You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
wuce"...harara ya sake 6alla mishi shi kuma yasa daria yace"da gaske bazan karaba mana..sorry".
Ranan Friday akayi pasting result dinsu na first semester wurin ya cika fam da jama’a kowa na kokarin duba nashi wanda sukayi passing mata murna while masu resitting suna jimami...Aysha dai na kwance a hostel dan ko fitowa batayi ba sai Billy ce tayi kokarin duba musu da taimakon Sa’eed sbd turereniya akeyi sosai a wurin...bayan ta samu fitowa daga hayaniyar ta samu waje ta zauna tareda dialing number dinta...cikin muryan bacci ta daga da fadin"Hello"..Billy tace"so u are still sleeping"..tace"eh mana ban dade ma da kwanciya ba"...cikin excitement Billy tace"anyi pasting results yanxun nan and gues what?.."a hankali tace mata"what?.."da sauri Billy tace"as usual ke kikayi overall..and this time around bestynki ma yayi abun kirki"...daria ta saki dukda baccin dake idonta tace"kema dai kinsan my besty is always intelligent kece dai kawai baki ganin haka"...ta6e baki Billy tace"oho ku kuka sani..am hanging up now"..da sauri Aysha tace"wait..baki fadamin naki ba ai"...wani murmushin Billy ta saki kafin tace"congratulations to me..inada 4.55"..tun kafin ta rufe baki Aysha ta saki wani ihu tana fadin"are u serious Billy?..gaskia am very happy bari in kira besty this calls for celebration"...murmushi Billy ta kara saki tana jin yanda take farin ciki ko nata result din bataima wnn murnan ba koda yake idan da sabo ai ya kamata abun ya zaman mata jiki dan tun shigowarsu college din bata ta6a scoring below 5 points ba...kafin ma ta jira jin ta bakinta tayi hanging kiran and for sure tasan bestyn nata zata kira kamar yanda ta fada.
Bobby da bai samu shigowa college din da wuri ba sai after jumu’at prayer motanshi na shigowa ya hangi crowd din dake wajen sai ya tuna ashefa Nur ya fada mishi cewa yau zasu kafe result...daga dan gaban inda aka kafe result din ya hango katon banner da suke kafewa duk shekara na best students of the year kowa da grade dinshi da department sai kuma picture dinshi a jiki...driver bai karasa inda ya kamata yayi parking ba yace ya saukeshi nan wurin..ba musu yayi parking daga gefe kafin ma yazo bude mishi kofan ya bude ya fita...inda aka manna babban banner ya nufa...haka nan yaji yanason ganin da akwaita a jiki ko babu...aikam yana karasa yayi ido biyu da pic dinta tana sanye da uniform da glasses dinta a ido...qasan pic din nata ya kalla baisan time daya wara idanu yana sake kallon points din nata ba...gani yake kaman karya ne bazata iya scoring wnn points din on her own ba...hoton su biyu ne kadai a jikin banner daga ita sai Sa’eed da yayi overall a Nursing department...dukda baisan yaron ba amma ya jinjina mashi sosai dan points ba kadan ba shima yakeda...ita kuwa nata har yanxun bai gama yadda ita taciyoshi da kanta ba...bayan ya gama kallon ya shiga takawa a nutse zuwa office dinshi saidai kafin yakai office din kusan mutum uku sukazo suna gaisawa dashi snn suka nufi office din tare...deep down wani irin feeling yakeji...like gaba daya sai baiji dadin ganinta da yayi jikin banner ba...not because yana mata bakin ciki but because yana ganin yin hakan kaman talla ne akeyi da ‘ya’yan mutane tunda yasan yanxu duk wanda ya shigo college din sai ya gani and hakan will make her popular da bai zama lallai parent inta su so haka ba..especially ita da dama ba wani cikakken nutsuwa gareta ba...ya fuskanci kanta na rawa shiyasa ko mahaifinta baya sassauta mata...har ya isa office dinshi bai bar tunanin ba and yanaso yayi ma Nur mgnr kuma yanajin tsoro kar yazo yayi misquoting dinshi amma seriously baiji dadi ba sam...sai yakejin kaman yaje ya yageta daga wurin amma ba hali...hakura yayi da yima Nur mgnr saidai ya kudirce a rai kafin next year zai samu yayi mgn dashi kawai a hakura da banner ma gaba daya...sam baiga amfanin yin hakan ba...dukda ba yanxu aka fara ba amma wnn karon kam abun baiyi mashi dadi ba.
Shirye shirye sukeyi sosai for the upcoming Annual Festival da ake gabatarwa cikin college din every year...shiri ba daga 6angaren students ba ba kuma daga 6angaren social department ba...week guda suke cinyewa suna abu guda and wnn year din ma kaman ko wacce shekara sun gama tsara duk yanda festivities din zasu kasance...ranan farko daya kama Monday zasu gabatar da dramas da wasu daga cikin students din zasu gabatar..da akwai English drama sai Hausa drama...rana na biyu kuma zasuyi cultural activities rana na uku ne ake inviting mawaqa daban daban suzo suyi performing a wurin sai rana na hudu wich is Thursday zasuyi Public Lecture and Fun Walk ma’ana za’ayi picking one among cututtuka da suke damun mutane a wnn lokacin sai daga cikin doctors da ake inviting zuwa wurin suyi fashin baqi akan cutan bayan an gama sai su fita fun walk dasu police bands da masu dj suna tafe suna waqa da rawa zasubi ta cikin gari har zuwa state road snn su dawo college din a qafa...ranan Friday wich is the last day of the festival sukeyin sport activities such football,volley ball,table tennis,snooker,basket ball dama sauran wasanni na maza dana mata.
Ranan Monday wich is the first day if the festival wurin 10 na safe auditorium dinsu na cike da students,doctors da kuma manya manyan baqi from every angle na kano da akayi inviting dinsu...kowa yana zaune a respective wurin da aka tanadar musu...mike na hannun mc yanata welcoming baqi tareda sanarwa cewan a jira wanda zasu gabatar da drama zasu bayyana in few minutes time...daga can waje masu yin draman ne a tsatsaye suna mgn da wani daga cikin organizers na festivals din...ba anko sukayi ba amma kowa cikin yayi kyau in his own way...saida ya gama musu karin bayani kan abunda zasuyi snn yace su shiga audit din...suka jera kansu a layi snn dj yasa musu waqa suka fara shiga wurin...Aysha na tsaye a gaba tana rikeda katon sign board da aka rubuta day 1 English and Hausa Drama...suna shigowa wurin ya kaure da sowa da tafi kowa sun burgeshi...Dr.Bobby dake zaune inda aka tanada domin shi a hankali ya dago idanunshi ya kallesu...as always idanunshi ita suka fara hango mishi...tana sanye cikin riga da straight skirt na atampa red da touches din black leaves a jiki...ta daura dankwalinta irin daurin da ake cewa Zara Buhari ta fito da gashinta ta qasan daurin snn ta kalmasheshi ya tsaya a wuyanta...daga bayan skirt din nata an dan tsagashi kadan ta kasa sbd yayi mata dadin tafia...takalmin kafanta flat ne sosai black sai veil dinta da tasa a kafadanta shima black...sai wrist watch da dankunnenta suma black...batasa sarqa ba dan haka fair wuyanta yana nan sai daukan ido yake...a hankali take takawa tana rikeda sign board a hannunta sai murmushi take dimples dinta na fitowa...wani irin abu yaji ya taso tun daga kwakwalwarshi yazo ya tokare mishi maqogaro shi bai tafi ba kuma shi matsa ya bashi sararin maqogaron ba...tunda yake bai ta6a tsintar kanshi cikin 6acin rai irin wnn ba..har wani zafi yaji yana rufeshi duk kuwa da sanyin ac dake wurin...lokaci daya kanshi yayi wani mugun sarawa kaman zai tarwatse..har yanxun kuma ya kasa dauke idonshi daga gareta har suka karasa suka zauna...lumshe idanunshi yayi yana karanta innalillahi a cikin ranshi wai ko zai samu sassauci...kai tsaye kuma yace ga abunda ke damunshi bazai iya ba dan shi kanshi bazaice ga dalilin wnn sudden change din nashi ba...sam baisan yaya zai misaltashi ba...kokari yayi sosai yayi kokarin danne abunda ke taso mishi ganin har za’a fara taron...yana kallo aka fara kiran sunan wanda zasuyi draman kawai ya runtse ido yana addu’a Allah yasa babu ita a ciki saidai kamar jiran addu’an nashi akeyi yaji mc na kiran "Aisha Ahmad Lamido"...sake runste idanun yayi yanajin wnn kuncin da yaketa kokarin 6oyewa yana sake neman hanyar dazai fito amma bai bashi dama ba dan kara dakewa yayi sosai wnn karon har yana dan muzurai snn ya bude idon...baisan ko shi yake kai idanunshi gareta ko kuma idanun ne ke kai kansu gareta ba dan yanxun ma ita ya sake gani bayan ya bude idon...karasawa sukayi suka zauna inda aka tanada domin yin draman...acting zasuyi itada Sa’eed matsayin mata da miji Billy kuma kishiyarta a cikin sauran kuma akwai yara snn akwai set of another couple da dai sauransu...cikin kwarewa da nutsuwa suka fara gabatar da draman nasu na English knn...wurin sai yayi tsit banda voices dinsu ba abunda akeji...gaba daya sun saki jiki suna acting dinsu sosai dan babu wanda zai gani yayi tunanin ba gaske bane sai wanda ya sani...dama kuma sunyi rehearsal sosai shiyasa basu samu wani problem ba...Bobby kuwa tunda yake bai ta6a sanin da akwai kunchi irin wnn yakeji a yanxu ba...kallon yanda suke acting itada Sa’eed kadai yasa yaji kaman zazzabi na neman kamashi...baisan meyasa yake feeling what he’s feeling ba...baisan why zai damu da rayuwar yarinyar nan ba..."sbd amanarta da mahaifinta ya baka"..cewar wani sashe na zuciyarshi...babu wata wata kuwa yayi na’am da wnn amsa don yasan da gaske kuwa ba abunda ya hadashi da ita bayan wnn...da wnn amsa na zuciyarshi ya dan samu sauki kadan daga cikin abubuwanda ke damunshi...haka yacigaba da daurewa yana kallonsu har wani murmushin yake yakeyi sbd kar mutane su dago halin da yake ciki...draman nasu ya dauki kusan one hour kafin su gama...wanda zasu gabatar da na Hausa akace su zama ready kafin mc yacigaba da surutanshi...sauran kuwa tafi aka shigayi musu sosai dan ba wanda basu qayatar ba a wurin Bobby kam shi kadai yasan halinda yake ciki...bayan lokaci mai tsayi masu draman Hausa suka shigo and to his biggest suprise wnn karon ma da ita a ciki...lokaci guda face dinshi ya sauya yana kokarin mance jarumtar da yace zai nuna...wnn karon kuma matsayin budurwar wani ta fito hakan kuma ya 6ata masa rai fiyeda tunaninshi...haka nan ya sake daurewa ya kalla har suka gama amma fa kafin a gama ya saki tsaki yafi cikin carbi...6acin ranshi kuwa ya ninka na dazu ninki ba ninki...gaba daya yaji zaman wurin ya gallabeshi burinshi kawai a tashi ya samu yarinyar can ya zabga mata rashin mutunchi...kwata kwata baisan dalilinda yasa bayason ganinta cikin irin wadan nan abubuwan ba...bayan sun gama masu jawabi duk suka tayi sukayi kayansu...wanda zasu bada kyauta ma duk suka bayar and Lamido na daya daga cikin wanda suka samu kyautar 50k da wani attajirin mutumi ya bayar...ran Bobby idan sun kai dubu duk a 6ace suke...ji yake inama yanada hali ya kar6e kudin daga hannunta gaba daya sai yaga ta gidan uban da zatayi amfani dashi dan yaga sai wani fara’a take tana jujjuya ido ita bata yadda ba celebrity...InShot har aka tashi daga wajen Bobby baisan ina kanshi yakeba...a zafafe ya koma office dinshi ya dauki waya da niyyan kiran secretary dinshi tasa a nemo mashi ita nan take kuma wani tunani yazo masa..."to idan na kirta ince mata me?.."ya fada a fili kaman he’s talking to someone...nan take kuma ya shiga girgiza kai yana fadin"no yanxu idan na fadi wani mgn tana iya misquoting dina ma tunda ba hankali gareta ba"...ya sake fadama kanshi...can kuma yace"amma ai sbd babanta zanyi hakan kou?.."yayi shiru kaman yana sauraran amsan da zuciyarshi zai bashi kafin yace"No I won’t talk to her...wai ma ina ruwana da ita taje taita haukanta mana is not as if i care"...ya fada yana daddaure face dinshi kaman tana zaune nan kusa dashi...da wnn shawara yayi amfani don bai kiratan ba a cewarshi wai baison raini...haka yayi dakon bakin cikin daya kwasa ya kaishi gida su Mummy sukaita aikin fama.😹
The next day kasa fitama yayi da wuri sbd tunanin abunda zuwan nashi zai haifar...yadai san a yanda take da shegen rawar kai yanda tayi performing a komai na jiya yau din ma zaiyi wahala idan batayi performing ba..shi kuma baisan meyasa yakejin abunda yakeji ba and Allah ya sani bazai iya kiranta ya hanata ba sbd kar tayi tunanin wani abun daban...da yanada ikon hana kanshi jin abunda yakeji da ya aikata hakan wlh ko don ya samawa kanshi salama amma bayada damar hakan...wnn dalilin yasa bai samu fitowa ba har saida yaga Nur ya fara kiranshi a waya and yasannshi da shegen naci haka zaiyita jera mishi kira idan har ba fitan yayi ba.
Wani daki ne kusada auditorium dinsu inda daya wanda zasuyi performing suke ciki kowa yana karasa shiryawa...cultural dance suka shirya na Hausa,Fulani,igbo da kuma yoruba...and kowa daga cikinsu yana sanye cikin traditional attire na tribe da zaiyi representing...Lamido sarkin rawa zatay participating kusan gaba daya sbd ita koya musu rawar...da farko cewa tayi only Fulani da Yoruba zatayi sai hod na social department dinsu yace tayi participating gaba daya...Hausa Dance shine na farko dan haka koda mc ya kira iya wanda zasuyi hausa dance din ne suka fita daga dakin...as usual itace a gaba tana rikeda sign board kaman najiya saidai shi an rubuta day 2 cultural activities...wata kuma daga cikinsu ta rike wani da aka rubuta Hausa Dancers a jiki...waqa aka sakar musu ta hausa mai dadi yayinda suke shigowa cikin wurin...gaba dayansu suna sanye cikin normal dogon riga na atamparsu iri daya kowacce ta daura dankwalinta babu mai mayafai cikinsu...bayan sun karasa dance floor sun tsaya dj ya samo waqar hausa ta gargajiya yayi playing snn suka fara dancing...yau ma Bobby yana zaune mazauninshi na jiya and gaba daya tunda ya dora idonshi a kanta ya samu gagarumar matsala don komai nashi tsayawa yayi cak banda zafi ba abunda yakeji har cikin heart dinshi...lumshe idanunshi yayi yana salati dan abunda yake jin yaji jiya was nothing compared to what he is feeling right now...ji yake kaman yaje ya dauketa ya fita da ita daga wirin...haka nan yakejin ciwon kallon da mutanen wurin zasuyi mata tana rawa kamar batasan ciwon kanta ba.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
22
Ranshi bai sake 6aci ba saida yaji yanda gaba daya wurin ya kaure da tafi da sowa ana hailing dinsu..nan take yaji wani abu yazo ya tokare masa wuya...abun bai tsaya haka ba har liki mutanen da akayi inviting suka fara tasowa suna musu...bayan sun gama aka kara tafa musu sosai snn suka fita mc yacigaba da zance kafin next dancers su fito...dakin da suka shirya suka koma nan kuma suka fara arranging next dancers da zasu fita wato Yoruba Dancers...Lamido ce kadai tayi changing dress dinta zuwa na yoruba snn ta shiga cikin sauran suka koma ciki...suma dai da tafi da sowa akayi welcoming dinsu...Dr.Bobby yana zaune sam baiyi mamakin ganinta ba dan yasan dama hakan zai faru saidai bai saniba ko zai iya cigaba da jure abunda yakeji har su gama...yau dai ya rantse kome zai faru sai yayi mata mgn saidai idan taga dama misquoting din nashi he no longer cares..kawai haushi yakeji that gaba daya festival din ma ya fita daga kanshi kuma ya rasa wnn masifa da akan yarinya guda daya yana neman rasa sukuni da nutsuwarshi...suna isa dance floor aka sa musu waqan yoruba suka fara dancing...tafi da sowa kam sun shashi kaman ba gobe ga kuma ruwan kudi da suka samu daga mazauna wajen...lokacin da suka fito zasuyi na igbo Bobby kasa dauke ido yayi a kanta sai yaga kaman duk kayan da ta saka ba wanda yayi mata kyau kamansu...baisan ko don shi ya kasance igbo din ba amma kayan sun amsheta kaman itama igbo din ce...sai yaga kaman idon kowa na wurin a kanta yake sbd kyawunda tayi...bata sake bashi mamaki ba saida suka fara rawar...sunyi kokari matuka kaman dama inyamuran ne su...har yanxu kuma wnn zafin da yakeji yana nan wanda shine yasa gaba daya baya enjoying zaman wurin...Fulani dance shine na karshe and lokacinda suka shigo Bobby baki da hanci ya saki yana kallonta...tunda yake bai ta6a tsaywa ya kalleta irin na yau ba...tayi mishi kyau fiyeda yanda bakinshi zai iya fada..shi baima ta6a ganin kyanta kaman na yau ba tunda ya santa...haka akasa musu waqar fulani sukayi rawa sosai yanda ya kamata...and again an watsa musu naira snn wani babban mutumi dake wurin yayi musu kyautar kudi masu yawa...wani kuma daga cikin baqin shima yace ya bawa Aysha kyautan sabuwan waya Smsung Galaxy...farin ciki sosai takeyi har hakan ya kasa 6oyuwa dan sai murmushi takeyi Bobby kuma kamar bala’i idanunshi suna kanta yana ganin yanda dimples dinta ke fitowa as a result of smile da take...kasa cigaba da zaman wurin yayi kawai ya mike kaman wanda yakeda mutanen 6oye ya fita daga hall din kusan gaba daya mutane suka bishi da kallon mamaki...Nur ne ya mike da sauri yabishi a baya yana dab da shiga office dinshi ya iskeshi yace"Bob are u alright?..lafia naga ka tashi ana taro ko wani abun ya faru ne?.."juyawa yayi a fusace yana kallon Nur din snn ya nunashi yatsa yace"Fuck you"..daga hakaya bude office dinshi ya shiga ciki tareda bugo kofar da karfi...Nur mutuwan tsaye yayi a wurin yana kallonshi da mamaki...to meya sameshi haka?..kodai wani saga ciki guests din yayi mishi abu?..duk kokarinshi na yaga yayi pointing finger kan dalilin tasowarshi daga wurin ya kasa...baiyi yunkurin binshi cikin office dinba kawai ya juya tareda komawa can wurin still yana tunanin abunda akai mishi.
Bobby na shiga office din ya zauna tareda dora kanshi kam table yana sauke numfashi da sauri kaman wanda yayi race...ko kusa baya son wnn sabon al’amari dake kokarin kunnowa cikin rayuwarshi..bayaso sam...baisan kan wane dalili zai dinga jin haka akan yarinyar da bai hada komai da itaba...shi tunda yake ma bai ta6a samun kanshi cikin yanayi irin wnn ba sai yanxu...gaba daya yarinyar nema take ta zame mishi tauraruwa mai wutsiya...ciwo yakeji sosai na raye rayen da taje tayi a bainan nasi..kuma sbd rashin sanin darajar kai ko dan mayafi bata yafa ba ballantana ayi mgnr hijab..gaba daya ya kasa gane wace irin yarinyace ita?..duk sai yaji kaman bai kyautawa babanta daya damka amanarta a hannunshi ba...kaman wanda akama allura ya mike da sauri ya fita daga office din...can inda audit din yake ya nufa yana shiga premises din wurin yaga Billy ta fito daga ciki tana waya tana ganinshi tayi saurin kashe wayan da takeyi tana kallonshi a tsorace...voice dinshi a cunkushe yace mata"where is ur friend?.."da sauri ta nuna auditorium din tana cewa"tana..ciki"..."go and call her"..ya fada hands dinshi zube cikin aljihu...ba musu Billy ta juya da sauri ta koma ciki...can tsakiyar dance floor ta hangota bayan sun gama performance dinsu aka sakar musu kida suka fara rawa gaba dayansu...haka Billy ta kutsa ta cikin mutane zuwa inda take kawai sai ji tayi ta kamo hannunta ta shiga janta...Lamido ta kwace hannunta tana turo baki tace"Billy rawa nakeyi dan Allah"...harara me kyau Billy ta watsa mata before tace"to kicigaba da rawa ai ga Proprietor can yana nemanki"..bata rufe baki ba Aysha ta zaro idanu tana fadin"dan girman Allah da gaske?.."kama hannunta Billy tayi suka fita daga wurin snn tace"Allah da gaske nake..yana can a waje fuskan nan kaman bai ta6a daria ba dan wlh har tsorata nayi dana kalleshi"...nan take hankalin Aysha ya fara tashi tace"na shiga uku meyasa yake nemana kuma?.."Billy tace"indai kinsan bakiyi laifin komai ba ki kwantar da hankalinki..kiyi addu’a kije ki sameshi in Allah ya yadda ba abunda zai miki"...girgiza kai kawai Aysha keyi tace"zo muje ki rakani dan Allah"...Billy ta kwalo idanu waje tana fadin"Ni?...rufamin asiri Lamido in mutu maza su kaini ba mata ba...haka nan inje yayita zazzaro idanun nan nashi yasani sakin fitsari a wando"...dukda tashin hankalin da take ciki saida mgnr Billy ya sata daria...sai kuma ta marairaice fuskanta tace"na shiga uku tsoron zuwa nakeyi wlh...nasan yanxu abu karami yake jira ya hadani da daddy"...Billy tace"ba fada miki inshaAllah ba komai kedai kawai kije kiji mezai fada idan ba so kike ki kara wani laifin ba"...jiki a sanyaye ta gyara mayafinta snn ta fita daga wajen...bata sameshi nan waje ba dan haka ta wuce office dinshi...tana shiga ya dago fuskanshi da yayi murtuk kaman na marasu imani kawai ya mika mata hannunshi murya a cushe yace"bani wayarki"...mika masa wayar tayi da sauri tareda sunkuyar da kanta kasa tana wasa da fingers dinta...shi kuma yana amsan wayan yasa digits dinshi snn yayi dialing...wayanshi dake ajiye kan table dinshi yayi ringing alaman kiran ya shigo snn yayi quitting call din tareda ajiye wayan a kusada nashi...Aysha dai har yanxun kanta na kasa tana kwararo mishi addu’a cikin zuciyarta...tsoronta Allah tsoronta kada ace wani laifin tayi ya kira daddy ya fada masa...shi kuwa kallonta yakeyi yanajin tamkar ya kwada mata mari don haushi..dubi dai yanda ta wani nustu a gabanshi kaman mutumiyar kirki amma dazu taje ta gama bayyanar da jikinta wa mutane suka kalla...ko rantsuwa yayi yasan da kyar babu wanda bata burgeba a cikin wadanda suke wajen...kawai ciwo yakeji that a gaban idonshi abun ya faru and he couldn’t do a thing...cikin muryan daya kusa sanyata fitsari yace"wato ke bakida hankali kou?..sbd bakisan ciwon kanki ba kikaje kina rawa gaban mutane kina musu tallan jikinki kou?.."dan dagowa tayi ta kalleshi kafin ta mayar da kan nata da sauri dan tsoro idanun ma suka bata...saida ta dan marairaice snn tace"tallan jikina kumah?.."a fusace yace"if u dare say another word a wurin saina kwada maki mari...tambayana ma kikeyi sbd bakida kunya kou?.."shiru tayi tana turo baki...yace"well let me call ur Father and tell him all you’ve been doing"..yana karasa mgnr ya dauki phone dinshi dake nan kan table ai batasan time din da ta kama hannun nashi ta rike gam ba sbd tsoro...cikeda tashin hankali tace"Sir dan Muhammadu rasulillahi kar ka kirashi..i beg of u please"..ta karasa mgnr hawaye ba zubowa kan cheeks dinta...Bobby dake kallon yanda ta rike mishi hannun yace"how dare you?.."sakin hannun nashi tayi da sauri tana cewa"am sorry...Sir dan girman Allah ka rufamin asiri karka fada wlh fada zaiyimin"...sake daukan wayan yayi yana searching contact din daddy yace"da kina tsoron fadan ai bazaki aikata abunda ba daidai ba"...wnn karon hannayenta ta hade waje daya in a pleading tone tace"Sir na rantse da Allah ban karawa kayi hakuri plss"...ajiye wayan yayi yana kallonta..dama baida intension din kira yayi haka ne kawai dan ya tsoratata tunda already yasan yanda take tsoron mahaifinta...idonshi a kanta yace"fadamin meyasa bakijin magana?.."tana cigaba da hawaye tace"am sorry"...yace"ba wnn na tambayeki ba..i said meyasa bakyajin mgn?..why kikeda fitina?.."shiru tayi tana goge hawayenta sai can kuma tace"nima ban saniba"...tsaki ya saki tareda daukan wayanta yana mika mata yace"leave my office immediately..and if u like gobema kizo kiyi abunda kikayi yau kiga idan ban sanar dashi ba"..kar6an wayan tayi tana turo baki ta juya ta ta fita daga office din..tana ganinta a waje ta sauke wani ajiyar zuciya a fili ta furta"kuma Allah ya isana wlh..inyamurin banza"...shi kuwa sai daga baya duk haushin kanshi yabi ya kamashi...wai ma ina ruwanshi da rayuwarta ne at the first place...mamakin kanshi yakeyi shi that ya tsani Fulani especially na Gombe amma wai shine har yake kokarin protecting yarinyar da yasan asalin ‘yar Gombe ce?..baisan ko don sbd mutuncin mahaifinta da yake gani bane...abu guda daya sani shine dukda kasancewar babanta bafulatani kuma na Gombe yana matukar ganin kima da darajarshi and shine mutum na farko daya faraji ya kwanta mishi a rai bayan sanin cewa shi din bafulatanin Gombe ne...kilan sbd kyawawan maganganun da yayi kan Dad dinshi ne amma maganan gaskia mutumin yayi mishi dari bisa dari...itama kuma ‘yar tashi yasan sbd mahaifinta yakejin abunda yakeji and nothing more.
The next day which is Wednesday ranan ne ake inviting mawaqa from different states suzo suyi performing a makarantan...Bobby na kwance tun safe a daki ko parlor ya kasa fitowa...kawai jin jikinshi yakeyi wani iri that har yake tunanin kilan hakura zaiyi da shiga college din nan kawai...dukda yayi mata mgn jiya and yanada tabbacin ta tsorata sai yakejin kaman yayi zamanshi a gida or better still ya tafi Hospital dinshi kawai ba sai yaje ba balle yaga abunda zai 6ata mishi rai...haka yayita kwance a daki bai fito ba saida Mummy ta aiko a kirashi...yana saukowa daga gado ya fada
Book Chapters
Chapter 17
Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59