ArewaNovels
Telegram

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gama kalle hotuna tsaf tana zuzutasu snn ta mikama Aysha tana ce mata"ungo wnn ki fara gani Aysha kafin Mummy ta gama da sauran".. Mummy tace"aah kuyi kallonku ni zan gani a nutse ba lallai sai yanxu ba"..Aysha batayi musu ba amsa album din tana kallon yanda cover dinshi yayi bala'in kyau tasan cikin ma dole yayi kyau shiyasa aunty sumy tayita exergerating..page din farko ta bude nan taci karo da wani beautiful picture dinsu ita dashi ya wani rike mata hannu yana kallonta itama tana kallonshi tana murmushi..a can saman page din kuma in italics aka rubuta The Waziri's Meets The Lamido's sai daga can kasa kuma aka rubuta Attahir Waziri Weds Aysha Lamido..sbd tsabar farin ciki batasan sanda ta lumshe ido takai hannu tana shafa ilahirin page din ba..yayi mata kyau ne nesa ba kusa ba..ya kuma kayatar da ita kwarai..a nuste tacigaba dabin pictures din tana kallonsu daya bayan daya tana murmushi daidai lokacin kuma Miemie da Sab suka shigo parlon..tun safe suka fita ya rakata tayi registration na jamb shine sai yanxun suke dawowa..Bobby najin sallamarsu ya juya da sauri yana kallon Nur sai kuma ya fashe da daria har yana tafa hannu..Mummy tace"kai bakada hankali ne?..wnn wane irin daria ne?."tsayar da dariar yayi yana kallon Nur yanxu yace"Mummy karki damu abokina nake yiwa"..juyawa Mummy tayi ga Nur tace"is he alright?.."da sauri Nur yace"wlh he is not Mummy..amma ki barni dashi nasan yanda zanyi maganinshi"..girgiza kai kawai Mummy tayi tana jinjina wnn iskancin na Bobby..daga yin aure kuma sai ka zama shashasha?..to Allah ya shirya..su Miemie na karasowa da taji sunyi komai normal ta mike zuwa flat dinta don bazata iyama wnn iya shegen na Bobby ba..cikin ranta kuwa farin ciki take sosai na ganin yanda walwalarshi ya dawo haka..bata ta6a tsammanin zuwan lokaci irin wnn da Bobby zai dawo rayuwa normal kmr kowa da kowa ba..ko a haka saidai tace Alhamdulillah don ubangiji yayi mata komai sai kuma fatan gamawa da dunia lafia..Nur da tun daxun kanshi ke kasa sai yanxu ya samu damar dagowa yana kallon Miemie don har yanxu aunty sumy bata gama kallon pictures ba..daidai lokacin itama ta kalli inda yake aikam suka hada ido Nur har cikin ranshi yaji wani abu amma ya danne ya shiga kallonta yana murmushi..murmushin itama ta saki tareda karasawa ta zauna kusa dashi tana kallonshi tace"uncle Nur ina yini"..da sauri yace"la..lafia..lau..ina kukaje..haka?.."Miemie tace"registration din jamb naje nayi kasan mun kusa graduation"..gyada kai ya shigayi yana dubanta da murmushi yace"MashaAllah ashe pretty ta kusa graduation..to Allah yasa albarka"..tana murmushi tace"Ameen..saura baifi 2 months ba mu fara waec"..yace"Allah ya bada sa'a"..tace"Ameen Uncle Nur"..daga haka kuma sai ta bar inda yake ta koma wurin Aysha ta wani rungumeta tana murmushi tace"aunty Aysha sannu da zuwa"..kafin Aysha tayi mgn Bobby yayi saurin janyeta daga jikinta yana mata wani kallo yace"are u mad?.."dan turo baki tayi tace"naji dadin ganinta ne fa"..Bobby ya matsar da ita daga wurin yace"oya San inda dare yayi maki kuma kar na sake ganin kinyi mata irin wnn abun dan ranki saiya 6aci"..zaunawa tayi kusada mamanta tace"to kayi hakuri"..Nur dake gaisawa da Sab duk yana sauraron wnn iskancin na Bobby yasan kuma da gayya yakeyi haka sbd ya kular dashi and he succeed..sbd presence na aunty sumy a wurin yasa bazai kulashi ba amma dole ma yayi maganinshi wlh don ya fuskanci walakancinshi karuwa yayi bayan auren nan nashi..bayan sun gama kallon albums din an gama lunch don haka duk sukaci abincin tare daga nan kuma Bobby yabi Nur suka fita zuwa hospital bayan yayi sallama da matarshi yace ta zauna nan tare dasu Miemie idan ya dawo sai ya biyo ta nan ya dauketa.

Bayan sati biyu...

Rayuwa suka gudanar mai cikeda soyayya cikin sati biyun nan..duk wanda ya zauna dasu yaga yanda suke concentrating akan junansu abun zaiyi matukar burgeshi don sai kayi tunanin a cikin gidansu aka halicci soyayya..they are the perfect couple da basa gajia da nunama juna love and affection..duk au biyun are meant for each other and each one of them can die for the other..hatta su Mummy da sauran yan gidan sun auren nasu aure ne irin na soyayya wanda ba ko ina ake samun irinshi ba..kusan kullum suna tare a gida don hutun one month ya dauka na zuwa aiki dan haka bai fita sai idan akwai emergency case da babu wanda zai iya handling sai shi..kullum yana nan tareda ita sai kuma main house da yake shiga gaida su Mummy amma ita ba kullum yake barinta zuwa ba..a halin yanxu batada problem din komai domin ko kewar su Ammi da takeyi yanxu ya ragu sosai sbd tsabar kulawan da yake bata wani lokaci har mantawa ma takeyi da kowa na dunia🤣..saidai kusan kullum zatayi waya dasu dan ko bata kira ba Ammi na kiranta ko su Husna sbd haka rayuwa is full of happiness a garesu baki daya sai dan abunda baza'a rasa ba na bahaushe da yake cewa zo mu zauna zo mu sa6a..masu aiki har biyu Mummy tasa aka kawo mata amma tace guda daya ma ta isa dan haka aka sallami dayar ita kuma daya ta zauna tana dan tayata su shara da mopping da sauran aiyukan gida..girki dai da kanta take abunta saidai ta dan taimaka mata haka gyaran 6angaren mijinta da bedrooms dinta shima da kanta takeyi ita mai aiki iyakarta gyaran parlor,dinning dasu kitchen sai kuma ta kama mata wasu abubuwan..dakinda take kwana yana daga can gefe so tana kammala aiyukanta dama can take komawa dan haka babu takura a tsakaninsu..abu daya dake dan damunta shine rashin fita da baya barinta..shi koda yaushe yafiso suyita zaune a gida kmr a nan aka halicce su musamman ita da ko compound bai cika son tana zuwa ba wai ko baki zata raka ta tsaya iya kofar parlor shi bai yadda ta fita compound masu gadi na kallonta ba..wnn shine kadai damuwarta sai kuma asibiti da takeso ya barta ta fara zuwa sbd mates dinta gaba daya suna asibiti waiting results amma banda ita hakan kuma ba karamin damunta yake ba..gani take kmr idan ta dauki lokaci mai tsaho bata aiki skills dinta na iya guduwa su barta and ko Allah yasan batason haka ita da takeson wucewa Cyprus ta cigaba da karatu ai bazata so tayi loosing skills dinta sbd rashin practicing ba dan haka ta kuduri niyyar sanar dashi ya barta ta fara zuwa ko Freedom ne don tasan ko rasuwa zatayi bazai bari taje wani asibiti apart from nashi ba..ita sai yanxu wnn kishin nashi ke damunta wlh..ta lura ba karamin kulle hakan zai haifar mata ba and Allah ya sani ita bazata juri kullum tayita zaune a gida kmr wata mara abunyi ba..yanxu ko aiki ta samu batasan da yaya zai barta tayi ba da wnn shegen kullen da yake mata..kullum kuma tana cikin hijabi kmr matar malam..ko Nur ne zaizo gidan haka zai zunduma mata jibgegen hijabi a jiki tayita fama dashi wani lokaci ma sai taji kmr tasa kuka..tun jiya take tunanin yanda zata fada mishi tana son komawa asbiti amma batasan ta yaya ba kawai addu'a take Allah yasa kai tsaye yace mata ya amince taje aiko da batasan farin cikin da zata tsinci kanta a ciki ba.
Tun daxun da ya kirata yace gasu nan zuwa tareda Nur tayi saurin karasa girkin da take tareda taimakon mai aikinta mai suna saude suka jera komai kan dinning snn ta wuce dakinta don yin wanka ita kuma saude ta karasa gyara kitchen snn ta dauki abincinta ta wuce dakinta kmr yanda ta saba...Aysha na fitowa daga wanka ta dauko wani riga da skirt na atampa ta saka ta kafa daurin dankwalinta da yayi das a kan nata snn ta kawo veil daya shiga da atampar jikin nata ta yafa tunda dai tasan ko rasuwa zatayi bazai barta ta fita ba tareda wani abu a jikinta ba..mayafin ma tasan da kyar idan ba cewa zaiyi ta cire ba amma addu'a take Allah dai yasa ya barta dashi yau daya dai itama ta saka abunda takeso..bayan ta gama gyara fuskarta ta dauki turare daga kan madubi zata shiga fesawa a jikinta kawai taji an rike hannunta kmr daga sama ya kwace turaren daga hannun nata ya ajiyeshi nan inda yake snn ya juyo ta yana kallon fuskanta yace"wai bana hanaki sa turare idan Muna tareda baki ba?.."marairaicewa tayi tana kallonshi bata dai ce komai ba..shi kuma ya saki smile yana sake matsawa jikinta yaja cheeks dinta da hannayenshi yace"kinyi kyau sosai"..murmushi kawai ta saki tana gyada kai har yanxu bata ce komai ba shi kuma yace"tareda Nur muke dauko hijab dinki muje"..sake marairaicewa tayi tana dubanshi da puppy eyes tace"partner dan Allah inje a haka..kaga veil din dana yafa fa mai girma ne"..girgiza mata kai Bobby ya shigayi tun ma kafin ta rufe baki yace"bazan iya ba wlh..there is no way da zan bari ki fita bayan duk wnn kyan da kikayi"..kallonshi kawai take kmr tasa kuka..a fusace ta bar wurin ta koma kan gado ta zauna ta rungume hannaye tace"to kaje ka sallameshi da kanka ba sai nazo ba"..karasawa yayi shima ya zauna yana yin kasa da murya yace"yanxu baby sbd..."bai karasa ba ta mike ta bar mishi dakin duk rai a 6ace..da sauri shima ya mike yabi bayanta nan yaga ta bude kofa zata shiga daya bedroom dinta yayi saurin kamota yana cewa"ki tsaya muyi mgn plss..ya kamata ki fahimceni love..inada kishi sosai akan duk wani abu da nakeso..yanxu kina ganin.."still bai karasa ba ta katseshi da fadin"shine nace kaje ka sallami bakonka kai kadai ba tareda ni ba"..ganin juyawa tayi zata shiga dakin yasan kuma tana shiga kulle kofa zatayi yayi saurin rungumeta ta baya ya lumshe ido yace"to..kiyi hakuri..yanxu kije da veil din amma next time bazan yadda ba"..banza tayi dashi ta wani tureshi ta wuce parlon tana murguda masa baki shima yabi bayanta yana jijjiga kai..ita dai har abada bazata dena wnn rikicin nata ba..kan a very minor abu zata daga mashi hankali kuma idan baiyi yanda takeso basu ba zaman lafia..ya fuskanci ita din hukuma ce saida lallashi..zaune ya sameta a parlor suna gaisawa da Nur daga nan kuma tayi mishi introducing abinci dake dinning ba musu suka karasa dinning don dama tareda yunwar su suke..saida ta gama serving dinsu komai snn ta bar dinning din tanajin yanda Nur da har ya fara cin nashi abincin keta santi yana cewa abokinshi yayi sa'ar mata data iya sarrafa abinci..itadai murmushi tayi tareda komawa parlor..saita tuna a gida yanda sam bata son girki..shiyasa kusan kullum suke rigima da Ammi kan aiki ita kanta bata ta6a zaton akwai time da zaizo wai taji bazata iya bari wata tama mijinta bincin da zaici ba..duk kiyayyanta da shara dasu wankin toilet yanxu da kanta take na flat dinshi kuma ko kadan hakan baya damunta saima faranta mata da yakeyi..at least bata bama wata mace kofar da zata shigo rayuwar mijinta ba..hakan da takeyi kuma na burgeta..yanxu ta dauki full responsibility dinta na house wife duk wani aiki daya kama na mijinta ne da kanta take yinshi..tana nan zaune har suna gama cin abincin suka dawo parlor Nur har yanxu bai bar santin girkinta yana cewa ta ita abinci ba..ita kuma kallonshi tayi tana murmushi tace"Sir kar ka damu da kaina zan koyawa Miemie yanda nake girki sbd idan ta iya ta dinga yi maka a gidanka"..wani irin zare Ido Nur yayi yana mamakin abunda take..jmya juya yana kallon Bobby dake danne daria yace"amma kaci amanata..yanxu zuwa kayi duk ka fada musu nace ina sonta?.."da sauri Bobby yace"ni ba wanda na fadawa sai ita kuma itama believe me bani na fara fada mata ba da kanta ta gano sbd shegen rawar kanka dan haka stop blaming me..wnn rawar kan naka yasa ta gane ni kuma data tambayeni nace mata its the truth"..dafe goshi Nur yayi yana murmushi kmr bazai sake mgn ba can yace"amma dai baku bari ta sani ba koh?.."harara Bobby ya watsa mashi yace"kasan ko aikena kayi bazanyi such mgn da itaba balle baka aikeni ba..da bakinka zaka fara fada mata inshallah"..ajiyar zucia ya sauke yana murmushi ita kuma Aysha ta koma dinning din ta gayar inda suka bata snn ta koma daki don bata cika son zama if yana tareda baki ba musamman Nur da har yanxu ta kasa sakewa dashi as abokin mijinta.

Da dare suka shiga main house sakamakon kiranshi da Mummy tayi tace yazo tareda Aysha tanason magana dasu.














Rano✨




Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
62
Tun daga compound da yaga bakuwar mota yasan lallai sunada baqi a gidan maybe ma shine dalilin kiran nasu da Mummy tayi saidai suna shiga parlor yaci karo da akasin haka..baban su Miemie ne zaune cikin parlon sai aunty sumy da yaran nasu gaba daya..duk yanda yaso kar ya tuna abun da suka faru a baya kasawa yayi dan yana ganinshi yaji komai ya shigo dawo mishi kmr yanxu abun ke faruwa..yana ganinsu ya taso da sauri yazo inda suke yana mika mai hannu da murmushi..Mika nashi hannun shima yayi yana kokarin ganin ya danne abunda yaji cikin ranshi suka shiga gaisawa a haka..bayan sun gama ya kalli Aysha itama suka gaisa duk yayi congratulating dinsu on their marriage..du Miemie ma suka gaidasu snn ya kama hannun matarshi suka nufi flat din Mummy..tana zaune parlor ita kadai suka shigo ciki..tana ganinsu ta saki murmushi har suka karaso ta kama hannun Aysha dake kokarin durkusawa a kasa ta zaunar da ita nan kusa da ita tace"har yanxu bazaki dena wnn ba koh"..murmushi kadai tayi kanta kasa..batasan meyasa har yanxu ta kasa sakewa da itaba..kunyarta takeji sosai ba kadan ba..bayan sun gaisa Mummy na dubanshi tace"Kun hadu da Isma'il a parlor?.."yace"na ganshi Mummy"tace"Waziri ne ya kira wai yazo su sake daidaitawa tunda auren bai yiwu tareda naku ba idan sun daidaita sai a maidashi nan da sati biyu"..gyada kai kawai yayi yace"to Allah tabbatar da alkhairi".. Mummy tace"Ameen ko har yanxu bakason mgnr ne?.."da sauri yace"aah indai taga zata koma ai inaga hakan zaifi ko dan sbd yaran ma".. Mummy tace"ko daxu da yazo bakaga murnan da yaran sukayi ba ni har tausayi suka bani wlh"..gyada kai Bobby yayi yace"to Allah ya za6a mafi alkhairi..dama shiyasa kikace muzo?.."tace"aah mgnr zuwa Enugu ne bikin Tauhid"..Bobby ya dan wara ido yana kallonta yace"wai bikin har yazo?.."tace"yazo mana jibi nakeso mu wuce shiyasa nace kuzo tare in fada muku don kuje ku fara shiri"..dan marairaicewa yayi yana kallonta yace"yanxu Mummy sati biyu.."ai bata bari ya karasa ba tace"nace kuje ku shirya Bobby banason mgn..itama Sumayya dasu Miemie duk tare zamu wuce shi Sab dai tunda yana makaranta banda shi"..kallonta kawai yake bai sake cewa komai ba sai kai daya daga mata..Mummy kuma ta juya tana kallon Aysha tace"ai kinason zuwa ko Aysha?.."da sauri ta gyada kai tana murmushi tace"sosai ma Mummy..i love travelling"..da fara'a Mummy tace"MashaAllah"..Bobby da yaji haushin reply din nata ya dungure mata kai yana dan hararanta yace"sarkin yawo kawai"..bai ajiye hannu ba shima Mummy ta dungure nashi kan tace"kai kuma sarkin kulle ba"..da sauri ya dafa kan yana kallonta kmr zaisa kuka..a tare Mummy da Aysha suka tuntsire mishi da daria..he look funny ne yanda yayi squeezing face dinshi..shima dan murmushi ya saki yana relaxing kan kujera shi bason tafian nan yakeyi ba wlh..yasan yanxu idan sukaje sai suyi sati a can shikuma takura zaiyi ya sani..dan ba yanda zaiyi da Mummy ne amma da bazai je ba wlh..yasan idan taso abu irin haka dole ne yayi hakuri yayi yanda takeso musamman idan abu ya shafi zumunchi don shi gani yakeyi duk dunia babu mace mai son yan uwan da zumunchi kmr ita..sun dan ta6a hira kadan har su aunty sumy suka shigo bayan baban su Miemie ya tafi suma aka cigaba da hiran dasu..farin ciki kawai suke na tafia Enugu amma banda Bobby da ba haka aka so ba wai qanin miji yafi miji kyau.

Koda suka koma gida haka yayita kumbure kumbure wai shi bayaso ita kuma tana mishi daria..da kanta ta hada musu kayan tafia kowa akwatinshi daban amma yana gani ya fito da kayan ya hadesu cikin guda daya wai yanda ba wanda zai rabasu tunda kayansu na hade dole a bar masa matarsa..itadai daria yake bata dan tasan duk sbd me yake wnn abubuwan...washegari ma haka tayita shirye shirye tana bude jaka ta fito da wani kayan ko ta saka wani aikin knn tunda ta tashi daga bacci kmr wadda bata ta6a zuwa wani gari ba..murna kawai take ta samu saken fita don tun da akayi biki idan aka dauke gidan Mummy babu inda take zuwa.. she's always at home kmr matar malam..suna gama lunch ya dauketa zuwa daki wai zaiyi maganin dariar da take mashi aikam nan da nan ta shiga hankalinta ta fara bashi hakuri kmr zatayi kuka..shi kuma bai saurara mata ba saida yayi maganin bakin da take dariar dashi..bayan sunyi wanka ya sake janta suka koma gado wai duk yau ta jama kanta a haka zasu yini tunda take mishi daria itadai batace komai ba don tasan ko zata shekara cewa ya kyaleta ba kyaletan zaiyi ba shiyasa tayi shiru da bakinta..ganin kmr he is in a good mood tace bari tayi using wnn opportunity tayi mashi zancen komawa hospital..tana kwance a jikinshi tana wasa da gemunshi tace"partner"..hannu yakai ya sake matseta jikinshi yafin ya amsa da"yes partner"..murya can kasa tace"So nake in koma asibiti"..da sauri ya dago yana kallonta yace"are u sick?.."tace"No inaso in koma aiki ne..kaga duk yan class dinmu fa suna waiting results amma ni banda ni"..ta karasa mgn tana kwabe fuska kmr zatasa kuka..Jan cheeks dinta yayi yana murmushi yace"kema zaki koma ai amma ba yanxu ba"..da sauri tace"when"..yace"when the right time comes"..kallonshi ta tsaya yi kmr zatasa kuka..sai kuma tale baki ta shiga bubbuga legs dinta akan gadon tace"nidai inaso in koma plss..so kake skills dina ya gudu"..daria yakeyi sosai bayan yayi pecking lips dinta yace"ba wani skills dinki da zai gudu.. believe me very soon zaki koma"..banza tayi dashi tana cigaba da diddirza kafafunta..baiyi yunkurin hanata ba sai matsar da bakinshi da yayi saitin kunnenta yace"naga alama u want some more and believe me idan kika cigaba da abun nan kome ya biyo baya ke kika siya"..tun bai rufe baki ta shiga hankalinta don tasan kadan daga aikinshi yayi yanda yace wlh..ita wani lokaci har mamaki yake bata..shidai kullum ayita abu daya ko gajia bayayi.

The next morning kmr yanda Mummy tace suka tafi Enugu gaba dayansu...basu sauka a can ba sai around 3 don haka bayan sun huta gajia Mummy da kanta ta kaisu gidan wani uncle dinta suka gaisheshi daga nan kuma sukaje bikin da ya kawosu.. traditional Igbo day sukayi suma exactly irin wanda akayi na bikinsu saidai Lamido gani take kmr wnn din yafi nasu batasan ko sbd su din gaba daya inyamuran bane amma abun ya burgeta matuka haka ta dinga daukan pictures da videos tana turama su Ammi da Billy wai su kalli bikin inyamurai..ranan basu dawo masaukinsu ba sai dare sosai..gida ne guda na Mummy da sauran 'yan uwanta suka sauka a ciki..daki daya aka basu da Miemie,aunty sumy da Ilham Mummy kuma ita kadai sai Bobby tareda wani cousin dinshi..yaji haushi sosai da aka rabashi da matarshi amma ba yanda ya iya da Mummy dan yanxu yana mgn ne zatace ya zama mara kunya snn ita kanta Ayshan ya fuskanci murna ma takeyi da hakan..bayan sun dawo duk sukayi shirin bacci kowa ya kwanta saidai tana kwanciya kiranshi ya shigo wayarta dan haka ta mike zaune bayan ta daga kiran tace"partner bakayi bacci ba"..tana rufe baki yace"how do u want me to sleep without u?..plss kizo parlor ina nan ina jiranki mu tafi..i can't sleep without u"..dan murmushi ta saki tana girgiza kai tace"yanxun partner kawai sai Mummy taga nazo dakinka?..no can't do that plss..besides naga ba kai kadai zaka kwana a dakin ba"..tun bata rufe baki ba yace"we're not sleeping here hotel zamuje..plss baby kiyi sauri kizo am waiting for u here"..dan langabewa tayi kmr yana ganinta tace"partner kayi hakuri i can't come out now..kaga Mummy fa bazata ji dadi ba idan na b..."tun bata karasa ba yace"then bari inzo in daukoki tunda cewa kikayi u can't come out now"..zare idanu tayi hadda su rufe baki jin abunda ya fada..ita fa bazai sata jin kunya ba wlh..sanin zai iya aikata abunda ya fada ta mike da sauri ta sama kofar key tareda dawowa cikin dakin ta zauna tanaji ya kashe kiran tasan nan din ya taho..yana zuwa kuwa ya murda kofa yaji a rufe ya kira bata dauka ba dan haka ya koma daki cikin ranshi yace yasan yanda zaiyi maganinta.

Da safe bayan duk sunyi wanka suka fito yin breakfast a nan parlor..Aysha na lura da Bobby tunda ta shigo parlon ko gaisuwarta bai amsa ba ya maida hankali sosai yanacin abincinshi..jikinta taji yayi sanyi sosai tasan duk tsiya bai cancanci walakancin da tayi masa ba jiya amma ba laifinta bane ai da zaina wani daure mata fuska..bata sake bi ta kanshi ba itama ta fara cin abincin saidai loma daya tayi taji bazata iya ci ba don bata saba dacin irinshi ba..gashi dai abinci ne sosai amma bazata iya ci ba sam..bata bari sun fahimci bata ci ba tacigaba da jujjuya spoon dinta a ciki suma kuma da yake hankalinsu bai wurin basu gani ba..Bobby da gaba daya hankalinshi yake kanta ya lura sarai bacin abincin take ba and dama yasan hakan zai iya faruwa..ko gama cin nashi baiyi ba ya mike yana goge bakinshi da tissue yace"Mummy let me take out taci abinci nasan ba iya cin wnn zatayi ba"..da sauri Mummy ta juya tana kallonta tace"da gaske bazaki iya ci ba daughter?.."a hankali ta daga mata kai alamar eh dan haka Mummy tace"to tashi kuje ya sama maki wani abun kici zamu jira ku dawo sai mu fita gaba daya"..a hankali ta mike ta koma daki ta dauko mayafinta snn ta dawo parlon inda ta tarar shima har ya fita dan haka tabi bayanshi..a cikin mota ta sameshi ta karasa a hankali itama ta shiga snn ya tada ta suka bar gidan sai a lokacin ta dan juya tana kallonshi..taga fuskan nan a tamke dan haka ta dauke kanta gefe har suka isa eatery ba Wanda yayi mgn cikinsu..shi kadai ya fita ya siyo abunda zai siya ya dawo tareda zuba ledojin a baya shima ya shiga ya tada motar..a hanakli ta sake juyowa tana kallonshi still taga hankalinshi bai kanta kawai sai itama ta daure nata fuskan tana turo baki..suna isa gida ta bude motar kmr zata fita sai kuma tayi saurin dawowa ta fada jikinshi murya can kasa tace"partner kayi hakuri"..rungumeta yayi shima gami da lumshe ido yace"wahala kikeson bani don kinga ina sonki Koh?.."da sauri ta shiga girgiza kai tana cewa"me nayi?.."..yace"u refused me yesterday sbd kinga na damu dake"..dan murmushi ta saki tana sake kwantar da kanta a chest dinshi tace"to am sorry"..idanunshi lumshe yace"u have no idea how i missed u..i missed u so much"..murmushi takeyi ta dago tana kallonshi sai kuma ta lumshe ido ta shiga bashi the hottest kiss of his life..Bobby is just sitting there looking at her kaman wani statue..he is far far gone da wnn kiss din nata..he never thought she can do this..tunda yake da ita ko kallon eyes dinshi na tsahon lokaci bata iyawa balle ayi mgnr wnn..duk yanda zaiso tayi mashi bata ta6ayi ba sbd kunyanshi dake dawainiya da ita har yanxu..yanxun kuma da tayi sai yaji kaman an tsundumashi a aljannah don dadi..ko kwakwkwaran motsi kasayi yayi har saida ta janye bakinta a nashi snn ta sake kwantawa a chest dinshi tana sauke numfashi..hannu daya yakai ya dora a bayanta dayan kuma ya sake tada motar dashi kawai sai ji tayi yajata da gudu sun sake fita daga gidan aikuwa ta dago daga jikinshi da sauri tana kallonshi hankalinta har ya fara tashi tace"innalillahi partner where are u taking me to?..mu koma gida dan Allah"..bai iya ce mata komai ba sai

Please Login or Register in order to submit comment