You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
be the best... "yafada cikin sanyimurya, cikij kuka tace
"mun zame maku burden... You people are spending a lot kan mu... "still hannu ya dora a bakinta yace
"pls ki bar magana haka mana... Allah ne yaga heart dinki ya hadamu dake... Yasan we're capable of helping you and the children ko da kuwa they're dozens of them... Pls ki bar cewa you're a burden kinji kou? "ya fada mata cikin calmness, ahankali ta daga mashi kai, amma bata bar kuka ba, matsawa yayi kusa daita ya jawota ta dora kai a shoulder dinshi ta dinga kuka, daman wannan is something she does on a Daily basis, ko kadan bayason Tana kuka amma she won't stop, hannu ta zagaya ta rike kugunshi gam Tana kuka, bayanta ya dinga shafawa yana bata hakuri in a very sweet and calm way, bayan kaman minti biyar tace.
"yaya..."ta kirashi cikin rawar murya,
"Naam dear.."ya amsa mata in a gentle way,
"pls in kana kaunar Allah da manzonsa let me go to my family today... Nasan bazasuyi accepting dina ba amma I need to know how they're... Pls... "ta rokeshi while holding he's waist tight,
"tou shikenan... Amma pls promise me one thing... "
"anything... "tafada mashi
"that zaki dawo ki zauna da yaranki... Kinga you can't take them home.. Am sure bazasu yarda ba.. Don haka ki dawo pls... "ya rada mata,
"OK... "ta amsa mashi,
"good... Yanzu ki saki waist dina ki shiga bathroom ki wanko face dinki ki shirya I will go with you... " yafada mata, da sauri ta saki waist dinshi tare dacewa
"sorry... "ta fada mashu Don kar yayi tunanin she's flirting with him, murmushi kawia ya sakar mata, mikewa tayi ta shiga bathroom shi ma ya Mike ya fita daga dakin sai sauri yake kaman mara gaskiya, yana fita ya bude gate sannan ya koma cikin mota yana jiran fitowanta.
Alhaji bello yayi developing wani irin so for habib, he loves him kaman she ya haifeshi, kullum yana studying dinshi and he never finds a single flaw in him, hes flawless to him, ga respect GA amana sannan he don't talk much, kullum he's quite kaman nai tunanin wani abu, sau kusan biyar alhaji ke gwadashi Don yaga gaskiyarshi amma luckily bai taba disappointing din alhaji ba, da akwai ranar da ya bashi kudi masu yawa ya Kai bank, he told him kudin is 20m alhalin it's 25m, daman habib bai counting sai dai ya kai bank direct. Yana zuwa bank ya kira alhaji ya fada mashi kudin is 25m instead of 20m da alhaji yace, idanuwa alhaji ya lumshe saboda jin dadi Don yaranshi biyu basu ci wannan jarabawan ba, he will intentionally gice you extra money and decrease the amount, wasu sau suc e kudi yayiwa alhaji yawa bai San yawansu ba shiyasa yake basu dayawa yace it's small, basu San he's looking for someone to trust ba, yau MA kudi ya bashi da extra 10millions ya bashi ya kai bank yau kam yana dawowa yace
"sir pls kayiwa Mai lura da kudinka ya dinga fada maka exactly the amount... Now look wanna fa extra ne.. "ya fada yana ajiye bag din kudin kan table din alhji bello, relaxing alhaji bello yayi tare da lumshe ido, yasan yanzu baka iya rantsewa mutane but he can swear for this poor boy, yana da amana sosai for that he has gain the trust of the multi billionaire alhaji bello tanimu,
"are you sure?.. "alhaji bello ya tambayeshi,
"yes sir... Kawai na shigar da 128m din kuma GA sauran.. Kusan sau shida kenan yana haka... Yanzu if mutum bai tsoro Allah yana iya guduwa dashi.. Pls tell him ya dinga Shiryawa da kyau ."habib ya fada mashi in a respective way,
"seat... "alhaji ya fada mashi Don tunda yake magana he's still standing, ahankali ya zauna, alhaji kura mashi ido kawai yayi for a moment sannan yace
"kasan yanzu a wannan zamanin baa bawa mutum 100% amma kai I give you 100% when it comes to amana...i can't grade you on some other things amma ba baka thumb up wajen amana da tsoron Allah... Kasan tunda ake baka kudi it's not extra..it's test... Nayi yara sun kai biyar basu ci wannan jarabawan ba, da sun kawo na farko na nuna ban San dashi sai su rike ba biyun, believe me ba kudi bane Mai yawa kaman naka... Bai wuce 200k to 500k, amma sai su rike ni kuma inyi kaman ban San me sukayi ba, I have never asked them kuma bana koransu...nasan nan hanyar samun abincinsu ne kuma ni bazan hanasu ba sai dai in sauya masu department... Congratulations... "alhaji bello ya fada yana mika mashi hannu, habib daga weak hands dinshi yayi ya dora cikin na alhaji bello sanna alhaji bello yace
"you're now given the appointment of financial secretary... Kaine zaka lura da kudina, my shares, da duk incomes and spends nawa...and this job comes with a house, car and driver... "habib zuba mashi ido yayi yana kallon bakinshi, har lokacin alhaji bello na rike da hannun habib, shima habib rike nashi hannun yayi gam kaman he's his life saver, har ya kai karshen maganar bai saki hannunshi ba sannan kuma baiyi magana ba, alhaji bello kokarin zare hannunshi yayi amma sai ya kasa, saboda yanda habib ya rike mashi hannu saboda trauma, murmushi alhaji ya saki sannan yace
"you can free my hand now... "alhaji ya fada with a smiling face, da sauri habib ya saki hannunshi amma wannan trauma bai sakeshi ba, dukda he's previous life is dark to him yasan wannan mutumin have Done alot for him,
"sir... Yayi yawa.. "shine abinda habib ya fada cikin karfin hali, dariya alhaji bello yayi yace
"aa.. Nothing is too much for you... You have a Golden Heart... "ya fada mashi, ahankali habib ya zame daga kan kujerar ya dawo kasa yayi kneeling gaban alhaji yana mashi godiya,
"pls stand son... Don't ever do that again... Just keep you good job up.. That's all I ask of you... "yafada mashi cikin so da kulawa,
"yanzu abinda zaayi is... Zansa mujahideen ya kai ka gidan..."da sauri habib yace
"sir dan Allah in zauna da ku.."gira daya alhaji ya daga tarw dacewa
"why... Don't you want to be in your own house?..don't you want to start a family and decorate your own house to your taste?.. " ya tambayeshi,
"ina so... Amma am scared... In na rufe idona ina ganin abubuwa... Da mutane da faces da ban San ko na waye ba... Wasu fuskokin suna firgita ni dayawa... " yafadawa alhaji for the first time what he's going through,
"tun yaushe ka fara ganin wannan faces din? " alhaji ya tambayeshi,
"an kwana biyu... "ya amsa mashi
"well nasan faces din are people you know... But kar ka damu zamuyiwa doctor magana let's see what he can do about it... Yanzu dai zaa kaika ka gano wajen, sai kayu magana da decorators su gyara maka to your taste anytime kake son komawa you're free to..."alhaji ya fada mashi,
"tou.. Nagode... Allah ya biya... Allah ya saka da alkhairi... "habih ya fad'a voice disnhi na rawa,
"Ameen Ameen... Kaima Allah ya baka lafiya yasa mu gano mutanen ka... In dai suna bukatar taimako now is the right time Don kaima zaka iya taimaka masu yanzu... " alhaji ya fad'a mashi cikin natsuwa, habib dai shuru yayi but deep down he can't wait to be with he's people, he really wants to know where he's from.
Thanks43🧡💜💛💚💙
Sirrin wasu gayun
❤🧡💛💜💚
®Zuwairat (ummumaryam)
4⃣3⃣
Don't read if you didn't pay, if you do I owe you.
Yanda alhaji bello ya kamu da son habib haka itama mufida ta kamu da son halin habib, she always stairs at him for very long, yana gani at times amma sai yayi kaman vai gani ba, he's heart is blank bai San ainahin who he is ba, heart dinshi bani space for wani avu wai love, he's always thinking of daga inda ya fito. Mufida us always talking about him kawia dai abinda take so da bata samu is he's attention, sai kuma magana, tanason ya ganta zaune Tana labari dashi amma bai bada wannan daman, kawai he reply her with one simple word, jiya kwalliya taci tazo kofar part dinshi ta dinga kiran Muhammad amma bai amsa ba, daga baya gajiya tayi ta koma ta kira maigadi ya shiga ya kirashi because she's learn a lesson of being a lone with a man in the room, ko kadan bazatyi gigin shiga part dinshi ha because she knows a man will always be a man, abun yana bata mamaki because batayi tunanin wani namiji zai kara shiga kanta bayan halin data shiga a hannun safwan ba amma sai ga wannan mutum da bata San asalinshi ba yana neman dauke mata zuxiya, sai ta kwana Tana tunanin shi, sai yanzu yasan indai da tausayi da akwai so, Tana tausaya mashi sosai that before she realize she has fallen for him. Amma the most annoying part is bainuna ya damu da ita, bayan driver ya kirashi ya fito ta sakar mashi murmushi tare dacewa
"Dan Allah yaya Muhammad ka kaini shan ice cream,... "tafada mashi cikin shagwaba, Shima Dan murmushi ya saki before saying zamu fita da alhaji... " ya amsa mata atakaice, bai kalli reaction dinta ba ya juya ya koma ciki. Wajen magrub taga bai fita ba taje tasa aka kirashi ta tambayeshi way yace zasu fita kuma basu fita ba sai ya amsa mata da cewa
"AI alhaji ne bai ce mu fita bq... "ya amsa mata ya sake juyawa yayi tafiyarshi, wannan abun yana batawa mufida rai da yawa, bai bata room for conversation, sanna datayi magana ya bata amsa bai jiran what she will say Next zai juya ya shiga ciki, at times sai ta dinga tunanin ko har yanzu haukan na kanshi but yasan exactly what he's doing, kawai baison long conversation daita, dukda yasan he's previous life is blank yasan bazai rasa someone important a rayuwar shi.
Amra kam sai up and down take a dakinta, kawai she wants to say it yau and get it over with, tasan tana kaunar limitless and da wuya ta kara samun wani Wanda zata so kaman shi, she loves the way he talks and everything and above all he's limitless, the guy with the biggest company in Africa. Kofar dakinta aka bude afra ta shigo, kallon yanda ta fita hayyacinta tayi tace
"wai Meye kika yi zuru kaman mara gaskiya... "afra ta tambayeta, ajiyan zuxiya amra ta saki sannan tace
"wallahi kan limitless ne...yace in ban fadawa dad ba yau bazai kara kirana ba... Gashi wallahi sister I can't do without him... "tafada kaman zatayi kuka,
"sister go and tell him mana.. AI kinsan dole wata rana muyi aure... Don haka tunda ke Allah ya kawo Mai kaunarki sai ki fad'a mashi... "
"you talk as if Bakisan halinshi ba, zaice despite he's warning na kula wani.. Wallahi am confused... "tafad'a tana dafa goshinta,
"ke dai in kina fada maahi go and talk to him about your Romeo before it's late... Nidai give me your shower gel, nawa ya k'are..."afra ta fada Tana shige bathroom dinta, few seconds later afra ta fito ta bar ta nan tsaye, shahada amra tayi ta fita zuwa part din dad dinta, sallama tayi alhaji Mai saa dake zaune ya daga kai tare da ansawa,
"angel kece?" ya fad'a cikin so da kaunar ta, duk cikin yarasnhi baiga wacce Allah ya jarabceshi da sonta kaman amra ba, her gentle nature and her obedience is something that makes him love her more, yana kaunar yaranshi sosai amma da wani abu ya taba amra gwanda wannan abun ya kasheshi, face dinta ya kalla yaga damuwa kwance, hannu ya mika mata yana cewa
"angel waya taba minke... Come to daddy... "yafada yana mata stretching hannunshi, ahankali ta taka takama hannunshi ta zauna kan hannun kujerar da yake Zaune, massaging hannunta ya farayi yana ceaa
"my angel tell me mana waya taba min ke?..ko so kike daddy yayi kuka?.. " ya fada mata cikin so da kulawa, idanuwa ta Dan Lumshe sannan tace
"ba kowa daddy... Kawai alfarma da yafiyarka zan nema... " ta fad'a voice dinta na rawa kawai. Alhaji Mai saa sai yaji hankalinshi duk. Ua tashi
"yafiyata kuma... Angel tell me ko Meye in ba so kike zuciya ta tabuga ba yanzu... "yafada kaman zaiyi kuka,
"daddy.. Kace kar in kula kowa.. Na ketara umarnin ka... Har na kamu da son wani... Dan Allah daddy am. Sorry... "tafada trying not to cry,
"inna lillahi waina ilaihi rajiun...angel. ina kike zuwa har da zaki hadu da wani?.. Ya akayi kika sanshi... Wayeshi... Bana fada maki ni zan nema maku mijin aure ba?.. "ya jero mata questions tun kafin yasan who she's in love with, yanda yake magana yasa ta fashe da kuka,
"daddy kayi hakuri... "tafada cikin kuka, bai bari ta karasa ba yace
"kar ki bani hakuri... Kunsan dalilin da yasa nake protecting dinku?.. " ya daka. Mata tsawa, cikin kuka tagirggiza mashi kai,
"because the world Is a dangerous place.. " nikam I was like laughing in Chinese, shuuuuu see this man ooo, the way you make your bed is exactly the way you lay on it, Dan Adam yayi Kadan yayiwa Allah wayau, if you do to others dole zaayi maka, the only way to prevent it is by not doing to others, bakayi ba anyi maka balle kayi, no peace for the wicked, ko an samu peace it's just for a while, mata ku zabawa yaranku uba na gari, that's if kema mace ta gari ce because you can wear expensive clothes on slippers.
"it's endtime.... Mutane babu imani yanzu.... Basu tsoron Allah... Shiyasa nace dole ni zan aurar daku da kaina ga wanda ya dace... But you went behind my back and date someone.. Now tell me ina kika San shi and shi waye..dan gidan uban waye shi... "ya fada sounding so Angry kaman ba shi ba, amra kuka kawai take Don bata ganin mahaifinta haka ba, the anger in him is something she have never seen tunda ya haifeta, he always pet them especially her amma yanda yake magana ya mugun tada mata hankali, da sauri ta Mike Tana cewa
"daddy kayi hakuri... Na hakura... Bazan kara mashi magana ba... "tafada Tana Jan baya,
"come back here!.. "ya daka mata tsawa, da sauri ta dawo gabanshi Tana kuka sosai saboda tashin hankali Don ko kadan she's not use to violence.
"nace ina kike zuwa har kika hadu dashi?.. " ya daka mata tsawa
"wallahi bana zuwa koina... Nan gidan yazo... Sai yabini islamiya... Ya amshi number ta... Shikenan.. Wallahi daddy Inason shi shima yana sona... Kuma he's not a bad person tunda yana yawan zuwa nan wajen ka... "ta fada mashi jikinta na rawa, surprise look ne kwance kan face dinshi yana tunanin who it could be Don mutane da yawa suna zuwa wurinshi, ko kadan it will be safwan ba,
"banason long story.. Waye shi... "yafada kaman zai doketa, da sauri tace
"sunanshi safwan.. Limitless... "ai wannan kalmar is the most frightened word of the century to alhaji Mai saa, ji yayi numfashi na neman yi mashi kadan saboda tashin hankali, dafa kirji yyi zai yi magana amma nothing is coming out sabida trauma, he can't believe safwan zai biyo baya despite he's careful with him ba, farat daya ya zabura Don all the things he was talking daga zaune yake, yana jin actual tashin ya zabura ya Mike tsaye, da sauri amra tayi baya har Tana faduwa sabida yanda idanuwan mahaifinta ya sauya kala zuwa Wanda bata taba gani ba, duk idanuwanshi babu fari ko guda duk yayi baki, kullum he always control he's anger Don kar aga the real him but yau abun ya fi karfinshi, da gudu amra ta fita daga falon saboda tsoro don bata taba ganin mahaifinta haka ba sai yau, Tana kuka ta bar wajen da gudu, she don't know what exactly to think of, all she knows is taga yanda idanuwanshi suka sauya kala, wani irin kuka alhaji Mai saa ya saki kman dabban daji, bai San he have such anger ba sai yau, wani irin zafi yakeji cikin ranshi, kawai Hangen da yake safwan ya riga ya gama da yarshi, he so afraid of safwan saboda ko shigabansu yasan da zaman safwan saboda rashin imaninshi at times yana kiranshi da successor, tunda ake cikin kungiyar babu Wanda ke yin abu anyhow sai Safwan, bai taba kai pants sama da biyar ba amma sai safwan ya kai ishirin and more, kullum cikin fadin misterous death na mutane ake as a results of safwan, shine safwan yake da daman zuwa ga yaranshi despite komai, saboda yaranshi su tsira ya hadashi da big mama,
"you have touched the lion by the tails, ..you might be stubborn but I bet you, you won't live to finish this fight,.."yafada sounding so furious, ko takalmi babu kafarshi ya fita da sauri yana fadawa driver
"open that car... "ya fada a hargitse while heading for the car.
,nothing much is happening a Bangaren su Mamanmu, kawai dai sun koma normal life dinsu while little modiibo na kara girma, Mamanmu kam Tana ciniki sosai kuma kayan gona Allah yasa masu albarka don haka basu da matsalar komai, mamanmu ta saida wasu kayan gona ta kara da jarinta sai ta ajiye sauran Don suci, ta zamewa Fatima da danta uwa, uba da miji Don bata bari suyi lacking wani abu kuma alhamdulillah babu wata matsala a gabansu.
Suna daf da zuwa Unguwarsu rabia dake zaune da long hijab besides Dr ta kalleshi tare dacewa
"gabana na faduwa da yawa.. I don't know if I can do it... "tafada Tana hadiye wani abu, ahankali Dr ya juya ya kalleta tare dacewa
"ko dai mu koma... Kinsaj har yanzu you're not still strong to face any problem... In kinsan you're not comfortable with mu koma zuwa next time... "yafada while slowing down, ajiyan zuciya rabia ta saki tare da busar da iska sannan tace
"ko bayan shekara goma zanzo nan dole I will feel same thing, dole in daure and get it over with... "ta fada voice dinta na cracking sosai,
"then take a chill pill.. Am with you... "yafada driving down inda ta fada mashi, ahaka har suka isa kofar gidansu, da kyar rabia ta iya sauke kafa daga cikin motar, har dafa chest dinta take saboda yanda yake bugawa, wani irin ajiyan zuciya ta saki sannan ta sauko daga motar, har bakin gate suka kai sai Dr yasa hannu ya buga gate din, babu abinda rabia take maimaitawa sai inna lillahi waina ilaihi rajiun, shuru bayan kaman minti biyu Dr ya sake bugawa, rabia najin kafar mutum tayi saurin komawa bayan Dr saboda tsoro, wata yarinya ce ta bude kofar Dr na ganinta yasan kanwar rabia ce saboda resemblance dinsu, zata bude baki tayi magana taga rabia dake lekowa, idanuwa yarinyar ta zaro Tana cewa
"GA anty rabia!!! "ta fada da karfi, da sauri ta kama hannun Dr tanacewa
"let's go back... I can't do this pls... "tafada hawaye na taruwa idonta, kai ya girgiza mata yace
"it's a bit late for that now, "ya fada yana rike da hannunta har cikin gidan, yarinyar sake ihu tayi Tana cewa
" GA anty rabia ta dawo," this time mutane gidan sunji kuma da gudu suka fito, mahaifiyar ta ce ta fito da gudu rabia tayi sake boyewa bayan Dr, da gudu tayi kanta haka sauran matan uban da sisters dinta suka fara dukanta, Dr na kokarin kareta amna sunyi mashi yawa, mahaifiyar ta na dukanta Tana
"Allah yaisa... Allah yaisa... Allah yaisa... Kin kashe ubanki... "wannan statement ya tsayawa rabia a kai, duk Dukan da ake mata batajishi kaman wannan maganar ba, wata Babban mace ce wace da gani itace babban matar alhaji Ibrahim ta fito da gudu Tana korar masu dukanta, mahaifiyarta cikin kuka ta cigaba dacewa
"tir da halinki ubanki ya mutu ta sanadiyar ki... Nayi dana sanin Haihuwar y'a irinki... Allah yaisa tsakanin mu dake... "mahaifiyar ta tafad'a cikin matsanacin kuka, rabia dake kwance kasa rike da kafar doctor mikewa tayi tana yarfa hannuwa idanuwanta duk waje Tana
" na shiga uku...wayyo daddyna.. Wayyo ubana... Wayyo... "kawai take maimaitawa kaman wata sabuwar shigar mahaukaciya, duk iya hawayen rabia kam yau bata samu hawayen ba, her facewas dry down to her throat, Dr ya tausaya mata sosai Don har da hawaye a eyes dinshi, kamata yayi yaji duk jikinta sai rawa yake, yasan she's not strong enough for all this now, not after undergoing surgery da yara biyar da kuma wahalal data sha lokacin cikin,
"ku fita ke da Dan iskarki... "inji wata kanwarta,
"kar ki sake dawowa gidan nan tsinanna... Duk ranar da kika sake dawowa sai nasa mutanen unguwa sun jefeki..."inji another sister dinta,
"Dan Allah kuyi hakuri... Ku dauki kaddara...ku godewa Allah da yarku ta rayu..." Dr yake fada masu cikin karfin hali, bai karasa ba mahaifiyar ta tace
"rayuwar amfanin me zaiyi mana... Ku fita ku bar gidan nan... "
"wallahi in kunji halinda yarku ta shiga zaku tausaya mata sannan zakusan kaddara ne ya hauta... Yara biyar ta haifa... "
"nace ku bar gidan nan...Allah yasa duk duniya ta haifa banason ganinta, Mai kama daita ma banason gani... "mahaifiyar ta tafad'a mashi idabuwanta duk waje, rabia da ta kasa magana sai wani irin kuka mara hawaye ko sauti takeyi, hannunta ya kama yana janta zuwa waje, mota ya bude mata ta daga idanuwanta taga wani mota ya taho da gudu aikam kaman walkiya ta nufi titi, Allah ya taimaka Dr yayi hanzari riketa da babu abinda zai hana wannan motar bin ta kanta, tirje tirje ta farayi wai ya kyaleta she wants yo die, mutane taruwa sukayi suna kallon yanda yake kokarin janta zuwa cikin mota ita kuma Tana kokarin guduwa kaman mahaukaciya, ganin ya kasa janta yasa ya dauketa ya turata cikin mota shima ya shiga ya kulle Motar dasauri yaja ya bar Unguwar.
Drver da alhji bello yasa ya dauki habib ya kaishi wannan gidan ne yayi driving har suka isa wannan gidan, tun a gate habib ya zama motionless, keys da alhaji ya bada drver ya saka ya bude gidan ya shiga, da kyar habib ya iya shiga gida, dga inda yake tsaye babu abinda yake sai fargaba saboda girman gidan, dukda baisan pass life dinshi ba yasan da wuya in taba shiga irin wannan gidan in ba gidan alhaji bello ba, gidan makeken flat ne wanda yasha expensive doors, kudin doors din gidan sun ishi wani talakan rayuwa Don wasu irin expensive Italian doors ne, gidan sabuwace dal Don har da sauran interlock Wanda suka rage, kawia bai San lokacin da ya fara sujud yana godewa Allah ba, ba kowa ke zama irin wanna gidan ba, ko a cikin masu kudi. Shuru yayi yana lumshe idanuwa, in a blink of an eye ya hangi wata yar karamar kauye sai kuma komai ya dawo normal, before bai ganin komai sai in ya kwanta yanzu kam ko ido biyu yana ganin wulgin wurare Wanda baisan ko ina ne ba.
Haka suka gama zagaya koina suka koma, habib kam bai San iyakan dakuna dake gidan ba.
Alhaji Mai saa bai ce a zarce koina ba sai a gidan a family house din safwan, kaman zai tashi sama ya shiga da kafa bayan driver ya tsaya a waje, he knows whereto find safwan amma sai baije ba yazo gidan inda yasan iyayen safwan suke, direct part dinsu inna ya shiga ba sallama ya harbe kofar da kafa duk Wanda ke cikin gidan sai da ya razana saboda yanda kofar tayi kara, inna ce ta fito da gudu taga wannan bawan Allah da bata taba gani ba, juyawa alhaji yayi ga inna da idanuwanshi Wanda babu fari ko guda yace
"nazo ne Don in fada maki... Danki ya fita harkar iyalaina... In ba haka ba... In har na sake dawowa wallahi wallahi wallahi duk sai na kasheki...duk sai na kashe ku... Wallahi it's only a stubborn fly that follows the..."sai kuma yayi shuru ya juya
Book Chapters
Chapter 40
Chapter 41Chapter 42Support ArewaNovels
Your support helps us maintain the platform and build a sustainable reward system for writers.Enjoying this story? Help us keep ArewaNovels growing.
Your subscription keeps the platform running and helps us support the writers who create the stories you love.
Choose how you want to support
You can continue reading free for now, or subscribe to help us grow and unlock premium access.
Weekly Support7 days of premium access
₦500Monthly Support · Most Popular30 days of premium access
₦1,500