gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Dr.bob Complete Hausa Novel by by Aysha Rano Chapter 27 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abincinshi a gaba amma ko loma daya ya kasa kaiwa bakinshi...goshi ya dafe da both hannayenshi yanatunanin abubuwanda suka faru...kawai gani yake dalilin kauracewa yan uwan daddy da yayi Allah yakeson ya hukuntashi da ita...shi gani yake wnn abun da yakeji gameda ita yayi yawa...tunda yayi mgn da ita zuwa yanxu bai samu peace of mind ba sbd yanda tayi reacting da yace yana sonta..kawai tasa mishi kuka sbd da gaske ta tsaneshi ne ko kuwa sbd tsabagen ta6ara da yake dawainiya da ita...yayi zurfi cikin tunani har baisan sanda Mummy tazo ta zauna kusadashi ba sai hannunta da yaji ta dafa shoulder dinshi..da sauri ya dawo hayyacinshi tareda daukan spoon dake nan cikin abincin nashi da sauri ya shiga cin abincin kamar mayunwaci..bayason ta gane halinda yake ciki baisan kuma ta riga ta gano ba...batace mishi komai ba sai kallon yanda yake tunkuda abincin take tana jira ya gama suyi mgn dan yau ko yaki ko yaso saiya sanar da ita damuwarshi...tausayi yake bata yanda yake kokarin 6oye suffering dinshi bayan bayyanawa kadai ne maslaha...bata katse mishi cin abinci ba saida ya gama ya kora da drink snn ta kira sunanshi...kasa amsawa yayi sai juyawa da yayi yana kallonta...kallonshi takeyi itama sosai tace"Bobby wai meye matsalarka?..why kake kokarin 6oye abunda ba kai ka dorama kanka ba kuma 6oyewan bazai haifar maka da komai ba..kanaso ciwon zucia ya kamaka sbd wnn damuwan daka dorama kanka ne?..baka tunanin halinda ni da ‘yan uwanka zamu shiga idan wani abu ya faru dakai?..duk bakayi wnn tunanin ba kake kokarin cutar da kanka koh?.."shiru kawai yayi yana kallonta yasan duk mgnr data fada gaskia ne..da gaske abunda yakeji bashi ya dorama kanshi ba..kuma kokarin 6oye hakan ba abunda zai haifar mashi sai dana sani amma ya zaiyi?..soyayya ne Allah ya jarabceshi dashi na yarinyar nan kwata kwata bai ganin zata soshi..shi kuma so yake ya yakiceta daga zuciyarshi amma zuciyar taki bashi hadin kai dama tun ba yanxu ba yasan zuciyarshi tafi shi kanshi taurin kai sbd yanda yayita kokarin dakatar da abun tun yana dan karami abun bai yiwu ba har yanxu aka kawo wnn matakin...yasan yanxu tana gama makaranta kilan a hadata da wani ta aura ko kuma ta fitoda wanda takeso tunda tasha fada mishi ita tanada wanda zata aura...tunanin hakan yasa yaji wani irin nauyi a cikin zuciyarshi...idonshi suka kada sukayi jaa har wani shinning suke sbd dan kwalla daya cikosu...da sauri ya kifa kanshi jikin Mummy ya sauke wani ajiyar zuciya irin na wanda yaci kuka ya koshi...numfashinshi ma da kyar yake shaqa sbd kokarin 6oye hawayenshi da yake...baison Mummy ta gani shiyasa yayi haka amma yasan da kyar ma idan bata gani ba...saida ya dauki almost 3 minutes a haka kafin ya dago daga jikin nata yana sauke kanshi kasa...wnn raunin da yake zuwa mishi duk yayi mgn da itane bayaso shiyasa bai cika son yin mgnr da itaba..da akwai wani irin rauni da karyewar zuciya dake zuwa ma mutum duk yake gaban mahaifiyarshi idan ya tsinci kanshi cikin wani yanayi mara dadi...baisan ko kowa haka yakeji ba amma shidai haka yake tun yana dan karaminshi...hannu Mummy takai ta dago fuskanshi tana kallon idanunshi da har yanxun suke shinning sbd hawaye da suka kuma taruwa a ciki tace"let them out son..zakaji sauki"..da sauri ya sauke kanshi yana sake kokarin mayar dasu amma wnn karon sai yaji kamar turosu akeyi da gayya dan haka ya sake maida kanshi jikinta da sauri daidai lokacin kuma hawayen suka silalo kan fuskanshi...bayanshi Mummy ta shiga shafawa a hankali itama nata muryan a raunane tace"cry as much as u want zaka samu sauki"..shidai bai iya cewa komai ba sai hawaye da har yanxu basu dena zubowa fuskanshi ba...mamaki da haushin kanshi suka dirar mishi lokaci guda...shi kanshi he can’t remember when last ya zubar da hawaye da idonshi amma wai yanxu shine ke kuka sbd karamar yarinya..wnn wace irin jarabawa ce?..some months back idan kace mishi zai kamu da soyayya kuma har yayi kuka sbd wata mace kallon you are not normal zaiyi maka amma yanxun gashi dumu dumu cikin soyayya snn kuma gashi yanata kwararar da hawaye abunda zai iya cewa rabonshi dayi tun bayan rasuwar mahaifinshi...Allah ma yasoshi ba kowa a wurin da kunya zaiji wlh...Mummy ce tasa hannu ta dagoshi tana goge mishi hawayen da yayi saura fuskanshi kafin tace"fadamin..what exactly happened?.."hannunta ya kama duka biyun yana dubanta cikin voice dinshi daya fara disashewa yace"she doesn’t love me Mummy..she despise me..da bakinta tacemin tanada wanda zata au.."kasa karasawa yayi sbd wani abu dayazo ya tokare mishi wuya..sake dora kanshi yayi shoulder dinta yana jujjuaya kan nashi from side to side yace"mutuwa zanyi Mummy...wlh duk ranan da ta auri wani i won’t survive zuciyata bugawa zatayi in mutu Mummy ki taimakamin please!.."rungumeshi Mummy tayi itama nan take hawaye suka ciko idanunta tace"u won’t die inshaAllah..Bi’iznillah batada mijin aure sai kai sbd haka ka kwantar da hankalinka"...girgiza kai yacigaba dayi yace"Mummy wlh i can’t..dan bakisan yanda mukayi da ita bane..she even cried da nace ina sonta kuma nasan halinta Mummy da gaske bata kaunata shiyasa takemin haka...bansan meyasa Allah zai..."bai karasa ba Mummy tayi saurin rufe mishi baki tana cewa"karkayi sa6o Bobby..kayi hakuri mubi komai a sannu inshaAllah komai zai wuce..komai zai zama tarihi"...wani numfashi ya sauke mai karfi tareda fadin"Allahumma Ameen Mummy..Allah sa ya zama history kaman yanda kikace"..tace"Ameen InshaAllah..yanxu tunda ka gama cin abincin ka samu kaje ka kwanta naji jikinka da zafi anya ma zaka iya bacci a haka kuwa?..kodai muje asibiti?.."girgiza mata kanshi yayi kafin a hankali yace"don’t bother haka yakeyi dama"..da mamaki tace"u mean haka kake kwana da fever kullum kuma bakayi kokarin kayi wani abu ba?.."dagowa yayi ya kamo hannunta yace"Mummy ai bai dade da farawa ba..for the past few weeks ne kawai and inashan magani"..girgiza kai Mummy keyi tace"ban yadda ba..nasan ba maganinda kakesha"..yace"da gaske inasha Mummy..kinsan bazanyi wasa da lafiyana ba"...tace"ya kamata dai kar kayi wasa dashi din idan kuma baso kake Lamido tace batason mai yawan rashin lafia ba"..da murmushi ta karasa mgnr aikam shima saiga wani hadadden murmushi kwance akan fuskanshi...Lamido kawai da aka kira yaji kaman anyi mishi gagarumin kyauta wnn baisan yanda zaiji duk akace ta zama matarshi ba...ganin yanda Mummy ta tsareshi da ido sai ya mike yayi mata sallama ya kama hanyar Flat dinshi...da kallo Mummy ta bishi tausayinshi na sake kamata..ta tabbata authentic so yakema yarinyar nan har tunda taga yayi abunda ita kanta ta manta yaushe rabonda yayi shine hawaye...addu’anta bai wuce Allah ya karkato da hankalin yarinyar kanshi ba snn yasa ayi komai da komai cikin sauki da kwanciyar hankali.

Shiko Bobby yana shiga Flat dinshi kulle kofanshi yayi ya wuce direct zuwa bedroom dinshi...bayan yayi wanka yasa pyjamas dinshi snn ya kwanta ya dora wayanshi kan kirji wani sashe na zuciyarshi sai azalzalanshi yake ya kirata ko muryanta yaji yasan zai danji sauki yayinda daya sashen kuma yake cewa idan har ya kirata bayan duk wulakancin da tayi mishi daxu to ya tabbata a kirashi da mara zuciya...shiru yayi gamida runtse ido yanajin shawarwarin da ko wane sashe na zuciyar ke bashi...shi kanshi yayi na’am da kin kiran nata dan haka ya sake kulle ido ya lullu6e da duvet shi a lallai bacci yakeso ya daukeshi sbd kwata kwata bayason yawan tunanin nan da yake amma kememe bacci yace baiga daman daukanshi ba..haka ya karaci juyi yana rungume pillow daga karshe dai dole kasa daurewa yayi saida ya danna mata kira...har ya gama ringing bata dauka ba dan haka ya sake kira..yana gab da katsewa ta daga cikin magagin bacci tace"baby ka bari in tashi daga bacci sai muyi waya kaji?.."wani irin abu yaji yazo ya tokareshi a wuya har numfashinshi na barazanar daukewa...bai iya ce mata komai ba ya kashe wayarshi gaba daya...ita kuma jin baice komai ba ta dago wayan tana kallon screen sai taga proprietor a jiki nan take baccin dake idonta ya wartsake ta wani zare ido tareda fadin"na shiga uku"...sam bata duba wanda ya kira ba tayi zaton shine tunda daxun yace mata idan ya isa gida zai kirata..hankalinta taji ya tashi tasan yanxu da kyar idan basuyi rigima dashi ba..sake kiran wayanshi tayi amma har ya gama ringing bai dauka ba..data sake kira kuma sai taji wayan gaba dayanta ma swicth off...haka nan ta hakura ta kwanta tana tunanin yanda zasu kwashe dashi gobe...shi kuma Bobby tsabar 6acin rai ne ya hanashi mgn...sbd wulakanci shine zai kirata ta wani kirashi da sunan saurayinta sbd bata da hankali..haushin kanshi ka yaji ya kamashi ga zafi da zuciyarshi ke mishi..shidai ya hakura da yarinyar nan kawai inyaso idanma mutuwa zaiyi sbd ya mutu amma bi’iznillah bazai sake nuna yanada wani feeling gameda itaba tunda ita batasan mutuncin hakan ba...wnn daren ma kamar sauran saida dare ya tsala sosai snn ya samu bacci.

Washegari Thursday ranan shiga college dinshi ne amma yana sane yace bazaije ba sbd bama yaso ya ganta ballantana ya karya alkawarin daya daukan ma kanshi...ko a gida bai zauna ba ya shirya ya tafi hospital sbd yasan idan Mummy ta ganshi a gida zata tashi hankalinta ne and shima kanshi yana bukatar ya fita ko dan wani wurin ne yaje at least zai shaki fresh air.
Lamido na shigowa makaranta ta nufi office dinshi kaman yanda yace kullum taje ta gaidashi da safe and ita kanta tanada bukatar yin mgn dashi akn abunda ya faru jiya..ga mamakinta bata sameshi office dinba haka ta koma class tana sake trying numbershi yana shiga amma bai dauka ba...suna fitowa break ta sake komawa office din nashi still baya nan kuma tanata kiran wayanshi har ta gaji bai dauka ba...hankalinta ya tashi sosai tasan yanxu kilan yace zai hadata da daddy...tasan dan abu karami ke 6ata mishi rai amma ita ai bada niyua tayi ba...ranar har suka bar school bata ganshi ba kuma bai dauki wayanta ba...hankalinta ya tashi fiyeda yanda take zato duk sai taji wani iri dan tunda suke bai ta6ayi mata haka ba...a ‘yan kwanakin nan da yake mata mutunchi ta fara fahimtan waye shi...sure tasan yanada fada amma kuma yanada kirki and yasan darajan mace...gaba daua jinta take wani iri addu’anta bai wuce Allah yasa kada ya hada da daddy ba.
Washegari friday same thing happens shima har suka tashi Lamido na nemanshi bata ganshi ba wayanshi kuma tun yana kin dauka har ya fara rejecting call din...hankalinta yayi mugun tashi har hakan yaso bata mamaki dan bata taba tunanin zata damu haka ba...da dadewa tasan ta saba dashi amma batasan sabon yakai hakaba sai yanxu...koda yake bataso ya hadata da daddy ne shiyasa hankalinta yaki kwanciya...a takaice saida ta kwashi three days tana nemanshi bata samu ganinshi ba...ranan Sunday tana zaune dakinsu itca kadai saida ta bari Billy ta fita snn ta kira Nur a waya sbd tasan idan sukayi mgn a gabanta zatacigaba da cewa soyayya ne tsakaninta dashi ita kuma bata son haka..yana dauka tace"sir dama ina neman proprietor ne"..Nur yace"baki sameshi a waya ba?.."a hankali tace"baya dauka"..da mamaki Nur yace"ban gane baya dauka ba?.."tace"sir inata kira bai dauka..rejecting call dinma yakeyi"..Nur ya danyi shiru for some minutes before yayi adding"kinyi mishi laifi knn?.."a hankali tace"sir kawaifa kirana yayi bansan shi bane na zata baby ne shknn fa yaketa fushi dani har yanxu..kuma sir ni ina tsoron kar ya hadani da daddyna"..shiru Nur yayi yana saurarnta yana murmushi...addu’a yake Allah yasa itama ta damu dashi koda baikai rabin damuwar da yayi da itaba..saida ya gama smiling dinshi before yace"bani two minustes inyi mgn dashi"..a hankali tace"toh"snn ta kashe wayar...suna gama mgn Nur ya dannawa Bobby kira..ringing biyu ana uku ya daga da sallama...Nur yace"maza ina ka shigane kwana biyu?.."Bobby yace"wlh banjin dadi ne shiyasa kajini shiru..ya aiki".."Alhamdulillah kana gida ne?.."Nur ya tambayeshi kai tsaye shi kuma ya amsa da fadin"no ina hospital"...da sauri yace"ohk gani nan zuwa asibitin yanxu..bakada lafia ne naji muryanka somehow?.."ajiyar zuciya Bobby ya saki before saying"sai kazo din dai kawai"..Nur ya amsa da"ohk"..daga haka kowa ya ajiye waya..sake kiran Lamido Nur yayi tana dauka yace"munyi mgn dashi yace yana hospital yanxu haka..ko zaki shirya in kaiki?.."shiru tayi tana nazari for a while sai kuma a hankali tace"toh.."yace"ki shirya yanxu gani nan zuwa"..ta sake amsawa da"toh.."snn ta kashe wayar..mikewa tayi ta dora dogon hijab akan jessy da straight skirt dake jikinta..tazo fita daga dakin saiga Billy ta shigo ciki..kallonta takeyi from sama zuwa kasa tana ta6e baki tace"ina kuma aka nufa hakia indo?..fushin ya kare knn?.."wani irin harara Aysha ta watsa mata snn ta bangajeta ta fice daga dakin Billy ta bita da kallo baki bude tana cewa"anya kuwa Lamido batada aljanu?.."

A hankali take tafiya har ta iso first gate na hostel din dan haka Nur na karasowa bai karasa ciki ba yayi picking dinta a nan suka wuce...suna hanya da yaga yanda tayi shiru ta zubama spot daya ido yace"duk Dr Bobby ya sanyaki a damuwa koh?.."da sauri ta daga kai tana cewa"eh mana..kumafa ni banga abun jin haushi a mgnr dana fada ba"..murmushi Nur yayi yana girgiza kai cikin ranshi yace"ai bazaki ganiba dama"..daga haka ba wanda ya sake mgn cikinsu har suka iso Freedom...yana gama parking duk suka bude mota suka fita zuwa cikin asibitin...saida sukazo daidai office dinshi taji wani irin faduwar gaba ya risketa..ko wane kalan masifa zai sauke mata oho?...Nur ne ya fara tura kofar ya shiga kafin itama tabi bayanshi...Bobby dake kwance kan sofa ya bude idanu a hankali ya saukesu kan Nur then back to Lamido dake tsaye bayanshi sai faman sunkuyar dakai take...da sauri ya mike zaune yana kallonta da kyau duk idanun nan a waje kaman yaga abun tsoro..yakai hannu yana murza idanuwan nashi wai ya tabbatar ba mafarki yake ba ba kuma gizo take mishi kmr yanda ta saba ba..ganin da gaske itam ce nan tsaye a gabanshi baisan sanda ya wani daure fuska yana kallonta ba...a hankali tayi kasa da idonta tanajin yanda tsatstareta da wnn idanun...kafin tayi mgn ya nuna mata kofa yace"out of my office"..da sauri ta dago tana kallonshi wnn karon shi ya kawar da nashi idon kafin ya sake fadin"i said ki fitarmin daga office"...kafin tayi mgn Nur yace"Haba Bobby"..k kallonshi baiyi ba ya sake nuna mata kofa ita kuma tayi tsaye taki tafia kawai sai ya dafe head dinshi da hannu bibbiyu yana sauke numfashi...ganin haka Nur ya dan matsa kusada ita murya can kasa yace"karki yadda kibar office din nan ba tareda kun daidaita dashi ba..idan yacigaba dayi maki masifa kawai kuka zakisa shknn kinyi maganinshi"..yana gama fadan haka ya juya ya bar office din..jin karar kofa ya sashi bude ido sbd yana tunanin itace ta fita amma sai yaga Nur ne...sake dawo da kallonshi yayi gareta murya can kasa yace"ba cewa nayi kibar min office ba?.."da sauri tace"sir dan Allah kayi hakuri"..girgiza mata kanshi yayi yace"kimin laifi ne kike bani hakuri?.."kwabe fuska tayi zatasa kuka tace"nifa bansan kaine ba Allah"..kallonta kawai yake ganin zata fara mishi kuka bayan ba abunda yayi mata..shi baisan dalilinda yasa ma Nur ya daukota ya kawo mashi ita har nan ba..ajiyar zuciya ya sauke gamida dauke kanshi daga gareta ya sake komawa ya kwanta kan sofa...ita kuma ganin yanda yaba banza ajiyarta sai ta daddage ta rushe da kuka kmr yanda Nur yace tayi..da dadewa tasan bayason kuka tasan kuma shine kadai abunda zatayi ya saurareta...sake runtse ido yayi jin yanda take mishi kuka ya dauki throw pillow ya danne face dinshi dashi wai ko zai denajin kukan nata amma a banza..da dane ya tabbata ko zata shekara tana kuka a gabanshi bazai dameshi ba amma yanxu wani irin rauni kukan nata ke haifar mashi..sai yaga kaman yayi mata wani abun alhalin kuma ba uwar da yayi mata..har cikin zuciyarshi yakejin kukan..kasa daurewa yayi ya mike zaune yana kallonta da idonshi da sukayi red yace mata"wani abun nayi maki da zaki sani a gaba kina kuka?.."cikin kuka tace"sir kaine fa kaki hakura"..yace"cewa nayi ban hakura ba?..ni bakiyimin laifin komai ba kawai kije I don’t want to see u"..haushi sosai mgnrshi ya bata dan haka ta juya a fusace zata bar office din garin sauri ta take hijab dinta dake jan kasa aikuwa ta tafi luu saura kiris ta fadi Bobby yayi hanzarin mikewa ya tareta a jikinshi...ta runste ido tana sauke numfashi dan yanda ta gama tsorata ta gama sadakarwa zata jita a kasa sai kuma taji ba haka ba...shi kam kallonta kawai yakeyi kaman an aikoshi...the more ya kalleta the more yake sake ganin asalin beauty dinta wanda da bai cika gani ba sam...zuciyarshi yaji tayi wani tattarewa ta dunkule waje daya sai wani irin harbawa take da mugun karfi...ya lumshe ido ya bude still yana kallon yanda har yanxu ta kasa bude idanunta baisan ya akayi ba kawai shidai yaji ya hadata da jikinshi..rungumeta yayi da kyau yana sauke numfashi a jere kaman wanda yayi race tareda lumshe ido yanajin wani irin mixed feeling tattare dashi...Lamido kuwa mutuwar tsaye tayi jin yanda ya cacimeta sbd tsabar tsorata kasa ko motsi tayi balle tayi kokarin kwatan kanta..Bobby kuwa is far gone sam bai ankara da abunda ya aikata ba saida yaji ta fara mutsu mutsu a jikinshi..sakinta yayi da sauri yakai hannu ya dafe head dinshi tareda fadawa kan sofa...sai sauke ajiyar zuciya yake kmr wanda yayi tsere..he just can’t believe what happened..he can’t believe he hugged her after all alqawuran daya daukan ma kanshi...runtse ido yayi yana salati dama abunda yske gudu knn shiyasa tun farko yace ta tafi amma taki tafiya...yasan idan yacigaba da ganinta abubuwanda yake 6oyewa suna iya kokarin tona mashi asiri and now see what happened..ya kasa controlling kanshi har yayi hugging nata wanda yakeda tabbacin mutuncinshi ja iya zubewa a idonta...Aysha kuwa shiru tayi ta kurawa spot daya ido kawai tana mamakin abunda yayi mata...gani take kodai aljanu sun shafeshi ko kuma yana fama da serious rashin lafia tunda ga alama nan ta gani yanda yake dafe da kanshi..kuma tasan yana cikin hankalinshi bazai aikata abunda ya aikata ba for she trust him..tasan yanda suke rigima dashi ko wani ya gani tareda ita so ta tabbata bazaiyi hugging dinta for his selfish interest ba..kilan yayi haka ne don ya taimaketa ko kuma sbd wani abu dake dawainiya sam bata kawo wai da gaske sonta yake ba...ganin har yanxu bai motsa ba ta karasa a hankali ta zauna kan one of kujerun office din tana dubanshi murya a hankali tace"sir ai ka hakura koh?.."a hankali ya bude ido yana kallonta..ta wani sake langabewa tace"nace fa bansan kaine ba"..gyada kai kawai yayi kafin ya safe maida eyes dinshi ya rufe..tace"kuma bazaka fadama daddy ba?.."nan ma kan ya daga mata without saying anything..shiru sukayi a office din shi yanajin kaman ya fallasa mata asirin zuciyarshi ita kuma tana tunanin wane irin ciwo ke damunshi da duk yabi ya canxashi haka?..mikewa tayi tana murmushi tace"sir zan tafi"...kai kawai ya sake daga mata ta juya ta fita shi kuma ya sake dafe kanshi yana cije lips dinshi...baisan garin ya yayi loosing control dinshi ba wlh..Allah dai yasa yarinyar nan batayi masa muguwar fahimta ba.






Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
33
Tana fita taga ba motan Nur a parking space dan haka ta kirashi a waya..yana dauka yace mata"Lamido kiyi hakuri wani abu ne ya tosomin yanxu nan aka kirani shiyasa na tafi..kiyi mgn da Dr Bobby nasan zai maidaki"..bata iya cewa komai ba har ya gama bayaninshi ya kashe wayar...kuyawa tayi a hankali ta koma office din nashi...ta tura kofar ta shiga kai a kasa..yana zaune yanda ta barshi ya dago idonshi da kyar yana dubanta yace"what?.."tace"provost ne yace mu tafi tare waishi ya tafi wani wuri"..bai iya cewa komai ba ya mike zuwa wani drawer ya dauki drugs dinshi ya 6alla snn yayi dispensing ruwa yasha maganin dashi...duk wnn abun da yake bai sake kallon inda take ba sbd baison ya sake aikata wani abun..yana gama sha ya dauki waya da keys dinshi yace mata"muje.."ba musu ta juya suka fita daga office din...yasa key ya rufe snn suka wuce parking lot...dirver na hangoshi yazo ya bude mishi kofa as usual yana karasowa ya shiga ita kuma Aysha ta bude front seat zata shiga da sauri yace mata"are u mad?..C’mon come back here"..batace kala ba ta maida kofan ta rufe snn ta bude nan kusa dashi ta shiga..shima driver ya shiga tareda tayar da motar suka fita asibitin...ko a hanya Bobby bai kallon inda take..haka nan yajishi duk a takure sbd kusancinda sukayi da juna..gaba daya bai yadda da kanshi bane a yanda yakeji din nan yasan tsaf zai iya sake aikata wani abun kwatankwacin na dazu shiyasa duk yaki ya saki jikinshi ya wani takure can karshe kaman ba motarshi ba...Aysha kuwa bata ma lura da abunda yakeba don duk a zatonta bashida lafia...shiru motar babu mai cewa komai banda sanyin ac ba abunda ke tashi sai Lamido dake dan motsawa time to time...har suka isa FCNM Hostel ba wanda yace qala..driver na gama parking ya bude motar ya fita ya rage su biyu kadai a ciki...a hankali ta kama handle zata bude kofar sai kuma ta juya tana kallonshi nan kuma taci karo da idonshi a kanta kusan a tare kowa ya janye nashi idon...dan murmushi ta saki tana dubanshi tace"sir nagode..sai anjima"..kafin ta bude motar taji shima a hankali yace"am sorry"..sake juyowa tayi tana kallonshi still da murmushi sai kuma ta girgiza kai tana cewa"bakayi laifin komai ba sir..nasan u are a good person and bakayi kama da irin wnn mutanen ba..so u don’t have to apologize"..wani ajiyar zuciya da bai shirya ba ya sauke har dan wani smile yayi sbd samun relieve najin abunda tace...at least dai yasan batayi mashi kallon mutumin banza ba..shi sai yaga yau tayi wani irin nustuwa na musamman kaman dai ba Lamido da kullum suke rigima da ita kan rashinji ba...baisan ko sbd ya fara sonta ne kuma ya fara ganin nutsuwarta ba amma dai yau ta burgeshi fiyeda tunaninshi...bude motar tayi ta fita kafin ta rufe ta sake sunkuyowa tana dubanshi har yanxu da wnn murmushin kan fuskanta tace"thank u so much sir..sai anjima"..kai kawai ya iya dagawa yana kallon yanda murmushin keyi mata kyau kaman wani soko..rufe mishi kofar tayi snn ta juya ta tafi shi kuma hadda su sauke glass yana sake binta a kallo yanajin wani abu kaman maganadisu nason janshi gareta dan haka ya sauke glass din tareda maida kanshi yayi relaxing akan kujera yana cigaba da tunaninta...gaba daya ta mamaye jini da tsokarshi ta yanda bai iya cikakken mintuna 10 ba tareda yayi tunaninta ba...ta 6ata mishi rai jiya amma yau ta faranta mishi matuka..kawai sai yaji dadin yanda yaga ta nutsu da kuka yanda batayi misunderstanding dinshi ba..sai kuma yanda ta damu har saida ta nemo inda yake ta bashi hakuri..she really is amazing and ya tabbata if abubuwa zasu cigaba da kasamcewa haka watarana yana iya samun soyayyarta..tunanin hakan kadai ya sake saukar mashi da wani farin ciki...duk wnn kunci da 6acin ran da yake ciki sai yaji sunyi disappearing..a haka driver ya shigo ya sake tayar da motar suka dauki hanyan gida.

Da fara’a ya shigo cikin gidan saidai mutanen daya gani parlon zaune tareda su Mummy yasa yaji new 6acin rai na neman taso mishi...suna jin shigowarshi suma gaba daya suka maida hankali kanshi kaman dai jiran zuwanshi suke...dauke kanshi yayi ba tareda yace qala ba ya kama hanyan flat dinshi Mummy da aunty sumy suka hada ido kafin Mummy ta mike ta dubi mahaifiyar Isma’il grandma din su Miemie knn tace mata"ina zuwa bari inyi mgn dashi yanxun nan"..daga mata kai matar tayi duk jikinta yayi sanyi..ita gani take kaman shi zai hana su samu yafiyar da sukazo nema wurinsu..dukda already sun riga sun gama mgn har Mummy tace itakam bata rikesu ba dama ta yafe musu itama aunty sumy jin Mummy tace haka itama sai bataja zancen da nisa ba tace ta yafe..su Miemie kuwa ya rage nasu su yafe ko karsu yafe amma sunsan komai dadewa watarana zasu yafe musu tunda duk tsiya

Please Login or Register in order to submit comment