You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
asuba abban Fatima ya shigo yana tambayan Abunda ya faru yake Jin ihu yau,
,"Dan Allah ku taimaka min...banason rasa modibbo..." Mamanmu Tafada Tana hawaye,
"Wai daman shine ke ihu?... Nayi tunanin ko wani né ko kuma barawo aka kama." Yafada sounding so surprised, kallon habib yayi yana tambayanshi yana cewa
"Me yasa meka?.."
"Kawu mafarki né kawai..." Habib da duk ya rame ya fada mashi
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...aljanu né...bakake..." Yafada yana rike da waist dinshi , ajiyan zuciya habib yayi ya rafka tagumi
"Sunfi aljanu..." Yafada cikin ranshi,
"Rukiya zaa yi mashi...Insha Allah zaa dace..." Kawunshi ya fada, habib dai bayason yi mashi gardama amma yasa nothing can save him now, he feels he's soul is not with him, ko Yanzu da yake zaune yana ji kaman he's in another world, he feels like ya Dora hannu bisa Kai ya dinga ihu ko ya samu sauki,
"Kawu..." Ya Kirashi, amsa mashi yayi Sannan habib yace
"Nidai a bar zancen auren nan..." Bai karasa ba duk mutanen tsakar gida suka saki salati har da gwaggo,
"Amma wannan yaron yana néman haukacewa...in ba hauka ba ka taba ganin an fasa aure Ana kwana biyu daurin aure?.." Gwaggo ta fada cikin bacin rai, hakuri habib ya basu ya Mike jiki babu kwari ya fita daga gidan, shidai kawai he wants nothing, ji yake Jin dadin duniyar na gushe mashi ahankali, yana ji kaman an fixgar wani Abu cikin jikinshi, takawa ya dingayi har ya bar cikin gari ya samu waje ya zauna ya dinga kuka, kawai he's feeling so bad and weak, ko appetite bai dashi kuma bai ci komai ba. Gidan su kam har yanuwa na nesa sun fara zuwa biki kunsan yan kauye da akwai su da zumunci, duk da it was on a short notice bai hanasu zuwa ba, Fatima kam sai shirya ta suke in their own little way, Ana gobe daurin aure akayi jere, it looks so beautiful dukda it's in the villa, Tana da complete set na gado da komai da mutum ke buka na rayuwar yau da kullum, nasiha ake bata kan zaman aure, shi kam habib bai zama gida Yanzu, gari na wayewA yake komawa bayan gari ya zauna ko abinci baici, mamanmu ta shiga damuwata sosai saboda yanda yake komawa, kullum Rama yake then he's acting weird, at times sai ya firgita ya juya da sauri, hakan na Kara tadawa mamanmu hankali, wurin abban Fatima taje ya gaita gidan babban malami a kauyen tayi mashi bayanin abinda ke faruwa dukda bata da details, nan ya ce a dinga zuwa Ana amsar mashi rubutu kullum.
A gidan alhaji bello kam Ana cikin tashin hankali, alhaji bello yana daga cikin yan kasuwa masu néman kudinsu ta hanyar halal, Sannan abun duniya bai rufe mashi Ido ba Don in har yana da million biyar yana iya bada kyauta da rabi, Sannan a sanaar shi bai zalunci bai cin hakkin mutum Sannan yana fita hakkin neighbors dukda a unguwar dayake babu talaka sai masu Hali irinshi, kap family dinshi babu Mai kuka dashi saidai kawai aki shi saboda nasu dalilin, yana da mata daya da yaran shi hudu, yan mata biyu sai Maza biyu, babban danshi is married da Nashi family so is he's second daughter sai na ukun Mai suna shahid than autarshi mufida, duk yaranshi suna da allowance da yake basu har masu auren bai Bari a baya ba, farin cikin shi shine ya gan duk na kusa dashi cikin walwala, he helps lots of people Don in har kayi 5years kana mashi aiki zaiyi settling Dinka to become your own boss, bai yarda da enslaving mutane for a long time ba, ba karamin adua yake samu wajen jamaa ba Don da wuya ya wuce talaka bai taimaka mashi ba, bai siyasa amma most yan siyasa suna kamun kafa dashi saboda yanda yake da jamaa, yanda da arziki da bai kamata yana néman wani Karin kudi ba, kullum matarshi Tana fada mashi he should step down ya huta haka nan because life is short sai yayi murmushi ya amsa mata da
"If I can't spend am sure da akwai people that can spend..If I stop working who will take care of them?.....its better inyi hustling Yanzu ko Allah yasa in huta a Chan..." Wanna shine reply da yake bata duk sanda ta nemi ya rage stressing kanshi, he's rich da yakama ya tara uwayen dukiya amma bai Tara ba, because he normally says
"Wai mutum na iya kwanciya cikin daki biyu at a time?..then why should I keep many houses while da akwai wani da bashi da rabin nawa?..", hakan yasa yana da mansion guda daya tal a garin Kano Sai kuma wasu abroad shima Don kar su nemi masauki da family dinshi in sun fita waje kawai in yaje inda life dinsu is so poor sai yayi choosing lucky ones ya samu contractors su sake masu gida zuwa modern building or in renting kake kana iya Jin an Baka kyautar gida from unknown person, Family dinshi are happy until what happened to mufida, har bayan kwana uku mufida bata iya takawa da legs dinta, she's taking drugs and Doctor yana kula daita a gida amma it's not working, family na tsoron fita daita hospital saboda yanayin case din zai bata masu suna, dad dinta kullum cikin kuka yake saboda wannan bakin cikin, he loves mufida so much, he never knew ita ta Kai kanta despite duk kokarin da yake kanta, tun ranar babu ranar da bata ganin jini, mufida ce kwance kan gado da drip hannunta mahaifiyar ta na zaune gaban gadon, duk Wanda yaga mufida sai ya tausaya mata, duk ta koma kaman baita ba, she looks so pale and weak, kullum babu abinda take cewa sai she's sorry, dad dinta ya hanata cewa sorry amma kullum bata da word daya wuce she's sorry, kawai abinda take tsoro shine in dai ta mutu a haka she's going to hell straight saboda she have everything but was still greedy, dukda Tana da lavish spending dad dinta bai barinta babu kudi amma 500k was huge that she can't turn her back on, gashi 500k ya kaita ya baro ta, she never knew namiji yana iya yiwa mace abinda wannan mugu yayi mata, she don't even know he's name, Yanzu she will give a million to go back to her normal self, kawai ji take inama if she can tell her mother exactly abinda ya faru amma tasan he mom will strangle her to death, idanuwa ta daga ta kalli mahaifiyar ta,
"Mommy..." Ta kirata cikin sanyinmurya,
"Yes dear..."
"A bani pad....yana zubowa..." Tafada mata hawaye na taruwa idonta, ahankali mahaifiyar ta ajiye phone dinta ta taka zuwa inda suke ajiyewa ta dauko mata, daga ind take kwance ta tura pad din gabanta ta Dan matse legs dinta, few minutes later alhaji bello ya shigo da sallama, amsawa sukayi,
"Ki shirya nayi Making arrangements da doctor victor...gobe ku tafi Chan adubata..." Yafadawa matarshi, Tana Jin Doctor victor tasan England né,
"Alhaji Tana iya long flight kuwa" Ta tambayeshi
"she will try..." Ya fada kuka na néman kufce mashi sai ya bar dakin, falo ya koma ya zauna yana cewa
"Who ever have hand in this will know no peace...ya Allah ka sakawa mufida ka sakawa family Dina.....ya rabbi ka wulakanta Wanda ya wulakanta rayuwar mufida..he should suffer more than she's suffering..." Yafada cikin hawaye. Itama mufida kuka ta dingayi Tana Danasanin yanda akayi ta jefa family dinta cikin wannan tashin hankali,
"Am sorry..." Ta furta cikin kuka,
"Wai mufida wannan am sorry din da kike cewa is getting me suspicious...tsakanin ki da Allah kin San Wanda yayi maki wannan abun?.. If you know just say it...or ko ke kika Kai kanki?.. Because I could remember ranar bada amincewa ta kika bar gidan nan ba..." Ta fada idanuwanta kan mufida dake zubar da hawaye kaman tap,
"Aa mommy...kawai Ina bakin ciki halin da kuka shiga né..."
"Aikin banza...baki damu da halin da kika shiga ba sai halin da mu muka shiga?.. You're so undispicable ..." Tafada atakaice, bakinta taja ta rufe kar mom dinta ta gano ta.
Wajen karfe uku safwan né zaune, idanuwanshi kaman ba nashi ba, he look so terrible, ba komai yake tunawa ba sai khairat, he so angry and mad, mikewa yayi ya shiga dakin da ya loda kudi daga na jiya ya debo masu uban yawa ya saka cikin aljihunshi ya bar gidan, unguwar su ya koma, Yanzu Rabon shi da gida kwana hudu kenan, tun daga nesa ake kallon Wanda ya taho cikin mota dake walkiya kaman rana, kallo gabanshi yake hai damu da wayand ke cewa
"Wancan kaman safwan ba..." Duk Wanda ya kalli motar sai ya sake kallonta for the second time, daidai Kofar gidan alhaji Ibrahim yayi parking duk matasa suka taru suna kallon safwan dake fitowa daga cikin mota,
"Ikon Allah...Ashe dai da gaske safwan né..." Inji daya daga cikin su, banza yayi dasu ya maida motar ya kulle tare da saka mata alarm, ya wucesu duk bai mance dasu ba, most of them ya nemi taimako daga garesu when he needed them most babu Wanda ya bashi komai sai excuses, yanda ya kure parking din babu Wanda zai iya shiga da mota ko fita daita cikin gidan alhaji Ibrahim, daf da gate din yayi parking. Ahankali ya taka ya gangara cikin unguwar zuwa hanyar gidansu kasancewan mota bata shiga wurin, hannunshi cikin aljihunshi yana tafiya cikin kasaita kaman he's not born and brought up here, yana zuwa gidan su Habib ya tsaya yana kallon gidan, he felt something amma it's just for a second, wucewa yayi kaman he feels nothing, asiyace ta hangeshi daga nesa, tsayawa tayi Tana kallon shi sai taga kaman bashi ba, he's face its somehow, hakan nan he scares her, yana daf da zuwa inda take tayi saurin shigewa ciki, daddaure fuska yayi ya shiga gidan ko sallama babu balle ya gaida Inna dake kitchen
"Asiya..." Yafada da karfi, da gudu ta fito daga cikin daki jikinta na rawa
"Baki ganni ba?.." Ya tambayeta kaman bai taba dariya ba, Inna mikewa tayi Tana kallon ikon Allah Don tamkar bata wajen,
"Yaya...ban..." Aikam Bata karasa ba ya dauketa damari, idanuwa Inna tazaro Tana cewa
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...safwan..." Tfada Tana rike asiya, afusace ya juya gareta yana cewa
"Wai Dan uwarta Tana ganina amma sai ta wani wuce kaman bata San ni ba?.. Tana hauka?.. Ko ni mate dinta né?.."
"Inna banganeshi bane..." Asiya Ta fada cikin kuka, Bata karasa ba ya sake dauke ta da Mari yana cewa
"Ki kara cewa tak kiga abinda zanyi maki..." Yafada yana nunata da yatsa, afusace Inna ta daga hannu zata mareshi, afusace ya juyo ya kalleta, irin kallon tabani ki gani, abinda ta gani ya bata tsoro, idanuwanshi ta gani kaman ba nashi ba for just a second Sai kuma ya dawo normal,
"Safwan..." Tafada zufa na keto mata..
"Inna Yanzu dukana zakiyi saboda na mareta?..Lallai ma..." Yafada sounding so tensed, Inna kasa magana tayi saboda she don't know if her eyes are deceiving her ko kuma abinda tagani it's real, wuri ya samu ya zauna Sannan yace
"Next week zanzo daukar ku zuwa Sabon gida...doc haka ku shirya...bana bukatar ko,Ai daga nan gidan..." Yafada atakaice, Inna sai kallon idanuwanshi take ko zata sake ganin wannan Abu data gani dazun amma nothing, mikewa yayi da hannunshi cikin aljihu yace
"Da akwai Abunda kuke bukata?.." Yafada sounding calm, for the first time Inna tace
"Aa..." Kallon mamaki yayi mata yace
"Inna ban gane aa ba... Kudi nakeson baki...baki taba cewa no ga kudi ba..Don haka Yanzu ba zaki ce baki bukata ba..." Yafada yana fiddo kudi da yawa dashi, mika mata yayi yace
"gashi...ki rike..ki sayi duk abinda kikeso...in mun koma Sabon gida zan baki da yawa kinji innata..." Yafada cikin zolaya, ahankali Inna ta mika hannunta karba, this is the first time data lura da changes a kan danta, ficewa yayi daga gidan,asiya ta fashe da kuka da karfi Tana cewa
"Inna wannan kaman ba yaya ba..Inna ya Chanza da yawa..." Tafada cikin matsanacin kuka, ahankali Inna ta samu wuri ta zauna rike da wannan uban kudin hannunta, asiya dawowa tayi kusa da Inna Tana kallon kudin hannunta
"Inna ki tambayi yaya aikin da yake da ya samu kudi cikin kankanin lokaci...ni Wallahi Inna tsoronshi nake ji..." Tafada cikin kuka,
"Ke dalla rufemin baki...ki barni Inji da Abunda ke damuna...ko ranan baki ji yace alhaji Mai saa ya bashi aiki ba.."
"Amma Inna wane irin aiki né haka?.. Inna ko sati baiyi da fara aiki ba amma har ya sayi gida...Kodai yayi ya fara..." Sai kuma tayi shuru Tana kuka,
"Ya fara me..." Ta tambayeta sounding angry, bata sake cewa komai ba har sai da ta Kai bakin kofa tace
"Gaskiya ni Inna ban zuwa wani sabon gida..kawai muyi zaman mu nan..." Tafada Tana komawa ciki abinta,
Safwan bai tsaya koina ba sai Kofar gidan su khairat, wani yaro ya tura a kirawo ta, few seconds yaron ya fito yace
"Inji wa?.."
"Inji safwan..." Ya amsawa yaron yana jinginawa da bango, bayan kaman minti goma wata yar yarinya da bazata wuce shekara 19 ba tafito sanye da doguwar hijab har kasa, murmushi ya sakar mata itama ta Dan saki murmushi tare dayi mashi sallama, amsawa yayi yana kallon ta,
"Nayi kewar ki khairat...Yanzu ko nawa mahaifin ki keso zan bashi ya amince in aureki...Wallahi khairat inason ki sosai..." , Yafada mata Kai tsaye,
"Ai an yansa bikin..kawai muyi hakuri haka Allah yaso..." Tafada mashi calmly,
"Aa ni bazan yi hakuri ba..khairat shekara nawa muna tare...kawai sai wani ya daukeki? ...gaskiya ba zanyi hakuri ba...da danayi hakuri Don bani dashi né..Yanzu kam daidai nake da uban kowa...Don haka shiga ciki ki Kira mahaifin ki muyi magana..." Yafada sounding so commanding, Kai ta daga ta kalleshi Tana mamakin in Wanda yayi magana safwan dinta né, he sound so different and rude,
"Nidai kayi hakuri...komai sai in Allah ya amince...kawai Allah bai yarda muyi aure ba..." Bata karasa ba yace
"Khairat Yanzu baki sona kenan..." Ya tambayeta feeling like strangling her, ahankali ta girgiza mashi Kai tace
"Bazan taba kinka ba...kawai dai Ina bin umarnin mahaifin nane..kayi hakuri..."
"Nace ba zanyi hakuri ba...Allah kar ki Kira ce min inyi hakuri...kawai shiga ciki ki Kira shi..." Yafada ranshi bace,
"Bai nan..." Ta amsa mashi Sannan tace
"Zan koma ciki..sai anjuma..." Batajira taji abinda zaice ba ta juya ya shige ciki saboda yanda yake bata tsoro da kalaman bakinshi, tsoki yaja ya juya yana cewa
"I will come back in three days..." Yafada yana barin wajen, ta Kofar gidansu ya bi ya wuce bai Kara shiga ciki ba, yana fitowa zuwa inda motarshi take yaga yanmatan gidan Alhaji Ibrahim suna waje da alaman unguwa zasu amma babu hanyar da zaa fito da motar, face dinsu daddaure, yana zuwa ya kalli each and everyone faces har da driver,
"Haba malam...ya zaayi ka tare hanyar Kofar gidan mutum...ka kyauta kenan...munfi minti talatin nan muna jiran ka dauke motar ka..." Inji babban babe din wacce zata Kai 19, tunda ta fara magana safwan ya kura mata Ido bai ko kaftawa, sai da ta gama magana yace
"Dan Allah kiyi hakuri...banson na batawa Angel kaman ki rai ba...let me move away..." Yafada yana shiga cikn motar, cikin ranshi fal cike da farin ciki, yarinyar murmushi ta saki looking at the hurt dude, bata San he has been living in the area all he's life ba she has never notice him sai yau that he has classy car parked at the front of their home, yana cikin motar yana kallon dukkan yanmata,
"I will definitely have you all..." Yafada yana moving motar daga Kofar gidan,16💙💛💚❤️💜
Sirrin wasu gayun
💜💚💛💙❤️
® zuwairat (ummumaryam)
1️⃣6️⃣
Don't read if you didn't pay, if you do you owe me
Dedicated to my anty...
Yana cire motar driver ya koma cikin gida shi kuma safwan ya fito daga cikin nashi motar, wurin babes din ya dawo duk suka dauke Kai daga gareshi dukda he looks so hot to them, sallama yayi suka amsa while Ana budewa driver gate
"Dan Allah ki Dan bani minti daya ..." Yayi directing maganar to babban, Dan juyowa tayi while sisters dinta suka nufi mota,
"Dan Allah ki bani phone number dinki zamuyi wata magana...I dint want to waste your time..." Yafada mata idanuwanshi cikin nata, Dan murmushi ta saki Sannan tce
"Ni bani da phone..." Tafada cikin shagwaba like a spoiled brat, Dan dariya ya saki yace
,"Haba..kawai just say you won't give me...amma how will a lady like you be without a phone...nidai pls give me your phone number and I promise you won't regret it..." Yafada sounding so cute, idanuwa tayi rolling Sannan tace
"Ai banga inda zaka rubuta number din ba..." Tafada atakaice, da sauri ya jiya ya shiga cikin mota ya dauko wayarshi, bata Kara jiran Abunda zai ce ba ta shiga cikin mota because daman tuntuni sisters dinta suna ciki, safwan bin bayanta yayi da kallo yana tunanin she won't play hard to get, juyawa shima yayi zai shige cikin mota yaji ance
"Shege safwan..kaine ka Faso gari haka?.. Dan Allah meye sirrin?.." Ahankali safwan ya juyo ya kalli Wanda yayi maganar, wani Saurayine age mate dinshi, kallon banza safwan ya watsa mashi yana cewa
"Sirrin me...and pls don't pretend to be friend...Kai da ko mutum zai mutu ya nemi taimakonka Baka taimakawa..." Safwan ya fada yana bude motar shi, dariya mata shin yayi yace
"Hmm ai ba roko nazoyi ba...kawai nace meye sirrin ...Don wannan yayi sauri da yawa..Kodai..Kodai..." Saurayin Yafada yana dariya, yar dariya shima safwan ya saki Sannan yac
"Kodai me?.."
"Kodai kun hau titi né?.. " maganar ya mugun batawa safwan rai amma yasan is f baiyi controlling ba Yanzu ya tonawa kanshi asiri, tsoki kawai yaja ya shige motarshi ya bar wajen, yana tuki yana tunanin abinda wannan matashin yace,
"He's right..it's too sudden..kar In jawa Kaina many eyes...just last week we're begging and now am riding the latest car" Yafada yana tuki,
"Gaskiya let me slow down...kar all eyes ya dawo Kaina...am laying low for now..." Yafada yana tunawa da maganar da alhaji idris ya fada masu lokacin na cewa su bude business a gari suce shine source of money dinsu,,
"Haka zaayi..." Yafada atakaice,
"Am not coming back now...ba Yanzu ba..." Yafadawa kanshi, driving yayi ya shiga restaurant yaci abinci ya Kira alhaji idris kan ya hadashi da Wanda zaiyi decorating gidanshi, nan alhaji idris ya bashi number wata mata sukayi magana, yace ta sameshi gidanta gan wajen sai ayi maganar kudi, haka akayi, wajen karfe bakwai matar da yaranta da suke aiki a karkashin ta sukazo gidan, nan sukayi estimates na abubuwan da kowannen part zaici Wanda ya tashi kusa million hamsin saboda safwan ya zabi irin design da yake so cikin pics da suka nuna mashi, nan ya bata wasu cash yace zai cika mata sauran if an gama, nan dai ta fada mashi abubuwan order zaayi Don haka sai nan da sati uku zasu fara gyara wajen. Bayan sun tafi ya koma kasa ya kwanta yana tunanin rayuwa, right now he's not exactly happy but he have what he always wanted, wayarshi ya dauka yayi dailing number dayayi saving da next victim, ringing ya dingayi ba'a daga ba har ta tsinke ya sake Kira still ba'a daga ba but he never give up har sai da ya Kira a na shida aka daga cikin muryar bacci tayi sallama, Dan lumshe idanuwa yayi yana imagining this same voice crying for mercy
"Haba dear I have been calling you..." Yafada kaman zaiyi kuka, hamma yaji tayi before saying
"Sorry I was napping...waye pls..." Tafada mashi calmly
"Nine dazun na amshi number ki..,sunana safwan..I want to tell you are the most beautiful lady I have ever seen..." Yafada yana gatsine,
"Nagode..." Ta amsa mash atakaice,
"Pls I want you to be my girl...zanyi maki komai...zan baki duk abinda kikeso..." Dariya yaji tanayi, baki ya tabe yana cewa
"Am serious..Wallahi Kim dauke min hankali...zan iya biyan million Don in ganmu tare Yanzu..." Yafada cikin sanyinmurya,
"Hmm we just met today...wannan words din are above me..."
"Kawai Ina fada maki yanda nake ji né...Dan Allah ki fito in ganki....zan baki 500k cash if you let me look at you for the whole night.." Yafada face dinshi daddaure kaman bai taba dariya ba, dariya yarinyar tayi da karfi Sannan tace you call money kaman you have the tree in your home..." Tafada sounding interested,
"Eh mana..Ina da bushiyar gidana...kizo ki tsinka to your satisfaction..." Yafada yana dariya,
"Funny you..." Ta amsa mashi
"What are your plans for tomorrow..." Ya tambayeta,
"Well nothing much..kawai dai zaa kaini gidan kitso then sai zanje gidan kawata..." Ta amsa mashi,
"Ok ki Bari zan zo in daukeki...Sannan zan kaiki sai ki gano bushiyar kudin..." Yafada yana fatan zata amince, dariya tayi tace
"Ai ni duk inda zani driver ke daukata...dad bai yarda in fita haka nan on my own..." Baki ya tabe yana cewa
"Over protective greedy man..." Yafada cikin ranshi, Sannan yace
"Hmmm daddy's little girl....nidai I want to be your driver...ki bani dama kawai..." Yafada mata, shuru tayi bata amsa mashi ba,
"Kinji pLS...Zaki ji dadin tarayya Dani...am hot and rich...komai zaki samu..."
"Wai let me ask...wane irin tarayya kake nufi né?.." Ta tambayeshi,
"Kawai tarayya tsakanin mace da miji...am sure you understand what am saying..." Ya tambayeta,
"Lallai...abun naka azimun né....sai anjuma..." Ta fada mashi, Tana kaiwa nan ta katse wayarta, Dariya safwan yayi yana cewa
"Wato Kim kashe wayarki...Lallai zaki ci ubanki...when am through with you kudin ubanki zai kare wajen nema maki magani. Nan kasa ya kwAnta yana latse latse wayarshi, tunawa yayi da number da alhaji idris ya bashi
"Wai big mama..." Yafada yana dariya, shi tunanin dayake is big mama wata katuwar matace bai San she's a woman da take zaune campus Tana hada yanmata da manyan mutane ba, da ita ake ciniki sai a bata kudi ita kuma ta biya yarinyar da zata tura, yanmata da dama a hostel suna hulda daita but da akwai few ones da ko hanyar da take basu bi,
"Let's see what you have got..." Safwan ya fada yana dailing number big mama, ji yayi she's busy on another call, ajiye wayar yayi bai sake Kira ba, Dan Shafa manhood dinshi yayi yana cewa
"You need to feed..." Yafada yana wata banzar dariya,bayan kaman minti goma ya sake Kira but still busy, tsoki yaja yana cewa
"Fuck you..." Yafada Hanna mikewa daga inda yake kwance, Kaya ya sake ya fita daga gidan zuwa hunting yarinyar da zaiyi quench thirst daita. Bayan kaman hour daya ya dawo da wata, shi kanshi yana tunanin yanda akayi wasu matan suke iya saida rayuwarsu saboda kudi, it obvious yanda suke bin Wanda basu sani ba zuwa inda basu sani, ko yankata yayi babu Wanda zai sani, he's thinking wane irin saida rai né wanna.
Yau né aka daura auren habib da Fatima, amarya kam Tasha kyau in her own way sai waazi ake mata kan ko sau daya kar ta kuskura ta yi mashi ba daidai ba, Sannan duk abinda yace yana so kar tayi mashi gardama. Bayan an daura auren habib ya samu quite spot dinshi ya zauna yana tunani, kawai he's thinking if Allah yasa yayi impregnating Fatima shi kuma ya mutu who will take care of he's unborn child, yana tunanin yanda mamanmu ke hustling for survival da siblings dinshi Sai kuma ya Kara Dora mata wani nauyin.
"Hmmm five more days to go..." Yafada hawaye na taruwa eyes dinshi, bayan sallah ishai aka Kai Fatima dakinta which is few feets away daga gidan iyaye ta, ko kadan bata yi kuka ba idanuwanta bude Tana kallon mutane, har suka isa dakin mamanmu, nan mamanmu ta amsheta hannu bibbiyu, habib bai dawo gida ba sai wajen karfe tara da rabi, yana shiga gidan ya fara lekawa dakin Fatima yaga babu kowa ciki ya leka the other room still babu kowa, jiki ba kwari ya dinga takawa zuwa dakin mamanmu Don ko kadan babu irin wannan zumudin ango a jikinshi he looks so dull and pale, duk ya rame sosai, da sallama ya shiga dakin mamanmu dake zaune Fatima na rakube kusa daita, ahankali ya zauna yana kallon yanda take takure jikin mamanmu, gaida mamanmu yayi
Book Chapters
Chapter 15
Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500