ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sannan yayi mata kiss a hannu yana cewa
"Mamanmu kenan...har naji sanyi da kika kwantar da hankalinki..." Baki ta tale with out saying a word, da ganin ta she's not happy. Hannu ya saka cikin aljihunshi ya fiddo kudi kaman dubu ashirin yace
"Mamanmu gashi ki ajiye koda zaki bukaci wani Abu..." Da sauri tace
"Aa..ka ajiye su...Kai ma Ai zaka bukaci kudi..kaida bakasan inda zaka ba?.."
"Aa mamanmu nasan bazan rasa komai ba...ki ajiyesu tunda ce mana yayi mu shirya zamuyi tafiya,,bamu San yaushe zamu dawo ba..banason ki nemi komai ke rasa..." Yafada yana sake mika mata kudin,
"Aa modibbo ...ko wata biyu zakayi bazamuyi ra shi ba ...ka bani kudi kwanakin nan da yawa..ka rike su..." Ta fada mashi cikin so da kulawa,
"Aminatu..." Ya Kira sister dinshi dake wanke wanke, da sauri ta taso, kudin ya mika mata Sannan  yace
"Aminatu ki ajiye koda mamanmu zata bukaci wani Abu ku saya ciki..kinji kou?.." Ahankali ta mika hannu ta amshi kudin tayi cikin daki dashi, kallon mama shi yayi ya saki murmushi yana yace
"Aminatu Dan Allah ki kula da mamanmu sosai...ki kula daita sosai..." Ya fadawa aminatu dake fitowa daga cikn daki, yar dariya mahaifiyar shi tayi tare dacewa
"Wallahi inda Hali dakaje kauye kayi masu sallama..." Bata karasa ba yace
"Gaskiya mamanmu bazan iya zuwa Kauye yau in dawo yau ba...in na dawo zanje gaidasu...daman na dade banga Fatima ba..." Yafada yana dariya,
"Shikenan nan ..." Ta amsa mashi cike da Jin dadi, cikin ranta Tana aduar Allah ya tsare mata danta, ita dai haka take, she always pray for her children, dukda basu da kudi they're her number one priority. We have different variety of parents, wasu kawai sun haifi yara né basu damu da abinda ya shafesu ba sai in abun yayi tsanani, wasu suna sane da duk moves da yaransu sukayi, they study them and know their secrets, haka mahaifiyar habib take she's the exact opposite of mahaifiyar safwan.

Shi kam usman daya fadawa iyayen shi gobe zasu tafi su fara aiki ba karamin farin ciki sukayi ba, suma dai bawani bincike garesu kan yaron su ba, kawai they're happy then son is progressing.

Nana kam hankali ya kwanta tunda ta dawo hostel jiya, su biyu né cikin daki daya ita da Maryam, Banda rawa babu Abunda yake wai she's happy she's away from home, Maryam zama tayi Tana kallon the way she's behaving, tare iyayen su suka ajiyesu suka basu advice kan kar su kuskura suyi ba daidai ba amma nana Tana ji Tanan yana fita through the other side, ita kawai she want to be away from home, yau wani irin dadi take ji ganin gata babu uwa da zata sata wani aikin gida, bayan sun gama breakfast sukayi wanka nana ta fara wanka in a fito daure da zani, wata karamar bag ta dauko ta bude , duk Kayan. Kwalliya ne da perfumes amma Mara tsada né, zama tayi ta tsara kwalliyarta looking breath taking, Maryam na fitowa ta bude baki Tana kallon ta, batace komai ba ta Shafa Mai Sannan ta shirya cikin doguwar Riga ta dauko hijab ta saka ta koma bakin katifa ta zauna Tana jiran nana dake kallon kanta over and over again kaman she's seeing her self for the first time. Saida ta gama ta dauko skirt da Riga Wanda mussanman ta Kai aka Kara sha  mata su ta saka, Maryam kallon yanda Kayan suka dameta Maryam tayi Sannan tace
"Bestie wannan Kayan Wallahi kaman baki saka komai ba..." Maryam Tana fada Tana kallon yanda bombom dinta da shape din jikinta ke waje, juyawa nana tayi ta kalleta from head to toe Sannan tace
"Hmm ke Wallahi da ban mamaki kike...wannan fa damace garemu to be free...bawai wata rayuwa zamuyi Wanda bai kamata ba amma Ai we have to look like a university babes...ko har Yanzu kina tunanin a secondary muke...nan Baka San kowa ba babu Wanda ya San ka...lets be free " Tafada Tana jawo skirt dinta kasa, kallon mamaki Maryam tayi mata tace
"Bestie baki tsoron umma ko abba ta ganki?... Sannan Wallahi irin wannan dressing din zai jawo hankalin mutanen banza kanki..gaskiya bestie ki Chanza Kaya or better still ki saka hijab..." Maryam ta fada mata advisably, baki nana ta tabe Sannan tace
"Pls ki bar min wannan abun...ya zaayi first day a school ki nemi bata min mood Dina?..an fada maki tsoron Allah a saka hijab yake?.. " Tafada sounding so angry, tsoki Maryam taja ta juya Tana cewa
"Wallahi bamu fita tare a haka..." Maryam ta fada Tana barinta tsaye nan dakin, bayan ta nana tabi da harara Sannan taja tsoki Tana cewa
"As if I care....haka nan sai in Kama dressing kaman secondary school girl alhalin Ina university?... No way..." Tafada Tana jujjuyawa, long note daya ta dauko cikin kayanta ta saka cikin yar karamar bag ta fito, wasu yan mata su uku dake sanye da bump shot suka juyo suka kalleta, itama kallon su tayi tare da sakar masu murmushi suma suka maida mata martani, wata daga cikinsu wacce zata Kai 25 ta kalli Bayanta from head to toe, sai da nana ta kulle door dinsu ta bar wajen Sannan tace
"Babes wannan is a new comer kou?.." Babban cikinsu wacce zata Kai 28, fair in complexion da hudan hanci Ta fada hannunta kan cinyarta dake sheki kaman company din Mai ta tambayi sauran,
"Gaskiya I think sune sukazo jiya..." Daya  Ta amsa mata, Dan murmushi babban ta saki Tana kallon bayan nana daga nesa
"Hmmm alhajis will pay lots of money for such babe....kinga slender jikinta kuwa...I personally love her...I think we will get along..." Tafada  Tana lumshe idanuwa, dariya sauran sukayi daya daga cikin su tace
"Big mama kenan....lets watch her and the other new comers..." Wata Ta fada mata Tana mikewa,
"Abeg make I go dress for lectures..." Ta fada Tana mikewa.

Yau né zasu tafi anambra state, kowannensu kwana yayi yana Allah Allah gari ya waye su shirya su Sami alhaji idris a gidashi kaman yanda ya umarcesu, Ana kiran sallah asuba duk suka Mike, safwan fita yayi zuwa cikin gida yayi alwallah is a tafi masjid inda suka hadu da Junansu, gaisawa sukayi kowa ya koma gida Don shiryawa. Cikin sauri sufwan ya dawo gida yay wanka ya shirya cikin wasu new shadda ya Dora da hula looking corporate, wata bag  daya saya ya saka kayanshi kaman kala biyu ya fito lokacin gari ya fara wayewa, cikin gidan ya sake shiga ya yaye labulen Kofar Inna ya shiga ciki, Inna dake zaune kan praying mat ta kalleshi from head to toe Sannan tace
"Amma Kai da son kanka kake...Yanzu wa zai ganka yace daga wannan matsiyacin gidan ka fito?.. Amma mu ka barmu kaman almajirai...gaskiya da akwai sakal..." Dan murmushi ya saki yana cewa
"Inna kar ki samu damuwa...indai kudi ya samu kome kikeso zaki samu..."
"Allah yasa..." Ta amsa mashi atakaice,
"Yanzu zan wuce..."
"Tou a dawo lafiya..." Ta amsa mash , mikewa yayi ya fita zuwa compound, Kofar Dayan dakin yaje yayi sallama sisters dinshi uku suka fito, nan yayi masu sallama Sannan in a fito ya kaman hanyar gidansu usman kasancewan gidansu safwan shine a baya duka, yana zuwa shima usman ya fito shirye cikin Jean da Riga, yayi kyau sosai,ciki safwan ya shiga ya gaida iyayen usman sukayi masu aduar saa Sannan suka fito zuwa gidansu habib, sallama sukayi suka shiga ciki suka ga mamanmu rike da habib sai kuka take kaman wata yarinya, habib najin sallamansu ya juya da red eyes dinshi ya kallesu, ahankali yace
"Kawai ku tafi...ni na fasa zuwa..." Yafada masu, cikin kuka mamanmu tace
"Aa ka tafi...Allah ya karemunka...ya kaiku ya maidoku lafiya...Allah ya kauda idanuwan makiya kanku...kawai zanyi kewarka né..." " Ta fada Tana sakinshi,
"Aa mamanmu...nasan bakison Inyi wannan tafiya...kawai na hakura..Allah zai bani wani aiki...bazan je ba..." Yafada mata sounding firm. Safwan da usman tsayawa sukayi suna kallon su, daman sun San this will happen tunda lokacin da suna school duk sanda zai tafi sai tayi kuka,
"Aa kaje..." Ta fada mashi cikin sanyinmurya Sannan ta juya ga safwan da usman
"Dan Allah ku kula da kanku...Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya...kunji kou?.."
"Ameen..." Suka amsa mata cikin sanyinmurya, safwan kam he's feeling inama shi mom dinshi take ma haka, ciki habib ya shiga ya dauko Dan karamin bag kaman nasu safwan saboda lokaci daya suka sayi shi, wayar safwan né ya fara Kara ya fiddo ta yaga alhaji idris,
"Kayi sauri gashi yana kirana..." Safwan ya fadawa habib Sannan yayi piçking wayar, alhaji idris ya fada mashi he's waiting for them.
Karfe 8:30 suna gidan alhaji idris, bai tsaya bata lokaci ba suka Kama hanya yaja cewa
"Next time ku dinga sauri...tafiyar ba ta nan bace" Yafada yana tuki, safwan  zaune gaba sai habib da usman zaune baya, tunani suke why is he's driver not driving Sannan why bai hau jirgi ba tunda yana cewa it's a very long journey. Babu Mai cewa komai har sukayi tafiya na hours biyar, tsayawa yayi sukaci abinci Sannan suka cigaba da tafiya. Ganin bayan asar suna tafiya yasa gabansu fara faduwa, habib Sufwan kallon habib da usman yayi ta mirror suma suka kalleshi, wayarshi ya dauko daga cikin aljihunshi ya rubuta
"Ina wannan Mutumin zai kaimu?...ka maida wayarka silent kar ya gane..." Ya turawa habib, Jin Kara message yasa habib ya fiddo wayar shi, silent ya maida wayarshi Sannan ya rubuta
""Nima wannan tafiyar is scaring the hell out of me...Kodai mu fada mashi ya tsaya in yaki mu zaneshi?.." Ya turawa safwan, Sannan ya mikewa usman wayarshi Don ganin abinda suke tattaunawa, Sufwan na ganin message din ya saki murmushi Wanda yasa alhaji idris dake tuki ya Dan juyo ya kalleshi,
"Lafiya dai?.." Ya tambayeshi wearing a smile
"Wallahi ba komai.." Safwan ya amsa mashi, Sannan ya rubuta
"Ka ban dariya Wallahi..kawai dai mu tambayeshi inda zamu haka..Don mi Wallahi na gaji..." Ya turawa habib, habib na karantwa ya saki hamma tare da mika Sannan yace
"Ranka shi dade wannan tafiyar tayi nisa da yawa...." Habib Yafadawa alhaji idris, Dan dariya alhaji yayi Sannan yace
"Zaku Saba né...Nima lokacin da aka fara kawoni har fargaban kar a kasheni na dingayi...amma Yanzu na Saba..." Yafada sounding so friendly
" tab gaskiya Nisan is too much..." Usman ya fada mashi
"Ai Dadin abun Baku sake dawowa sai nan da wata daya...kunga da sauki kenan..." Alhaji idris ya fada masu
"Ni Wallahi Ina da kudi kaman Kai ban wannan doguwar tafiya a mota...jirgi zan dinga hawa..." Inji safwan, dariya alhaji idris yayi Sannan yace
"That means you want people to know where you go every month..." Yafada mashi, habib zaiyi magana alhaji yac
"Pls ku barni in maida hankali kan driving...inason mu Kai before 7.." Yafada atakaice, shuru sukayi babu Wanda ya sake cewa komai har suka Isa cikin garin anambra. Hotel daya Saba sauka ya nufa yayi parking, a gajiye suka fito suna kallon hotel din dake walkiya kaman rana, duk Wanda ke wajen babban Mutum né, suna shiga ciki alhaji idris yaje wajen receptionist ya bukaci rooms guda biyu, safwan da habib da usman baki suka bude suna kallon wannan wajen, wani matashi né yazo ya amshi bags dake hannunsu,
"Follow me..." Saurayin ya fada masu, suna dab da juyawa wani babban Mutum ya shigo wajen, dariya alhaji idris ya saki ya nufo Mutumin Wanda da ganin shi he's Yoruba, gaisawa sukayi  Sannan suka Shafa zobensu kaman yanda sukeyi, idanuwa su safwan suka zuba masu suna kallon irin wannan gaisawa, Mutumin Dan lekawa yayi yaga yanda suka zuba masu Ido, kallon alhaji idris yayi ya rada mash wata magana, dariya alhaji yayi Sannan yace
"New recruits..." Ya fada mashi yana kallon su safwan, dariya Yoruba man din yayi da karfi Sannan yace
"Welcome to the world of power..." Mutumin ya fada masu, murmushi suka sakar mashi not understanding what he meant. Baya suna gama gaisawa suka hau upstairs, kafin su shiga dakin alhaji idris yace
"You should relax and rest...za'a kawo maku abinci..." Ya fada yana kokarin shiga nashi dakin
"Sir Ina kibla?.."habib ya tambayeshi, wata direction ya nuna masu sanna ya shige abinshi. Suna shiga duk sukaware idanuwa suna kallon wannan makeken dakin,
"Wanna shine five stars hotel...." Inji safwan dake wulla tired body dinshi kan wata large cushion, 
"Wannan waje abin tsoro né...ya hadu da yawa..." Inji habib,
"Wai wane irin gaisuwa sukayi dazun?.. Abun ya tsaya min a rai..." Inji usman,
"Nima abun ya bani mamaki...kaman na matsafa Wallahi...wai Shafa zobe kan junansu Sannan irin zoben daya..." Inji habib
"Well zato zunubi...muje muyi sallah ..." Safwan ya fada yana mikewa cikin kasala, hanyar wata kofa yabi ya bude yaga makeken gado daya sha duvet cover, 
"Wow....duniyar Hutu..." Safwan ya fada cikin natsuwa, bayanshi habib da usman sukabi sukayi tsaye bakin Kofar suna kallon irin gadon da koma film basu Taba ganin irin ta ba, safwan né ya shiga ciki sukabi bayanshi, wata kofa ya sake budewa yaga bathroom, few minutes later ya fito da alwallah, Sannan habib ya shiga shima fito then usman, daya daga cikin rigarsu suka dauka suka shimfida sukayi sallolin da ake bin su Sannan aka kawo masu abinci Mai rai da lafiya suka zauna nan sukaci, kwanciya sukayi nan kasan carpet, basu farka ba sai wajen Karfe shida na safiya, da gudu suka shiga bathroom sukayi alwallah tare da sallah asuba, Karfe goma aka kawo masu breakfast, bayan sun gama suka koma bakin window suna kallon compound din hotel din,  manyan mutane dake shige da fice suka zubawa Ido, bayan kaman minti goma aka bude kofa, alhaji idris né ya shigo,
"Ku taho mu tafi..." Ya fada masu ,
"Mu dauki bags dinmu?.." Habib ya tambayeshi
"Aa..leave them here...zamu dawo nan Ai..." Ya fada masu,  fitowa sukayi still wearing Kayan da suka zo dasu, inda motarshi take sukaje suka shiga bar wajen, tafiya ya dingayi har suka kaman hanyar dajin da gidan haduwansu yake, dukkan su tashin hankali da tsoro né kwance kan face dinsu,
"Sir Dan Allah ka tsaya...wannan dajin na bani tsoro..."  Habib ya fada cikin tashin hankali, dariya alhaji yayi yac
"Haba be a man mana...ai ku Yanzu Baku da sauran tsoro..sai dai aji tsoron ku ba dai ku kuji na wani ba..." Yafada cikin confidence, bayan kaman minti ashirin da wannan maganar suka hango wata katuwar gida kaman cattle a tsakiyar daji,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..." Duk suka fada atare
"Dan Allah kar kayi mana komai....ka rufa mana asiri..." Safwan ya fada yana kokarin fashewa da kuka, Banda dariya babu Abunda alhaji idris yakeyi
"Haba babu abinda sanyi maku...inda Ina da niyyan cutar daku da tuntuni nayi hakan...kawai I want to give you what any guy out there is hustling to have...money and power..." Yafada yana kaiwa gate din gida, horn yayi sau uku aka bude gate din, motocin da suka gani a compound din ya Kara tada masu hankali, kulle giant gate din akayi alhaji idris yayi parking a available space,  fitowa alhaji idris yayi while su safwan suka makale cikin mota
"I always heard a bad feeling...gashi..." Habib ya fada hawaye na taruwa idanuwanshi, Bai karasa ba yaji alhaji ya bude masu kofa,
"Ku fito mu shiga ciki..." Yafada yana kallon faces dinsu that is all looking so frightening,
"Kuma banson any fuck up..accept anything you're asked to do..." Yafada sounding firm and strong.7💛💜💙💚❤
Sirrin wasu gayun
💜❤💚💛💙


® zuwairat (ummumaryam)



7⃣



Don't   read if you didn't pay

Dedicated to the strongest woman I have ever known, anty Allah ya kare ki daga sharrin masu sharrin.


" mudai if truly Baka da niyyan cutar damu then let us go..." Habib Yafada voice dinshi na breaking,
"I told you bazan cutar daku ba...pls trust me..I want to help you né...pls ku fito mu tafi before the meeting starts..." Ya fada face dinshi babu wasa,
"Ku fito pls you're wasting my time..." Yafada sounding angry, kin fitowa sukayi,
"Do you guys want the hard way?.." Ya tambayesu cikin fada sosai, da sauri habib da har yau fara hawaye ya girgiza Kai, ba komai yake tunawa ba sai mamanmu, shi kawai gani yake he's dead already because he's life is flashing before he's eyes,
"Always trust your Instincts..." Habib ya fada ciki hawaye yana fita daga cikin motar, yana fitowa sufwan da usman da duk suka koma kaman sunga malaikan mutuwa suma suka fito, gaba alhaji idris yayi yana juyowa to make sure suna biye dashi,
"Wallahi tunda na hadu da wannan Mutumin nakejin jikina babu dadi..." Habib ya fada cikin hawaye, safwan goge nashi hawayen yayi Sannan yace
"Nima...amma we all paid deaf ears to our feelings..." Safwan Yafada new tears na taruwa idonshi,
"Way yo mamanmu...who will take care of mamanmu..." Habib ya fada cikin matsanacin kuka yana biye da alhaji idris sauri ganin the meeting is about the o start,
" Ni Wallahi banjin Zzai Kashe mu...kawai ku kwantar da hankalinku....in wani Abu ya samemu our parents know who we followed..." Inji usman,
"Ko sun sani me zasuyi mashi?... Can they even come close to inda yake?.. In yau ya kashe mu ya kashe banza..." Inji safwan, bakin kofa suka isa alhaji idris da face dinshi ke daure kaman bai taba dariya ba ya juyo ya kalli frighten faces dinsu Sannan yace
"Now zaku shiga ciki, remember there's no going back now...duk abinda akace kuyi zaku amsa...kuna jina.. Remember na tambayeku several times what lengths are you ready to go to make money kuka ce to any length...Yanzu it's the time...remember one thing..daga yau you will never be the same..." Yafada yana shiga cikin makeken hall dake dauke da chair and tables, kaman an zare masu veins suma suka shiga, wurin suka gani cike da mutane kaman kasuwa, wasu suna sanye da same uniforms wasu kuma basu saba, gani sukayi duk Wanda bai sa Kayan ba yayi hanyar upstairs, gani sukayi alhaji idris ya bace masu, kalle kalle suka tsaya yi amma babu Wanda ke kallon su, abin mamaki shine da akwai faces da suka sani a politics da musicians, da akwai wani saurayi who is a popular musician da suka gani, Dan matsawakusa da safwan usman yayi yace
"Wannan kaman wannan mawakin?.. Ko kamace?.." Yafada mashi cikin whisper, shuru safwan yayi baice komai ba amma yasan he's the one, fuskokin mutane suka dinga kallo suna mamakin Abunda ke faruwa, the most suprising thing is duk mutanen wurin babu mutanen banza...masu kudi né da ganinsu, Sannan ko kallon inda su safwan ke tsaye basuyi ba duk Wanda ya chanzo Kaya daga upstairs sai ya sauko ya hau kujera,
"I think this is a cult,,." Safwan Yafada tsoro na kwance kan face dinshi,  bayan kaman minti shabiyar duk sukayi settling sanye da same dress as usual sai su safwan da wani saurayi sukayi daban cikinsu. Yan hayaniya ke tashi until babban cikinsu ya sauko, safwan kurawa alhaji idris Ido yayi yaga duk sun Mike tare da kneeling har wannan shugaban yazo ya zauna Sannan suka Mike suka koma suka zauna,  as usual abubuwan da suka Saba sukayi kaman no new faces is looking at them, jinin su safwan kamewa yayi saboda yanda ake presenting kawunan mutane da pants din mata sai abubuwa kala, the most scary part is the giant snake Sannan and yanda wannan katon shugaban yake chnazawa ya ci raw meat, dukkan su tsaye suke amma can't move an inch saboda yanda jikinsu ya mutu, they're having the shock of a life time Don gani suke har su bar dunyi nothing will scare them as this, sai da suka gama Sannan alhaji idris ya Mike daga seat dinshi ya dawo tsakiyar hall din yace
"My lord..we have new members..." Yafadawa shugaban su, ahankali shugaban ya daga idanuwa ya kalli su safwan dake tsaye kaman ruwa ya cinyesu, habib kam tuni hawaye suka kame daga face dinshi saboda tashin hankali, hannu Mutumin  yayi masu, kaman wayanda ake remote controlling suka taka har sai da Mutumin ya sake daga Masu hannu su tsaya suka tsaya, dukkan su nobody have the ability of o think, kawai everything seem so blank, juyawa alhaji idris yayi yace masu
"Kneel..." Babu musu sukayi kneeling,
"You're all welcome to the world of power...affluence...wealth...now I want you to know there's no turning back..." Yafada da karfi yana kallon idanuwansu,
"You will do exactly as you're told...no argument...do you understand what am saying?.." Yafada da karfi, ahankali duk suka daga Kai, inda kasan robot haka suka koma saboda shock, kurawa safwan Ido yayi yana surveying dinshi, he's looking straight into he's soul, sai da ya gama da kallon shi Sannan ya juya ga usman shima yana kallon idanuwanshi, daman ance the eyes are the window to the soul, sai da ya kurawa usman Ido sosai Sannan ya juya ga habib, kallon shi kawai yake yana bata rai,
"You ..." Ya nuna habib, kaman Wanda akayi pinching habib ya firgita
"I smell strong bond...." Yafada idanuwanshi cikin na habib, habib da ko kiftawa bai iyayi sai bakinshi dake kyarma kaman Mai Jin sanyi.

At this same time mamanmu kam ji Tayi Ina ta rasa inda zata saka kanta saboda faduwar gaba, kawai ji tayi gabanta na wani irin mummunar faduwa, ahankali ta Mike ta dauki buta ta shiga bathroom ta Kama ruwa Sannan ta fito tayi alwallah ta Kama sallah, Tana sallah Tana rokon Allah ya kare mata danta a duk inda yake. She's so deep in her prayers
"Ya Allah ka rabamu da mugunji da mugun gani..ya rabbi duk wata hanyar mugunji ka toshe mana shi...rabbi duk inda Dana yake na mika alamranshi a hannunka..rabbi kar ka Bari a cutar dashi..." Kawai she was praying like a real mother should pray for her child, ba kawai Allah yayi maka albarka ba, it's a prayer amma duk danda uwa take zama ta yi adua da suna danta bazai taba tabewa ba, aduar uwa bai taba faduwa banza, go deep in prayers for your children because it's and end time, duk cikin iyayensu everyone is having this feeling but nobody is taking it serious to pray, maman safwan na kwanciya tayi Tana ganin tiredness ke sata Jin some how, amma because of the bond dake tsakanin habib da mahaifiyar shi she felt it from far that her son is in danger, adua ta dingayi Tana kiran sunanshi Tana mika duk alamranshi ga Allah Sannan Tana karawa da sunan safwan da usman,

Achan kam bayan shugaban ya gama enchanting abubuwan yayi stretching hannunshi a gaban safwan, cikin rawar jiki safwan ya Dora hannunshi kan nashi, idanuwa safwan ya lumshe Jin kaman wani Abu na yawo from he's palm to he's body, sakin hannun safwan yayi ya mikawa usman hannun, shima usman Dora mashi hannun yayi he felt something traveling through he's body,  then habib, yana kama hannun habib yayi saurin sakin hannunshi yana mashi wani irin kallo,
"Hmmmmm..." Mutumin ya fada Sannan yace sake cewa
"You're all great....now the rule is you will never say anything to anyone about this place ..if u do you will die... If  you refuse to do what you're asked to do you will die...." Dukkan su kallon shi sukay amma he's power is beyond words Don ko bakin magana basu dashi balle suyi gardama, kaman yayi dominating dinsu haka yake sukeji, komai na jikinsu bai da wani amfani sai abinda akace suyi, hannu shugaban ya daga sama sai ga wasu tiny little cups guda uku abinda ke ciki is so small da sipping daya zakayi ya kare, hannunshi ya mika gabansu sukayi saurin dauka cup din kaman wasu slaves to he's charm,
"Drink..." Yayi commanding din dinsu,  jiki na rawa suka Kai baki suka juye, the expression on their faces is undiscribleable, kowa hadiyewa yayi kaman yana hadiye wuta, habib dafa chest dinshi yayi da karfi duk idanuwanshi da suka Chanza kala sukayi waje, kaman he's struggling for breath, hannunshi biyu rike da chest dinshi ya durkusa nan kasa sai ya fara aman jini, shugaban zaro idanuwa yayi yana kallon shi face Dinshi dauke da damuwa, safwan da usman kura mashi Ido sukayi suna kallon shi amma couldn't help, duk wayanda ke zaune idanuwa suka zaro suna kallon abinda bai taba faruwa ba, habib ya fi minti uku yana wannan aman Sannan ya daina, jini nan kasan inda ya durkusa kaman an yanka rago, kasa mikewa

Please Login or Register in order to submit comment