kawun ya girgiza Kai yana cewa
"Ka ajiye duk abinda kake dashi,,,nasan Baka da karfin noma..Don haka in lokacin noma yazo sai Kayi da kudin ka..." Kawunshi ya fada mashi, ahankali habib ya Kama hannunshi ya Dora kudin
"Kawu ka rike wannan...ai in Allah ya amince in lokacin yazo bazai gagaremu ba..." Yafa mashi cikin natsuwa, abban Fatima kurawa Carbon copy din elder brother dinshi yayi yace
"Allah ya saka da alkhairi ya tsareka...nagode..." Yafada mashi yana tura kudin a aljihunshi,
"Haba kawu..Don Allah bai kawo aiki bane ba...inda Ina da aiki Ai nauyn ka rataya zaiyi a Kaina..." Habib ya fada cikin sanyinmurya,
"Ai nauyina bazai rataya a kanka ba.,tunda kaima iyali zakayi..wai bari in tambayeka...anyi maka baiko da kowa a birni?.." Ya tambayeshi, sadda Kai kasa habib yayi Sannan ya girgiza Kai,
"Tou nan mu bamu Bari matasan mu su zauna haka nan...Don haka sai ka fara néman yarinyar da zaka aura a garin nan...in Allah ya yarda bazai gageremu ba..." Ya fada mashi, murmushi kawai habib yayi thinking inama he has long way to go da babu abinda zai hanashi auran Fatima his cousin sister, amma Yanzu it's to late for him, tunawa yayi da life ambition dinshi tare da su safwan, they all wanted to make it, suna ganin in har Allah yasa suka gama karatu lafiya Allah zai dubi alamransu ya basu aiki Mai kyau amma aa, Allan's way is always different from man's way,
"naji kayi shuru..Kodai duk garin nan babu wacce tayi maka?.." Da Sauri habib yace
"Aa kawu..kawai Ina tunanin me zan bawa mata tunda bani da aikin yi..." Bai karasa ba kawunshi yace
"Ai indai nan kake abinda zaka bawa mata bazai gagareka ba, sai dai in halin yan binni na kar ya zakayi amma mu nan abinci ba matsalar mu bane...kawai indai da gaske kake nan zaka zauna damu dole ka nemo mata Kayi aure..." Kawunshi ya fada mashi, shuru yayi wani Abu nayi mashi yawo a Kai, kawai he's thinking what if he could get married before ya mutu, yasan it takes only one sex to have a baby, what if he's lucky ya sa matarshi ciki kafin ya mutu, at least he will have a linage,
"Ai kawu ko yau Allah yasa na samu wacce nake so zan aura...sai dai bani da kudi kuma da wuya su yarda su bani yar su tunda bani da komai..." Bai karasa ba kawunshi ya saki dariya yana cewa
"Jairi...tou ka kwantar da hankalinka..mu nan ba sai Mai kudi ake bawa yarinya ba..kawai munfi duba asalin mutum, inda mutum Mai asaline shikenan ..." Da sauri habi yace
"Kawu ko nan da sati guda nakeso zaayi auren?..'" Ya tambayeshi gabanshi yana faduwa all he wants to hear is yes,
"Eh mana..indai an San asalinka ko yau kace kanason yarinya Baka zaayi iyakan ba Lallai ayi mata abubuwa kaman yanda ya Kama ba..." kawunshi ya fada mashi, ajiyan zuciya habib ya saki yana cewa
"Tou kawu misali in inason auren Ina zan ajiyeta tunda bani da gida?.." Ya tambayeshi sounding so anxious, yar dariya kawunshi yayi before saying
"Ga dakuna nan har guda biyu Wanda babu kowa a gidan gwaggo?..ai sai a gyara maku...ni burina a Yanzu shine kayi aure..." Kawunshi Yafada sounding so friendly Don yanda ya natsu yana hira dashi tamkar wasu friends, ajiyan zuciya habib ya saki Sannan yace
"kawu..." Ya Kira shi voice dinshi na cracking,
"Naam modibbo,..." Ya amsa mashi cikin natsuwa
"Indai zaayi mini aure nan da sati daya na amince..." Yafada kan shi kasa, dariya shakiyanshi abban Fatima yayi Sannan yace
"Alhamdulillah...amma meyasa kakeso nan da sati daya?.." Ya tambayeshi, an Shafa bayan Kai habib yayi not knowing what to say, kawai sai abban Fatima yace
"Na gane...a matse kake kou?.." Yafada mashi yana dariya, da sauri habib ya rufe face dinshi yana cewa
"Aa kawu..kawai dai.." Bai karasa ba yace
"naji ba sai ka fadamin ba..Yanzu gaya mun...wa kakeso a wannan kauyen tamu?.." Ya tambayeshi,
"Ai kawu ban San kowa ba...sai..." Sai kuma yayi shuru,
"sai wa?.." Kawunshi ya tambayeshi,
"Kawai dai kawu a bar maganar..."
"Aa bazaa Bari ba...kawai ka fada..ko yar sarkin garin nan ce sai naje na nema maka aurenta..." Ya fada mashi with confidence,
"Hmmm kawu Ai ba sai an je wani wajen ba..." Yafada mashi trying to make him understand amma the dullard man bai gane ba,
"Abin dai ya zama shiririta...in ba'a je waje ba Ina zaa samo maka matar aure?.."
"Ai kawu...ni kawai..." Sai kuma yayi shuru because it feels so heavy,
"Kawai me..Dan Allah kayi magana kaman namiji mana..sai magana kake kaman yanmatan amarya..."
"Fatima..." Habib ya katseshi dashi kanshi kasa,abban Fatima Jin ya ambaci Fatima yasa yayi kasake kaman Wanda ruwa ya cinye, sai chan yace
"Amma Kai sakarene Wallahi..." Habib lumshe idanuwa yayi cikin ranshi yana tunanin Allah bai yarda ba kenan
"Yanzu Fatima ka tsaya yiwa kame kame?.. Kai da yaruwarka?..." Ajiyan zuciya habib ya saki yana dafa chest dinshi,
"Ai auren Fatima saidai Kai ka Hana wani amma ba daina Hana ka ba...Maza tashi kaje ka fadawa mahaifiyar ka yanda mukayi da Kai..ni kuma zan je wajen Mai unguwa mug magana..." Bai karasa ba Habib ya Mike jikinshi na rawa, da sauri a zagaya ya shiga cikin gida, gani yayi babu mamanmu cikin compound sai ya bita har daki, yana shiga ciki ya fada jikinta yana dariya sounding so happy, tureshi mamanmu tayi sai yayi saurin rufe face dinshi kaman mace,
"Ikon Allah...Kai kuma meye haka .." Ta tambayeshi Tana kallon yanda duk ya rufe face dinshi ruf,
"Mamanmu albishirinki..." Yafada still not opening he's face, kallon shi tayi from head to toe tace
"Goro..." Ta amsa mashi duk hankalinta kanshi, Dan bude idanuwa yayi yaga she's looking at him
"Tou mamanmu ki bar kallo na mana..." Ya fada mata yana turo mata baki, sauke idanuwa tayi tace
"Na daina kallonka..." Ta fada mashi kanta kasa,
"Kawu yace...yace...hujmmm.." Yafada Sai kuma ya kasa magana, yanda yake behaving kana iya rantsewa bai taba Shan inuwar ceiling na university ba but he's doing it purposely to please he's mother, yasan Abunda take so, Tana son kunya sosai,
"Dan Allah modibbo me kawu ya fada maka?.." Ta tambayeshi
"Cewa yayi hummmm...yace zaiyi..." Sai kuma yayi shuru, baki mamanmu ta tabe ta juya ta kwanta Tana cewa
"In ka gama hmmmm ka fadamin..." Tafada mashi atakaice,
"Mamanmu yace ..zaiyi mun aure nan da sati daya..." Yafada idanuwanshi duk waje waiting for her reaction, da sauri ta Mike zaune Tana cewa
"Da gaske kake?.." Tafada sounding so happy for her son Don Tana daga cikin iyaye masu shege so suga jikokinsu,
"Eh mamanmu...yace ya bani Fatima...."yafada looking at her face,
"Alhamdulillah...gurina zai cika...Allah nagode maka...Ashe dawowar mu kauye alkhairi né...Allah nagode maka..." Tafada cikn excitement, da sauri ta Mike Ta nufi inda ta boye kudin da ya bata ta daukosu ta mika mashi Tana cewa
"Modibbo gasu ka rike..."
"Aa mamanmu..kawai bani Dari da hamsin ka rike sauran...." Ya fada mata,
"aa ka rike rabi..." Bai Kara yi mata gardama ba ya amshi bundle din 1k guda biyu.
"Mamanmu yace zaa gyara wancan dakuna..." Yafada yana nunasu ta window,
"Kaidai ga kudi hannunka..kayi duk abinda ya kamata.." Mikewa tayi ta bar dakin zuwa dakin gwaggo Don fada mata abinda ake ciki, Tana zuwa ta zayyana mata komai sai taohuwa ta kama guda saboda farin ciki.
Suna fita bakin titi zasu hau adaidaita sai ga mota ta fito daga gidan alhaji Ibrahim, wannan yanmatan gidan alhaji ibrahim zaa Kai school, safwan kallon su kawai yake hannunshi rike da bag din dake shake da kudi Wanda duk Wanda ya gani sai yayi tunanin Kaya né,
"Dan Allah ka rage wannan kallon mana..." Inji usman, baki safwan ya tabe yana aiyana abubuwa da dama cikin ranshi, he has many things to do, the number one abu is learning how to drive a car, then followed by buying a gigantic house sai finally abinda yake tunani shine koyawa mutane da dama hankali, he has so many things a cikin kanshi, adaidaita usman ya tsaida Sannan safwan yace
"Malam kasan wani babban gidan Kaya inda ake saida Kayan gayu cikin garin nan?.." Safwan ya tambayeshi feeling proud
"Eh mana...sosai ku shigo..." Inji Mutumin, adaidaita suka shiga akayi cikin gari dasu, wani makeken stores da ba kowa da kowa ke shiga ba Mai adaidaita ya kaisu shima ba Don ya taba shiga ba kawai dai yana wucewa wajen sometimes and he knows it's for rich people, boutique din ba nakowa da kowa bane, yana ajiyesu safwan ya bude wan bag ya dauko 5k ya mika mashi, godiya Mutumin Ya dinga yi su kuma suka shige without saying a word, baki suka bude suna kallon wannan wajen , da sauri wani matashi ya taso Wai zai amshi bag dake hannun safwan, janye bag din yayi still looking at the place, babu wasting of time suka yi shopping kusan 500k for both him and usman Kayan suka fita dash suka samu wata adaidaita sukace ya kaisu the biggest hotel a gari, shidai Mai adaidaita Bristol ya kaisu suka biyashi, wurin reception sukaje safwan yayi masu booking manyan dakuna guda biyu for a whole week, the thing is kudin dake cikin bag din bai karewa, tamkar suna multiplying, kowannensu dakinshi ya shiga sukayi wanka suka Chanza, no body will say they're from poor families, Don Kayan da suka saka ya amshesu sosai especially safwan dake sanye da carton color combat trouser da navy blue long sleeve, babu Wanda zai gansu ya yarda suna da hannu in any evil thing, restaurants suka shiga sukaci abinci, relaxing safwan yayi yana kallon wasu yanmata guda biyu dake zaune da wani classy dude suma suna cin abinci, biting lips safwan yayi yana kallon bayan wuyar daya daga cikinsu dake sanye da doguwar Mai show me your back, kusan Rabin bayanta a waje yake sai cin abuncin ta take in a classy way,
"Kai wallahi kanason zama na mamajo..." Inji usman dake kallon yanda safwan ya kurawa yarinyar Ido,
"Me yafi Raina...I have done worst in my life...so kawai all I need is pleasure..." Yafada idanuwanshi kan yarinyar, dariya kawai usman yayi yana cewa
"Ni kawai gurina in koma gida in ga millions..." Yafada yana dariya, dariya safwan yayi yana cewa
"I need that girl..." Yafada sounding so naughty,
"Ai she's together with another man..." Usman Yafada mashi, gira daya safwan ya daga yana cewa
"Indai she's not he's wife shikenan..." Yafada yana mikewa,
"Ina zaka?.."
"Just watch me..." Yafada mashi atakaice ya nufi table da suke, cikin kasaita ya isa table din, yana zuwa ya fara mikawa Saurayin hannu suka gaisa kaman abun kirki, yarinyar dayayi targeting daga zarara idanuwanta tayi ta kalleshi, sai lokacin ya gane sister dinshi ce Don suna Kama, he don't know of the other girl,
"Pls Dan uwa minti daya...inason magana da wannan..." Yafada yana nuna wannan yarinyar, ahankali ta sake daga Kai ta kalleshi ta watsa mashi harara Tana kallon shi from head to toe,
"Ke baki ji abinda yace ba?.." Danuwanta ya fada mata
"Yaya am eating for cry out loud.." Tafada sounding angry
"Sorry..I promise ko minti daya it won't take..." Safwan Yafada sounding so innocent, shi brother din yarinyar just like that, tsoki yarinyar da take takama da kanta taja tare da Mikewa, wani irin shuumin murmushi safwan yayi yana juyawa, gefe daya ya ko,a yarinyar ta taka zuwa inda yake tsaye, kwantar da murya yayi Sannan yace
"I want you in my room by 8pm..." Baki yarinyar ta bude zatayi magana yayi saurin cewa
"500k for a night...the room number is 21...if har 8:30 yayi I will assume no deal..." Yarinyar couldn't believe what she's hearing, still zatayi magana yayi saurin cewa
"And San Baki kudin before you step into the room..." Bai jira yaji abinda zata ce ba ya juya abinshi, yarinyar kasa magana tayi, she don't know what to think of, kawai abinda ke yawo cikin kanta is 500k,
"Unbelievable..." Yarinyar ta fada Tana komawa seat dinta, shima safwan komawa yayi inda ya taso,
"What did you tell her?.." Usman ya tambayeshi, murmushi kawai safwan yake without saying a word, itama yarinyar Tana komawa seat dinta kawarta tace
"Me ya fada maki?.."
"Rabu da banza...wai in bashi phone number Dina...ban bashi ba..." Tafada Tana tura abinci daga gabanta alaman she's no more eating the food, juyawa tayi zuwa seat dinsu safwan suka hada ido dashi ya kashe mata Ido daya.
Bayan sallah magrub nana na zaune a dakinsu sanye na wando na Jean but gwanjo that looks good on her sai singlet pink Tana cin abunci while Maryam Tana zaune kan praying mat da alaman ta idar da sallah sai adua take, sallama akayi a bakin Kofar nana ta amsa Tana Kai spoon din indomie bakinta, wata tace ta shigo tace
"Wai big mama tace nana tazo..." Ta fada mata atakaice, da sauri nana ta Mike ta fita Maryam tabi Bayanta da kallo, har dakin su big mama yarinyar ta rakata Sannan ta koma ita kuma nana ta shiga ciki da sallama, amsawa sukayi suna kallon ta, su uku né daya Tana kwnace Tana chatting while Dayan idanuwanta kan Kayan kallo sai big mama Tana zaune, nana Tana shiga ta bude baki saboda ko a cikin gari bata taba ganin daki daya sha Kayan gayu irin nasu ba, komai na dakin looks expensive, cikin respect nana ta gaidasu suka amsa, without wasting of time big mama ta dauko
Book Chapters
Chapter 10
Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500