gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAGAYAR DUTSE Dawowa Mai Hatsari book 1 By Nana Haleema Chapter 7 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

interview. Nasan duk capacity da yake ji dashi, bai kai gwamna ba."""

"Saleem ya kalli Safeera ya ce, ""My love da alama Islaha bata san waye Ray ba wallahi, da ta san"

"waye shi da ko kuWi za a bata ta faWi abinda ta faWa bazata iya ba. Amma muna yi miki fatan nasara, in ki ka samu damar ganin Rehaaan, ko ba ki yi hira dashi ba, abin alfahrin mu ne balle"

"kuma a kai ga kin yi hira dashi. Daga ranar zamu sake tsada, ganin mu sai an cike form."""

"Ta yi tsaki, cike da takaicin yadda ake koWa sa ta ce, ""kamar wani sahabi?."""

"Safeera ta ce, ""ke dai Allah ya bamu sa a kawai, amma ya wuce tunaninki wallahi."""

"Saleem ya yi dariya ya tattara kayansa, dan tunda bata ra'ayi bazata karSi ra'ayinsu ba, sun san"

"halinta kaf, akwai jan magana. Saleem ya kalle ta ya ce, ""ina jiran ki"" ya faWa yana fita daga office."

"Safeerata ce, ""Islaha in tambaye ki don Allah."""

"Eslaha ta kalle ta ta ce, ""ina jin ki."""

"""don Allah meyasa ake yawan jifanki da sunan karuwa? Wanne abu ne ya faru da hakan yake"

"kasancewa?."""

"Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, ""ni kaina ban sani ba Safeera, abinda na sani yana da ala™a da"

"zaman gidansu Saheer. Shiyasa maganar bata damuna ko kaWan, duk yadda ka ke kallona a haka nake, sai me?."""

"Safeera ta ce, ""Haka ne. Amma magana mai kyau daga bakin mutane ma rahama ce Islaha."""

"Ta taSe baki ta ce, ""ki wuce record office, mu mun wuce"" ta faWa tana fita daga office Win."

"Safeera ta bita da kallo, a bayyane ta ce, ""tabbas zamanta a gidan su Saheer zai saka a dinga yi"

"mata wannan zargin saboda kowa ya san wacece Mama. Amma meyasa ake zargin tun a gidan da ta tashi ta lalace? Meyasa bata damuwa?."" Babu mai bata amsa, ta yi ajiyar zuciya ta fita daga office Win."

*********

"Mama tana zaune a gabansa malamin duba yana duba mata ™asa, ta yi shiru tana jira ya"

"gama ya zayyano mata abinda ya gano. Yana gamawa ya kalle ta ya ce, ""tabbas akwai dawowar Rehaan ™asar nan, nan ba da jimawa ba."""

"Ta yi ajiyar zuciya ta ce, ""na ji daWin hakan sosai."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""kuma zamu yi nasarar aikin mu a wannan lokacin."""

"Mama ta yi dariyar jin daWi ta ce, ""yauwa, haka nake so. Amma bazai koma ba dai ko?."""

"Ya sake dubawa kafin ya Wago ya ce, ""eh to, akwai yuwar komawar sa ™asar waje gaskiya, amma"

"kafin ya koma za a Wan sha ™alubale kaWan."""

"Mama ta ce, ""ni yanzu abinda nake ka yi masa, ayi masa bazai sake marmarin komawa can ba,"

"sannan yadda yake shiri da Janan, yadda Janan take bashi abu ya ci, a sake haWa ala™arsu ta yadda komai ta ce masa zai yi."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""wannan abu ne mai yuwa Hajiya"" ya faWa yana juyawa ya Wauko magani ya"

bata.

"Sannan ya ce, ""gashi nan ki ri™e."""

"Ta karSa ya ce, ""wannan jan maganin, a bashi a abinci ya ci, zai yi rashin lafiya mai yawa wacce zai jima a kwance, harkar kasuwancin nasa ma zai manta da ita. Wannan koran kuma a bashi a abin sha, ruwa ko kunu ko dai wani abun, a tabbatar da ya sha. Za ki ga aikin maganin ko ban faWa miki"

"ba."""

"Mama ta saka maganin a jaka, ta kalle sa ta ce, ""na gode Malam. A Waukaka su Zayyad, ya zama yadda suke manya a gidan, su ne dai manya gaba da baya, ya zama komai dasu za a dinga damawa ba Rehaan ba. Bana son ace Rehaan shine ™arsmi kuma shine a kan gaba, bana ™aunar hakan. So nake yadda na kafu a gidan, ΄a΄ana ma su kafu, yadda na gagari kowa, suma su gagari"

"kowa malam."""

"Malam ya yi dariya ya ce, ""tunda mu ka iya ya™i da tsafe-tsafe ΄an india a kan ki, wannan ™"

"arsmin abu ne a wajan mu."""

"Mama ta yi dariya ta ce, ""Na sha wahalar Nadira, na sha ba™ar wahalar matsafiyar nan. """

"""Yadda mu ka yi maganinta shima zamu yi maganinsa. Ko a wajan mijinta bata da wata power,"

"komai yana hannunki."""

"""Shiyasa nake jin daWin aiki dakai Malam, kana yi min komai yadda nake so."""

"""Sai maganar matar auren da aka ce na samo masa. Tunda an bani komai a hannuna, zan nemo"

"daidai da ra'ayina. Bana so ya samu mace ta gari, tabaWaWWiyar ΄ar iska nake so a samar masa, saboda hakan zai yi min amfani nan gaba."""

"Ya yi murmushi ya ce, ""ki Wauka an gama Hajiya, ki rubuta wannan kamar an yi an gama. Zan yi"

"miki duk abinda ki ke so."""

"Ta yi dariya ta ce, ""indai komai ya tabbata, umarar bana da kai za a yi."""

"Malam ya sake gyara zama ya ce, ""wallahi Hajiya babu abinda bazan yi miki ba, Allah ya ja"

"zamaninki ki, allah ya ja zamanin uwar gidan Alhaji AbdulAziz Yola, Allah ya ja zamanin uwar Zayyad da Sameer."""

"Ta yi dariyar farin ciki da jin daWin yadda yake zugata, ta ce, ""yadda Daada ta dawo hannuna, haka nake so komai ya dawo hannun Malam, bana so a samu matsala. Ni ce a gaba, ΄a΄ana su biye"

"min a baya, sai jikokina, sannan sauran su biyo baya."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""an gama Hajajju, duk abinda ki ka ce haka za a yi."" Mama ta mi™a masa kuWi"

tare da mi™ewa.

"Shima ya mi™e ya yi mata rakiya har mota, ta shiga ta tafi shi kuma ya koma."

*******

"Mamy tana zaune a falo ta yi shiru tana tunani. Riyya ta shigo ta zauna a kusa da ita ta ce,"

"""Mamy!."""

"A hankali ta kalle ta, ta ce, ""Riyya kin dawo?."""

"Ta Waga kai ta ce, ""na dawo. Mamy tunanin me ki ke yi haka?."""

"Mamy ta ce, ""Riyya Rehaan nake tunani, bana son dawowarsa ™asar nan, bana so ya saka ™afa a"

"gidan nan, domin baya taSa kwana lafiya."""

"Riyya ta ce, ""Mamy nima bana so, last time da ya zo har ya koma bai samu lafiya. Ni ban san"

"meyasa ake so ya dawo ba, wasu suna son ya dawo, wasu kuma basa so."""

"Mamy ta ce, ""tsanar da suka yi min itace ta shafi Rehaan, sannan ana ganin shine autan maza a"

"gidan nan, kuma shine mafi arzu™i da Waukaka a cikinsu. Wannan shine dalilinsu, basa sonsa basa"

"™aunarsa."""

"Riyya ta dafata ta ce, ""Mamy ki daina saka damuwar nan a ranki, babu abinda aka isa a aikata"

"wanda Allah bai rubuta ba. Dan ba sa sonsa ai mu muna sonsa."""

"Mamy ta ce, ""Abba ya fito ne?."""

"""A'a, yana falonsa a zaune."""

"Ta girgiza kai ta ce, ""ina son magana dashi."""

"Riyya ta ce, ""in yi masa waya?."""

"Ta girgiza kai ta ce, ""zan je in same sa."" Ta faWa tana mi™ewa ta saka hijjab zuwa bangaren Abba."

"A ciki ta samu Umma, suna haWa ido ta haWe rai, Mamy dai bata ce komai ba ta yi mata sannu."

Sama-sama suka gaisa.

"Mamy ta ce, ""Abba yana nan?."""

"""Eh yana ciki."""

"""ki yi min magana dashi don Allah."""

"Umma ta wani kalle ta ta ce, ""ki yi masa me?."

"Mamy ta kalle ta jin abinda ta ce, sai kuma Umman ta yi tsaki ta shiga ciki. Mamy ta nemi waje ta"

zauna tana jiran fitowarta.

"Ba jimawa sai gashi ya fito, Mamy ta mi™e tsaye tana kallonsa har ya ™araso wajan. Mamy ta ce,"

"""Barka da fitowa."""

"Ya Wan kalle ta sannan ya ce, ""barka."""

"Ya zauna a kan kujera ya ce, ""lafiya ki ke nemana da safiyar nan?."""

"Mamy ta zauna itama ta ce, ""Akan maganar dawowar Rehaan ne, yaushe aka saka ranar da zai"

"dawo?."""

"""Ban zaSi lokaci ba, amma zuwan nasa bazai wuce cikin satin nan ba."""

"""To shikenan."""

"""lafiya?:"""

"""tsakani da Allah zuciyata bata kwanta da zuwan Rehaan ba wallahi, haka kawai nake ji bana so"

"yazo ™asar nan."""

"Abba ya dafe kansa ya ce, ""Nadira ba mun gama maganar nan dake ba?."""

"Zata yi magana ya katse ta ya ce, ""meyasa ki ke yin abu kamar ke kaWai ki ka haifi Rehaan ne?"

"Meyasa ki ke yin abu kamar ke kaWai ki ke sonsa ne?."""

"Mamy ta girgiza kai ta ce, ""Ba haka bane, kawai dai """

"Ya dakatar da ita ya ce, ""yadda ki ke sonsa haka nake sonsa nima, yadda bakya so ya cutu nima"

"bana so ya cutu. Meyasa ki ke haka ne?. Ko kina ganin zan cutar dashi ne?."""

"Mamy jin ya fara faWa sai ta yi ajiyar zuciya ta ce, ""ba haka nake nufi ba, i'm sorry."""

"Abba ya ce, ""to ki dakatar da maganar nan don Allah, ki bari na yi abinda nake ganin ya dace, kin ji"

"ko?. Zan ™i yin abinda mahaifiyata ta ce in yi ne, ko zan zaSi abinda ki ke so na bar nata?."""

"Ta yi shiru bata ce komai ba, ganin haka sai ya sassauta murya ya ce, ""Nadira don Allah ki nutsu,"

"nima bazan so abinda zai cutar dashi ba. Tun ranar muka gama magana dake, ban yi tunanin za ki sake dawo min da batun ba."""

"Mamy ta ce, ""to babu komai. Allah ya dawo dashi lafiya."""

"Abba ya ce, ""Amin ya Allah. Abinda za ki ce kenan. Ki je zan shigo."""

Ta Waga kai alamun to. Ta faWa tana mi™ewa ta fita zuciyar ta gabaWaya babu daWi.

"Umma da ta ji komai, Mamy tana fita itama ta daga Sangaren ta shiga wajen Mama."

"Mama ta cire hajjibi ta ajjiye, Umma ta shigo ta zauna ta ce, ""Mama."""

"Ta kalle ta ta ce, ""ya aka yi?."""

"""Wallahi in ba mu sake shiri ba, Nadira zata hana Rehaan dawowa ™asar nan."""

"Mama ta ce, ""me ya faru?."""

"""yanzu ta samu Abba akan maganar, kamar zata yi kuka saboda damuwa. Ita bata so ya dawo,"

"waye waye."""

"""Me ya ce?."""

"""faWa ya yi mata, ni ban taSa ji ya yi mata tsawa kamar yanzu ba."""

"Mama ta ce, ""dakyau, ai duk bala'inta sai ya dawo ™asar nan wallahi, yadda ΄a΄anmu suke ™"

"asar nan, ake ci ake sha dasu, shima sai ya dawo. Ai ba fin kowa ya yi ba."""

"Umma ta ce, ""an tattara masa dukiya a ™asar waje, sai an yi magana ace dukiyarsa ce. Har nawa yake da zai tara wannan uban kuWin shi kaWai?. Ai in Abba ya mutu a yanzu akwai tashin hankali"

"wallahi."""

"Mama ta ce, ""ki bar ni dashi, ba dai zai dawo ba? Hmmm! zai ga abinda zanyi wallshi, a wannan"

"karon bazan ™yale sa ba wallahi."""

"Umma ta ce, ""gwara a san abinda za a yi kam, dan lamarin yana neman lalace mana. Bara in koma,"

"kar ya neme ni"" ta faWa tana tashi ta koma."

"Mama ta bita da harara ta ce, ""Shashasha, wai in Abba ya mutu akwai rigima."""

"""Mtsw! To kema ba sai abinda na Wauko na bawa ΄a΄anki ba? In aka ce yau babu Abba ai kakata ta yanke sa™a wallahi. Shiyasa kafin hakan nake so yarana su zama sune akan dukiyar ba Rehaan ba, yadda ko mutuwa ta zo sai abinda na ga dama zan bayar. Mu zuba mu gani"" ta faWa tana yin ™"

wafa zuciyar cike da mugun nufi....

Nana Haleema
'<Ψϋί

*RAGAYAR DUTSE.*

©ώ *Nana Haleema.*

Arewapen@nanahaleema11.

*Book 1*

*Page 007.*

"A hankali yake cin abincin kamar ba ya so, abincin ma cikin steeze ake cinsa, yana yi yana kaWa ™"

afa.

Rabin abincin ya ci ya tashi daga kan dining Win ya dawo cikin falo ya zauna yana shan ruwa.

"Tunda ya zauna ake kiransa a waya, wata wayar ya Wauka wata kuma ya share."

"A lokacin Jaafar ya sakko daga sama, ya kalle sa ya ce, ""baza ka je aiki bane?."""

"Ya Waga ido ya kalle sa ya ce, ""zan je, sai dare."""

"Jafar ya ce, ""to ka san kana da meeting ko? Kuma ka ba da time."""

"Ya Wan furzar da iska daga bakinsa ya ce, ""na sani Jazy, zan san abinda zan yi."""

"Jafar zai yi magana aka kira wayar Rehaan, ya duba ya ga video call ne kuma mahaifinsa ne."

"Sai da ya yi connenting da laptop Win gabansa sannan ya gyara zama, dan Abba ya fi so ya dinga"

"yi masa magana da fulfulde, a ganin Abba in ba ya yi zai manta da yaren ne."

"Rehaan ya Wauki wayar ya ce, ""jam bandu na Abba."" (Barka da safiya)."

"Abba ya ce, ""Jam Noi a woni? Noi kuuWe?"" (Ya ka ke, ya aiki?)."

"Rehaan ya ce, ""Jam Alhamdu lillah."""

"Abba ya yi gyaran murya ya ce, ""sai na ga ka rame, ina fatan kana lafiya?.."""

"ya kalli Jafar ya ce, ""Jafar ya yi rashin lafiya ne?."""

"Jafar ya cire glasses Win idonsa ya ce, ""bai yi ba, kawai kwana biyu baya son cin abinci, sai ya ce"

"komai ba ya yi masa daWi."""

"Abba ya ce, ""Rehaan yaushe zaka zo Nigeria?."""

"Sai da gaban Rehaan ya faWi, ya daure sannan ya ce, ""Abba!."""

"Abba ya katse sa ya ce, ""kar ka yi musu Rehaan, wannan lokacin zuwan ka ya zama dole, bazan"

"karSi uzuri ba."""

"Rehaan ya ce, ""Abba akwai aikin da zan je in yi a Jedda, a bari in na kammala sai in dawo nan."""

"Abba ya bisa da kallo ya ce, ""yaushe zaka je aikin?."""

"""Nan da four weeks."""

"""Ka dawo gida ka yi four weeks Win, in ya so daga Nigeria sai ka wuce."""

"Ya yi ajiyar zuciya ya ce, ""to Abba, zan shigo in sha Allah."""

"Abba ya ce, ""yaushe?."""

"""next week."""

"""A'a Rehaan, this week nake so ka shigo."""

"RehAn sauke ido ™asa bai kalli mahaifinsa ba ya ce, ""To Abba, zamu dawo."""

"Abba ya ce, ""Allah ya kaimu."""

"Rehaan ya amsa da amin, Abba ya ce, ""Kar ka damu, haka rayuwa ta ke, yau da gobe sai Allah."""

"Ya gyaWa kai ya ce, ""in sha Allah."" Basu jima suna magana ba suka yi sallama Abba ya kashe wayar."

"Rehaan ya daki kansa yana yamusha gashin kansa ya ce, ""bana son zuwa, bana son zuwa gida,"

"bana son Jazy!."""

"Jazy ya zauna a kusa dashi ya ce, ""Baka so ka ga Mamy, Banisha da Riyya?."""

"Ya kalli Jazy da idanunsa da suka fara canja launi ya ce, ""ina so, amma bana so in je can. In ina son"

"ganin su zan iya aikawa a Wauko min su, amma bana son zuwa nigeria."""

"Jay ya ce, ""ka yi ha™uri mu je."""

"""Ina ji a jikina kamar akwai abinda zai faru in na je Jazy, Ina ji kamar in na je bazan dawo da rai"

"ba."""

"""Ka cigaba da addu'a, babu abinda zai same ka in sha Allah."""

Ya sauke numfashi yana gyaWa kai cikin gamsuwa da maganar Jazy. Ya san addu'a ce kawai

"maganin damuwarsa. Jafaar ya mi™e ya ce, ""zan fita, Chef zai zo, sai ya yi maka abinda ka ke so."" Ya sake gyaWa kai bai ce komai ba Jazy ya fita."

"Jazy bai jima da fita ba ya ji ana danna doorbell, kamar bazai mi™e ba sai kuma ya tashi ya buWe ™"

ofar suka haWa ido da Alma a tsaye tana murmushi.

Kafin ya bata hanya ta shigo ta mayar da ™ofar ta rufe tana kallonsa tana murmushi. Fuskarsa

"babu murmushi, ya bita da kallo ganinta da jaket abinda bai cika gani ba. Alma ta yi pecking Winsa"

"a kumatu tana shafa fuskarsa, wacce take da kwantaccen gashi mai kyau da Waukar hankali."

"""Where is Jazy?"" Ta faWa tana kallon sa."

"Girgiza mata kai kawai alamun ba ya nan. Sai ta ji daWi a ranta, ta ri™e hamnunsa suka zauna ta"

"fuskance sa sosai ta ce, ""me yake damun ka?."""

Ya Wan kalle ta kafin ya janye ido ya yana girgiza kai alamun babu.

Alma ta mi™ewa tsaye ta cire jaket Win jikinta ta juyo da fuskarsa dan ya kalle ta.

"Ya kalle ta Win ya ganta sanye da riga ΄ar ™arama wacce bata wuce yace mata bra ba, sai ™"

armin wando wanda ko cinyarta bai gama rufewa ba. Ta zubo da gashinta tana sake juya gashin a gabansa.

"Ya Wauke kai daga kallon ta, ya rasa meyasa ™irar turawa bata burge sa, gasu dai farare tas, ko ina yana Waukar ido, amma sam baya so, bai sani ba ko dan a cikinsu ya tashi ne oho. Shi ko ΄an"

"nigeria farar fata bata cika Waukar hankalinsa, farar fata in dai ba Mamy ba, bata wani burgesa."

"Rehaan yi tsamani ba ya ji t ta zauna a kan cinyarsa, ya Wan yi ™aramin tsaki jin tana kai hannunt"

fuskarsa tana shafa gashin fuskarsa.

"A hankali ya ce, ""Alma please."""

"Ta matso da bakin ta kusa da fuskarsa ta ce, ""Please Ray, i want to you"" ta faWa tana niyar saka"

bakinta a cikin nasa.

"Da hanzari ya janye ta daga jikinsa ya mi™e ya ce, ""bana son haka, please ki je."""

"Ta bi sa da kallo tana sake matsowa kusa dashi, ya bita da kallo yana ji kamar kansa yana sarawa"

"ya ce, ""Alma ki ™yale ni."""

"Ta marairaice ta ce, ""Why?."""

"Ya rufe ido ya buWe ya ce, ""just go"" ya faWa yana hawa sama da sauri ya barta a tsaye a wajan."

"Alma ta bi shi kallo cike da takaici da ba™in ciki, ta kalli camera da ta saka a jikin laptop Winsa da take kan table, ta cire tana tsaki dan ba haka ta so ba, koda an Wauki video yadda ya kamata yanayinsa bai yi daidai da yadda take so ba. So take ta yi masa video a yanayin da kowa ya gani ya"

"san baya cikin hankalinsa, kowa ya san ya shiga wani Sangare da ya zama private a rayuwarsa."

"A lokacin aka yi mata waya, tana Wauka ta ce, ""We fail, next time"" ta faWa tana saka rigar da ta zo"

"da ita, ta Wauki abinda ta zo dashi ta fita."

Rehaan yana hawa sama ya faWa kan gado yana sauke numfashi cikin wani irin yanayi.

"Wani irin abu yake ji yana tafiya jikinsa, ya dafe kai cikin wani yanayin da bai san meye ba."

"Ya mi™e ya tsaya a gaban madubi yana kallon kansa, ya saka hannu ya hargitsa gashin kansa yana"

girgiza kai.

"A hankali ya dinga sauke numfashi, yana jan ajiyar zuciyar, ya diga maimaita Subahanallahi a"

"zuciyarsa, a hankali ya fara jin nutsuwa tana shiga jikinsa."

"Ya buWe ido a hankali yana kallon kansa, ya zubawa kansa ido yana ™arewa fuskarsa ido, yana"

kallon yadda Allah ya yi halita mai kyau a fuskarsa.

"Tabbas shi kansa ya san yana da kyau, indai kyau ake zance ya san yana sahun gaba a layin masu"

"kyau. Shi Win mai kyau ne, kyau wanda ake kira kyau, kyau na shiga gasar masu kyau."

"Bai san meyasa ba, yana jinsa kamar fanko, kamar akwai abinda ya rasa. Ya rasa me ya rasa haka?"

Meyasa yake jin kanasa a yanayin da yake ciki meyasa?.

*******

Tunda suka gama haWa record Win ranar suka rabu da Salim sai nufi hanyar gidan marayu da ta

"tashi a can. Sai sauri take yi sboda kar ta je an kulle gate, dan yamma ta kusa ta san ™arfe shida ake rufe shiga."

"Tun daga gate ta ka gaisawa da mutane cikin raha da wasa da dariya, kowa ya santa, tunda gidan"

"gidansu ne, a nan ta tashi, ta rayu, ta yi makaranta, da komai da komai."

"Kai tsaye office Win wacce suke kira da Mama ta nufa, ta Wan yi knocking kaWan aka bata damar"

shiga ta tura ta shiga da sallama.

"Mama ta amsa kafin ta ce, ""A'a Islaha, kece tafe?."""

"Ta Wan yi murmushi ta ce, ""ni ce. Ina yini?."""

"""Lafiya lau, ya aiki?."""

"""Alhamdu lillah."""

"""Yau ke ce kika shigo?."""

"""Eh ni ce, na kawo ziyara ne."""

"Mama ta ce, ""kin kyauta kam. Gashi ΄an uwan naki basa nan, sun Wan fita."""

"Da mamaki ta ce, ""sun fita kuma Mama, yanzu shida ta kuaa, daman ana kaiwa after six a waje?."""

"Mama ta ce, ""tunda na ce basa nan sai ki yarda ba nan, kin san suna sana'a. Šaya tana ™unshi,"

"Waya tana zuwa koyan Winki. Na san yanzu za ki gansu."""

"Islaha ta Wan girgiza kai ta ce, ""shikenan, in sun dawo ina gaishe su"" ta faWa tana Waukar handbag"

Winta ta fita.

"Mam ta bita da harara ta ce, ""sai da na faWa mata yarinyar nan tana da matsala amma ta ce ita ba haka ba. Mtsw! Ni na san matakin da zan Wauka a kanta, in ba haka ba akwai damuwa babba."

"Yarinyar nan ΄ar jarida ce, zata iya aikata komai, dan ba mutunci ta cika ba."""

"Islaha lokacin da ta fita cikin gidan ta shiga, ma'aikata gidan suna ta gaisawa kafin ta shiga asalin"

Wakin da take kwana.

"A guje ΄an mata biyu suka taho wajanta suna faWin, ""Adda Islaha."""

"Suka rungumeta itama ta rungume su tana murmushi ta ce, ""˜anena ya ku ke?."""

"Šaya daga ciki ta ce, ""Lafiya lau muke Adda, jiya na kira ki a waya baki Wauka ba."""

"""Ayya ban gani ba ma, da na gani a guje zan kira ki Hafsy."""

"Ta ce, ""ku zo mu je daga waje."""

"Suka fita suna hira, cikin nishaWi Hafsy ta ce, ""Adda tunda ki ka bar gidan nan ba ya yi mana daWi"

"wallahi."""

"Ta yi dariya ta ce, ""ni kaina da tunanin ku nake kwana nake tashi. Yanzu meye labari? Ina su"

"Humaira da Sauda? Ban gansu ba."""

"Hafsy ta ce, ""Hmm!"" Ta faWa tana kallon bayanta alamun bata so ta yi maganar a ji."

"Zainab ta ce, ""Adda lamarin Sauda da Humaira sai addu'a kawai, yanzu sai su kwana biyu basa"

"cikin gidan nan."""

"Islaha ta gyara tsayuwa ta ce, ""ina suke zuwa?."""

"""Waye ya san inda suke zuwa Adda?."""

"""Kuma Mama ta san suna fitar?."""

"Zainab ta ce, ""wani lokacin ma tare da ita suke fita da ita."""

"Ishala zata yi magana suna ji an ce, ""Ke Zainab, Hafsa! Ku koma ciki!. Bakwa ganin yamma ta yi"

"ne?."""

"Islaha ta kalli Mama sannan ta kalli su Zainab, ta ce, ""Ku koma, zamu yi waya."""

"Suka gyaWa kai suka koma. Mama ta ce, ""lokacin ziyara ya ™are, sai wani lokaci."" Islaha bata ce"

"komai ba, ta wuce ta fita daga wajen."

"Tana fita Mama ta koma office, ta Wauki waya tana zagaye tana jira a Wauka. Ana Wauka ta ce, ""Ni fa yarinyar nan Islaha tana bani tsoro, kun san yarinyar nan ΄ar jarida ce, abu kaWan zata yi ta"

"saka a shiga tashin hankali."""

"""Yanzu nan na tarar da ita ta tsare yara tana yi musu tambayoyi, kun san tana da yawo, kuma"

"jarida aikinta ne, dole mu samu mafita kafin wani abun ya zo ya faru."""

"Ta yi shiru alamun ana bata amsa sannan ta ce, ""ya dai kamata, ya kamata a san abinda za a yi, in"

"ba so ake lamari ya lalace ba."""

"Ta sake gyaWa kai ta ce, ""shikenan"" ta faWa tana kashe wayar tare da buWe window tana kallon"

islaha a harabar gidan.

"Ta girgiza kai ta ce, ""tauraruwa mai wutsiya, ganin ki ba alkhairi bane. Kin bar gidan ma baza ki"

"bari mu yi rawar gaban hantsi ba. Ina godewa Saheer da ya zama silar barin ta gidan nan, da nan ta cigaba da rayuwa ban san ya zamu yi ba"" ta faWa tana sakin labulen ta koma ta zauna tare da dafe kanta."

"Ko kaWan bata yarda da Islaha ba, ta san halin yarinyar, dan ba sanin yanzu ta yi mata ba. Tun tana depty head of orphanage ta san illar ta, yanzu gashi Head Win ta bata waje har yanzu ba a huta ba. Ta santa tun bata kai haka ba, zata iya aikata komai dan ganin ta binciko abinda yake faruwa, in"

kuma hakan ya faru za a tafka babban tashin hankli a faWin garin Yola.

Islaha bayan ta gama gaisawa da mutanen gidan ™ofar gate Win ta tsaya tana jiran abin

hawa dan lokacin magriba ta yi.

"Sai kuma ta tsaya tana tunanin ina zata je, dan gaskiya bata son komawa gidansu Saheer, gwara ta"

ta san inda zata nufa.

"Horn ta ji ana yi mata daga bayanta, ta juya ta ga bata san motar ba ta Wauke kai ta cigaba da"

kallon titi.

"Na cikin motar ya fito ya ™araso wajan, yana hararata ya ce, ""ke

Please Login or Register in order to submit comment