You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
rufeta ruf..wato don rashin Imani kama gabanshi ma yayi ya tafi wani wurin sbd ya gama da ita..kuka takeyi sosai wanda sautinshi bai fita da karfi sbd zafin da jikinta yayi..shi kanshi kukan cikin karfin hali take yinshi don Allah kadai yasan yanda takeji..Bobby dake wanka a bathroom yana jiyo kukan nata ya zari towel dinshi ya fito da sauri ko karasa wankan baiyi ba sbd yanda hankalinshi ya tashi..karasawa yayi kusada ita ya zauna tareda dagota ya hadata da jikinshi yanajin yanda zafin temperature dinta har cikin jikinshi..a hankali ya ajiyeta tareda mikewa ya shiga closet dinshi ya jira jallabiya bayan ya zame towel din jikinshi ya fita da sauri zuwa main house don dauko drugs da injections daya kamata yayi mata..Saida yazo daidai kofan dazai maidashi gidan nasu ya tuna bai fito da key din kofar ba dan haka dole yabi ta gate ya fita snn ya zagaya zuwa gate din gidan nasu ya shiga ta nan..addu'a yake kada Allah ya hadashi da Mummy ko aunty sumy a parlor amma addu'anshi bai kar6u ba dan yana shiga yaci karo da gaba dayansu a dinning suna yin dinner..cikeda mamaki suka bishi da kallo Mummy tace"Kai lafia kuwa ka shigo a hargitse haka?..meya fito dakai ma a daren nan ka baro yarinyar mutane ita kadai"..juyawa yayi yana kallon inda suke yace"batada lafia ne Mummy shine nazo in sauki injection da zanyi mata"..hankali tashe tace"subhanallah meya sameta?.."a hankali yace"fever"..mikewa Mummy tayi daga inda take zaune ta shiga karasowa nan inda yake tana cewa"hope it's not that bad?..kodai asibiti zaka kaita?.."girgiza kai yayi yana kokarin kwantar da hankalinta yace"ai ba sosai bane Mummy nasan inayi mata alluran zata samu sauki"..ajiyar zucia Mummy ta sauke tace"to Allah yasa..yi maza ka dauka ka koma ka barota ita kadai"..da sauri yace"toh"..snn ya kama hanyar flat dinshi da sauri..aunty sumy dai na daga dinning tanayi musu daria daga shi har babar tashi..duk sun wani bi sun tashi hankalinsu kmr basu san abunda ke damunta ba..ita dai ko rantsuwa zata iyayi da kyar idan ba cin zali Bobby yayi mata take wnn fevern ba..dama a yanda taga take takenshi ai bazai yi sanya da yarinyar nan ba ko don sbd kaunar da yake mata..banda murmushi ba abunda take saki cikin ranta tana addu'a Allah yasa ma rabo aka samu shine ya haifar mata da fever..so kawai take taga ance yau ga Bobby da d'a ko 'ya sai taga wane irin kauna zai nunama 'ya ko 'dan..she just can't wait matarshi ta samu ciki ta haifa musu little Bobby.
Yana daukan abunda zai dauka ya fito da sauri ya sake komawa can gidan..har lokacin kuma tana nan kwance yanda ya barta tana hawaye..karasawa yayi da sauri ya dagota zuwa a jikinshi ya shiga share mata tears din yace"kukan ya isa haka please"..kasa cewa komai tayi sai lamo da tayi a jikinshi..jin yanda har yanxu zafin jikinta bai ragu ba dole ya sake ajiyeta ya shiga bathroom ya debo lukewarm water a bowl ya hado da towel ya fito..wnn temperaturen nata yasan bazai ta6a sauka ba idan ba tepid sponging ya samu yayi mata ba..yana zama gefen gadon ya sake dagota zuwa jikinshi ya zare dan rigan dake jikinta snn ya jika towel cikin ruwan ya shiga shafa mata a jikinta a hankali..Aysha ta sake yin luf a jikinshi tanajin dadin yanda ruwan ke ratsa ilahirin jikinta..idanuwanta a kulle har ya gama shafa mata a ko ina snn ya dauko wani rigan yasa mata ya Kuma kwantar da ita kafin ya wuce zuwa kitchen..ruwa ya jona a kettle yana nan tsaye ruwan yayi zafi ya zuba ruwan a mug bayan yasa sugar,Milo da Madara yasa spoon a ciki yana juyawa ya fita daga kitchen din..yana shiga ciki ya dagota ta jingina da gado snn ya shiga bata tea din tanasha a hankali dukda ba wani dadinshi takeji ba don all of a sudden taji tayi loosing appetite dinta..Saida tasha sosai snn ya ajiye mug din ya dauki ruwan daya fito dashi daga fridge tun daxu ya 6alli magani ya bata tasha snn ya sake kwantar da ita yana tunanin yanda zaiyi mata allura..hannunta ya kama ta rike cikin nashi yana kallonta duk a rikice yace mata"baby anya ba injection zamuyi ba kuwa?.."girgiza kai tayi da sauri hawaye na fitowa daga idanunta tace"no plss..banaso".. marairaicewa yayi yana kallonta yace"amma fevern nan bazai sauka ba fa..indai ba alluran akayi ba i don't zai sauka da wuri"..kasa ce mishi komai tayi sai kai kawai ta iya girgiza mishi tana wani tale baki zata rushe mai da kuka yayi saurin rungumeta ga jikinshi yana shafa kanta yace"to yi hakuri na fasa..bazanyi maki ba Kuma"..shiru tayi tana sauke numfashi..sun dade sosai a haka yaji fevern nata ya sauka sai a snn ya samu ya taimaka mata zuwa bathroom ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallolinta duk a zaune don ko tsayuwa bata iyayi sbd azaba gashi sai wani bacci takeji don akwai maganin bacci cikin Wanda ya bata daxun..tana idarwa ya mikar da ita snn ya dauke carpet da hijabin da tayi sallahr dasu ya maida inda suke snn ya kwantar da ita na da nan kuma tayi bacci shi kuma yana nan zaune rike da hannunta sai kallonta yakeyi kmr abunda zai warkar da ita knn..jin ciwon nata yakeyi har cikin ranshi..gaba daya dana sanin abunda ya aikata ya shigeshi..da baiyi hakan ba yasan da kilan wnn zazza6in bai kama mashi ita ba..duk sai yaji inama ana iya transferring rashin lafia from one person to another shikam da yayi transfer nata zuwa jikinshi tunda yasan shi namiji ne zai fita dauriya and ciwon bazai wahalar dashi kaman yanda zai wahalar mashi da ita ba..ko abinci ranan kasa ci yayi tun Wanda sukaci da rana tareda ita..Mummy da aunty sumy sai kira sukeyi suna tambaya ya jikinta shi kuma yana ce musu taji sauki..har dare ya tsala sosai Bobby kasa runtsawa yayi..yana nan zaune yana gadinta kmr idan yayi bacci wani abun ne zaizo ya sameta..karfe daya ya shiga bathroom yayi alwala snn yazo yayi nafilah raka'ah hudu yayi addu'o'inshi snn ya hau kan gadon ya kwanta bayan ya sanyata a jikinshi yaji har zuwa lokacin zazza6in bai dawo ba dan haka shima bai jima da kwanciya ba baccin yayi gaba dashi..can dare ya sake dawowa sabo don har baccin ma kasa komawa tayi sbd zafin da jikinta ya dauka dole haka Bobby yayi mata alluran dai da bataso shima kuma bada son ranshi ba..dambe sosai sukayi da ita kafin ya samu yayi mata har mamaki ma ta bashi ganin ba lafia gareta ba amma ta iya kokawa dashi kawai sbd batason injection..shi duk randa akace ta samu ciki baisan yanda zai nayi da itaba tunda dai ko rashin lafia baisa anyi mata allura ba dole za'ayi mata tt idan taje antenatal..shi kanshi haihuwan ma idan yazo dole za'a mata allura so duk idan Allah ya kawosu baisan yanda za'ayi da ita wajen yin alluran ba..rigima ne yasan zai Sha daga wurinta kala kala amma zai dauki duk me zata mishi ko don son da yake mata..wani murmushi ya saki kawia sbd tunanin yanxu watarana haka zata samu ciki ta haifa mashi baby mai kama dashi ko mai kamada ita..baisan irin farin cikin da zaiyi ba idan Allah ya nuna mashi wnn rana..yanason gani sosai..yanaso yau ace ga d'a ko 'ya Lamido ta haifa mashi..yasan kilan duk wani so da kaunarshi zai tattara ya koma kan babyn sbd tsananin son da yakewa mamanshi.
Washegari Alhamdulillah ta tashi da sauqi sosai don babu fever a jikinta snn duk wani wuri dake mata ciwo jiya yau bata tashi da ciwon ba saidai tunda ta tashi da shagwa6a ta tashi don banda kuka ba abunda take mishi wai ya tsaneta shi kuma ya rikice sai aikin rarrashi yake..ko wanka saida yayi da gaske snn ya samu tayi daga nan ya bata tea da magani tasha maimakon tayi bacci sai ta dora daga inda ta tsaya..kuma duk tana sane take wnn iskancin wai acewarta wahalar daya bata jiya ne take fanshewa sbd shima yaji a jikinshi kmr yanda taji..dama a dunia ba abunda take so kmr tayita zuba ta6ara ana biye mata yau kuma sai abun nema ya samu wai matar driver ta haifi mota..sosai ta rikitashi da wnn iskance iskancen ko breakfast bai samu yayi ba har yanxu don hanashi motsawa tayi ko na da can yana tashi zata fara kuka tana bubbuga kafa wai zaije ya barta..haka nan bawan Allah zai dawo yayi zaune yana rikeda ita yana bata baki amma duk a banza..kallonta kawai yake yanda take shagwaban yana lallashi sa abun ya burgesu matuka..bai taba sanin akwai ranar da zaiji irin wadan nan abubuwan na burgeshi ba saida ya hadu da ita..wato dai ita koma me zatayi yanaso kuma abun sha'awa ne a wurinshi..saida tayi bacci snn ya samu ya shiga bathroom don yin wanka..ita kuma yana shiga ta bude ido tana kyalkyala daria cikin duvet sbd kar yajiyota..draman nasu ba karamin kayatar da ita yake ba..ai wlh saita fanshe duk walakancin da yayi mata jiya shima sai yaji idan da dadi kasa mutum a gaba kayi masa abunda bayaso..tanajin fitowarshi tayi saurin maida idonta ta kulle shi Kuma ya karaso ciki dakin daure da towel a waist dinshi sai wani karami a hannunshi yana gashin kanshi..stool din gaban mirror ya janyo ya zauna snn ya shiga shafa cream ita kuma ta bude ido tana kallonshi daga kwncen da take yanda bazai gane tana kallonshi ba..broad shoulders dinshi ta tsaya kallo yanda suke nan fari tas don jikinshi har yaso yafi face dinshi haske..ga skin dinshi har wani glowing yakeyi sbd tsabar gyara kmr skin din mace..yana gama shafa cream ya shiga shafa mayukan gashinshi tana combin kanshi daga nan kuma ya dawo kan sajenshi da duk fuskanshi babu abunda take qauna kamarshi..tana kallon yanda ya shafeshi da mayuka masu kyau snn yayi using brush comb ya taje tun daga sajen har zuwa gemunshi..kallonshi kawai Lamido keyi tana murmushi ashe dai haka mijinta yake dan gayu bata sani ba..haba no wonder kullum wnn sajen nashi ke kara laushi da sheqi ashe kudi yake kashe mashi haka..yana gamawa da sajen ya shiga shafa turarukanshi masu masifar qamshi..tun tana kallonshi a kwance har batasan lokacinda ta mike zaune tareda tallabo cheeks dinta da hannayenta ta wani tsura mishi ido tana murmushi ba..duk yanda takai da son tayi fushi da mutumin nan bazata taba iyawa ba..she loves him to the extent that kome zai mata bazata iya dogon fushi dashi ba..yanxu dai gashi duk wahalan da tasha jiya a dalilinshi kallonshi kadai yasa ta manta da duk wahalan data sha sai more kallonshi takeyi kmr yau ta fara ganinshi..Bobby kuwa tunda ya fito bathroom dama yasan idonta biyu don ya lura da yawan motsin da take nuna mata ne kawai baiyi ba yayi pretending kmr baisan tana idon nata biyu..and koda ma baiyi noticing motsinta ba ya tabbata daga lokacinda ta kafa mashi wadan nan idanun nata dole zai fahimci kallonshi takeyi sbd tasirin da idanun nata ke dashi a tareda shi..kai tsaye suke piercing har cikin zuciyarshi so babu yanda za'ayi ta dauki tsahon minti guda tana kallonshi dasu ba tareda yaji a jikinshi cewa kallonshi takeyi ba..abun kuma ba karamin qayatar dashi yayi ba..gashi dai ita take kallonshi amma yasan ko ita bazata kaishi enjoying kallon nashi da take ba don kallo ne mai cikeda so da kauna ba ordinary kallo bane da ake iya samunshi wurin kowa da kowa..special kallo ne da sai mutumin da ake mutuwar so za'ayi ma irinshi and he's glad she does that don hakan ya sake tabbatar mashi da cewa matarshi Aisha na tsananin kaunarshi kmr yanda shima yake tsananin kaunarta dukda yasan nata son bai kama kafar wanda yakeyi mata ba..murmushi ya saki bayan ya kammala duk abunda zaiyi ya juya ya nufi closet dinshi bayan ya kashe mata ido daya..daria ta saki itama tana binshi da kallo sai kuma ta sauka daga gadon daga ita sai yar rigarta da baifi iya guiwarta ba ta nufi closet din nashi itama..ciki ta shiga ta ganshi yana neman kayan da zai sa..a hankali ta karasa ta tsaya a bayanshi tareda fadawa jikinshi tayi mashi kyakykywan hug ta baya..saida ya lumshe don dadi har baisan time din da rigar dake hannunshi ya zame ya fadi kasa ba..yana jinta a jikinshi yaji kmr komai nashi aka dakatar sbd tsabar shaukin da ta shiga..shi har yanxu mamakin wnn emotions din da kullum sake sabunta kansu suke..a tunaninshi tunda sunyi aure kuma har sun zama daya zai samu saukin wnn emotions din amma it's like abun ba haka yake ba sam..sai yakega ma kmr abun karuwa yakeyi akan na baya..lumshe Ido yayi yanajin yanda duk wani ga6a na jikinshi ke amsan sakonnin da take tura mashi in a breaking voice ya kira sunanta"Ay..sher"..kasa amsawa tayi ta kwantar da kanta a bayanshi tanata faman murmushi..a hankali ya juyo da ita suna facin juna yayi cupping fuskanta da hannayenshi full of excitement yace"I love u so so very much baby..duk dunia nasan idan aka dauke daddy da Ammi baza'a samu Wanda ke sonki kmr yanda nakeyi ba..i love u sosai"..ya karasa mgnr yana hada face dinshi da nata..Lamido da farin cikin dunian nan ya isheta sbd wnn kalaman nashi sai kace yau ta fara jinsu daga bakinshi kasa dena washe baki tayi kmr gonar audugu..dan dagen kafa tayi ta dafa shoulders dinshi da both hands dinta sbd yafita tsaho sosai ta samu ta manna mashi peck a tip of hancinshi don tsayinta kasa kaiwa forehead dinshi yayi sbd tsayinshi..tana gamawa Bobby ya rungumeta da kyau yana blowing mata kisses ta ko ina yana murmushi..wlh bai ta6a sanin haka aure yake ba..tabbas da yasan haka zama aure yake kilan da tun lokacinda ya fara sonta zaiyi duk yanda zaiyi yaga ya aureta tun kafin a kawo wnn lokacin..baisan ko nashi auren ne yazo a haka ba sbd sonda yake mata oho..bakinta yakai saitin kunnenta ya sake mata whispering"i love u"..murmushi take sosai ta dago tana kallon idanunshi tace"nima ina sonka sosai..i can't imagine my life without u..i love u so much"..pecking forehead da cheeks dinta yayi yana cigaba da smiling..a hankali ta janye daga jikinshi ta sunkuya ta dauko mashi rigan daya yar a kasa..Mika mashi tayi tana murmushi instead of ya kar6a sai ya makale mata shoulder dinshi yanayi mata nuni da finger dinshi wai tasa mashi da kanta..batayi musu ba ta balle botles din rigan shi kuma ya rage tsayinshi daidai yanda zata iya sa mashi ta zura mashi rigan snn ya mike yana gyara collarn rigan..ita tayi mashi buttoning rigan ta saka mashi links snn ya Miko mata trouser wai shima ta saka aikuwa ta fice daga wurin da gudu tana mishi daria..shima darian ya saki yana ayyana lallai ta wareke tunda har take iya gudu har haka..Sharp sharp ya karasa sa kayan ya sake gyara gashinshi jikin mirror dake nan ciki snn ya fita..bai sameta nan dakin ba harta gama gyara gado ta fita dan haka ya fice shima zuwa bedroom da yasan dole nan zai sameta..bai sameta a nan ba saida ya bude another one ya ganta a ciki tana kokarin saka skirt dinta..tayi wanka dama tun daxu so tana shigowa kaya ta dauka ta fara sawa don yau kome zaiyi sai taje gaida Mummy wlh..yana karasowa ciki ta gama veiling dinta dan haka ta shiga dubanshi tana dan daure fuska tace"nifa yau zuwa zanyi in gaida Mummy"..kallonta ya danyi kafin ya saki murmushi gamida girgiza kanshi yace"ba sai kinje ba tace da kanta zata shigo dubaki anjima"..ai tun bai rufe baki ba ta sake dinke fuska tana binshi da wani kallo tace"nidai wlh sai naje..ai ba daidai bane ace har sai itane zatazo inda nake ni banje na gaisheta ba"..murmushi yake cigaba dayi cikin ranshi yace"abubuwan sun motsa knn?.."a zahiri kuma matsawa yayi kusa da ita ya kama hannunta yace"to meye abun 6ata rai kuma baby..shknn kisa hijab dinki muje".. kallonshi da wani expression a fuskanta tace"ban gane hijab ba..daga nan zuwa gidan naku zakace insa hijab?.."hannu yakai zai sake kamo dayan hannunta tayi sauri kaucewa tana hararanshi..bai sake cewa komai ba ya karasa ya kama hannun nata suka fita daga dakin..wanda aka fara ajiyeta a ciki suka shiga ya saki hannun nata a nan shi kuma ya shiga closet ya dauko mata katoton hijab ya dawo ko mgn baiyi mata ba ya janyota ya zura mata shi ba tareda ko veiling dinta ya cire ba..ya kalleta from sama zuwa kasa then from kasa zuwa sama yaga komai na jikinta a rufe yake dan haka ya saki murmushi yana shafa gemunshi yace"perfect..now we are good to go"..banza tayi dashi ta dauke kai tana turo baki..shi kuma ya kama hannunta a haka suka fita daga gidan..bayan sun fito compound ya saki hannunta yayi locking kofa snn ya sake kama hannun nata suka nufi kofan da ake koma cikin gidan nasu ta nan..sai yanxu Lamido ta samu damar karema compound din gidan nata kallo don tunda aka kawota bata sake fitowa ba balle ta kalleshi da kyau..yanada girma sosai da akwai motocinshi guda biyu daga can gefe sai kofan da suka nufa shima yana daga gefe don ba kowa ma zai fahimci akwai kofa a wurin ba..tayi mamaki da taga ashe gidanta da main house din nasu kusa da kusa suke saidai kowanne gate dinshi daban sai dan kofa da akayi wanda zasu iya shiga main house din ba tareda sunbi ta gate ba..sosai yanayin tsarin wurin ya burgeta..suna karasawa Bobby ya bude kofar nan suka fada gidansu Mummy.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
61
Suna shiga aunty data fito daga kitchen ta rike baki baki tana kallonsu da mamaki sosai tace"yanxu Bobby mara lafiyan ka dauko ka fito da ita sbd rashin hankali?.."tana gama fadin haka kuma ta karasa inda suke tareda kama hannun Aysha ta rike cikin nata tana kallon with concern tace"kema kika yadda ya fito dake bakida lafia Aysha?.."sunne kai tayi tana murmushi tace"ai naji sauki aunty"..cikin ranta kuwa haushi taji da yazo ya tona mata asiri a wurinsu..yanxu shknn tasan da kyar idan basu san menene ma yayi coursing zazza6in nata ba..amma dai ya cuceta wlh..kamata aunty sumy tayi suka karasa parlor yayinda shi kuma yabisu da kallo yana murmushi..wnn son da suke nuna mata ba karamin faranta mishi rai yake ba..yana son yanda suke tayashi sonta sosai ba kadan ba..karasawa yayi ciki shima ya zauna yana kallon aunty sumy yace"ita fa da kanta tace sai na kawota shine zaki wani tsaremu da mgn ko welcoming dinmu bakiyi ba"..harara ta juya ta sakar mashi tana nuna Aysha tace"ita dai ya kamata inyi welcoming amma ba kai ba..dan rainin hankali kawai"..daria sosai yasa hadda girgiza kai yace"siriki ne dai dake kuma har yanxu baki dena wadan nn abubuwan ba"..shiru aunty sumy tayi tana kallonshi don dama ranar daya fada mata haka Saida taga alamun da gaske yake..ta bude baki zatayi mgn Mummy ta fito daga flat dinta tace"hayaniyar me nakeji ne haka?.."da sauri Bobby ya mike ya karasa gareta yana kokarin fadawa jikinta cikin igbo yace"Mummy nah"..Mummy dake murmushi tayi saurin kaucewa tana daria tace"let me welcome my daughter first"..daga haka ta wuce cikin parlon tana cigaba da mishi daria shi kuma ya wani tale baki kmr zaisa mata kuka yace"Mummy ni Koh..ni kikaima haka Koh..shknn nagode"..batace mishi komai ba tana isa inda Aysha take ta dagota tareda rungumeta a jikinta tana cewa"welcome to your Family daughter"..wani irin kunya ne ya kama Aysha tama rasa inda zata 6oye kanta sbd ita..gashi Mummy ta rungumeta har yanxun taki rabata da jikinta..aunty sumy na kallonsu with a very wide smile tace"Mummy bakiga kyan da kukayi a haka ba wlh..let me call Sab yazo da camera yayi muku hoto a haka a gaskia..kunyi kyau fa sosai kaman a daukeku a gudu"..Murmushi Mummy tayi tareda janye Aysha daga jikinta tana kallonta da fara'a tace"ya jikin naki?..hope bashi ya takura maki zuwa bayan bakida lafia ba"..girgiza kai Aysha tayi tana sunne kai duk kunya yabi ya isheta wlh..Bobby dake tsaye inda Mummy ta baroshi yana binsu da kallo tun daxu sai yanxu ya samu damar karasowa cikin parlon shima ya samu wuri ya zauna nan inda suke zaune yana fadada murmushin fuskanshi sbd farin cikin yanda suka tarban mishi ita..durkusawa tayi har kasa tana gaishesu yayinda Mummy ta dawo da ita zaune tana ce mata ta dena wnn durkuson ita dai ta yafe mata..aunty sumy da kanta ta shiga kitchen ta kawo mata lemo da ruwa dasu cupcakes tace ta fara ci kafin a karasa abinci..sai nan nan sukeyi da ita kmr zasu maidata ciki sbd soyayya ita sai kunya suke bata wlh..Mummy sai ce mata take duk Bobby yayi mata abunda ba daidai ba tazo direct ta fada mata ita kuma zatayi mata maganinshi itadai har yanxu babu bakin mgn sai na murmushi..mutanen nan ba karamin burgeta suke ba..dama tun ba yau ba tasan yanda suke gudanar da rayuwarsu cikin so da kaunar juna tasan Kuma inshaAllah bazata samu matsala dasu ba..ganin bata ta6a komai da aka kawo mata ba Bobby da kanshi ya zuba mata lemo a cup ya hada da cup cake din yana mika mata ita kuma tayi kmr bata gani ba don kunya yake bata..aunty sumy na hada Ido dashi ta sakar mashi harara shi kuma ya kashe mata ido daya yana cewa"to ko abinci bataci ba matsa saina kawota wurinku..yanxu kuma an kawo naga kunya ya hanata ci shine zan bata da kaina"..ba aunty sumy kawai ba har Mummy Saida tayi darian wnn rashin kunyan nashi.. Bobby da Aysha dama ai tasan zaiyi rashin kunya tunda tasan soyayyar da yake mata ba ordinary so bane..fatanta dai Allah ya dawwamar da wnn farin cikin da suke ciki har karshen rayuwarsu.. Allah kuma ya basu zuri'a masu albarka...suna nan zaune sunata janta da labari tun tana jin kunya har daga baya ta ware suka cigaba da labarin da ita..Kiran Nur ne ya shigo wayanshi ya dauka nan yake ce mashi photo albums dinsu ne na biki aka kawo mashi so yana kofar gida ya fito a amsa..Bobby yace ya shigo main house kawai don suna nan tareda Ayshan..babu wasting of time Nur ya shigo cikin gidan yana cin karo da aunty sumy sai yaji kunya ya lull6eshi musamman daya ga irin kallon da Bobby ke jifanshi dashi yana murmushi.. Allah dai yasa ba zuwa yayi ya tona mashi asiri yace musu yace yana sonta ba..yasan halin kayanshi tsaf zai iya aikata hakan amma dai daya gama dashi..har ya karaso cikin parlor ya zauna bai yadda ya hada ido da itaba yana zaunawa ya shiga gaida Mummy ita kuma ta amsa mashi with smile tana tambayanshi ya gajiyar biki yace gajia yabi lafia..a nutse ya juya yana gaida aunty sumy da hankalinta gaba ke ga albums data gani a hannunshi..bayan ta amsa gaisuwan nashi tace"wnn albums din biki ne a hannunka?.."kai a kasa Nur ya mika mata allbums din yana cewa"eh"..aunty sumy ta amsa ta fara dubawa yayinda shi kuma Nur suka shiga gaisawa da Aysha..sai tsokanarta yake wai har ta fara kumatu itadai sai murmushi don ba saba irin wnn wasan tayi dashi ba..har yanxu daukanshi take matsayin College Provost dinsu so bata iya sakewa tayi wasa dashi kmr yanda yake mata..aunty sumy dake kallon pictures din biki sai zuzuta kyan da sukayi take tana nunama Bobby dake zaune kusada ita wani picture da sukayi gaba dayansu tace"dan Allah wnn baiyi kyau ba Bobby..kallemu fa kmr wasu larabawa".. Bobby dai daria kawai yake yana kallon Nur da yake satar kallonshi yana Maka mashi harara..for the first time yau yakejinshi wani irin cikin familyn Bobby..wani sabon kunya ne ya shigo tsakaninsu sakamakon son nan da yakewa Miemie amma da shi ba haka yakeji idan yana cikinsu ba wlh..sakewa yake yayi abunda yaga dama don daukansu yakeyi daya da family dinshi amma yanxu wnn is gone sai jin kunya da sunkuyar da kai kawai..Saida ta
Book Chapters
Chapter 50
Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59