gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAGAYAR DUTSE Dawowa Mai Hatsari book 1 By Nana Haleema Chapter 4 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na bawa Rehaan ba. Ke ko ita kanta ™anwar tawa, wallahi bazan iya bari ta auri Rehaan ba. Komai a Wakina nake so ya tare, bana so Waukaka ta tsallake ni ta je wani waje."""

"Zuhra zata yi magana ta dakatar da ita, cikin fusata ta ce, ""ya isa malama, ki bar batun nan bazan"

"amince ba. Babu ta yadda za a yi in bari ta auri mijin da yafi na ki kuWi. Rehaan ga kyau, ga kuWi, ga iko, ga farin jini, ga Waukaka. Ba iya nigeria ba, a kaf ™asashen ™etare babu inda Rehaan bashi da alfarma. A hakan zan bari wata wacce ta raSe ni ta same sa?. Da dai ace akwai aure a tskaninku ne, ko ba ya so sai ya auri Janan wallahi."""

"Zuhra ta ce, ""Kamata ya yi mu zauna ayi magana sosai akan hakan, yanzu dare yana yi."""

"Sameer ya ce, ""Mama ya kamata a san abinda za ayi in, in ba haka ba wallahi muna gani komai zai"

"fi ™arfin mu."""

"Zayyad ya girgiza kai ya ce, ""To ku ™yale Rehaan Win mana, shekara nawa ana wahala a kansa an"

"kasa samun nasara?."""

"Mama ta kalle sa cike da harara, ta ce, ""babban banza, a haka zaka ™are ai. Ina kishinku amma kai"

"kana zuba min ™asa a ido, dama Sameer ko Zubair ne babba ba kai ba."""

"Ya yi murmushi, bai ce komai ba ya fita."

"Mama ta dafe kai ta ce, ""innalilahi! Na auri mutum tun yana saurayi, amma saboda tsafi irin na ΄"

"an india tana shigowa rayuwarmu ta tarwatsa komai. Ni da nake da ku mu ne manya a gidan nan, amma itace take ri™e da gidan."""

"Zuhra ta ce, ""gabaWaya sunan Abba ya Sata, sunansa ake ambato. Ko ni, in aka ganni sai ace ga ™"

"anwar Rehaan Yola."""

"Mama ta dafe kai, ta girgiza kai ta ce, ""mu zuba mu gani. Sai na dakusar da wannan Waukakar"

"wallahi. Ina zuwa"" ta faWa tana shiga Waki da gaggawa."

*****

"""Rehaan yana gab da shigowa nigeria, kana da labari?."""

"Wanda yake zaune a gefensa, ya girgiza kai ya ce, ""bani da labari, sai yanzu."""

"Shima ya zauna yana girgiza kai sannan ya ce, ""na sanar da kai yanzu, duk yadda za a yi a"

"wannan lokacin ayi. Kar a saSa saiti, a tabbatar da Rehaan ya daina numfashi. Barinsa duniya kaW ai, shine zai zama silar Wagawarmu. Matu™ar yana da rai, babu inda zamu iya zuwa."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""za a san abinda za a yi ranka ya daWe, a ko yaushe umarninka kawai nake jira."

"Zan san duk abinda za a yi da zarar ya shigo nigeria."""

"Ya Wora ™afa kan Waya sannan ya ce, ""a wannan karon bana son matsala, wannan karon bana"

"son kuskure. Ina so na ji labarin Rehaan ya mutu, ina so na ji labarin babu shi a duniya. ."""

"""An gama ranka ya daWe."""

"""Aje a yi abinda ya kamata, duk abinda ake bu™ata a yi min magana."""

"""An gama"" ya faWa tana fita. Ya yi ™wafa yana girgiza kai zuciyarsa cike da mugun nufi."

"*LONDON, UNITED KINGDOM.*"

"A hankali yake kaWa ™afarsa idonsa a rufe, sanye yake da ™aramar riga mai gajeren hannu,"

hannunsa ri™e da glass cup yana juya ragowar drink Win da yake ciki.

"Fari ne tass, kallon farko zaka yi masa ka san haskensa ba na ΄an Nigeria ba ne, kana kallonsa ka"

san haske ne ba gama gari irin wanda mu ka saba gani ba.

"Yana da dogon ba™in gashi, wanda ya sakko har shoulders Winsa, gashin Saki ne sosai, mai tsaho da cika. Yadda ya rufe ido, eyelashes Winsa sun kwanta akan fuskarsa, ga dogon hanci mai tsaho da kyau. Yana da cikakken sajen da ya zagaye fuskarsa, bai yi yawa ba, kuma ba a cire sa ba, ya sha"

"gyara, kai daga gani ba sai ance yana shan kuWi ba."

"Yana da smallest lips, masu kyau da Waukar hankali. Ta ko ina ya haWu, kana ganinsa ka san kyau ne ya haWu da kyau. Fulani ne ya haWu da india, shiyasa aka samar result mai Waukar hankali. In"

"ka kalle sa sai ka kuma kallo, domin kyaunsa ba na kallo Waya ka ha™ura bane."

"REHAAN ABDULAZIZ YOLA kenan, wanda ake yiwa la™abi da RAY, saurayi matashi Wan shekara"

"talatin da uku zuwa da huWu. Cikkaken likita a Sangaren tiyata, kuma shararraen Wan kasuwa, wanda sunansa ya ratsa duniya gabaWaya."

"Ray ya Waukaka, Allah ya saka masa albarka a cikin kasuwancinsa, sunansa shine ta™amar ΄an garin Yola. Yadda ΄an Kano suke alfahari da sunan Wangote, haka ΄an Adamawa suke alfahari"

da sunan Rehaan. Yana daga cikin matasa mafiya shahara a Nigeria.

"""Ray kana ji na?."""

Kyakykyawan saurayi mai irin shekarunsa ya faWa yana zama a kusa dashi.

"Jafaar Ahmad Zubair Yola kenan, wanda Rehaan yake yiwa la™abi da Jazy ko ya ce Jay. Cousin W"

"insa, kuma amininsa. Tare suka tashi, tare suke yin komai. Tsiran shekara Waya ne a tsakaninsu, Rehaan ya girme sa da shekara Waya."

"Kowa akwai abinda ya saka a gaba, Jazy ba a ™ar™ashin Ray yake aiki ba, shima da kansa ya dogara, aiki ne yake kawo shi uk kamar Rehaan Win. Mamy ta Wauki amanar Ray kacokan ta tam™"

"awa Jazy, dan ko yaushe suna tare."

"Sai a lokacin ya buWe kyawawan idanunsa masu kama da madara, ga girma ga haske, gasu"

"zagayayyu, sun fito waje kamar ka saka hannu ka cire."

"Ray ya sauke ™afa ™asa, ya kalli Jafar ya Wan girgiza kai."

"Jazy ya ce, ""mun yi waya da Mamy Wazu da baka nan, ta ce min akwai batun zuwan ka Nigeria a"

"kwanakin nan."""

"Rehaan ya Wan yi tsaki, cikin harshen fulfulde, wanda suka fi amfani dashi in suna tare ya ce,"

"""Makircin tsohuwar nan ne ko?."""

"""Kaima ka san itace zata ce ka dawo, in ba ita ba babu mai takura maka."""

"""Ni ban san me na tare mata ba. Ko in na koma can Win me zan yi mata oho"" ya faWa yana Waukar"

band a gefensa ya Waure gashin kansa a tsakiya.

"Hakan da ya yi ya sake ™ara masa kyau, ya fito da asalin zatin da Allah ya yiwa fuskarsa."

"Jazy ya kalle sa ya ce, ""kamar kuwa kasan Mamy ta ce min na saka ka Wan rage gashin nan, bata"

"son abinda zai jawo mata magana."""

"Ya yi masa kallon ™asan ido, sannan ya ce, ""Bazan cire ba wallahi, sai dai duk abinda Daadan zaata yi ta yi. Na gaji da wannan abubuwan na su, komai sai abinda suke so za a yi, dan sun ga ina"

"™yalewa sai a dinga za™ewa? Ya isa."""

"Jazy ya yi dariya ya ce, ""To Rehaan ba ni na ce ka koma ba fa, wannan faWan na me ye?."""

"Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya ce, ""bana son zaman Nigeria Jazy. Bana son zama a gidanmu,"

"bana son abinda zai haWa ni da gidan nan. Ba dan Mamy da Abba dasu Riyya ba, babu abinda zai mayar dani Nigeria. GabaWaya gidan nan ba ™aunata suke yi ba, Janan ce kaWai take kula da ni a gidan, sai kuma Hamma, amma kowa burinsa. "" Sai ya dafe kai ya yi shiru bai ce komai ba."

"Jazy ya ce, ""sorry Ray, ko wacce nasara haka take zuwa da ™alubale."""

"Ya kalle sa ya ce, ""Ni meyasa jarabawar ta zo a kan gidanmu? Jazy babu wanda bana so a gidan"

"nan, ina ™aunar ΄an uwana ka fi kowa sani, amma su ba haka ne a wajansu ba. Riyya da Kiddo sune ™annena, sai Janan. Bana jin daWin hakan da suke yi min."""

"Jazy ya ce, ""na sani Ray, kai mutum ne mai son ΄an uwa da son kyautata musu, jarabawarka ce a"

"haka shiyasa hakan ya faru."""

"Ya sauke numfashi tare da Wora hannayensa duka biyun a gashin kansa, ya cire band Win da ya"

"saka, ya yamutsa gashin yana barbaza s ko ina."

"Ya Wan cize baki ya ce, ""Zan shiga Jedda Jazy."""

"Jazy ya ce, ""yaushe kenan?."""

"""Soon."""

"""Amma akwai batun zuwa Nigeria fa."""

"""Aiki ne dani a can Jazy, zan tsalleke aikin na tafi nigeria ne?."""

"""Amma tunda har aka fara batun nan gwara mu je Win, in ya so daga can sai ka wuce."" Ya Wan"

girgiza kai bai ce komai ba.

"Jazy ya yi murmushi ya ce, ""Mamy ta ce min baka da budurwa har yanzu?."""

"Kyakykyawan murmushi ya yi, wanda ya bayyanar da fararen ha™oransa farare masu kyaun kallo."

"Ya shafa fuskarsa ya ce, ""Mamina kenan. Me ka ce mata?."""

"""Na ce mata babu kowa har yanzu."""

"""Ka yi mata ™arya kenan, bayan ka san akwai Alma ko?."""

"Jazy ya haWe rai ya ce, ""Ray meyasa lokaci Waya ka ke son sako Alma a cikin rayuwarka? Ka san"

"aurenka da ita ba abu ne wanda zai yu ba."""

"Ya Wora ™afa kan Waya yana Wan taSe baki ya ce, ""akwai haramci a aurena da ita ne? Infact Alma musulma ce ba arniya ba, ko arniya ce addini ya bani damar auren ta balle musulma ce. So Alma"

"she's my girlfriend, zan faWawa Mami, next month zamu yi court marrige a nan."""

"Jazy ya ce, ""Rehaan! Me ka ke faWa haka? Kana so ka jawowa Mamy wani abun ne?."""

"Ya mi™e tsaye yana Wan stretching kaWan ya ce, ""Mamy babu ruwanta dan na auri Alma, haka Abba ma babu ruwansa, dan shima ya auri Mamy, bazai damu dan zan auri ΄ar Uk ba. Sauran"

"mutanen gida duk abinda zasu ce su ce, i'm ready to face any challange for that."""

"Jazy zai yi magana aka danna door bell, Ray ya ™arasa ya buWe yana kallon wacce ta shigo."

"Siririyar baturiya ce, mai farin gashi mai tsaho. Sanye take cikin dogon jeans da riga wacce ta rufe"

"iya ™irjinta kawai, gabaWaya cikinta a waje yake. GabaWaya flat tummy Winta a bayyane yake, ga navel Winta a bayyane, an yi mata ado da stone mai kyau a cikinta."

"Rehaan ya Wan kalle ta, kafin ya yi magana ta yi hugging Winsa harda Wafewa jikinsa. Bai yi"

"denying ba, ya yi hugging Winta back hannunsa zagaye da cikinta wanda ya kasance a bayyane."

"Šagowa ta yi daga jikinsa, ta yi pecking goshinsa tare da shafa gashinsa ta ce, ""I missed you Ray."""

"""I'm just talking about you sai ga ki kin zo. Ina ki ka je."""

"""I'm here to invite you to go on vacation with me. Can you come?."""

"Ya kalli Jazy da yake kallonsa, sannan ya kalle ta ya ce, ""Alma ina da aiki yanzu, amma na yi al™"

"awari next time."""

"Ta yi murmushi tana shafa gajensa ta ce, ""take your time Rehaan, i'm leaving."""

"""Okay, byee."""

"Ta sake hugging Winsa ta ce, ""byee"" ta faWa tana fita, ya raka ta har bakin ™ofa ta tafi, sannan ya"

juyo yana kallon Jazy da yake aiko masa da harara.

"""Amma ka san hakan ba yi daidai da addininka da al'adarka ba ko? Kai bafulani ne, wannan kuma"

"ba al'adarmu ba ce."""

"Ray ya kalle sa ya ce, ""Nan ba a Yola nake ba, a Uk nake. Ina so ka tuna Alma ™awata ce tun ina"

"school, tare muka fara karatu tun daga farko har ™arshe. Alma ta taimake ni, musamman akan karatuna. And hug and kiss normal abu ne."""

"Jazy ya ce, ""kana son jawowa Mamy wani abun kenan?."""

"Ya Wan rausayar da kai ya ce, ""na faWa maka auren Alma zan yi."""

"""yaushe ka yanke wannan hukuncin? Ko dai..."" sai ya yi shiru bai ™arasa ba."

"Rehaan ya ce, ""ko dai me?."""

"""Nothing."""

"""Jazy ya zama dole na auri Alma, a jikina nake ji aurenta ya zamar min dole."""

"Da mamaki ya ce, ""meyasa ka ce haka?."""

"""I dont know, amma a jikina nake ji ya zama dole na aureta Jazy. Ban san me yake damuna ba, ban"

"san me nake ji ba. Bana son Alma a matsayin wacce zan aura, amma ina ji a jikina ya zama dole na aure ta Jazy."""

"Jafar ya bi sa da kallon mamaki ya ce, ""ni ka Waure min kai."""

"Ray ya ce, ""nima kaina a Waure yake Jazy, nima ban san me zan yi ba."""

"Ya faWa yana zama a akan kujera yana rufe ido, dan shi kansa bazai ce ga abinds yake damunsa ba."

"Jafaar ya yi ajiyar zuciya ya ce, ""Rehaan ka cigaba da addu'a kawai."" Ya Waga masa kai alamun to,"

ya dafe kai bai ce komai ba.

"Jafar ya buWe window, sai ya taSe baki ya ce, ""ban san meyasa hausawa mu suka zubar da"

"mutuncinsu ba. Ka ga wannan apartment Win? Wani bature ne a ciki, ake kawo masa ΄an nigeria"

"kala-kala, yana biyansu ya yi abinda yake so da ita. Kalli dai wannan yarinyar, kana ganinta ka san"

"yarinya ce, sannan kana ganinta ka san yar ™asar mu ce."""

"Ray ya mi™e ya ™araso ya kalli Window Win ya kalli yarinyar ya kalli Jay ya ce, ""hmmm! Shiyasa"

"ma gwara ka auri turawa ka huta, ΄an ™asar mu sun lalace da zuwa outside countries suna zubar da mutuncinsu."""

"Jazy ya kalle sa ya ce, ""Amma kai ka ce min baka sha'awar auren farar mace, ka ce black beauty ka"

"ke ra'ayin aure. Me ya kawo Alma?."""

"Ya sake kallom window ya, ya jingina da bango yana Wan murmushi kaWan ya ce, ""nima ban sani"

"ba, but brown skin is my favorite!."""

"Jazy ya ce, ""kamar wacce kenan?."""

"Ya sake kallon window yana kallon wacce ya nuna masa, ya kalli Jazy yana taSe baki bai"

ce komai ba ya Wauki wayarsa ya hau sama.

"Jazy ya bisa da kallo yana sauke ajiyar zuciya, a kaf duniya shi kaWai ya san waye Rehaan, ko"

Mamy bata san halayensa kamar yadda ya sani ba.

"Shi kaWai ya san abubuwan da suke baibaiye da Rehaan, ya tabbatar shigowar Alma rayuwarsa kawai nufi mara kyau. Haka kawai yake ji a ransa kamar zuwanta rayuwar Rehaan plan ne, gabaW aya ba ya so ya dinga ganinta tana zuwa inda yake. Tana son cewa zata taSa shi, duk da hug and kiss ba komai bane a wajenta, shima tunda a Uk yake rayuwa kusan ya saba da hakan. Amma na"

"Alma ya yi yawa, akwai abinda take nufi da Rehaan."

Waye ya turo ta? Shine abinda bai sani ba.

******

Alma tana fita daga apartment Win wata luxury car da take ajjiye shiga. Ta kalli wanda yake ciki a

"zaune, ta mi™a masa abin hannunta ta ce, ""here is his hair."""

"Ya karSa ya ce, ""his signing?."""

"""We are coming there."""

"""Dont forget, we need everything from Ray."""

"""I know."""

"Ya sake kallon ta ya ce, ""can you do me a favor? If you do it, i will give you fiffty million naira."""

"Alma ta yi murmushi ta ce, ""i can."""

"Ya sauke numfashi ya ce, ""ki yi ™o™arin jan hankalinsa, ku gama sabawa, sannan zan faWa miki."""

"Ta yi murmushi ta ce, ""Okay Sir."""

"Ya yi murmushi, suka gaisa ta sauka daga motar shi kuma ya ja motar ya tafi."

Nna Haleema
'<Ψϋί

*RAGAYAR DUTSE.*

©ώ *Nana Haleema.*

https://whatsapp.com/channel/0029VbC1pVN42DcoY0dAzq46

*Book 1*

*Page 004.*

"Da mamaki Baba yake kallon ta jin abinda take faWa, ya yi shiru ya zuba mata ido har ta gama"

bayaninta yana girgiza kai.

"Ya bita da kallo ya ce, ""Maimuna kin san abinda ki ke faWa kuwa?."""

"Umma ta kalle sa ta ce, ""na sani mana."""

"Baba ya ce, ""kuma kina cikin hankalinki?."""

"Itama da mamaki ta ce, ""in bana ciki ai bazan faWa ba. """

"Baba ya ce, ""na fi tunanin bakya hankalin naki, dan mai hankali bazai faWi abinda ki ka faWa ba."

"Cewa ki ke yi za ki tura Safeera ™asar waje aiki, a gidajen fararen fata fa."""

"Umma ta ce, ""eh haka na ce. KuWi ake samu, kai ka san ba halin aurar da ita muke dashi ba. In ta"

"je ta yi aikin koda na shekara Waya ne, abinda ta samu ba sai a aurar da ita dashi ba?."""

"Baba ya girgiza kai cikin mamaki, dan shi gani yake kamar bata cikin nutsuwarta, ya ce, ""Safeera za"

"a tura aikatau wata ™asar? Ni tantama nake yi; anya kina cikin hankalinki?."""

"""Haba don Allah, ina hankalina mana, mahaukaciya ce ni?. Duk wata akwai gidan da ake biyan"

"miliyan Waya a kuWin nigeria, ko da dubu Wari biyar za a dinga bata, a wata sha biyu nawa mu ke"

"dashi?. In ta je ta yi na shekara Waya ba sai ta dawo ba?. Wannan banzar tashar da suke aiki ita da Islaha uwar me suke samu? Tashar tasu har yanzu bata wani Waukaka ba, albashin bai wuce dubu hamsin ba. Kai kana gida ba aikin kirki ka ke yi ba, nima Wan buge-bugen da nake yi ba samu ake yi ba. Ga yara, ga Safeera budurwa wacce aka yiwa baiko, shi kansa wanda zata aura Win ba wani"

"abin hannu ne dashi ba. Ya ka ke so na yi?."""

"Baba ya girgiza kai ya ce, ""kuma kawai sai na sallama ΄ata ta tafi wata ™asar aiki, saboda a kaina"

"aka ™are talauci ko?."""

"Ta yi shiru bata ce komai ba, Baba ya gyara zama ya ce, ""Ai wallahi ko bara nake yi akan titi, bazan"

"amince Safeera ta yi aikatau a garin nan ba, balle har sai an bar ™asar nan. Ita woman leader Win da ta zugo ki, ki faWa mata ita ta tura ΄a΄anta mana, sai ke za ki tura naki dan baki da hankali?."""

"Umma ta Waure fuska ta ce, ""ina fa da hankali Malam, ka daina cemi bani da hankali. Kuma in"

"Safeera ta je aikin nan ai cigaban mu ne."""

"""Cigabanki dai, amma ni ban dani. Kuma baza ta je ba, wallahi Allah Safeera baza ta je aiki wata ™"

"asar ba, matu™ar ina da rai ina numfashi. Ke ko na mutu ban yafe ba in ki ka turata. Tunda na lura abin naki ya tashi daga na masu hankali, ya tsallaka ya koma na mahaukata."""

"""Ka ji ai, matsalar talaka kenan wallahi. Baka dashi ka ce baza ka bi hanyar samu ba."""

"Baba ya girgiz kai bai ce komai ba, dan ba ya so ya biye mata saboda yara, ba ya son yin abinda zai"

bar musu suna tunawa dashi.

"A lokacin Safeera ta shiga da sallama cikin hijjab. Baba ya amsa yana kallonta, ta dur™usa ta ce,"

"""Baba zan mi™awa Islaha wainar fulawa na dawo."""

"Baba ya kalli agogo ya ce, ""™arfe tara ta yi Safeera, in kin je ki dawo, ban da zaman hira."""

"Ta yi murmushi ta ce, ""To Baba"" ta faWa tana mi™e ta fita."

"Umma ta ja tsaki ta ce, ""yarinya budurwa kamar wannan ace baza a amfana da ita ba. Woman"

"leader ΄a΄anta ne suke kawo mata kuWi kullum, kuma ba neman maza suke yi ba, da dabara irin ta mata suke samu su kawo. Amma ni aiki na ce zata yi ka ce baza ta yi ba. Ni sai na wanke ™afata"

"na tafi, ai baza a hana ni ba!. In ka hana ΄arka, ni ai ba haifata ka yi ba!"" Ta faWa tana mi™ewa."

"Baba ya ce, ""Allah ya kai ki lafiya, ΄aata dai baza ta je ba wallahi."""

Mama ta fita suka haWu da Safeera tana kwashe kayan wankin da suka zube ™asa saboda iskar

sanyi.

"Umma ta kalle ta ta ce, ""Ke kina son zuwa ™asar waje aiki?."""

"Da mamaki ta ce, ""Umma wanne aiki kenan?."""

"""Aikin Saudia, na gidan larabawa ko turawa.Kina so?."""

"Safeera mamaki ya hana ta magana, ta dinga bin Umma da kallo ganin yadda ta canja kamar ba"

ita ba.

"Umma ganin ta tafi tunani sai ta dafata, ta ce, ""a wata ana samun albashi kusan miliyan Waya, to in ki ka je ki ka tara kuWin ba sai a zo a ajiiye, kin ga in bikinki ya zo an huta da babu wannan babu wancan. Kin san ba ™arfi ne da ni ba, babanki ma haka. In ki ka je ki ka samo kuWin, sai a rufawa juna asiri. Shi kansa Saleem Win naki ba kuWi ne dashi ba, kin ga sai a taimaka masa da wani abun"

"in an samu, ko ya ki ka gani?."""

"Safeera a sanyaye ta ce, ""Umma wai da gaske ki ke?."""

"""Da gaske nake mana. KuWi ake samu, musamman ke da ki ke jin turanci, za ki iya zama a ko ina."

"Ga ki fara, kyakykyawa."""

"""Umma ni bani da ra'ayin zuwa aikatau wata ™asar gaskiya."""

"Umma ta yi murmuahi ta ce, ""jeki ki kai mata ki dawo mu tattauna, bazan bar wannan alkhairi ya"

"wuce mu ba. In ki ka yi katari ki ka samu gidan aiki a saudia riba biyu, ga ki a garin ma'aiki, ga kuWi, sannan ga labarawa da kyauta. Me ki ka manta?."""

"Safeera ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba ta fita, dan ta ga yanayin Umma baza ta fahimce ta"

wuri ba.

Islaha tana zaune a kan kujerun da aka yi su na gini a compund Win gidan sanyi yana

"ratsata, ta ™an™ame jikinta tana rawar sanyi cikin rashin mafita."

"Ta kalli ™ofar da zata kai falo, ta Wauke kai tana lumshe ido tana jin numfashinta yana yin sama."

Ta san ko me zata cewa Mama baza ta bar ta ta shiga ba sai ta ga dama. Mama indai akan kuWi ne

"bata Waga ™afa, bata damu da inda zaki samo ba, ita dai kawaai ki bata shine kwanciyar hankalinta."

Sau da dama Islaha tana ji har gwara zaman gidan marayu akan gidan Mama. Can babu mai

"takura mata ta kawo kuWi, in ta gama abinda take yi ta dawo ta kwanta shikenan."

"Duk da can Win ma akwai ™ananun ™alubale, ta buWe ido kawai ta ganta a gidansu Saheer, bata"

"san ya aka yi ta amince ta biyosa ba. Dan ta san a dokar gidan marayu, in dai mutum zai yi adopting Winka, kuma ka wuce shekara sha biyu, dole sai da amincewarka kafin hukumar gida ta"

"yarda. Balle ita, da ta kusa gama university a lokacin."

"Da kanta ta amince masa ta biyosa, ba ta san meyasa ya yi adopting Winta a lokacin ba, ta san sha"

"™uwar da suka yi ne sila, amma wani lokacin tana danasani."

"In Mama ta yi wani abun, sai ta ji kamar ta haWa kayanta ta koma, duk da ta san baza a karSe ta ba, kamar an yaye ta ne. Amma tana da yayyun da ™awayen da suka tashi tare, suka yi aure a manyan gidajen da zata iya zuwa can ta zauna. Kawai bata son zubawa Hamma ™asa a ido ne, da"

wata ran sai dai ya buWe ido ya ga bata nan.

Šankwalinta ta jawo ta rufe kunnenta ta jin sanyi yana shigar mata kunne ta ko wanne Sangare.

"BuWe gate Win aka yi aka shigo, sai ta Waga kai ta kalli wanda ya shigo."

"Safeera ta gani, ganinta a zaune a wajan sai ta ™araso da roba a hannunta ta ce, ""Islaha lafiya ki"

"ke zaune a nan? Kin san dai wajan nan ba wajan zamanki bane, tunda ba cikakkiyar lafiya ce dake ba ko?."""

"Islaha ta kalle ta tana ™an™ame jikinta ta ce ""Safeera Mama ce ta ce in fito na zauna."""

"""Akan me?."""

"""Akan ban kawo kuWin ba, kuma bani da kuWin ne shiyasa. Da meye dubu goma ko ashirin da na"

"bata?."""

"Safeera ta zauna kusa da ita, cikin fusata ta ce,

Please Login or Register in order to submit comment