gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Dr.bob Complete Hausa Novel by by Aysha Rano Chapter 44 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk wanda yaga how he's talking yana lumshe ido zai gane da mace ne yake waya..kawai baqin cikin da yake na Kara mishi one month duk yayi disappearing sbd tunawa da wani abu da yayi..hakan kuma yasa yaketa sakin murmushi yana shafa kai kmr wani sabon kamu...Alhajia indo kuwa jikinta ba karamin sanyi yayi da wnn kalaman nashi ba..ta lura fa dama these days wani sabon iskanci yakeji dashi haka zaiyita 6aro mata mgn yana sata jin kunya shi kuma ko a jikinshi..ita bata ta6a sanin there is this side of him ba sai yanxu..duk ya wani dawo mai dabi'un 'yan iska shiyasa yake bata tsoro ma...jin yanda tayi dif kmr bata jinshi ya sake relaxing yana lumshe ido kafin yace"baby"..banza tayi mishi tana turo baki kmr yana gabanta..ya sake cewa"partner"..still taki tankashi kawai sai ya saki murmushi yana girgiza kai yace mata"duk wnn abun fa love wasa nake maki..ke bakisan wasa bane?.."murguda baki tayi tana sake dinke fuska tace"ba wani wasa..Allah idan kacigaba da tsokana na fasawa zanyi"..Bobby ya dan wara ido yana sake murmusawa yace"baby idan kika fasa kuma ai mutuwa zanyi"..tace"to ka dena tsokana na nidai"..tun kafin ta rufe baki yace"na bari..ban karawa believe me"..ajiyar zucia ta sauke kafin tace"shknn"..ajiyar zuciyar shima ya sauke tareda lumshe ido yana sake relaxing kan seat dinshi yace"I..love..you..and i can't wait to..marry you".

Bayan sati hudu...














Rano✨






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
53
Bayan sati hudu...
Yau Friday sukayi final laper dinsu and tun da suka fito daga exam hall around 11 kowa yaje ya sake shiri cikin sign out shirts da sukayi iri daya kowa nashi dauke da sunanshi a jiki..hall da suka saba gabatar da celebrations aka bude musu suka shiga nan sukaita celebrating kammala exams dinsu saura fitowa results kuma..har dj suka kira yaketa playing musu waqoqi iri iri masu rawa nayi masu daukan pictures ma sunayi...a extreme end of the hall Lamido zaune tana kallon su Billy daketa dirkan rawa kan stage da sunga wani da bai musu signing jikin shirts dinsu ba zasu bar rawan suje ayi musu signing din suma suyima wanda basuma ba snn su sake komawa dance floor..haka suketa yi tun daxun ita tana nan zaune tana kallonsu..kawai tunanin yanda zasu kwashe da Bobby takeyi idan yaga shirt dinta da signing musamman ma signing na namiji sai kuma rawa Kiri kiri da takeso tayi amma sbd tsoron kishi irin nashi ta kasayi..har sha'awan Billy da sauran colleagues dinta dake wurin takeyi sai taji inama ba'a college din nan yake ba itama da ba abunda zai hana mata enjoying wnn ranan amma yanxu bata isa ba...Billy ce ta nufo inda take zaune da sauri tana zuwa ta Mika mata wayanta dake hannunta tana cewa"Ur Hamma wants to speak to u"..ba musu Aysha ta karbi waya suka fara mgn dashi ita Kuma Billy ta dauki bottled water dake ajiye nan kusa da ita ta zauna tana sipping ruwan tana sauke numfashi...after like 4 mins suka gama mgn da Hamma Aysha ta shiga mikawa Billy wayanta kafin tace"Billy dan Allah zan danyi rawa ko kadan ne kinga fa ba zuwa zaiyi ba nasan yana hospital wlh"..girgiza kai Billy ta shigayi tace"aah fa ba ruwana Lamido bazaki hadani da wnn rigimammen mijin naki ba..haka nan kisa yazo yana tsareni da idon nan nashi da dadine dasu ba"..langa6ewa tayi tana kallonta kmr zata sa kuka tace"yanxu knn kinfi sonshi akaina Billy?..dan girman Allah in dan shiga inyi Allah ba dadewa zanyi ba"..girgiza Kai Billy ta sakeyi saidai kafin tace wani abu Aysha da ta riga tazo wuya sbd haushi tace"ko baki yadda ba sai nayi wlh saidai kije kiyita fada masa din i don't care"..daga haka ta mike zata bar wurin Billy ta dawo da ita da sauri tareda mikewa itama tana kallonta tace"amma banda signing kou?..kinsan fa halin mutumin nan Lamido banson kuxo kuna samun matsala akan haka"..kwace hannunta Aysha tayi ta bude bag dinta ta fito da wani shirt din sabuwa sak irin na jikinta tana nunawa Billy rigan tace"indai ba kece munafukar da zaki fada masa ba ba yanda za'ayi ya sani..ana gama min signing kafin mu fita hall din nan ma zan cire in saka wnn"..kallonta kawai Billy keyi ita wnn abun bai gamsheta ba..a yanda taga yake mgn jiya tasan wlh da kyar idan basu samu matsala kan haka ba tunda he made it clear cewar bayason wnn abun...ganin har ta kama hanyan dance floor ta daga shoulder alaman ba ruwanta snn itama ta bita a baya...tana hawa kan stage din sai kuma ta juya zata sauka da sauri colleagues dinta suka kamata suka maidata wurin..daya daga cikinsu taje ta samu dj tace mishi class rep dinsu ta shigo don haka ya samu Waqar favorite dinta mai azabar dadi yayi playing musu zasu cashe yanxun nan..dj kuwa ba musu ya sakar musu waqa mai dadi nan suka shiga rawa suna janta wai itama dole sai tayi..tun tana nokewa tanajin tsoro har dai daga baya ta saki jiki ta dilliqi rawar ta son ranta..at that moment gaba daya mantawa ma tayi da wani warning dinshi na jiya kan baiso tayi rawa and bai yadda wani ya taba rigarta da sunan signing ba..enjoying dinta takeyi kawai tana cashiya kmr ba Lamido ba...saida tayi me isarta snn ta fara zuwa ana mata signing jikin shirt dinta duk wanda ta gani da sauri take zuwa wurinshi yanayi mata zatayi sauri ta rufe wurin da kimono din jikinta wai duk sbd kada ya samu labari idan yazo...a takaice har after five suna cikin hall din nan suna abu daya..ganin yamma ya farayi hankalinta ya dawo jikinta tasan yanxu duk inda yake ya kusa shigowa college din don haka baki alekum ta fita daga cikin hall din zuwa wani dan small room dake kusada wurin ta shiga ciki da sauri ta zare kimono dinta tana kokarin cire sign out shirt din kawai taga mutum a gabanta..batasan sanda gabanta yayi wani irin yankewa ya fadi ba..lokaci daya ta saki rigar tana yarfa hannayenta hawaye har ya ciko eyes dinta tace"wayyo Allah na"..kala bai ce mata ba sai kimono daya dauka ya mika mata..da sauri ta kar6a ta maidata jikinta tana kallonshi..tana gamawa ya kama hannunta a fusace suka fita daga room din..direct office dinshi ya nufa da ita mutane nata kallon yanda ya riko hannunta amma kobi ta kansu baiyi ba don abunda ya dameshi kadai ma ya isheshi..yana bude office din ya turata ciki snn shima ya shiga ya maida kofar ya rufe ya shiga kallonta da eyes dinshi da sukayi jaa sbd bacin rai...kuka sosai ta fara tana yarfe hannayenta shi Kuma baice mata komai ba sai tsareta da yayi da eyes dinshi da taji sun dawo mata eyes dinshi data sani a baya masu sanya mata firgici da nutsuwa ba tareda ta shirya ba..da sauri ta matsa zuwa kusa dashi ta dan daga Kai tana kallonshi sbd yafita tsayi sosai kawai sai ya lumshe eyes dinshi don bazai iya juran kallonta a haka ba karyar mishi da zucia zatayi...ba zato ba tsammani kawai yajita fada jikinshi ta kankameshi tana sakin wani kukan da koshi yasan na shagwa6a ne kawai muryanta na rawa tace"am so..rry"..lumshe idanu ya sakeyi yana sauke ajiyar zucia..baisan ya zaiyi da rashin jin Aysha ba amma ko Allah yasan ba karamin wahalar dashi take ba..bude idanunshi yayi tareda dagota daga jikinshi ba tareda ya kalleta ba yakai hannu ya bude kimono dake jikinta nan take uban signings din dake jikin riganta suka bayyana..kallonsu kawai Bobby keyi ranshi na sake 6aci..duk Wanda yayi signing din nn yasan ya ta6a masa jikinta Kuma shidai Allah ya isanshi wlh..da iya class mates dinta ne ma da sauki tunda mata ne amma yasan baza'a rasa 'yan nursing a cikin Wanda sukayi mata signing din ba...runtse Ido yayi da karfi da yaga har wurin chest dinta saida akayi signing..ya juya bayanta nan ma yaga har waist dinta signing ne kaca kace kawai sai ya juya tareda zaunawa kan sofa yana date head dinshi da yaji kaman zai 6alle sbd ciwo..karasawa tayi ta zauna kusa dashi tareda dora kanta a shoulder dinshi tana hawaye sosai tace mishi"dan Allah kayi hakuri partner..zaka iya punishing dina da any kind of punishment amma don't be mad at me plss..am sorry"..hannunshi yakai a hankali yana shafa kanta sbd yanda kukan ke ta6a zuciarshi kwarai...sake langabewa tayi tana sauke numfashi..shi Kuma murya can kasa yace mata"you danced right?.."shiru tayi tana rarraba ido kmr munafuka shi Kuma ya saki murmushi mai ciwo dama ya tambaya ne wai ko hasashenshi zai zama ba gaskia ba amma shirun da tayi ya tabbatar mishi da cewa tayi rawa..zafi sosai yakeji cikin ranshi Wanda inda zai fito dashi ya nuna mata yanda yakeji kilan tsorata zatayi ta gudu shiyasa yake kokarin dannewa kawai..zuwa yanxu ya fuskanci zafi da takura babu abunda zai kara mata sai kangarewa so it's better ya fara binta da lallami da nasiha kilan Allah yasa ya dace..sake Kai hannayenta tayi ta zagaya bayanshi zuwa stomach dinshi dasu dukda ba gama zagayawa sukayi ba tace"partner am sorry please"..Kai kawai ya iya gyadawa yana shafa kanta a hankali yana karanta duk addu'an da yazo bakinshi..inshort sun duki lokaci mai tsaho a haka tana bashi hakuri kafin ya samu saukin abunda yakeji..Saida ya dan nustu snn ya shiga nata nasiha sosai Wanda har kusan kuka yasata sbd yanda yake mgnr shows ba karamin zafin abun da tayi yakeji ba..bata bar office din ba saida ta tabbata he is no longer upset with her snn yayi dropping nasu a hostel da kanshi bayan sun sha love dinsu.
Washegari da safe bayan sun gama 'yan koke kokensu na rabuwa da juna Hamma Najeeb yazo ya kwashesu dasu da komai nasu sai jihar Gombawa diban fari..ba'a kwana daku ba wai sai a tashi daku.
Wnn knn..

Kwananta biyu da komawa small mom dinta tazo ta dauketa suka wuce Bauchi wai za'a fara mata gyaran jiki and stuffs dai da akeyi na gyaran amarya..dukda Ammi bataso haka ba sbd zaman Fiddausi da Aysha a cewarta ba abunda yake karawa sai lalata Ayshan sbd ba wani fada take iya mata ba..amma da daddy yasa baki haka nan ta hakura suka tafi Bauchin bada son ranta ba..ita fa so tayi a dan zaman nn da zatayi ta gyara mata zama sosai ta yanda bazata je gidan miji tana basu kunya ba don tasan halin kayarta tsaf har yanxu ba cikakken hankali ne da ita ba.
Tunda ranan da suka isa Bauchi ko kofar gida bata sake fitowa ba wai idan ana gyara ba'a son shiga rana...mai gyaran jiki sosai auntyn nata ta dauko takanas take gyara mata ita ciki da waje don komai daya danganci gyaran amarya ana mata and ita da kanta ta fara ji da kuma ganin canji a jikinta..biki ya rage saura 3 weeks Billy ta dawo gidan aunty Fiddausi da zama sbd shirye shiryen biki da suka fara ka'in da na'in...events sosai Billy suke shiryawa ita da Provost don sune Organizers na komai da zasuyi a bikin..dama Kuma halinsu ya kusa zuwa daya dan haka suketa planning events kala kala hadda na shirme dan kusan week guda za'a kwashe ana bikin..ko Lamido da take mayyar biki Saida tace ma Billy events din sunyi yawa da taga uban abubuwan da suka rubuta za'ayi amma sai Billy tace mata babu ruwanta nata kawai zuwa ne amma ko event guda baza suyi cancelling ba.

Shirye shirye sosai akeyi ta kowane 6angare..baga ahalin Lamido da Waziri ba..ba Kuma ga ahalin hajia Mummy da aunty Sumayya ba...bride and groom dai nasu Ido ne kawai almost komai na bikin shirya musu akeyi so nasu kawai suyi attending ne..lokacinda aunty sumy ta fada mishi events da zasuyi cewa yayi a rage that shi bayason big wedding wai gajia zaiyi ma da attending events din..amma aunty sumy tace ko event daya bazasuyi cancelling ba idan yaga dama kar yazo su zasuyi abunsu tareda amarya...murmushi kawai ya iya sakar mata ya wuce flat dinshi yana dialing number amaryarshi da rabonshi da sanyata a ido tun ranar da tabar Kano..kiri kiri yanason zuwa ya ganta yarinyar nan ta hanashi wani wai aunty Fiddausi bazata bari ba which he knows she's lying of course..kawai shima sai ya rabu da ita cikin ranshi yace zaiyi maganinta ne idan ta shigo hannunshi..ganin har Kiran ta katse bata dauka ba ya ajiye wayar ya shiga wanka don dawowarshi knn daga clinic.

Aunty Fiddausi ta shigo dakin da take kwance hannunta rikeda bottled water mai sanyi sai sachet na inflanil a hannunta ta karaso ciki ta zauna gefen Aysha dake kudundune cikin bargo tace"oya mike ki samu Kisha maganin nn yanxu zaki samu sauki inshaAllah"..dan bude Ido Aysha tayi tana ganin magani a hannunta ta wani yatsine fuska tana marairaicewa tace"aunty dan Allah kiyi hakuri da kanshi zai dena wlh"..a fusace aunty Fiddausi tace"kinsan Allah zan kira Adda in fada mata wnn iskancin da kikeyi..Shan magani kawai ya gagareki kuma don walakanci har likita na kira tazo ta dubaki kememe kina hana ta maki allura yanxu maganin ma Kuma bazaki Sha ba sbd kin maidani yar iska"..sake marairaicewa tayi tana duban small mom din tata tace"aunty na rantse da Allah idan nasha bakina sai yayi sati yanamin daci..shi Kuma allura fa kinsan dai yanda yakemun ba saina fada maki ba"..a fusace aunty Fiddausi ta ajiye drug da ruwa dake hannunta tace"sai kiyita zama da ciwonki har bikin naki yazo ni ba ruwana"..daga haka ta mike tayi ficewarta daga dakin..a waje suka kusa karo da Billy zata Kai mata tea tasha..ganin yanda ta fito rai a 6ace Billy tace"bata Sha maganinba Koh?.."aunty Fiddausi tace"inafa tasha..yarinya dai shege taurin kai kmr mutanen farko"..girgiza kai Billy tayi tace"bari in kai mata tea din nan inzo aunty nasan wanda ko bataso zai iya mata allura"..daga haka ta wuce dakin ta dire mata tea din gabanta ko kallonta batayi ba ta juya ta fita Aysha ta bita da harara kmr Idonta zasu Fadi kasa..kawai batada lafia ma bazasu daga mata kafa ba kowa sai yayita nata masifa kmr an gaji da ita...Billy na fita ta iske aunty Fiddausi zaune a parlor samun wuri tayi itama ta zauna snn ta dauko wayanta tana searching contact dinshi tace"aunty proprietor ne kadai zai iya mata allura komai isakancin da zatayi"..kallonta aunty Fiddausi tayi kafin tace"sai Kuma mu tasoshi tun daga Kano sbd yazo ya mata allura Bilkisu"..Billy tace"zaizo wlh aunty shima nasan da kyar idan ba son ganinta yake ba yanxu..rabonshi da ita fa tun da mukayi graduation"..ajiyar zucia aunty Fiddausi ta sauke tana cewa"to kirashi ki fada mishi yazo yasan yanda zaiyi da ita nidai..dan wlh idan ta kaini bango ubanta zanci babu ruwana da ita amarya ce tunda batada mutunci"..Billy na murmushi tayi dialing number dinshi tana fadin"bama za'a Kai ga hakaba zaizo yayi maganin kayarshi"..yana daukan waya bayan ta gaisheshi tace mishi aunty Fiddausi tace idan zai iya zuwa Bauchi yazo ya duba musu ita batada lafia as usual Kuma taki yadda ayi mata allura snn taki tasha magani..Bobby da yaji abun kmr gaba ta kaishi nan take yace zai taho yanxun nn don shima son ganinta yakeyi musamman yanxu da akace batada lafia yasan ko yace sai gobe ma ba iya baccin kirki zaiyi ba so gwara ya taho yanxun..suna gama waya ta sanar da aunty Fiddausi yanda sukayi dashi dan haka tasa aka fara shirya mishi abinci kala kala yayinda hajia Ai ke kwance daki tana bacci bata ma San abunda ke faruwa ba.
Bobby na gama waya da Billy ya shirya kanshi sharp sharp ya dauki duk wani abu da yasan zai bukata tareda key din mota ya fita ka tsaye ya shiga flat din Mummy ya mata sallama kan zaije Bauchi wai Aysha batada lafia..Mummy batayi yunkurin hanashi ba ta bishi da addu'an dawowa lafia don tasan yanda duk ya rikice din nn idan ma ba'a barshi ya tafi ba hankalinshi ba kwanciya zaiyi ba...yana fita ya fada mota direct ya wuce gidan su Nur haka ya azalzaleshi ya shirya sharp sharp snn suka shiga motanshi suka kama hanyan Bauchi..Nur sai mita yake mishi wai daga dawowa gida ko hutawa bai barshi yayi ba yazo ya wani jajibeshi zuwa Bauchi sbd rashin hakuri ba yanda baiyi dashi akan ya bari sai gobe ba amma ya dage sai yau sai kace dai a kanshi aka fara soyayya.

Karfe hudu da wani abu suka shigo cikin Bauchi..driver aunty Fiddausi ta tura ya taho dasu daga inda suke har zuwa gidanta..shi ya fara shiga ciki kafin suma su shiga da nasu motan..parking Bobby ya karasa ciki yayi yayinda driver daya rakosu ta shiga cikin gidan ya sanar da aunty Fiddausi karasowarsu..Jim kadan ya dawo yace musu tace su shiga ciki..basuyi musu ba suka fita daga mota dukabi bayanshi har zuwa cikin gidan..a main parlor suka zauna shi Kuma driver ya fita..bayan few minutes Billy ta shigo parlon rikeda tray din su juice a hannunta..ta karaso ciki ta ajiye tray akan table snn ta zauna kan one seater tana dan sunkuyar da kanta tace"barkanku da zuwa"..Nur ya fara cewa"barka Bilkisu..ya jikin Lamidon?.."tace"da sauki sosai"..juyawa tayi tana kallon Bobby ya sakar mata murmushi..murmushin itama ta saki snn ta shiga gaishesu..bayan sun gaisa ta mike ta bar parlon can sai gata ta sake dawowa da wasu dirka dirkan warmers ta ajiye snn ta sake komawa ta kawo wasu ta kuma ajiyewa snn ta wuce don kiran aunty Fiddausi..tare suka dawo da ita parlon ta karaso ciki ta zauna opposite to them tana dubansu da murmushi sosai fuskanta tace"sannunku da hanya"..durkusawa sukayi har kasa suka gaisheta dukda ko zata girmesu ba irin sosai din nan ba..aunty Fiddausi ta amsa gaisuwarsu tana murmushi bayan sun zauna tace"ku fara cin abinci sai raka ku inda take..bacci ma takeyi don batasan da zuwanku ba"..tana rufe baki Bobby da ya matsu ya sanyata Idonshi yace"am..ni bana tareda yunwa aunty"..dan murmushi aunty Fiddausi ta saki kafin tace ma Billy"ki rakashi dakinda take"..ba musu Billy ta amsa da toh ta juya ta kama hanyar dakin Bobby yabi bayanta yayinda oga Nuruddeen ya baje ya shiga bama cikinshi haqqinshi don a cewarshi soyayyar Bobby bazai hanashi cin abinci ba shikam...Billy na nuna mashi dakin ta juya ta bar wurin yayinda shi Kuma ya tura kofar dakin a hankali ya shiga da sallama...wani irin sanyi dakin ya dauka sosai sbd ac dake kure ita Kuma tana kwance can karshen gado ta kudundune kanta cikin blanket tana bacci peacefully kmr ba mara lafia ba..a hankali ta shiga takawa har zuwa bakin gadon ya tsaya yana kallon yanda tayi coiling kanta a kan gadon kmr ba mutum ba..stool ya janyo ya zauna dab da gadon yana facing dinta kafin yakai hannunshi a hankali ya janye blanket din..da uban gashin kanta dake tsefe ya fara cin karo sai kuma cute and beautiful face dinta da yaga har wani glowing yakeyi a Idonshi..baisan ko sbd ya jima bai ganta bane amma yaga ta Kara kyau sosai ba kadan ba...janye blanket din yayi daidai stomach dinta sai yaga tayi motsi tareda jan blanket din zata sake rufewa dashi yayi saurin janyeshi tareda daukan remote ya kashe air condition din dakin gaba daya...kallonta yacigaba dayi yanajin wani abu mai matukar karfi yana kokarin fizgarshi zuwa gareta baisan lokacinda ya lumshe ido tareda sunkuyawa yayi pecking forehead dinta ba..hannunta ya kama ya rike yana cigaba da kallonta kmr Wanda keson gano wani abun..left hand dinshi da yake free ya mika yayi feeling temperature dinta yaji jikinta normal babu wani zafi kawai sai ya saki wani hadadden murmushi yana shafa gemu zuwa sajen fuskanshi Kuma still hannunshi na cikin nata..a hankali ta fara motsawa sbd zafi data faraji as a result of kashe ac da yayi..lokaci daya Kuma ta bude Idonta tar tana kallonshi shima sai ya tsayar da nashi idon a kanta yana kallonta...mikewa tayi zaune da sauri tana Mirza idonta to make sure ba dreaming take ba Kuma sai taga its real ba mafarki bane..wara idon tayi da kyau tana kallonshi kallo irin na mamaki kafin tace wani abu ya rigata da fadin"ya jikinki?.."hadiye yawu tayi da sauri tana gyada kanta tace"naji..sauqi..amma ya akayi kazo nan?.."murmushi ya saki yana kallonta yace"kirana sukayi wai bakida lafia kuma kinqi yadda ayi allura and kinqi shan magani"..turo baki tayi tana hade rai lokaci guda tace"to nidai bazaka mun allura ba wlh"..murmushi yakeyi har yanxu yace"baby bakida lafia fa?.."rau rau tayi da Ido kmr zata fara kuka tace"Allah kamun allura fasawa zanyi"..daria ta bashi sosai jin abunda ta fada..ya fuskanci these days rigima takeji dashi dan abu kadan zata ce mishi fasawa zatayi..Saida ya gaji da dariarshi kafin yaja dogon hancinta yana cigaba smiling yace"da yake fasawan a hannunki yake Koh?.."turo baki tayi tace"nidai kada kamin allura dan Allah"..gyada mata kai yayi alamar bazaiyi ba..dan kura mata ido yayi for like 3 mins sai Kuma ya saki murmushi yana kallon eyeballs dinta yace"meke damunki?.."a hankali tace"fever"..tun kafin ta rufe baki ya shiga girgiza kai yana cigaba da kallonta yace"ba fever ba dai..ki fadi gaskia"..daure fuska tayi tana harare harare tace"nidai fever ne ke damuna"..shiru yayi yana kallonta kawai sai ya girgiza kai..Aysha da gaba daya ta gama tsarguwa da wnn abun nashi tace"and what does that mean?.."shoulder ya daga mata alamar nothing..da sauri tace"ban yadda ba wlh..da akwai wani abu cikin ranka"..girgiza mata kai yayi alamar ba komai ita kuma ta wani hade rai zata kwanta baisan lokacinda ya janyota jikinshi yana danne dariarshi ba..murya can kasa yace"kawai ki fadamun period kike ba sai kina wani 6oye 6oye ba mana..am ur soon to be husband"..tun kafin ya rufe baki ta daddage ta tureshi daga jikinta ta sake juyawa zata kwanta yayi saurin dawo da ita jikinshi yana cigaba da dariarshi yace"nifa bada wani abu na fada ba..am sorry"..banza tayi dashi ta shiga kokarin kwace kanta..ya dagota tareda cupping fuskanta still yana murmushi yace"bafa laifi kukayi ba ni kyautamun ma kukayi keda period din naki da kukeyin abunku tun yanxu ba sai..."bata bari ya karasa ba ta toshe mishi bakin da hannu daya tana dukan chest dinshi da dayan hannun tace"banaso..banasoo"..sake rungumeta yayi yana sakin daria sosai yace"to kuyi hakuri na dena"..sake dukan chest din nashi tayi yace"to kiyi hakuri love..am sorry ba period kike ba"..daga haka ya dagota daga jikin nahi yana kallonta da kyau yace"yanxu kici abinci sai muyi allura"..girgiza kai ta shigayi tana cewa"No pls"..da sauri yace"ohk to ki samu kici wani abu sai kisha magani"..gyada mishi Kai tayi alamar toh..shi Kuma ya mike daga inda yake zaune ya mika mata hannunshi yace"tashi muje parlor kici abinci"..girgiza kai ta sakeyi tace"rigana baida tsayi kaje zan fito"..yace"U sure?.."Kai ta gyada mishi meaning she's sure..bai sake cewa komai ba ya fita daga dakin ita Kuma ta mike da kyar ta janyo hijab ta zura snn ta shiga takawa a hankali ta fita zuwa parlon..itadai tsoronta Allah tsoronta kada yace zaiyi mata allura dan bataso wlh..haka kawai salon azo bikinta allura nayi mata ciwo.

















Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
54
Biki ya rage sati daya Aunty Fiddausi ta tattara su gaba daya suka wuce Gombe sbd preparation na biki da zata taya yayarta...zuwa lokacin sosai amarya Aysha ta canxa tayi wani 6ul 6ul da ita kaman ba amarya ba don ba wani stress na biki data daurama kanta..duk wani abu daya kamata ayi Billy ce takeyi tareda sauran cousins dinta sai kuma Aunty Fiddausi...sbd cika fa gidansu ya farayi da mutane na nesa da suka fara zuwa Ammi tace ita da Billy suje can gidan wani small uncle dinta da bai dade da aure ba su zauna tareda sauran friends dinsu da zasuzo idan an fara biki...haka kuwa akayi suka tattara duk wani abu da sukasan zasuyi amfani dashi har a kammala biki suka wuce can gidan uncle din nata dake few houses away from nasu gidan...sun rage yawan events da suka tsara zasuyi sbd Lamido ne yace lallai lallai duk yawan events dinsu

Please Login or Register in order to submit comment