You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
haka shima ya sa su gaba ko magana basuyi, Inna bata San gwarjini ba sai kan safwan m Yanzu ko kallon idanuwanshi bata iyayi balle tayi complaining, a da yanda ya shigo gidan babu sallama ba karamin fada zatayi mashi ba amma Yanzu he's presence scares her, bata iya bude baki a gabanshi balle tayi mashi fada, yana bayansu yana latsa wayar hannunshi suka USA bakin titi inda motarshi take, daman basu San ya sayi mota ba Don haka koda yazo daidai motar ya bude motar Inna couldn't hide her surprise anymore
"Kana nufin wannan motar naka né?.." Ta tambayeshi Tana kallon face dinshi cikin duhu,
"Eh..." Ya amsa mata atakaice, asiya kam ji tayi duk jinin jikinta ya kafe, batasan abinda ke damunta ba amma batason zama kusa da safwan, sai sata kallon shi kawai take Tana tsoron kar su hada Ido, haka nan Tana ji a jikinta yayanta is not that good person anymore, tasan something bad has happened amma bazata iya cewa ga abinda ya faru ba, baya ya bude masu without saying a word but he knows they t
Understand abinda yake nufi, tsaye sukayi babu Wanda ya samu courage din shiga motar,
"Dan Allah ku shiga dare nayi..." Ya fada sounding so fed up. Sa sauri asiya ta shiga followed by Inna sai sauran kannenshi,maidawa yayi ya kulle Sannan ya zagaya ya shiga yaja motar ya bar wajen, Inna sai kallon cikin motar take not knowing what to say, asiya kam ta rasa abinda ke mata dadi, tuki ya dingayi ahankali kaman babu komawa cikin motar sai shi sabida they're so quiet, bayan kaman minti goma Inna tace
"Safwan Wai yaushe ka iya tukin mota?.." Ta tambayeshi, he can hear her fear from where he's sitting,
"Ya akayi né Inna...kina tsoron kar in zubdaku né?.." Ya tambayeta yana kallon ta tamirror,
"Aa..kawai Ina...mamaki né..." Ta fada voice dinta na rawa,
"Inna kenan...ai ke baki lura da komai..shiyasa bakisan na iya tukin mota ba..." Ya amsa mata, bata Kara cewa komai ba, tuki ya dingayi ya iso wata snack joint yayi parki ya fita daga cikin mota, kaman asiya Tana jira tayi saurin cewa
"Inna inajin tsoro...yaya yana bani tsoro..." Tafada jikinta na rawa, ajiyan zuciya Inna ta saki Sannan tace
"Kar ki damu in mun je gidan in baiyi mana ba sai mu dawo.." Tafada sounding out of point, idanuwa asiya ta zaro tace
"Yanzu Inna tunanin da kike kenan?.. Baki tunanin ina yaya ya samu kudi ya sayi run wannan katuwar mota Sannan har ya sayi gida?.. Inna bakijin wani iri in kin kalleshi?..Inna tsoron yaya nake ji..,da kyar in San iya zaman gidanshi..." Tafada kaman zatayi kuka,
"Wai ke mene tunanin ki...kina tunanin yana sata né kou wani Abu?..kullum aduar mu Allah ya yaye mana wannan bakin talauci...Yanzu Allah ya rufa mana asiri amma shine kike son kawo wata maganar banza?... Tou ki sani muddin baki zama gidan safwan sai ki nemi wata uwa bani ba..." Inna ta fada mata cikin bacin rai, safwan na daf da shiga ciki ya tsaya yana Jin Abunda asiya take cewa, yayi taki kusan 15 but he can hear her loud and clear, wani irin tamke fuska yayi yana cewa
"Don't let me hurt you...asiya I love you so don't let me hurt you.." Yafada sounding angry,
"Inna Don muna néman arziki bazaisa yaya ya samu kudi rana tsaka mu kiyin bincike ba...ya Kama ta mu bincika aikin da yaya keyi har yayi kudi haka cikin kankanin lokaci..." Asiya ta cigaba da fadawa Inna while safwan na sauraron su,
"Amma wannan yarinyar anyi mayya...Wallahi sai naci ubanki kika Kara magana...ko me ya keyi Ina ruwanki,..ke baki godewa Allah da ba namiji bace ke?.. Kina gida zaa kawo kici...amma din bakin Hali irin naki zaki fara maganar da bai da amfani..shiyasa har Yanzu bakiyi aure ba...duk saaninki sunyi aure suna gidan mazaajen su...to Wallahi ayir dinki...ubanki zanci matsiyaciyar banza..." Inna ta fada cikin matsanacin fada, fashewa da kuka asiya tayi Tana cewa
"Wallahi Inna kiyi bincike...tun ranar da yaya ya dawo daga tafiya ya koma kaman am sauyashi...ya Chanza min sosai...Inna har Mari na yayi kwana kin baya..yaya da bai yarda wani Abu ya taba ni....Inna na rasa ya akayi bakijin abinda nake ji...wannan ba yaya bane...in kuma yaya né to an cire mashi wani Abu Mai amfani..." Bata karasa ba taji sauka. Mari, safwan dake tsaye waje yana Jin su yaji face dinshi da damshi, yana tabawa yaji hawaye, da sauri yasa hannu ya goge, he's so surprised yanda akayi asiya ta gane he's changed tun ranar daya dawo saga tafiya while it's hard for he's own mother to see, he's heart hurts so much yayin da yake Jin asiya Tana cewa bayason abinda zai Taba ta amma just now he's thinking of killing her if har bata daina prying ba, Kai UN
"What the fuck have they done to us..." Yafada new tears na fita idanuwanshi, da sauri ya sake goge su, cikin kuka asiya ta juya ga autarsu Mai suna shamsiya tace
"Yaya bai baki tsoro?.." Ta tambayi yarinyar wacce bata wuce 12 years,
"Nima Ina tsoron shi...." Yar yarinyar ta amsa mata , safwan sake fashewa yayi da kuka, yana ji Inna ta bugi shamsiya Tana cewa
"Wallahi sai kunci ubanku..kar kuja bakinku kuyi shuru..." Tafada masu sounding so pissed off,
"Wai yara basu son karuwar Dan uwar su?.. Lallai ma...", safwan lumshe idanuwa yayi, UVahankali ya sake goge face dinshi Sannan ya taka ya shiga ciki, wasu yanmata né zaune suna Shan ice cream yana shiga suka bishi da kallo, bai ko kalli inda suke ba ya sayi ice creams da pies da sauran su ya fito, daya daga cikin babe din mikewa tayi tabi bayanshi, Tana hi, sai Kara sauri kawai yake saboda baison magana, Tana ganin bai juyo ba ta koma ciki
"You're lucky am in a good mood..." Yafada yana bude motarshi, yana shiga ciki asiya tayi saurin goge face dinta, ajiye ledar yayi ya juya baya tare da kunna hasken motar, asiya boye face dinta tayi Don kar ya ga face dinta,
"Asiya ..." Ya Kira sunan ta,
"Naam..." Ta amsa mashi,
"Kishiga hankalinki...." Yafada mata atakaice Wanda yasa tsoro Kara Kama asiya
"Me akayi?.." Inna ta tambayeshi sounding so surprised Don inadauwnata duka waje,
"Kawai sai ta shiga hankalinta...." Yafada atakaice yana tada motar, Inna kasa motsi tayi saboda yanda yayi maganar ya tabbatar mata yaji komai, hakan ba karamin bata tsoro yayi ba, tasan ko a jikin mota ya tsaya bai kamata yaji abinda suka ce ba, asiya Kara volume din kukanta tayi saboda ko minti daya bata son karawa kusa da safwan, saga inda yake zaune tsoron shi Kara shiga cikinta. Basu isa gidan ba sai wajen karfi 9, har Inna tsoro ya kamata da taga inda ya dosa a wajen gari, kawai sai take tunanin he can never harm them ita kam asiya har ta fidda rai ga rayuwa Don gani take saidasu zaiyi, yana zuwa wajen wannan gidan ya sauka ya bude gate sai leke suke, dawowa yayi ya shiga dasu cikin gidan dake haske kaman ba dare ba saboda solar, komawa yayi ya kulle gate ya dawo ya bude motar yayi tsaye alaman su fito, jiki na rawa Inna ta fito shamsiya ta fito, asiya kam Tana zaune bata da alaman fitowa ta hada Kai da gwiwa sai hawaye take, a fusace ya zagaya ya bude ya fixgo ta waje ya maida Kofar ya rufe, Inna kam baki ta bude Tana kallon inda suke tsaye
"Safwan..." Takira shi kaman Wanda yayi race saboda yanda take nishi, ba Don komai na sai Don shock din abinda ta gani,
"Ku biyoni..." Yafada yana Kama hanyar part dinsu, Inna data rungume hannunta a chest dinta Tana kalle kalle ta fara takawa kaman Ana ingizata, asiya ma daina kuka tayi duk idanuwanta waje Tana kallon wannan gidan, duk jikinta yayi sanyi ta bishi, tasan dole yayanta ya shiga wani mugun Abu da zai samu kudi haka cikin kankanin lokaci, ko kadan bata kawo cultism kanta ba, kawai abinda take tunani is fashi da makamo ko kuma kidnapping tunda su suka fi yawa, yana zuwa bakin Kofar dakin ya bude ya shiga cikin falon daya sha gyara kaman bazaka mutu ba juyowa yayi yaga babu Inna ke kallo sai Italian bulb dake tsakiyar dakin, duk reaction dinsu ya tsaya yana kallon har cikin heart dinsu, kannenshi are happy but Banda asiya, Inna is now scared ya ga hakan a heart dinta,
"Nan né bangaren ku...da akwai dakunan bacci guda hudu kowanne da kewaye ciki, Inna ki dauki daya, asiya ta dauki daya shamsiya da bilki su dauki daya dayan kuma a barwa baki..." Yafada yana kallon face dinsu,
"Inna wannan gidan yayi ko a nemi Wanda yafi wannan?.." Ya tambayeta idanuwanshi kanta, Inna kasa magana tayi balle ta amsa mashi,
"Inna kiyi magana in baiyi maki ba zaa samu wani...Sam banason kina kirana matsiyaci,...Sannan inason in dinga samun aduraki " Yafada kaman zaiyi kuka amma he's face look strong,
"Safwan wannan gidan waye?.." Ta tambayeshi sounding so scared
,"gidana né..." Ya amsa mata atakaice,
"Ina ka samu kudin sayan wannan gida?.." Ta tambayeshi duk idanuwanta waje, murmushi ya saki yana cewa
"Inna. Yanzu ba lokacin tambaya bane...lokacin shagali né...Don haka kiji dadin rayuwa kaman yanda kike bukata...Don ke na zage damtse har nayi kudi haka..." Yafada yana dariyar da bai Kai ko throat dinshi ba, Inna kasa magana tayi Sannan ta kasa moving ko kafarta, fita yayi ya koma cikin mota ya dauko ledar Kayan daya sayo ya dawo ya ajiye masu Sannan yace
"Gashi ...kowa yasha...gobe zan kaiku kasuwa ku sayi duk abinda kuke bukata na abinci ko sawa..." Yafada Sannan ya juya ya bar su nan tsaye, yana kulle Kofar asiya tayi saurin lekawa taga ya nufi makeken part dinshi da sai yayi ukun Wanda suke ciki, sai da ta tabbatar ya shige tace
"Inna mu gudu...Inna mu tafi kafin gobe da safe..Inna Dan Allah kar mu zauna nan..." Ta fada cikin matsanacin tashin hankali, ko kallon ta Inna batayi ba ta dinga takawa ahankali Tana duba falon, ta taba kujerun ta taba kayan kallo,
"This girl..." Safwan ya fada while listening to abinda asiya tace,
"Allah yasa ba mafarki nake ba..." Inna ta fada
"It's not a dream..." Safwan ya fada yana cire Kayan jikinshi, atakaice dai Inna batayi bacci ba Tana tsoron kar ta kwanta ta farka daga mafarkin da take, asiya kam a tsaye ta kwana saboda tsoro. Jinin Dan Adam ba abun wasa bane, gidan da aka saya da kudin blood money will definitely be scary, wani ma ko kusa da gidan yazo sai yaji babu dadi, ita dai asiya she's having a crippy feeling amma Inna is not having such, ita kawai Tana tsoron kar a tadata daga Wannan mafarkin.
The following day safwan bai fito ba sai wajen karfe goma part dinsu ya shiga sanye da jallabiya duk suna zaune falon Inna Tana kwance kasa, idanuwa yayi rolling alaman takaici yace
"Ku tashi mu shiga kasuwa..." Yafada babu sallama babu gaisuwa, idanuwa Inna ta bude tare da mikewa zaune, kallonta yayi yace
"Why kike kwance kasa..." Ya tambayeta, shuru tayi Tana murza idanuwa,
"Ku fito nan da minti ashirin.." Ya fada atakaice, sanna ya fita, Kayan jikinshi ya Chanza ya fito yana tunanin yana bukatar maigadi da Mai aiki, suma fitowa sukayi suka shiga mota suka tafi, wasu irin mahaukatan shopping yayi masu na sutura, shi ya dinga selecting duk abinda yaga zaiyi daidai dasu, daga nan ya sayi Kayan abinci Wanda aka bawa Mai taxi ya biyo su dashi. Gida suka shiga aka shiga da Kaya part din Inna, bilki da shamsiya har waya ya saya masu, itama asiya ya saya mata ta amsa né sabida tsoro amma ba Don zatayi amfani da shi ba, Inna kam duk San abun duniyar ta bata taba hango kanta cikin irin wannan arzikin ba, this is far far more than she bargained for, matar datayi mashi decorations ya Kira ya fada mata yana bukatar Mai aiki data iya aiki da komai na gidan Sai kuma maigadi.Abunka da Mai kudi ko hour biyu baayi ba matar ta aiko driver dinta da wani saurayi sai wata yarinya da bazata wuce 18, safwan kallon yarinyar yayi from head to toe ya Lura Tana da rawar Kai kuma he's ready for.
Two days later safwan yana busy kan Aisha cousin sister dinshi Sannan yana shirin barin kasar, kullum sai sunyi waya yafi na hour yana fada mata how beautiful and grown she have become, yarinyar is so happy and excited yanda yake da sweet words, kullum Abunda yake ce mata is tazo taga gidanshi tunda babu abinda zata ji tsoro tunda su Inna suna. Gidan, sai tace zata zo weekend tare da sister dinta. Sam bai son hakan, he wants to have her first then her sister, ita Aisha Tana da wayau, duk wayar da sukayi da safwan sai ta fadawa mom dinta, ita kuma mahaifiyar ta fadawa alhaji musa, shi kuma he's happy safwan is falling for Aisha yana tunanin zai aureta né,
Inna kuma ya gano ba mafarki take ba it's real, batayi wani kokarin bincike kan business din safwan ba sai da asiya ta matsa mata kan dole ya bincika ko ta gudu daga gidan, safwan na tsane da duk abinda ke faruwa, zaune a falonshi yaji Ana kokarin bude Kofar falonshi, baki ya tabe ya Mike ya zo bakin Kofar ya bude, Inna ce tsaye sai leken falon take shi kuma ya tare Kofar not allowing her come in,
"Safwan inason muyi magana né.." Tafada cikin respect, shuru yayi for a moment Sannan yace
"Maganar me?.." Ya tambayeta Kai tsaye
"In shigo mana..." Tafada taga lekawa
"Aa...me nene..." Ya tambayeta kaman baisan why she's here ba.
"Hmmm daman ni maganar aikin da kake ne...abun né yayi yawa..Wallahi asiya Taki cin komai .." Bai Bari ta karasa ba yace
"Saboda me taki cin abinci ?.."
"Wai arzikin nan naka yana tada mata hankali..." Still Bata karasa ba ya katse ta cewa
"Ai tunda bake yake tadawa hankali ba let me be..ki kiramin asiya..." Yafada atakaice zata bude baki tayi magana ya maida Kofar ya rufe, only God knows how angry he is with her, ko kadan bai kawota Don taji wani dadin rayuwa ko wani Abu ba, no ya kawota né Don ya nuna mata what he's into let's see how she will feel, Inna baki ta bude Tana kallon Kofar, she's so surprised Wai safwan ke behaving haka
"Ko Dan yayi kudi né?.. Oho..." Tafadawa kanta tana tabe baki, kaman kaza da aka tsoma a ruwa Inna ta koma part dinsu, asiya dake zaune da swollen face dinta tace
"Kije yana kiranki..." Tafada mata atakaice, da sauri asiya ya girgiza Kai Tana cewa
"Aa Inna..tsoron zuwa nake..banason daga ni sai shi..." Tafada cikin tsoro,
"Ai sai ki Bari ya zo nan ya sameni..." Ta fada atakaice Tana zama kan cushion, ahankali asiya dake sanye da Wannan Kayan da tazo dasu ta Mike ta fita waje, wannan shine karo nabiyu data fita tun daga part dinsu, ahankali ta nufi nashi part din Tana tafiya ahankali while gabanta na mugun faduwa, Safwan dake zaune mikewa yayi sanin shies coming, Tana zuwa bakin Kofar zatayi knocking ya bude ya jawota ciki, nan ta tsula ihu, wullata yayi tsakar falon ya maida Kofar ya kulle, kallonta yayi from head to toe yaga bata Chanza Kaya ba sanna her face is pretty swollen saboda kuka, belt dake cikin wandon shi ya fara zarewa yana cewa
"Now tell me abinda ke damunki..." Yafada yana zare belt din sauri taja bata Tana crawling Tana kuka tace
"Yaya Dan Allah kar ka dokeni..,Baka Taba dukana ba...Wallahi babu abinda ke damuna..." Ai Bata karasa ba ya zuba mata belt din yana cewa
"Bazaki fada min Abunda kike gani a jikina har kike tsoro na ba?.." Ya fada yana sake daga belt din, asiya najin belt a jikinta ta wani bankare saboda azaba tare da sakin ihu Mara sauti Tana scratching inda ya Zane ta, kasa magana tayi balle ya amsa mashi, ganin ya sake dagawa yasa tayi wuf ta rungume shi gam har zanin jikinta na kwance,
"Free me Dan ubanki..." Yafada yana tureta saboda ya samu daman dukanta amma ta rike shi sosai Tana kuka Tana cewa
"Wallahi yaya zan fada..."
"Good...ki fada in ba haka ba Wallahi yau sai dai a dauki gawarki..." Yafada yana kokarin tureta daga jikinshi,
"Wallahi yaya...haka nan...nakejin..,tsoron ka....Wallahi..yaya..tsoro kake bani..." Tafada cikin matsanacin kuka, tureta takeson yi amma no way ta rike rigarshi ta baya gam,
"Tsoro kou...Bari in baki tsoron Mai dalili..now sakar min rigar..." Yayi commanding dinta, Kim saki tayi ta Kara rikeshi gam Tana cewa
"Ka yi hakuri...Baka Kara bani tsoro...Dan Allah yaya..." Tafada still holding him tight, sakin belt din yayi ya rike mata wuya yana cewa
"Me nayi na tsoro?.." Yafada idanuwanshi da Chanza kala, asiya da taji yana néman aikata lahira ta sakeshi ta dawo ta rike mashi hannu idanuwa waje,
"Me nayi?.." Ya sake tambayan ta da karfi, bata da bakin magana,
"Laifi né burning in hell for you?." Ya fada yana kasa rike wuyar ta sosai, ganin he's close to killing her ya wurgata kan kujera, asiya rike wuyar tayi Tana shure shure kaman zata mutu, komawa yayi ya zauna yana kallon ta sai bayan kaman minti biyar ta dawo idanuwanta duk sunyi ja, kallonta yayi yace
"Kome nayi it's because of you..." Yafada yana dafa bakinshi trying not to cry,
"I anything I do it's for you.." Ya sake fada mata this time sai ya fashe da kuka,
"Ni da nake konewa banyi complain ba sai ku?...." Yafada in parables, asiya duk bata Jin abinda yake cewa, ahankali ya Mike ya koma wajen ta, ja baya tayi daga ita sai Riga da old pant Don tunda ya bugeta da belt wrapper dinta ya kwance, zaninta dake kasa ya dauka ya bata tayi saurin amshewa,
"Asiya bazan taba cutar dake ba...Sannan duk Wanda yayi kokarin cutar dake sai naga bayanshi..Don haka ki bar cewa kina tsoro na..." Yafada cikin sanyinmurya yana hawaye, asiya kasa magana tayi saboda abinda yayi mata few minutes back, kawai Tana Jin yana cewa he can't hurt her, bayan Abunda yayi mata,
"Yanzu kiyi min duk tambayan da kike so..." Yafada sounding calm. Ahankali ta girgiza Kai alaman aa
"Kiyi min duk tambayar dake ranki..."
"Dukana zakayi..." Tafada cikin walaha, Kai ya girgiza mata Sannan yace
"Aa nayi maki alkwarin bazanyi maki komai ba..." Ya shaida mata, zaninta ta daura Sannan tace
"Dan Allah yaya...wane irin aiki ya Baka kudi haka? " tafada cikin fargaba amma she have to say it, shuru safwan yayi ya dafa goshinshi,
"Wallahi yaya gwara talauci ya kashe mu da muci haram komin kankantarta..." Shuru tayi dataga ya daga Kai,
"Kina tunanin Ina wani mugun aiki né?.. Ya tambayeta sounding calm but he's deep angry,
"Aa yaya..." Ta amsa mashi atakaice out of fear,
"Asiya kina ganin zan iya mugun Abu sabida kudi?.." Ya tambayeta sounding so innocent,
"Aa... ,"
"Tou if aa meyasa kike zargina?.." Ya tambayeta Kai tsaye,
"Yaya kudin né sukayi yawa...shiyasa Kayi hakuri..."
"Asiya Dan Allah kar ki Kara yi min wani irin kallo, kisan bana wani mugun Abu, wani company na alhaji idris Mai saa nake aiki, nan na samu kudi na tara na sayi gjda da mota.." Yayi mata karya, he's checking if she believes him amma no,
"Wallahi da gaske nake...in kuma baki yarda ba ki shirya zan kaiki har wajen aikin mu...kinji asiyata..." Yafada cikin rarrashi, ahankali ta girgiza Kai tace
"Yaya na yarda...kilan Don ban saba da kudi haka ba..." Ta fada cikin shessheka, San murmushi ya saki Sannan yace
"Nima...komai ban iya ba...abokan aikina sun iya komai amma Banda ni sabida ni na tashi cikin talauci..." Yafada cikin sanyinmurya,
"Yaya Ai komai talauci tunda Allah yasa Kayi arziki Don haka komai zamu Saba..." Ta fada mashi, murmushi yayi Sannan yace
"Yanzu ki tashi ki koma kiyi wanka ki shirya cikin daya daga cikin Kayan Dana sayo maki...inason ganin kwalliyanki..." Yafada sounding so friendly kaman bashi ya kusa aikata lahira just few minutes back ba, mikewa tayi still holding her neck, mikewa shima ya kamata tare dacewa
"Kiyi hakuri kinji ban Kara tabaki..." Yafada mata, murmushi ta saki Sannan ta daura zaninta da kyau ta fita, Tana fita ya daure face tare dacewa
"Serves you right..,gobe ma tell me you're afraid of me and I will give you something to think of.
Suna dai cikin waya da Aisha har lokacin tafiyarshi Spain yayi kuma tare suka tafiya da rabia Don guduwa tayi daga gidan anty da aka kaita, duk tsaro da aunty dinta ta dinga bata a banza, Ana gobe zasu tafi tabi ta katanga ta dire ta hau motar Kano zuwa hotel room da safwan ya amsar mata , wannan labarin na iske alhaji Ibrahim zuciyar shi ta buga, nan take yayi collapsing akayi hospital dashi.
Shi kuma alhaji idris Yanzu ya fara samun kwanciya Hankali yana tunanin Yanzu safwan bata yaranshi yake ba, he thinks safwan ya fita ba tun yaranshi, one thing bai sani ba is that safwan don't give up easily, he takes what ever he wants he's a desperate person with a desperate majors,.
Sati saya safwan da rabia sukayi a Spain suka dawo suna cikin jirgi ta dinga amai sosai, kafin su isa kasar da zaayi transit ta jagata sosai, ko kadan safwan bai taba tunanin ciki ko wani Abu ba, he was thinking kilan stress né yayi mata yawa kasancewan he used her more than ever, suna sauka hannunshi cikin nata sai magana yake rada mata kan she should be patient har su isa Nigeria kasancewan meeting dinsu gobe, bata ce uffan ba tacigaba da binshi har suka hau wani jirgin zuwa Kano, ganin yanda take ta kokarin amai amma ba komai cikin ta yasa ya samu taxi a kaita hospital shi kuma ya wuce gida. Don shiri tafiya anambra. He's a little bit scared da bai ga habib ba, baisan waje irin hukunci zaa yanke mashi ba.
Tunda habib ya dawo gidan mutum daya da zama bai taba hawan titi ba, he's always by the side of the road, yau kuma alhaji bello da wani amininshi suna kan hanyar katsina Don suyi gaisuwa a gidan governor, kawai kana daga sama aka wullo mutu, before the driver zai taka break it's late, duk mutanen dake zaune mikewa sukayi da gudu ganin abinda ke faruwa, habib né kwance yana shure2 while jini nafita ta kanshi. Cikin tashin hankali alhaji bello da abokinshi dake zaune bayan mota suka fito.26💛💚💜💙❤️
Sirrin wasu gayun
💚💙💜💛❤️
® zuwairat (ummumaryam)
2️⃣6️⃣
Don't read if you didn't pay, if you do you owe me.
Salati alhaji bello yayi yana zagayawa gaban motar, ganin mutum kwance cikin jini yasa ya dauke driver da Mari without knowing when he did it,
"Baka duba gabanka?.." Ya fada cikin tsananin tashin hankali,
"Wallahi...sir ..Kayi hakuri...Nima...kawai kaman an wullomin shi..." Driver ya fada jikinshi na rawa, har lokacin habib bai motsa ba, alhaji bello Dora hannu yayi a Kai not knowing what to do, mutane daga habib sukayi suna bashi taimako ta gaggawa like tare hanyar zubar jini daga kanshi da sauran su, alhaji bello ya kalli baya ya kalli gaba, he don't, know what to do, kaman wani mahaukaci haka ya koma sai kallon mutane kawai yake,
"Ku taimaka kar ya mutu.." Yaji wani yafada cikin tashin hankali, abokinshi né yayi karfin halin cewa
,"Yanzu Ina zamu kaishi...da akwai hospital a nan?.. In munce zamu kaishi wani waje yana iya mutuwa..." Yafada cikin tashin hankali,
"Eh da akwai wani karamin asibiti...a fara kaishi wajen..." Wani ya fada masu, shi kam alhaji bello ko word daya bai Kara cewa ba tun daga maganar datayi wa driver,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Ya fada kaman an fixgo maganar daga bakinshi yana kallon yanda jini ke fita daga kanshi Sannan same jini daga bakinshi, Kayan jikinshi ya kalla yaga he's a typical mad man, Kai ya girgiza yana kallon yanda kusan half mutane dake garin suka taru, baisan yanda akayi ba yaga sunyi hanyar wani waje dashi,
"Ina zaku dashi?.." Ya tambayesu idanuwanshi duk waje saboda tashin hankali m duk Wanda ya ganshi yasan he's so messed up to the brain saboda bai saba da such
Book Chapters
Chapter 25
Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500