gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Dr.bob Complete Hausa Novel by by Aysha Rano Chapter 55 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara kishi dashi?.."a hankali ta girgiza mashi kai alamar no..yace"then meyasa kike mashi abubuwan da ni kadai ya kamata kiyima a matsayina na mijinki?..kina tunanin bana jin haushi ne?.."a hankali ta dago kanta tana kallonshi shi kuma yayi cupping fuskanta yana cigaba da kallonta yace"if u think bana jin haushi u are very mistaken baby..kishi nakeji sosai duk naga kina mishi wnn shagwaban..banaso"..hannunta ta mika itama tayi cupping nashi fuskan tareda dan dage ta manna mishi peck a forehead snn tace"to na dena partner..am sorry".. pecking nata back shima yayi yana cewa"na hakura love..yanxun yaushe ne zasuzo?.."da sauri ya dago taga jikinshi tana cewa"gobe..inaso in kira Ammi ince ta barsu su kwana yace saidai inyi mgn da ita"..ba musu ya kama hannunta suka zauna snn ya mika mata wayarta dake hannunshi yace"ohk call her"..da sauri ta karba tayi dialing number din Ammi..tana dagawa Aysha ta wani marairaice tana langabar da wuya kmr Ammin na ganinta tace"Ammi banida lafia"..daga daya bangaren Ammi tace"Amin wa'alaiki salaam"..da sauri ta gyara mgnrta da cewa"sorry salamu alaykum Ammi"..Ammi tace"wa alaiki salaam..ya gidan"..tace"lafia lau amma banida lafia"..ta karasa mgn kmr zatasa mata kuka ta wayar..Ammi tace"rashin lafiar kikema wnn abun sbd har yanxu bakida hankali"..turo baki tayi tace"Ammi zazza6i nakeyi sosai fa..kuma hadda amai"..Ammi tace"to Allah ya sawake..laifin Bobbyn ne da bai danqara maki allura ba"..daria sosai mgnr Ammi ya bata aikam ta shiga yinta kmr ba gobe..Saida tayi me isarta snn tace"Ammi wai su Husna zasuzo gobe?.."Ammi tace"eh zasuzo inshaAllah..tareda Bilkisu da Najeeb"..Aysha tace"Ammi dan Allah dan annabi su kwana"..Ammi tace"aah Aysha su da zasuzo da yawa banason suzo su takurama mijinki ne gwara suzo a goben su dawo ai yafi babu"..da sauri tace"Ammi dan girman Allah su kwana shida bama a dakina yake kwana b.."bata karasa ba Ammi tace"zakici ubanki wlh..wa kikaji ya tambayi inda yake kwana..wato har yanxu wnn shashancin yana nan kanki koh?.."shiru tayi tana danne dariarta tace"to Ammi kiyi hakuri..amma dan Allah su kwana ai munada dakuna da yawa"..Ammi tace"shknn sai suyi kwana biyu..dama shi Najeeb yace akwai aikin da zaiyi a garin na kwana biyu so idan ya gama sai su dawo tare"..cikeda farin ciki tace"yauwa Ammi nagode sosai Allah ya kara girma..Ammi kema dai ya kamata kizo wlh"..Ammi tace"zanzo amma ba yanxu ba..saiki daure ki dinga shan magani ba sai ama tilastaki ba..Allah ya baki lafia ya maku albarka gaba daya"..cikin tsananin jin dadin addu'an na Ammi tace"Ameen Ameen Ammina..nagode"..Ammi tace"shknn sai anjima..ki gaida Bobbyn dasu mamanshi"..da sauri tace"zasuji inshaAllah..sai da safe"..daga haka sukayi sallama..Bobby kmr jira yakeyi ta ajiye wayar ya shiga kyalkyala mata daira sosai..dama da dadewa ya fuskanci there is a little drama between the mother and the daughter..hakan kuma its the sign of love they have for each other..yanda ta dauko zancen ba'a dakinta yake kwana ba ita kuma Ammin ta katseta was so very funny to him..kallonshi tayi yanda yake mata daria tana dukan chest dinshi tace"what?.."ya kama hannunta ya rike yana kokarin dakatar da darian nashi yace"nothing baby..kawai dai am happy gobe su Husna zasuzo"..lokaci daya ta washe bakinta itama tace"nima am happy sosai sbd nayi missing dinsu..i can't wait to see them"..tana rufe baki ya dauketa suka fita daga dakin yana cewa"yanxun muje ki karasa cinye apple dinki sai muje mu kwanta sbd mu tashi da wuri koh?.."kai ta gyada tana sake lafewa a jikinshi..daga haka suka fita daga dakin..parlor ya koma ya dauki sauran apples dinta snn ya wuce flat dinshi..zaunar da ita yayi kan sofa tareda dora mata plate din apples din akan laps dinta yace he's coming..parlor ya koma ya kashe su tv da bulbs snn ya rufe gidan da key ya koma flat din nashi..kwanciya yaga tayi bayan ta ture apple din nata gefe..ya karasa da sauri ya dagota yana cewa"baby what?..why baki cigaba da cin apple dinki ba?.."hannunshi ta kama ta dora a forehead dinta idonta har ya ciko da hawaye tace"kaji fevern nefa zai dawo"..da sauri ya zauna tareda dorata a jikinshi yana girgiza mata kanshi yace"no don't cry plss..bazai dawo ba inshaAllah"..kuka ta fara mishi sosai tace"Allah zai dawo..yanxu haka su Husna zasuzo gobe ni banida lafia"..rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta cikin sanyin murya yace"baby dan Allah stop crying..idan kina kuka zakiyi ciwon kai fa"..shiru tayi mishi tana cigaba da hawayenta as Allah kadai abunda takeji..nan take hankalinshi ya tashi ya shiga aikin rarrashi..gani yake kmr wnn kukan zaiyi affecting babyn cikinta..yasan yanda baason pregnant woman da damuwa shiyasa yake tsoron wnn halin nata.. yanxu idan wani abu ya samu babynshi ya zaiyi?..lalla6ata ya dingayi sosai har tayi bacci a jikinshi ya samu ya kwantar da ita..har zuwa lokacin kuma jikinta akwai zafi sosai dan zafin ma yafi wanda yaji a jikin nata daxun..lumshe ido kawai yayi yana tunanin taimakon daya kamata ya bata..yasan babu treatment din da zai dauke mata wnn zazza6in indai ba lokacin daukewan shi ne yayi ba..gashi kuma yanxu tunda yasan tanada ciki dole bazai dinga bata drugs anyhow tana sha ba tunda yafi kowa sanin illar hakan..addu'a kawai yake kada Allah ya dora mata laulayi mai wahala dan baisan yanda zaiyi da ranshi ba..shi kanshi yasan daga mashi hankali zata dingayi da wnn koke koken nata shiyasa yake fatan Allah ya bata mai sauki yanda bazasu sha wahala sosai ba..ya dade nan zaune yana kallonta saida dare yayi nisa snn ya samu ya gabatar da sallah shima ya kwanta nan kusada ita tareda sanyata a jikinshi.

Washegari har wajen goma bata tashi ba sbd baccin da bata samu tayi sosai ba jiya..Bobby na nan zaune yana kallonta ko nan da can ya kasa matsawa sbd gudun kada ta tashi baya kusa..saida yaga rana ta farayi gashi kuma yau Friday snn ya samu yayi wanka ya shirya kanshi cikin farin shadda da akama dinkin kaftan..yasa hula white sai takalmin kafarshi shima white..bayan ya gama feshe jikinshi da turaruka ya dauki wayarshi ya fita sbd kiran da Nur keta mishi tun daxun..yana fita parlor yayi picking call din yana cewa"yane"..a daya bangaren Nur yace"normal..ya jikinta?.."a hankali yace"gata nan dai wlh..har yanxu tana kwance".. Nur yace"subhanallah zazza6in dai?.."zaunawa Bobby yayi kan one of kujerun parlon before yace"shine fa..amma dai yanxu naji da sauki sosai..bata samu bacci bane jiya shine yanxun take ramawa"..Nur yace"ohk Allah ya kara sauki..gashi kuma kace yau zatayi baqi koh?.."Bobby na shafa kanshi yace"sun kusa zuwa ma yanxu haka..kana ina yanxu?.."Nur yace"ina shiryawa kafin sallahr jumu'a".. Bobby yace"alright mu hadu a masallacin nima yanxu zan fito"..yace"alright sai ajima"..shima yace"sai anjima"..daga haka suka aiye waya..Bobby ya sake komawa dakin har lokacin bacci takeyi..ya taba forehead dinta yaji babu zafi sosai sai ya gyara mata kwanciya tareda pecking forehead dinta snn ya dau keys dinshi ya fita zuwa main house..bayan sun gaisa da Mummy yace mata zaije masallaci daga nan zai biya eatery ya siyo ma su Husna abinci tace he shouldn't buy anything tasa ayi musu girki sbd tasan dama Ayshan ba lafia..godia yayi mata sosai snn ya mata sallama ya fita bayan yace Miemie ta dinga shiga tana duba mashi ita time to time idan ta tashi ta kira ta sanar dashi.

Around 2:17 su Billy suka shigo Kanon Dabo.. Husna ce ta kira Bobby ta sanar dashi karasowarsu yace su karasa gida shima yanxun zasu wuce..kusan a tare motocinsu suka yi parking a compound din gidan..nashi da na Nur sai kuma na Hamma Najeeb da sukazo a ciki..shi ya fara fita ya nufi inda suke sukayi musabiha da Najeeb snn yace su shigo su fara gaisawa da Mummy sai suje inda Aysha..Mummy ta tarbesu da farin ciki sosai suka gaisa tana tambayarsu ya Ammi da daddy suka amsa da suna lafia..bayan Miemie ta gama setting dinning tace suje su fara cin abinci kafin Aysha ta tashi daga bacci sai suje itama su gaisa.

Bayan sun kammala suka nufi gidan nasu gaba daya tareda Najeeb dake sauri ya wuce aikinda ya kawoshi...suna shiga compound Yusra tayi saurin kwace hannunta cikin na Billy ta shiga cikin gidan da gudu tana kiran"Addah..Addah"..da sauri Bobby yabi bayanta gudun kar ta tasheta a bacci..suna shiga parlor yace they should make themselves comfortable shi zaije ta fito musu da ita..Husna ta bishi da kallo tana kunshe daria tace"Allah sarki Uncle Bobby..da gani Adda ba karamin wahalar dashi takeyi ba"..Miemie dake kusa da ita ta dan matsar da kunnenta kusa da nata tace"ke batada lafia"..da sauri Husna ta juya tana kallonta tace"da gaske?..ko ciki ne da ita?.."gyada kai Miemie tayi tana sake yin kasa da murya tace"but don't tell anybody oo.. Uncle Bobby might slaughter me"..hada ido sukayi suka tafa Billy dai kallonsu kawai take tana mamakin yaushe suka zama kawaye...Bobby na shiga dakin yaga kan gadon wayam dan haka ya bude bathroom da sauri ya shiga sai ya ganta tsaye jikin sink ta zubama mirror idanu tana hawaye..da sauri ya karasa tareda janyota jikinshi hankalinshi har ya fara tashi tace"what?.."goge tears dinta tayi tana girgiza masa kai..rikota yayi ya fito da ita snn ya zaunar da ita gefen bed shima ya zauna yana rikeda hannunta yace"baby menene plss?..akwai inda ke maki ciwo ne?.."girgiza kai ta sakeyi tana cewa"No"..hannu yakai ya karasa goge mata tears din snn yace"kinga su Husna sunzo dan Allah ki bar kukan nan indai baso kike suyi tunanin wani abu ke damunki ba"..kai ta sake gyada mishi without saying anything..shi kuma yayi pecking cheeks dinta snn ya mike yana cewa"let me get u something to wear sai muje parlor ku gaisa dasu"..kallonshi kawai tayi batace komai ba shi kuma ya fita da sauri zuwa bedroom dinta don dauko mata kayan da zatasa..tagumi tayi da both hands dinta tana tunanin abunda ya dameta..lissafi tayi yau kusan 2 weeks knn ya kamata period dinta yazo amma baizo ba sai kuma ga fever ta farayi da amai..dukda ba test tayi ba tanada tabbacin morning sickness take..tasan ciki ne da ita wlh.. musamman data tuna yanda suka rungumi juna suna farin ciki jiya a hospital sai ta sake tabbatar da zarginta..kawai gani takeyi baici ace ta samu ciki yanxu ba..Ina ma laifin tayi ko 6 months ne idan batayi 1 year ba amma wai ciki tun yanxu knn dai haihuwan 9 months din da bataso shi zatayi and Allah kadai yasan what will people say about her..kilan haka za'a zauna ayita gulmarta kaman yanda take zama tayi na mutane itama..ita bawai haihuwan ne bataso ba kawai bataso mutane suce daga yin bikinta ta samu ciki sai kace dama jira take..tayi nisa cikin tunani har batasan time din da ta fara hawaye ba..she knows for sure yasan da mgnr cikin yana sane ya boye mata..bayan few minutes ya dawo da kayan nata a hannunshi..ya taimaka mata tasa snn ya dan gyara mata fuska yanda bazasu gane tayi kuka ba ya kama hannunta suka fita zuwa parlon.















Rano✨




Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
67
Hannunta na cikin nashi har suka shigo cikin parlon..tana hada ido dasu Husna batasan sanda ta kwace hannunta daga nashi tayi saurin karasawa inda suke kawai sai ta shiga kokarin daukan Yusra da itama tana ganin nata ta taso cikin farin ciki sosai take cewa"Habibty"..itama Yusra rungumeta tayi tana daria tana kuma jin yanda har yanxu take kokarin dagata amma ta kasa..ta dago tana kallonta tana daria tace"Addah bazaki iya daukana ba yanxu"..da sauri Bobby daya karaso ya zauna kusada Nur yace"tell her"..Aysha tayi pecking forehead dinta snn taja hannunta suka zauna tana cewa"I missed u guys sosai wlh"..itama Yusra zaunawa tayi kusada ita tace"muma munyi missing dinki Addah"..daga haka ta juya tana kallon Billy data wani kura mata ido tana kallonta tace"what?."Billy tace"aah me kikaji nace?.."dan murmushi ta saki tareda matsawa tayi hugging dinta itama tana cewa"nayi missing dinki"..Husna da tun daxun bakinta ke kaikayi ganin hug din nasu bana kare bane tace"Adda kinga yanda kikayi kyau kuwa..kinyi wani fresh kin canxa"..juyawa Aysha tayi tana kallonta sai kuma ta dungure mata kai tana murmushi tace"idan bakiyi haka ba ai ba sunanki Asma'u Lamido ba"..Husna da har yanxu ke murmushi itama tayi hugging dinta tana cewa tayi missing dinta..Hamma dai na zaune yana kallon wariyar launin fata..saida ta gama da kowa snn ta dawo da kallonta gareshi tana wani murguda baki tace"ba ruwana ni dakai"..daria ya saki tareda juyawa yana kallon Bobby yace"inaga saika lamarin nan Dr..wnn matar taka rikicinta yawa ne dashi wlh"..dan murmushi Bobby ya saki yana kallonta yace"baby C'mon mana..ko me yayi ai yakamata ya wuce tunda har ya taso yazo inda kike"..da sauri Najeeb yace"exactly..kuma bayan zuwa ma har matata na kawo mata da qannena amma still take cewa ba ruwanta dani"..ya karasa mgn yana kashe ma Billy dake kallonshi idanu..tayi saurin kawar da kan nata tana daria..ita bazata iya wnn abun nashi ba..Lamido kuwa tasowa tayi daga inda take ta dawo nan kusa dashi ta zauna tana kallonshi da smile din nan nata dake sa both dimples dinta fitowa tace"to Hamma sannu da zuwa..Ina yini"..juyawa yayi yana kallonta da kyau shima yace"lafia lau my Maama..hope kina lafia"..tace"am fine..ya aiki".. yace"Alhamdulillah"..juyawa tayi ta kalli Billy da wani dan iskan murmushi snn ta sake dawo kallonta gareshi tace"Ya Billy?.."kallon Billy shima yayi kafin ya dawo da dubanshi gareta yace"aminiyarki ce ai..so Kunfi kusa"..da sauri tace"aah wlh ni Kunfi kusa yanxu"..daria ya saki yana girgiza kanshi yace"yanxun dai tunda na kawo maki su i have to take my leave"..da sauri ta mike tana marairaicewa tace"ko ruwa fa baku sha ba..kuma ni banyi girki ba"..Najeeb yayi relaxing yana cigaba da kallonta yace"kuma gaskia yunwa mukeji"..sake marairaicewa tayi tana kallonshi sai kuma ta juya gasu Billy suma duk tana sunyi wani kalar tausayi Husna hadda cewa"yanxu Adda mu taso gari ya garara tun daga Gombe muzo gidanki amma ko abinci bakiy mana ba..gaskai saina fadawa Ammi"..hankalinta ya sake tashi jin tace zata hadata da Ammi tayi rau rau da ido kmr zatasa kuka tace"ai dai banida lafia"..daga haka ta juya zata nufi kitchen Bobby yayi saurin mikewa ya kamota yana fadin"baby wasa fa suke maki sunci abinci"..dagowa tayi tana kallonshi a hankali tace"da gaske?.."hannu yakai yana goge mata dan guntun hawayen daya gani a Idonta tace"da gaske nake mana..Mummy tasa anyi musu abinci"..rungumeshi tayi da karfi tana sakin murmushi tace"Allah ya sakama Mummy da aljannah"..ya dagota yana jan dogon hancinta yace"Ameen Ameen love"..daga haka ya dawo da ita parlon sai taga duk suna mata daria..samun wuri tayi ta zauna tanata daure dauren fuska shidai Najeeb ya mike yace zai wuce don ana can ana jiranshi..sukayi sallama da Bobby da Nur snn ya fita su kuma suka bishi a baya..har mota suka rakashi suka sakeyi sallama snn suka dawo ciki shi Kuma yaja motar yayi gaba...suna dawowa Nur da gaba daya hankalinshi ke gare Miemie yace"pretty yau ba zuwa gidan aunty knn?.."da sauri Miemie ta dubi Aysha tace"zamuje mana..ko aunty Aysha?.."Lamido da taga yanda Bobby ya wani tsareta da ido yanason yaji amsar da zata bada ta hade ranta itama tareda fadin"eh mana"..tana gama fadan haka ta jasu suka wuce bedroom dinta Bobby yabisu da Ido..suna shiga ciki Nur ya kwashe da wani daria yana cewa"tofa kai saidai kayi hakuri na yan kwanakin nan dan naga alama Lamido tunda ta samu mutanen nan mantawa zatayi dakai"..harara mai kyau Bobby ya watsa mashi yana cewa"do u know ur problem?.."Nur yace"nope"..Bobby yace"dan iska ne kai wlh..kuma a haka kake tunanin zan dauki 'yata in baka..u better wake up dan idan ba canxa hali kayi ba tsakaninka da Miemie saidai kallo daga nesa"..ya karasa mgn yana wani daure fuska kai kace da gaske yake..shi kuma Nur nan take ya shiga hankalinshi sai ya hau bashi hakuri yana cewa"kaifa matsala na dakai bakasan wasa ba"..kallonshi Bobby yayi yana kokarin sakin dariar dake cinshi yace"inyamurin banza"..yana rufe baki shima Nur yace"Kai kuma bafulatanin banza ba"..gaba daya suka hada baki suka sheke da daria kaman wasu kananun yara..bayan sun gama Nur yayi saurin cewa"yauwa ya mgnr cikin?..did she knows?.."a hankali Bobby yace"anya kuwa?..i don't think so..kawai nidai addu'a nake koda ta gane kar ta daga hankalinta da yawa"..dafashi Nur yayi ganin kmr abun na damunshi yace"don't worry bazata damuba inshaAllah..mutum nawa ne ke neman haihuwan basu samu ba so ita da Allah ya bata am sure bazata kasa nuna farin ciki ba"..gyada kai kawai Bobby ya iyayi yana cewa"i hope so".

Suna shiga daki Aysha da Billy suka baje kan gado suna hirar yaushe gamo yayinda su Miemie,Husna da Yusra suka bar musu dakin suka shiga dayan bedroom dinta suma suka dasa nasu labarin..yanda Husna da Miemie suka sake da juna zakayi tunanin tun tasowarsu dama suie qawance while ba haka bane..kawai hali ne yazo daya shiyasa qawancen nasu yayi daidai..har yamma yayi suna nan suna abu daya dan sallah kadai ya tada su shima suna idarwa suka sake dorawa daga inda suka tsaya..magrib na kawo kai jikinta ya fara rufewa da zazza6i wanda a daidai lokacin shima Bobby da suka fita da Nur tun daxun duk hankalinshi ya dawo gareta dan yasan daidai wnn lokacin zazza6in yake rufeta..sallama sukayi da Nur ya dawo gidan da sauri don yanaso yaga halinda take ciki..gashi yinin yau dama duk bataci wani abincin kirki ba..yana shiga ya iske Miemie da Husna sun wani baje a parlor suna labari suna kallo..suna ganinshi kowa ta shiga taitayinta har hada baki sukayi wajen fadin"Uncle Bobby sannu da zuwa"..yana dan murmushi yace"yauwa..Ina Bilkisu da Aysha?.."Husna tace"suna daki.. should i call them?.."yace"eh kice musu suzo"..da sauri ta mike zuwa bedroom din da suke ba'a dauk lokaci ba sai gashi sun dawo tareda su..tun daga nesa yake kallonta yana ganin yanda fuskan nan nata ke a daure yasan abunda ake gudu ya afku..suna karasowa ciki Billy na dan murmushi tace"Sir sannu da zuwa"..yace"yauwa Bilkisu..dama ce muku zanyi u should go get ready we are going out for dinner"..da sauri Miemie tace"Uncle Bobby Mummy tace an gama abinci fa"..kallonta yayi kmr bai gane me tace ba ita kuma ta sake cewa"tun daxu ta kirani tace zata aiko suwaiba ta kawo abincin nan..that ba sai Aunty Aysha tayi girki ba"..ajiyar zucia ya sauke yana gyada kai kafin yayi mgn Billy tace"Sir basai an kawo ba zamuje can muci"..tana rufe baki Husna ma tace"eh zamuje can Uncle Bobby"..kai kawai ya gyada tareda cewa"ohk"..yana kallon Lamido da har yanxu batasa baki cikin mgnr nasu ba..karasawa yayi inda take tsaye ya kama hannunta suka nufi flat dinshi..Husna tabisu da kallo tana murmushi Saida suka shige snn ta dawo da kallonta ga Miemie tana cewa"gaskia kuna ganin love a gidan nan..anya kuwa nima ba inyamurin zan samu in aura ba..naga kaman sunfi hausawa iya soyayya"..tana rufe baki Miemie ta sheke da daria tace"kamar a kunnen Uncle Bobby kika Fadi mgnr nan"..Husna ta wara ido da sauri tana cewa"ki rufamun asiri dan Allah in mutu maza su kaini ba yammata ba"..Billy dai daria ta saki tareda juyawa ta koma bedroom.

Suna shiga ya zauna nan parlor tareda zaunar da ita kusa dashi yana kallonta kmr zaisa mata kuka yace"zazza6in ne koh?.."Kai ta dora a shoulder dinshi tareda gyada mishi kai..a hankali yakai hannu yana shafa kanta yace"kiyi hakuri kinji..zai dena inshaAllah"..lumshe ido kawai tayi hawaye na cikowa cikinsu ta kira sunanshi"partner"..yace"na'am baby"..runtse idon ta sakeyi nan hawayen dake ciki suka silalo ka fuskanta tace"ciki ne dani koh?.."yayi shiru yana kallon spot daya kmr bazai ce komai ba sai can yace"who told u that?.."da sauri tace"i don't have to wait sai wani ya fadamun..i noticed some changes a tareda ni and koda banyi test ba na tabbata am pregnant..morning sickness nakeyi"..ta karasa mgn tana rushewa da kuka..da sauri ya juya tareda rungume gaba daya a jikinshi yana patting bayanta yace"stop crying plss"..batace mishi komai ba saida ta gama kuka iya son ranta snn ta sake dagowa tana goge tears dinta tace"kasan ciki ne dani koh?.."yayi mata shiru kawai dan baisan me zaice ba..ta shiga gyada kai tana cewa"ko baka fada ba nasan u knew it all along..ai jiya Ina kallon yanda kuke murna kai da Provost bayan an kawo result"..kallonta yakeyi har yanxu ya kasa cewa komai..saida ya bari ta gama mitarta tsaf snn ya mikar da ita tsaye yana cewa"now u need to stop talking..muje kici abinci sai kisha magani before fevern naki yayi yawa"..batace mishi komai ba itama tabishi suka fita daga dakin..gaba daya suka fita tareda su Billy zuwa main house tunda sunce a can zasuyi dinner...Mummy na ganinsu ta tarbesu da fara'a snn tace su karasa dinning ga abincin can..duk suka isa suka zazzauna Miemie na kokarin serving Husna tace a barta tayi..ba musu kuwa suka barta duk tayi serving din nasu suka fara ci shidai Bobby na tsaye kusada Aysha yana kallon yanda take ta faman jujjuya abincin ta kasa kaiwa bakinta..kujera dake kusada ita ya janyo ya zauna yana kallonta kmr zaisa kuka yace"eat mana baby"..kallonshi tayi a hankali sai kuma ta girgiza kai tace"bashi nakeso ba"..matsawa yayi kusada ita sosai tareda kama hannunta yace"then me kikeso?.."ta juya ta kalli su Billy taga duk hankalinsu naga abincin da sukeci snn ta dawo da idanunta gareshi tana wani hade rai tace"Custard zansha"..ya dan marairaice mata yace"amma baby custard kadai bazai rikeki ba tunda duk yau bakici abinci sosai ba"..kallonshi ta danyi yanda taga duk ya tashi hankalinshi sai ya bata tausayi dan haka ta sake janyo plate din abincin tana jujjuyawa tace"to zan faracin wnn idan mun koma sai insha custard din".. kanshi ya shiga gyada mata yana murmushi sosai yace mata"yauwa partner"..ta saki dan smile snn ta shiga cin abincin a hankali shi kuma yana aikin kallonta..ganin shi baida niyyar cin abincin ta juya tana dubanshi tace"kai bazaka ci ba?.."hannunta ya kama ya rike idanunshi a kanta yace"ni ke nakeso kici..banso kina zama da yunwa"..murmushi ta Kara saki snn ta maida plate din nan tsakiyarsu tasa mashi spoon tana cewa"to muci wnn din tare"..murmushin shima ya saki bayan yayi pecking hannunta snn ya dauki spoon ya shiga cin abincin shima..daurewa kawai take tana turawa amma ko kadan batajin dadinshi a bakinta..bayan sun kammala suka dawo parlor inda Mummy ke zaune tana jiransu suka dan taba hira bayan sunyi sallahn isha yace su mike su koma gida..Husna dai tace"Uncle Bobby nidai zan kwana a nan tareda Miemie"..Bobby na murmushi yace"to Mummy kinada baqi knn"..Mummy tace"aikam kin kyauta Asma'u dan da baki Fadi haka ba nasan ita kanta Miemien cewa zatayi a can zata kwana"..Aysha dai kunyarta takeji yasa ta kasa cewa komai..bayan sun mata sallama suka koma gidan tareda Billy da Yusra..duk yanda taso ya bari taje inda su Billy hanata yayi sbd fever dake sake sauko mata..dole tayi sallama dasu ta dawo dakinshi inda yake nan zaune yana jiranta...custard din da tace tanaso yaje ya dama ya kawo mata tasha sosai snn ya rage mata kayan jikinta suka kwanta..can dare ta tashi tana ta kwarara amai don kaf abincin da taci saida ta amayar dashi..duk hankalinshi ya tashi haka ya gyara wurin tsaf snn yayi mata wanka ya dawo da ita ya kwantar a kan gadon tanata faman kuka kmr karamar yarinya..hankalinshi yakai kololuwar tashi gaba daya ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi..da dadewa dama yasan zaisha fama da ita musamman daya fuskanci dan banzan raki ne da ita..dan ciwo karami da bai taka Kara ya karya bama langwai take mashi balle laulayi da kowa yasan yanda yake da cin rai musamman daya kasance shi ba wani specific magani yake dashi ba dole saidai mutum yayi hakuri har lokacin tafiarshi yayi..duk yanda yaso ko black tea ne tasha kasa Sha tayi wai idan tasha zatayi amai haka nan ya hakura ya kyaleta bayan ta gama kukan bacci yayi gaba da ita.

Wahsegari ta tashi normal babu fever as usual dama kullum kalau take tashi da safe sai dare yake sake dawowa..da kanshi ya mata wanka ya bata one of three quarters dinshi ta saka da wata shirt dinta dake dakin nashi snn ta fito zuwa wurin su Billy..da mamakinta sai taga suma sun tashi itada Yusra har ma sunyi wanka sun shirya..zama tayi suka fara labari kafin Kuma daga baya tace su shiga kitchen su fara girki don yau dai ba bazata bar Mummy da sawa ayi musu girki ba tunda ta

Please Login or Register in order to submit comment