You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kaman minti biyar sai ya tuna da big mama da yarinyar da zaa kawo mashi, yana tuki ya saki mika sosai sabida yanda ya keji,
Two whole weeks babu mace...this girl is getting a lot tonight.." Yafada yana biting lips dinshi, da kyar ka yarda he's the only one a cikin motar saboda yanda yake murmushi yana magana time to time, wani hold up ya tsaya wata mata itama ta tsaya suna jiran a basu hannu, juyawa tayi taga safwan dake waka da yanda lips dinshi ke moving, zama tayi Tana kallonshi shi bai San tanayi. Ba, matar zata Kai 40 years amma da gani irin yan duniya nan ce, he feels Ana kallon shi yana juyawa suka hada Ido daita, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi Ido daya, murmushi shima ya saki yayi mata alaman kiss da bakinshi cikin ranshi yana tunanin
"End time..." Hannu matar ta Dora mashi a kunne alaman call, shi kuma sai yayi mimicking bakinshi yana cewa
"Number..." Wayarta ta dauko Tana kallon bakinshi yana fada mata number din har ya gama,
"I will call you..." Tafada mashi da alaman bakinta,
"Can't wait..." Ya amsa mata yana tunanin duk balain duniya kudi né sila, yasan ya su inda bashi da komai he's walking on the street babu hajiyas da zata nuna interest a kanshi, amma yanzu that he looks neat, hot, classy, handsome mutane suke throwing kansu gareshi, daman yana Jin Ana maganar sugar mommies, hajiyoyin basu da aure ko kuma suna da aure amma Mazansu basu gamsar dasu, suna néman young guys da zasu dinga servicing dinsu, ji yayi wayrshi tayi Kara ya daga tayi mashi alaman it's her number he should save it, babu musu yayi saving da old bitch daidai lokacin da aka basu hannu, bye yayi mata ya ja motarshi itama ta bar wajen, yana daf da zuwa gidan rasu war ya kashe wakar dake tashi cikin motarshi tare da sauya yanayin face dinshi kaman he's really sympathetic, kofar gidan cike da mutane kala kala da motoci, gefe daya yayi parking ya dauki wannan kudin ya saka a aljihu ya fito face dinshi Sam babu walwala, cikin gidan ya shiga ya wuce zuwa part din uncle dinshi, hmmm safwan na shiga sai ya fashe da kuka sosai Wanda nobody will ever know shi ya kasheta, kuka ya dinga yi har kawunshi ya fara bashi hakuri, babu abinda yake cewa sai he loved her,
"Nasota amma banfada mata ba...wayyo zuciya ta..." Yafada cikin matsanacin kuka, sai da yayi Mai isanshi Sannan ya wanke face dinshi ya shiga part Din mahaifiyar ta, dakin cike da mutane mahaifiyar Aisha na kwance kasa sai fita ake mata ba kuka take ba amma sai nishi take Wanda yafi kuka ciwo, safwan na shiga dakin wata yar yarinyar goye ta fashe da kuka sosai Tana kallon shi, gaisuwa yayi yasan har lokacin gawan Aisha na ciki Ana mata sutura, wata ya tambaya ina baraka ta nuna mashi hanyar dakinta, cikin mutane ya kusa wannan yarinyar sai ihu take kaman taga dodo, daman dodone sai da ba kowa ke gani ba, yana shiga yaga baraka zaune sai kuka take shima sake fashewa yayi da kuka safwan is a real drama king Don yanda yayi kuka ko yan gidan basuyi ba, baraka data hada Kai da gwiwa daga Kai tayi ta kalli safwan da ke kuka, tun shigowanshi kamshin turarenshi ya amshe koina na dakin, ahankali ta daga hannu ta Dora a bayanshi ya daga wet face dinshi ya kalleta,
"Kiyi hakuri baraka...Allah ya jikan Aisha..." Yafada yana Dan satan kallon chest dinta Don bata cikin Kayan kirki, Kayan bacci ta dorawa zani, ,
"Yaya..." kawai baraka ta fada cikin kuka Sai kuma kuka ya kufce mata ta sake Dora Kai kan gwiwarta ta cigaba da kuka kaman ranta zai fita, hanna ya Dora a bayan wuyanta yana shafawa ahankali yana hawaye, mutane dake dakin ba su dauki wani Abu ba kawai sun San he's family saboda yanda yake kuka kanan ranshi zai fita,mikewa yayi ya fita ya koma dakin alhaji musa kawunshi ya mika mashi wannan 400k daya dauko daga same kudi daya sacrificing Aisha, Godiya alhaji musa ya dingayi. Tare dashi aka yiwa Aisha sallah aka kaita, ko kadan bai wani Jin remorse ko fargaba abinda ya aikata gareta, he feel so free and he's at peace, kawai babu abinda yake tunawa sai yarinyar da zaa kawo mashi da dare, kawai daya tunata sai yayi mika tare da biting lips dinshi.
Lokacin da safwan ya bar dakin Inna, Inna zama tayi Tana kallon shi har ya fita, Tana ganin maigadi ya maida gate ya rufe ta fito da sauri ta Kama hanyar part din safwan, Kofar parlor ta isa Tana kokarin budewa taji shi kulle gam, tsayawa tayi ya rasa yanda zatayi ta bude, maigadi na zaune yana kallonta har ta juya zata fita maigadi yace
"Hajiya ki gwada Kofar baya mana..." Ya fada mata,
"Da akwai Kofar baya né?.." Ta tambayeshi,
"Eh mana...yanda naki yake da wata kofa ta wajen kitchen haka wannan am yana da wata Kofar..." Ya fada mata, cikin ranshi yana aduar ta shiga Don taga if da akwai abinda yake boyewa saboda shima tsoron safwan yake kallon daya yake mashi bai Kara samun karfin halin kallon shi, Sannan shi yana sane da duk yan Matan da yake kawowa gidan,
"Ta wajen Ina zanbi?.." Inna dake zaro Idanuwa Ta tambayeshi, nuna mata yayi yana inda yake zaune yanda ko da safwan ya dawo unexpected ba sai shafe shi ba, jiki na rawa Inna ta zagaya ta inda maigadi ya nuna mata sai sauri take gabanta na faduwa, tasan something is fishy about safwan and tanason ganin ko meye da idanuwanta, wannan ihun dataji jiya ya tsaya mata a rai, Tana zagayawa taga kofa ta saka hannu Tana murdawa ya bude, ji tayi gabanta ya mugun faduwa, ahankali ta shiga ciki Tana waige waige, jikinta sai rawa kawai yake, Kai da danka amma kana fargaban shiga inda yake sabida tashin hankali, kitchen ta fara shiga Sannan ta shiga zuwa falonshi, she was surprised da yanayin falonshi kasancewan bata taba shiga falon shi ba sai a ranar in short bata taba shiga part disnhi ba, the last time datayi knocking ya bude bai barta ta shiga ba ya tare bakin Kofar din kar ta shiga ciki,
"Safwan...safwan..safwan...wannan arziki yayi yawa..." Tafada Tana kallon yanda saki shi ke cike da Kayan duniya kala kala, kullum Tana tunanin cikin daula take amma Ashe Wanda safwan ke ciki ya linka nata sau goma,
"wannan yaron ka fara bani tsoro..." Tafada Tana tsaye Tana kallon makeken falon, sai wayar dake kan table, ahankali ta nufi wata kofa ta bude taga gadone amma da gani ba'a taba kwanciya samanshi ba, it looks so new and neat, rufewa tayi Tana Jin sanyi na kamata from no where, ahankali ta Kai bakin Kofar da yake ajiye yadi da bag din kudin shi, kafa daya ta saka a dakin taji kaman an daure mata kafa, lokaci guda taji her blood is on her finger tip, wani irin tsoro né da bata San ko na meye ba ya mamaye zuciyar ta, ji take kaman ta gudu sabida tashin hankali, babu kowa dakin amma it seem so full of people, waige waige ta farayi tayi saurin maida Kofar ta rufe, tunda take bata taba Jin abunda taji ba, her whole body was trembling with fear, she's feeling shivering running down her spine, tamkar Tana mayanka haka take ji, daya Kofar ya sake budewa kudin da ta gani yasa taja baya da sauri har tana faduwa kasa, hannunta Dora kan chest dinta idanuwanta duk waje Tana kallo mint din dake gabanta, kudin ya mugun bata tsoro, daga kan gado har kasar tiles duk kudi né, salati ta farayi Tana mikewa tsaye.
Idanuwa duk waje Tana kallon wannan uban kudin da suka amshe koina na dakin, ko kadan bata kawo wa ranta kudin tsafi bane, kawai ta dauka kilan fashi da makami yake ko kuma kidnapping kasancewan su sukayi yawa Yanzun, bata taba tunanin safwan zai salwantar da rayuwar wani ko wata sabida kudi ba, ko kadan hankalinta bai Kai nan ba, jikinta sai rawa yake saboda yanda dakin shi kanshi na tsoratarwa, ahankali ta maida Kofar ta rufe da hannunta kan chest dinta, sai kalle kalle take Tana juyawa da sauri kaman da akwai wani bayanta. A firgice taso barin dakin ta Kama hanyar kitchen sai wayar dake kan table ya dau ringing, karar wayAr yasa ta Kara firgita ahankali ta juyo ga wayar dake faman Kara, to her surprise sai picture Aisha datayi saving as her screen saver, she was stunned Don har bending tayi Tana kallon wayar dake ringing
"Ai wannan Aisha ce..." Tafada Tana nuna phone din, gabanta né ya sake faduwa da karfi saboda she's thinking me photos din Aisha keyi cikin wannan wayar Sannan Tana tunanin who owns the phone, salati ta farayi Tana tunani kala kala, ahankali ta bar dakin not knowing exactly what to think about, Tana komawa part dinta tayi tagumi Tana tunani
"Inna meye?.. " asiya ta tambayeta , kasa amsa mata tayi Don gani take zai zama abun kunya ita asiya ta rigata gano safwan is into something bad Sannan asiya was trying to tell her amma she won't listen, tasan Yanzu it's a bit late for her amma she have to talk to her son,
Yau kam dr Salem da kanshi ya zo inda rabia take ya dauketa zuwa hospital, bayan sun isa ya dauketa zuwa dakin da ake scanning, shi da kanshi bashine keyin scanning ba sai wasu amma he decided to do it for her himself, bayan sun isa dakin ya umarceta ta kwanta kan gadon, mazurai tafarayi having a negative thoughts, murmushi ya saki yana cewa
"Pls sister relax...dubakizanyi...it won't take time..." Ya fada mata cikin natsuwa, ajiyan zuciya ta saki ta hau kan yar gadon tare da lumshe idanuwa, she regrets wearing gown Don daga rigar ya farayi, da sauri ta bude Ido ta kalleshi,
"Sorry your mistakes..don't wear gown to the scanning room..." Yafada mata, rigar ya daga har sai da yazo wajen cikinta Sannan ya Bari, iska ya fitar Sannan ya juya ga inda suke ajiye man scanning ya dauko ya zubawa cikinta ta Dan saki Kara saboda sanyin abun, maidawa yayi ya rufe Sannan ya dauki Abun scanning ya Dora aci kin yana juyawa ahankali yana juyawa while looking at the scanner, as a doctor bai gane abinda yake gani ba sabida it's too early but abinda yake gani is not one, matsawa yayi kusa da tv din yana kallo sosai har da pointing da finger dinshi trying to count, sai Yanzu ya gane why the pregnancy is coming out fast, baby dake ciki ba daya bane ko biyu, ajiyan zuciya ya saki Wanda yasa rabia bude Ido ta kalleshi Tana cewa
"Da akwai matsala kou?.." Ta tambayeshi Tana kokarin kuka, dariya yayi yace
"Matsala kuma?.. Haba babu matsala...you're alright..." Ya fada mata, Kai ta girgiza mashi daga inda take kwance Tana cewa
"I saw the look in your face...Wallahi da akwai matsala...Dan Allah kar ka damu kanka.?daman nasan yanda nake Shan wahala kan wannan cikin da wuya ace it's normal..." Tafada hawaye na fita daga idanuwa ta, murmushi ya saki tare dacewa
"Hmmm Lallai you're funny...who told you you're in trouble...cikin fa lafiya lau né..sai dai babyn ba daya bane,..." Idanuwa ta zaro Tana cewa
"Ban gane ba..."
"Yan biyu né." Yayi mata karya Don shi kanshi yasan ba biyu ya gani ba amma he can't say the exact number, kawai he prays she made it,
"Doctor biyu fa kace?.." Tafada Tana kuka,
"Yes mana...it's a good thing..." Ya fada yana goge abin gel dake cikinta,
"Yanzu yaran biyu zai Haifa?.. Yaran wannan azzalumin biyu zan Haifa?.."ta fada cikin matsanacin kuka,
"Ki bar kuka mana...komai na rayuwa da akwai reason...ki dauki hakan as your own destiny...tashi in maidaki gida..." Yafada mata nicely, kuka rabia ta dingayi Tana Dana sanin haduwa da safwan, she hates him as much as she hates herself,
"I want to die..." Shine abinda ta fada cikin kuka, hannunta ya Kama ya zaunar daita Sannan yace
"Kinsan da akwai lots of people da suke kashe kansu batare da Allah yasa wani ya hanasu ba, if har Allah bai yarda kin kashe kanki ba then da akwai dalili..Sannan be happy you didn't commit suicide....ya zakiyi da hakkin yaran dake cikin ki...stop crying ki rungumi kadda kinji kou..." Ahankali ta daga mashi Kai,
"Nagode...Allah ya saka da alkhairi...Allah ya yi maka fiye da yanda kayimin...Allah ya jikan mahaifanka..."
"Ameen ameen sister..." Ya amsa mata, ahankali ta sauka ya maida ta gida.
Yau mamanmu ta shiga gidan Abban Fatima tun da sassafe ta mika mashi dubu talatin Wanda zaayi masu Noma daita Sannan tayi mashi sallama kan zata kasiwar Kano Don tayo siyayyar Kayan da tace zata dinga sayarwa, babu musu ya amshi kudin ya kuma yau mata aduar Allah ya maidota lafiya, fita tayi ya koma cikin gida tayi wa Fatima sallama da gwaggo Sannan suka tafi da daughter dinta yar shekara 19.
Big mama kam ta Kai kudinta account kaman yanda ta Saba, tunda take bata taba amsar kudi kan yarinya kaman wannan ba, highest da take samu bai fin 500k shima ciki take sallaman victims dinta sai ta rike sauran, kaman wasa when safwan mentioned sati guda sai tace two million, she was expecting zaice it's not possible amma he's reaction surprised her, ita kanta will like to be with the guy sabida yanda ya hadu, 1.2 ta ajiye a bank ya rage 100k ta nufi kasuwa dashi, supermarket inda ake saida komai har sutura ta shiga ta dauko wasu Arabian gowns guda biyu worth 60k sai oil perfumes na 20k daga nan taje inda suke siyayyar Kayan mata tace a mata magani Mai kyau na sauran 20k din, daga nan ta Kama hanyar hostel, nana kam tasha jinin jikinta sabida yanda gabanta ke faduwa kaman hauka, nana yarinya ce Mara tsoro but yau she's so scare to death, sai biyu Tana shiga bathroom trying ta saka finger dinta a gabanta amma bai shiga amma sai ta tuna namiji zai shigeta a Daren yau, Sannan zatayi har kusan sati daya, dafa chest dinta tayi trying to lessen the beating amma tamkar Tana Kara bugawan zuciyar ta, duk Wanda ya ganta yasan Tana cikin tashin hankali Don dukda the weather is not hot she's sweating, as a human if an saka yin Abu and bakaso or kanasamun doubt kan abun you should forget about it amma nana is so scared but can't say no maybes it's because Tana da Rabon wahala né sabida Abunda tayiwa mahaifiyar ta,Yau taje lectures amma in saa kasheta she don't know abinda aka koyar kawai ta shiga tsaka Mai wuya, wajen 2 ta dawo hostel ganin bata gane komai, dakinsu ta shiga ta watsa ruwa Sannan ya dawo ya kwanta, wajen karfe uku wayarta yayi ringing Ta dauka taga big mama, Dan tsoki taja Sannan tayi piçking,
"Baby kina Ina né?.." Ta tambayeta,
"Cikin daki..?" Ta amsa mata cikin calm voice,
"Oh Ashe kin dawo shine baki shigo ba..kizo I have something for you.." Tafada mata cikin so da kauna, nana bata Kara cewa komai ba ta Mike cikin kasala ta fita zuwa dakin big mama, sallama tayi ta shiga, hannu big mama ta mika mata ta Kama ta jawota kan kafarta, kura mata Ido tayi Tana kallon yanda face dinta ya Dan rame, she did ask about it sabida tasan tada zance né wannan, ledar dake gefenta ta mika mata Tana cewa
"Ki tsaya nan ji saka Kayan nan mu gani..." Ta fada mata, babu musu nana ta sauka daga kan kafarta ta dauki ledar ta bude ta dauko daya saga cikin gown din , yau kam bata yaba kaman yanda ta saba ya bawa ba, kawai she wanted to wear it kan rigar dake jikinta sai big mama tayi saurin cewa
"Baby cire wannan na jikinki mana...kina Jin kunyata né?.." Ta fada cikin zolaya, murmushin karfin Hali ta saki ta ajiye Sannan ta cire doguwar Riga dake jikinta, big mama zama tayi Tana kallon jikin nana dake kyalli kaman madubi, daga ita zai pant and bra, tasan ko makaho ya shafa zai gano yanda take, she's happy safwan won't be disappointed by her choice, Kayan ta dauka ta saka yayi daidai ita, sai da ta gama sawa ta kalli big mama with a formal look Sam babu wanna rawar Kai ko rawar jiki tattare daita,
"Wow baby kinyi kyau...ki saka daya mu gani?.." Ta fada mata, babu musu ta cire wannan ta saka daya shima shima look so beautiful on her, admiring dinta big mama ta dingayi amma nana bata ce komai ba, take way data kawo ta mika mata ta amsa taci kaman spoon uku ta ajiye big mama dai bata tambayeta what's wrong with her balle ta kawo mata excuse, ta lura nana is having a second thought ita kuma she won't let that happen, Tana ajiye sauran abincin big mama ta hada mata hadin magani which will help her have desire for him, in da akwai desire the pain will not be much, babu gardama nana ta amsa ta sha Tana lumshe idanuwa Banda kasala babu Abunda take ji, bayan kaman minti biyar ta kalli big mama tace
"Anty...in Maryam ta fadawa su mamana cewa bana hostel fa?..nasan muddin I leave for a whole week Zataje gidanmu taji how far..." Tafada voice dinta na rawa,
"Ai wannan ba wani Abu bane...kawai you should tell her zaki tafi gida....an kiraki zakuyi wata important tafiya...in kin fada mata sai ki shirya ki tafi bakin gate ki jirani zanzo mu tafi gidana..sai bayan magrub in kaiki gidan..." Big mama ta fada mata atakaice as she's not human,
"Anty am scared..,In ya kashe ni fa..anty ya zaayi ya bani such money just to sleep with me?... Inda haka ake bawa masu kwanciya da Maza Ai da Yanzu babu talauci..."Bata karasa ba big mama tace
"Ai shiyasa nake cewa you're lucky...ai a cikin yanmata ba kowa ke da irin saanki ba....believe me ba kowacce mace zaa bata just 5k just because zaayi sex daita ba...amma ke tashin farko sai ga huge money...if you like daga wannan kar ki Kara shikenan..babu Wanda sai gane..Don haka ki kwantar da hankalinki kinji my dear..." Ahankali nana ta daga mata Kai
"Now tashi ki je ki fada mata zaki tafi gida..." Big mama ta fada mata,
"Bata dawo ba..nimaban gama lecture ba na dawo..."
"Then ki kirata ki fada mata...be fast about it..." Ta fada mata, babu musu nana ta Kira Maryam ta fada mata exactly abinda big mama ta fada mata, Maryam bata zargeta ba tayi mata a dawo lafiya. Fita nana tayi ta saka kaya just like that sai taji she wants to speak to her mother, ahankali ta koma ta zauna tayi dailing nun mamanta, saida ya kusa tsinkewa ta dauka, cikin sanyinmurya nana ta gaisheta, mom dinta was surprised Don nana bata taba Kiranta a waya ba sai yau, ita dai ke Kiranta shima sai ta gandama tayi piçking,
"Meke damunki ?.." Mahaifiyar ta tambayeta Kai tsaye,
"Babu komai...kawai nace in gaisheki né.." Ta fada sounding so calm, abunka da uwa sai sake cewa tayi
"Nana meke damunki?.." Ta sake tambayan ta, dariyar karfin Hali nana ta saki Tana cewa
"Mama Don na Kira kuma laifi nayi ?.. "
"Ba ce kinyi laifi ba..yaya karatu tou?.."
"Lafiya lau...Ina baby?.." Ta tambayi younger sister dinta
"Tana lafiya...kiyi karatu da kyau...banaso excuses..kinji kou.?.sannan banda kawayen banza...Banda kwadayi...kina jina?.." Mahaifiyar ta fada tamkar tasan abinda ke faruwa ,
"Naji mama...sai anjuma..." Tafada mata, Sannan ya saki ajiyan zuciya, she feels like returning the money and run back home, for the very first time dataji she wants to go back home amma sai kuma tuna da classic and luxurious lifestyle that awaits her ta tuna da makeken gidan big mama, she don't know what really comes with it but she wants to have it. Mikewa tayi tare da busar da iska deciding what to do ta fice ya bar hostel din ya koma bakin gate ta jira big mama tazo suka wuce gidan ta.
Thanks33 ❤️💙💚💜💛
Sirrin wasu gayun
💛💚❤️💜💙
® zuwairat (ummumaryam)
3️⃣3️⃣
Don't read if you didn't pay if you do you owe me.
This page contains matured content...read at your own risk.😬💁🏿
Safwan na dawowa gida ya shiga part dinshi , a har gitse ya fito knowing that Inna ta shiga part dinshi, part din Inna ya nufa looking very angry asiya dake zaune falo na hangoshi daga nesa tayi saurin mikewa ta shiga bedroom dinta gabanta na faduwa, banging Kofar yayi ya shiga looking so angry,
"Me ya kaiki bangarena?.." Shine tambayan da yayiwa Inna dake zaune Tana mazurai da idanuwa Don yana shiga duk wannan shirin datayi na in ya dawo zata tambayeshi ya wargaje, kawai ji tayi Tasha jinin jikinta sabida tashin hankali,
"Me ya kaiki bangarena?.." Ya sake tambayan ta looking super duper angry
"Wai...Wai...waya fada maka na shiga bangaren ka?.." Ta tambayeshi sounding so scared kaman ba Dan da ta durkusa ta Haifa bane, wannan love and respect din is gone, sai tsoro da shakka, nunata yayi da yatsa daga inda take zaune yana cewa
"Daga yau sau yau....kar ki kuskura ki Kira shiga bangarena...shiyasa na baki wajen ki daban...wajena daban...in inaso ki shiga inda nake waje daya za samar mana...Don haka ki zauna inda na ajiye ki..." Yafada idanuwanshi rufe ruf Sannna yana nunata da finger kaman zai mareta, yasan in har ya bude idanwau she will definitely run away Don he's so angry and he hates her with passion, Inna dake zaune batasan lokacin da ta fara hawaye ba, she cant believe danta né ke magana haka yana nunata da yatsa kaman zai mareta, daga idanuwa tayi full of tears tace
"Safwan tunda abun ya kawo kazo ka tsaya Kaina Kana yi min ihu bar maka gida zanyi...daman ba kan titi ka dauko ni ba ..." Tafada voice dinta na cracking sabida yanda take hawaye, tsoki safwan yaja yasan she's crying dukda he's eyes are still closed, ,
"Ai Inna nidake mutu ka raba..,duk inda na saka kafa muna tare dake...Wai kin mance Abunda kike cemin?... Kina kirana da sunan matsiyaci...kina cewa kashin talauci gareni kaman mahaifina...kince yanda ubana ya mutu cikin talauci Nima haka zan mutu...sai Yanzu nayi kudi saboda ke kice zaki bar gidan?... Ai you're day dreaming Wallahi...we're in this together...ni dake takalmin kaza ne...babu Mai rabamu sai mutuwa..." Yafada idanuwanshi lumshe amma tears are rolling,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...safwan ban fadi hakan Don ka shiga wani mugun Abu saboda arziki ba..." Bata karasa ba yace
"Inna mugun Abu me nayi saboda kudi?.." Ya tambayeta yanason yasan what she knows because he can't open he's eyes to examine her, shuru Inna tayi Tana kuka, shima hawaye yake amma he's face is as strong as ignite rock, asiya na labe Tana sauraron abinda suke cewa,
"Wallahi in baki bar wajen ba sai na ballaki..." Yafada yana daga Kai zuwa bakin Kofar da asiya ke labe, da sauri ta koma baya hannunta kan bakinta sai kuka take, duk yan cult suna da one ability or the other amma na safwan is so clear sabida anger dake cinshi, he's always angry can only pretend to be happy considering the situation amma when ever he looses it bai da kyauwun gani,
"Inna tambayanki nake..nace wane mugun Abu nake ?."ya sake tambayan ta sounding so hot, cikin kuka Inna tace
"Safwan da ganin kudin da ke dakinka ba na halal bane...." Tafada cikin matsanacin kuka, dariya ya saki tare dacewa
"She have the guts to complain, ..Wai ban gane ba na halal bane?..kin taba zaunar Dani kin bani shawara a matsayinki na uwata?...kin taba ce min Dana kar Kayi kaza kar Kayi kaza?.. Sai Yanzu zaki zauna kiyi magana kaman uwar kirki?... Think again.." Inna Kara volume din kukanta tayi Tana cewa
"Safwan ni kake cewa ba uwar kirki ba?.. Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..."ta fada cikin matsanacin kuka, baki ya tabe Sannan yace
"Oho..Nidai nace kar ki Kara shi har min part...kuma babu inda zaki...kudi né ke zauna kici ki koshi...kaman yanda kike bukata..ai lokacin da nake kawo
Book Chapters
Chapter 31
Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500