gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading Dr.bob Complete Hausa Novel by by Aysha Rano Chapter 26 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

plss"...narkewa tayi tana kallonta kafin tayi mgn aunty sumy ta sake fadin"please!.."haka nan ta bita suka cikin gidan ba don tanaso ba...mai gadi taba key ya shigo mata da motar snn suka wuce...matar ce tayi mata kwarjini wlh amma ita sam bata son shiga yazo yana wulakantata...suna shiga compound ta ware idonta tana kallon lafcecen compound din dake zube da uban motoci kaman na siyarwa..cikin ranta tace"babban burin inyamuri a dunia kenan..a danqara gida snn a hau motoci"..ganin bata daga kafa aunty sumy ta kama hannunta suka nufi entrance...basu samu kowa central parlor ba dan haka direct ta nufi parlon Mummy da ita...Mummy na zaune da Ilham akan cinyarta shi kuma yana rikeda hannun ilham din yanayi mata alluran jijiya..yarinyar tayi luf jikin Mummy sai sauke numfashi take...saida suka isa ciki aunty sumy ta saki hannunta tana doka wani uban murmushi tace"Mummy ga bakuwa na kawo maki"...dagowa Mummy tayi tana kallon yarinyar da kanta ke kasa kafin tace"to bismillah zauna kinji bakuwa"..karasawa tayi ta zauna a hankali har yanxun kanta yana kasa...Bobby da sai yanxun ya gama mata alluran yana dago kanshi yayi ido biyu da ita tana zaune kusada aunty sumy sai wani sussunne kai take...cikeda mamaki sosai yake kallonta yace"ke bakida hankali ne?..waya baki izinin shigowa gidan nan?.."juyawa Mummy tayi tana dubanshi tace"ka santa ne?.."dauke kai yayi yana huci ya kasa cewa komai...tambayoyin nan ne bai shirya amsawa ba shiyasa yace tayi zamanta cikin mota amma sbd tsabar rashin ji irin nata saida ta fito...yanxu shknn yasan ya shiga uku da tambayoyi a wurin su Mummy...ganin bazaice komai ba aunty sumy tace"ganinta nayi fa a cikin motarshi shine na tambayeta tace tare dashi suke amma yace ta zauna nan cikin mota karta fito"..juyawa Mummy ta sakeyi ta kalleshi sai taga ya sake hade rai yana muzurai sai ta maida dubanta ga Aysha da har yanxun kanta ke a kasa lokaci daya ta saki wani murmushi dan tasan zaiyi wuya idan ba itace Lamido ba dan haka tace"yammata meye sunanki?.."a hankali tace"Aysha"..Mummy ta shiga gyada kai tace"MashaAllah Aysha me babban suna ce ashe?.."daga kai kawai Lamido tayi tanajin kamar ta saki fitsari a wando sbd yanda takejin idanun Bobby nata kaiwa da kawowa a kanta..ko baa fada ba tasan kallonta yake...Miemie ce ta shigo parlon rikeda tea data hadoma Ilham..tana karasowa ta mikawa Mummy snn ta zauna tana kallon Aysha dake zaune tace"Mummy bakuwa mukayi?.."Mummy da har yanxu bata bar smiling ba tace"wlh bakuwa mukayi Miemie”..Miemie ta matsa kusada ita tace"sannu da zuwa ina yini?.."dan dagowa Aysha tayi ta kalleta kafin tace"lafia lau"..wara ido Miemie tayi da taga face dinta tace"laa Mummy ai na ta6a ganinta a FCNM wall..."bata samu karasawa ba sbd wani kallo da Bobby ya watsa mata ba shiri taja bakinta yai tsit..aunty sumy da tun daxu take kallonshi ganin yanda duk yabi ya takura kanshi kawai ta saki murmushi..ita bata ta6a ganin mai hali irin na Bobby ba wlh..kiri kiri ga abu kana sonshi amma wai kake kaiwa kasuwa?...mikewa Mummy tayi ta ba aunty sumy tea din Ilham tace"ki bata tasha"..snn ta karasa inda Malama A’ee take zaune ta kama hannunta ta mike tsaye snn ta jata zuwa dakinta tace"tashi muje mu gaisa ‘yata"...daga haka suka shige bedroom din Mummy..Bobby yabisu da kallo kaman idanunshi zasu koma jikin kofar dakin...hankalinshi yaji ya tashi kardai Mummy taje ta fadama yarinyar nan abunda zaisa ta rainashi fa..gabanshi har wani faduwa yakeyi wlh...kaman wanda aka tsikara yabi bayansu zuwa dakin da sauri kamar zai tashi sama...





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
31
Yana shiga ya marairaicewa Mummy yace"Mummy dan girman Allah mu tafi..bama ta da lafia shine na kaita asibiti"...murmushi Mummy tayi kafin tace"to ka jiramu a waje yanxun nan zata fito"..da sauri ya canxa yare yace"Mummy me zaki fada mata?.."da yaren itama tace"akwai abunda kake 6oyewa wanda bakaso ta sani ne?.."girgiza kai yayi da sauri duk yabi uzzurawa kanshi babu gaira babu dalili...kofa Mummy ta nuna mishi alaman ya fita haka ya juya ya bar dakin yana sake sake...bayan fitarshi Mummy ta dawo da dubanta ga Aysha tace"zauna mana Aysha"..maimakon ta zauna saita risina har kasa tana kallon kasan tace"Ina yini"..Mummy ta amsa da"lafia lau..ya karatu?.."tace"Alhamdulillah"..Mummy tace"to dawo nan ki zauna tunda mun gama gaisawa"..ba musu ta mike ta zauna inda ta nuna mata...kallonta kawai Mummy keyi taji ta shiga ranta sosai...irin wnn kyau da take dashi ai ba Bobby ba kowane namiji ma yana iya samun matsala idan aka jarabceshi da qaunarta...tana cigaba da dubanta tace"da gaske bakida lafia?.."kai kawai ta iya dagawa...Mummy tace"to Allah ya baki lafia..yanxu bari a kawo maki abinci kici"..da sauri tace"wlh mama na koshi banajin yunwa"...Mummy ba girgiza kai tace"aah dole kici wani abu"..daga haka ta kwaloma Miemie kira...tana shiga Mummy tace"jeki kawo mata abinci"...kafin ta fita Aysha tace"wlh ban dade da cin abinci ba banajin yunwa"..Mummy tace"to shknn dukda haka dai ko tafiya sai kinyi dashi...Miemie ki samu abu ki zubo mata pepper chicken sai ki hada mata da lemo"..ba musu Miemie ta fita don yin yanda aka sata...suna nan zaune ta dawo da wani bag mai kyau datasa pepper chicken din a ciki...Mummy tace"to ki rike mata saiki rakata waje dashi"..a hankali tace"toh.."snn ta juya ta fita...mikewa Mummy tayi zuwa wadrobe dinta ta dauko wasu turaruka masu kyau guda biyu ta zuba mata su cikin dan karamin jaka mai kyau snn ta bude drawernta ta dauko two sets na sarkoki suma masu azabar kyau duk ta zubasu cikin jakan...hajia indo dai tana zaune kai a kasa kamar munafuka..hannunta Mummy ta kama suka fita daga dakin...Bobby daketa safa da marwa ya juya yana kallonsu kamar idonshi zasu fadi kasa..saida daria ya subucewa Mummy sbd ganin yanda duk yabi ya addabi kanshi ba gaira ba dalili..shi kuma ya wani kwabe fuska da igbo yace"Mummy me kike ce mata dan Allah?.."bayan ta staida dariyarta tace"gata nan ka maidata kuma wlh ban yadda kayi mata fada ba Bobby..idan kayi kuma zai dawo kunnena"..daure fuska kawai yayi baice komai ba...aunty sumy ma ta fito daga dakinta rikeda wani dan box mai kyau tana karasowa ta mikama Aysha tana murmushi tace"to ga wnn Aysha..i hope zaki sake kawo mana ziyara?.."murmushi kawai tayi bata iya amsawa ba duk sun sata jin wani iri wlh..sunada kirki sosai unlike Proprietor da sukayi hannun riga da kirki...ta amsa abun tayi godia..Mummy tace"ai zai sake kawota mu gaisa"..aunty sumy tace"kwarai kuwa..idan ma bai kawota Mummy da kaina zanje har hostel dinsu in dauko mana ita"..shidai yana fsaye fuskan nan a tamke baice musu kala ba...after long surutunsu finally ya samu aka bashi ita suka fita..Miemie ta rakata har mota da kayanta ta zuba mata su back seat snn ta zaga inda take da nufin tayi mata sallama Bobby dake cika yana batsewa ya wani 6alla mata harara tareda fadin"bar nan"..ba shiri ta koma ciki tana turo baki...tada motar yayi da wani irin gudu suka bar layin nasu..Ita dai a tsorace take sai rarraba idanu take...suna hanya wayanta ya fara ringing ganin wanda ke kira sai tayi silencing wayar taki dauka sbd gudun masifanshi...sake kira akayi ta kuma sawa a silent shi kuma ganin batada niyyar dagawa yakai dubanshi kan wayar dake cinyanta sai yaga baby boo kan screen aikuwa ya sake dinke fuskanshi tsaf yana sake figan motan a guje kmr zai tashi sama...gani take kaman tsoron dunian nan a kanta ya sauka wnn uban gudun da yake idan yaje ya watsar dasu fa?..bata dai ce masa komai ba har suka isa gate din hostel...ya cire mata lock ba tarefa ya kalleta ba yace"fita"..da sauri ta kama kofar zata bude sai kuma taji yace"bana hanaki kiramin wani besty idan muna mgn ba?..ke wato bakyajin mgn koh?.."da sauri tace"kayi hakuri"..yace"sbd kinga banaso shiyasa kike fada wato koma me zanyi inyi koh?.."ta dan lankwasa wuya tace"sir nace fa kayi hakuri"...dauke kanshi yayi daga gareta yace"fitamin daga mota"..ta sake langabewa tana kwabe fuskanta tace"sir i said am sorry mana..kayi hakuri bazan kara ba"...juyo da kanshi yayi yana kallonta yace"idan kika kara inyi maki me?.."hannu takai tana shafa cheeks dinta kafin a hankali tace"ka mareni"..murmushi kawai ya saki tareda jinginar da kanshi jikin kujera..dama yasan fushin ma ba wani iyawa zaiyi da ita ba..itama murmushin ta saki tace"sir kacigaba da smiling dan Allah..yana maka kyau"..bude idonshi yayi ya zubasu a kanta..wasu sabbin al’amura yakeji suna zagayawa cikin jini da tsokarshi...mikewa yayi daga inda ya jingina still yana dubanta ina serious note yace"da gaske banason jin wani besty ko waye a bakinki..banaso idan kuma kika sake kiramin shi muna mgn marinki zanyi kaman yanda kika fada"..murmushi take tace"bazan ma kara ba inshaAllah"..yace"shknn u can go..and make sure kinsha drugs dinshi akan lokaci kuma banda skipping idan ba haka ba kuma alluran da bakiso shi za’a kuma yi maki"...bude motar tayi ta fita still tana murmushi tace"aah banason allura zansha maganin..saida safe"..kanshi kawai ya iya daga mata snn ta juya ta tafi bayan ta kwashi kayanta dake baya...saida yaga shiganta ciki snn yaja motarshi ya kara gaba.

Tun daga wnn ranan suka sake dinkewa abunsu...tanajin magananshi sosai and hakan ba karamin farantawa Bobby yake ba..zuwa yanxu ya gama admitting ya kamu da soyayya..soyayya kuma na bafulatana data fito daga jihar Gombe..what a miracle..tunda yake bai ta6a tunanin zaiso wata mace ba ballantana ‘yar Gombe amma ita sai yaga kaman turota akayi dan tazo ta wargaza duk wani tanadi da alqawura da yayima kanshi...shida yake shiga college only Thursdays da Fridays amma yanxu kusan kullum sai ya shiga sbd kawai ya samu ya ganta domin ganin nata shine kadai samun nustuwarshi...yanayi mata sonda shi kanshi bai tunanin yana yiwa kanshi amma har yanxu ya kasa nuna mata dukda yasan wani lokacin actions dinshi suna nunawa sbd kasa controlling kanshi da yake amma ita kota fahimta bata ta6a nuna mishi ba...abu biyu dake damunshi sune na farko amanarta da mahaifinta ya bashi yana gudun kada mgnr sonda yake mata ya fita shi kuma mahaifinta yaga kamar bai rike mashi amana ba tunda har shi da kanshi zaice yana sonta..sai na biyun kuma shine Gombe..bayan kasancewarta ‘yar Gombe muma tazo a bafulatana..har yanxu bai mance yanda ‘yan uwan dad dinsu fulani sukayi treating Mummy ba..shima yana tsoron kada yaje neman aurenta ace dan inyamura ne shi baza’a bashi ba..ga kuma su kansu ‘yan uwan daddyn da matukar zaiyi aure dole saiya nemi inda suke sbd su shige mishi gaba kan mgnr saidai sam baiji zai iya zuwa ya samesu ba..har yanxu yana nan akan bakanshi na babushi babusu amma kuma tayaya zai samu auren Lamido ba tareda sa hannunsu ba?..gaba daya ya zama wani iri yanxu ko abincin kirki baici..aiyukan nashi ka neman tsaywa suke cak sbd damuwar da yake ciki..har dan ramewa yayi sbd tunani..Mummy tayi tayi dashi ya sanar mata abunda ke damunshi amma kullum mgnrshi daya shine babu komai...ganin yana neman rasa nutsuwarshi yau dai ya yanke shawaran zaije ya samu Nur suyi mgn ko yanada solution da zai bashi...gashi itama yarinyar wahalar dashi takeyi these days baisan laifin da yayi ba duk ya kirata a waya bata dauka...hankalinshi ba karamin tashi yayi ba yau kusan 5 days knn baiji muryanta ba kuma bai ganta ba dan haka yake jin kanshi kaman mara lafia..baisan meyasa take mishi irin wnn ba..haka nan babu laifin zaune babu na tsaye saita dauke mishi wuta sai yayita binta yana lallashi snn zai samu kanta amma this time around yace bazai ske nemanta ba inyaso sonta yayi ajalinshi shima sai ya samu ya huta.

Yana shigowa College zuwa office din Nur da yace mashi yana jiranshi a ciki...da sallama ya shiga yana takawa da kyar sbd matsaloli da suka taru suka cika mashi brain...Nur na ganinshi ya mike ya koma kan sofa shima karasawa yayi ya zauna nan kusa dashi tareda jingina da jikin kujeran yana lumshe ido...Nur yace"kace zamuyi mgn i hope dai lafia?.."girgiza kai Bobby ya shigayi tareda bude idanunshi yace"ba lafia ba Nur..ina cikin damuwa"..gyara zama Nur yayi yace"to inajinka"..ajiyar zuciya Bobby ya sauke yana shakar iska da kyar yace"it’s about Lamido..i think..i think i’ve fallen for her"...dukda Nur ya dade da sanin yana sonta yayi mamaki sosai jin a yanayin daya fada mashi...kamo hannunshi Bobby yayi yana kallonshi da idanunshi da suka sauya kala muryanshi cikin raunin da Nur zai iya rantswa bai ta6ajinshi a ciki ba yace"i am in a serious mess Nur..na rasa nustuwata gaba daya..komai bayamun dadi..komai banajin dadinshi abu daya da yake keeping dina company shine tunaninta..zuciyata ta cuceni duk iya kokarina na ganin na kaucewa abunda nakeji abun yafi karfina Nur..bansan meya kamata inyi ba nasan yarinyar nan bazata ta6a sona ba"..yana rufe baki Nur da yaji asalin tausayinshi na ratsashi ya dafa shoulder dinshi yace"Man take it easy plss..idan kana wnn damuwan kana iya samun problem ka sani..nayi maka alqawarin i’ll help you in anyway possible dan inga ka samu soyayyarta..wnn matsalan nake guje maka shiyasa tun farko naso ayima tufkar hanci baka bani dama ba"..sake damke hannunshi yayi yace"yanxu na baka do your best plss..ka taimakeni before i loose my sanity..inajin zafi sosai duk lokacinda na ganta da wani..yanxu haka da nake mka mgn ko wayana bata dauka kuma bansan laifinda nayi mata..nasan kilan Allah yanaso yayi punishing dina ne kan abubuwanda nayi mata a baya amma wlh bada son raina bane..bansan meyasa ina ganinta raina yake 6aci har yasa nayi mata abubuwanda nayi ba"..rungumeshi Nur yayi cikeda tausayinshi sosai yace"it was all the love Bobby ganewa ne bakayi ba..tun daga ranan da tacemin kace baza tayi presentation ba nasan da akwai wani abu a ranka gameda ita..Lamido is a good girl..tanada hankali sosai and am sure ko bata soka yanxu ba watarana zata soka"...dagowa yayi daga jikinshi yana kallonshi with a wide smile jin abunda ya fada yace"nagode sosai Nur..thank u..kasan a da nayi tunanin sonta kake sai kuma daga baya naga ba haka bane"...Nur yace"well a gaskia bazan boye maka ba i once had a crush on her amma tunda ja fahimci kana sonta saina hakura sbd nasan sonda kake mata yafi wanda zan mata..kuma dakai tafi dacewa bada ni ba and inshaAllah i will do my possible best inga na hada wnn soyayyan..ba karamin matching couple zaayi ba kai da Lamido"...murmushi sosai Bobby yake wanda ya manta when last yajishi so lively haka...maganganun da Nur ya fada sai yajisu tamkar diamond da gold sbd tsananin dadinsu da yaji...cikin murmushin da yaki bajewa fuskanshi yace"thank u so much friend..u are really a friend indeed"...shafa kai Nur ya fara yana wani murmushin shakiyanci yace"gaskia ya kamata ayi saluting Lamido data canxaka haka?..yau Dr Bobby ne da godia haka ba kakkautawa?.."murmushin shima ya kara saki shi kanshi ya dade yana mamakin kanshi..ya dade yana mamakin yanda ya canxa ta 6angarori da dama duk kuma a dalilin Lamido...Nur dake kallon yanda yake blushing yace"amma wait..laifin me kayi ta dena daukan wayanka?.."da sauri Bobby yace"nima i dont know..haka nan ta daukemin wuta rabon dana samu peaceful sleep tun ranar dana ganta last..ina cikin damuwa sosai Nur ka taimakamin dan Allah..I really want to see her..na dade ban ganta ba"...wani murmushin Nur ya saki kafin yace"karka damu yanxun kuwa zaka ganta..let me call her"..yana fadan haka ya dauki wayanshi dake kan table ajiye snn ya nemo numberta yayi dialing..da sauri Bobby ya matso kusa dashi yana kallon wayan kamar zai ganta ne a ciki..Nur yasa a speaker nan kuma sukaji kiran ya shiga..tana dauka tace"Sir ina yini"..Bobby ya wani lumshe ido yanajin yanda muryan nata ke zagayawa cikin dukkanin systems dinshi..he missed her like crazy..jin muryanta kuma sai ya sake kwadaita mishi son ganinta..yasan yau idan bai ganta ba matsala zai samu gaba daya..he don’t think zai iya daukan rashin ganin nata anymore..he just can’t..he need to see her...idon Nur na kallonshi yana kallon yanda ya fada duniar shauki sbd jin muryanta yace"hajia Lamido manyan mata..ya studies?.."tace"Alhamdulillah sir dama inaso inzo wurinka akan mgnr malam Mukhtar"..yace"then kizo office yanxu dama nima nemanki nake"..tace"ohk gani nan"..daga haka Nur ya kashe wayar yana duban Bobby yace"she’s coming"..kai kawai Bobby ya iya daga mashi yana tunanin yanda zasu kwashe da ita...mikewa Nur yayi ya koma seat dinshi yana zama sai gata ta shigo office din sanyeda uniform dinta as usual da glasses dinta a ido...tana gama kulle kofa ta juyo zata nufi inda yake zaune kawai idanunta duka hango mata shi a zaune ya waniyi crossing hands dinshi yana kallonta kaman wani soko...dan daure fuskanta tayi ta dauke kai snn ta karasa gaban table din Nur tace"Sir i think zanje sai in dawo some other time"..da sauri Nur yace"amma why?.."bata amsa mashi ba ta juya da sauri zata fita Bobby ya mike da saurin shima yasha gabanta...ta dago tana kallonshi fuskan nan a kwabe tace"nifa wucewa zanyi"..mai mata bazan sai aikin kallonta da yake kaman ba gobe...matsawa tayi zatabi gefenshi ta wuce nan ma ya sake tare mata hanya kawai saita dago tana kallonshi kaman zatasa kuka...Nur da yaga wasan nasu ya fara daukan zafi sai ya mike daga inda yake ya ra6a ta gefen Bobby zai fita daga office din ya dan rankwafa saitin kunnenshi yace"Man karka raga mata wlh..make her fall for u"..yana gama fadan haka ya fice daga office din Lamido tabishi da kallo kamar zatasa kuka...sake matsawa tayi zata wuce shima ya sake tare mata hanyar...tayi kasa da kanta kawai tana turo baki kawai sai jin mutum tayi dab da ita dan har numfashinshi a jikinta ke sauka..ta matsa baya tana sake turo baki shima ya sake matsawa inda ta matsa din..ta sake taking two step backward shima yayi haka kawai saita shiga yarfa hannunta tace"sir ni me nayi?.."baice mata komai ba sai binta da yacigaba dayi har ta fada kan sofa..maimakon ya zauna kan sofa sai ya janyo table dake wurin ya zauna a kai yanda zaina kallonta da kyau..muryanshi kasa kasa yace"why are u ignoring my calls?..no why are u ignoring me?.."sake turo baki tayi tace"sir ni banyi ignoring dinka ba"..yace"shi kuma kin daukan wayana na meye?.."tace"ba komai"..kallonta ya tsayayi for like five minutes kafin ya sauie ajiyar zuciya ya sake yin kasa da muryanshi yace"nayi maki wani abun ne?.."ta girgiza kai...yace"then why all these?..why are u doing these?..if saboda na kwace maki rings dinki ne zan maido maki kayanki amma ki dena wahalar dani haka plss"...kallonshi tayi jin abunda ya fada kafin tace"nifa bakayi min komai ba..kawai naga mutane sun fara tunanin soyayya mukeyi shiyasa na dena kulaka"..diff yayi yana kallonta jin kalamanta...yace"yanxu sbd ana tunanin muna soyayya shine zaki dena daukan wayana?.."tace"to sir muda ba soyayya muke ba meyasa zamu ba mutane kofar da zasuyi tunanin soyayya muke?.."tana rufe baki yace"nina fada maki haka?..ko kinsan mind dina ne?.."dagowa tayi ta kalleshi da mamaki sai kuma ta kawar da kanta tana wani daure fuska tace"wlh ba soyayya muke ba"..cikin 6acin ran da yaji ya fara diran mishi yace"wai yaushe kika rainani ne haka?..kinsan zuciyata ne?..well idan baki saniba to let me tell you now..i love you..i love you with my whole heart kuma i want to marry u"..a rikice ta sake dagowa tana kallonshi taga yanda ya tsareta da ido kawai saita rufe fuska da hannayenta ta rushe da matsnancin kuka...hankalinshi yaji ya tashi sosai ga wani irin rauni da yakeji kawai saiya dafe goshi yana sauke numfashi..wai dama haka soyayyan yake ko kuwa nashi ne yake zuwa mishi da wann problems haka?..yana kokarin solving matsala sai kuma ga wani ya kawo kai sun taru suna neman fasa mashi zucia..ganin da gaske kuka takeyi yayi kasa da murya yace"yi hakuri i was kidding..bana sonki..amma seriously idan baki dena ignoring dinaba zaki sani cikin matsala wlh..koma meye ya faru I apologize and idan laifi nayi maki you are free to punish me amma ki dena bani wnn attitude din i beg of u plss"..dakatar da kukan tayi tana kallonshi hawaye sha6e sha6e a fuskanta tace"kace da wasa kake?.."da sauri yace"yea wasa nake..i never loved u"..ajiyar zucia ta sauke tana goge hawayen idonta tace"thank you"...kallonta kawai Bobby keyi yanajin wani irin daci a bakinshi sbd 6acin rai..yanxu tsanar da tayi mishi har yakai tasa mishi kuka sbd yace yana sonta?..anya kuwa zai samu soyayyar yarinyar nan?..anya kuwa zai iya jure wnn matsalolin?..ganin ya tafi wani dunian daban ta mike tsaye tana dubanshi tace"sir ni zan tafi"..dagowa yayi ya kalleta from head to toe before saying"ina hijab dinki?.."kallonshi tayi tace"wane hijab?.."rai a dan 6ace yace"ba nace ki dinga sa hijab idan zakizo makaranta ba?..wato mantawa kikayi koh..?"da sauri tace"nazo dashi fa yana class"..nuna mata inda ta tashi yayi yace"to zauna bamu gama mgn ba"..ba musu ta koma ta zauna tana wani ta6e baki tace"amma dan Allah kayi sauri ana jirana ne"...kallonta kawai yake dan baisan amsan da zai bata ba..wai shi yarinyar nana take gayawa mgn haka...idan ba ruwa daya daki babban zakara ba ita ta isa ta zauna gabanshi tana fada mashi mgn haka bai gaura mata mari ba..amma yanxun wai shine nan zaune tana zuba mishi iskanci iri iri kuma bai iya ta6uka komai ba sbd soyayya..amma soyayya baima Dr Bobby adalci ba wlh...saida ya bari ta gama ta6e ta6en bakinta snn yace"kinaji?.."tace"ehh.."yace"dan Allah inaso daga yanxu duk nayi maki laifi ki fadamin ba kije kiyita fushi kinakin daukan wayana ba..banajin dadi..snn kullum kika shigo school ki dinga zuwa office ina ganinki kinji?.."kallonshi tayi kaman zatasa kuka tace"sir kullum kuma?..ai ba kullum kake shigowa ba..kumani banaso inzo kayita min fada fa"da sauri yace"ina shigowa kullum mana..every morning zan shigo idan muka gama gaisawa sai in wuce hospital...kawai nidai ki dinga picking calls dina and ki dinga zuwa ina ganinki?..fada kuma indai ba ganinki nayi da wani ba ba abunda zaisa na miki..duk abunda kikaga na maki rashin jinki ne ke janyowa"mamaki sosai ya bata jin abunda yake fada...ba tareda ta kawo komai a ranta ba tace”zanzo..kuma ni ai bana kula kowa..besty ma da ya taf..."bata karasa ba yace"enough..zaki fara kou?.."da sauri ta dora hannu kan bakinta tace"yi hakuri toh..na dena"..kofa ya nuna mata yace"jeki"..da sauri ta mike ta fita shi kuma ya lumshe ido tareda jingina da kujera...shidai zaiga ranara da za’ayi mgn na minti goma da ita ba tareda tayi mentioning wnn bestyn ba...duk yanda yakai da son ganinta da kuma son kasancewa da ita gara ta tafi akan dai ta zauna tana mishi hiran wani wai besty..shi tunda yake bai ta6ajin ya tsani wani kaman yanda ya tsaneta da bestyn nan ba...ya samu ganinta kuma yayi mgn da ita maimakon ya samu farin ciki sai yajishi akasin haka..sam abunda yakeji is not close to farin ciki...wai shi soyayya dai haka yake cikeda rudu da matsaloli dama?..meya jefa kanshi a ciki ne?..innalillahi wainna ilaihi rajiun..yaketa maimaitawa a cikin ranshi...Nur na ganin fitarta daga office din ya dawo ciki yana kallon Bobby yace"Man how far?..ka samu ka shawo kanta?.."ba tareda ya bude idanunshi ba yace"for where?..yarinyar nan tanada rigima wlh..maimakon in samu sauki fa karamin tayi akan damuwan da nake ciki"...zaunawa Nur yayi kusa dashi yana murmushi yace"ai dama da ganin Lamido nasan mijinta sai yaci ubanshi wlh..at times sai inyita tunanin da wnn shagwa6an nata ya takeyi da boyfriend dinta ne kam?..i never tought it’ll turn out to be you sai yanxun"...kallonshi kawai Bobby daya bude idanunshi yakeyi..yasan abunda yake fada gaskia ne..shi kanshi ko a da din ya kanyi tunanin ya mijinda ya aure ta zaiyi coping da wnn halayyan nata sai gashi ya tsinci kanshi cikin tafkin sonta tsundum kuma baya fatan fitowa har abada...fatanshi ya samu ya shawo kanta idan tayi accepting love dinshi to duk abunda zai biyo baya mai sauki ne.

Ita kuwa tana fita ta kama hanyan class dinsu tana fadin"kam lallaima mutumin nan wani wai yana sona?..to ni ko rasa miji nayi me zanyi da inyamuri Allah na tuba...Allah ya kiyaye na auri dan yaro ma kamanshi wlh..aini matar manya ce ba matar irinsu kananun yara ba..dan rainin wayo kawai".












Rano✨





Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
32
Da misalin 9 na dare yana zaune dinning yasa

Please Login or Register in order to submit comment