gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAGAYAR DUTSE Dawowa Mai Hatsari book 1 By Nana Haleema Chapter 1 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþ*RAGAYAR DUTSE.*

©þ *Nana Haleema.*

Wattapad@NanaHaleema

ArewaPen@nanahaleema11 Tiktok@Nanahaleemawriter Ig@nana_haleema_writer.

"_Da sunan Allah mai rahama mai jin™ai, godiya ga Allah maWaukakin sarki mai kowa mai komai, da ya ba mu aron rai da lafiyar da mu ka kawo wannan lokacin da rai da lafiya. Ina ro™on Allah, yadda ya bani ikon fara rubutu littafin nan cikin lafiya da aminci, Allah ya sa na gama lafiya. Allah ya bani ikon rubuta abinda zai amfani al'umma baki Waya, Allah kar ya bani ikon rubutu Sarna, ko"

abinda ya saSa addininmu amin._

"_Jinjina da godiya ga mutane masu kirki da karamci, waWanda suka taimaka suka bani goyan baya har muka kawo wannan lokaci. Na gode da goyan bayanku, Allah ya saka da alkhairi ya bar"

"zumuncin mu har aljanna, amin._"

"_Wannan labari mai suna RAGAYAR DUTSE ™ir™irarre ne, bai faru a gaske ba. Ban rubuta littafin dan cin zarafin wani ko wata, hukuma ko gwamnati, ma'aikata ko mutanen gari ba. Na rubuta shi saboda jan hankali da faWakarwa, kamar yadda aka saba a littattafan hausa ko finafinai. In ya yi"

"kama da labarin ki, ko labarin ka, a yi ha™uri rashin sani ne ya kawo hakan._"

"*Note: Akwai wani Sangare da ake Wan taSa zagi a labarin, a yi ha™uri labarin ne ya zo da haka.*"

"_Ban yarda a canja min labari zuwa wata siga daban ba, ban amince a juya min labari zuwa wata"

fuska ba ba tare da izini ba!._

https://chat.whatsapp.com/IkYPgd4DkXD8mUAAeCIZax?mode=gi_t

*Book 1*

*Page 001.*

*MAFARI.*

"""Bawan Allah ba mu san ka ba, ba mu taSa ganinka ba, amma mun ji a ran mu zan iya dam™ a a amanar yarinyar baiwar Allah nan a hannunka. Barinta a wajen babarta barazana ne ga"

"rayuwarta, barinta a gare ta tamkar an Wauketa an cilla ta a wuta ne."""

"""Bawan Allah, ga amanar ´arta nan, ka ri™e ta hannu biyu, ka bata tarbiyya irin wacce ka ke da"

"ita, ka bata ilimi daidai ™arfinka."""

"""Da amincewar babarta muka baka ita, in muka barta a hannunta rayuwarta zata iya lalacewa. Ka"

"ri™e ta hannu biyu, ko da zata waiwayo neman amanarta, ka tabbatar ka san inda zaka Wauko ta"

"ka bata. Tana matu™ar son ´arta, dole ce ta saka zamu rabata da ita."""

"Ta Wan kalli matar da take zaune bata ce komai ba, sai hawaye da yake sakkowa daga idanunta."

"Sun san ba a son ranta za a rabata da ´ar ta ba, amma dole ce ta kawo hakan."

"Matar ta juyo ta kalli wanda yake tsaye ta ce, ""³arta ´ar halak ce ba shegiya ba, ko da wata ran za a yi mata gori ka share mata hawaye, ka tabbatarwa da duniya tana da uba. Ka je da ita, Allah"

"ya baka ikon ri™e amanar da aka baka."""

"Ya bi matar da kallo kamar yadda take kallonsa tana hawaye, ya juya zai fita jiki a sanyaye."

"Kafin ya ™arasa fita ya ji dashashshiyar muryarta, cikin harshen fulani ta ce,"

"""Ka kula min da ita, zan zo na karSe ta duk daren daWewa!."""

"Duk suka juyo suna kallon ta cikin mamaki maganar da aka ji ta yi, a daidai lokacin idanunta ya"

rufe ruf ta zube a wajen babu numfashi.

" " " " " " "

"*SHAGARI PHASE 2,*"

"*YOLA, ADAMAWA STATE NIGERIA.*"

"""To ke yanzu har sai an ce miki ki kashe aurenki sannan zaki kashe? Har sai an faWa miki ki kashe"

"aurenki ki zo a buga miki visa ki Waga ™asashen duniya sannan za ki kashe?."""

"""Hmmm! Ban san me yake damun matan arewa ba wallahi, kuna da dama da lokacin da za ku"

"mori ™uruciyarku, amma sai ku bari Wa namiji yana walagigi da rayuwarku. Akwai namijin da ya isa ya yi min haka ne, ko akwai wanda ya isa ya yi min iyaka da burina?. Wallahi babu shi."""

"Wacce take zaune a gefenta, ta Wan taSe baki cike da damuwa ta ce, ""Woman leader baza ki"

"fahimta ba ne babu wanda ya kai ni son zuwa Saudia aikatau, ina so na je, amma bazai bari ba."""

"Wacce aka kira da Woman leader ta kalle ta she™e™e ta ce, ""shiyasa na ce har yanzu ana wannan"

"™arnin, har yanzu ana cikin ™arnin da sai da izinin namiji zaka yi abinda zai amfane ka?."""

"Sai kuma ta taSe baki ta ce, ""ki ta zama a gida, kar ki fito ki nemi kuWi. Aikin saudia duk wata naira dubu Wari biyar ne, ban da kyautttuka irin na larabawa da ake samu. Sannan ga ki a gari mai tsarki, ko yaushe ki ke son shiga harami faWawa za ki yi baki da wata damuwa. Allah na tuba ko barbaWe ne ba sai na yiwa mijina na tafi ba, me ye ™arshen abun ne, saki ne fa. To a sake ni Win,"

"sai me?."""

"Maimuna da zaune ta ce, ""wayyo Allah! Garin daWi ba kusa ba, in ji ungulu da ta le™a masai."

"Woman leader da gaske naira dubu Wari biyar duk wata?."""

"Woman leader ta Wan harareta ta ce, ""in ba haka bane kin san bazan faWa miki ba, tunda ke kin zauna sai yadda namiji ya yi dake sai ki yi ai. Ga wata da na santa a bayan bayan ki, wani satin zata"

"hau jirgi. Amma ku waWanda na sani, duk matsorata ne, rakiyar mata ku ka yo duniya."""

"Ta yi ajiyar zuciya ta ce, ""wannan ya zama dole ayi dani wallahi, duk hanyar da zan bi wajan ganin"

"na tafi aikin nan wallahi sai na yi."""

"Woman leader ta bata hannu suka tafa ta ce, ""daga lokacin za ki nunawa duniya mata suna da ´"

"anci, kuma dan ka ajjiye ´an mata da sunan ´a´a ba hakan yana nufin ka dakusar da rayuwar ka bane."""

"""Dakyau Maimuna, ki san yadda za ki yi ki zo a tafi dake, in ba haka ba kina ji kina gani zaki cigaba"

"da tsufa a gida. Kina aurar da Safeera kin tashi aiki, dan jikoki za ki fara raino."""

"Maimuna ta ce, ""Ko kuWin auren Safeera na je na haWo ban rage ba.?"""

"""Muguwar ragewa ma, ke aikin nan fa alkhairi ne. Ke kin taSa ganin wacce ta je saudia ta baro"

"aikin ta dawo?."""

"""Ban taSa ba."""

"""Tabbacin akwai alkhairi Win kenan. Ki zo mu haWa ™arfi da ™arfe, ki Waga kawai. Sai me dan ya"

"sake ki, a kan ki aka fara?."""

"""In sha Allah, dani za a tafi."""

"""Assalamu alaikum!."""

"Wata kyakykawar yarinya ta yi sallama cikin siririyar murya tana shigowa falon, wacce bazata"

wuce shekaru ashirin da biyar ba.

"Kyakykyawa ce sosai, doguwa mara jiki, baza ka saka ta a layin masu ™iba ba ko kaWan, kuma bata shiga layin siraran matan nan ba. Tana da brown skin mai kyau da Waukar hankali, fatar har ™"

yalle take yi kamar wacce take shafa cakuleti.

"Tana da manyan idanu zagayayyu masu haske, wanda suke haska brown skin Winta. Tana da"

"dogon hanci mai tsaho, ga Wan ™aramin bakinta mai saurin Waukar hankalin mutane."

"Tana da cikakkiyar gashin gira, kallo Waya zaka yiwa girarta kasan Allah ya yi ajiyar gashi. Kallo W"

"aya zaka yi mata ka san tana da kyau, in ka kalle ta sai ka kuma kallo, saboda baiwar da Allah ya yi mata."

"ISLAHA kenan, matashiya ´ar jarida mai aiki a gidan tv da radio, mai ji da Waukaka da farin jini."

"Fuskarta ta samu karSuwa a wajen jama'a, saboda kyau da murmushi, ga kirki da iya magana a"

"gaban camera. Ga rashin tsoro da sa a, ga iya magana da wayo."

"Islaha bata jin magana, bata da kunya, tana da tsiwa sosai. Tana da Waukar dala ba gammo,"

abinda ya fi ™arfinta zata ce zata iya dashi.

"Tana da gaggawa, bata tsayawa ta nutsu a kan abu, sau tari tana yanke hukunci da zarar abu ya"

"burge ta, bata tsayawa ta yi nazari mai kyau kafin hukunci. Islaha bata da tsoro, kuma bata W"

"aukar rainin wayo. Sai dai tana da kirki, fara'a da girmama na gaba da ita, in ya girmama kansa."

"Duk suka amsa suna kallon ta, kafin woman leader ta Wauke kai ta cigaba da abinda yake gabanta"

bata ce komai ba.

"Islaha dawowar daga wajan aiki kenan, ganin Ummansu Safeera a zaune kusa da Mama sai ta yi"

"murmushin da ya bayyanar da kyauwanta, ta Wan taka kaWan ta ce, ""Umma ashe kina nan, yanzu mu ka rabu da Safeera, bata san bakya gida ba da tabiyo ni"" ta faWa tana kallon ta."

"Wacce ta kira da Umma ta Wan murmushi, ba yabo babu fallasa ta ce, ""Ina nan, ya aikin?."""

"""Alhamudu lillah."""

Sanin ba wani shiri suke yi da Umma ba sai bata sake cewa komai ba. Kar ta faWi abimda zata kasa

jurewa ta mayar mata.

"Ta kalli Mama ta ce, ""barka da hutawa."""

"Mama ta kalle ta kallon sama da ™asa har tana taSe baki, ta ce, ""maza ki je ki Wora min abinci."""

"Islaha ta sauke numfashin gajiya, a sanyaye ta ce, ""To"" ta faWa tana wucewa dan har ga Allah a"

"gajiye take sosai, amma bata isa ta faWawa Mama haka ba."

"Tana barin wajan Maimuna ta kalle ta ta ce, ""wani lokacin kamar tana da hankali, amma ni haka"

"kawai bata yi min ba. Amma dai kin yi sa'ar sirika."""

"Mama ta ce, ""bata yi miki ba, ko bata yi min ba? Ina ™yaleta ne kawai dan wani lokacin ina son"

"aurenta da SAHEER."""

"""Kin ganni nan, bana son sirika ta shigo ta juya min Wa, na fi so na juyata kamar yadda zan juya W"

"ana. Bazan lamunci ina uwarsa da ta haife sa, kuma ace wata mace ce take da iko dashi ba, bazan yarda da sai ya fara kai mata kafin ya kawo min ba."""

"""Shiyasa na amince ya auri Islaha, dan ita ta sanni na santa, ta san bana son raini, kuma duk"

"abinda na shinfiWa shi zata hau kai ta zauna. In ba dan haka ba ya za a yi na amince ya aure ta?."""

"Ta yi dariya ta ce, ""Amma ke kanki kin san Islaha bata da kunya, kema ba raga miki take yi ba wani"

"lokacin."""

"""Tunda tana son Wana dole ta kwantar da kai. Ba fa son auren nake yi ba, ko yanzu zan iya soke"

"shi wallahi."""

"""Ke dai Allah ya rabaki da sharrin sirikan zamani, ita Islahan ai ba a goshinta aka rubuta zata yi"

"miki abinda ki ke sba. Kin san halinta sarai, bata jin magana, buWaWWen ido ne da ita. Tunda a gidan marayu ta girma."""

"""Rashin kunya ai bata isa ta yi min, tunda tana matu™ar son Saheer dole ta bi duk abinda nake so. Ta isa ta ™i yin abinda nake, a gidan nan ta ke zaune ina so ki tuna, babu dangin uwa ko na uba a tsakaninmu, kawai shegen taurin kan Saheer ne ya saka ya kawo min ita na karSa. Kuma ko da ya fito da maganar aurenta zai yi saboda haka na bashi dama, bata isa ta aikata abinda bai yi"

"daidai da ra'ayina ™yale ta ba."""

"""Ya kamata ki dage, dan irinsu in suka kama yaro basa saki da wuri. Islaha tana da buWaWWen ido, babu inda aikin jaridar nan ba ya kaita, har kwana tana yi a waje. Akwai abinda za a nuna mata"

"wanda bata sani ba?. Ke bakya ganin yadda ta kanainaye Saheer Win, yake sonta kamar ransa."""

"""Kamar ya haWWiyeta kuwa, ni wani lokacin son har tsoro yake bani wallahi, yarinya kamar ta lashe"

"masa kurwa? Ko ni ba ya nunawa son da yake nuna mata."""

"""Ahaf, ba na faWa miki ba. Sai kin mi™e tsaye, in ba haka ba wallahi kina ji kina gani zata mallake"

"miki Wanki. Islaha, ke dai ki kalli yarinyar nan kawai, ta wuce tunaninki."""

"""Duk shegantakar da take ji dashi na fita, duk wani iskanci da yawon duniya da take ta™ama dashi"

"wallahi na fi ta."""

"""Ke ba dan kura ta yi lafiya ba, da na aikata abinda har ta koma ga Allah bata isa ta yi sa ba."

"Dalilina Waya, saboda na mallake Saheer ya saka na ™yale mata shi, na san halinta, babu wani motsi da zata yi ban fahimta ba. Kin ga bata isa ta kawo min kissa akan mallake min Wa ba, na dame halayenta na shanye."""

"""Tana ji tana gani zan juya Waya, sai dai ta zama ´ar kallo. Kuma daman ya fi ™arfinta, yaro fari"

"kar dashi jiki duk madara, ita kuwa fa?. Waye ya san me iyayenta suka aikata aka haifo ta, aka kasa rainonta aka cillata gidan marayu? Ke daga ganinta kin san ba dukkanta ce fulani ba, akwai sirki."""

"""Ai haske kawai Saheer zai nuna mata, amma wallahi ta fi sa kyau. Ki duba zagayyun idanun da"

"Allah ya yi mata mana, wallahi kaf gidan nan babu mai kyaun Islaha. Shiyasa nake faWa miki ta waye, ta san komai, manyan mutane sun daina yayin mata masu haske, irinsu ake kai musu. Sun ce sun fi laushin jiki."""

"Mama ta taSe baki ta ce, ""shegiya, sai taurin kai da rashin kunyar tsiya. Amma zan yi maganinta"

"wallahi."""

Dariya Umma ta yi suka cigaba da tattaunawa akan fita ™asar waje aikatau.

"Sallama aka sake yi aka shigo, Mama ta amsa tana kallon kyawawan ´an matan ´a´anta guda"

"biyu, ko wacce ta ci kwalliya ta yi adon gashi, sai tashin ™hamshi suke yi."

"Mama ta bisu da kallo har suka zauna sannan ta ce, ""haka mu ka yi da ku, tun safe baza ku dawo"

"ba, sai yanzu magrib ta kusa?."""

"Šaya daga ciki, fara mara jiki, mai kyaun fulani, wacce take amsa sunan Hanan ta ce, ""Mama aiki ne ya tare ni, sai da na ciko jakata sannan na dawo"" ta faWa tana buWe jakarta, ta Wauko rafar Wari"

biyar guda uku ta ajjiyewa Mama.

"Mama ta harari kuWin ta ce, ""duk wannan jimawar a naira dubu Wari da hamsin kawai?."""

"Hanan ta ce, ""Sai a gode Allah."""

"Mama ta kalli Wayar, wacce take ba™a mai kyau ta ce, ""sai wani cika ki ke kina batsewa, ke kuma"

"nawa ki ka ™wamuso?."""

"Labiba ta Wan kawar da kai ta ce, ""dubu Wari biyu ce, kuma na bayar zan canja waya. Ni na gaji"

"Mama, bacci nake ji"" ta faWa tana niyar mi™ewa."

"""Zauna dan ubanki, ki kashe kuWin kuma ki ce min kin gaji, aikin uban me ki ka yi da ki ka gaji?. Me"

"saurayin na ki ya yi miki?. Ban ja mu ku kunne akan ban da iskanci ba, me ya aikata miki ki ka gaji?."""

"Labiba ta ce, ""Mama ni babu abinda na yi, kawai na gaji ne"" ta faWa tana tashi ta bar wajan Hanan"

ta bi bayanta.

"Umma da take kallon Mama da mamaki, tana girgiza kai ta ce, ""kina tura su wajan samarinsu"

"samo kuWi, amma sai ki ce kar su yi iskanci. To in ba iskanci suke yi ba me zasu yi maza su basu kuW i irin wannan?."""

"Ta kalli Umma, sai ta haWe rai ta ce, ""Uhum Maimuna, bana so a saka min ido a lamarin gidana"

"dana ´a´ana, dan na tura su samo kuWi ai ba ta hanyar iskanci da maza ake samun kuWi ba, akwai hanyoyi da yawa da zasu ciko jaka ba sai sun bada kansu ba."""

"""Kina da abin mamaki, to me suke yi suke samun kuWin, wa'azi suke yiwa mazan?."""

"""Maimuna ya isa haka, in ma karatu suke koya musu babu ruwanki. Na tabbatar ´a´ana basa"

"neman maza, suna samun kuWi da dabara irin ta mata. Sai anjima."""

"Maimuna ta mi™e ta ce, ""Allah ya kyauta, ke kika haife su ai"" ta faWa tana fita daga falon."

"Mama ta bita da harara ta ce, ""munafukan banza, ko yaushe aka ce musu sai ta hanyar ba da kai"

"mace zata samo kuWi a wajan maza oho"" ta faWa tana kwashe kuWin da Hanan ta ajjiye ta shiga W akinsu. Dan tana ta je ta samu Islaha, bata isa ta ce bata samo kuWi ba. Ko a ina ne sai ta nemo ta bata, ba a banza take ciyar da ita ba."

"*MAFI AS QUATERS,*"

"*YOLA, ADAMAWA STATE.*"

"Alhaji AbdulAziz Zubair Yola, babban mai kuWi ne a faWin garin Adamawa, kuma mahaifin matashin mai kuWin da ake ji dashi a kaf faWin africa. Mutum ne mai kirki, girmama mutane,"

"biyayya da sanin ya kamata. Yana ™aunar iyalansa, abinda suke so shima shi yake so."

"Alhaji AbdulAziz yana mata guda huWu, Hajiya Saddi™a itace uwa gida sarautar mata, AbdulAziz number two kenan, domin kuwa in AbdulAziz ba ya gari itace take zama tamkar itace shi. Tana da iko a gidan, kowa a ™asanta yake, hatta mai gidan a hannunta yake. Yadda ta dama haka ake sha,"

"babu mai ja da ikonta, dan ko ka ja kaine zaka sha wahala."

"Duk manyan ´a´an gidan yaranta ne, mazan huWu mata biyu. Duk wani abu na harkar gida ´a´"

"anta ne a kan gaba, dan su ne manya dasu ake damawa."

"Matarsa ta biyu Hajiya Salamatu, Wanta guda Waya namiji, kuma ya kasance mara lafiya kamar"

"mai taSin ™wa™walwa, duk ragowar da suka biyo baya mata ne, su ne manyan ´a´anta."

"Hajiya Nadira itace matarsa ta uku, haifaffiyar ™asar india, cikakkiyar likita a Sangaren mata,"

"karatu ya kai sa ™asar india, suka haWu ya aure ta."

"Mace ce mai sanyin hali da son jawo mutane a jiki. Sai dai ta zama kamar bare a cikinsu, babu"

"wanda yake shiga sabgarta balle a je inda take, sun ajiiyeta a gefe basa mu'amala da ita, saboda ta kasance ´ar wata ™asar ba jinin fulani ba. ³a´an Nadira uku, namiji Waya mata biyu."

"Hajiya Amina itace amarya, mai ™arancin shekaru da yarinta, dukkansu sun haifeta. ³a´anta"

biyu duka mata.

"""Mama!."""

"Ta Wago ta kalli wanda ya kira ta da ta ce, ""meye?."""

"Ya zauna a kusa da ita ya ce, ""Mama abin nan yana Waure min kai, kin san me ya faru?."""

"Ta ajjiye wayar hannunta ta ce, ""me ya faru?."""

"Ya sauke numfashi ya ce, ""REHAAN!."""

"Ta bisa da harara tana jan tsaki, in akwai sunan wanda ta tsana a duniya to Rehaan ne, bata son"

"jin sunansa a kusa da kunnenta, ba ta so ambace sa in tana waje. In an ambacin sunansa ta ji daWi, to tabbas an faWi faWuwarsa, ko an faWi wani mai muni. Amma indai aka faWi alkhairinsa, yanzu zata ji ranta ya Saci."

"Ta ce, ""me ya samu Rehaan Win?."""

"""Mama yaron nan yana neman wuce tunanin mu, yana so ya zarce inda mu ke tunanin yake."""

"Cikin fusata ta ce, ""dallah ka faWa min, meye ya faru?."""

"Ya sauke numfashi ya ce, ""Sunansa ya dawo na biyu a jerin sunayen masu kuWin africa masu ™"

"arancin shekaru."""

"Idanu ta buWe tana kallonsa ta ce, ""Sameer kar ka yi min ™arya."""

"""Ba ™arya nake yi miki ba, kalli ki gani"" ya faWa yana nuna mata wayarsa."

"Bata musa ba ta karSa, ta ga yadda aka yi analysis ga sunansa nan a layi na biyu, saura kaWan ya"

tarar da na farko.

"Ba™in ciki ya mamaye mata zuciya, ta mi™a masa wayar, ta mi™e tana zaga falon cike da tunanin"

mafita.

"Ta rasa yadda zata yi da Rehaan, kuWin da ya kamata ace ´a´anta ne suka yi shine yake"

"mallakarsu. Hakan yana taSa zuciyarta, yana sakawa mata ba™in ciki da hassada."

"Mama ta ce, ""ya aka yi haka yake faruwa, Ya aka yi abubuwa suke jagule mana ne Sameer?."

"Rehaan fa, kai kanka ka girmesa da shekara Waya. Ya aka yi yake samun Waukaka, bayan ku ne manya a cikin gidan nan?."""

"Sameer ya ce, ""wallahi zamansa a england babbar illa ce a gare mu, ni ban yarda ba dukiyar Abba"

"ce a hannunsa ba. Ta ya yaro ™arami ace ya mallaki abinda mahaifinsa bashi dashi, Hamma Zayyad da yake babba bashi dasu, mu ma da muka biyo baya bamu dashi. Kina jin wannan kin san haWawa aka yi, gabaWaya dukiyar Abba tana hannunsa, mu muna nan an haWa mu da ™ananun abubuwa na banza. Babu damar mu yi magana sai ace ai shi a nan ya girma ba, shi a a can aka haifesa, a can yake kasuwancinsa da sauran shirme. Mama in muka zuba ido, kaf dukiyar Abba da take can zata zama haram a gare mu."""

"Mama ta girgiza kai ta ce, ""ya aka yi hakan yake faruwa, ya aka yi abubuwa suke lalace min ne?."

"Meyasa na kasa Waukar mataki akan Rehaan, meyasa yake shigar min hancina na kasa fato shi?."""

"Sameer ya ce, ""dole a san abinda za a yi, bazai yu kina babba a gidan nan, muna manya a gidan"

"nan, ace komai yana hannun Rehaan ba, dole ki san yadda zaki yi ya dawo nigeria, in ba haka ba wallahi muna ji muna gani komai zai fi ™arfin mu."""

"""˜arya ne wallahi, yadda ku ka kasance manya a gidan nan babu wanda zai samu Waukaka sama"

"da ta ku, dole a dakusar da Waukakar Rehaan, dole Rehaan ya dawo ™asar nan.."""

"""Šaukaka ta nawa kuma Mama? Sunan Rehaan da labarin Ray ina ne bai shiga ba a faWin ™asar nan?. Sai dai a kiyaye gaba, amma wannan ya riga ya faru. Kai tsaye ki samu Daada da wannan"

"maganr, ki same ta ita kaWai ce zata zama silar dawowarsa ™asar nan har abada."""

"Ta girgiza kai cike da gamsuwa ta ce, ""yanzu nan zan je na same ta, indai a kan ganin bayan W"

"aukakar Rehaan ne babu abinda bazan yi ba Sameer, zan iya sadaukar da duk abinda na mallaka dan ganin Rehaan ya dawo ™asa, ku kun hau sama."""

"Sameer ta mi™e ya fita cikin gamsuwa sa kalamanta. A ganinsa ta ya ya suna manya a gidan, ™"

"aninsu wanda ya zama shine namiji ™arami a kaf gidan, ya zo ya fi su Waukaka."

"Mama kuma ta dafe kai cikin rashin mafita, a bayyane ta ce, ""Rehaan! Rehaan! Rehaan! Ka shiga"

"rayuwata, ka hanani sakewa Rehaan, ka hanani cika burina. """

"Ta girgiza kai ta ce, ""Baka isa ba wallahi, baka isa Waukakarka ta disashe ta ´a´ana ba, yadda na kasance gaba da kowa a matan gidan nan, dole ´a´ana su kasance gaba da kowa a yaran gidan nan. Babu wanda ya isa ya sha gabansu, su Win su za a kalla aje ace su bayar, ba kai ba. Tun"

"kana yaro ka ke bani wahala, amma a yanzu bazan barka ba Rehaan, bazan taSa barin ka ba."""

A fusace ta ja hiijabi ta fito daga part Winta zuwa part Win Daada.

"Daada mahaifiyar Abba ce, tsohuwa mai rigima, duk abinda ta ce a gidan babu wanda yake"

"tsallakewa, duk dokar da ta shinfiWa sai an hau kai ba a karkacewa. Daada mace ce mai fitar da ™ o™on usuli, nata nata ne, wanda ba nata ba, ba nata bane. Daada bata son Nadira ko kaWan, duk abinda zata yi zata ce daman ba jinin fulani ba ce ba."

"Mama ta shiga da sallama, Daada da take zaune ta amsa mata zauna a akan carpet."

"Mama ta ce, ""Daada barka da yamma."""

"Ta yi murmushi ta ce, ""Yauwa Saddi™a."""

"""Na same ki lafiya?."""

"""Lafiya lau."""

"Mama ta gyara zama ta ce, ""Daada wata magana ce take tafe dani."""

"Daada ta murmusa ta ce, ""Uwar gida kenan, kina gaba da kowa a gidan nan, kuma kin fi kowa"

"hankali. ina jinki."""

"Mama ta ji daWi, ta sake samun ™arfin guiwa sannan ta ce, ""Yanzu Daada fisabinillahi haka zamu zuba ido abubuwa

Please Login or Register in order to submit comment