gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAGAYAR DUTSE Dawowa Mai Hatsari book 1 By Nana Haleema Chapter 16 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda suka bar wajan Daada take ta murmushi ita kaWai, in ta tuna rigimar matar bata"

sanin lokacin da take dariya ita kaWai.

Musaamma yadda take faWar sunanta da yadda take cewa zata aura mata jikanta. A haka ta ™

"arasa gida, ta biya mai keke kuWinsa ta shiga cikin gidan."

"Tana shiga suka haWa ido da Umman su Safeera, ta Wuka ta ce, ""Mama ina yini, Umma ina yini"" ta"

faWa tana niyar wucewa.

"Mama ta ce, ""tun ™arfe huWu na asuba ki ka bar gidan nan, baki dawo ba sai yanzu bayan sallar"

"i'sha. Ace kin je yawon ta zubar ki ce ke ba haka ba."""

"Islaha dai bata ce komai ba, tana jin Umma ta ce, ""to ke har san tabbatar miki? Ai ko baki faWa ba kowa yana ganin idanun yarinyar nan ya san ta san maza. Kai tsaye take kallon idon ka ta yi"

"magana, in ba mata irinsu ba babu mai kallon idon na gaba dashi ya yi magana."""

"Islaha ta shiga Waki ta yi alwala ta yi sallah, sai a sannan ta ji tana jin yunwa sosai."

Ta fito fito a sanyaye tana jin Umma da Mama suna tattaunawa akan tafiya aikatau wata ™asar.

"Islaha zata gifta Mama ta ce, ""ga baiwa kin ajjiye ko? Sai dai ki je yawon ki, ki dawo ki tarar na"

"dafa miki abinci ko? To baki isa ba wallahi, yau ba ki da abinci a gidan nan."""

"Ta tsaya cak bata ™arasa ba, ga yunwar da take ji tana neman hallakata, dan ji take kamar ana W"

"aure mata cikin ta. Iya tea kaWai ta sha tun safe, bayan shi bata cin komai ba."

"Ta koma da baya ta Wauko rabin kuWin da Saheer ya bata jiya, ta fito ta ™arasa gaban Mama ta"

ajjiye.

"Islaha ta Wan kalli Mama sannan ta ce, ""ayi ha™uri da wannan, babu yawa."""

"Mama ta kalli kuWin ta ga basu wuce dubu goma ba, ta harari kuWin ta ce, ""iya abinda aka biya ki"

"daga daren jiya zuwa yau kenan?."""

"Shiru ta yi bata ce komai ba, dan tana gudun buWe bakinta akan Mama, duk ranar da ta mayar"

"mata bazata ji daWi ba, tana ha™ura ne kawai in ta tuna Saheer, shiyasa bata cewa komai."

"Mama ta ce, ""baki ji me nace ba?."""

Islaha ta du™a ta Wauki kuWin ta juya da niyar barin wajan.

"Mama ta ce, ""ke dakata, dawo da kuWin nan."""

"Ta Wan yi murmushi kafin ta ce, ""kin ce ya yi kaWan ne, shiyasa na Wauka."""

"""Ajjiye malama, ki je ki zuba abinci."" Islaha ta juya tana murmushi, wato ita Mama indai da kuWi"

an wuce wajan kawai.

"Tana barin wajan Umma ta ce, ""yanzu yarinyar nan ce tace baza ta je aikin nan da ki ka faWa min"

"ba?."""

"Mama ta ce, ""shiyasa na juyo gurin ki, in Safeera zata je a satin nan za a yi mata komai ta wuce, in"

"kuma baza ta je ba, ke ki girgije yaran nan ki Waga kawai. In kina zaune wallahi zaki ga zaunau."""

"Umma ta ce, ""wannan a rubuce yake wallahi, ki Wauka an yi an gama, dan ni zan je ba Safeera"

"ba."""

"""Ya fi dai, dan wallahi kuWi ake samu lokaci Waya. Kuma tsaf zasu yi miki kyautar mota ko kyautar"

"gida. Ga kwana a c, ga aikin ba wani yawa ne dashi ba, sai kinga dama zaki Wan motsa. Bakya ganin waWanda suka tafi suna yin ™iba?."""

"""Ina gani woman leader."""

"""Kaza ce, da ac, da hutu ga albashi mai tsoka. Ni ina mamakin matan da suke dan™arewa a gida su kasa taSuka komai saboda miji. Mtsw! Allah na tuba ba dan ina samu daga inda nake zaune ba,"

"babansu Saheer Win banza? Da yanzu ina can ina haWa hajata wallahi."""

"""Ai kin lasa min zuma a baki ne yar uwa, wannan tafita dole a yi ta."""

"Mama ta Wan taSe baki ta ce, ""ki dai gama komai da gaggawa, in ke ce Win gobe ki zo a je a san"

"abinda za a yi, in Safeera ce itama ki turo ta gobe a gama komai."""

"Umma ta ce, ""haka za a yi Woman leader, zan san abinda zan yi kuwa yanzu nan. Bara ma ki ga"" ta"

faWa tana mi™ewa ta fita daga falon.

"Islaha tana jin su har Umma ta fita, ta san dai ko me za a yi Safera baza ta amince ta bar ™asar nan saboda aiki ba, kuma itama Umman tasan ba zuwa zata yi ba, saboda Baba ba irin Baffa bane. Shiyasa hankalinta bai wani tashi ba. Ta zuba abinci ta zauna a kitchen Win ta ci ta sha ruwa"

sannan ta fito.

"A lokacin Hanan ta shigo tana yatsine fuska kamar mai na™uda. Mama ta bita da kallo ta ce, ""sai"

"yanxu?."""

"Hanan ta ce, ""Mama na tsaya na samo kuWi mai tsoka ne fa, kin ga"" ta faWa tana nuna nata bandle"

"na rafar ΄an dari biyar biyar guda goma, sababbi kar mi™a™™u."

"Mama ta buWe ido tare da mi™ewa tsaye cikin mamaki da farin ciki, ta karSi kuWun tana kallo,"

"kafin ta rungume Hannan ta ce, ""Hanan a ina ki ka samo kuWin nan masu yawa haka?."""

"Ta Wan yi murmushi ta ce, ""Haba Mama, yaushe ki ka fara tambayar a ina na samo kuWi?."""

"""Ke dallah ba ina nufin ki faWa min ba, wanda ya baki nake so na ji."""

"""Tunda na samo ai shikenan Mama."""

"""Farar haihuwa kenan, masu baiwar da maza suke basu kuWi ba tare da sun ba da kansu ba. Ina ji"

"daku ΄a΄ana."""

"""ki ri™e duka Mama, ni na gaji bacci zan yi"" ta faWa tana wucewa ciki."

"Mama ta buWe murya cikin murna ta ce, ""Allah ya yi miki albara, Allah ya ™arawa neman ki"

"albarka."""

"Labiba da take kallonsu kishi ya kamata, ta ji a ranta ta ya Hanan zata kawo dubu Wari biyar ita"

bata kawo ba? Ta ya zata zuba ido Hanan ta fita kawo kuWi gidan?.

"Ta girgiza kai tare da yin ™wafa, ta yi tsaki ta ce, ""dubu Wari biyar ce ba fa Mama, ba wata tsiya ba."

Sai murna ki ke yi kamar ta bani miliyan biyar.

"Mama ta kalle ta ta ce, ""wata tsiya ce mana Labiba, ke kin kawo Wari biyar Win ne?."""

"""Ai na fi ™arfin na kawo ™ananun kuWin wallahi. Nawa ce dubu Wari biyar?."""

"""Tunda baki taSa kawowa ba ki yi shiru."""

"""Ai dan na canja waya ne. Amma ki zuba ido, zan kawo wanda ya fi na ta wallahi."""

"""Mu gani a ™asa."""

"""Zaki gani Mama"" ta faWa tana shiga Waki cike da hassada da ba™in cikin an fita."

"Islaha dai bisu da kallo, ganin yadda ake gasa akan samo kuWin da ba a san daga ina suke zuwa ba,"

har kishi ake nuna ™arara akan Waya ta kawo Waya bata kawo ba.

"Ta girgiza kai, tana koyar darasi mai girma a gidan Mama, tana ganin dramar da take so ta ga ™"

"arshenta, dan ta san ba za a yi happy ending ba. Bata ce komai ba ta shiga Waki jikinta duk a gajiye..."

Nana Haleema
'<Ψϋί

*RAGAYAR DUTSE.*

©ώ *Nana Haleema.*

*Book 1*

*Page 016.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina

"so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah."

"Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su"

suna nan kamar haka.

Kabbasa spray

Dufr khumrah Mahlab khumra Body milk Kuleccam

Matan Maiduguri Ready to use dilka Halawa

Shuwa Arab hair mist Cotton incense Dorut after period Dukhaan stool Gabgab

Sandal flex Sandal sukkaria Kajiji

Halud Arabian oud Oil perfume Room fresh

Multi purpose sprays Curtains incense Kabbasa

Farce

Marshoosh

Senegalese Kajiji

Dilka soap Dilka cream

"Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku"

lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168

08164570032

"Umma tana fita daga gidansu Saheer gidan ™awarta Atika ta shiga, aminiyarta kuma abokiyar sirri."

"Tana shiga ta Wauki kujera ta zauna a tsakar gida ta ce, ""Atika kina ina?."""

"Tana daga Waki ta fito ta ce, ""Gani nan, aminiya ta samu ne?"" Ta faWa tana fitowa ta zauna akan"

kujera itama.

"Umma ta ce, ""ta samu, ga bikin zuwa babu zanin Waurawa ™awata."""

"""Ina jinki, meya faru?."""

"""batun tafiya Saudia aikin nan ne, kin ji kuWin da ake samu?."""

"""Allah ™awata?."""

"""Bari kawai ™awata. Ga gidan aikin an samu a hannu, kawai ma'aikaci ake nema."""

"Atika ta ce, ""ba kin ce Safeera za ki tura ba?."""

"Umma ta ce, ""Yarinyar baza ta yarda ba, kin san tana tare da Islaha, kullum cikin kushe abin suke."

"Babanta ma ya ce indai shi ya haife ta bazata je ba. Shine nace masa amma ni ai ba shi ya haife ni ba, zan dire su in yi tafiyata."""

"Atika ta ce, ""abinda zan ce miki kenan, da ™arfin ki da lafiyarki ki tsaya ana Sata miki rai da"

"lokaci?. Meye amfanin ki, meye amfaninki in ba ki je ba?."""

"Umma ta ce, ""Atika ba Baban Safeera nake ji ba, mutanen Katsina nake ji. Baza su Waga min ™afa"

"akan haka ba, Yayanmu fata-fata zai yi min."""

"""In sun sani ba, sai ki tafi ba tare da sun sani ba. In dai kin je ba shikenan ba?."""

"Umma ta Wan ti jimm alamun tunani kafin ta ce, ""Ina son zuwan nan wallahi, amma ban san ya"

"zan yi ba."""

"""Maimuna ki daina tunani, ki ajjiye ΄a΄an nan ki, ki je ki tara kuWin auren Safeera. An kawo kuW inta fa, ko yaushe za a iya maganar aurenta. Me Baban nata yake dashi, ke me ki ka tara da zaki"

"aurar da ita?."""

"""Babu Atika."""

"""Amma kin samu dama zaki bari ta gudu?in wannan damar ta kubce mana a ina zamu samo"

"kamar ta?."""

"""Babu."""

"""Ki rufe ido kawai ki yi, indai kin je Win dai ba shikenan ba? Duk faWan da za a yi sai ayi, tunda kin"

"je ai komai ya ™are. Shi kuma Baban in ya sake ki fa shikenan."""

"Umma ta buWe ido ta ce, ""Saki Atika! Da girmana?."""

"""To sai ki zauna ai. Kin san in da aurensa a kan ki bazai bari ki tafi ba, in kuwa ya sake ki ba shikenn"

"kin huta ba, ki yi tafiyar ki babu nauyin kowa a kan ki."""

"Umma ta ce, ""Gaskiya ne wannan, kin ™ara min ™arfin guiwa sosai Atika."""

"""Ahto, akan me zaki bari Baban Safeera yana juya ki? Dan ya hana ΄arsa ke ai bai haife ki ba."""

"""Gaskiya ne wannan, kuma zan iya tafiyata mutanen Katsina basu san na tafi ba."""

"""DaWina dake akwai Waukar haske."""

"""Bara in je na same shi"" ta faWa tana mi™ewa ta fita ta nufi gidanta."

"Tana zuwa ta samu Baba ya dawo, ta zauna tana sake yi masa magana a kai."

"Baba ya bi Umma da kallo ya ce, ""amma na faWa miki bana son wannan maganar ko? Na faWa miki"

"kar ki sake gangancin yi min irin wannan maganar ko Maimuna?."""

"Umma ta ce, ""kuWin nan fa in an samu ba ni kaWai zan saka a gaba na cinye ba, amfani zamu yi"

"dasu in auren Safeera ya tashi. Baka dashi, kuma baka da hanyar samu, laifi ne dan na nemo mafita domin gaba?."""

"Bab ya ce, ""to baza a yi ba, babu inda Safeera ko wani a gidan nan zai je, wallahi."""

"Umma ta kalle sa cike da mamaki ta ce, ""harda wallahi?."""

"""Wallahi Allah baza su je ba, matu™ar ni na haifesu babu wacce zaki Wauka ki kai wata ™asar"

"neman kuWi."""

"Umma ta girgiza kai ta ce, ""na ji, kai ka haifesu kana da iko dasu. Amma ni ai ba kai ka haife ni ba"

"ko?."""

"Baba ya bita da kallon mamaki jin abinda ta ce, ya gyara zama ya ce, ""bani na haife ki ba, amma"

"akwai aurena a kanki. Yadda na isa da ΄a΄ana haka na isa dake, kafin na samu ΄a΄an ke na samu, kafin na faWa su ji, ke zan fara faWawa ki ji. Dan haka kema babu inda zaka je."""

"""Ai kuma baka isa ba, wallahi baka isa ba. Ka hana ΄a΄ana zuwa nima ka hana ni? Kaima ka san ai bazai yu ba. ³a΄anka ka ke da iko dasu amma bani ba, ΄a΄anka zaka hana tafiya bani ba. Aure da ka ke magana aki kalma uku zata warwaresa, daga nan babu komai tsakanina da kai, zan"

"je duk inda na ga dama."""

"Baba ya bita da kallo, jin tana maganar saki har haka, har tana cewa kalm uku ce ta raba auren ya"

"ce, ""shikenan Maimuna, Allah ya taimaka"" ya faWa yana mi™ewa ya bar mata wajan, kar zuciya ta tunzurasa ya aikata wani abun da zai yi danasani."

"Safeera ta shigo falon a sanyaye ta ce, ""Haba Umma, me ki ke aikatawa haka? Ina ke ina tafiya"

"wata ™asar aiki?."""

"Ta bi ta da harara, cikin faWa ta ce, ""ba kin biyewa ubanki ba?."""

"""Umma ko Baba hana ba, wallahi ni bazan je ba."""

"""Kar ki je Safeera, kar ki je Win mana. ³ar iskar yarinya mai taurin kan tsiya, wacce bata son abinda uwarta take so. Matsa ki bani waje ko na tsinka miki mari!"" Ta faWa a fusace tana kallon"

Safeera.

"Safeera ta ja gefe ta tsaya tana kallon Umma da Wubun mamaki. Bata Wauka abin Umman ya kai haka ba, bata Wauka lamarin Umman ya kai wannan matakin ba sai yanzu. Akan zuwa wannan"

"aiki wat ™asa take ce mata ΄ar iska, har take cewa zata mare ta?."

"Umma ta ce, ""in baki je ba ai ni zan iya zuwa ko? Ina da ™arfi da lafiyar da zan iya yin ko wanne"

"aiki ne. Ki zauna Safeera, ni zan je, bazan taSa ganin arzu™i yana tunkaro ni n tsallake ba. Zan bar gidan nan in tafi, sai ki zauna ki cigaba da kula da ΄an uwanki, amma wallahi sai na je!."""

"Baba ne ya shigo ya dawo Waukar wayarsa da ya bari, ya ji kalaman Umma. Sai ya ga Safeera ta zube a ™asa tana kuka, ta ce, ""don girman Allah Umma ki rufa mana asiri, Umma don Allah kar ki tsallaka ki bar mu a nan. Ki zauna a tare damu, kar ki tafi wata ™asar saboda neman abin duniya."

"Da yawan aikin nan yaudara ce, wahala ake zuwa a sha a can."""

"Baba ya ce, ""™yaleta Safeera, matu™ar da aurena a kanta babu inda zata je wallahi!."""

"A fusace Umma ta ce, ""idan na kashe auren fa? In ka sake ni ba shikenan ba!?."""

"""Sai dai hakan, dan in dai kin ga kin bar ™asar nan tabbas babu aurena a kanki!."""

"""Ai daman sakina zaka yi, bazan zauna da auren ka ba nima.."""

"Safeera ta fashe da kuka ta ce, ""Umma na yarda zan je, na yarda zan je Win. Ki daina faWar wannan maganar don Allah, ni zan je na samo miki duk abinda ki ke so!. Ki zauna dasu Rukayya, ni"

"zan js na samo duk abinda ki ke so ki samo a can"""

"Cikin tsawa Baba ya Wago Safeera ta mi™e tsaye, ya ce, ""wallahi baza ki je ba! Ni na haife ki, ina"

"da ikon saka ki ko na hana ki, babu wanda zai yi miki dole akan wanann. Baza ki je Safeera, ita dai tunda bani na haife ta ba ki ™yaleta ta je!."""

"Umma ta ce, ""nima ai ban ce ta je ba, ta yi zamanta ita da kai, zan je na yi abinda nake so. Sai ka"

"zauna dasu su maye maka gurbina"" tana faWar hakan ta fita daga falon."

"Safeera kuka take yi sosai, murya tana rawa ta ce, ""Baba don Allah ka bar ni in je, ka ji!."""

"Baba ya kalle ta cikin sigar kwantar da hankali ya ce, ""ki kwantar da hankalinki, barazana take yi"

"miki dan ki ce zaki je, amma babu inda zata je. Ki daina kuka."""

"Safeera ta goge ido ta ce, ""Baba Umma da gaske take, ban taSa ganinta cikin irin wannan yanayin"

"ba sai yau, ni ka bari in je don Allah, ka ™yale ni na tafi don Allah!."""

"Baba ya girgiz kai ya ce, ""babu inda zaki je wallahi, ki bar maganar nan dan ba yuwa zata yi ba."""

"Ta yi ajiyar zuciya tana goge hawaye, ta juya ta kalli ™annenta mata guda uku duka mata."

"Rukayya da ta kasance babba mai bin Safeera, ta ™araso ta ce, ""Adda ina Umma zata je?."""

"Baba ya ce, ""Rukayya ki zauna da ΄ar uwarki, ina zuwa"" ya faWa yana fita daga falon."

"Safeera kuwa bata iya amsawa Ruky ba, kuka kawai take yi tana tunanin ya zama dole ta je"

"Katsina dangin Umma ta faWa musu halin da ake ciki, dan gaskiya baza ta bari Umma ta aikata wannan Sarnar ba."

*******

"Suna zaune a compond Win gidan, ta saka hijjab har ™asa shi kuma yana gefenta a zaune."

Suna ta hira cikin nishaWi da soyayya.

"Saheer ya ce, ""na fito dake bayan na san a gajiye ki ke."""

"Islaha ta Wan murmusa ta ce, ""Babu komai, ai na Wan huta kaWan."""

"""To ya aikin? Kin samu ganin Mr Ray Win?."""

"""A'a, amma mun ga Mr Jafaar, ko yaushe ance suna tare."""

"""Good. Sai aka yi ya kenan?."""

"Ta Wan kalle sa ta ce, ""dashi mu ka yi magana, ya tabbatar min da kansa zai neme ni in lokacin hirar ya zo. Amma a yanzu ya faWa min hira dashi bazai yu ba, dan ya faWa min gaskiya bai rufe ni"

"ba."""

"Saheer ya ce, ""hakan yana dakyau, Allah ya taimaka matar Hamma."""

"Ta yi murmushi ta ce, ""Amin ya rabbi Hamma."""

"Sai ta ja numfashi ta ce, ""ka san me na gani?."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""sai kin faWa."""

"Islaha ta ce, ""Hafsa na gani a hotel Win fa, kuma da ita kaWai na gani da sau™i, zan iya cewa wani"

"abun ne ya kai ta, amma ita da wani ne har na ga sun shiga Waki."""

"Ya buWe ido cikin firgici ya ce, ""Hafsa dai ta orpahange?."""

"Ta Waga kai ta ce, ""ita fa. Lokacin da na gansu mu kuma lokacin mun fito, sai hankalina bai kwanta"

"ba, sai na koma daga baya. Ka ga"" ta faWa tana nuna masa hoton da ta Wauka na Hafsa."

"Ya karSi wayar ya yi zooming yana kallon fuskar Hafsa, cike da mamaki ya ce, ""ai kam itace. Amma"

"me ya kai ta hotel su da ba a barinsu su fita past six?."""

"""Ashe ka fahimci abinda yake a raina. Kuma kasan na je gidan, an tabbatr min da kwanan Hafsa"

"biyu bata nan."""

"Ya bata wayarta sannan ya ce, ""waye ya faWa miki?."""

"""Zainab ce, kuma tana cikin faWa min Fadwa tazo ta hanata, sai hakan ya sake jefa min zargi a"

"zuciyata Hamma."""

"""Zargin me ki ke yi?."""

"Ta kalle sa suka haWa ido ta ce, ""ina zargin ana aikata mummunan abu a gidan nan, zuciyata tana"

"bani ana fitar ΄an matan gidan a kai su inda bai kamata ba."""

"Saheer ya girgiza kai cike da gamsuwa ya ce, ""gaskiya ne wannan, nima kaina yanzu na fahimci"

"zarginki. Amma meyasa da ki ka ™i faWa min?."""

"Ta rausayar da kai ta ce, ""zargi ne ai shiyasa, yanzu da na samu hujja ai na faWa maka."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""yanzu what next?."""

"Ta sauke numfashi sannan ta ce, ""zan sake samun evidance mai girma, daga nan sai na yaWa"

"maganar zuwa gaba."""

"Ya kalle ta kaWan ya ce, ""amma in hakan ya tabbata sun ci amana wallahi, Allah ya ba su amana"

"suna ci."""

"Sai kuwa ta ta sake fusata, ta fara magana cikin kaushi ta ce, ""bari kawai, na rantse da Allah babu"

"wanda zan sassautawa, wallahi ko waye yake da hannu a lamarin nan sai na tabbatar da ya tafi gidan yari."""

"""zan baki goyan baya Wari bisa Wari. Allah ya kare min ke, ya cigaba da baki nasaraa a rayuwarki."""

"Ta yi murmushi tana kallonsa, ™aunarsa na sake shiga cikin zuciyarta."

"Ta sunkuyar da kai tana blushing ta ce, ""Amin Hammana."""

"Murmushi ya yi ya ce, ""ina ji kamar na...."" Sai bai ™arasa ba ya zuba mata ido kamar yadda ta W"

ago tana kallonsa.

"Ganin kallon da yake yi mata sai ya bata kunya, ta sunkuyar da kai tare da rufe fusksrta da tafukan"

hannunta masu matu™ar kyau.

"Hannunta ya bi ta kallo, muryarsa a ™asa ya ce, ""zaki jira ni in je Waki na dawo?."" Ta Waga kai"

bata buWe fuska ba.

Ya mi™e ya shiga ciki ta bisa da kallo cikin ™auna da soyayyar da take yi masa. Ta sauke ajiyar

"zuciya, domin kuwa Hamma ya cancanci soyayyarta mai girma, ya zamar mata komai a rayuwarta, bata da wani sai shi Win kawai."

"A lokacin ta hangosa yana tahowa, ta tsaya tana ™are matsa kallon yadda yake takawa kamar baya so. Hammanta duniya ne a wajan kyau, kai da ka gansa ka ga jinin fulani gaba da baya. Yana"

"da kyaun fulani, ga kwantaccen gashi ba™i irin nasu."

"A nutse ya ™araso ya zauna kusa da ita, ya Waga mata gira ganin yadda take kallonsa kamar bata"

"gane shi ba. Sai ya sake ya bata kunya, ta sunkuyar da kai tana murmushi."

"Ya yi murmushi ya ce, ""΄an mata wannan kallon fa?."""

"Ta rufe fuska da hannunta tana ΄ar dariya. Ya yi dariya ya ce, ""buWe fuskarki ki ga abinda na kawo"

"miki."""

"Ta cire hannunta ta ga ya Wauko sisirin bracelet kamar chain Win sar™a, silver colour mai hook a"

jikinsa.

"Ya mi™a mata hannu ya ce, ""i brought it for you, only Matar Hamma."""

"Ta yi murmushi tana kallon abin, ya mi™a mata hannu ya ce, ""kawo hannunki in saka miki."""

"Ta Wan zaro ido ta ce, ""In Baffa ya zo wucewa fa?."""

"Ya Wan Sata fuska ya ce, ""ba matata bace?."""

"""Ba a Waura ba Hamma."""

"""Amma an kusa ko, matar Hamma?."""

"Murmushi ta sake yi, ya ri™o hannunta a hankali ya Waura mata bracelet Win a hannunta."

"Ya bi hannunta da kallo, kasancewar abin silver ne ya haska brown skin Winta sosai. Ya kalle ta"

"suka haWa ido, ya ce, ""Ya yi miki kyau, matar hamma."""

"Kafin ta yi magana ya kai hannunta bakinsa, ya yi pecking hannun yana kallonta ya ce, ""mi yidi"

"maa, debbo Hamma"" (Ina sonki matar hamma)."

"Ta Wan sauke ajiyar zuciya, cikin duniyar masoya ta ce, ""miWo kadimi yidi maa, gorko debbo"

"Hamma"" (Nima ina sonka, mijin matar Hamma)."

"Bai saki hannunta ba sai murmushi da yake yi ya ce, ""Zan tafi Niger."""

"Ta kalle sa ta ce, ""yaushe?."""

"""Wata™ila gobe in sha Allah."""

"""In ka tafi sai yaushe?."""

"""Zan Wan kwana biyu, zan je in samo kuWin aurenki. Da na dawo nake so a gama ginin can mu yi"

"aure mu huta."""

"Ta marairace fuska ta ce, ""Ni bana so ka tafi."""

"Shima ya yi yadda ta yi ya ce, ""dole na tafi debbo Hamma, zan je na nemo mana kuWin da zamu"

"rayu cikin farin ciki."""

"Ta Wan sauke ajiyar zuciya ta zame hannunta ta ce, ""bana so ka tafi wallahi."""

"Ya bita da kallo dan ya san Mama tafi takura mata in baya nan, cikin rarrashi ya ce, ""ki cigaba da"

"ha™uri Islaha, komai ya kusa ya ™are in sha Allah."""

"Ta Waga kai ta ce, ""ni fa babu komai, kawai bana so ka tafi ne."""

"""In na tafi ai zan dawo, ki cigaba da yi min addu'a kin ji, My

Please Login or Register in order to submit comment