You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
ya shirya cikin kayan da ta fito mashi dasu snn ya fita don cin abinci..yana hangota zaune tana shan custard dinta yace"baby rowa koh?.."dan dagowa tayi tana kallonshi daidai lokacinda ya karaso dinning din ya ja kujera ya zauna kusada ita ta mika mashi bowl din tace"to Bismillah"..makale shoulder dinshi yayi yana hararanta yace"banaso ai saida na roka kika bani"..da sauri tace"to zan dama maka wani"..tabe baki yayi yana girgiza kai yace"No"..nan da nan ta tale baki ta shiga mishi kukan karya tana bubbuga legs dinta kasa tace"Allah nidai sai kasha"..murmushi yayi sosai gamida dan matsawa saitin kunnenta yana shafa gemunshi yace"baby da kiyi saving wnn strength din for later..naga kaman zaifi maki amfani a can"..da sauri ta hadiye kukan nata tana hararanshi tace"ni saloon zaka kaini ai"..plate ya dauka ya fara serving kanshi tayi saurin mikewa ta karba tacigaba dayi shi kuma ya relaxing ya rungume hannu yana kallonta da murmushi yace"saloon da yamman nan baby?.."da sauri tace"eh ai Kaine kace yau zamuje kuma nidai bazan sake kwana kaina ba kitso ba"..kama hannunta yayi bayan ta gama serving dinshi yace"baby da ki bari sai gobe"..tun bai rufe baki ba tace"ni yau nakeson zuwa"..bai sake cewa komai ba ya shiga cin abincinshi itama tacigaba da Shan custard dinta..yana cin abinci yana santi dan da gaske tana maida hankali tayi mashi girki yanda ya kamata shiyasa a kullum yakejin abincin nata so delicious kaman abunda ta karanta knn a school..tana gama Shan custard din ta mike zuwa flat dinshi ta dauko car keys dinshi tun ma kafin ya gama yace mata ba yanxu ba snn ta wuce bedroom dinta ta zumbula zumbulelen hijab dinta ta fito rikeda phone dinta a hannu alamar she's ready to go..yana gama cin abincin yayi clearing dinning din da kanshi snn ya koma parlor yana sipping drink..kokarin kunna tv yake kawai sai ganinta yayi tsaye a gabanshi tana mika mashi key din mota..daria ya saki yana kallon yanda ta wani hade rai yace"yanxu baby ko hutawa bazanyi ba?.."kai tsaye tace mishi"idan mun dawo sai ka huta..nasan da hutawa wlh cewa zakayi sai gobe ni kuma am tired of zama da gashina a haka so kawai ka tashi muje ko kuma wlh in kira Mummy"..ajiyar zucia ya sauke tareda mikewa ya amsa key din suka fita daga gidan..tunda tasama ranta sai taje yasan idan ma baije ba ba barinshi zatayi ya sarara ba and tana hadashi da Mummy yasan nashi ya kare.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
64
Kai tsaye suna barin gidan saloon din da yasan su Miemie na zuwa ya kaita..tare suka shiga ciki ya zauna a reception yayinda ita kuma aka shiga da ita inda ake gyaran gashin..wash and set aka yi mata hade da kitso duka..lokaci mai tsaho suka dauka suna kitson sbd tsayin da gashinta ke dashi ga kuma kitson kananu ne..Bobby dai na nan zaune yana jiranta har zaman wurin ya fara gundurarshi sai gata ta fito bakin nan a washe kmr gonar auduga...tun a nan wurin ta bude mishi kitson ya gani aikam yayita santi yana yaba irin kyawun da yayi har matar dake wurin ta zauna kallonsu..kudi sosai ya debo ya bata snn ya kama hannun matarsa suka wuce bayan sun mata sallama..suna shiga mota ta dan juya tana kallonshi tana marairaicewa tace"partner i have a request plss"..tada motar yayi suka fita daga harabar saloon din yana cewa"just say what u want love"..da sauri tace"cinema zaka kaimu muyi kallo dan Allah"..da sauri ya girgiza mata kai yace"No"..sake marairaicewa tayi tana hada hannayenta wuri daya cikin sanyin murya tace"partner dan girman Allah muje..Manchester ne suke wasa kuma nasan ana haskawa a can plss don't say no please!.."juyawa yayi ya dan kalleta kafin ya dauke idon yana dan furzar da wani iska a bakinshi yace"bana sonki da kallon ball din nan bakiji koh?.."a hankali tace"only this once plss..daga yau bazan sake cewa ka kaini cinema ba wlh i promise"..banza yayi mata yacigaba da driving dinshi as baiga dalilinda zaisa ya dauki matarshi ta Sunna ya wani kaita cinema da yasan almost wayanda ke ciki maza ne ba..ganin yanda yayi banza da ita sai ta kawar da kanta gefe tana matsar kwalla ganin still yaki ce mata komai kawai sai ta hade kai da guiwarta ta shiga rera masa kuka kmr wanda yayi ma dukan tsiya..still Bobby bai tanka ta ba duk kuwa da yanda kukan ke ta6ashi amma ya daure bai ce mata kala ba..ganin abun nata bana kare bane kawai ya dauki hanyar Cinemar da yasan dole ana haska wasan a can..dalili daya zaisa ya kaita wlh amma ba don wani abu ba..har suka isa Cinema bata dago kanta ba shima baice mata kala ba..yana gama parking ya mika hannu ya dagota ya dora a cinyanshi yana nuna mata wurin da hannayenshi ai kam tana ganin Platinum Cinema rubuce a wajen ta saki wani ihun farin ciki tareda kwakwumeshi ta manna mashi peck a cheeks dinshi snn tace"nagode partner"..dungure mata kai yayi yana murmushi at least dai yaga darianta yanxu..hannunta na cikin nashi suka shiga cikin cineman bayan sun fito daga mota..a bakin kofar ya tsaya ya siya musu tickets snn ya sake rike hannunta zasu shiga tayi saurin dakatar dashi tana nuna mashi popcorn daga dan gefen inda suke tana wani kwabe fuska tace"baka siya mana popcorn ba"..kallonta kawai yayi gamida girgiza kai snn ya juya zuwa inda popcorn din yake..ita kuma ta samu wuri ta zauna tareda rungume hannunta daga nan inda take tana kallonshi tana murmushi..ita bataki su dauwama a haka ba wlh..ace mutum da matarshi wai bazai na kaita cinema kallo ba saida 'yan dabaru..mikewa tayi da sauri ganin yana dawowa nan wurin garin saurin da take ta take hijab dinta ta kasa aikuwa ta zame da tiles din wurin ta tafi luu zata fadi wani guy da yazo wucewa yayi saurin tareta ta fada jikinshi akan idanun Bobby da har ya kusa karasowa inda take..wani irin abu yaji ya daki chest dinshi kmr an harbeshi da kibia..Lamido kuwa runtse idanunta tayi tasan tunda tajita a jikin mutum to tabbas shi ya tareta shiyasa ko bude Ido batayi ba don ta riga ta gama sadakarwa zata jita zube a kasa sai kuma yazo ya tareta har wani sake matseshi tayi ta hannunta tana cigaba da sauke numfashi..mutumin daya riketa da sauri yakai hannu ya janyeta daga jikinshi yana kallonta daidai lokacin itama ta bude idanunta sbd qamshin perfume dinshi da taji ba irin na Bobby bane..gabanta ya bada wani irin sauri rass ganin wani mutumi ne daban tsaye a gabanta and bisa ga dukkam alamu shine wanda ya riketa ba Bobby da tayi tunani ba.. innalillahi wainna ilaihi rajiun..yanxu hakan na nufin ta rungumi kato knn..duba takai da sauri izuwa inda ta hango tahowarshi aikuwa ta ganshi yayi tsaye a wurin kikam yana kallonta kmr wani statue ga popcorn din da ya siyo gaba daya sun tarwatse a kasa..wani irin dummm taji wuta ta dauke mata gaba daya har wani juwa taji yana daukanta ta sake tafia da baya zata fadi the same man daya tareta daxu ya sake matsawa zai rikota Bobby da baisan lokacinda kafafunshi suka karaso dashi wurin ba yayi wani irin kukan kura ya gaura ma mutumin mari a fuska..da sauri ya safe cheeks dinshi yana kallon yanda take huci kmr wani tsohon zaki yace"how dare u..how dare u touch my wife with those filthy hands of yours..how dare u"..ya karasa mgn da wani irin karfi da hatta sauran mutane dake wajen saida suka tsorata..eyes dinshi sunyi wani jajir sun kankance sbd tsabar bala'i..da sauri guy din yaja baya har yanxu yana dafe da cheeks dinshi yace"am sorry gani nayi zata fadi kuma bansan matar aure bace"..hannu Bobby ya sake kaiwa zai kwada masa another mari mutane sukayi saurin shiga tsakani suna bashi hakuri..Lamido dai tunda tayi zaman 'yan bori a kasa a kasa tabuka komai sai kallonsu da take ga gabanta na tsnanta faduwa kuma ko digon hawaye babu a idanunta..wato idan masifa yayi masifa shi kanshi kuka bazai zo inda kake ba..ashe duk abunda akewa kuka ba wani babban abu bane..da wani irin force Bobby ya juya zuwa inda take kawai saiji tayi ya dauketa cak sun fita daga wurin sai a snn taji cikinta yayi wani irin murdawa kaman zataje toilet sbd tashin hankali..yanda taga face dinshi cunkus dama tasan yau mai rabata dashi sai Allah..ya dawo mata Proprietor sak data sani a FCNM mai shegen masifa da takurawa mutane...shiko Bobby tafia kawai yake yana yin karo da duk wani dake gabanshi don gaba daya hankali da nutsuwarshi basa tare dashi..he can't still believe what just happened..he can't believe a gabanshi kuma a kan Idonshi wani Wawa can ya samu damar ta6a masa mata kuma wai har da kanta take sake hugging dinshi.. innalillahi wainna ilaihi rajiun..da kyar ya iya isa inda motarshi yake ya bude baya ya sakata a ciki snn shima ya zagaya ya shiga ya tada motar ya figeta da wani irin gudu kaman zasu tashi sama..gudu kawai yake shararawa baya ko la'akari da yanayin hanya da kuma motoci dake wucewa a wurin burinshi kawai su isa gida yaji dalilin ta na cewa sai sunzo Cinema at the first place..su Lamido dai ana baya sai wuwwurga idanu akeyi kmr munafuka..ga wani zufa da takeyi duk kuwa da sanyin acn dake motar sbd tsabar rudani..duk wani addu'a da yazo bakinta yinshi kawai takeyi don bata ma San wanda ya kamata tayi ba a halin yanxu..suna isa gida bayan yayi parking ta runste ido tana jira taji yazo ya fito da ita daga motar ya fara kwallo da ita tun daga nan wurin amma sai taji shiru kmr ma baya cikin motar..bude ido tayi da sauri tana kallon driver seat sai taga wayam ya bude motar ya fita..da sauri itama ta fita tabi bayanshi taga har yakai entrance door dinsu ya bude ya shiga ciki itama da gudu gudu ta karasa ta bude kofar ganin baya parlor direct ta kama hanyar flat dinshi amma sai tajishi a kulle alamar rufewa yayi daga ciki..zaro ido tayi tareda jingina bayanta da bango ta dora hannu a ka sai yanxu hawaye suka kawo idanunta tace"na shiga uku na lalace..mena janyoma kaina haka ni Aysha?..wane masifa ne wnn na janyoma kaina..wayyo Allah na shiga uku"..daga haka ta durkushe a wurin tana sakin wani marayan kuka..kuka sosai irin na wanda uwa da uba suka mutu suka barshi shi daya tak a doron dunia ba tareda wani shaqiqi ko masharci ba..kmr an tsokareta ta mike ta fara buga kofar da karfi tana cewa"partner dan Allah ka bude kaji..i can explain everything plss open door plss"..ta karasa mgn cikin kuka sosai amma bataga alamar zai bude kofar nan ba..shima ya a ciki yana jinta kawai takaici yakeji na duk wani abu daya faru.. gani yake dama on purpose tace suje cinema din kilan dama tasan hakan might happen shine zata raina mashi wayo..wai ace agaban idonshi..akan idonshi wani ya rungume masa mata kuma kiri kiri ya kasa yin komai akai?.. innalillahi wainna ilaihi rajiun..gaba daya wani irin zafi yakeji all over his body..ga zuciarshi da yakeji kaman fashewa zatayi sbd takaicin da yake ciki..gani yake kmr bai ladabtar da yaron yanda ya kamata ba..ita kuma baima san hukuncin dazai dauka a kanta ba dan a halin da yake ciki yasan tsaf zai iya Marin nata itama shiyasa bazai ma bari ta doso inda yake ba don zai aikata mata abunda he might end up regretting..kawai dai ta riga taci amanarshi kuma ta gama dashi data bari wani tsinanne can ya rungumeta..har yanxu ganin hug din yake a cikin idanunshi tamkar yanxu abun ke faruwa..wnn wace irin rayuwa ce ne?..wane irin masifa ne wnn ya kutso kai cikin rayuwarshi Kuma?..wane irin bala'i ne wnn?..gani yake duk dunia a yanxu da kyar za'a samu wanda zai kaishi baqin ciki da tashin hankali..he feel like doing something stupid amma bazaiyi ba sbd gudun dana sani...haka nan yayita zaune cikin dakinshi sai kaiwa da kawowa yake ko zama ya kasayi sbd tashin hankali..Aysha dai har yanxu na bakin kofa tana faman kuka tana bashi hakuri amma to no avail tunda gashi har anyi sallahn magrib bai bude kofar ba..mikewa tayi da kyar ta shiga dafa bango sbd jirin da takeji ta koma zuwa dakinta ta zame hijab dinta a hankali tareda kwanciya kan gado ta rufe face dinta da pillow tana sake rushewa da kuka..Bobby na dena jin sheshshekar kukanta yayi saurin shiga bayi yayi alwala snn ya fito ya bude kofar ya tabbatar bata wajen snn ya wuce masallaci..koda yayi sallahn magrib bai dawo gidan ba har akayi Isha..daga masallacin kai tsaye eatery ya wuce yayi mata takeaway din abinci don shidai yasan bazai iya sa komai a bakinshi ba..koda ya shigo gidan bai ganta a parlor ba dan haka ya ajiye mata abincin a dinning hoping Allah yasa taci snn ya wuce flat dinshi..kayan jikinshi ya rage snn ya kwanta kan gado yayi pillow da hannayenshi ya lumshe ido scene din daxu na sake dawowa kwanyarshi..har yanxu hango abunda ya faru yake kaman a mafarki..ciwo yakeji sosai cikin heart dinshi wanda yasan if care is not taken yana iya samun gagarumin problem..dauriya kawai yakeyi amma Allah kadai yasan halin da yake ciki..gyara kwanciya yayi ya rungumi pillow wai yanxu after duk abunda ya faru ji yayi yana missing dinta..he missed her warmth body a jikinshi and yasan yau bacci barawo ne kadai zai iya zuwa daukanshi don a yanda yakejin eyes dinshi dai babu alaman bacci a tare dasu..bai tana tunanin zuwan rana irin wnn da zai kasance suna gida daya amma bazasu kwana the same room ba..sam bai taba kawo irin wnn thought din ba a zuciarshi..gani yake ko nawa za'a bashi bazai iya bari hakan ya faru ba amma now gashi.
A nata 6angaren itama tayi kuka tayi kuka har wani bacci ya lalla6o ya dauketa a nan inda take zaune ba tareda ta shirya ba..ba ita ta tashi a baccin ba sai after nine ta shiga bathroom tayo alwala snn tazo ta gabatar da sallah tareda da addu'an Allah ya daidaita tsakaninta da mijinta don bazata iya jure wnn fushin nashi ba..tana idar da sallah ko hijab din jikinta bata cire ba ta sake komawa flat dinshi wai ko Allah zaisa ya bude mata kofa amma iya tsaiwanda tayi a wurin ko motsinshi bata ji ba balle tasa ran ya bude mata kofar..tana kuka sosai ta sake komawa bedroom dinta ta wurga kanta kan sofa tareda kudundunewa cikin hijab dinta nan take kuma zazza6i mai zafin gaske ya rufe mata jikinta..dama tun safe takejin alamun zazza6in amma bai sauka ba sai yanxun tasan kuma bazai rasa nasaba da zullumi da kuma uban kukan da taci bane..ko baccin ma kasayi tayi don basu taba kwana separate room ba tunda sukayi aure sai yau..kuma ita tsoro takeji don ko a gida bata saba kwana ita kadai ba suna tareda Husna a school kuma tareda Billy so zata iya rantsewa ma ita bata taba kwana ita kadai a daki ba ko gidan aunty Fiddausi taje tareda Mufida suke kwana..tun kukan nata na fita tareda sound har ya koma zallar hawaye takeyi babu saurin komai sbd disashewa da muryanta yayi...har dare yayi nisa sosai bata samu bacci ba sbd zazzabin dake jikinta sai gabannin asuba ta samu baccin yayi gaba da ita shima kuma cikeda mafarkai marasu dadi.
Shima Bobby sbd rashin samun enough bacci har ya makara sallahn asubah dan lokacin da ya tashi an idar da sallah a masallaci..alwala ya shiga yayi snn ya gabatar da sallah yacigaba da zama nan yayi su azkhar da addu'o'i har saida gari yayi haske snn ya mike daga wurin ya fita direct to her bedroom dan tashinta tayi sallah..a nan kan sofa ya sameta kwance ta kudundune da hijab dinta..ya karasa a hankali ya zauna kusa da ita yana kallon yanda face dinta yayi jaa sbd kukan da kwana tanayi..lumshe ido yayi ya bude tareda kai hannu da nufin ya zare hijabin dake jikin nata sai yaji jikin ya dauki wani irin zafi kaman ana hura mata wuta..da sauri ya daga hijab din nata yana sake dora hannu jikinta yaji still temperature yayi rising baisan lokacinda ya dagata gaba daya ya cire mata hijabin ba..a firgice ta tashi taga baccin tana hada ido dashi ta mike zaune da sauri tana kwabe fuska tace"par..tner"..daure fuska yayi yana kallonta yace"what's wrong with u?.."kuka ta farayi tana cewa"partner dan Allah let me explain"..bai bari ta karasa ba ya dora finger dinshi akan bakin nata still fuskanshi daure yace"i said me yake damunki?.."kasa tayi da idanunta hawaye na sake cikowa cikinsu tace"fever.."yace"only fever?.."kai girgiza tana share hawayen tace"da ciwon kai"..dauke idonshi yayi daga kallonta dan yanda yaji kukan nata na neman karya mishi da zucia yace"kinyi sallah?.."Kai ta girgiza mashi alamar no yace"then shiga bathroom kiyo alwala"..kallonshi ta tsaya yi zatayi mgn ya dan daga murya yace"just go don't waste my time"..mikewa tayi da sauri ta shige bathroom tana shiga ta durkushe nan kasa ta fashe da matsanancin kuka..gaba daya gani tayi ya dawo mata asalin Dr Bobby data sani..gabanta har wani faduwa yakeyi duk ta kalleshi taga fuskan nan nashi a cunkushe..da kyar ta iya mikewa tayi easing kanta tayi brush snn ta daura alwalan ta fito tana takawa a hankali sbd zazza6i dake sake rufe mata jikinta..tana karasowa ya nuna mata inda ya shimfida mata praying carpet ya mika mata hijab dinta without looking at her yace"kiyi sallah"..ba musu ta amsa hijab din ta saka snn ta tsaya kan carpet ta tayar da sallah shi kuma ya mike zuwa kitchen don nema mata abunda zataci kafin ya bata drugs..hankalinshi ya tashi sosai da jin yanda temperature dinta yayi high hakan Sam bazai hanashi nuna mata girman laifinda ta aikata ba..takeaway din daya ajiye mata jiya a dinning yaga yana nan untouched meaning bataci abinci ba ta kwanta knn..duk sai ya sake jin jikinshi yayi sanyi kawai ya shiga kitchen yana tunanin abunda ya kamata yayi mata yanxu taci kafin ya bar gidan.. custard dinta ya gani inda ta ajiyeshi jiya dan haka ya dora ruwa a gas da sauri ya dama mata custard din ya zuba Madara da sugar snn ya koma dakin nata..a kwance ya sameta inda ta idar da sallah ta sake lullu6e kanta da hijab ya karasa ya ajiye custard din akan table snn ya mikar da ita tsaye bayan ya cire mata hijabin ya nuna mata custard din da hannunshi fuskan nan ba sarari yace"dauka Kisha"..kallon custard din tayi kafin ta dawo da kallon gareshi kmr zatasa wani kukan tace"na..koshi"..saida gabanta ya fadi da ganin yanda ya sake hade rai yana kallonta..murya a cunkushe yace mata"ina wasa dake ne?.."da sauri ta hau girgiza kai tana goge hawayen dake zubowa face dinta tace"ah..ah"..yace"then ki dauki custard din nan kisha idan baso kike kiga other side of me ba"..wani yawu ta hadiye mai daci snn takai hannu ta dauka custard din ta fara sha a hankali tana yatsine fuska kmr mai Shan magani..baifi spoon biyar tasha ba zata ajiye cup din yace"don't u dare..shanye shi zakiyi gaba daya"..haka tacigaba da danna custard din cikinta tana hawaye tana komai har Allah ya nufa ta gama shanyewa..dauka cup din yayi ya fita daga dakin can sai gashi ya dawo da drugs da goran ruwa a hannunshi..daga nan inda take ya tsaya ya 6alli drugs din ya mika mata tareda ruwan dake hannunshi yace"amsa Kisha"..nan ma ba musu ta amsa drugs din daga hannunshi ta fara zuba ruwan a bakinta snn ta watsa drugs din ta hadiyesu aikam tana hadiyewan taji wani irin amai ya taso mata tayi saurin mikewa tana toshe da bakin zata wuce bathroom saidai kafin ta karasa bathroom din ta durkushe nan kasa ta shiga kwarara aman a nan..Bobby na tsaye rungume da hannu yana kallonta..tausayinta yakeji sosai amma taurin kai da kuma zafin abunda tayi bazai bari ya nuna hakan ba..karasawa yayi shima ya durkusa nan inda take ya dagota jikinshi bayan ya fuskanci ta gama aman ya dauketa cak ya shiga bathroom da ita..ruwan zafi ya hada ya mata wanka da kanshi yanata wani daure dauren fuska shi a dole baiji wani abu ba har ya gama ya daura mata towel ya fito da ita..da kanshi ya shiryata yasa mata simple doguwan riga mara nauyi snn ya kwantar da ita kan gado ya fita daga dakin..tea ya sake hada mata da Milo kadai sai sugar snn ya hada da injection ya dawo dakin nata..wnn karon da kanshi ya bata tea din tasha snn ya shiga withdrawing alluran da zaiyi mata..tana ganin allura duk ta rikice tana kuka tana rokon yayi hakuri shidai baice mata komai ba har ya gama hada alluran sai kawai ya tsaya yana kallonta..duk wnn abun da yake Allah ya sani karfin hali ne kawai amma shi kadai yasan yanda yakeji a cikin ranshi..yasan halinta ne indai ba wuta wuta yayi mata ba bazata shiga hankalinta ba shiyasa zaiyi iya bakin kokarinshi yaga bai bar tausayinta da yakeji yayi tasiri a yanxun ba har saita fahimci kuskuren data aikata..zaunawa yayi kan gadon ya dagota yayi mata alluran tanata faman ihu amma bai saurara ba saida ya gama snn ya rungumeta a jikinshi yana patting bayanta a hankali..wnn zafin na jikinta har tsoro yake bata wlh..ji yake kaman yayi transferring ciwon daga jikinta zuwa nashi da kilan bazai dingajin yanda yakeji yanxu da ciwon yake a jikinta ba..karfin hali kawai yakeyi amma yana cikin damuwa sosai..bai ajiyeta ba saida bacci ya dauketa snnya kwantar da ita ya rufeta da duvet ya fita daga dakin..wanka yayi shima ya shirya snn ya sake komawa dakin nata ganin baccinta yayi nisa sosai yayi deciding ya dan leka hospital kona few hours ne ya dawo tunda yanada aiyuka a can..ko abincin shi baici ba ya karasa shiryawa ya bar gidan tareda driver dinshi..yau ko main house bai shiga ya gaida Mummy ba sbd baison ta tambayi abunda ke damunshi.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
65
Har wajen 1 yana Hospital yanata duba patients ga kuma hankalinshi gaba daya yana kanta..so yake yaji halinda take ciki kuma yanata Kiran wayanta bata dauka dan haka yayi deciding ya kira Mummy tasa aje a duba mashi ita..bayan ya sallami patient din gabanshi bai sake Kiran wata ba yayi relaxing kan seat dinshi yana dialing number Mummy..tana dauka ko gaisawa bai bari sunyi ba yace"Mummy aje a dubamun Aysher plss..batada lafia and inata kiran wayanta bata picking"..da dan damuwa Mummy tace"subhanallah what's wrong with her?.."murya can kasa yace"fever da headache"..Mummy tace"amma kasan batada lafia shine baka zauna tareda ita ba Bobby?..yanxun idan wani abun ya sameta fa?.."a hankali yace"Mummy nothing will happen to her inshaAllah..ya kama dole ne fitan nima da bazan fito ba..yanxun dai ko Miemie ki tura taje ta ganomun halinda take ciki plss..i still have lots of patients ne da zuwa zanyi da kaina in ganta"..ajiyar zucia Mummy ta sauke kafin tace"don't worry yanxu zataje ta ganota..i will get back to u"..yace"alright Mummy.. nagode"..Mummy bata sake cewa komai ba tayi hanging Kiran..fitowa tayi da kanta tacema Miemie dake karatu sbd sun kusa fara waec taje ta duba mata Aysha wai bata da lafia..da sauri ta warware veil dinta data daura a kai ta yafashi snn ta fita daga gidan..ta main gate ta fita sbd taga kofan cikin kaman a kulle ne..tana zuwa ta kwankwasa mai gadi ya bude mata ta shiga cikin gidan kai tsaye..a bedroom dinta ta sameta tashinta daga bacci knn sai kuka take har lokacin kuma akwai fever sosai jikinta..hankali tashe ta kira Mummy ta fada mata halinda ta sameta a ciki don haka Mummy ta turo driver dinta tace ya daukesu kawai su wuce asibiti tunda Bobby yana can sai ya dubata..Miemie ta dauki hijab dinta tasa mata snn ta kamata suka fita compound inda driver je
Book Chapters
Chapter 53
Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59