gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading RAGAYAR DUTSE Dawowa Mai Hatsari book 1 By Nana Haleema Chapter 19 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su"

suna nan kamar haka.

Kabbasa spray

Dufr khumrah Mahlab khumra Body milk Kuleccam

Matan Maiduguri

Ready to use dilka

Halawa

Shuwa Arab hair mist Cotton incense Dorut after period Dukhaan stool Gabgab

Sandal flex Sandal sukkaria Kajiji

Halud Arabian oud Oil perfume Room fresh

Multi purpose sprays Curtains incense Kabbasa

Farce Marshoosh Senegalese Kajiji Dilka soap

Dilka cream

"Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku"

lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168

08164570032

Islaha a kiWime take bincika wayarta amma babu hotunan Hafsa babu alamarsu. Ta duba trash da

duk inda take tunanin zata gansu amma babu.

"Mamaki da al'ajabi ya kamata, ta ri™e baki zuciyarta tana bugawa cike da tsoro."

"Da hanzari ta juya ta koma office Winsu Safeera, tana shiga ta ce, ""Safeera kin goge hotunan da na"

"nuna miki ne?."""

"Safeera da mamaki ta ce, ""ban goge ba, ta ya zan goge waWannan hotuna nan masu amfani?."""

"Islaha ta dafe kai ta ce, ""Safeera daga fita ta daga office Win nan an goge hotunan nan, an goge su"

"wallahi."""

"Safeera ta mi™e tsaye cike da tashin hankali, ta kalli Saleem da yake kallonsu, ta sake kallon Islaha."

"Cikin mamaki ta ce, ""An goge kuma!."""

"""An goge su, babu inda ban duba ba, amma ban gansu ba."""

"Safeera ta ce, ""Islaha wallahi ban goge ba, ni ban san ma kin bar wayar nan a office Win nan."""

"Saleem ya ce, ""me yake faruwa? Wanne hotuna ne?."""

"Islaha bata kula shi ba ta ce, ""da ki ka fita daga nan waye ya shigo?."""

"""Ban sani ba, da na san wayarki a nan bazan fita na barta a nan ba."""

"Ta dafe kai ta ce, ""Daga ni sai ke, sai Hamma da Barr ne kaWai muka san da hotunan nan, waye ya"

"san dasu har ya biyo ni office ya goge?."""

"Safeera ta ce, ""Wallahi nidai ban goge miki ba, akan me zan goge to?."""

"Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, ""dallah bana zarginki, ki daina yi min rantsuwa. Abin ne"

"ya.....""sai ta kasa ™arasawa ta dafe kanta cikin yanayin da bata san meye ba."

"Saleem ya ce, ""kun barni a duhu, ku faWa min abinda ya faru mana. Wanne hotunana aka goge?."""

"Islaha ta kalle sa ta ce, ""ka yi ha™uri, bazan iya faWa maka a yanzu ba, amma nan gaba kana daga cikin waWanda zasu sani. Safeera in kin gama mu wuce kawai"" ta faWa tana fita daga offife Win"

cikin mamakin wanda ya san da hotunan har ya goge.

A wannan yanayi ta kira Saheer ya zo ya Wauke su a mota suka tafi.

"Tunda suka shiga bata ce komai ba, tana tunanin wanda ya goge hotunan nan, tana mamakin ya"

"aka yi aka san dasu har aka biyo ta aka goge?. Kuma gashi a wajen aiki ne, kenan an san ta Wauki hotunan?. Amma babu wanda ya ganta, ko an ganta ai ba a san ta yi hoto da video ba. Lallai akwai lauje cikin naWi, dole ta dage sosai akan lamarin nan, dan taga ba abin wasa bane ba."

"Saheer ya katse mata tunani, ya ce, ""Baffa ya ce na mayar dake gida, ko gidan Addn kar ki je."""

"Ta Wago ido ta kalle sa suka haWa ido, ya Wauke kai ya ce, ""Ya kira ki ba ki Wauka ba, ya ba da umarnin in mayar dake gida. Amma in baza ki koma ba ki kira sa ki faWa masa, sai in kai ki inda ki"

"ke so."""

"Shiru ta yi bata tanka ba dan bata san me zata ce ba, ta ya zata iya yi masa musu akan maganar"

Baffa? Ai ko bata so dole ta yi ha™uri.

"Har suka je ™ofar gidan bata ce komai ba, sai da ya tsayar da motar Safeera ta ce, ""Hamma sai"

"anjima."""

"Ya yi murmushi ya ce, ""To Safeera, a gaishe da Umma."" Bata ce komai ba ta fita ta shiga gida."

"Islaha ta sauke ajiyar zuciya ta ce, ""Ka san meye?."""

"Ya kalle ta ya ce, ""ina jinki."""

"""Hotunan nan da na nuna maka na hafsa?"" Ta faWa da sigar tambaya."

"Ya girgiza kai ya ce, ""ina ji."""

"Ta yi ajiyar zuciya ta ce, ""wallahi an goge su Hamma."""

"Ya buWe ido cike da mamaki ya ce, ""kamar ya an goge? Waye ya goge su?."""

"Ta Wan tafa hannunta ta ce, ""wallahi ban sani ba Hamma, abinda na sani na gama nunawa Safeera kenan, sai na bar wayar a office Winsu na fita naje na dawo. Ashe itama ta fita bata san na"

"bar wayar a wajan ba, wallahi dana dawo na duba babu su ko alama."""

"Saheer ya ce, ""Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!. Mu ga wayar."""

"Ba musu ta mi™a masa ya karSa yana dubawa, kafin ya Wago ya ce, ""An goge su gabaWaya."""

"Cike da damuwa ta ce, ""ban san waye ya goge ba."""

"""Waye ya san dasu?."""

"""Daga kai sai safeera, sai....."" sai bata ™arasa ba tana kallonsa."

"Ya bita da kallo ya ce, ""Sai waye?."""

"Ta Wan sauke numfashi ta ce, ""Barr Suraj. Na sanar dashi ne saboda shine lauyan da nake so ya yj"

"handling case Win. Kuma na tura masa, amma view once."""

"Ya zuba mata ido yana kallon ta har ta kai ™arshe, kafin ya ce, ""waye ya saka ki tura masa?."""

"Ta kalle sa ta ce, ""Saboda lauya ne, dole ina da bu™atar lauya."""

"""To yanzu amfanin me hakan zai yi miki?."""

"Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya yi tsaki ya ce, ""Bakya jin magana Islaha, bakya jin magana"

"kwata-kwata shiyasa bakya jin maganata. Sai da na faWa miki kar kowa ya san maganar nan amma sai da ki ka zagaye ki ka faWa masa. Dan kin faWawa Safeera ba laifi bane, Safeera ΄ar uwa ce a"

"gare mu gabaWaya. Amma shi fa?."""

"Ta rausayar da kai ta ce, ""shima Wan uwa ne a gare ni."""

"Ya harare ta ya ce, ""yanzu me gari ya waya? Meye amfanin faWa masa Win?."""

"Ta sauke numfashi ta ce, ""Wallahi bana zargin Barr ko kaWan, na san bazai aikata min haka ba."""

"Ya kalle ta yana harWe hannu a ™irji ya ce, ""tunda shi bakya zarginsa, faWa min ni ko Safeera waye"

"abin zargi?."""

"Ganin yadda ya kafe ta da ido sai ya bata dariya, ta yi dariya dan ta san yana matu™ar kishi da"

"Suraj, tunda Suraj ya furta yana sonta shikenan Hamma yake jin haushinsa."

"Ta kalle sa ta ce, ""ni na isa? Wace ni da ce haka?."""

"Bai ce komai ba ya Wauke kai daga kallonta bai kula ta ba. Islaha ta ce, ""duk wanda ya goge ma ya"

"je dan kansa, sun yi a banza dan wallahi bazan bar maganar nan ba."""

"Ya kalle ta yana girgiza kai ya ce, ""hakan alamu ne na ana bibiyar ki, hakan alamu ne da an san"

"kina bincike akan lamarin nan."""

"""Hakan kuma shine alamar da take nuna min zargina gaskiya ne Hamma. Zamu haWu dasu Hafsan,"

"zan san duk abinda zan yi akan maganar nan."""

"Ya bita da kallo a sanyaye ya ce, ""ki bi komai a hankali, kin ga gobe zan yi tafiya, don Allah ki"

"nutsu."""

"Ta yi murmushi ta ce, ""To Hamma."""

"Ya Wan sauke numfashi ya ce, ""akwai abinci na siya miki"" ya faWa yana Wauko ledar ya mi™a mata"

"ya ce, ""ki bawa Safeera sai ki ri™e sauran. Kayanki na kai miki Wakinki na ajjiye."""

"Ta yi murmushi tana wasa da hannunta bata ce komai ba. Saheerya ce, ""ya jikin, kin daina jin"

"ciwon?."""

"""Na daina, daman yanayi ne kawai."""

"Ya Waga kai ya ce, ""ki shiga ciki, zan shigo in anjima."""

"Ta Waga kai tana murmuahi yana kallon ta. Ya ce, ""Debbo am."""

"Ta kalle sa ya ce, ""da na dawo daga Niger za a yi auren mu in sha Allah, ina so na mallake ki nan"

"kusa."""

"Ta yi dariya ta ce, ""Allah ya dawo min da kai lafiya Hamma."""

"""Amin matar Hamma. Ki je ciki, ki fara shiga wajan Baffa yace yana son ganinki. Nima yanzu zan"

"shigo."" Ta amsa da to ta fita daga motar ta fara shiga gidansu Safeera."

"Da ™anwar Safeera suka haWu, ta bata abincin ta koma dan bata son haWuwa da Ummansu"

Safeera.

"Kamar yadda ya ce wajen Baffa ta shiga, yana ganinta ya yi murmushi ya ce, ""Islaha kin dawo?."""

"Ta yi murmushi itama, ta ™arasa ta zauna ta ce, ""na dawo Baffa. Ina yini?."""

"""Lafiya lau, ya aikin na ki?."""

"""Alhamdu lillah Baffa."""

"""To ma sha Allah. Saheer ya faWa min duk abinda ya faru, ki cigaba da ha™uri kin ji? Ko wanne bawa akwai irin tasa jarabawar, ke taki ga a yadda tazo miki, ki yi ™o™ari ki cinye sai ki dace. Kar"

"komai ya dame ni, indai ina gidan nan baza ki wula™anta ba."""

"Ta yi murmushi ta ce, ""In sha Allah Baffa. Amma Baffa sai na ga kamar baka da lafiya."""

"""Eh haka ne Islaha, kwana biyu bana jin daWi. Ina fama da ciwon ha™ar™ari, ga zazzaSi. Kin san"

"jikin tsufa, abin sai a hankali."""

"Islaha ta ce, ""Allah ya ™ara lafiya."""

"""Amin."""

"""Ki cigaba da ha™uri, kar wani abu ya kuma faruwa ki ce zaki bar gidan nan, har abada nan"

"gidanku ne, kin ji?."" Ta yi murmushi bata ce komai ba."

"Baffa ya ce, ""Tashi ki je, Allah ya yi miki albarka."" Ta amsa da amin ta mi™e ta fita daga Wakin"

Baffan.

"Da ta shiga Sangaren Mama bata nan, Sangaren shiru babu kowa. Hakan ya yi nata daWi sosai, ta"

"ci abincin da Saheer ya bata, ta gama duk abinda zata yi babu mai takura mata."

"Islaha har ta yi bacci Mama bata dawo ba, hakan ya saka ta yi baccinta hankali kwance ba tare da"

wata damuwa ba.

"Bayan sallar asuba Saheer ya shigo yiwa Mama sallama, ya shiga Wakinta ya samu ta koma bacci."

"Yana fitowa ya haWu da Hanan, Saheer ya bita da kallo ya ce, ""jiya a ina ki ka yini har dare?."""

"Hanan ta ce, ""muna tare da Mama fa."""

"Ya girgiza kai ya ce, ""ki yi yadda ki ka zaSa Hanan, duniya dai ta ishe ki."" Daga haka ya bata waje ya"

fita yana kiran Islaha a waya.

"Tana zaune tana azkhar taga kiransa, ta mi™e ta fito ta gansa ri™e da jaka yana kallon ta."

"Hawaye suka cika mata ido, haka kawai ta ji bata so ya tafi ya barta, duk da yana irin wannan"

tafiyar amma wannan karon sai ta ji ta damu.

"Ta ™araso a sanyaye ya bita da kallo har ta zo inda yake, ya ce, ""Matar Hamma zan tafi, ki yi min"

"addu'a."""

"Hawaye ya sakko mata, ta Wago ta kalle sa ta ce, ""bana so ka tafi."""

"Saheer ya kalle ta, cikin damuwa da rauni ya ce, ""meye na kukan? Kina so na fasa tafiyar ne?."""

"Ta Waga kai alamun eh, ya gyara tsayuwa yana gifanta da murmushi ya ce, ""In na zauna da me zan"

"aure ki? Kin manta kina da tsada, dole sai na dage na nemo sannan zan mallakeki?."""

"Ta kalle sa har tana Waga hannu sama, ta ce, ""ni na yafe maka komai, kawai a Waura auren, ba sai"

"ka bani komai ba."""

"Ya wara ido waje cikin tsokana ya ce, ""duk wannan halittar a kyauta za a bani?."""

"Islaha ta Waga masa kai alamun eh, dan da gaske bata so ya tafi, da ya tafi gwara a aura masa ita"

Win ba tare da ya bata komai ba.

"Ya yi murmushi ya ce, ""DaWin sai ya yi min yawa ai, sai na zama mai son kaina. Ina ni ina Waukar matar Hamma a kyauta? Daraja da matsayin matar Hamma ya wuce haka, dole na fita na nemo"

"na aure ta. Dan tana da tsada sosai, dole sai na dage da neman kuWi."""

"Cikin rauni ta ce, ""Allah ni bana so ka tafi, indai akan neman kuWin aurena zaka tafi gwara mu"

"zauna a Waura auren, ni ko sadakin sai in yafe."""

"Saheer ya yi dariya mai sauti, ya bita da kallon ™auna ya ce, ""Har sadakin sai a yafe min matar"

"Hamma?."""

"Cikin shagwaSa ta ce, ""i'm not joking, Allah so ka je ko ina. Haka kawai yau bana son tafiyar nan, ji"

"nake kamar in ka tafi komai zai canja, don Allah ka zauna."""

"Ganin da gaske take ba shagwaSar da ta saba yi masa bace sai ya nutsu ya ce, ""Meyasa bakya"

"so?."""

"""Ina ji kamar wani abun zai faru in ka tafi. Kamar...Kamar ni dai ina jin kamar komai zai canja in"

"baka nan."""

"""Babu abinda zai faru sai alkhairi, wani lokacin samuwar alkahiri tana zuwa a haka, kafin ya samu"

"haka ake ji kamar abu mara kyau zai faru. Ki kwantar da hankalinki, zan dawo mu yi aure, ki haifa min kyawawa yara, masu irin fatarki, hancinki, girar ki, da bakin ki """

"Ta Wan sunkuyar da kai tana murmushi, shima ya yi murmushi ya ce, ""kin san abinda ya fi komai"

"burge ni a fuskar ki?."""

"Islaha ta Wago ta kalle sa, ya lumshe ido ya buWe ya ce, ""Bakin ki! Yana Waukar hankalina sosai,"

"musamman a yanayi irin wannan."""

Ta sunkuyar da kai tana wasa da hijjab Win jikinta bata ce komai ba.

"Ya kawar da tunanin da ya zo zuciyarsa, ya ce, ""ki yi min addu'a."""

"""Allah ya tsare ka, ya baka nasara akan duk abinda ka je nema."""

"Saheer ya bita da kallo, ya kasa jure abinda yake ji, ya Wan matso kusa da ita ya ce, ""zan iya"

"pecking Win ki?."""

"Ta sake sunkuyar da kai bata ce komai ba, dan nauyinsa da kunyarsa take ji sosai."

"Saheet ya Wan mtsa baya ya ce, ""na bari sai na dawo daga Niger, daga wannan lokacin zan fara"

"rungumeki a ™irjina, matar Hamma..."""

"Ta runtse ido saboda kunyar maganarsa. Ya ce, ""Amin, na gode da addu'ar ki, ki cigaba da kula"

"musamman akansu Hafsa, ki cigaba da saka ido, duk abinda ya faru ki faWa min, zan taya ki aikin daga inda nake in sha Allah."""

"Ta Wan buWe ido ta ce, ""zaka jima a can ne?."""

"Ya Wan Waga mata kai ya ce, ""at least wata Waya."""

"Ta buWe ido tare da rausayar da kai ta ce, ""wata Waya! Allah ya yi yawa."""

"Ya yi murmushi ya ce, ""bai yi yawa ba Matar Hamma, da na tafi zaki ga lokacin ya yi na dawo."""

"Ta sunkuyar da kai ta ce, ""Allah ya kiyaye."""

"Ya kalli agogo jin ana yi masa horn a ™ofar gidan, ya kalle ta ya ce, ""Amin debbo am, na gode da"

"addu'arki. Dana sauka zan kira ki."""

"Ta Waga kai ta ™araso ta ri™e masa jaka ta ce, ""mu je in raka ka."""

"Ya Wan tsaya yana kallonta ya ce, ""akwai iska sosai, kar ta cutar dake."""

"Ta ja hijjab Winta ta rufe hancinta ta ce, ""zan iya."""

"Ya ce, ""to bani jakar, ta yi miki nauyi."""

"""Zan iya"" ta faWa tana no™e kafaWa kamar yarinya ™arama. Ya yi murmushi suka fara tafiya har"

suka fita waje.

"Sadik da zai kai sa tasha yana zaune a mota, ganinsu tare ya yi murmushi ya ce, ""Matar Hamma,"

"kin yi masa rakiya kenan?."""

"Ta yi murmushi ta ce, ""ina kwana."""

"""Kin tashi lafiya?."""

"""Lafiya lau. Ga amanar Hammana, ka kai sa tasha lafiya, ka ji?."""

"Ya yi murmushi ya ce, ""in sha Allah, uwar gida."""

"Ta Wan harare shi ta ce, ""Uwar gida kawai?."""

"Sadik ya rufe bakinsa, ya girgiza mata kai ya ce, ""Kuma Amaryar Saheer. Ai ke two in one ce, uwar"

"gida, kuma amarya."""

"Ta yi murmushi ta kalli Hamma da yake kallon ta yana murmushi ya ce, ""ki koma, akwai iska sosai,"

"kar ki samu attack."""

"Ta Waga kai ta ce, ""Allah ya kai ka lafiya, ya dawo da kai lafiya."""

"""Amin matar Hamma, ki koma. In Mama ta farka ki ce mata na tafi, na shiga tana bacci."" Ta Waga"

kai tana koma ciki jikinta a sanyaye.

"Saheer sai da ya ga ta shiga sanna ya sauke ajiyar zuciya ya shiga motar. Sadik ya kalle sa ya ce,"

"""Hamma na Islaha, Allah ya bar soyayyarku."""

"Ya amsa da amin kafin ya ce, ""Allah da na dawo auren nan za a yi, ko meye ajjiyesa zan yi na"

"fuskanci aurenmu. Na kusa gazawa akan ha™urin da nake yi, gwara mu yi a wuce wajen."""

"Sadik ya yi dariya ya ce, ""yanzu ina zamu je?."""

"Ya harare sa ya ce, ""ina ka san zamu je?."""

"Ya yi dariya ya ce, ""Tasha."" Bai kula ba sa Sadik ya ja mota suka bar unguwar yana sauke numfashi"

cikin kewar masoyiyarsa.

"_Kamar da gaskiyar Islaha, tafiyar Saheer zata iya canja mana labari. _"

Nana Haleema
'<Ψϋί

*RAGAYAR DUTSE.*

©ώ *Nana Haleema.*

*Book 1*

*Page 020.*

SCENT BY SAPNAH BORNO.

Hajiya ta kina son gidan ki yayi Kamshi? Kina so kiyi wannan kamshin irin na matan borno? Kina

"so tun kafin isowarki waje k amshin kabbasar ki ta rigaki isowa? To indai wannan ne kizo scents by Sapnah Borno, zaki samu fiyeda yadda kike bukata da yardar Allah."

"Sapnah takawo muku turaren kabbasa irin na manyan matan Borno Wanda ko turara Kaya kikayi indai kika zauna waje sai kin bar kamshin ki, tanada kabbasa spray mai musulmin dad i, sannan tanada turarukan wuta masu bada nutsuwa, bata tsaya iya wannan ba tana saida ready to use dilka, sannan tana zuwa duk garin da mutum yake tayi gyaran amarya, abubuwan datake saida su"

suna nan kamar haka.

Kabbasa spray

Dufr khumrah Mahlab khumra Body milk Kuleccam

Matan Maiduguri Ready to use dilka Halawa

Shuwa Arab hair mist Cotton incense Dorut after period Dukhaan stool Gabgab

Sandal flex

Sandal sukkaria

Kajiji

Halud Arabian oud Oil perfume Room fresh

Multi purpose sprays Curtains incense Kabbasa

Farce Marshoosh Senegalese Kajiji Dilka soap

Dilka cream

"Tana nation wide delivery ko wacce k asa. Sannan Tana promo a yanzu haka, karku sake a Baku"

lbr.

Zaku sameta ta wannan number Kai tsaye 08093772168

08164570032

"Islaha ko bacci bata iya komawa ba, tana zaune kawai tana kewar Hamma. Har Saheer ya yi mata"

"waya yace motarsu ta tashi, ta sake yi masa fatan alkhairi kafin ta kashe."

"A sanyaye ta tashi ta gyara Wakin da take ciki, ta fita ta damawa Baffa kunun kanwa da yake"

"yawan sha, ta dafa tea ta juye a flask sannan ta Wauko doya ta fara gyarawa dan ta soya."

"Har ta kammala ta yi wanka babu wanda ya tashi, ta fito ta sha tea Winta dan zata je su haWu"

Zainab a inda ta ce su haWu.

"Ta gama kenan Mama ta fito tana amsa waya, Islaha ta tsaya cak har ta ™araso, sannan ta ajjiye"

wayar tana bin Islaha da banzan kallo.

"Islaha ta ce, ""Mama ina kwana? Hamma ya ce in faWa miki ya wuce, ya shigo kina bacci"" ta faWa"

"lokaci Waya, dan kar Mama ta Sata mata rai ta manta bata faWi sa™on Hamman ba."

"""Uwar iyayi, dashi nake waya ai. Šanki ne ko Wana?."""

"""Šanki ne Mama, ki yi ha™uri"" ta faWa a sanyaye dan haka kawai take jin kanta babu daWi."

Mama ta bita da harara tana ™wafa ya wuce bata ce komai ba.

Islaha ta yi ajiyar zuciya ta Wauki handbag Winta ta fita daga gidan. Sai da ta fita sannan ta saka

"facemask, ta kawo cotton ta toshe kunnenta saboda iska, bayan ta saka hijjab har ™asa."

"Lokacin ™arfe tara na safe, ta hau napep ta nufi makarantarsu Zainab dan a nan suka yi zasu haW"

u.

"Tana sauka ta yiwa Zainab waya bata Wauka, ta ajjiye wayar tana jiran Zainab. Babu jimawa ta ™"

"araso ta saka ni™ab, dan Islaha bata gane ta ba sai da ta ™araso. Zainab ta zauna a kusa da ita ta ce, ""Adda ina kwana."""

"""Lafiya lau Zainab, na fito dake da sassafe ko?."""

"""Babu komai Adda. Ki yi sauri kafin a farga bana nan, yau sun san bana zuwa lecture kuma ban"

"sanar zan je yin kitso ba."""

"""Hafsa ta dawo gida ne?."""

"""Ta dawo, amma jiya da daddare an sake fita da ita. Hafsa gabaWaya ta canja Adda, kashe kuWi"

"take yi yadda take so. Haka su Sauda suke yi suma, to itama ta shiga sahun su."""

"Islaha ta ce, ""ba ki ga wata alama a tare da ita na rashin gaskiya ba?."""

"Ta girgiza kai ta ce, ""yanzu sun daina hira dani, ko yaushe warewa suke yi ita da Fadwa."""

"Islaha ta Wan yi shiru tana tunani, Zainab ta ce, ""ranar da mu ka haWu dake sai da aka kai ni wajan"

"Mama, ta ce in dai ta sake ganina tare dake wallahi sai ta yi maganina."""

"Ta kalli Zainab Win ta ce, ""ke ba a taSa neman fita dake ba?."""

"""Na faWa miki lokacin da aka kira mu office Win nida Hafsa cewa aka yi ni na je waje, daga ranar"

"Hafsa ta canja. Dan yanzu ma ance babbar makarantar kuWi zata koma da karatu."""

"Islaha ta dafata ta ce, ""Zainab don Allah kar a kira ki ki aikata wani abun mara kyau, ki taimaki"

"maraicinki, ki cigaba da sana'arki, har ki yi aure."""

"Ta Waga kai ta ce, ""in sha Allah Adda bazan yi komai ba."""

"Islaha ta ce, ""Yauwa, na san ke rainona ce, baza ki yi wani abu mara kyau ba. Na gode sosai, zaki"

"iya komawa"" ta faWa tana buWe jaka ta Wauko dubu goma ta bata."

"Islaha ta ce, ""ki yi kuWin mota, sannan ki siyi abinda ki ke so. Ko da za a ce ina ki ka je, ki nuna kuW"

in kice kin je kin yiwa wata kitso ne ta baki.

Zainab ta girgiza kai tana ji kamar ta faWa mata matsalar da take damunta amma bakinta ya yi

nauyi ta kasa. Daga nan suka yi sallama suka rabu kowa ya kama hanyarsa.

"Islaha gida ta koma dan bata da inda zata je, bata da aiki kuma baza ta wahalar da kuWinta"

ta je babu abinda zata yi ba.

"Tana shiga ta ga Mama ta fito daga Wakin Baffa hankali a tashe tana faWin, ""Islaha Baffa ba ya"

"motsi!."""

"Gaban Islaha ya faWi, bata taSa jin kalmar da ta soki zuciyarta lokaci guda ba sai wannan, ta ji wani iri yarr a jikinta, kanta ya sara, naman jikinta ya fara rawa. Da hanzari ta bi Mama, ta shiga Wakin taga Baffa kwance ya kumbura kamar wanda aka hura. Hankalinta ya tashi ta gigice, ta fito jikinta"

yana rawa ta rasa ya zata yi.

"Waya ta Wauka hannu yana rawa ta kira Sadik, yana Wauka ta ce, ""Hamma Sadik! Ka zo gidanmu,"

"kazo gida, Baffa ba yamotsi, ka zo don Allah!."""

"Tsabar ruWewa bata tsaya ta ji me yake faWa ba ta kashe wayar tana kai kawo, suna tsaye ita da"

"Mama da Labiba da Hanan, Islaha ta fi ce da gudu."

"A lokacin Sadik ya shigo a ruWe, ganin halin da Baffa yake ciki ya saka ya fita da hanzari nemo"

"maza biyu a ™ofar gida, suka Wauki Baffa aka saka mota."

"Islaha ta shiga gaban motar, Mama da Labiba suka shiga kusa da Baffa aka ja motar suka tafi."

"Babban asibiti suka tafi Sangaren emergency, aka karSi Baffa da gaggawa dan yanayin nasa abin"

"tsoro ne, yana bu™atar kulawa da gaggawa."

"Sun kasa tsayawa sai kai kawo suke yi ciki kiWima da tashin hankali, Islaha kamar ta shiga ta ga abinda yake faruwa haka take ji. A lokacin take ji ina ma karatun likita ta yi, da yanzu ta san me ake yi a ciki, da tana ciki ana duba lafiyarsa tare da ita. Mintina ashirin da shigarsu, sannan nurse"

"Win ya fito, ya kalli Sadik ya ce, ""a je a siyo wannan maganin yanzun nan."""

"Sadik ya karSa ya fita, ba jimawa ya dawo ya shiga ciki ya kai musu ya dawo ya zauna."

"Har azahar ta yi suna wajan a tsaye, a wajan suka yi sallah suna jira su ji abinda za a faWa musu"

akan Baffa amma shiru.

"Sai ™arfe biyu na rana sannan Sadik ya koma yake tambayarsu jikin Baffa. Likitan ya kalle sa ya ce,"

"""yauwa daman ina neman ka, kai Wansa ne?."""

"Sadik ya ce, ""ni abokin Wansa ne."""

"""Okay, ina iyalansa?."""

"""Suna waje."""

"""Kira su."""

Sadik

Please Login or Register in order to submit comment