gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Dr.bob Complete Hausa Novel by by Aysha Rano Chapter 54 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiransu..suna shiga motar ya tadata suka fita daga gidan.

Suna shigowa hospital din Miemie ta fita da sauri zuwa office dinshi ta banka ta shiga ko sallama batayi ba ta fada mashi halinda ake ciki..yanda ya fito a rude har mutane saida sukayi mamaki dan lokaci daya yaji komai nashi yayi tsaye cak..da sauri ya karasa inda motar yake ya bude back seat nan ya ganta jingine jikin seat din idonta na fitar da hawaye..hannu yakai ya ta6a forehead dinta yaji still da zafi a jikin kawai sai ya dauketa a hannunshi ya fito da ita daga motar zuwa cikin asibitin..sauri kawai yakeyi ya karasa office dinshi bai ko damu da kallon da jama'a ke binshi dashi ba..yana shiga ya kwantar da ita kan gado snn ya cire mata hijabin jikinta kawai sai ya tsaya yana kallonta without saying anything..Miemie data shigo office din da sauri yace ta shiga bayi ta kawo mashi warm water da towel..ba musu tayi yanda yace ta kawo mashi yace taje driver ya maidata gida..shi kuma ya fara jika towel din yana shafa mata ruwan a jiki sbd temperature nata ya sauka..bayan ya gama ya fita zuwa pharmacy da kanshi ya kar6o drip da allurai snn ya koma office din nashi..tana ganin drip da allurai hannunshi ta fara kuka shidai bai iya ce mata komai ba ya samu ya lalla6a yasa mata drip din don yasan ba wani abinci zata iyaci ba..yana gamawa ya mata alluran da zaiyi saurin saukar mata da fever din snn yaja seat dinshi ya zauna nan kusada ita yana kallonta..Aysha na kuka sosai tace"partner am so sorry plss"..hannunta ya kama ya rike cikin nashi baidai ce mata komai ba..mikewa ta shiga kokarin yi shi kuma yayi saurin maidata yana nuna mata cannular dake hannunta yace"careful mana"..komawa tayi ta kwanta tanacigaba da kallonshi tana hawaye..shima kallonta yakeyi yanajin wnn abun da yazo ya tsaya mashi a throat dinshi tun jiya yasan indai ba mgn ya samu yayi da itaba wnn abun bazai fada ba dan haka ya dan runste eyes dinshi kafin a budesu a kanta voice dinshi kasa kasa yace"so da gangan kikayi hakan koh?.."da sauri ta hau girgiza kai tace"wlh coincidence ne..i never knew such thing will happen am sorry"..yace"but u even hugged him..why did u do that?.."tace"i thought it was u sbd eyes dina a kulle suke saida naji perfume dinshi ba irin naka ba nasan u are not the one..kayi hakuri ka yafemun dan Allah"..ta karasa mgnr tana kuka sosai..shiru kawai yayi yana kallonta yasan shima yayi over reacting jiyan nn amma it wasn’t his fault..sake matsawa yayi yuana rikeda hands dinta yace"nima am sorry for reacting the way i did..i shouldn’t have done that so kiyi hakuri"..kai kawai take gyada mishi..ganin yanda har jikinta na rawa sbd kukan da takeyi yace she should stop talking zasuyi mgn anjima..sosai ya sake bata hakuri yana cewa yasan bai kyauta ba..itama tace mishi ko dan gaba if wani abu irin wnn ya faru saurin fushi bayada amfani gwara su zauna suyi communicating that communication is a solution to any problem..shiru kawai Bobby yayi yana kallonta dan kunya yaji sosai wai itace take fada mashi what is right..sauka ajiyar zucia yayi yana ayyana idan fa bai dena wnn saurin fushi da zafin ran ba watarana zaiyi dana sani duk sai yaji jikinshi yayi sanyi yace inshaAllah zaiyi kokarin gyarawa kuwa..ita kuma tayi shirun bata sake mgn ba har drip din ya kare zuwa lokacin kuma fevern dake jikinta ya dan sauka shima sai a lokacin ya dan samu peace of mind..a hankali ya mike zuwa inda wayanshi keta ringing ya dauka snn ya samu wuri ya zauna bayan yayi picking call din..a daya bangaren Nur yace"hey are u at the office?.."kmr bazaice wani abu ba sai can yace"what?.."Nur yace"just answer me dan rainin wayo"..lumshe ido yayi yana kallon inda take kwance kafin a hankali yace"ina nan".. Nur yace"ohk gani nan zuwa"..daga haka ya ajiye wayar tareda mikewa zuwa inda take ya maida mata hijab dinta yana cewa"do u need anything?.."a hankali ta girgiza mashi kai alamar no..yace"bazaki ci komai ba?.."nan ma kan ta sake girgiza mashi yace"bari Nur yazo idan ya tafi sai in maidaki gida tunda zazza6in ya sauka"..kai kawai ta iya gyada mashi shi kuma ya fita daga office din..can parking space yaje ya tsaya tana jiran isowar Nur bai dade da tsaiwa ba kuma sai ga Nur din ya karaso..bai bari ya karaso nan inda yake ba ya nufi wurin motar shi..yana zuwa ya bude ya shiga tareda relaxing yana kallon Nur din a hankali yace"daga ina kake haka?.."maimakon ya bashi amsa sai cewa yayi"wai what's wrong with ne?..u look disturbed..ina Lamido?.."a hankali Bobby yace"she's inside"..Nur ya dan wara idanu yace"inside kuma?..yanxu wurin aikin ma saika taho da ita Bobby sbd gajen hakuri"..harara ya watsa mashi mai kyau tareda sakin wani tsaki yace"u are annoying wlh..to batada lafia kuma ni bana gidan shine aka kawota na dubata"..wani murmushi Nur ya saki yana shafa gemu yace"so meke damunta?.."Bobby yace"fever..amma nasa mata drip yanxu fevern ma ya sauka"..Nur na gyada kai yace"Allah bata lafia..amma why ba'a yi mata test ba?.."juyawa yayi ya kalleshi rai a dan 6ace ganin kmr neman zance kawai yakeyi yace"ban saniba".. Nur ya kwashe da daria yana kallon abokin nashi yace"kaga malam ka maida wukar ka ni bani na kar zomon ba..am only trying to be of help"..a dan fusace Bobby yace"to hell with u and ur help"..kallonshi kawai Nur yake har yanxu bai bar murmushi ba yace"ohk let me keep quiet tunda bakaso..dama cewa zanyi kasa ayi mata pt kilan she's pregnant"..da sauri Bobby ya juya yana kallonshi idanu a waje yace"what do u mean?.."Nur yace"Ina nufin kilan ciki ne da ita mana..kai ina ka taba ganin anyi haka kawai matarka ba lafia kazo ka wani farayi mata blind treatment baka tunanin ko karuwa ka samu"..wani irin diff Bobby yayi yana bin Nur da kallo kmr bai gane abunda yace ba..tunani ya tafi yi tabbas tunda akayi bikinsu bata ta6a period ba and idan ba wai manta lissafin yayi ba bikinsu saura 2 weeks tayi period and idan akayi adding two weeks to that shine ovulation period dinta kuma a daidai wnn time din akayi bikinsu so there is 90% possibility na zata iya samun cikin within wnn kwanakin sbd time din ovulation dinta ne..nan take fuskanshi ya washe da wani irin murmushi yana sake wara idanu akan Nur hannunshi dafe da bakinshi cikin tsananin farin ciki da kuma mamaki yace"oh my Goddess..why didn't i think of this?.."harara Nur ya watsa mashi yace"oho banza"..sake juyawa yayi yana kallon Nur da kyau yace"Nur ina kyauta zaton wnn mgnr naka gaskia ne..she might be pregnant oh Allah"..ya karasa mgnr full of excitement kaman an tabbatar mishi tana dauke da cikin already..shi gaba daya tunaninshi baizo nan wurin ba all he was thinking was incident daya faru jiya har ya kulle mashi kai ya kasa zargin cewa cikin ne da ita.."ikon Allah"..ya sake fada out of excitement Nur dai na zaune yana kallon ikon Allah at the same time yana mishi daria..shi kanshi zai so ace yau Lamido tanada ciki ko dan yayi kallon uban rawan kan da Bobby zaiyi akan cikin...bude motar yayi ya fita shima Bobby ya fito da sauri ya kama hanyan cikin asibitin yana fadin"we need to conduct this test now..i pray it turn out to be truth"..Nur dake bin bayanshi ya amsa da"Ameen"..har suka shiga cikin building din..direct office dinshi suka shiga lokacin tana kokarin mikewa tsaye Bobby yayi saurin karasawa inda take yana kallonta full of love and excitement yace"baby where are u going?.."a hankali tace"ruwa zansha"..ruwan ya dauko da sauri ya kawo mata yana cewa"here u go"..ta saki dan murmushi snn ta amsa ruwan tasha cikeda mamakin sudden change din nan nashi?.. it's like ya gama saukowa completely..saida ta gama Shan ruwan snn ta lura da Nur dake zaune kan sofa yana kallonsu..ta danyi kasa da kanta tace"sir Ina yini"..yace"lafia ya jikinki?.."tace"naji sauki"..yace"to Alhamdulillah".. Bobby dai drawer ya bude ya dauko duk wani abu da zaiyi amfani dashi snn ya koma wurinta ya shiga lallabata wai zai dauki blood sample..itadai batace komai ba ya dauki sample din snn yaba messenger bayan ya rubuta test din da za'ayi a paper yace ya kai lab yace yana jiran result yanxun nan.

Ana kawo result din Bobby yayi saurin karba daga hannun messenger daya kawo har ya fara budewa sai kuma yayi saurin maidata yanda take tareda juyawa yana kallon Aysha da har yanxu ke zaune tana kallonsu..juyawa yayi suka hada ido da Nur sai kuma ya sake juyowa gareta ya sakar mata murmushi.. Lamido data kasa gane what they are up to kawai sai ta sauka daga gadon a hankali tana kallonshi ta nuna bathroom dinshi tace"zanyi alwala"..da sauri kmr jira yake yace"ok babe"..ta saki murmushi snn ta juya ta shiga bathroom din...tana shiga Bobby yayi saurin bude papern ya wara ido sosai yana karanta content din dake ciki idanunshi na sauka inda yaga an rubuta positive yayi saurin yar da papern tareda juyawa ya kankame Nur sosai kmr zai maidashi ciki..cikin so much excitement ya juya language zuwa Igbo yanda bazata fahimta ba yake cewa"Nur it's positive.. it's positive wlh.. Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah"..ya karasa mgn still yana rungume dashi kaman shine mai cikin..shima Nur farin ciki sosai ya taya abokin nashi dan haka yayi hugging nashi back tareda daka tsalle yana wani iri ihu shima da Igbo yace"ekele bro..ekele"(congratulations bro.. congratulations)..shima Bobby tsallen yayi exactly irin yanda Nur din yayi kawai sai Hamdala yake yama rasa inda zaisa kanshi sbd excitement..haka suka rungume juna suna ta faman tsalle a dakin kmr kananun yara..Aysha dake la6e bakin kofa tana kallonsu batasan lokacinda ta fashe da daria ba..yanda suka rungumi juna suna tsalle tsalle sai suka koma mata kaman small kids..wato dai su biyun nan are so something else..dama tunda taga yanda suke kallon kallon tasan kilan space sukeso ta basu and gashi nan ta gani saidai Allah kadai yasan dalilinda yasa suka wnn farin cikin because ba gane language da suke speaking take ba..daria takeyi sosai wanda rabonta da irinshi tun kafin faruwar incident din jiya...Saida suka gama tsalle tsallensu Nur yayi saurin daukan paper da Bobby ya yarda a kasa shima ya karanta..nan take ya wara ido yana sake duban abokin nashi da wani killer smile ya danyi kasa da voice dinshi yanda bazata jiyoshi ba yace"oh my Goodness yanxun five weeks knn da aurenku and the pregnancy is four weeks..what a sharp shooter"..ya karasa mgn yana kashe mashi ido shidai Bobby bai iya cewa komai ba tsabar farin ciki kawai sai ya durkusa ya fara sujood shukur shi kuma Nur ya kama kugu da hannunshi daya..dayan hannun kuma ya dafe forehead dinshi dashi snn ya danyi bending kaman zaiyi ruku'u ya shiga juya waits dinshi yana taka rawa a hankali yana cewa"aga m abu nna..aga m abu nna"..(am going to be a father..am going to be a father)..cikin excitement sosai yake rawa yana waka Kai kace shine za'ayi ma haihuwan..Bobby daya gama sujood dinshi tun daxu dagowa yayi kawai yana kallonshi with a very wide smile..yanda yake rawan ba karamin daria ya bashi ba..da dadewa dama yasan Nur yafi karfin aboki a wurinshi saidai ya kirashi da brother so ko kusa baiyi mamakin wnn farin cikin da yake tayashi ba..shi din mai sonshi ne kuma tsakani da Allah..ya tabbata wnn excitement da yake ciki da za'a bincika zuciarshi za'a ga har cikin ranshi yake tayashi farin cikin..he is one in billion..samun aboki irinshi yana da wahala sosai and shiyasa yake godia wa Allah for having him..soyayyan da suke ma juna genuine ne ba fake ba...Lamido dake bathroom tana kallonsu tayi daria kaman cikinta zai kulle..dukda batasan me sukema wnn farin cikin ba ta tabbata it's something huge don tunda take bata taba ganinsu cikin such excitement ba..Saida ta gama kallon snn tayi alwalan ta fito daga bathroom din kanta a kasa tana kokarin boye darian dake son sake kufce mata.. Nur daya dage yana dirkar rawa yana ganinta yayi saurin mazewa yana wani shafa kai shi a dole ba kamashi tayi ba...Bobby dake kokarin danne dariar dake cinshi juyawa yayi ya isa gareta kafin ta zauna kan bed ya janyota jikinshi kawai sai ya rungumeta so tight yana sauke numfashi..ta kwalo ido waje tana kokarin kwace kanta sbd presence na Nur amma sam yaki sassauta rikon da yayi mata balle ta samu daman kwacewa din..wani irin farin ciki ya tsinci kanshi a ciki.. right now gani yake dunia babu Wanda ya kaishi farin ciki kaman dai ba shine yake ganin babu wanda ya kaishi shiga kunchi da damuwa a while a go ba..wato Allah ba yanda bayayi da bayinshi a duk lokacin da yaso..idan yaso ya saukar Maka da farin ciki haka idan yaso ya saukar maka baqin ciki.. that's how life is shiyasa masu iya mgn sukace ba kullum ake kwana a gado ba and it's true..ba koda yaushe mutum ke dawwama cikin farin ciki ko akasin haka ba..dole watarana za'a jarrabaka da either happiness or sadness saidai Allah ya bamu ikon yadda da qaddara mai kyau da mara kyau...yayinda yake rungume da ita Nur sai ya zaro phone dinshi daga aljihu ya shiga camera ya fara musu video yanajin yanda shi kanshi suka burgeshi sai yaji inama shi da pretty ne haka..at this point sai yaji wani shaukin sonta ya kamashi..yaji inama a bashi ita ya aura koda bata gama secondary din ba amma yasan that can never be possible..Saida Bobby ya dauki lokaci mai tsaho yana rungume da ita yana kuma sake ma Allah godia cikin zuciarshi snn ya raba jikinshi da nata tareda hade goshinshi da nata ya lumshe ido yana sakejin wani extraordinary feeling yana sake bijiro mishi..he missed her like crazy sai kuma abun ya hadu da farin cikin samu karuwa tsakaninsu..he just can't thank Allah enough for such a blessing..hannu ya sake mikawa ya zagayo waist dinta dashi pulling her more closer to himself snn ya lumshe ido ya manna mata peck a goshinta followed by cheeks da tip of her nose..yana bude ido yaci karo da Nur da har zagayowa yayi ta saitin da faces dinsu zaifi fitowa sosai yana cigaba da recording video din yana sakin murmushi hadda su gyada kai..suna hada Ido yayi saurin saving video din ya wani kashe mashi ido daya yana cewa"ahuru m ihunanya"..(I see love)..murmushi Bobby ya saki tareda gyara mata hijab dinta snn yayi mata side hug yana kallon beautiful face dinta yace"i think we should go home now"..batayi musu ba ta gyada mishi kai alamar ok shi kuma ya sake pecking forehead dinta snn ya kama hannunta suka bar office din Nur na binsu a baya..sallamar driver dinshi yayi yace ya wuce da motar gida su kuma suka shiga motar Nur suka nufi gidan a cikinta..duk yanda Aysha taso ya zauna front seat kin yadda yayi wai saidai ya zauna kusada ita gashi kuma ya kasa dauke ido a kanta daidai da one second..gani yake kaman idan ya rufe idanun za'a tasheshi daga bacci ace dreaming yake..ita dai mamakin wnn sudden change din nashi take don batasan meya sauko dashi daga dokin zuciar da ya hau all of a sudden ba..amma koma menene she's happy tunda ta dalilinshi ya dena fushi da ita..sai satar kallonshi take tanajin yanda tayi missing dinshi itama..ba dan presence na Nur ba da babu abunda zai hanata mannewa a jikinshi kafin su karasa gida amma bazata iya ba sbd tanajin nauyinshi sosai..gashi kuma suna hada ido dashi sai yayi pecking forehead dinta dan haka tilas ta dena kallon nashi sbd batason wnn abubuwa da yake mata gaban provost wlh..idan shi yana ganin friend dinshi ita fa har yanxun tana mishi kallon gentle provost dinsu mai bala'in kirki da mutunta students dinshi.

Suna isa gida dama direct main house Nur ya shiga yayi parking snn ya bude kofa ya fita..shima Bobby fitowa yayi snn ya zagaya ya fito da ita sai wani hadata da jikinshi yake ita kuma tana kaucewa amma still bai bari bar har suka shiga gidan..Nur dai a baya yake binsu yana murmushi har yanxu kasa dena smiling sbd excitement..he is so happy for the both of them..suna zuwa daidai entrance Lamido ta dakata tareda zare hands din Bobby daga jikinta tana kallonshi da dan marairaicewa tace"partner just stop it mana..Mummy fa tana ciki"..murmushi ya saki tareda bending ya danyi pecking lips dinta snn ya kama hannunta ya rike yana kallon eyeballs dinta yace"is this ohk?.."girgiza mishi kai tayi da sauri tana kwabe fuska tace"Noo"..sai kuma ta shiga bubbuga kafa zata fara mishi kukan karya yayi saurin sakin hannun nata yana cewa"No no don't do that plss..gashi na saki hannun naki is that ok?.."kai ta gyada mashi tana sakin murmushi sai kuma ta shige cikin parlon..da kallo ya bita har ta 6ace ma ganinshi snn ya sauke wani ajiyar zucia mai karfi daidai lokacinda Nur ya karaso inda yake dan haka suka shiga ciki a tare..Lamido na shiga Miemie dake zaune dinning tana karatu tayi saurin mikewa tazo gareta tana wara idanu cikeda mamaki tace"Goodness!..aunty Aysha me yayi maki haka naga kin samu sauki?.."Bobby da yaji duk abunda ta fada ya dan watsa mata harara yana cewa"gidanku nayi mata"..da sauri ta kama bakinta tana yin kasa da kanta tace"ohh yi hakuri Uncle Bobby"..bai sake ce mata komai ba ya wuce flat din Mummy shi kuma Nur ya karaso nan cikin parlon ya zauna yana kallon Miemie da yakejin kmr ya maidata ciki yace mata"hey pretty"..kama hannun Aysha tayi suma suka karasa ciki suka zauna snn ta dawo da kallonta gareshi tana murmushi tace"Uncle Nur ina yini"..yace"fine pretty..ya exams?.."tace"Monday zamu fara"..yace"MaashaAllah..Allah bada sa'a..yasu aunty da Ilham?.."..tace"Ameen Ameen Uncle Nur nagode..su Aunty suna gidansu muma gobe zamuje ko aunty Aysha?.."ta karasa mgn referring to Lamido dake zaune tana sauraran conversation dinsu tana daria kasa kasa..da sauri tace"yeah indai naji sauki sosai gobe zamuje inshaAllah"..sai kuma ta mike tunawa da batayi sallah ba tace ma Miemie"rakani daki inyi sallah plss"..ba musu Miemie ta mike suka nufi dakinta dake nan cikin parlon don ta baro flat din aunty sumy tun baya barinta gidan..suna shiga Aysha tace mata ta koma kar su bar Nur shi kadai a parlor dan haka Miemie ta koma parlor yayinda ita kuma ta tayar da sallahrta..har yanxu kuma ba wani karfi takeji a jikin nata sosai ba.
















Rano✨


Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
66
Bobby na shiga ya iske Mummy a parlor suna waya da aunty sumy..bai damu ko ta gama wayan ko bata gama ba kawai yana zuwa ya zauna kusada ita tareda mata side hug ya kwantar da kanshi a shoulder dinta cikin so much farin ciki yace"nwunye m di ime Mummy"..(my wife is pregnant Mummy)..da sauri Mummy ta dago kanshi tana kallonshi cikin tsananin farin ciki tace"are u for real?.."da sauri yace"yes i am Mummy..she is four weeks pregnant"..wani irin zare idanu Mummy tayi cikin so much excitement kafin tace wani abu aunty sumy data gama sauraran duk abunda ya fada sbd call dinsu is still connected ta saki wani irin guda tana cewa"My Bobby is becoming a Father.. Alhamdulillah"..da sauri Bobby ya dauki wayan daga jikin Mummy ya manna ta kunnenshi yace"yes aunty am becoming a father..am becoming a father"..wani murmushi ta karasa saki before tace"congratulations qanina..Allah kawo mana babyn nan lafia and extend my regards to Aysha kace mata nace she should take care of our baby sosai"..ajiyar zucia ya sauke yana cewa"aunty ai har yanxu bata sani ba..i didn't tell her"..da sauri aunty sumy tace"why?.."yace"rigima zataimun ne..i have to wait for the right time..yanxun allow me to talk to my Mummy plss..my regards to Ilham..kice mata her Uncle Bobby yayi missing dinta da yawa"..yana gama fadin haka bai jira jin me zata ce ba yayi disconnecting call din don yasan aunty sumy da zance sake dauko wani dogon surutun zatayi..yana ajiye wayar Mummy dake kallonshi full of surprise tace"meyasa baka fada mata ba Bobby?.. what's the meaning of this?.."kama hannunta yayi yana dan marairaicewa yace"Mummy nasan halinta rigima zataimun wlh..kullum cewa take ita batason ta samu ciki da wuri and tunda Allah baisa ta gane ba we shouldn't tell her plss"..a hankali Mummy tace"amma kasan zata iya ganewa ko ba'a fada ba Bobby..she is a health worker too..zata iya noticing some changes a jikinta da zaisa ta fahimci ciki ne da ita"..yace"na sani Mummy amma we shouldn't tell her now..gwara mu bari har zuwa lokacinda zata fahimci tana dashi din da kanta maybe by then bazata dagamun hankali ba"..ajiyar zucia Mummy ta sauke sai Kuma ta rungumeshi cikin so much happiness tace"am so happy for u son..Allah ya basu lafia ita da abunda ke cikinta snn Allah ya sauketa lafia"..rungumeta back shima yayi yana wani lumshe ido sbd dadi yace"Ameen Ameen Mummyna..i can't love u less".

Da dare bayan sun dawo gida ya tilasta mata taci abinci snn ya bata paracetamol sbd fevern da yaji kaman zai dawo mata..suna zaune parlor suna kallo tanata faman cin apple daya yanyanka mata a plate daga ita sai dan sweet pants dinta blue da crop top baby pink..kanta da akayima kitso a bude sai daukan ido yake sbd kyan da yayi..yayinda ta maida hankali wajen cin apple dinta Bobby kuma yana zaune yana kallonta kmr yau ya fara ganinta..she looks do adorable right now..so looks cute that har baison ya dauke idanunshi daga kanta..kallonta kawai yake yana imagining yanxun da akwai da ko 'yarshi inside her tummy..banda smile ba abunda yake saki yana shafa saje zuwa gemunshi cikin so much happiness..kawai he's eager to see tummy dinta ya zama qato..he can't wait for the baby to come..he wants to hold the baby's hands snn yayi kissing forehead dinshi yace he loves him or her..he just can't wait for the baby's arrival..he's so desperate..yayi nisa sosai cikin tunaninshi sai sakin smile yake kuma har yanxun yana shafa beard dinshi kmr wani sabon kamu..kamar daga sama yaga ta mike da sauri ta kama hanyar bedroom dinta har tana hadawa da gudu sbd ringing din wayanta data jiyo..nan da nan ya dawo hayyacinshi tareda mikewa shima yabita da sauri yanajin wnn gudun da take har cikin zuciarshi wlh..yayi zaton wani gagarumin abun zatayi a dakin but to his biggest surprise yana shiga yaga ta dauki wayanta da bai dena ringing ba tayi saurin picking call din ganin Hammanta ke kira ta zauna gefen gado tareda Kara wayan a kunnenta tana wani cunno baki tace"ba ruwan ni dakai"..daga daya bangaren Hamman nata ya saki daria yana cewa"C'mon mana Maama..ba'a jin tsakanina dake fa?.."sake turo bakin tayi tace"ba wani Maama ni ka dena kirana Maama tunda baka damu dani ba"..jingina Bobby yayi jikin kofar dakin tareda rungume hannu yana kallon ikon Allah..yanxun Najeeb din takema wnn shagwaban sai kace muharraminta?..Najeeb dake dariar wnn rikicin nata yace"ohk wait kiji abunda zan fada maki..gobe zamuzo Kano"..batasan lokacin da ta saki wani irin ihu ba sbd farin ciki tace"dan Allah da gaske Hamma?.."yace"of course mana..tareda su Husna da Bilkisu"..nan take ta Kara sakin wani ihun tana cewa"Hamma amma dai kwana zakuyi koh?.."da sauri yace"Ammi tace banda kwana so a goben zamu dawo"..dan marairaicewa tayi kmr yana ganinta tace"haba mana plss..ya kamata ku kwana ai"..yace"idan kinaso su kwana saidai ki kira Ammi da kanki"..yana gama fadin haka tace"alright let me call her yanxu"..daga haka ta kashe kiran sai kuma ta shiga neman number Ammi zatayi dialing..a hankali Bobby ya karasa inda take ya wani daure fuska ya fizge wayar daga hannunta yace"are u mad?..bakida hankali zakizo kina gudu haka?..and waya fada maki ana yima cousin irin wnn shagwaban?.."murmushi ta saki tana kallon yanda ya hade girar sama dana kasa..batace dashi komai ba sai mikewa da tayi tareda matsawa inda yake ta shige jikinshi..a tare suka saki ajiyar zucia Bobby ya zagayeta da hands dinshi murya can kasa yace"how many times do i have to tell u this?..na fada maki cewa duk wani cousin dinki ba muharraminki bane amma bakiji..ko so kike na

Please Login or Register in order to submit comment