You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
gida ko asibiti?.."yace"ina asibiti"...daddy yace"alright send me the address na shigo kano sai inzo mu gaisa"..da sauri yace"right away sir..itama tana asibitin yanxu haka"..murmushi daddy yayi kafin yace"ni kai zanzo gani ba itaba"..murmushin shima yayi kafin suyi sallama ya tura mishi address din...cikin mintina qalilan daddy ya karaso hospital din..Bobby da kanshi ya fita ya shigo dashi yanata yaba kyau da tsaruwar asibitin har suka dangana a office dinshi...zaunawa yayi shi kuma Bobby ya bude fridge ya kawo mashi ruwa da lemo snn shima ya zauna suka sake gaisawa...daddy yayita janshi da hira yana yaba asibitin nashi shidai tun yana jin kunya har ya sake ya shigayi mishi bayanin yanda suke gudanar a aiki a asibitin..har Schools da Colleges da yake dasu a sauran states saida ya fada mashi...ya kuma sanar dashi cewa yanxu haka yana preparation na bude Freedom University a Lagos...daddy ya jinjina ma kokarin yaron sosai ya kuma jinjinama kwazonshi da yake iya hada aiyuka da dama haka shi kadai..dukda cewa yana assistant a ko ina shima ba karamin kokari yake ba..nan take yaji ya sake burgeshi matuka..soyayyarshi ta ninku a cikin zuciyarshi fiyeda na baya..saidai ko kusa baiyi mamaki ba sbd yasan jinin Col Attahir zai iya aikata fiyeda haka ma a doron kasa matukar ya gaji mahaifinshi...suna zaune suna wnn hira Aysha ta shigo office din tana kokarin zaro wayanta daya dameta da kara sakamakon kira da akeyi tace"ko uban waye wnn yake damuna da kira oho?.."a tare suka juya suna kallonta jin abunda ta fada...daddy yace"sannu shugaban masu hankali"..batasan lokacinda ta saki waya da jakan nata ya fadi kasa ba sbd muryan wanda taji..sam batayi tunanin ganinshi ba wlh...lokaci daya kuma ta saki murmushi bayan ta dauki bag da wayanta ta karasa cikin office din tace"daddy sannu da zuwa"..girgiza kai kawai daddy yayi yana kallonta..can kuma ya juya yana duban Bobby da kanshi ke kasa yace"nasan kana nan kana fama da ita kou?.."dan dagowa yayi ya kalleta sai kuma ya saki murmushi yana girgiza kai yace"ai tayi hankali yanxu"..daddy yace"kana dai kareta amma ni nasan akwai abubuwanda dole saita yisu zataji dadi"..murmushi kawai Bobby yayi baice komai ba..ita kuma ta wani turo baki a cikin ranta tace"wato da kallon mara hankali sukemin knn da za’a wani ce nayi hankali yanxu"...muryan daddy ya dawo da ita daga tunaninda take nan ta gaisheshi snn yace taje ta kira Bilkisu..bayan few minutes suka dawo tareda Billy itama ta gaida daddy yana tambayarsu ya posting sukace Alhamdulillah...bayan sun gama yace suje kafin ya wuce zai nemesu zaiyi mgn da proprietor dinsu ba musu suka bar office din..shi kuma daddy ya shiga tambayan Bobby if da akwai abunda takeyi wanda ya kamata ya sani Bobby yace sam tayi hankali yanxu ta dena rashin ji..daddy yaji dadi sosai ya kuma ce still dai yanaso yacigaba da monitoring dinta har zuwa lokacinda zata bar makarantan domin koshi a yanxu yaga canji tattareda ita hakan kuma alamane na Bobby ya rike amanar daya bashi knn...Bobby ya amsa mashi da zai kula da ita sosai can cikin zuciyarshi kuma wani abu yaji yazo ya tokare mashi wuya...tunda daddy ya ambaci har zuwa lokacinda zata bar makarantan yaji wani irin sanyi ya kamashi...ashefa watarana gama karatun zatayi ta koma garinsu koh?..shi wlh sam baya kawo hakan a cikin ranshi...baisan ko sbd yanxu yana son kasancewa tarea ita ba amma sam tunanin haka bai taba zuwa mashi ba..yanxu kuma da daddy ya fada saiya tuna mashi cewa watarana da gaske zata bar college dinshi dama kano gaba daya kuma hakan na nufin bazai sake ganinta ba har abada...tunanin hakan saida yasa gabanshi yayi mummunan faduwa..to meyasa bayason rabuwa da ita?..meyasa a kullum yakejin sabbin al’amura gameda ita?..meyasa kuma idan ya ganta da wani yakejin kaman ya rataye kanshi sbd kunci?..for sure zuwa yanxu yasan kishinta yake saidai ko kusa bayaso yayi admitting yana sonta sbd hakan na nufin wargajewar abubuwa da dama a tare dashi..yayi nisa cikin tunani har baiji lokacinda daddy ya mike yana mishi mgn ba...saida ya dafa shoulder dinshi snn firgigit ya dawo hayyacinshi...daddy ya zuba mashi ido sosai yana kallon yanda duk yanayinshi ya sauya lokaci guda...bai tambayeshi dalilin hakan ba sbd a ganinshi ba huruminshi bane dan haka yayi mishi sallama yace zasu wuce Gombe...Bobby yayi mashi rakiya har inda motocinshi suke bayan ya sallami su Aysha ya shiga motar suka fita daga asibitin...Aysha kuma kai tsaye ta bishi office dinshi sbd mgnr changing posting da yace zaiyi mata.
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba... masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
30
Kallonta kawai yakeyi tunda ta shigo office din zuwa yanxu...duk yanda yaso ya dauke idonshi a kanta kasawa yayi...baisan meyasa yakejin wani new feeling tattare dashi ba...baisan meyasa mgnr daddy ya tsaya mashi a rai ba..abu daya daya sani shine ko kusa bayason rabuwa da ita..baiki ta dawwama tana karatu a FCNM ba sbd ya dinga samun ganinta kullum amma saidai sam hakan ba mai yiwuwa bane...sanin kanshi ne hakan bazai ta6a yiwuwa ba koda a garin ga6a ga6a suke kuwa...watanni kadan da ya tabbata basu kai shekara ba suka rage mata ta gama karatunta and this means watanni kadan ya rage masa a tareda ita..watanni kadan ya rage masa kafin ya dena ganinta har abada tunda shidai yasan nor matter the situation bazai ta6a kai kanshi Gombe ba balle watarana yace zai nemeta su gaisa tunda ya shiga garinsu...gaba daya wadan nan tunanin sun cika mashi zuciya sun kuma hanashi sukuni...Aysha da taga idanunshi ne kadai a kanta amma mind dinshi is elsewhere ta dan buga table dake gabanshi tace"Sir am talking"..da sauri ya lumshe idanunshi kafin kuma ya budesu a kanta yanayi mata kallonda zata iya rantsuwa da Allah tunda suke bai ta6ayi mata irinshi ba...voice dinshi can kasa yace"what happened?.."narkewa tayi tana wani kallonshi kasa kasa tace"sir kace fa idan nayi two weeks zaka canxamin posting"...dan wara idonshi yayi a kanta kafin yace"then ki dawo office dina"..ta wani turo baki tace"nidai no dan Allah..cewa fa kayi duk inda nakeso zaka kaini?.."gyara zama yayi still yana kallonta yace"to ina kikeso?.."da sauri tace"eclamptic ward nakeso naje nayi two weeks..the remaining two weeks kuma sai inyisu a Ante Natal Clinic"...gyada kai yayi alaman ya gamsu kafin yace"zakije inda kikeso but on one condition"...da sauri tace"meye condition din?.."yace"bazaki shiga harkan kowane doctor ba a wurin..infact bama doctors kadai ba kowane staff indai namiji ne i want u to stay far away from him"..da sauri ta shiga gyada kai tana murmushi tace"bazan shiga harkan kowaba wlh..aini bana da interest kan doctors ko health workers sbd son matan su yayi yawa..besides inama da wanda zan aura"..fuska a tamke yace"to waya tambayeki?..nace maki inason ji ne?.."dan turo baki tayi tace"to kayi hakuri nidai"..yace"tashi ki barmin office"..ta marairaice tace"sir posting dinfa?.."yana nuna mata kofa yace"i said out"...maimakon ta fita saita fara bubbuga legs dinta a qasa zata fara mishi kuka tace"toba kai kace zaka canxamin idan ma nutsu ba?..alqawari fa ka dauka"...kallon yanda take tale baki yayi kawai sai ya saki murmushi hade da girgiza kai...wnn yarinya shidai bai ta6a ganin irinta ba wlh...ita kuwa kuka ta fara na karya kafin ya dakatar da dariyan da yakeyi yace"da nace saikin nutsu ai ba nutsuwan kikayi ba..yanxun fa kika gama min rashin kunya a nan"...ta wani zaro ido tana cewa"rashin kunyan me nayi?.."fuska a dan daure yace"kikace baki son doctors da health workers..sbd tsabar rashin kunya hadda cewa kinada wanda zaki aura"..if u see yanda ya karasa mgn face dinshi daddaure zakayi tunanin bashi ne ya gama daria a while ago ba..abun yayi mashi ciwo da har ta iya bude baki ta wani ce mishi tanada wanda zata aura?..sai kace cewa yayi shi zai aureta?...ganin yanda ya sake dinke fuska sai tayi kasa da murya tace"to am sorry"..a takaice yace"naji..tashi ki tafi"..kaman zata tashi sama haka ta dauki jakanta ta fita daga office din nashi rai a 6ace tanata faman bambami ita kadai...shi kuwa tana fita ya kifa kai da table din gabanshi ya shiga sauke numfashi.
Washegari haka tazo office din nashi fuskan nan cunkus dashi kaman bata taba daria ba...sbd presence na Dr Aslam yasa bai nemi jin dalilin fushin nata ba yayi mata posting dinta kawai ta tafi...ranan har ya bar hospital din bai sake sanyata idonshi ba...washegari ma same thing happens kuma har ward din da take yaje bai sameta ba..duk jinshi yake wani iri da bai samu ganinta ba...a haka suka cinye satin nan tas bai sake ganin Lamido ba...damuwan da ya shiga a dalilin haka har mamaki yake bashi...yaudai yayi alqawarin dukma ina take zuwa ta 6oye idan ta ganshi sai ya nemota tunda ya tabbata zai iya samun matsala wajen bacci matukar bai sanyata a idonshi ba...cikin toilet dinsu aka ganota wai ashe tana hangoshi ya taho sai tayi wuf ta fada bandaki kuma bazata fito ba har sai ya fita..yaudai asirinta ya tonu dan har office dinshi yajata snn yace ta zauna suyi mgn..idanunshi a kanta kaman yau ya fara ganinta yace"why are u doing this?.."dan turo baki tayi tace"ba kaine ba"..yace"me nayi?.."ta sake turo bakin batace komai ba..shi kuma ajiyar zuciya ya sauke mai karfi kafin yayi lowering voice dinshi sosai yace"to kiyi hakuri"...dagowa tayi ya kalleshi da mamaki...ya sake cewa"kinji?.."murmushi ne ya kwace mata ganin yanda ya maida face dinshi abun tausayi...murmushin shima ya saki mai kyau yana kallon dimples dinta da yakejin kaman ya saka finger dinshi a wurin...ya sake yin kasa da murya yace"kin hakura?.."tace"eh mana..amma zaka denamin masifa koh?.."kallonta ya tsaya yi for some minutes kafin ya sauke numfashi yace"idan kin nutsu kin dena aikata abunda zanyi maki masifan ba?.."murmushin dai ta kara saki tareda fadin"na dena".
Bayan sati hudu...
Tuni sun gama posting dinsu sun koma makaranta...’yan year 3 su besty kenan tuni suma sun rubuta Hospital Final exam dinsu wanda sukayi passing sune suka fara rubuta council exam cikin satin nan...gaba daya Aysha ta zama wata iri daga ita har Billy ba karamin missing Sa’eed suka fara ba tun ma kafin ya tafi...kuka kuwa yana shanshi dan kullum ne idan suka hadu sai anyi mishi kukan nan hadda Billy data kasance abokiyar rigimarshi...shi kanshi shima ji yake kaman yayi kukan amma bazaiyi ba sbd namiji da dauriya aka sanshi amma only Allah knows yanda yakejin zafin rabuwa da zaiyi dasu...ranan Thursday bayan ya fito daga exams yaje hostel ya kwashesu suka fita wai yanaso su ragema juna radadin rabuwa da sukeji...duk inda yasan suna so saida ya kaisu including market da Lamido bata da burin da ya wuce ta shiga kasuwa a kano idan ta koma Gombe tayita bada labarin taje kwari taje sabon gari taje singa taje wambai taje bakin asibiti saidai wnn karon yawon sam baya masu armashi as kowa yanada damuwa cikin ranshi...a takaice sun shafe almost 3 hours suna abu daya kafin daga bisani ya saukesu gidan Hajia itama kuwa hadda dan kwallarta wai ta kusa dena ganinsu tunda Sa’eed zai tafi...kuka sosai sukasha a gidan nata kafin ya sake daukansu sai hostel dinsu..a bakin hostel din ma sun kwashi lokaci mai tsayi yanata aikin rarrashi da basu baki amma har suka rabu baiga alaman zasu dena kuka ba...the next day which is friday ranan sukayi final exam ma’ana sun gama da council saura waiting results kuma...ranan ma haka suka hada kai sunata faman kuka a cikin makaranta har mutane na kallonsu...saida akayi da gaske snn aka samu suka daina kukan yayi musu rakiya da kanshi har cikin hostel dinsu.
Washegari Saturday tun safe Bobby ke kiran wayarta sbd saqo da babanta ya aiko mata dashi amma bata dauki waya ba...saida ya kiraya kusan sau shida snn yayi sa’a ta dauka...kafin yayi mgn Billy tace"sir nice..batada lafia ne bazata iya daukan waya ba"...zaro idanu yayi sosai hankalinshi a tashe sosai yace"meya sameta?.."a takaice Billy tace"fever.."yace"kun kaita clinic?.."tace"sir kasan halinta ai..taki yadda"...da sauri yace"kice mata nace ku sameni a clinic yanxun nan"..Billy ta amsa da"toh.."snn ta ajiye wayar tana duban Aysha da tun daxu ta kudundune cikin bargo ko oxygen na kirki bata shaka...as usual sai da kyar da sidin goshi ta samu ta mike suka tafi clinici din...tun kafin su shiga Bobby dake zaune cikin motanshi ya hangosu..gabanshi yaji ya fadi da yaga situation da take ciki dan ko tafiya ma da kyar take yinshi ga wani irin haske da yaga ta kara tun daga nan inda yake...bude motan yayi kawai ya fita kafin su karasa ya iskosu hankalinshi a kanta yace"kin tabbata only fever ke damunta?.."Billy tace"maybe baza’a rasa headache ba tunda kuka taita yi har yasa mata zazza6i"..kallonta kawai yayi kamar zai tambayi dalilin kukan sai kuma ya fasa...Billy ta sake cewa"sir ciki zamu shiga?.."girgiza kai yayi hankalinshi gaba daya na ga Aysha data samu wuri ta zauna tana sauke numfashi yace"i think saidai muje hospital sbd inaso ayi mata test shi kuma lab din nan ciki sun tashi..ki sata a mota kawai"...ba musu Billy ta sake kamata zuwa inda motarshi yake ta sakata a back seat snn ta rufe kofar...karasowa yayi shima ya shiga yana dubanta yace"ke bazaki jeba?.."girgiza kai Billy tayi tana murmushi tace"no sir..inaso inyi mata girki kafin ku dawo"..gyada kai kawai yayi ya rufe glass dinshi snn ya tada motar suka tafi Billy ta bisu da kallo tana fadin"love birds".🤪
Kai tsaye Freedom ya nufa da ita...yana shiga ciki ko parking daidai bai tsaya yi ba ya bude motar da sauri ya fita zuwa cikin asibitin...few minutes later ya dawo tareda wasu nurses mata guda biyu suna tura trolley bed...bude motan yayi matan suka taimaka mata ta fito suka dorata kan trolleyn snn suka shiga ciki...direct office dinshi suka kaita suka dorata kan bed da yake scanning da other examinations akai snn suka fita...maida kofa yayi ya rufe bayan sun fita ya shiga takawa a hankali zuwa inda take...idanunta yaga a kulle amma still hawaye basu dena fitowa daga cikinsu ba...hannu yakai forehead dinta yaji akwai zafi sosai dan haka ya koma seat dinshi yayi using landline ya kira lab yace a kawo mashi sample bottle...babu wasting of time aka kawo mashi..ya bude wani drawer nan cikin office din nashi ya dauko 5cc syringe da tourniquet kana ya koma inda take...hannunta ya kama a hankali ya daura tourniquet din a jiki aikuwa da sauri ta bude idanu tana kallonshi..ya wani hade rai tareda rike hannun nata da kyau dan yasan tsaf zata iya sawa yaji mata ciwo snn ya soka needle din cikin vein dinta...wani irin kara data saki saira kiris ya ya zare needle din daga jikinta sbd shiganshi da karan nata yayi...haka tana buge buge tana kuka ya dauki sample din nata ya zuba cikin sample bottle da aka kawo snn ya bada yace mp/widal yakeso ayi mashi yanxun nan...bayan fitar mutumin yayi checking vital signs dinta yaga all normal snn ya koma seat dinshi ya zauna waiting for the results...ana kawo mishi ya duba yaga da akwai malaria kadan babu typhoid dan haka ya rubuta drugs da injection da zaiyi mata ya bada aka amso mashi a pharmacy...saida ya gama withdrawing alluran da zaiyi mata snn ya karasa inda take yana tunanin ta yanda zaiyi alluran nan ba tareda ta tara mishi jama’a ba..kallonta kawai yakeyi yanda bacci ya fara daukanta yasan yanxu yana tashinta tayi ido hudu da allura ba karamin rikicewa zatayi ba...hannu yakai forehead dinta ta bude idon a hankali...tana ganin injection a hannunshi ta mike zaune da sauri idonta na cikowa da hawaye tace"Allura zakaimin?.."shiru yayi yana kallonta duk sai yaji ta bashi tausayi yanda tayi tambayar...zaunawa yayi kusada ita yana kallonta a hankali yace"bakya so?."da sauri ta hau gyada kai tana goge hawayenta...yace"amma Aysha alluran ne kadai zai saukar da wnn temperaturen naki da wuri?..bakiji yanda jikinki yayi zafi ba?.."ta shiga yarfa hannayenta hawaye na ambaliya fuskanta tace"nidai banson allura"...kallonta yacigaba dayi not knowing what to do or say...harga Allah yafison ya mata allura sbd fevern zaifi sauka da wuri amma kuma tausayi take bashi da wnn kukan da takeyi...lalla6ata ya shigayi da bata baki amma sai botsarewa take wai ita baza’a mata allura ba...nan kuma yayi abunda bayaso wato forcing dinta dan matseta yayi yayi mata alluran tanata rizgar kuka tana ihu bai saurara ba saida ya gama...sai kuma ya hadata da jikinshi ganin yanda legs dinta ke trembling murya can kasa yace"am so sorry"..kuka kawai take har breathe dinta yana kamar zai dauke...zaunar da ita yayi kan gadon shima ya zana gefe tareda cupping fuskanta yana kallon cute face dinta yace"stop crying mana..yanxu fevern zai sauka kinji?..am sorry"...kasa ce mishi komai tayi sai hawaye da sukaki tsayawa...Bobby ya lumshe ido ya bude shima kaman zaisa mata kukan yace"nace fa am sorry Aysher..kukan ya isa haka mana"..hannu takai tana goge tears din nata baisan lokacinda ya daga hannunshi ba kawai sai ganinsu yayi akan fuskanta yana goge mata tears din...saida ya gama snn ya sake kasa da murya yace"zakici abinci?.."girgiza mishi kai tayi tana turo baki shi kuma ya saki murmushi kafin yace"toki kwanta abinki..idan fevern ya sauka sai in maidaki hostel"...batayi masa musu ba ta juya masa baya ta kwanta shi kuma ya sake lumshe ido yanajin wani abun mai kamada magnet na kokarin janshi gareta...ganin ta cure legs dinta wuri daya ya janyo kujera ya zauna bayan ya gyara mata kafan sai ya tallabi cheeks dinshi yana kallonta...ta dauki almost an hour tana bacci shi kuma yana nan zaune inda yake yana kallonta..he just can’t take his eyes off her baisan meyasa ba...he drives pleasure staring at her..har wani smile yake saka akai akai ba tareda saninshi ba...a hankali yaga ta fara mosti kaman zata bude ido saita fasa ta wani turo baki inda kasan idonta biyu...daria sosai ya saki ganin yanda ta turo bakin..ya lumshe ido tareda kai hannunshi a hankali ya aza kan lips din nata sai kuma ya janye da sauri yana yarfa hannun idanunshi a kanta sbd wani abu da yaji kaman electric shock...sake juyawa tayi nan hulan dake kanta ya zame tareda faduwa kasa black silky hair dinta da bata cika yima kitso ba ya bayyana...saida breathe dinshi ya dauke na wucin gadi ganin gashin nata...da dadewa yasan tanada gashi tunda ya ta6a ganin kan nata amma sai yaga kaman daga wancan lokacin zuwa yanxu an kara mishi tsayi da baqi dan har wani daukan idonshi yakeyi...sake lumshe idonshi yayi a karo na ba adadi kawai sai ya mike daga wurin ya koma kan sofa ya zauna because abubuwan nan da yakeji bana lafia bane ya sani...tsaf zai iya mancewa ya aikata abunda daga baya zaizo yana regretting so it’s better he leaves kafin azo a samu matsala...haka yayaita zaune yana duban agogo saida tayi baccin 3 hours cur snn ta tashi tana wani yatsine fuska kaman wanda taga poopoo...mikewa yayi daga inda yake zaune ya karasa kusada ita yana dubanta with concern yace"how are u feeling now?.."a hankali tace"da sauki..inajin yunwa"..murmushi ya saki tareda sunkuyawa ya dauko hulanta dake kasa ya mika mata yana cewa"ki shiga bathroom ki farayin brush kafin a kawo abincin"...batayi mishi musu ba ta sauko daga gadon zuwa bathroom dinshi...da mouth wash tayi amfani da wanke bakinta snn ta dauro alwala ta fito rikeda hulan nata a hannu...kallon gashinta daya sauka shoulders dinta yayi yace"ya kika cire hulan kuma?.."turo baki tayi ta mayar da hulan batace komai ba...carpet ya shimfida mata da kanshi snn ya dakko jilbab dinta daya cire mata daxu shima ya mika mata..amsa tayi ta zura ta tayar da sallah shi kuma ya koma ya zauna waiting for abincin da yayi mata order yazo...tana idar da sallah ta sake dubanshi tana kwabe fuska tace"yunwa fa nakeji"...murmushi ya kara saki yace"Aysher ki kara hakuri mana..nayi ordern abincin ne and nasan suna hanya inshaAllah"...gyarawa tayi zata kwanta nan kan carpet din yayi sauri tasowa daga inda yake yace"karki kwanta kasa"..ba musu ta mike ta koma gado...bayan few minutes akayi delivering abincin nata dan haka ya mika mata gaba daya snn ya zauna yana kallonta...ita kuwa cik abincinta take hankali kwance sai kallon dimples dinta dake lotsawa idan tana tauna abincin yake...ba kanta ya fara ganin dimples ba amma nata kullum shi yake tempting dinshi yaji kaman yaje yasa finger dinshi a wurin...tana gama cin abincin tasha drink din kadan snn ya bata drugs suma tasha badon tanaso ba...saida yaga ta nustu ta dawo hayyacinta snn yace"can we talk now?.."kallonshi tayi batace komai ba...shi kuma yana kallon eyes dinta da sukayi luhu luhu sbd kukan da taci yace mata"what happened to ur eyes?.."raurau tayi da ido zatasa mishi kuka yace"I didn’t ask u to cry...cewa nayi meya samu idonki?.."tana kwabe fuska tace"kuka nayi"..."kuka?.."ya maimaita abunda ta fada kafin yace"me aka maki kikai kuka da har ya sanya maki zazza6i haka?.."lumshe ido tayi nan hawayen dake ciki suka silalo kan fuskanta tace"Bestie ne zai tafi"...cak yaji komai nashi ya tsaya including breathe dinshi...nan take face dinshi ya sauka murya a dakile yace"sbd shi kike kuka knn?.."cigaba da kukanta take tace"tafiya fa zaiyi ya barmu...ba sun gama council ba"..a kufule ya mike zuwa inda ya ajiye wayoyinshi yace"sai ki bishi ai"...harara ta watsawa bayanshi tana turo baki...ya dauki wayoyinshi daya ajiye nan wurin snn ya kama hanya zai fita yace mata"fito mu tafi"...da kallo kawai ta bishi tana mamakinshi..har yanxu bata bar mamakin yanda he can change forms in a blink of an eye ba..he can be nice for a second and become annoying the other second...shiyasa kwata kwata bata gane mashi...mikewa tayi ta zura jilbab dinta snn ta fita daga office din..a bakin kofa ta sameshi yana ganin ta fito yayi locking office dinshi snn ya wuce parking space...motanshi ya bude ya shiga itama tana karasowa ta shiga sai turo baki take...bayan sun dauki hanya ta dan saci kallonshi ganin yana driving..tunda suke bata ta6a ganin ya tuka kanshi ba saidai yayi d’urum a baya mota ana driving dinshi yau kuma wane salon ne yasa shi driving din oho?...motan yayi tsit ba abunda kakeji sai sanyin ac dake tashi...wayanshi dake ajiye kan dashboard ne ya fara ringing...yayi connecting Bluetooth snn ya daga..daga daya 6angaren da igbo Mummy tace"Bobby where are u?.."shima da igbo din yace mata"ina kan hanya Mummy..what happened?.."tace"jikin yarinyar nan ne naga kaman gaba yakeyi wlh..ko asibitin zamu kawota?.."yace"aah Mummy gani nan zuwa gidan yanxu"..Mummy tace"to kayi sauri dan Allah"..yace"toh.."snn ta kashe kiran...Lamido data kasa kunne tana jinsu bata fahimci komai a zancen nasu ba tace"kilan mamarshi ce"...yaji abunda ta fada sarai kulata ne kawai baiyi don a yanda ta kular dashi tsaf zai iya kwada mata mari wlh...haka ta ringa baza ido tana kalle kalle har suka iso kafar gidansu...maimakon ya shiga da motar ciki sai yayi parking a nan waje ya bude motar ya fita ya wani sake hade ranshi yace"saura kuma ki fito daga ciki kiga me zanyi maki"...tabe baki tayi ta kauda kai shi kuma ya juya ya nufi gate..kwankwasawa yayi mai gadi na lekowa yaga shine ya bude mishi da sauri ya shige cikin gidan...Lamido na ganin ya shiga ta bude motar ta fito tana karema gidan nasu kallo tace"ai wlh saina fito na bawa idona abinci"..sake juyawa tayi tana kallon zabgegen mansion din tana girgiza kai tace"gaskia mutumin nan me kudi ne..ji gida kaman ba’a Naija ba ni Aisha"..karasawa tayi jikin gate din ta shiga lekawa ta wata ‘yar karamar kofa kamar daga sama taji an danne mata horn ta bayanta...a rikice ta matsa daga wurin tana kallon motar dake kokarin shiga gidan sai tayi saurin komawa inda motarshi yake kafin ta shiga taji ance"yammata"..juyawa tayi tana kallon matar duk sai taji kunya ya kamata tana leka musu gida..ta shiga washe baki tace"ina..ina yini"..aunty sumy ta bude mota ta fito zuwa inda take tana kallonta da fara’a tace"lafia lau yammata..zaki shiga ciki ne?.."da sauri tace"aah tareda proprietor muke shine nake jiranshi"..ta karasa mgnr duka daburce kaman matsoraciya...aunty sumy ta saki smile jik tareda Bobby suke tace"to mu shiga daga ciki mana saiki jirashi a can"..tun kafin ta rufe baki Aysha tace"aa ba saina shiga ba wlh..yace kar in shiga"..dafa shoulder dinta aunty sumy tayi tace"karki damu bazaiyi maki komai bafa..aini nace ki shiga sbd haka muje
Book Chapters
Chapter 25
Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59