You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
halinda take ciki amma tsoron kiranta ma yakeyi sbd yasan ba dauka zatayi ba...yasan Nur ne kadai zai iya taimakonshi a halinda yake ciki dan haka ya danna masa kira..yana dauka ko salam dinshi bai amsa ba yace"Nur inaso inji halinda take ciki plss..kunyi mgn da ita?.."Nur yace"bamuyi ba..ka kirata a waya mana"..da sauri yace"ba dauka zatayi ba..nidai taimako na zakayi zako gida saika kiramin ita a wayanka..inaso inji ya jikinta"...ajiyar zuciya Nur ya sauke kafin yace"shknn gani nan zuwa"..da sauri Bobby yace"nagode sosai friend..nagode"..Nur ajiye waya yayi yana mamakin wnn so da Bobby kema Lamido haka?..duk yabi ya koma kaman wani soko sbd soyayya...shi kanshi daxu ba karamin tausayi ya bashi ba...yaji inama Lamido zata amince ta aureshi kawai a wuce wajen...keys din motanshi ya dauka ya fita daga gidan...su Mummy na zaune parlor lokacinda ya shigo tabishi da kallo kawai..tun daxu ta fuskanci akwai abunda damun Bobby zuba ido kawai tayi taga gudun ruwanshi and wnn zuwan na Nur ya sake tabbatar mata da lallai ba lafia ba...ko zama baiyi nan parlon ba kawai ya gaishesu ta wuce ciki Aunty Sumy da kanta saida tayi mamakin hakan...a kwance ya samu Bobby har yanxu eyes dinshi basu dawo normal ba..yana ganinshi ya mike zaune shima Nur din karasawa yayi kusa dashi ya zauna snn ya shiga kiranta yasa a speaker...har ya gama ringing baa dauka ba ya sake kira wnn karon yaji an daga amma maimakon ita sai yaji muryan Billy na fadin"bacci takeyi sir"..Nur yace"ya jikin nata?.."Billy ta juya ta dan kalli yanda kafan har ya fara swelling tace"sir kumbura kafan yakeyi..yanxu ta gama kuka sai da kyar muka samu bacci ya dauketa"..ba Bobby ba shi kanshi Nur din hankalinshi tashi yayi da sauri yace"i will get back to you"..daga haka ya kashe wayar yana kallon Bobby daya dafe head dinshi da hannu bibbiyu yana jujjuya kan cikeda tashin hankali yace"Nur na shiga uku..zuciyata bugawa zatayi wlh"..da sauri Nur ya kama hannayen nashi ya rike tareda fadin"ba abubda zai faru inshaAllah..ka kwantar da hankalinka yanxu zanje in nemi doc saratu muje can hostel din ta dubata"..mikewa yayi da sauri har wani juwa ke neman daukanshi yace"muje ka kaini in ganta plss..hankalina bazai kwanta ba idan banga halinda take ciki ba"..kamashi Nur yayi ya zaunar dashi yana dubanshi yace"relax dan Allah..kaga yanda jikinka ke rawa kuwa?..kaima kana bukatan medication sbd haka kasha magani ka kwanta ka huta ni zanje inyi duk abunda ya kamata ayi mata"..tun kafin ya rufe baki Bobby ke girgiza kai yace"u won’t understand..kona zauna hankalina ba kwanciya zaiyi ba..i need to see her"..shiru kawai Nur yayi yana kallon yanda yake mgn da kyar sbd tashin hankalin da yake ciki...basu san sanda Mummy ta shigo ba jin mgnrta sukayi kusa dasu...Bobby na daga ido daya ganta kawai sai ya mike tsaye da sauri ya fada jikinta murya a raunane yace"Mummy inaso inje in ganta plss..zuciyata bugawa zatayi"...da mamaki Mummy ke kallon Nur tace"Nuru meya sameshi haka?.."a nustu Nur ya bata labarin iya abunda ya sani itama nan take taji nata hankalin ya tashi..kada dai ace Bobby wani abu yaje yayiwa yarinyar mutane fa...dagoshi tayi daga jikinta tana kallonshi..tambaya take son mishi kan abunda ya haddasa faruwar haka amma sai ta kasa sbd tsantsar tashin hankali data karanto a fuskanshi da kuma yanda idanunshi suka juye lokaci guda tasan tsaf zuciyan nashi zai iya bugawa kaman yanda fada..batayi gaddama ba ta kalli Nur tace"kaje dashi ya ganta..snn duk halinda ake ciki ka kira ka sanar dani and make sure shima kayi mishi treatment sbd zazza6i ne sosai naji a jikinshi"...kallonta Nur yake kafin yace"amma Mummy shima yana bukatar hutu fa"..tace"idanma bakuje dashi hutun da muke so yayin ba samun yinshi zaiyi ba..banason zuciyar nashi ya samu matsala kaman yanda nace kuma nasan halinshi muddin baa kaishi ya gantan ba yana iya samun problem"..gyada kai kawai Nur yayi snn ya kama hannun Bobbyn suka fita...kwace hannunshi yayi daga na Nur yana cigaba da tafiya da kanshi gamida tattaro duk wani sauran jarumta da karfin halin da sukayi mashi ragowa ya dorasu bisa kanshi snn yacigaba da tafiya har zuwa inda Nur yayi parking..da kanshi ya bude front seat ya shiga shima Nur ya shima driver seat snn ya tada motar suka dauki hanyan FCNM..zuciyarshi sai bugawa takeyi sbd baisan me zai tarar a wurinta ba amma ya gwammaci duk wani wulakanci da zatayi mishi akan dai yayi zaune a gida batareda yazo yaga halinda take ciki ba..gani yake kaman Nur ba tafiya yakeyi ba don bai ta6a ganin nisan college din ba irin na yau...suna shiga makarantan direct suka wuce hostel nan ma Bobby yaga nisan hostel din kaman yau ya fara shigoshi...saida sukazo daidai gate na female hostel Nur yayi parking snn ya sake dialing number Lamido...Billy ce ta sake dagawa yace"gamu hostel din naku zaki iya fito da ita?.."juyawa Billy tayi ta kalli Aysha dake rikeda kafan tana sauke ajiyar zuciya cikin bacci itama kaman zatasa kuka tace"sir bazan iyaba..bacci takeyi tun daxu ni bansan yanda zanyi mata ba"...Nur kashe wayan yayi yana duban Bobby daya gama jin duk abubuwanda Billy ta fada...daya daga cikin matrons sukasa akayo musu mgn da ita...ta bada sanarwan zasu shigo hostel din snn ta dawo tayi musu jagora har cikin apartment din da yayi tsit sbd kowa ta shiga daki sbd sanarwar da akayi musu...kai tsaye dakinsu suka nufa Bobby najin each taku na kara masa adadin tashin hankalin akan wanda yake ciki already.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
36
Matron da Billy ne suka fara shiga dakin snn Nur shi kuma Bobby ya shiga daka karshe...har lokacin bata dena sakin ajiyar zucia cikin baccin da take yi ba...a hankali ya karasa inda take hannayenshi zube a aljihu ya tsaya kusada gadon yana kallonta tun daga fuskanta da yayi jaa as a result of kukan da tayi har zuwa legs dinta da rigan jikinta ya danyi sama kadan sai fair skin dinta daketa glowing...kallonta kanta yayi shima ya ganshi a bude duk gashinta a waje kawai sai yaji ranshi ya baci..kan wane dalili zasu barta a haka tunda sunsan zasu iya shigowa har inda take..kawai sun bar jikinta da gashinta a bude gashi nan Nur yana ta kallo abunshi..kallon Billy yayi da face dinshi dayaji kaman shi yake daure kanshi da kanshi a takaice yace"batada hula ne?.."da sauri Billy tace"sir da kanta ta cire wlh..wai bazata iya bacci dashi ba"..yana sake dinke fuska yace"shi kuma jikinta da kuka bari a bude fa?.."kallon jikin nata tayi da sauri tanaso taga inda suka bari a buden sai taga rigan ta ya danyi sama..batace dashi komai ba ta karasa ta janyo mata rigar har kasa snn ta dauki hulanta data yar nan kasa shima ta shiga kokarin zurawa a kanta daidai lokacin kuma ta dan bude ido snn ta sake mai dashi ta rufe..Billy na gama sa mata hulan takai hannu zata cire murya a cushe Bobby yace"idan kika cire hulan nan sai ranki ya 6aci wlh"..bude ido tayi da sauri tareda mikewa zaune tana kallonshi...ta dauka a mafarki taji muryanshi amma sai taga da gaske shi din ne a gabanta..to me kuma ya kawoshi bayan abunda ya gamayi mata daxu..daure fuskanta tayi ta wani kauda kai gefe tana harare harare..shima ya daure nashi fuskan dan yasan idan ba haka yayi mata ba tsaf zata sake cire hulan ta bar gashi a bude tunda ba hankali ne ya isheta ba..Nur dai na tsaye gefe yana kallon ikon Allah..mamaki yake na ganin yanda Bobby ya wani hade rai yana mata fada kaman ba shine yake kokarin sa mishi kuka ba daxun sbd ita ba..wato har yanzu dai wnn ki fadin nashi yana nan baije ko inaba..idan ba haka ba why kaida ke dab da shiga matsala sbd son yarinya kuma still kanada kafin hali daure mata fuska haka...karasawa yayi ya durkusa nan kusa da ita yana kallon legs dinta dake nan kan gadon yanaso ya gane wadda take ciwon a ciki amma ya kasa..daga ido yayi ya dan kalleta sai kuma ya kawar da kan nashi jin wani bakon abu dake zagayawa cikin jikinshi..duban nashi ya maida ga Billy kafin yace"wanne kafan ne yake ciwo?"..a hankali tace mishi"na dama"..bai sake cewa komai ba ya juya yana kallon kafan damar nata..ganin bai ganin komai sai yakai hannunshi a hankali da nufin ya dago kafan Aysha ta saki wani irin kara tana fadin"Noo"..kallonta kawai yayi baice komai ba sai kuma ya mike still yana duban Billy yace"ki bata hijab tasa muje asibiti"..wara idanu Aysha tayi jin abunda ya fada idonta har ya cicciko da hawaye tace"nidai bazanje asibiti ba wlh..ni bazaa yi mun allura ba banaso"...kallon Nur Bobby yayi cikin sigar ka taimaka mun...Nur ya saki murmushi tareda karasawa inda take yace"Lamido ba allura za'a maki bafa..duba kafan kawai za'ayi ko da akwai matsala ta ciki"..yana rufe baki tace"nidai dan Allah banason zuwa sir..bazan iya takawa ba"..kallonta kawai yakeyi rungume da hannu ita kuma sai tayi kasa da ido tana goge tears dinta tace"to zanje..amma dan Allah banda allura wlh ciwo yakemun"..Nur yace"baza'ayi maki allura ba inshaAllah..yanzu matron da Billy zasu taimaka maki ki mike tunda bazai iya tafiya ba"..batace komai ba sai hawaye data cigaba dayi..tsoro takeji kar suje suyi mata allura ita dai..a muguntan Dr Bobby tasan wlh da kyar idan baiyi mata allura ba tunda baida imani...Billy ce ta dauko hijab ta saka mata snn suka kama hannunta itada matron din don fita da ita waje...taku daya ta iyayi ta saki wani kara da saida Bobby yaji shi har cikin zuciyarshi...nan da nan saiga hawaye a fuskanta ta shiga kokarin durkushewa nan kasa sbd azabar zafi da taji har cikin bones dinta...girgiza kai kawai take murya can kasa tace"bazan iyaba"..kallonta duk suka tsaya yi harda Bobby da yakejin kukan nata har can cikin ranshi..ji yake kamar yaje ya sungumeta yayi waje da ita amma ba halin yin haka...sai da kyar da taimakon Billy suka samu ta yadda ta mike suka riketa har zuwa inda sukaƙi parking...kafin su karasa Nur ya bude musu kofa dan haka suna zuwa suka Sanya ta ciki Billy ma ta shiga suma suka shiga snn Nur ya tada motar suka tafi...Bobby dake zaune front seat jingina kanshi jikin kujeran yayi tareda lumshe idanu..jin kukan nan nata yakeyi har cikin zuciyarshi yayinda wani irin zafi da kunchi suke sake rufe shi..Allah kadai yasan yanda yakeji nunawa ne kawai baiyi amma yana cikin matsala gagaruma ma kuwa...kasa cigaba da hakuri yayi ya juya yana kallon yanda take rikeda kafan tana kuka..murya can kasa yace"kukan ya isa haka dan girman Allah"..ko kulashi ba tayi ba ta cigaba da kukan ta...a takai ce har suka isa Freedom bata bar kuka ba...Bobby duk ya rikice ya tasa inda zai tsoma kanshi yaji dadi..Nur na gama parking duk suka bude mota suka fito banda ita da ko motsawa ba tayi ba...Billy ta zagayo ta bude mata kofa tareda kamo hannunta tace"ki daure mu karasa ciki"..rike hannun nata tayi snn ta sakko da kafan a hankali sai kuma ta gagara mikewa..Nur dai na tsaye yana kallonsu shi kuma Bobby ganin sake bata musu lokacin take kawai ya karasa wurin baiyi wata wata ba ya daga ta cak ya nufi cikin asibitin da ita..sai ihu taka tana ita ya sauketa amma ko tanka mata baiyi ba har ya karasa office dinshi su Billy na binsu a baya..Nur ya karasa ya bude office din suka shiga..kai tsaye ya direta kan gadon dake nan cikin office din fuskan nan a daure kamar bai taba dariya ba...yana ajiye ta ya bude wani drawer ya dakko wani muscle pain killer ya ajiye kan trolley snn ya shiga bathroom ya zuba ruwa cikin wani bowl mai zurfi ya hada da towel dan karami snn ya dawo dakin..daga Nur har Billy kallonshi kawai suke ba wanda yace kala..kujera ya janyo ya zauna nan kusada ita snn ya zaka towel din cikin lukewarm watare daya debo ya matseshi snn ya kama kafan nata ya rikeshi da kyau yanda bazata iya kwacewa ba ya shiga danna mata towel din a wurin..banda ihu da musu mutsu ba abunda take amma ta kasa kwace kafar daga hannunshi sbd rikon da yayi mata bana wasa bane..danna mata kawai yakeyi ba tareda ko kallonta yayi ba sbd gudun abunda hakan zai haifar mashi..yasan idan ba haka yayi mata ba ba bari zata yi ayi mata abunda ya dace ba and Allah ya sani bazai taba samun sukuni ba idan ba gani yayi kafan nata ya warke gaba daya ba..idan zai biye ta zuciyarshi nan ma bazai iya mata abunda ya dace ba kuma shidai akan ya bari wani ya tabata gwara shi yayi mata duk abun daya kama ta idan yaso daga baya sai yayi aikin rarrashi dan dai yasan rigima ne zai sashi kamar ba gobe..tunda ya fara bai saurara mata ba sai da ya tabbatar kafar ya gasu snn ya kyaleta..ya dauki towel da bowl din ya maida su bathroom ya dawo sai kuma ya dauki maganin da zai shafa mata a kafar yana kallonta..kuka take yi sosai har numfashinta na seizing kamar zai dauke..ga wani uban zufa data hada sharkaf kaman wanda aka gasata a oven..tausayinta yaji ya kama shi ganin yanda take kuka yasan dole zataji zafi amma ya zaiyi?..shima ba a son ranshi yayi mata haka ba babu yanda zaiyi ne kawai..janyo kujeran yayi a hankali ya zauna still yana kallonta duk sai yaji ya kasa aikata komai..juyawa yayi ya kalli Nur wai ko zai taimaka mashi amma sai yaga shi dariya ma yakeyi abun shi sai kuma ya juya ya fita daga office din...Billy ma ba tayi wata wata ba tabi bayanshi don Allah ya gani bazata iya zama nan ciki ba...juyawa yayi yana kallonta suna hada ido ya dauke nashi da sauri ya shiga matsa maganin a hannunshi..sam baison wnn raunin dake kokarin dakatar dashi ne...runtse ido yayi ya bude snn yayi watsi da raunin dake dake kunno mishi kai ya kamo kafan nata a hankali zai shafa maganin kawai sai yaji ta kanakameshi tana sakin wani marayan kuka..lumshe ido yayi yanajin wani irin yanayi a cikin jikinshi...wani irin weird feeling da bai taba tsintan kanshi ciki ba..cikin muryanta da bai fita sosai tace"sir dan Allah..dan Annabi kayi hakuri"...lumshe ido ya sakeyi yanajin zuciyarshi na wani irin tattarewa ya cunkushe can wuri daya yana bugawa da mugun karfi...a hankali yakai hannunshi ya zagaye bayanta dasu bakinshi saitin kunnenta yace"am..sorry..plss"gyada kai kawai takeyi tana cigaba da kuka tace"toh bazaka shafamin ba koh?.."dagota yayi daga jikinshi yayi cupping fuskanta yana kallon cikin idonta yace"hakan bazai yiwu ba Aysher..kiyi hakuri a shafa maki ko yayane zakiji sauki"..girgiza kai ta shiga yi tana cigaba da hawaye tace"dan girman Allah No..mutuwa za.."bata karasa ba ya rufe mata bakin yana girgiza kai duk ya gama goge maganin hannun nashi a jikinta...kamata yayi ya kwantar da ita kan gadon snn ya sake matsa maganin a hannu yayi saurin kama kafar ya shiga murzawa a hankali..banda kuka da ihu ba abunda Lamido take har wani shidewa take sbd azaba shi kuma bai saurara mata ba saida ya tabata maganin ya shiga ciki snn ya ajiye kafar..har yanzu kuka takeyi tana sauke ajiyar zuciya shi kuma ya kama hannunta a hankali ya sake cewa"am..so..sorry love"..ko sauraranshi ba tayi ba ta kwace hannunta tana cigaba da kuka shi kuma yayi tagumi kawai yana kallonta..Allah kadai yasan yanda kukan nan nata ke daga hankalinshi..ita kanta da tasan yanda yakeji idan tanayi da batayi ba ko dan sbd shi...haka yayita kallonta tana kuka da yayi yunkurin taimaka mata zatace bataso..duk tabi ta sake daga mishi hankali da kukan nata..saida bacci ya dauketa snn ya sauke ajiyar zuciya..mikewa yayi daga inda yake zaune ya leka ya tabbatar baccin tayi da gaske snn ya gyara mata kwanciya a hankali yanda bazata tashi ba..lumshe ido yayi yakai lips dinshi forehead dinta ya manna mata peck a hankali murya can kasa yace"get well soon love..i love you"..daga haka ya gyara mata kafar snn ya janyo kujeran dab da ita ya zauna tareda rike hannunta cikin nashi ya dora kanshi gefen gadon shima daga haka bacci ya sadado yayi awon gaba dashi.
Nur na barin office din dama kai tsaye inda ya ajiye motarshi ya nufa ya bude ya shiga ciki sai ga Billy itama ta karaso ta dan langabe kai tace"sir nima ka ajiyeni hostel plss"..kallonta yayi kafin yace"why?..bazaki bari ku koma tareba?.."da sauri tace"nasan proprietor zai dawo da ita sir dan Allah ka mai dani"..bai sake cewa komai ba ya bude mata motar yace"to shigo"..ba musu ta shiga ciki Nur ya tayar da motar suka fita daga asibitin.
Karfe sha daya da kusan rabi Lamido ta shiga bude idonta a hankali har ta waresu fes akan Bobby da har yanzun kanshi ke kife nan kusada ita yana nashi baccin..zare idanun tayi da kyau tana kallonshi da mamaki ganin ya wani kwakwume mata hannu ya rike cikin nashi..daddagewa tayi ta kwace hannun nata tana zabga masa harara kamar idonta zasu fadi kasa..daidai lokacin shima ya farka tareda dago kanshi a hankali sai yaci karo da nata idon tana hararanshi...baice komai ba ya mike da sauri ya fada bathroom..wanko face dinshi yayi ya fito sai yaga ta hade kai da gwuiwa kamar zatayi kuka...da sauri ya karasa inda take ya zauna nan gefen gadon yana dubanta a hankali yace"what again?.."dagowa tayi tana kallonshi fuska daure tace"ni ka mai dani hostel"..kallonta ya tsaya yi for some secs kafin ya hada hannayenshi waje daya in a pleading tone yace"nace fa am sorry..da gaske bazan kara ba kiyi hakuri plss"..batace komai ba sai juya mishi baya da tayi zata fara hawaye yace"idan Allah noo..please am sorry..ki yafemin"..goge hawayen tayi kafin ta juyo ba tareda ta kalleshi ba tace"to ka mai dani hostel nidai"..yace"zakiyi hakuri ki dena fushi?.."gyada mashi kai tayi..da sauri yace"thank u so much"..tana turo baki tace"kuma kada ka sake tabani nidai"..yace"ban karawa inshaAllah..ki tayani da addu'a"..da mamaki ta kalleshi tace"addu'an me?.."shiru kawai yayi yana kallonta dan baisan yaushe mgnr ya fito ba..a hankali yace"kafan yayi sauki?.."still kai ta daga mishi tana cigaba da turo baki shi kuma sai yayi kasake yana kallonta kaman wani soko..kallonta yakeyi full of love and affection..yarinyar na burgeshi fiyeda tunanin mai karatu..komai tayi burgeshi yake sai yaga tana kyau da duk wani abu da tayi shiyasa yake kishinta sosai...a yanda yake kishinta shi ko cewa za'ayi babu wanda zai na kallonta duk dunia sai shi kadai so zaiyi amma yasan hakan ba mai yiwuwa bane...agogon hannunshi ya duba yaga its almost 12 and Allah ya sani yana tunanin yanda zai maidata hostel cikin daren nan dan yasan Nur da kyar idan ba tafiya yayi ba..dagowa tayi ta kalleshi zata sake mgn wayanshi dake cikin aljihu ya fara ringing..ya zaroshi da sauri ganin Mummy ke kira yayi picking tareda kaiwa kunne..a daya bangaren Mummy tace"kana kina Bobby?..ya jikin nata?.."yace"da sauki Mummy"..tace"ka tabbata da sauki ba wani problem din?.."yace"yes Mummy"..sai kuma ya juya yare zuwa igbo yace mata"Mummy babu mota hannuna and inaso in maidata hostel yanzu..Nur ya wuce tun daxu"..Mummy tace"saidai in turo Sab ya kawo maka..amma why not ka bari ta kwana asibitin sbd a sake tabbatar da samun saukin nata..kuma ga dare yayi"..ajiyar zucia ya sauke yana kallon Aysha da tayi masa kuri da ido tana kallonshi jin ya wani canxa yare cikin ranta tace"dan kyar idan ba gulamana yakeba wlh..inyamurin banza"..ba tareda ya dauke idonshi daga kanta ba yace"bazata yadda ba Mummy..nima kaina ba son zuwa hostel din nasu nake da daren nan ba amma idan ban maidata ba daga min hankali zata yi nasani"..shiru yaji Mummy tayi kafin can tace"ko zaka kawota nan gida ta kwana zuwa safe ka maidata hostel din?.."shirun shima yayi kamar me nazari yace"anya kuwa zata yadda Mummy?..rigima zatai tayi wlh"..dan murmushi Mummy ta saki jin abunda ya fada kafin tace"ba rigiman da zatai inshaAllah..if tana kusa ka bata wayan muyi mgn"..bai sake cewa komai ba ya mika mata wayan yana dubanta a hankali yace"My Mom..wants to..talk to u"..batayi musu ba ta karba tana turo baki tasa wayan a kunne..Mummy tace"daughter ya jikin naji?.."da sauri tayi kasa da kai kmr Mummy na ganinta tace"Mama ina yini"..Mummy daketa faman smiling tace"lafia lau daughter..ya jiki?.."tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"MashaaAllah..dama ce mishi nayi ya kawoki gida sbd dare yayi bai kamata yaje hostel dinku yanzu ba..snn ya sake duba kafan naki to make sure ba wani problem kuma..hope bazaki ce aah ba?.."Lamido tayi shiru tana tunanin amsar da zata bata..gani tayi gwara ta kwana gidan nasu akan dai ta kwana asibiti..afterall ba daki daya zasu kwana ba dan haka bazata damu kanta ba...saida Mummy ta sake mgn snn a hankali tace"toh Mama"..Mummy tace"nagode sosai daughter Allah miki albarka..yanxun zan turo Sab da mota yazo ya dauko ku"..Aysha tace"toh"..daga haka kuma Mummy ta kashe kiran..ajiye wayar tayi tana kallonshi kama zatasa kuka tace"shine zaka hadani da mamanka koh?.."murmushi ya saki kafin a hankali yace"am sorry"..turo baki kawai tayi ba tace komai ba..shi kuma sai ya cigaba da kallonta before saying"kinci abinci?.."banza tayi mashi kamar bataji ba..ya sake cewa"Aysher am talking"..nan ma shiru ba mgn dan haka ya dan daga murya yace"Lamidooo"..juyowa tayi a fusace tana kallonshi tace"ni banaso"..kmr wani abun tausayi yace mata"am sorry tou..zakici abinci?.."ta girgiza kai alamar no snn ta sake komawa ta kwanta..shima baice mata komai ba sai kallonta kawai da yakeyi kamar yau ya fara ganinta...after like 20 minutes Sab ya iso asibitin bai shigo ciki ba ya kirashi a waya ya fada mashi ya karaso dan haka ya mike ya isa inda take bayan ya tattaro mata takalmanta dake kasa yace"get dawn mu tafi..ya iso"..ba tace komai ba ta sauka daga gadon ta zura takalmanta snn ta shiga takawa a hankali sbd zafi da taji kafan na mata..daxun da yake kwance take sai bataji ciwon komai ba amma yanxu zafi takeji sosai saidai bai kai na daxun ba tunda tana dan iya takawa...ita ta wuce gaba Bobby na binta a baya har suka fita waje..ko yaya ta danyi kwakwaran mosti sai yaga kaman faduwa zatayi bai dai yi kokarin riketa ba har suka iso parking lot..Sab na hangosu ya fito ya bude musu motar..tana karasowa ya nuna mata front seat yana fadin"sannu"..wani harara Bobby ya sakar masa kafin ya bude back seat ya zurata ciki shi kuma ya shiga front seat din Sab dake murmushi ya shiga driver seat snn ya tayar da motar suka tafi...baya cikakken minti biyu bai juya ya kalleta ba..gaba daya hankali da zuciyarshi suna gareta..gani yake kmr wani abu zai faru da ita idan baya gani shiyasa yake juyawa akayi akayi..Sab dai driving dinshi yakeyi amma a karon farko yau yaga wani irin canji tattare da yayan nashi kuma dukda Mummy bata sanar dashi wacece Lamido a wurinshi ba shi ya gama tabbatarwa kanshi matsayinta sbd wnn special attension da Bobby yake bata bana wasa bane..ba ko wane ordinary mutum ake bama wnn attension din ba sai mutumin da ake mutuwa so da kauna shi kuma ya tabbata Uncle Bobby son yarinyar nan yake...haka har suka karasa gida ba wanda yace tak a cikinsu sai Bobby daketa faman juyawa yana ganin halinda take ciki sai kace wadda take labour...Sab na gama parking ya bude mota ya fita shima Bobby ya fita snn ya zagaye ya bude mata kofa yana dubanta a hankali yace"to sauko"..ba musu ta fito daga motar tana wani dangale kafa kmr mai karaya a jiki..taku daya biyu tayi sai ta koma da sauri ta zauna cikin motar da bai riga rufe kofar ba tana girgiza kai idonta har sun ciko da hawaye tace"bazan iyaba"..kallonta kawai Bobby keyi yana mamakin taki irin nata..durkusawa yayi nan inda kafan nata yake yana kallo shidai baiga wani alamun har yanzu yana ciwo ba tsabar langwai ne kawai irin nata..shi baisan yanda za'ayi duk ranar da akace ga Lamido a labour room ba..kilan saita daga hankalin kowa kafin ta haihu..tunanin haka ya sashi sakin murmushin da bai shirya masa ba kafin ya kama kafan a hankali ya shiga tofa mata addu'a akai
Book Chapters
Chapter 30
Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59