You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
hannu da ya kai ya sake janyota jikinshi gaba daya hankalinshi naga driving da yakeyi yace mata"relax"..tun bai rufe baki ta zame jikinta da sauri tareda komawa seat dinta ta zauna tana dubanshi kmr zata fashe da kuka tace"yanxu partner meye haka plss..me kakeso su Mummy suce..nidai take me back plss i beg u"..banza yayi mata baice komai ba don a halinda yake ciki gani yake mgnr ma 6ata mashi lokaci zaiyi..ita kuma ganin yanda yake sharara uban gudu ko a jikinshi kawai saita rufe fuska ta wani rushe da kuka kmr wanda akama dan banzan duka..daria ya saki sosai yana cigaba da driving dinshi don wlh ko me zatayi bazai hanashi abunda yayi niyya ba..haka nan mutum daga yin aurenshi an wani kawoshi nan an rabashi da amaryarshi ai kome ya aikata ma bai kamata aga laifinsa ba kmr yanda bai kamata a rabashi da amaryarshi ba at the first place..nearby hotel ya shiga yayi parking snn ya bude motar ya fito da ita tanata zabga ihu kmr karamar yarinya baice mata qala ba ya sunkuya zai dauketa tayi saurin matsawa baya tana kallonshi..sake matsawa yayi kusada ita ya janyota jikinshi murya kasa kasa yace"idan baki rufemun baki ba daukanki zanyi gaba daya wlh..kuma kinsan zan iya"..daga haka ya sake kama hannunta suka nufi cikin hotel din..daki yayi booking snn ya sake kama hannun nata suka nufi dakin..Saida ya family a tilasta mata cin abincin sa ya siyo snn ya sake janta jikinshi..duk wani kuka da kokawarta bai hanashi holewarshi ba har saida tayi dana sanin kissing dinshi don a ganinta shine ya janyo mata wnn abun kunya..kmr kullum yau ma har komai ya kammala bata dena kuka ba saidai wnn karon kukan na kunya da kuma tunanin yanda zata hada ido dasu Mummy ne don gani takeyi da kyar idan basu fahimci abunda ya faru ba..ita batasan wane irin mutum ne shi ba wlh..gaba daya baisan wani abu mai suna kunya ba..daukanta yayi da kanshi zuwa bathroom yayi wanka itama yayi mata da kanshi duk wani noke nokenta bai saurara ba saida ya gama snn ya sake daukota suka dawo dakin..shiryawa yayi itama ya shiryata snn ya sake janta suka kwanta wai bacci yakeji aikam data daddage ta kurma masa wani ihu ba shiri ya mike ya dauki car keys dinshi suka fita daga dakin..yana gama settling bills dinshi suka fita Lamido sai wani hade rai takeyi ita bata yadda ba ya 6ata mata rai shi kuma sai kunshe daria yake..har suka koma gida bata ce mishi komai ba yana gama parking ta bude motar ta fita kmr zata tashi sama shima budewa yayi ya fita yana sakin murmushi shi kanshi sai yanxu ya fara tunanin amsar da zai ba Mummy idan ta tambayi dalilin dadewarsu amma da Mummyn nashi ta musamman ce sai bata tambayi dalilin dadewan nasu ba saima shiri daya samu sunayi don tafia wajen biki..shima baiyi wasting time ba ya shiga daki don shiryawa..lokacinda ya fito itama ta gama shiryawa ta fito kuma yana sauke idanu kanta yaji wani abu ya taso tun daga brain dinshi har zuwa foots dinshi..hankalinshi yaji ya tashi ba dai a haka take tunanin zata fita ba?..anya kuwa tana ma da hankali yarinyar nan?..tana matar auren zatace zata fita da wnn veil din da shi a ganinshi dashi da babu duk daya..har sun kama hanya zasu fita itada Miemie yayi saurin kallon Mummy yace"Mummy kiyi mata mgn plss..ya zata fita a haka"..juyawa Mummy tayi ta kalleta snn ta dawo da kallon gareshi tace"ban ganeba"..yace"Mummy look at her mana da wnn dan mayafin zata fita"..tsaki Mummy ta saki ba tareda tace komai ba itama ta fita daga parlon..aunty sumy data fito yanxu tana ganinshi a tsaye tace"what again?.."da sauri yace"Mummy ce wlh..kawai ta bar yarinyar nan ta fita da wani dan karamin veil a jikinta..nasan kowa kallonta zai dinga yi wlh dan Allah kiyi mata mgn"..daria ta saki tana kama hannunshi tace"yanxu dai ka wuce mu tafi tun Mummy bata farajin haushinmu ba"..bai sake cewa komai ba ya bita suka fita amma shidai Allah ya gani ba haka yakeso ba..sam baiso ta fita a haka ba sbd yanda tayi kyau koshi da yake mijinta kasa dauke Idonshi yayi a kanta balle kuma wasu da ta6a ganinta ba kilan sai yau..duk ranshi yabi ya 6aci all of a sudden sai wani cin kunu yake yana daure fuska kmr wanda akama wani laifin.
Har suka dawo daga wajen bikin nan ranshi a 6ace yake don gani yake kowa ma ya gama kalle masa ita yau din nan..itama da yake haushin abunda yayi mata daxun takeji sai batabi takan fushin da yake ba tacigaba da harkokin gabanta..the next day ma haka suka yini a wajen biki sai dare suka dawo gida daga nan kuma suka shiga zagaya wa gidajen yan uwan Mummy duk tana introducing Aysha wa Family dinta wanda basuje biki ba cewa itace matar Bobby..sosai suka samu tarba mai kyau daga yan uwan nata kowa sai nan nan yakeyi dasu kmr a maidasu ciki..Lamido taga kara iya kara a wajensu abun har mamaki ya bata yanda sukeda son yan uwa haka..sunada zumunchi sosai ba kadan ba sai yanxu taga inda Mummy ta dauko zumunchi don yan uwanta kaf zumunchi garesu da kuma son nasu..bayan sun gama ziyara sai suka shiga yawo da ita cikin garin suna nuna mata wurare da dama a matsayinta na wadda bata ta6a zuwa ba aikam tayi kallo iya kallo ta kuma ji dadin zuwanta garin don taci karo da abubuwa da dama wanda suka burgeta..shi kanshi yanayin tsarin garin ba karamin kyau yayi mata ba don da gani take duk states din nan na kudu idan aka dauke Lagos ba wani kyau na kuzo ku gani ne dasu ba amma yanxu tasan she was wrong don Enugu dai kam tanada kyau iya kyau saidai batasan ko iya wurare masu kyawun taje ba..yanda ta ware take harkanta a cikinsu abun har mamaki ya bata don yanxu ta rage jin kunyansu sosai tana kuma iya sakewa cikinsu ayi labari yanda ya kamata tunda ita din dama gwanar surutu ce..tsakaninta da mijinta ma sai abunda yayi gaba don soyayya ne ake zubashi yanda ya kamata..tun tanajin kunya idan yayi mata wani abun gabansu Mummy har tazo ta fara sabawa don ta fuskanci shifa haka yake kuma ba iya denawa zaiyi ba.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
63
Ana gobe zasu tafi Aysha zaune parlor tareda bobbyda aunty sumy dake bata labarin yanda ya shiga damuwa sbd ita kafin ta fara sonshi ita kuma banda daria ba abunda takeyi tana kallonshi..shidai yana zaune yana jinsu jira kawai ta wuce gona da iri ya taka mata burki don bazai yadda ta 6arar masa da mutunci ba..aunty sumy na kwaikwayon muryanshi tace"Ina fada maki da farko idan akace yana sonki har wani masifa yakeyi yana denying cewa shi ba sonki yake ba amma daga baya har zuwa yake yasa Mummy a gaba yana mata kuka yana cewa mutuwa zanyi..indai ban aureta ba Mummy mutuwa zanyi for sure..Mummy kuma sai ta daga hankali tayita lallashi tana bashi bakin cewa ai watarana zaki soshi"..aunty sumy ta karasa mgn tana kallonshi tana cigaba da daria..Lamido ma daria takeyi iya karfinta tana kuma mamakin wai shine yake kuka akanta kmr dai bashine wnn mutumin daya takurawa rayuwarta ba..da sauri ta juya tana kallonshi da murmushi tace"do u really cry because of me partner?..i can't believe this?.."daure fuska yayi ya mike yana wani cin magani shi bai yadda ba kar a rainashi yace mata"hiran ya isa haka tashi mu tafi"..dan langabewa tayi still tana danne daria tace"please mana"..kamata yayi ya mikar da ita tsaye ya sake cewa"let's go"..kmr zatasa kuka tace"to where?.."yace"to my friends house"..aunty sumy tace"yaushe kakeda aboki a Enugu bamuda labari"..yace"gidan Mi'iraj zamuje"..gyada kai aunty sumy tayi tace"kaidai kawai bakason matarka tasan how much u love her"..tana rufe baki yace"ai ko yanxun tasan Ina sonta sosai..baby ai kinsan dai inasonki da yawa Koh?.."girgiza kai tayi tana makale shoulder dinta tace"nidai ban saniba"..wara ido yayi yana kallonta sai kuma ya shiga janta yana daria yace"to bazaki sani ba..now ki wuce muje idan ba so kike in daukeki da kaina ba"..juyawa tayi tana kallon aunty sumy kmr zatasa kuka tace"aunty kiyi mishi mgn plss"..aunty sumy na murmushi tace"karki damu idan kun dawo zamu cigaba daga inda tsaya"..da sauri ta saki wani murmushi tana cewa"yauwa aunty godia nake"..shi kuma ya juya yana kallonta ya saki wani murmushi yace"idan kika cigaba nima zuwa zanyi in samu saurayin Miemie in bashi labarin duk abubuwan da kikeyi ince masa to yayi a hankali 'yar gidan yarinya zai aura"..ai tun kafin ya karasa ta jefo mashi throw pillow dake kusada ita tana daria tace"sai nayi maganinka wlh..dan rainin hankali"..daria sosai shima ya saki tareda kama hannun matarshi suka fita daga gidan.. already dama Mummy ta fita tun safe tare dasu Miemie so su kadai suka rage a ciki.
Tunda suka shiga mota take juyawa tana kallonshi akai akai tana sakin murmushinda ya kasa tantance na menene..ganin yanda take kallonshi sai shima ya dan juya ya kalleta for like 2 secs snn ya dauke kanshi yanacigaba da driving..Lamido da ta matsu taji karshen labarin nan tace"dan Allah da gaske partner ka ta6a yin kuka sbd ni?.."kai ya gyada mata ba tareda kallon inda take ba yace"of course..ba sau daya ba ba sai biyu ba"..yana rufe baki tayi wani irin zaro ido kmr wanda taji abun tsoro hadda su rufe baki da hannunta cikin so much excitement tace"ikon Allah..i can't believe this"..juyowa yayi ya kalleta kafin ya maida kanshi ga titi yace"u have to believe..ba karamin wahala nasha kanki ba"..sake gyara zama tayi tana facing dinshi tace"tell me more plss..i want to know"..murmushi ya saki tareda gangarawa gefen titi yayi parking snn ya juyo yana kallonta..kallonshi itama takeyi with a smile don da gaske abun really get to her jin cewa mijinta har kuka yayi sbd ita..it's kind of romantic..kamo hannayenta yayi ya rike yana kallon cikin idanunta babu alamar wasa tattare dashi yace"i have suffered alot..na wahala sosai..duk wani taurin kai da zafi irin nawa saida na nemesu na rasa because of u..at first nayi tunanin tsanarki nayi sai daga baya na gane it was not hatred but love..duk wnn abubuwan that i have been doing to u inayinsu ne with the out of pain and anger..gani nake kmr zuciata batamun adalci data bari na fara sonki ba..wnn dalilin yasa koda yaushe nake maki masifa duk a kokarina na ganin nayi denying the fact that ina sonki amma the love was very powerful..it was more powerful than my heart shiyasa all my effort go in vain sbd na kasa cireki a raina"..dakatawa yayi yana kallonta eyes dinshi har wani ja sukayi sbd tunawa da mawuyacin halin daya shiga a wancan lokacin..itama kallonshi takeyi ko kifta ido batayi sbd yanda takeso lallai taji karshen wnn labarin nashi..ta lura har yanxun abun na ta6ashi don gashi nan ta gani a idanunshi..bata ta6a sanin ya wahala haka a kanta ba..hannunta ya saki tareda kai hannu ya kara karfin ac sbd zafi da yaji yanaji from no where snn ya dawo da idanunshi gareta kafin yacigaba"a lokacin Allah kadai yasan yanda nakeji idan na ganki da wani..ji nake tamkar zuciata zata tarwatse ta dalilin abunda nakeji..wnn dalilin yasa zakiga duk wani abu da zakiyi idona yana kanki musamman daya kasance kedin fitinanniya ce bakijin mgn"..tun kafin ya rufe baki takai mishi duka a chest dinshi tana wani narkewa tace"nine fitinanniya koh?.."janyota yayi jikinshi yana shafa bayanta yace"eh mana..kin bani wahala sosai amma yanxu duk ya wuce tunda na aureki"..dagowa tayi tana kallonshi da murmushi tace"ni kuma da gaske a lokacin na tsaneka..ko ganinka banason yi sbd masifan nan naka kuma tsoronka fa nakeji sosai nunawa ne kawai banayi"..murmushi shima yakeyi yace"na sani wlh..nasan maybe duk dunia ba wanda kika tsana irina a lokacin sbd takurawan da nake maki"..kanta ta gyada tareda kama hannayenshi tana dubanshi sosai tace"sosai ma kuwa..kawai gani nake u are against my happiness but i was wrong"..tsura mata ido yayi yana kallonta for some minutes kafin yace"kinsan tun yaushe nasan ina sonki?.."girgiza kai tayi da sauri alamar bata sani ba..yace"ranan wata Monday 11th of July around 8:15 am"..shiru tayi tana kallonshi ido a wajen jin har su date da time ya rike na tsahon wnn lokacin..kallon yanda ta bude idon yayi sai ya saki murmushi bayan yayi pecking dinsu yace mata"yes ranan da kuka fara clinic posting dinku na first semester year two..ranan kunzo zakuyi reporting a Freedom kawai naga kinshiga motar wnn tsohon mutumin"..kamo hannunta yayi ya rike sosai yace"wlh Aysha kasa fitowa daga cikin motata nayi..i was just sitting inside looking at direction na motar nashi inajin kaman inzo in fito dake daga ciki..yanda naji zuciata ta buga a wnn lokacin na tabbatar da cewa am in love amma naki admitting..kuma fa nike Shan wahala ba wani ba amma still naki amincewa sonki nake..ban kara shiga damuwa ba sai ranan da daddy da bakinshi yace ya bani amanarki..tun daga wnn lokacin abubuwa suka fara kwa6emun amma still ban yadda ina sonki bafa"..ya karasa mgn da murmushi a fuskanshi dan shi kanshi sai yanxu yake ganin wautan da yayi a wancan lokacin..Kiri kiri wai yana feeling abu kuma yana denying sbd wani dalili nashi mara tushe..rungumeshi sosai Aysha tayi tana tunawa da yanda yayita cin zalinta a wancan lokacin kuma wai duk a snn ma yana sonta...murmushi ya saki har yanxu tana rikeda hannunta yace"and kinsan the funny part of all these?.."girgiza mishi kai tayi alamar no..yace"farkon tsanar da nayi maki sbd kin kasance Fulani ne Kuma from Gombe..a wancan lokacin na tsani yan Gombe sosai especially Fulani sbd wani abu daya ta6a shiga tsakaninmu da su waziri..amma when i met u..komai ya lalace kmr dama turoki akayi don kizo ki rusa wnn hatred dake tsakanina da Fulani dama Gombe gaba daya..daga lokacin dana fara sonki da yawa daga halayena canxa ba tareda ni kaina nasan lokacinda suke canxawan ba..wayar gari kawai nakeyi in ganni kmr ba Bobby ba"..a akaice labari sukasha sosai kowa Saida ya bama dan uwanshi labarin yanda sukeji game da juna a baya sun ma manta da ba gida suke ba cikin mota suke kuma a kan titi..after a very long conversation ya sake tada motar suka tafi gidan Mi'iraj din da yace zasuje.
Washegari bayan sunyi sallama da kowa suka dawo Kanon Dabo..around 2 something suka isa gida dan haka kowa matsuguninshi ya wuce don huta gajia.
Kwanakin da suka biyo baya kuma shirye shiryen daurin auren aunty sumy suke da za'ayi this coming Saturday..dukda ba wani biki zatayi sosai ba sudai sunata shirinsu wai a cewarsu yanda ta dade batayi aure ba ya kamata tayi biki sosai ita Kuma tace baza tayi ba..maza ne kadai zasuje Gombe daurin aure mata kuma suyi yininsu a nan gidan nasu zuwa dare kuma akai amarya don Waziri yace bai yadda da a daura aure kuma amarya tacigaba da zama a gida ba gwara a hada komai ayishi lokaci daya a wuce wajen...tunda Aysha taji mgnr zuwa Gombe duk ta daga hankalinta wai dan Allah yaje da ita amma yace sam ba inda zataje tunda bada mata za'ayi tafiyar ba..haka ta karaci fushinta ta gama daga karshe ya lalla6o ya lalla6a kayarsa suka shirya kmr dai yanda aka saba.
Ranar Saturday kmr yanda aka tsara su Bobby sukaje har Gombe inda Waziri ya sake maida aurenta da Isma'il akan sadaki mafi kankanta...Kai tsaye daga wajen daurin aure wurin reception suka wuce inda Bobby keta tsokanar Nur wai 'yar yara zai aura tunda gashi bikin uwa da ubanta yazo kuma wai hadda reception..daria yakeyi sosai ya dauka aunty sumy ce kadai mai dabi'un yara ashe shima mijin nata haka yake idan ba haka ba meye wani reception kmr auren fari..gashi kuma sai wani farin ciki yake yana gaisawa da mutane yanda kasan bai ta6a aure ba shidai Nur sauraron iskancinshi kawai yakeyi babu bakin mgn don shi kanshi dai yaji abun wani banbarakwai wai namiji da suna hajara..gaba daya sirikar tashi baya tunanin ta bashi sama da four years amma ya zaiyi tunda yana son 'yarta?..shi kanshi dai zuwa yanxu ya tabbatar da 'yar yara din zai aura kaman yanda Bobby yace amma who cares?..shidai fatanshi bai wuce ya auri Miemie ba kuma yasan da yardan Allah zai samu so bashida wani matsala da yarintar iyayenta...kafin a tashi daga reception suka bar wurin zuwa Lamido's Palace don zuwa ya gaida daddy da kuma Lamido kmr yanda Waziri yace lallai kada ya bar Gombe ba tareda yaje ya gaishesu ba..suna daukan hanya shima Nur ya fara nashi iskancin shidai yanajinshi baice komai ba don tareda driver suke..gidan Lamido suka fara zuwa suka gaisheshi daga nan kuma suka karasa gidansu dama daddy da bai dade da shigowa gari ba..a parlonshi suka sauka bayan sun gaisa ya tambayesu aiki da sauransu suka amsa da lafia..daddy ya dora da tambayan ko Aysha tanayi mashi wani abun don a cewarta yasan har yanxu wauta bai saketa ba..shidai Bobby ya amsa da ba komai don harga Allah idan yace yarinyar nan tayi mashi wani abu daga aurensu zuwa yanxu to tabbas ya zalunceta..Ammi tasa Husna ta kawo musu abinci dasu ruwa duk suka kasa sakewa suci wai akan hanya suke..ko suna nan cikin parlon Aysha ta kirashi kusan say uku bai dauka ba sbd daddy and yasan duk Kiran bazai wuce akan yaushe zasu dawo ba?..Ammi ma tazo suka gaisa itama ta tambayi ko tana mishi wani abu da ha daidai ba yace shidai ba abunda take mishi lafia Lau suke zaune hakan kuma ya mara dadi matuka tace ashe dai 'yar tata ta fara hankali yanxu..nan dai sukayi sallama dasu suka wuce kai tsaye daga nan kuma suka dauki hanyan Kano..tun a hanya Bobby ya kira aunty sumy yana tsokanarta wai an daura itadai tayi mashi banza daga karshe ma kashe wayarta tayi tana ayyana kalar walakancin da zatayi mashi duk ya shigo hannunta...karfe biyar da wani abu suka sauka Kano inda kai tsaye gidan Bobby suka sauka don main house dai sunsan bazai shigu yanxu ba sbd jama'a don haka suka fara branching a nan kafin mutane su ragu...bayan sallahn magrib few mutane da Mummy tayi selecting suka raka amarya aunty sumy gidanta.
Wnn knn
Bayan sati biyu...
Tsahon 5 weeks knn da bikin Bobby da Lamido..cikin 5 weeks din nn Aysha ta sake tabbatar da ba wata mace a zuciar mijinta sama da ita..ta kuma tabbata tafi duk wata mace sa'a da kuma dacewa da samun miji kmr nata..he is such a loving and caring hubby..he is super romantic..he is handsome and rich..he is so so down to earth infact he is all in a man and she is so very lucky to have found him..yanda yake nuna mata tsantsan so da caring abun har mamaki yake bata..kawai sai takega kaman duk dunia ba namijin dake nunawa matarshi so haka..kullum bai gajiya da nuna mata how much he loves and care for her..wnn dalilin yasa itama ta sake kware mishi..zuwa yanxu duk wani abu da yakeso ta sani ta kumayi registering dinshi cikin brain dinta tana mishi baja kolin irin nata caring din..tasan a daidai lokacin da yake da bukatan wani abu a wurinta likewise she knows exactly how to handle him..ita kanta yanxu har mamakin kanta take yanda ta dawo fitsararriya sbd shi..sam ta dena wnn kunyan don gani tayi idan fa ta tsaya kallon ruwa tsaf kwado zaizo ya mata kafa shiyasa ta tattara dan ragowan kunyan ta ajiye a gefe ta kuma shiga nunawa mijinta shi kadai ne namijin da zataso har karshen rayuwarta..rayuwarsu is so full of soyayya,farin ciki da kuma girmama juna kmr ba Lamido da Bobby da basa ta6a jituwa a baya ba..bayan four weeks da biki Bobby yayi resuming office ranan har kuka saida tayi masa wai bazaije ya barta ita kadai ba batasan shima idan na son ranshi ne bazaije ya barta ba amma it's his work dole ba yanda ya iya haka zai koma tunda bazai taba dawwama zaune a gida ba..ranan yini tayi kuka saida ya dawo ya fara aikin lallashi ta hanyar da yasan iya taurin kanta sai ta saduda kuma hakan ne ya faru don tuni ta mance da wani kuka ta bada kai bori ya hau.
Yau Thursday karfe hudu da 35 mins ya dawo daga office..ya shigo ciki rikeda briefcase dinshi as usual ya kama hanyar flat dinshi sai Kuma yajiyo kmr motsinta a kitchen dan haka ya ajiye briefcase din nashi a nan parlor ya nufi kitchen din..tsaye ya ganta jikin gas tana kokarin juye ruwan zafin data tafasa a wani bowl daga ita dai jean da Jessy dinta na Man u red..kallonta ya tsayi from head to toe yanda shape dinta ya fito sosai a cikin kayan..ya hanata da Jessy din nan amma har yanxu taki denawa wai ita tafi sabawa dasu dole haka nan ya bari take sawa a gida bada son ranshi ba
..a hankali yana karasawa ciki ya dagata sama ya shiga juyi da ita cikin kitchen din yana kissing duk inda yaci karo dashi a jikinta full of excitement yake cewa"baby am back..i missed u so much..muahh"ya karasa yana sake manna mata peck a forehead dinta ita kuma ta zagaya hands dinta a wuyanshi tana kallonshi da murmushi tace"welcome back love"..makale mata shoulder yayi tareda nuna mata lips dinshi da hannu daya yana wani kashe ido yace"here"..makale nata shoulder itama tayi tana dungure kanshi tace"No"..fuska ya kwabe kmr zaisa kuka ya shiga bubbuga legs dinshi a kasa still Kuma yana daukeda ita a hannunshi kmr ba abu mai nauyi ya dauka ba yace"Allah sai kinyi"..daria ta saki tareda matsar da head dinta tayi pecking forehead dinshi snn ta dago tana murmushi tace"now saukeni"..shoulder ya sake makale mata alamar he won't..kallonshi tayi for some secs sai kuma ta lumshe ido ta dora finger dinta akan lips din nashi kafin ta bude idon tace"promise it won't pass that"..da sauri yace"i promise..only kiss"..lumshe Ido tayi bayan tace"ohk"..snn ta sake matsawa a hankali ta hade bakinshi da nata shima yayi grabbing da sauri kmr abunda yake jira knn..after like 5 minutes ta samu ta kwace bakinta da kyar tana kokarin sauka kasa tace"wnn shine promise din?.."ajiyeta yayi tareda sake janyota ya hadata da jikinshi yana sauke numfashi yace"sorry i couldn't stop myself"murmushi ta saki bayan ta janye hands dinshi daga jikinta ta shiga nuna mishi kofa tace"oya muje kayi wanka sai kazo kaci abinci"..shoulder ya sake makalewa yana kallonta kasa kasa yace"No..me kikeyi a kitchen?.."kama hannunshi tayi suka fita daga kitchen din tace"custard zan dama"..da sauri yace"nima ina shan custard din plss"..girgiza kai tayi tana murmushi tace"naji..amma muje ka farayin wanka first"..bai sake yi mata musu ba yabita har zuwa flat dinshi..suna shiga bedroom ta saki hannunshi snn ta zaunar dashi gefen bed ta shiga unbottoning shirt din jikinshi..kallonta kawai yakeyi yanda ta cire shirt din nashi ta ajiyeshi gefe ta zare singlet shima ta ajiye gefe sai kuma ta mikar dashi tsaye ta zame trouser leaving only shorts a jikinshi snn ta sake jan hannunshi har cikin bathroom shi kuma sai binta yake kaman wani rakumi da akala..tana gama hada mishi komai ta fita da sauri don tasan tsaf zai iya riketa ya hanata fitowa ita kuma bata shiryama wnn fitinan nashi ba shiyasa tayi saurin fitowa tun kafin ya rutsa ta...closet dinshi ta shiga ta fiddo mai kayan da zai saka snn ta fita don karasa dama custard dinta tunda already tayi setting dinning tun kafin ya dawo..saida ta sake kunna gas ruwan ya tafasa snn ta dama custard din ta fito dashi a hannu tana juyawa da spoon..a dinning taja kujera ta zauna tana cigaba da juyashi don so take ya danyi sanyi kafin tasha..tana sane taki komawa dakin sbd gudun kada ma ya ganta ya hanata fitowa..komawa tayi kitchen ta zuba milk da sugar cikin custard din nata snn ta sake dawowa dinning din ta zauna ta fara shan abunta hankali kwance..Bobby ko yana fitowa daga bathroom sharp sharp
Book Chapters
Chapter 52
Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59