gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Dr.bob Complete Hausa Novel by by Aysha Rano Chapter 13 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bazamu samu mai kyau ba"...wani murmushi Aysha ta saki tareda mikewa zuwa wardrobe dinta tace"tsakanin keda bestyn za'aga waye dan rainin wayo a cikinku...ke kice mishi dan rainin wayo shima ya kiraki da haka..duk zaku gaji da munafurcinku ne ma ku dawo kan hanya"...cak Billy ta tsaya da kokarin saka skirt da takeyi tace"what are u insinuating?.."Aysha ta fashe da daria itama ta fara zura kayanta tace"nothing ooo...am just talking to myself "...tsaki kawai Billy ta saki taci gaba da shiryawanta...ko ten minutes basu kara ba suka gama shiryawa kowa ta dauki abinda take bukata suka fita inda Sa'eed ke jiransu...yana daukansu direct sukayi Zoo road inda za'ayi musu make up.

Mummy ce ta Aunty sumy suka fito compound din gidansu kowacce sanye cikin lace dinta na alfarma sunyi kyau sosai da gani kasan gidan biki zasuje...sai Ilham da Miemie dake sanye cikin nasu lace din suma iri daya da yayi matukar amsarsu Sab kuma ya dade da komawa makaranta...aunty sumy har ta bude motarta da zasuje bikin da ita Mummy tace" sake kira min Bobby Sumayya...wlh idan baije bikin nan ba sai naci mutunchinshi"...aunty sumy murmushi tayi kafin ta sake dialing number Bobby ta mika mata wayan...saida ya kusan katsewa yayi picking Mummy ko jira yayi mgn batayi ba cikin igbo tace"wato ka rantse dai bazaje bikin nan ba ko Bobby?..haka daxu kiri kiri kaki zuwa daurin aure shine yanxu dinner ma kace bakazo ba?.."saida ta bari ta kai aya snn yayi kasa da murya yace"Mummy ina Hospital fa..wlh aiyuka ne a gaba na idan baki yadda ba ga Nur ki tambayeshi"...a takaice tace"bawa Nur din waya"...ba musu ya mika mishi wayan...shima yana amsa before yayi mgn Mummy tace"kana jina Nuru?.."yace"inaji Mummy"...tace"tell him duk ya sake muka bar wurin dinner nan baije sai yaga 6acin raina wlh...kan wane dalili zaiki zuwa bayan yasan yanda nake da uwar yaron nan...snn shima abokinshi ne amma sbd iskanci ya mishi yawa ya wani cemin yana aiki a gabanshi"...Nur yayi kasa da murya sosai yace"kiyi hakuri Mummy zamuzo tare inshaAllah...Allah ya huci zuciyarki"...bata sake cewa komai ba ta kashe wayar...suka shiga motar aunty sumy gaba dayansu suka fita daga gidan...shi kuwa Bobby dafe goshinshi yayi yana dan murzawa a hankali...duk yaji maganganun da Mummy ta fada and baiji dadin musun da yayi mata ba sam...ya mance when last Mummy tayi mishi mgn cikin fushi haka...kuma shi kanshi yasan bai kyauta ba...angon abokinshi ne sosai dan lokacin suna lagos shine babban abokinshi...Mom dinshi kuma aminiyar Mummy ce itama tun a Lagos suke zumunchi har zuwa yanxu basu dena ba shiyasa ma take kokarin hadashi aure da qanwar angon Rayhan shi kuma baya sonta sam...kafin Nur yayi mgn ya dauki car keys dinshi tareda mikewa yace"muje ka rakani wajen bikin nan plss..nasan yau idan banje ba mai rabani da Mummy sai Allah"...Nur daria ya dan saki shima ya mike tsaye suka fita daga office din snn yace"nima dai banga dalilinka na kin zuwa ba...angon nan fa abokinka ne kuma yayan matar da zaka aur..."Bobby bai tsaya jin karshe ba ya kara gudun tafiyarshi ya barshi a baya dan bayason ji sam...baisan meyasa ya tsani a hadashi da wnn Rayhan din ba wlh...he hates her with passion...saida suka tsaya nan gidansu Bobby sukayi wanka kowa ya sake shiri snn suka tafi wurin dinner a motan Nur...lokacin har anyi sallahn isha dan haka sukavfara tsayawa masallaci auka gabatar da nasu snn suka wuce...suna isa hall din amarya da ango na isowa...basu bi takan brides maida da sukaga anata faman jerasu ba wai da sunan zasu shiga da amarya kai tsaye suka shiga hall din...duk iya wulla idonsu basu hangi Mummy ko su antu sumy ba coz hall din nada girma sosai dan haka kawai suka karasa wani table suka zauna Bobby sai faman cika yake yana batsewa dan ko Allah yasan shi ba maison zuwa biki bane...sam bayason hayaniya shiyasa duk wani abu indai ya hada da taron jama'a shiga bai sonshi sbd tsabar rashin son mutane irin nashi...a can waje kuwa saida su Aysha suka shirya kansu tsaf snn mc yace ma dj ya sakar musu waqan shigowa da amarya...dj kuwa yasa waqan da sukace sunaso snn suka fara shigowa a hankali suna dan bin waqan hade da rawan da yayi matching song din sosai...Aysha ce a sahun farko sai Rahma a gefen ta su Billy kuma suna bayansu wasu kuma suna bayan amarya da ango ma'ana sun sanya su a tsakiya knn...tunda suka shigo hall din gaba daya kallo ya koma kansu gaba daya lace sukayi anko sea green har head dinsu ma sea green sai dinki kawai daya bambamta...su Aysha ansha make up sosai dam idan ka kalleta zaiyi wuya ka ganeta sbd tsabar kyau da tayi...Nur ne ya fara ganeta aikuwa ya wara ido sosai yana kallonta sai yaga almost gaba dayansu ma students dinsu ne...to me ya kawosu nan kuma?..bai samu amsar tambayan shi ba saida ya ga amaryar itama yaga student dinsu nan take ya saki murmushi yana fadin"No wonder...Bobby kasan yaran can gaba daya students dinmu ne...amaryar ma ai Nursing takeyi na ganeta a year two take"...Bobby da gaba daya hankalinshi ke kan wayanshi dan dagowa yayi a hankali yana kallonsu and idanunshi basu fada ko ina ba sai kan Lamido dake tikan rawanta hankali kwance tana smiling da gani tana enjoying abunta...wani irin haushi yaji ya turnukeshi...baisan meyasa these days yake yawan haduwa da ita ba...ya tsani ganinta wlh sbd duk ya sauke idonshi akanta yana sashi tunowa da abubuwanda ya faru dasu a baya...abun takaicin kuma duk yanda yaso dauke idonshi kansu kasawa yayi har suka raka bride and groom suka zaune snn sukayi dividing kansu into two wasu suka tsaya side din amarya wasu side din ango suna cigaba da rawansu...gaba daya hankalin kowa na hall din na wurinsu dan ba karamin burgewa sukayi ba...daya bayan daya sukw fitowa kowacce ta taka mutane suka fara zuwa suna musu liki abun dai dai wanda ya gani...Dr.Bobby kuwa haushi ne cikeda zuciyarshi yana mamakin yanda iyayen yaran nan suka bari suka fito biki haka gansansan dasu ko mayafi babu...saida suka gama rawarsu snn suka zauna nan kuma mc ya fara kodasu yana yabon irin rawar da sukayi...har zuwa yanxu basu hangi su Mummy ba bayan amarya da ango sun fito fili aka kira Maman ango snn ya gansu sun fito suna ma bride da groom ruwan kudi har su Miemie da suke kanana...suna hada ido da Mummy tayi musu alaman suzo da hannunta...ba musu suka mike zuwa inda suke shidai Bobby fuskan nan a daure kaman wanda aka aikoma sakon mutuwa...suna zuwa Mummy ta zaro bundle na 500 daga jakanta ta mika musu wai suyi liki dashi...Bobby ya dan dauke kanshi tareda zaro wanda ya fito dasu daga aljihunshi ya shiga likama amarya da angon...shima Nur ya zaro nashi ya fara likin...bayan sun gama ango ya mika musu hannu suka gaisa tareda congratulating dinshi suka bar wurin amarya dai kanta na kasa tana mamakin a ina mijinta yasan provost da proprietor dinsu...su Aysha kuwa suna zaune inda aka tanadar musu dan haka ba wanda ya lura dasu a cikinsu...biki yayi biki yayinda wayanta dake cikin bag dinta keta vibrating alaman ana kira ita kuma da gayya daki dauka dan tasan Prof ke kira ita kuma fushi takeyi dashi...saida taga ba dena kira zaiyi ba ta koma can bayan hall din inda ba hayaniya sosai ta samu seat ta zauna snn ta zaro wayan daga bag dinta tareda sliding takai kunne...ta wani cuno baki taki cewa komai kaman yana ganinta...a hankali taji yace"baby girl fushi kikeyi koh?.."saida ta murguda masa baki snn tace"nidai na dena kulaka"...yace"subhanallahi baby idan kika dena kulani ya zanyi?..kinaso kiyi kisan kai koh?.."sake murguda bakin tayi tace"to ba kaine ba...cewa fa kayi bazakazo in ganka ba"...yace"wlh ni kaina ina son ganinki baby girl amma baa wurin biki ba...haka nan sai in kama biyoki wurin biki niba karamin yaro ba"...ta wani tale baki kaman zatasa kuka tace"haka ma kace kou?..to wlh idan bakazo yanxu ba baka kara ganina sai mub gama Clinical Posting"...da sauri ya wara idanu sosai yace"Subhanallah baby how could u do this plss?..ai abun bai kai nan ba gani nan tahowa yanxun amma bazan shigo ciki ba zan kiraki ki fito kinji?.."nan da nan ta saki kasaitaccen murmushi har dimples dinta suka lotsa tace"that's my baby boo..ina nan ina jiranka plss and don't keep me waiting"..yana murmurshin shima yace"wane ni?..am coming right away inshaAllah"...tace"ohk bye sai kazo"..shima yace mata"bye snn suka ajiye waya...ta mike daga wurin tana kokarin maida nata wayan cikin jaka idonta ya sauka a kanshi ya wani hakimce kan seat yana kallonta with his big eyes...gabanta taji ya fadi tayi saurin kawar da kanta tana salati...meya kawo wnn mutumin nan wurin kuma fisabilillahi?..sake dagowa tayi still taga idanunshi a kanta yana mata wnn kallon dake sata nutsuwa ko batayi niyya ba...sunkuyar da kanta tayi ta hadiye wani yawu da taji ya cika mata baki snn ta juya a hankali ta bar wurin fatanta Allah yasa baiji abunda take fada ba...ko wane irin asiri yakema idanunshi oho?..batasan ko kowa yanajin wani abu idan sun hada ido ba amma ita dai Allah ya gani tsoronshi ma takeji...ta tabbata ba karamin mara imani bane dan ko a fuska baiyi mata ruwan mutanen kwarai ba uwa uba kuma gashi inyamuri...duk dunia a ganinta babu azzalumin qabila kaman inyamurai shiyasa sam bata son tana hada harka dashi dan a cewarta da kyar idan baya daya daga cikin masu assasa yakin biafra.😆
Shima a nashi bangaren kallonta kawai yake yana mamakin gangancin da yasa iyayenta suka turota karatu wani gari bayan sunsan halinta...duk mgnr da tayi a kunnenshi tayi su ya kuma tabbatar da cewa bayan sangarta dake damunta hadda rashin tarbiyya ma...idan ba haka ba why zata ringa behaving haka?..yanxu dubi yanda ta taho biki ko mayafi babu snn ta fito da gashi waje ga kayan jikinta sun matseta sbd tsabar rashin sanin darajar kai...ya saki wani hadadden tsaki shi baisan dalilinda yasa wasu matan ke neman maida kansu wawaye ba wlh..shi sam bazai iya auren mace mai irin halinta ba...macen da bata ajiye komai ba sai shegen shagwaba da rawar kai ai yanaga idan ya auri mai irin halinta kilan kullum sai yayi mata dan iskan duka sbd kular dashi da zatayi...tsakin da ya saki ne ya dawo da hankalin Nur daketa faman danna wayanshi kanshi...yace"hope lafia kake sakin wnn tsak haka?.."harara ya watsa mishi mai kyau ba tareda yayi mgn ba...kawai haushin kowa da komai ma yaji yanaji and he doesn't know why...Nur da yaga kallon da yayi mishi sai yaci gaba da abunda yake cikin wayanshi yana fadin"easy dude ai bani na kar zomon ba and ko rataya ba wanda ya bani"..wani hararan Bobby ya sake maka mashi duk yaji zaman wurin ma ya gundureshi...mikewa yayi zuwa wurin da ya hango Mummy ya samu ya lalla6ata wai yanaso yaje gida ya huta sbd zai fita aiki da safe gobe...bata hanashi ba tace suma sun kusa tahowa gidan...yana barin wurin kai tsaye ya wuce waje dan ko second daya baison karawa nan ciki dan wani irin haushi yakeji from no where...text ya turama Nur yace ya fito su tafi snn ya karasa jikin motar nashi ya jingina dashi...har bayan 20 mins Nur bai fito ba ran Bobby duk ya gama 6aci na barinshi da yayi a tsaye cox key yana hannunshi balle ya bude mota ya shiga...yana kokarin sake dialing number dinshi wani mota yayi parking kusada nasu...baisan meyasa a kallon farko da yayiwa motar ya ganeta ba...it was the same car da suka shiga itada mutuminda yakeda tabbacin saurayinta ne ranan da sukayi reporting a Hospital dinshi...wani tsakin ya kara saki yanajin haushin Nur for not coming out har wnn mutumin yaxo ya sameshi a wurin...yayi kaman zai koma cikin hall din idanunshi suka hango mishi ita ta fito daga ciki ana tafiya kaman baza'a taka kasa ba...fuskan nan daukeda murmushin dake sa dimples dinta fitowa sosai dan yana iya ganosu daga nan inda yake tsaye..da yake inda yake babu haske sosai har ta karaso wurn bata lura dashi ba shi kuma baisan dalilinda yasa ya kasa dauke idonshi akanta ba duk kuwa da yanda yaso yin hakan...as usual tana karasowa ya bude mata mota ta shiga snn shima ya shiga ya rufe kofa...Bobby ya runtse ido yanajin wani zafi sosai a jikinshi...shi baisan wnn masifa ba da babu dama yaga yarinyar nan sai ranshi ya 6aci kuma duk laifin Nur ne dan daya fito sun wuce tun daxu yasan babu yadda za'ayi yaga wnn kayan takaicin...gaba daya yaji yanajin haushinsu daga ita har saurayin nata...wai babban mutum dashi ya rasa inda zai kare sai akan wnn fitsararriyar yarinyar sangartacciya ma da bata ajiye komai ba sai dan banzan shagwa6a...ganin time na sake kurewa Nur bai fito ba ya danna mishi kira...yana dauka yace"malam you should have told me if u are not going to leave now ba wai ka shanyani waje inata faman jiranka ba"..da sauri Nur ya mike daga inda yake zaune yace"wai kana nufin kana waje?.."tsaki kawai Bobby ya saki tareda kashe wayarshi...shi kuma Nur fitowa yayi dan sam bai lura da message daya tura mishi ba...yana karasowa ya bude mota suka shiga snn yayi reverse suka fita daga wurin fuskan nan na Bobby a dinke tsaf kaman wanda bai san me ake nufi da daria ba.














Rano✨





Wnn littafin na kudi ne...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
17
A bangaren love birds kuwa musayar kallo aka shigayi bayan an shiga motar...sai daga baya Prof yayi breaking silence din da fadin"baby girl kinyi more than kyau..i don't how to put it but u look extraordinary gorgeous"...murmushi jin dadi ta saki tanata juya ido dan ba karamin dadin compliment din taji ba shiyasa ma ta dage mishi yazo dan bazata so tayi asaran duk wnn kwalliyan a banza ba tareda ya gani ba...sai kuma ya dan hade rai yace"amma baby haka kike yawo ko veil babu a jikinki?..look at yanda kika fito da gashinki kowa yana kallo this is not fair mana"...murmushi ta kara saki kafin tace"baby sbd biki nefa"yace"next time ko bikin wa akeyi banson ana ganinki a haka...banaso"...hannu takai tayi saluting dinshi still tana smiling tace"yes sir..ur wish is my command"...daria yasa sbd ganin yanda tayi itama tana tayashi...bayan sun gama daria kuma sai hira ya 6arke a tsakaninsu...labari sukesha sosai dan har ta mance da wajen biki suke tanata buga love abunta...yana fada mata zaiyi tafiya zuwa malaysia gobe ta dinke fuskanta tsaf kamar ba ita ke daria a while ago ba...shima nashi fuskan ya marairaice mata yace"baby bafa dadewa zanyi ba and believe me kullum zamu kasance tare a waya"...a takaice tace dashi"how many days?.."shiru yayi yana kallonta kafin a hankali yace"four weeks"...ganin zata fara mishi kuka yayi saurin matsawa kusada ita yana cewa"C'mon baby kar kimin kuka please...nima fa baa son raina bane ya zama dole ne shiyasa zanje but Allah kadai yasan how am going to miss u"...goge hawayenta tayi tana turo baki tace"kuma shine baka fadamin da wuri ba"..yace"am sorry kukan nan ne banaso amma am sorry kinji..pardon my manners"...sake turo bakin tayi wnn karon hadda dan murgudashi tace"kuma na dena kulaka"..ya saki murmushi yace"kicigaba da murgudamin bakin nan baby duk abunda ya biyo baya don't blame me"...sake turo bakin tayi tana taleshi kaman zatasa wani kukan yayi saurin dakatar da ita da fadin"ohk ohk yi hakuri da wasa nake..am sorry okay?.."to cut it short Aysha daga nan ko cikin hall din bata koma ba bayan sun gama hiransu ta kira Billy a waya ta fito suka tafi...as usual yayi musu takeaway na kayan kwadayi snn yayi dropping nasu a hostel.

Dr.Bobby kuwa Nur na ajiyeshi a gida ya shige ciki ko sallama bai tsaya sunyi dashi ba...kawai gaba daya jinshi yake wani iri shiba mai lafia ba kuma shi ba mara lafia ba...wanka kawai ya sakeyi ya kwanta amma duk kokarinshi na ganin yayi bacci abun gagaranshi yayi...har su Mummy duka dawo bai runtsa ba...yanajinsu yaji fitowa yasan suma sunyi tunanin yayi bacci shiyasa basu nemeshi ba shi kuma bacci kiri kiri yace bazai daukeshi ba...har dare ya raba bai samu baccin ba haka yayita juyi kan gado yana faman tunanin abunda sam bai shafeshi ba sai can wajen 3 baccin ya lalla6o yayi gaba dashi...rashin samun bacci da wuri yasa ya makara sallahn asuba dan time din daya tashi an idar da sallah sai a gida yayi nashi snn ya sake kwanciya amma still baccin bai daukeshi ta dadin rai ba saida ya gama ja masa aji...can cikin baccin ringing din wayanshi ya tasheshi...a fusace yakai hannu ya dauko wayan yayi sliding yakai kunnenshi ko sunan mai kiran bai tsaya dubawa ba...daga can 6angaren Rayhan tace"uncle bobby"...ya runtse ido yanajin wani irin haushinta na lullu6eshi...yanxu dama duk uban kiran nan da ake jera mishi wnn yarinyar ce?...yana kokarin kashe wayarshi dan yasan yana bude baki mgn zai fada mata mara dadi yaji ta sake cewa"uncle bobby kayi hakuri plss...na kasa hakura ne...jiya Mummy ke cemin kaje wurin dinner kuma har ka tafi ban karaso ba...a wurin make up ne aka 6ata mun lokaci amma naso haduwa dakai sosai"...shiru ya sakeyi yanajin kaman yakai hannu ya kwada mata mari ta cikin wayan..he is just trying to control his temper sbd idan ta kaishi bango bazataji da dadi ba...jin shiru bai still baice komai ba tace"uncle bo..."bata karasa ba ya katseta da fadin"ke hold it plss..how dare u call me at this time of the day?..are u insane?..bakisan safiya bane ko bakisan i might be sleeping ba?.."kwantar da muryanta tayi sosai tace"kayi hakuri dan Allah..naga 8 ya wuce so i taught kana Hospital..am sorry"..tsaki ya saki bayan ya duba wall clock din dakin nashi yaga it's 8:36 dan haka ya kashe wayan kawai tareda jan duvet ya lullu6e har kanshi dashi...kawai shidai gashi nan ne amma sam dadin jikinshi at all..wani irin weakness yakeji all over him ga kuma zuciyanshi da bai mishi dadi shima...haka nan ta kama kiranshi da sassafen Allah sai kace batada aikin yi...shi tunda yake bai ta6a ganin mayyar mace kaman Rayhan ba wlh...ace mace kaman chewing gum duk wulaqancin da yake mata har yanxu taki rabuwa dashi...haka yacigaba da juyi a kan gado shi bai koma bacci ba kuma shi bai tashi yayi abunda ya kamace shi ba...daga karshe dai da kyar ya iya mikewa yasa sport wears dinshi ya shiga jym wai ko zai dena tunanin abunda bai kamace shi ba.

Karfe uku dot yayiwa Aysha a Freedom Specialist Hospital...yau ko jiran bus bata tsaya yi ba besty ya kawota sbd tanaso ta wanke laifinta na jiya shiyasa ta fito as early as possible...tana shiga ward din taci karo da incharge na gaba daya maternity matron Salamatu sai midwife data rike mata aiki ranan da taje biki sai kuma wasu staff guda biyu da take ganinsu a eclamptic ward sai kuma alhaji Dr.Bobby dake tsaye hannayenshi zube a aljihu yana sauraronsu...wani irin dum taji gabanta ya fadi dan tasan taron bana lafia bane...Matron salamatu ceta fara ganinta dan haka tace"yauwa ga yarinyar nan doctor"..juyawa yayi a hankali ya kalleta sam baiyi mamakin ganin itace na sbd jikinshi ya bashi babu mai iya aikata wnn danyen aikin sai ita...gashi kuma hasashenshi ya zama gaskia..Aysha dai kasa tayi da kanta da sauri tana karanta lailaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimun a cikin zuciyarta...har yanxu heart beat dinta bai dawo daidai ba...saida matron ta sake yi mata mgn snn tayi karfin halin daga kafarta ta karasa ciki...daga gefe ta tsaya kanta kasa tana karanto duk abunda yazo bakinta...idanunta lumshe tasan ko bata gani ba idanunshi ke yawo a kanta dan taji wnn hadadden tsoro da firgici da take shiga idan ya kalleta...Matron ce ta fara jifanta da tambayan da ya kusa sata sakin fitsari sbd tsoro.."meya hanaki zuwa aiki jiya?.."tayi shiru tana tunanin karyar daya kamata tayi...matron ta sake cewa"kinsan asarar da kika janyo mana kuwa?..kin tafi kin bar daki ba kowa snn ga patients duk babu mai kula dasu har daya daga cikinsu ta rasu sbd carelessness dinki"...a razane ta dago tana kallon matron din abunda ta fada..she can't believe wata ta mutu sbd rashin zuwanta aiki jiya..."innalillahi wainna ilaihi rajiun mena janyoma kaina haka?.."ta fada cikin zuciyarta...lokaci guda hawaye suka ciko idonta yanxu hakan na nufin tayi kisan kai knn?...Dr.Bobby da tunda ya dora idanunshi kanta bai sauke ba ya daka mata wani tsawan daya sake firgita ta ganin yanda tayi banza da mutane kaman bada ita ake mgn ba...yace"bakida baki ne?.."da sauri ta shiga girgiza kai alamar tana dashi...ya sake tamke fuska snn yace"oya speak up..tell us exactly why u left them all alone har kika janyo mukayi asarar rai"...bakinta ta shiga motsawa tanason tace wani abu amma ta kasa...ta sai san ko kwaya takesha bazata yi karyan batada lafia ba tunda ya ganta jiya a wurin dinner... ganin batada mafita kawai ta shiga yarfa hannayenta hawaye na turereniya kan cheeks dinta tace"am...sor..ry"..Matron tace"ko dan gaba baa yin irin haka a asibiti..da kikasan bazaki zoba sai samu wata ta rike maki amma ba ki tafi ki bar patients on their own ba sbd ba wanda zaiyi tunanin su kadai ne...ba don Allah ya taimaka wadan nan sunzo jiyan ba da kilan asarar da zamuyi sai yafi haka"..kuka kawai takeyi tana gyada mata kai...Bobby ya zaro kudi a aljihu ya mikama mutum biyu da suka taimaka suka rike dakin snn yayi musu godia suka wuce...Matron da taga yanda ranshi ke 6ace tace"ayi mata uzuri dr kaga yarinya ce..zanyi mata fada inshaAllah bazata sake aikata makamancin haka ba"...bai ko kalleta ba bare tasa ran zai amsa idanunshi kan Aysha da har yanxu bata bar kuka ba yace"wuce muje"...a rikice ta dago tana kallonshi...ya zuba mata idanun nan nashi aikuwa ba shiri ta wuce gaba tana cigaba da kukanta...haka suka fito daga ward din tana gaba yana binta a baya har zuwa office dinshi...karasawa yayi seat dinshi ya zauna fuskan nan ba sarari yace"sbd bakida hankali kika wuce kika barmin patients su kadai dan bakisan aikinki ba koh?..anya kuwa bada malpractice kikayi passing Clinical skills dinki ba?.."dukda halin da take ciki mgnrshi ba karamin kular da ita yayi ba...wato ita yake nufi tana satan amsa amma Allah ya isanta wlh...cikin daga murya yace"are u deaf ina miki mgn zakimin shiru?..are u sick?.."runste idonta tayi sabbin hawaye na sake gangaro mata...itadai yau ta shiga uku da masifan wnn mutumin...sai ihu yakeyi mata kaman ita tajs ta shaqe matar ta kasheta...shima runste nashi idon yayi yana murza goshinshi trying very hard to control his temper don idan ya biye ta zuciyarshi yana iya gaggaura mata mari sbd haushin datake bashi...what did she think of herself da zai ringa mata mgn tana banza dashi...ganin bafa shiru zatayi ba ya buga table din gabanshi cikin karaji yace"kin rufemin baki ko sai na gaura maki mari a wurin...are u even alright da zaki sani a gaba kina min kuka?..are u mad?.."ya karasa mgnr cikin tsananin 6acin rai...sbd tsoratan da tayi batasan time data hadiye kukan nata tana toshe baki da hannayenta ba...shi kuma yacigaba da fadin"from today onwards aikinki ya dawo office dina...ke zaki dinga cleaning min office kullum kina wanke toilet dina...snn duk wani aike na office dina ke zaki dinga zuwa zan sallami cleaner da messenger dina har zuwa lokacin da zaki gama punishment dinki...if u like ki tafi gidan biki ku hadu da saurayinki kiqi zuwa aiki kiga yanda zanyi dake lazy fellow kawai"...har yanxun idanu a lumshe take sauraronshi...wato ma itace zata zama mishi cleaner kuma messenger sbd bashida imani...kuka kawai takeyi har yanxun batace mishi qala ba...shi kuwa kallonta yake har yanxu yana ganin yanda dimples dinta ke fitowa as a result of kukan da takeyi...ya sake daure fuska snn yace mata"go to the Nurses Station kice ina kiran Zarah"...ba tareda ta bude idon ba ta juya ta fita a office din...saida ta tsaya ta gama clearing face dinta dukda tasan a banza dan ana ganinta za'aga alamun kuka tattare da ita snn ta wuce nurses station din...tare suka fito sa nurse

Please Login or Register in order to submit comment