gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Dr.bob Complete Hausa Novel by by Aysha Rano Chapter 57 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanxu ba abunda basu gama siya ba tun daga kan kayan baby har zuwa ita kanta nata kayan..bedroom guda ya ware cikin nata yasa akayi renovating dinshi zuwa baby room mai kyau aka kuma cikashi da kayan yara iri iri tun daga kan furnitures har zuwa su toys da sauran kayan wasa na yara..tsakaninta da Amminta ma yanxu mutunci sukeyi sosai dan yanxu tayi hankali ta dena rashin kunya a cewar Ammi shiyasa suke dasawa abunsu..kusan kullum sai sunyi waya da ita dan ko ita Ayshan bata kira ba Ammi zata kirata taji ya jikinta..tana kuma turo mata addu'o'i tace taitayinsu daga nan har lokacin da Allah zai kawo haihuwar wai sai yazo mata da sauki..sosai itama take tausayawa 'yar tata sbd halin da take ciki shiyasa Husna na gama ssce daddy yace tazo ta zauna tareda ita ko ba sbd aiki ba at least zata dan dauke mata kewar gida da take fama dashi..zuwan Husnan kuma ya yayi mata dadi sosai dan kusan kullum suna tareda ita da Miemie a gidan su suke mata komai saidai mai aiki ta tayasu kawai..shima Bobby yana bakin kokarinshi kwarai wajen ganin batayi lacking wani abu daga gareshi ba including time dinshi da kuma caring..sosai yake tsayawa ya kulada ita don ko wurin aiki ma sai ya tabbatar ya gama mata komai snn yake wucewa hakan da yakeyi kuma ba karamin faranta mata rai yake ba..tana jin dadi sosai idan taga yanda daga shi har Mummy da siblings dinshi ke nuna tsantsar so da kula wa cikin nata har watarana takejin ta matsu ta haihu sbd taga irin kaunar da zasu nunama babyn..gani take kmr Mummy da Bobby sunfi ita kanta da babyn ke jikinta kaunarshi amma batasan ko dan riga yazo dunia bane..a halin yanxu dai duk wani fatanta bai wuce Allah ya sauketa lafia ba.

Yau Friday suna zaune parlor ita da Miemie da Husna suna kallon wani film Sab ya shigo gidan da sallama yana hararar Miemie da gaba daya hankalinta ke ga film da suke kallo..bayan ya karaso ciki ya zauna sai ya dan saki fuska yana duban Aysha da murmushi yace"sannu Aunty Aysha"..murmushi itama ta saki tana girgiza kai tace"bazaka dena cemun sannun nan ba koh?.."yana cigaba da daria yace"ai dole ace maki sannu matar Uncle Bobby..wnn babyn namu nasan da kyar idan baya baki wahala don da gani nasan fitina zaiyi wlh"..daria gaba daya suka saki har su Husna da hankalinsu ya dawo kan hiran nasu..Husna tace"wlh uncle Sab kmr kasan nima tunanin da nakeyi knn..na tabbata indai ya dauko halin Adda to wlh ba karamin fitinanne za'ayi ba"..ta karasa mgn tana daria Aysha Kuma tace mata"zanyi maganinki wlh..ki bari insamu time dinki"..Sab yace"ai idan ya dauko halin babanshi bayan fitina ma sai ya hada da masifa da rashin mutunchi..ta6 Uncle Bobby ai ba baya bane wajen wadan nn dabi'un"..da sauri Miemie tace"wlh kuwa uncle Sab..ni kaina gani nak..."bata karasa ba ya katseta ta cewa"C'mon keep quiet wayasa dake a wurin nan?.."turo baki tayi tana rungume hannunta tace"ai nima ba da kai nakeba"..kwafa yayi yace"kicigaba da murguda min bakin nn watarana saina karyashi wlh..badai ni kikaje kikama munafurci a wurin Mummy ba..zan kamaki ne"..sake daure fuska tayi tace"nidai gaskia na fada mata ai..kuma ba ruwanka dani Uncle Bobby yace ka dena shiga harkata"..ya bude baki zaiyi mgn Lamido tace"ya isa haka dan Allah..na rasa meyasa ku kullum cikin fada kuke kmr tom and Jerry".. Sab yace"yarinyar nan batada kunya bakisan halinta bane..wai har ni zataje tayima gulma a wajen Mummy"..Husna tace"ASP Uncle Sab da gaske ba gulma tayi Maka ba..a gabana Mummy ta tambayeta"..wani irin daria Sab yayi yana cewa"bazaki dena Asp Uncle Sab din nan ba koh?.."dariar itama takeyi tace"to ai Asp ne naga"..murmushi kawai yayi ya gyada kai kafin wani cikinsu ya sake mgn Bobby da Nur sun shigayi parlon a tare..da sauri Sab ya mike yana kallonsu da murmushi yace"sannunku da zuwa"..Bobby yace"kai baka zuwa sallahn jumu'a knn?.."Sab yace"yanxun na dawo ai..ask Aunty Zata fada maka ban jima da shigowa ba"..Bobby bai sake cewa komai ba suka karasa parlon suma suka zauna..Miemie da Husna suna gaishesu suka bar parlon shima Sab yana gama gaisawa dasu ya fita dan dama akwai inda zaije...kallon Aysha da har yanxu take zaune yayi kafin a hankali ya mike ya koma kusada ita ya zauna yayi mata side hug yana fadin"how is my baby doing?.."a dan kufule tace"ban sani ba"..yayi murmushi yana nuna cikin nata yace"bafa wnn babyn nake nufi ba wnn"..hannunshi ta ture daga jikinta tana duban inda Nur yake zaune tace"Sir Ina yini"..murmushi ya saki yana kallonta shima yace"lafia lau Lamido..ya jikinki?.."kanta a kasa tace"Alhamdulillah"..Bobby yace"baby bana hanaki kiranshi da Sir din nan ba..call him Nur mana ai sunanshi ne"..girgiza kai tayi tana dan murmushi tace"bazan iyaba"..tana rufe baki Nur yace"kinji mutumiyar kwarai..duk iskancinka dai haka zaka hakura ka barta tace bazata iyaba"..Bobby yayi daria kawai tareda dan rage murya yana kallonta yace"kinsan mene?.."kai ta girgiza mashi alamar bata sani ba..yace"zuwa mukayi dai yau mu fadawa Miemie cewa muna sonta"..dan wara ido tayi tana kallonshi tace"da gaske?.."yace"eh mana..nine ma zanyi masa zancen sbd a abokin Nur nazo yau ba Uncle Bobby ba"..murmushi kawai Aysha tayi tana girgiza kai tasan wnn mgnr wasa yake mata..mikewa zatayi yayi saurin kamata ya mikar da ita snn yace ta turo musu Miemie idan ta shiga..tana murmushi itadai ta wuce zuwa bedroom dinta ta tura musu Miemie kmr yanda suka bukata...tana zuwa ta nemi wuri ta zauna kasa Bobby yace ta koma kan kujera ta zauna..ba musu tayi hakan sai kuma duk sukayi dif aka rasa wanda zai fara mgn cikinsu..can Bobby ya nisa tareda Kiran sunanta..ta amsa kanta kasa dan har wani faduwar gaba taji tanayi ba gaira ba dalili..a nutse sosai ya fara mata bayani ta sigar da yasan zata fahimce shi sosai.. already dama Saida ya fara mgn da Mummy da parents din Miemie snn yazo gareta so ba tareda wani shakku yake mata bayani ba..itadai tsit tayi tana sauraran yanda yake koda mata abokinshi sai daga karshe kuma yace zai barta dashi ya karasa Mata sauran bayanin..bayan ya bar parlon Nur ya dora daga inda ya tsaya itadai kusan mutuwar zaune ma tayi jin wai da gaske Uncle Nur ne ke sonta..sosai ya kakkashe mata jiki da salon soyayyarshi wanda ita halin yanxu dai bazata iya gane shin tana sonshi ne ko kuma bata sonshi ba..shima baiyi gaggawa ba yace she should go and think about it idan ma tanada Wanda zatayi shawara dashi tayi idan ta gama yana jiran feedback dinshi..haka ta mike ta bar parlon jiki a sanyaye kmr kazar da kwai ya fashewa a ciki.
Wnn knn...

Washegari bayan ta idar da sallahr asuba ta dade sosai zaune inda tayi sallahr tana ta addu'o'i bayan ta kammala azkhar dinta..Bobby kuma na masjid bai dawo ba..sosai take addu'a tana rokon Allah ya sauketa lafia ya kuma raya mata abunda zata haifa cikin tafarki madaidaici..saida gari ya fara haske snn ta shafa addu'an snn ta shiga kokarin mikewa amma sai me?..kugunta taji ya rike gam ta kasa ko kwakwkwaran motsi a wurin..ta kai hannayenta biyu ta dafe waist din dasu snn ta sake yunkurawa zata tashi sai kuma taji bayanta shima ya rike da sauri ta sake komawa ta zauna ta rintse ido tana maimaita innalillahi a cikin ranta..Saida taji ciwon ya dan lafa snn ta sake kokarin mikewa a karo na uku still taji bazata iyaba dan haka ta koma tacigaba da zama tana salatin annabi..Bobby daya dawo daga masjid direct kitchen ya shiga ya hado mata tea da shanshi ya zama mata constant duk ya dawo daga sallahn asubah dama saiya fara hada mata yake shiga daki..yana shiga ya ganta zaune nan inda tayi sallah ya ajiye mug din hannunshi kan table da sauri ya nufi inda take yana dagota yace"baby are u alright?.."a hankali ta dago ido tana kallonshi yaga eyes din are so red nan take hankalinshi ya tashi baisan sanda ya durkusa nan kusada ita ya kamo hannnuwanta yana tambayanta what's wrong ba..dan murmushi ta saki ganin har hankalinshi ya tashi tace"ba komai fa partner..kawai tashi zanyi naji bayana ya rike amma believe me yanxu banajin komai"..kamata yayi ya mikar da ita tsaye snn ya shiga kare mata kallo wai ko zaiga wani canji tattare da ita still yaga ba komai dan haka ya rike hannunta ya zaunar da ita kan sofa bayan ya zare hijabin dake jikinta..tea dinta ya dauka ya mika mata yace"to ga tea dinki Kisha"..murmushi tayi ta karba shi Kuma ya dauke carpet da tayi sallah dashi ya ajiyeshi inda ya dace snn ya sake dawowa ya zauna nan kusada ita yana kallonta tana shan tea din...bayan ta gama ya sake kamata suka kwanta kan gado ya rufesu da duvet cikin lokaci kankani kuma bacci yayi gaba da ita shi kuma ya kasa baccin sbd har yanxu bai gama yadda she's alright ba..gani yake kmr idan ya rufe ido ya fara baccin wani abu na iya faruwa da ita har saida ya ga baccinta yayi nisa snn shima ya lumshe ido baccin yayi awon gaba dashi...can cikin bacci Lamido taji kaman ana yi mata suka a maranta nan take ta bude ido baccin ma gaba daya yayi kaura daga idonta..dan motsawa tayi da nufin ta gyara kwanciya sai kawai taji wani irin ciwon mara ya sake kamata har batasan lokacinda ta wani irin salati cikin tsananin tashin hankali ba..da sauri Bobby ya bude ido jin kmr kuka take aikam yana ganinta ya mike zaune da sauri yana janyota jikinshi yace"baby what's wrong"..hannayenta na rike da mararta tace"ba..ya..na..mara..ta..way..yo"..sauka yayi daga gadon da sauri ya dora t shirt akan singlet da three dake jikinshi snn ya dauketa cak ya fita daga dakin da ita..sbd tsabar bala'i ko kuka ta kasayi sai faman salati take dan da gaske tayi zaton karshenta ne yazo..Bobby ma duk a gigice ya fita daga gidan kai tsaye mota ya bude ya sakata ciki snn ya shiga ya tayar da ita suka fita daga gidan..direct hanyar clinic dinshi ya nufa ita kuma tana baya sai faman murkususu take tana maimaita innalillahi..har wani zufa ke keto mata despite air condition dake aiki cikin motar..Bobby gaba daya gigicewa yayi ko driving din yaji kaman bazai iya ba amma dole yacigaba dayi dan kafin ma yace ya kira driver dinshi yazo wani bata lokaci ne haihuwa Kuma ba zaman jiransu zaiyi ba ya sani.. addu'arshi dai bai wuce Allah ya sauketa lafia ba..yana shiga hospital ko parking space bai karasa ba yayi parking daga nan bakin gate tareda bude motar ya fita itama ya fito da ita da sauri yayi cikin asibitin..da yake safiya ne babu mutane sosai asibitin sai few daga cikin staff da masu jinya da suka kwana a nan..labour room ya nufa da ita kai tsaye yaci sa'a kuma ya tarar da matron salamatu on duty dan haka yayi saurin shigar da ita ciki yace tazo ta duba mishi ita..babu wasting of time matron tayi mata ve nan kuma taga cervix dinta is 4 cm dilated koda ta sanar dashi hankalinshi sake tashi yayi don yasan zaiyi taking nata so many hours before ya gama fully dilation tunda primi ce..ga kuma ciwo da take fama dashi tun yanxun dan yanda takejin maranta kamar zai rabe gida biyu ne dan azaba..waya ya zaro daga aljihunshi ya kira aunty sumy yace ta samesu asibiti that bazai iya fadama Mummy ba don tashin hankalinta zatayi sosai so gwara ya bari idan ta haihu sai a fada mata..suna gama waya da ita ya kira Nur shima ya sanar dashi suna asibiti daga nan kuma ya ajiye wayar tashi ya shiga taimaka mata da kanshi..hannunshi ta rike gam cikin azabar da takejin kmr shi zaiyi ajalinta tace"par..tner..zan..mutu..mutuwa..zanyi".. girgiza mata kanshi yakeyi duk a rikice yace"bazaki mutu ba inshaAllah baby..lafia zaki haihu"..girgiza kai kawai Lamido take tana karanta innalillahi wainna ilaihi rajiun..har yanxun bata dena zufa ba ga kuma ciwon yakici yaki cinyewa..tun tana ganin abun kmr wasa har tazo ta fara gaskata tunaninta da gaske mutuwarta ne yazo..sosai take shan wahala amma wai ace har yanxu 4 cm take?..anya kuwa zata iya haifan babyn nan da kanta?..Bobby dai na tareda ita duk ya rikice dan kmr ma bazai iya cigaba da aikin ba amma da taimakon matron ya samu yayi gripping kanshi snn yacigaba da bata duk wani taimako da yasan tana bukata at this stage of labour..bayan lokaci kada n aunty sumy ta karaso asibitin nan Kuma yace taje gida ta taho musu da kayan haihuwa Dan shi bai samu ya dauko komai ba sbd rudu daya shiga..ba musu kuwa ta koma gidan ta dauko kayan da taimakon su Husna da suke gidan ta kuma ce kar su bari Mummy taji labari har sai idan ta haihu..lokacinda ta dawo asibtin suka hadu da Nur a kofar shiga labour room din yanata kiran Bobby amma baya dauka..a karo na farko da taji wani irin nauyin Nur ya kamata kasancewar yanxu tasan shine yake son Miemie..gaba daya sai tajita wani uncomfortable dashi unlike before da har wasa da daria sukeyi a tsakaninsu..shima kanshi Nur din rasa abunda zai ce mata yayi sai yayi kasa da kanshi kawai yana gaisheta cikeda respect kmr yanda ya saba..aunty sumy ta amsa snn tayi excusing kanta ta shiga ciki ward din ta bada kayan aka Mika masu..waiting room aka bude mata ta shiga yayinda shi kuma yaketa sintiri yana kai kawo a wurin yanda kasan matarshi ce nan ciki zata haihu.

After a long suffering Allah ya taimaketa da kuma taimakon perfect hubby dinta ta haifi santalelen yaronta namiji..yana zuwa dunia dama daya tsala wani irin kuka hatta Nur dake waje saida ya jiyo sautin kukan..sosai Bobby ke farin ciki da kanshi yayi mata komai ya gyarata matron kuma ta gyara baby snn sukayi moving nata to postnatal matron na rikeda jaririn dake lullube da shawl..har lokacin Bobby bai amsa yaron ba duk kuwa da yanda yakejin kmr ya ajiye duk wani abu da yakeyi yaje ya karbeshi amma baiyi hakan ba saida suka kaita postnatal snn matron ta mika mashi babyn ya karba da Bismillah yana kallon cute face din babyn da at once yaji wani iri so da kaunarshi na sake mamaye ko wane lungu da saqo na heart dinshi..lumshe Ido yayi tareda matsar da bakinshi ya Karanta addu'a sosai ya shafama babyn sai kuma yayi kissing forehead dinshi tareda mannashi da chest dinshi a fili ya shiga furta"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah..Allah ya rayaka cikin tafarkin islam"..ya jima sosai rungume da yaron kafin ya kwantar dashi a cradle tareda karasawa kusada ita ya zauna ya kama hannunta ya rike bayan yayi pecking forehead dinta cikin tsananin happiness yace"Rabbi ya saka maki da aljannah..i love u so much"..itadai bata ma San yanayi as tunda ta samu ta haihu wani baccin wahala yayi gaba da ita..sai a lokacin ya tunada su aunty sumy dake waje nan yace matron ta turosu ciki shi kuma yayi saurin daukan wayanshi ya dannawa Mummy kira...tana dagawa cikin excitement yace"Mummy guess what?.."Mummy tace"just go straight to the point which one is guess what?.."murmushi ya karasa saki yana sake godema ubangiji cikin zuciarshi yace"Mummy Aysher ta haihu..u need to see my son Mummy he is so so very cute..he is more than handsome Mummy ina sonshi sosai wlh"..shiru Mummy tayi kmr bata fahimci me yace ba har saida ya sake kiran sunanta snn tace"u mean Aysha ta haihu?.."yace"yes Mummy tun asuba muke asibti and bata dade da haihuwa ba"..wani Hamdala yaji Mummy ta saki kawai sai yaji tayi disconnecting call din ya maida wayarshi aljihu dan yasan yanxun nan za'a ganta ta iso asibtin..aunty sumy na shigowa ta rungumeshi cikij farin ciki take cewa"Oh Allah mungode Maka..Alhamdulillah"..shima rungumeta back yayi har yanxu ya kasa dena murmushi yace"am now a father aunty Sumayya..i can't believe this"..rabashi da jikinta tayi cikin tsananin murna ta karasa inda babyn ke kwance ta daukoshi tana kallonshi with so much love tace"Allah ya Maka albarka"..daga haka ta ajiyeshi tareda komawa inda Aysha ke bacci itama ta rike hannunta tana kallonta with smile tace"sannu da kokari Aysha..Allah maki albarka kema ya baki lafiar breastfeeding"..Bobby dake tsaye yana kallonsu yace"Ameen Ameen"..daidai lokacin Nur ya shigo Bobby na ganinshi yayi saurin isa inda yake yayi hugging dinshi so tight yana ce mishi"u have become a father man.. congratulations to u"..rungumeshi back Nur yayi cikin so much excitement yace"Congratulations to u too bro..am so happy for u..Allah ya raya mana boy"..da sauri Bobby yace"Ameen..Ameen Ameen"..har yanxun sai suna rungume da juna sun kasa rabuwa musamman Nur da yakejin kaman ya taka rawa dan farin ciki amma ba halin yin haka sbd aunty sumy dake cikin dakin..duk sai yaji kaman baby expressing farin cikinshi yanda ya kamata ba..a hankali ya zame jikinshi shima ya nufi cradle din yaron..ya dagoshi yana washe baki kmr gonar auduga yace"Allahumma barikh ya Habibi..barakhallahu lakha"..ya karasa tareda yima yaron addu'a ya shafa mashi shima snn yayi saurin ajiyeshi ya fita daga dakin yana cewa"i will be back soon"..daga haka ya fita waje shi Kuma Bobby ya karasa inda babyn yake yanata kallonshi yanajin kmr zai maidashi ciki sbd son da yake mashi..ko 30 mins baiyi da zuwa dunia ba amma jin sonshi yake ta ko ina a cikin zuciyarshi wnn baisan ya zaiji ba idan yaron yafi haka girma Kuma.







Finally dai yau an haifi dan soyayya😂 welcome to parenthood Uncle Bobby and Aunty Lamido❤️🥰






















Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
70
Nur ne ya dawo dakin dauke da zamzam da dabino kai tsaye inda babyn ke kwance ya nufa ya daukoshi snn ya mikama Bobby ruwan zamzam din yace"come and give it to him"..ba musu Bobby daya kasa dena smiling ya matso yana bude zamzam din shi kuma Nur yana rikeda babyn haka sukayi bashi zamzam din yasha tareda dabinon da Bobby ya danyi chewing snn ya matsa mashi ruwan a bakinshi..aunty sumy dai na zaune tana kallonsu tana smiling..wnn friendship nasu ba karamin burgeta yakeyi ba tuntuni..they treat each other like brothers..Saida ta bari sun gama bashi snn tana dan murmushi tace"so doctors basa ma kids dinsu exclusive breastfeeding knn?.."kallonta sukayi gaba dayansu ba dai Wanda yace mata wani abun ita kuma ta sake cewa"naga dai kune kullum kuke counselling mutane kan su dinga ma yaransu ebf amma ku gaku nan Medical doctors daku kunzo Kuna bama yaronku ruwa ko one hour baiyi a dunia ba"..Nur dai kanshi na kasa ya kasa cewa uffan sai Bobby ne yace"aunty wnn ai ba normal water bane..zamzam ne fa"..daria kawai tayi bata sake cewa komai ba.

Mummy na shigowa dakin direct dama inda ta hango cradle ta nufa Bobby yayi saurin mikewa zakiyi hugging dinta tayi saurin kaucewa tana cewa"abeg let me pass..ana ta sabon jini wa yake ta kai"..daga haka ta karasa inda cradle din yake ta dauko babyn ta shiga kare mashi kallo..Bobby ya wani kwabe fuska yace"Mummy amma nine danki fa bashi ba"..harara ta sakar mashi tace"to daga yanxun shine yarona not u"..sake kwabe fuska yayi yana kallonta sai ta bude mashi hannu tana daria sosai tace"come here my son..the latest dad"..da sauri ya karasa ya shige jikinta Mummy ta hadasu shi da yaron mashi tayi hugging nasu so tight tana yima Allah godia cikin ranta..saida suka gama expressing farin cikinsu snn ya janye jikinshi Mummy kuma ta maida babyn cradle snn ta nufi inda Aysha..kallonta tayi yanda take bacci peacefully ta sauke ajiyar zucia tareda furta"Alhamdulillah Alhamdulillah..Allah shine abun godia".

Karfe 12 saura driver ya kawo Husna da Miemie tareda abinci da Mummy tace suzo dashi..zuwa lokacin Aysha ta tashi daga baccin har ma ta dan ware tana responding to mgnr da Aunty sumy ke mata har yanxun ko babyn bata dauka ba wai kunyar mummy takeji..ganin da gaske ba daukan nashi zatayi ba gashi ya fara rigima dole ta tashi suka bar dakin itada aunty sumy da Miemie ya rage daga ita sai Husna..cikeda farin ciki Husna ta karasa ta dauko mata babyn ta kawo mata shi tana cewa"take a look at him Addah..he is more than cute..har na kira Ammi na fada mata"..kallon nashi Lamido tayi tanajin wani irin sanyi na ratsa zuciarta..soyayya mai girma taji tanayima yaron just by looking at him..nan take taji she's so attached to him kaman dai ba yau yazo dunia ba..tana dan murmushi ta dagoshi ta mannashi da chest dinta snn ta sauke wani ajiyar cuzia tana godema Allah cikin zuciarta Husna Kuma na zauna tana kallonsu with adoration..shigowar Bobby yasa ta mikewa ta fita daga dakin bayan ta gaisheshi..a nutse ya karaso cikin dakin ya zauna nan kusada ita tareda yi mata side hug yana lumshe eyes dinshi yace"na gode sosai partner..May Allah reward u abundantly"..dan murmushi ta saki tana Kara rike babyn a jikinta shi kuma ya dagota daga jikinshi tareda durkusawa nan kasa ya kama hannunta yana kallon eyeballs dinta yace"i don't have enough words to thank u baby..i just want u to know that ina sonki and zan cigaba da sonki till my very last breathe..thank u for making a father today..Allah ya raya mana shi yayi mashi albarka"..kai kawai Lamido take gyada mishi tama kasa cewa komai.. shi kuma sosai ya rikice mata yanata faman godia hade da expressing mata how much he loves her..banda blushing ba abunda takeyi sbd dadi..itama tana sonsu fiyeda komai nata.

A ranar akayi discharging dinta suka koma gida bayan an tabbatar da itada babyn suna cikin koshin lafia..suna komawa gida ta samu kira daga daddy da Ammi duk sai murna suke sun samu grandson ita har ta kasa tantance wanda yafi wani murna da haihuwar nata..a ranar wata Goggonta tazo daga Gombe sbd ta zauna da ita ta kuma kula da ita da babyn gaba daya..Billy ma dake can tana ta faman shirin biki without her best friend tana samun labarin haihuwar ta kirata vid call tanata ihun murna wai a nuna mata danta ta gani..sosai suka bata lokaci suna video call Billy sai santin babyn take wai kmr tayi tsuntsu tazo Kano.

Bayan kwana hudu...

Cikin kwanakin nan Lamido taga asalin so da kauna daga wajen family da friends..ba family dinta ba ba kuma familyn Bobby ba..sosai suke samun kula itada baby abun har mamaki yake bata..mutanen Gombe zai zuwa suke ganin baby wasu kuma suna nan bazasu tafi ba sai bayan suna ciki hadda aunty Fiddausi..Besty ma yana samun labarin haihuwar a bakin Husna ya kirata ya mata barka tareda alqawarin zaizo ganin baby..haka zalika yan school dinsu ma da yawa sunzo abun dai ba'a cewa komai..Bobby kuwa bai cika zama ba yanxun as yanata shirye shiryen raka Waziri India ganin doctor dan Waziri da kanshi yace lallai saidai suje tare dashi..shima da kanshi yazo ganin baby har Kano tareda uncles din Bobby da kuma some of their family members..family din Mummy ma sunzo sosai kasancewar ita din mace ce mai zumunchi so kusan kowa yana kokarin yazo duk wani sha'ani daya shafeta...ahalin Lamido ma sunzo sosai tun daga kan uncles dinta da aunties dinta dama sauran family da friends..wasu sun wuce a ranar wasu kuma sunan nan sai anyi suna.

Yau ma kmr kullum tun safe suke fama da baki yan barka gashi babyn sai kuka yake an rasa abunda ke damunshi..har kuka itama saida tayi wai batasan me yakeso tayi mashi ba kuma..da kyar ta samu yayi bacci da taimakon Goggonta dake tareda ita..tana zaune gefen gado tana kallon yanda yake bacci peacefully sai taga ya koma mata kmr babanshi..he looks exactly like Bobby dan ko abu guda nata bai dakko ba..haskenshi eyes dinshi nose dinshi bakinshi and even fingers dinshi irin na Bobby ne sak..komai da komai irin nashi ga kuma dan banzan rigima da yake dashi shima ta tabbata na baban nashi ya dauko..hannu takai tana shafa soft hair dinshi tana cigaba da kallonshi tana murmushi Goggonta ta shigo dakin da ruwan zafi a flask tace"au yanxu Aisha har yanxu kina nan zaune kina kallon danki sbd rashin kunya so kike ruwan wankan ya gama wucewa ne kome?.."dan daure fuska tayi tana duban Goggon nata tace"yanxu dan Allah

Please Login or Register in order to submit comment