gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAGAYAR DUTSE Dawowa Mai Hatsari book 1 By Nana Haleema Chapter 25 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

™aunar auren."

"Hamma Zayyad ya ce, ""a ganina zata amimce, duk muna son haWin mu ma sosai, ai ™arfafa"

"zumunci ne."""

"Kowa ya amince da maganar Hamma har da Mamanta. Daada ta washe baki ta ce, ""Haka nake so"

"na ji, auren zumunci ai akwai daWi, musamman na uwa Waya uba Waya. Ba irin na Jafar da Juwairiyya ba, da suka Wauko ΄an uba."""

"Abba ya kalli Rehaan da bai ce komai akan maganar ba ya ce, ""Rehaan baka ce komai ba, meye"

"ra'ayin ka a kai?."""

"""A bata dama ta zaSi wanda zata aura. Aure ba abinda za a yiwa mutum dole bane, ita zata zauna"

"dashi ba wani ba. """

"ya Wan ja numfashi saboda ciwon cikinsa ya ce, ""In tana so sai ayi, in bata so a bata dama ta kawo wanda take so. Dan Jazy zai auri Riyya ba hakan yana nufin itama lallai sai ta auri wani daga family ba. Riyya tana son Jazy, ba Jazy ne kaWai yake sonta ba. Amma Janan bata son Khalil, shine yake"

"sonta. """

"""Don Allah kar a yi forcing Winta, a bata dama ta auri wanda take so kamar ΄an uwanta.""."""

"Abba daman ya san shi kaWai ne zai faWi gaskiya, shi kaWai ne bazai hangi kuWi ba. Dan ya san Maman ta kuWin Khalil take gani, dan yaron yana da abin hannu shima. Shi kuwa Rehaan babu kamar sa, kuWin Khalil bazai buWe masa ido ba, a wajen Rehan Khalil bai wuce ma'aikaci ba,"

shiyasa ya saka shi ya yi magana dan ya Wora a kan tasa.

"Abba ya ce, ""maganar Rehaan gaskiya ce Daada, kar a tilasta mata."""

"Kowa ya zubawa Daada ido ana jira a ji me zata ce, dan kowa ya san yadda take son Khalil, a cikin"

jikokin ta yana daga cikin wanda take mutuwar so.

"Daada ta ce, ""zan yi shawara akan hakan."""

"Kowa ya saki baki da hanci yana kallon Daada, yadda ta amsa maganar kai tsaye an san maganar"

da Rehaan ya yi ne ya dakatar da ita. Lokaci Waya hassada da ba™in cikin Rehaan ya sake ninkuwa a zuciyarsu.

"Mama ta kalli Daada tana ™wafa a ranta, sannan ta kalli Abba da Rehaan tana girgiza kai cikin"

mamaki da al'ajabi. A haka taron ya watse kowa ya kama gabansa.

"Mama da yaranta da suka koma apartment, suka saka ta a tsakiya kowa yana kawo mata"

suka akan maganar ta ko ina.

"Sameer ya ce, ""yanzu Mama Rehaan ya zama kamar shine babba a gidan nan? Hamma ya yi"

"magana, maimakon a karSi maganar sa sai aka karSi ta ™anin ™anin sa?. Hamma fa shine babba a gidan nan, Rehaan shine ™arami a cikinmu. Amma ace shine mai faWa a ji duk mun zama bola? Mu kenan bamu da amfani tunda ya fi mu kuWi?."""

"Ahmad ya ce, ""ku ne ba ku gane ba, amma wallahi duk abinda Rehaan yake so shi Abba da"

"Daada suke so. Akan auren nan da take son ma™ala masa ne kawaai suka taSa raba ra'ayi, amma komai akan ra'ayinsa take, duk abinda ya shinfiWa a gidan nan shi za a hau a zauna a kai. Mu an mayar damu koma baya, dan kawai ba a Englaand aka haife mu ba. Nan gaba gidan nan ma sai an"

"hana mu shigowa, balle kuma ΄a΄anmu."""

"Zubair da suke cewa Baba ya ce, ""Ban da rainin hankali, auren da mu ke so ayi shi zai lalata?."

"Khalil yana da madarar kuWi a hannunsa, yanzu yake tasowa, muna fatan nan gaba ya fi Rehaan. Aurensa da Janan babban alkhairi ne ga ΄an Wakin nan, zamu sake zama mu ne a sama, Janan itace take auren mai kuWin family. Amma dan rainin hankali ya buWe baki yana iyayin banza, yana kwaSawa mutane fulatancin da bai wani iya ba, wai baza a yi ba, ko a matsayinwa na wa oho."""

"Mama ta girgiza kai ta ce, ""duk ku barni dashi, wallahi sai na yi maganinsa a gidan nan, sai na"

"aikata masa abinda bai taSa zato ba."""

"Sameer ya ce, ""kullum haka ki ke faWa Mama, amma har yanzu kin kasa aikata komai."""

"""Ba kasawa nayi ba Samer, hakan taku ne, kuma babban shiri da babban tanadi nake yiwa hakan."

"Wallahi sai naga bayan Rehaan, sai na tabbatar da komai ya dawo hannuna."""

"""Bazai yu ku kasance manya a gidan nan ace shi zai dinga juya ku ba, karya yake yi. Ko babarsa ™"

"arya take yi balle shi da aka haifesa a kan idona. Ku bani lokaci kawai, kawai ku bani lokaci!"" Ta faW a cikin wani irin salo tana girgiza kai cike da abubuwa kala-kala a zuciyarta."

*****

"_Ki dakatar da wannan binciken da ki ke yi, in ba ki daina ba zaki yi danasani wacce baki taSa yi ba"

a rayuwar ki!._

"islaha ta sake karanta gajeren sa™on da aka aiko mata dashi, ta Wan yi jim tana tunanin wanne"

bincike take yi har da za a yi mata wannan barazanar?.

"Šan ™aramin tsaki ta yi, ta ajjiye wayar a gefe, wani sa™on ne ya kuma shigowa, ta kalla ta ga dai"

babu number kamar na farko.

"Ta sake dubawa ta ga an rubuta, _in ba ki daina shiga abinda bai shafe ki komai zai iya faruwa"

"dake, ki yi harkokin ki ban da shiga lamarin wasu._"

"""Mtsw! Ku ku ka sani kuma. Na san bazai wuce akan maganar Hafsa ba, kuma wallahi yanzu na"

"fara, babu wanda ya isa ya dakatar dani daga abinda na yi niya."""

"Kamar ma an tunzurata sai ta kira number Hafsa, ta gama ringing ba a Wauka ba, ta ajjiye ta yi"

shiru tana tunanin hanyar da zata bi ta gano abinda take zargi.

"Ta cigaba da aikinta ba tare da ta sake waiwayon abin ba, a haka har ta gama abinda take yi ta"

"koma asibiti wajansu Mama, bata bar asibitin ba sai bayan sallar i'sha sannan ta fito tana kallon hanya."

"Hanyar asibitin tana da haske sosai, kuma akwai cikakken security, hakan ya saka take tafiya ba"

"tare da wata fargaba ba, dan ta san babu abinda za a iya yi mana a area."

"Tana sauka daga kan titin da asibitin ta ga duhu ya mamaye hanyar, ita kanta sai da gabanta ya faW"

"i, ta juya baya ta ga babu abin hawa ko guda Waya."

"Babu zato ta ji mota kamar iska ta wuce ta gabanta a guje, Islaha ta kalli wajen tana dafe ™irji jin gabanta yana faWuwa. Cike da ruWani take tsaye jiran abin hawa, duk ta tsorata da tsayuwa a wajen, dan wajen babu haske. Ta sake ri™e handbag Winta da kyau, ta cigaba da tafiya a hankali"

cikin tsoro da fargaba.

"Ta juya baya ta ga wata mota tana tahowa a hankali kamar bata son tafiyar, ta Wan tsaya tana"

"kallon motar da take biyo bayana. Motar ce kaWai kan titin, bayan ita babu wata mota a wajan."

"Islaha ta yi salati a zuciyarta, ta cigaba da tafiya a hankali. Ta kuma juyawa ta ga dai motar bin"

"bayanta take yi, kamar na ciki ita yake kallo. Islaha ta tsorata sosai, ta nutsu ta cigaba da tafiya cikin sauri-sauri."

"Ta sake juyawa baya, taga da gaske dai motar bin bayanta take yi, ta tsaya cak tana jira motar ta ™"

araso ta wuce ko ta ga waye a ciki da yake bin bayanta.

"Motar tana zuwa gab da ita sai ta tsaya, ta zubawa motar ido kafin ta cigaba da tafiya cikin"

"tsananin tsoro da tashin hankali. A hankali ta juya ta ga dai an cigaba da biyo bayanta, ta tattare rigar jikinta saboda in abin gudu ya kama ta ji daWin guduwa, ta cigaba da sauri kamar zata tashi sama."

"""Islaha!."""

"Ta yi firgigit kamar wacce aka watsawa ruwan sanyi tana bacci, gabanta ya faWi, bata san lokacin ta furta, ""wayyo Allah na, na shiga uku! Innallahi wa'inna ilaihir raji'un!"" ta faWa a gigice jin yadda"

aka kira ta ba tare da ta shirya ba.

"Saleem ta gani a cikin mota a zaune, ta kalle sa a firgice tana sauke nunfashi ciki tsoro."

"Ya bita da kallo ganinta a firgice ya ce, ""shigo mu tafi."" Da sauri ta zagaya ta shiga motar, ya ja"

suka cigaba da tafiya.

"Ya bita da kallo ganin kamar bata cikin hayyacinta, sai juyawa take tana kallon bayanta tana sauke"

dogon numfashi.

"Sai da sauka Wan yi tafiya kaWan sai ya tsaya, ya fita daga motar ya siyo mara ruwa mara sanyi"

"sosai ya dawo ya mi™a mata. Bata ™i ba ta saka hannu ta karSa, ta Wan sha kaWan sannan ta koma ta jingina da kujerar tana sauke numfashi."

"Saleem ya ce, ""ya za ki fito daga asibitin nan ke kaWai? Kin san titin asibitin ne zuwa ™arshensa kawai yake da kyau, da kin baro wajan hanyar nan sai a hankali"" ya faWa yana jan motar suka"

cigaba da tafiya.

"Ta juya ta kalli bayanta ta ga babu wannan motar ta ce, ""Saleem wata mota ce take bin bayana,"

"shine abin ya bani tsoro sosai."""

"""Mota take bin ki? Dan me?."""

"""Ban sani ba, shine abinda ya bani tsoro."""

"""Wata doguwar van ba™a?."""

"""Ita fa."""

"""Anya kuwa ke suke bi? Sai na ga kamar motar ma'aikata fa."""

"""wallahi ni suke bi, dana tsaya suma zasu tsaya cak. In na cigaba da tafiya su biyo ni."""

"""Ki kwantar da hankalinki, babu komai in sha Allah. Kin tsorata da hanyar ne kawai, kuma kar ki"

"sake biyowa ke kaWai."""

"Ta sauke nunfashi bata ce komai ba, amma tabbas bin bayanta ake yi."

"A haka suka ™arasa gida, sai da ya ga ta shiga sannan ya ™arasa wajan masoyiyarsa zai bata sa™o."

Islaha haka ta kwana cikin rashin nutsuwa mai kyau.

"Ranar thursday bayan ta dawo daga wajaan aiki tana niyar tafiya asibiti Sadik ya kira ta a waya,"

"tana Wauka ya ce, ""Islaha har yanzu ba a siyi filin nan ba wallahi, abubuwa sai caSewa suke yi, ga aikin yana tahowa."""

"Ta mi™e tsaye ta ce, ""yanzu meye abin yi?."""

"""Ina tunanin zamu ba da jinginar filin a bamu kuWin, daga baya sai a siyar dashi ko?."""

"""Hakan ya yi sosai, nima yanzu zan shigo asibitin."""

"Daga haka ta kashe wayar, ta canja wanka ta saka doguwar riga ta fito daga gidan ta tafi asibitin."

"A can ta samu Sadik suka tattauna akan batun kuWin aikin, har bayan sallar magrib tana can, da Adda Sa'ida zasu tafi, amma kafin su rabu da Sadik tazo ta tarar Adda bata nan, haka ta fito ita kaW"

ai tana tunanin abinda ya faru da ita kwanaki.

"Yau garin bai yi duhu sosai ba, da sauri take tafiya tana kallon bayanta ganin babu kowa sai mai"

napep guda Waya da yake tahowa.

"Ta dakata da tafiya ta tsayar dashi ya tsaya, ta faWa masa unguwar da zai kai ta ya ce, ""shiga kawai"

"hajiya."""

"Har zata shiga sai ta kalle sa, ta ga ya Soye fuska da facemask sannan ga ba™in glasses, babu ta inda ake ganin fuskarsa. Tsoro sai ya kamata, ta ji bata yarda dashi ba, ta ja baya ta ce, ""jeka kawai,"

"na fasa."""

"Ys kalle ta ya ce, ""kin san zaki fasa ki ka tsayar dani?."""

"""Na hutar da kai tafiyar, ka je kawai."""

"""ai ba a tsayar dani a fasa shiga. Ki shiga kawai."""

"""Bazan shiga ba"" ta faWa zata tana wucewa daga wajen."

"Sai ta ga ya fito daga napep Win ya biyo bayanta da sassarafa. Islaha ta ™walalo ido, ta kwasa a"

guje mai napep ya rufa mata baya.

"Tuni ya cimmata tare da dam™o hannaunta, yana ™o™arin watsa mata abinda yake ™o™arin buW"

ewa a ™aramar.

"Islaha so take ta ™wace amma ta kasa, sai kokawa take yi amma ta kasa, da hannu Waya ya ri™e"

"ta, hannu Waya ya ri™e wata kwalba yana so ya buWe tana bashi wahalar buWewa."

"""Na shiga uku, a taimaka min, a taimaka min!"""

"Ta faWa da ™arfi, tana so ta ™wace hannunta amma ta kasa, ya yi mata ri™on da ba a taSa yi mata"

ba.

"Islaha ta shiga tashin hankalin da bata taSa shiga, a lokacin ya yi nasara buWe kwalbar, ya gyara"

zamanta a hannunsa yana ™o™arin kwarara mata a fuska.

"Kamar wal™iya ba™ar van Win jiya ta zo wajen a guje, aka finciki hannun Islaha aka ja ta motar da ™arfin gaske. Kamar ™iftawar ido haka ta tsinci kanta a motar, suka rufe ™ofar aka cigaba da"

sharara gudu akan titin.

End of Book 1

_Waye ya sace islaha? Ya za a yi da aikin Baffa? Ina labarin Saheer? Ina labarin Rehaan? Me zai

"yiwa Islaha?. Ya batun aurensu? Zai yu ko aa?. Saheer fa? Ya batun aurensu? Zai yu ko bazai yu ba?. Waye yake ™o™arin kashe Rehaan? Waye yaka bayyana binciken Islaha? Waye mai gaskiya? Waye zai yi nasara?. Za wai mallaki ISLAHA, REHAAN ne ko SAHEER?._"

"_Ku saka a ran ku bamu fara littafin RAGAYAR DUTSE ba, ku saka a ran ku yanzu ma muka fara."

"Book one gabatarwa da shimfiWa kawai muka yi, tafiyar tana cikin book 2&3, sai kun shirya, dan tafiya ce mai nisan zango. Akwai akasin lissafi, akasin tunani, akasin zato, akasin nazari, duk a cikin RAGAYAR DUTSE BOOK 2 & 3. Ku zo mu hau jirgin, mu lula duniyar RAGAYAR DUTSE. Ku gigita ni"

da shiga paid group _

"_Zaku mallaki naku akan naira 1k kacal akan telegram, ku tuntuSi wannan lambar domin biyan"

kuWin. 09030398006 ko 0701 809 8175._

"*Zamu fara posting Book 2 ranar Monday in sha Allah, akan manhajar Telegram.*"

Nana Haleema
'<Ψϋί


Downloaded From https://arewanovels.com


Please Login or Register in order to submit comment