You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
zamu yadda dake kaman bamusan halinki ba koh?..to bari kiji in fada maki babu fashi komawa makarantanki gobe idan kuma kika sake kika sake min mgnr nan sai kinci ubanki wlh...daidai nake dake ai kinsani"...nan da nan ta fara hawaye tana cewa"nifa Ammi Allah na gaji da Kano inaso in dawo gida...kuma Proprietor dinmj inyamuri bashida mutunci wlh"...Ammi mikewa tayi zata bar parlon tace"ur problem not mine..nidai na gama mgn kuma Allah yasa kar ki dena kukan nan kiga yanda zanyi dake a gidan nan...shashasha kawai"...daga haka Ammi ta wuce dakinta...ita kuma hajia indo ta rungumi pillow tana sake rushewa da kuka.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
15
Yau Sunday tun around ten Hamma ya tafi maidasu bisa umarnin daddy ya maidasu da wuri shima ya samu ya dawo gida da wuri kafin dare...karfe daya a cikin Hostel yayi musu...Hamma bai tafi ba saida ya tabbatar ba abunda suke bukata snn ya musu sallama ya wuce su kuma suka shiga area classes don duba Posting dinsu...gida biyu akayi dividing class dinsu first 19 aka turasu Freedom sauran 19 din kuma aka turasu Kinana...gaba daya ran Aysha taji ya 6aci itadai Allah ya sani ba son Freedom din nan takeyi ba...tasan ko baa fada ba Dr.Bobby mugun takurawa mutane zaiyi sbd yana ganin Hospital dinshi ne...ita kuma harga Allah yanxu batason abunda zai sake shiga tsakaninta dashi yazo yana mata rashin mutunci tunda ta fuskanci dabi'arshi ne...kallon Billy tayi tace"Billy zo muje muyi mgn da provost ko zaisa baki a canxa mana posting din nan...na tsani zuwa Freedom wlh"...Billy tace"but why?..asibitin yanada kyau fa Lamido..besides ko kinje wajen provost ma i don't think zasu canxa maki cox ba'a ta6ayima mutum posting kuma daga baya a sake mishi ba..kawai ki hakura dashi nasan muna fara zuwa zakiji kina enjoying"...girgiza kai ta shigayi bayan Billy ta gama mgn tace"nidai dan Allah ko rakani ne kiyi plss...Allah bazan iya zuwa Hospital din nan ba haka nan da kayi small mistake Proprietor yace zaiyi maka rashin mutunchi"...daga kafada Billy tana cewa"Fine tunda bakiji shawara na ba...nima kuma babu inda zan rakaki sai kije ki dawo ina jiranki a nan"...hararanta tayi ganin itama zata mata wulakanci kawai ta juya ta tafi ita kadai...kafin ta shiga office din secretary dinshi tace baya nan amma yace idan anzo nemanshi ta kira ta sanar dashi dan haka tayi dialing number dinshi yana dagawa tace"Sir Lamido tazo nemanka"...daga other side din yace"kice ta sameni office din Dr.Bobby"..tana kashe wayan tace mata"yace kije office din Dr.Bobby yana can"...Aysha ta wani zaro ido jin ta ambaci Dr.Bobby tace"tsaya..waye Dr.Bobby?.."dan murmushi Secretary din tayi kafin tace"Proprietor mana"...wani irin diff tayi kaman wuta ya dauke mata...tabbas da tasan inda yake knn da bata bari an kirashi bama in the first place bare har yace taje can ta sameshi...itafa ta tsani abunda zai hadata da inyamurin nan ko kadan..sam batason hada sabga dashi sbd ta lura ba karamin mara mutunchi bane...gashi kuma Secretary ta ambaci sunanta da wlh bazata jeba sai tayi wucewarta ta dawo daga baya amma yanxun tunda yaji sunanta tasan zuwa ya zama mata dole ko don posting da takeso a sake mata tunda gobe zasuyi reporting...ganin tana 6ata lokaci a banza ta juya ta fita daga wurin tayi hanyar office dinshi tana sake sake cikin ranta sai kuma taji haushin kanta for tsoron wnn inyamurin...kawai ma gara taje inyaso ta dake ta fadi abunda ya kawota tasan duk tsiya dai bai isa yasa hannu a jikinta ba...da wnn sabon courage ta isa zuwa office din...bayan an bata permission din shigowa ta tura kofar a hankali ta shiga kai a kasa...yana zaune kan kujera yayinda Dr.Bobby shima ke zaune kan office chair dinshi...ta karasa ciki ta tsaya snn tacema Nur"good afternoon sir"...yace"Afternoon Lamido ya holidays" ...ta dan kakalo murmushi tace"Alhamdulillah"..yace"to bismillah zauna inji meke tafe dake?.."tace"thank u ba saina zauna ba Sir...akan mgnr posting ne dama"...yace"Posting?..meya faru?.."saida ta hadiyi saliva trying very hard not to look at Bobby da zata iya rantsewa taji wann shegun eyes din nashi a kanta tace"Sir...banason inda akayi posting dina shine nace in maka mgn ko zakasa a canxa min?.."Nur dake kallonta yace"No problem ina akayi posting dinki?.."ta sake hadiye wani yawun snn tayi qundunbala tace"Freedom"...da mamaki sosai Nur yake kallonta yace"amma why bakison Freedom din?..naga students da yawa har so sukeyi ayi posting dinsu can"...kai tsaye tace"Sir kawai nidai banaso"...saida ya danyi shiru na wani lokaci kafin yace"shknn kije zanyi mgn da Isaac sai muga yanda za'ayi"..nan da nan ta saki smile tana fadin"thank u so much Sir..nagode"..wani mamakin ya sake kamashi ganin how happy she is kawai sbd xaa canxa mata posting...lallai bata son Freedom din kuwa kaman yanda ta fada...Dr.Bobby yayi shiru yana kallonsu saida suka gama yace"ba wanda za'a canxama posting"...a tare Nur da ita suka juya suna kallonshi...ganin kallon da suke mishi ya sake tamke fuska yana cewa"don me za'a canxa mata posting bayan ba haka akeyi ba...who did she think she is?.."Nur yace"amma..."bai bari ya karasa ba ya katseshi da fadin"if she can't stay..she leaves"...mamaki sosai ya kama Nur kawai yayi sakato yana kallonshi...ita kuwa Aysha right now ji take kaman ta kwada masa mari...dan rainin hankali har ita zai wani ce she leaves?..wlh da daddynta zai amince da daga office din nan ko Hostel bazata koma ba zatayi gida saidai Bilkisu ta taho mata da kayanta amma she won't sbd tafi kowa sanin halin mahaifinta...rai a matukar 6ace ta juya zata fita yace"dawo.."tsayawa tayi cak da tafiyar ita bata juyo ba kuma bata cigaba da tafiya ba...shi kuma ganin ta wani yi tsaye ta juya musu baya saiya tuna ranar da sukaje Hostel dinsu ma haka tayi musu...a kausashe yace"i said come back here...are you deaf?.."juyawa tayi ta koma gaban table din fuska a tamke...Dr.Nur dai relaxing yayi yana kallon wnn rigima nasu...ya shiga binta da wnn kallon da bata kauna snn ya nuna hannunta da fingers dinshi yace"remove those things"...a rikice ta dago tana kallonshi sai kuma ta dauke kan da sauri jin wnn abun da batasonji duk ya kalleta..hannun nata ta kalla zobuna ne na gold guda biyu ajiki kwata kwata mantawa tayi bata ciresu kafin ga bar gida ba...ta dan rage murya tace"Sir..."kasa karasawa tayi sbd wnn idanun dai daya zuba mata...bata sake yunkurin mgn ba takai hannu ta zarosu daga fingers dinta snn ta ajiye kan table din ta juya a fusace ta fita daga office din..shi kuma ya daukosu daga inda ta ajiye ya bude wani drawer dake kusa dashi ya watsasu ciki ya rufe...duk abunda yake idanun Nur na kafe a kanshi yana kallon latest behavior dinshi...mamakin ta yanda har ya lura da akwai zobe hannunta yake dan koshi da suke mgn da ita bai lura akwaisu a hannunta ba saida ya fada...wani murmushi ya saki yana shafa beard dinshi yace"Dr.Bobby tell me plss..do u love this girl?.."wani kallo Bobby ya bishi dashi kafin yace"what the hell...are you insane?.."Nur ya daga shoulders dinshi yace"no am not..kawai dai inaso in san ta yanda akayi ka lura da akwai rings a hannunta bayan koni da nake mgn da ita ban lurada hakan ba"...tsabar haushi kasa mgn yayi sai ido kawai daya zuba mishi yana mishi kallon da shi kanshi yasan zaiji ajikinshi...ilai kuwa Nur din ya dan yatsine fuska yace"C'mon stopping looking at me that way plss?..sbd kasan tasirin idanunka shiyasa kakeso kayita tsatstsare mutane dasu don kasa sunajin somehow..nidai stop looking at me plss tunda mgnr ne bakaso an barshi"...murmushin cin nasara ya saki tareda komawa yayi relaxing kan kujeranshi...Nur yace"dole kayi smiling mana tunda ka cuceni"...baice mishi komai ba sai shoulder dinshi daya daga.
Washegari Monday kowa zaije yayi reporting a Hospital da aka kaishi...kaman kullum karfe 8 school bus dinsu ya kwashesu zuwa Freedom Specialist Hospital...daidai lokacinda suka isa Hospital din shima Dr.Bobby yazo..bayan bus dinsu yayi parking duk suka fito shi kuma bai fitoba sbd waya da aka kirashi...daga nan inda yake ya hangota suna mgn da Billy baidai san me suke cewa ba yaga sun nufi wurin wata mota...suna fitowa Aysha da tun shigowarsu taga motar babynta a parking space tace ma Billy"wlh Billy shine ba gizo yakemin ba..dama yace yau ko office bazai iya zuwa idan baizo ya ganni ba"...Billy da zuwa yanxun ta dan fara sakewa dashi tace"ikon Allah..kinga har ya rigamu zuwa"..Aysha daketa blushing tace"ai Allah kadai yasan tun yaushe yake a nan...zo muje kar ya gaji da jira"..ba musu Billy ta bita zuwa inda yake...tun kafin su karaso ya bude mota ya fito idanunshi kan Aysha yanajin kaman ya rungumeta ga jikinshi tsabar kewarta da yayi...suna karasowa Billy ta gaisheshi ya amsa da tambayan ya baby girl dinshi tace"wnn baby girl din taka fa sai kai...bazan iya da fitinanta ba"...yayi daria yace"anya kuwa zan yadda dake Billy?.."itama tayi dariyan tace"ai dama bazaka yadda ba na sani...nidai bari na shiga ciki sai anjima"..yace"to shknn Bilkisu ina godia sosai"..bata sake cewa komai ba ta bar wurin..shi kuma ya bude front seat yana kallonta yanajin kaman ya maidasmta cikinshi...ba musu ta shiga ya rufe kofa snn ya zagaya shima ya shiga...kallon juna kawai sukeyi kowa yanajin soyayyan dan uwanshi na karuwa cikin zuciyarshi...a dan zamansu dashi Aysha ta fuskanci zurfin da yayi a karatun boko baisa ya zubar da addininshi ba...yanada addini sosai dan tunda suke bai ta6a yi mata anything dirty ba..ko dirty talk bai ta6ayi mata haka kuma bai ta6a kama koda hannunta ba...wnn dalilin yasa sonshi ke karuwa cikin ranta..tasan matukar ta aureshi tayi dace da salihi kuma muminin namiji...shi kam ganin time na tafiya and baiso ta makara ya dan saki smile yana cewa"i missed you"..ita kuma shagwa6e fuska tayi kaman wata baby tace"i missed you more baby"..yayi murmushi tareda dauke kanshi dab yanda tayi da face dinta yasa yaji kaman yayi hugging dinta...yanason yarinyar nan to the moon...hira suka dan ta6a kadan snn yace mata zai wuce amma su shirya itada Billy da yamma zaizo ya kaisu shopping...ta wani lankwasa murya tace"baby u shouldn't bother munada komai wlh"...hade rai yayi yace"banason musu baby..idan kuma ban isa ku amsa abun hannuna bane fine"...da sauri tace"to kayi hakuri na dena...zan fada mata inshaAllah"...yace"yauwamy little baby girl...yanxun ki shiga ciki kar suga kin dade baki shigo ba"..ba musu ta bude mota ta fita ta sunkuyo ta window suka sake yin sallama snn ya tada motar ya tafi ita kuma ta shige ciki...duk wnn abun da suke kan idanun Bobby daya gama wayan da yake tun daxu amma ya kasa fitowa daga motar...tunda yaga ya bude mata mota ta shiga da kuma yanda yake hango murmushinda take daga nan inda yake yasan confirm wnn boyfriend dinta ne...haka nan yaji wani irin haushinta ya kamashi cikin ranshi yace"she isn't only a spoiled brat she's also a flirt"...har saida yaga ta fito daga motan snn shima ya bude nashi ya fito...driver dinshi da tunda sukazo ya fito waje ya mika mashi briefcase dinshi ya amsa snn yasa kai cikin building din.
Tana zuwa ta samu colleagues dinta office din Chief Nursing Officer inda daga nan akayi posting dinsu various wards...Billy tana Antenal Clinic Aysha kuma tana cikin Labour Room...ranta duk ya 6aci an rabata da qawarta snn kuma an kaita maternity da bata kauna...sam batason aikin labour room sbd azabar wahala...aikine sosai suke yinshi kmr ba gobe shiyasa duk dunia ba ward da take son aiki kaman ANC ko Family Planning Unit...su aikinsu nada sauki and ba'a shifting amma yanxu tasa a labour room da kyar idan ba'a sata shifting ba...tanata 6ace 6acen rai suka fita daga office din..Billy ta wuce ANC tareda sauran da akayi posting dinsu tare itama Aysha suka wuce Maternity.
Karfe goma daidai Dr.Bobby ya shiga Maternity don yin ward round...wata Midwife dake zaune Nurses Station tana cike Register tazo da sauri ta gaisheshi snn ta koma ta fara harhada files din patents...ta dorasu gaba daya kan trolley snn ta turama Aysha data fito daga labour room yanxu tace"Aysha dan je kuyi ward round da Dr in samu in karasa cike Register nan"...ba yanda ta iya haka ta tura trolley din tayi gaba...yana tsaye kusada bed din wata patient da sukayima cs last two days yana mata tambayoyi Aysha ta karaso wurin...ta daure fuskanta sosai tana sunkuyar da kai kasa dan ko Allah yasan batason hada idanu dashi...tunda tazo wurin yaji zuwan nata amma yanda yayi zaka rantse babu wata hallitta a kusa dashi...hankalinshi gaba daya yana kan patient da yakema tambaya ko kallon bayanshi da yasan tana tsaye baiyi ba...tana fada mishi sunanta Aysha ta shiga nemo file dinta cikin tulin files dake kan trolley kawai sai ya kai hannu ya janyo trolleyn zuwa gabanshi ya dauki file din nata snn yacigaba da aikinshi...wani sabon takaici taji ya lullu6eta...meyasa mutumin nan keyi mata haka ne wai?..meyasa bashida kirki ko kadan?..ganin ya tura trolleyn da kanshi zuwa next bed itama ta ta6e baki cikin ranta tace"ka wutar dani nima"..ta juya ta koma ciki...midwife din da taga ta dawo tace"ya kika dawo kuma?.."kai tsaye tace"shi yace in dawo"...mikewa tayi daga inda take zaune ta fita zuwa inda yake..ita kuma Aysha ta zauna inda ta tashi tacigaba da cike nata register...bayan ya gama ward round har zai fita tace mishi akwai wadda ya kamata ya duba cikin labour room dan haka ya juya zuwa labour room din...Aysha na zaune tana aikin gabanta ko kallon inda suke batayi ba...sun shiga ciki suka samu matar dake ciki tanata fama har kan baby ya fara fitowa sukayi kanta da sauri...ganin harta jigata ranshi ya 6aci sosai...ita waccan zaman uban me takeyi da har patient ra kusa haihuwa bata sani ba...midwife da suke tare tana kokarin taimakawa matar ya dakatar da ita...tace"Sir babyn zaisha ruw..."bata karasa ba yace"call that useless da take zaune ta kyaleta ita kadai"...da sauri ta fita ta kira Aysha...yana ganinta ya sake dinke fuska yace"are u mad?..bakida hankali zaki wuce ki bar patient ita kadai cikin wnn situation din?..are u sick or something?.."dan turo baki tayi tace"ai ni bansan ta kusa haihuwa ba...kuma Register nake cikewa"...sbd tsabar takaici kasa ce mata komai yayi...yana nuna patient din yace"go and attend to her and make sure u did not make any mistake cox you'll regret knowing me"...cikin zuciyarta tace"ai ko a yanxu i regret knowing u wlh...me za'ayi da sanin masifaffen mutum irinka"..karasawa tayi inda matar ta shiga taimaka mata...yana tsaye rungume da hannu yana kallonta kaman bai ta6a ganin yanda ake kar6an haihuwa ba...so yake yaga tayi mistake komai kankantarshi yaci mata mutunchi amma baiga tayi mistake din komai ba...wato dai ba brain kadai takeda ba har skills tana dashi...sam baiji ta wani burgeshi ba duk abunda take...ta kar6i haihuwan successfully ta gama ta kuma yi duk wani necessary abu daya kamata tayima matar da babyn sai a lokacin ya juya ya fita..ita kuma ta bishi da harara kaman idonta zasu fado tace"duk wani baqin hali dai a gun inyamurai ya kare...har abada basu son a zauna lafia".
Around 5:30 suka gama shiri suka fito dan zuwa shopping da Prof kaman yanda suka tsara...bakin gate dinsu sukayi ido hudu da Sa'eed dake jingind jikin motanshi yana kokarin kiran one of them a waya...Aysha ta wara idanu tana kallonshi smilingly tace"my bestyyy"...dagowa yayi yana kallonta sai kuma ya daure fuska yana hararanta...ta karasa kusa dashi da sauri tana cewa"haba my besty...hope ba fushi kakeyi dani ba"...hararan nata ya sakeyi kafin yace"ba wani your besty...ni da aka manta dani"...da sauri tace"oh C'mon besty kaima dai kasan ba wanda ya isa ya mantaka..jiya fa na kira wayanka ban samu ba Allah"..kafada ya daga yace"baki damu ki ganni ba ai..ni da na damu ai gashi nazo har inda kuke"...kaman zatasa kuka tace"besty wai meye haka plss?..kanaso Billy tayi mana daria koh?.."juyawa yayi ya kalli Billy dake tsaye tana kallonsu ya wani kwa6e fuska irin yanda bestyn tashi keyi idan abubuwan suka motsa yace"Billy hadda ke ma koh?..kikaje kika biyewa besty kuka manta dani..is that fair?.."murmushin da bata shiryaba ta saki ganin yanda yayi da face dinshi...ta buda hannaye tace"ni babu ruwana da tsakaninku...kawai inzo in shiga anjima ku bani kunya"...murmushi shima ya saki yana kallonsu with smile yace"nayi missing dinku da gaske...sai nakeji kaman nayi tsuntsu naje Bauchi da Gombe"...murmushin suma suka kara saki Aysha tace"da gaske munyi missing dinka muma...yasu Mom da Lubna"..yace"they are all fine..amma ina zakuje ne haka?.."Aysha ta saki wani qayataccen murmushi kafin tace"wlh Baby ne yazo wai zai kaimu shopping.. muje kayi dropping namu bakin gate nasan yana can yana jiranmu"...kallonta Sa'eed yayi cikeda mamaki kafin ya juya yana kallon Billy yana neman karin bayani..ta daga kafada tana dan smiling dan ta gane me yake nufi tace"ai soyayya ya dade dayin nisa...bakaji har baby ma ake cemishi ba?.."Yace"shine nima nake mamaki ai..but when did this happened banida labari?.."tace"gaka ga bestynka ai"...juyawa yayi ya kalleta kafin yayi mgn tace"besty mu shiga mota idan mun tafi zanyi maka bayani"...baiyi mata musu ba ya bude motar suka shiga..yana gama warming dinta yayi reverse suka dauki hanyan fita hostel din...basuyi nisa ba yace mata"umhum ina sauraronki"...a nuste ta bashi labarin duk yanda sukayi dashi...saida ta gama yace"amma kina ganin ba matsala besty?..i mean kin tabbata mutumin kirki ne shi?.."da sauri tace"sosai mutumim kirki ne wlh besty...ask Billy ta fada maka tunda muke dashi bai ta6a min wani abu da bai kamata ba..he really is a gentle man"..gyada kai Sa'eed yayi yace"to Allah yasa..but still ya kamata muyi bincike a kanshi..i don't want you dating a wrong guy kar azo a samu matsala"..murmushin jin dadi ta saki kafin tace"i trust you completely my besty...kayi duk binciken da kaga ya kamata"...dan juyawa yayi ya kalleta sai ya saki murmushi yace"za'ayi min dadin baki a cuceni"...tana daria tace"ba wani dadin fa..it's the truth"..sake gyada kai yayi baice komai ba...Billy dama tana back seat tana chatting dinta so ko sauraronsu batayi...suna fitowa main gate suka hango motarshi parke daga gefe..saida ya karasa har kusada motan nashi snn yayi parking...suka bude mota suka fita shima ya fito daga cikin nashi motan...Sa'eed ya karasa ya bashi hannu suka gaisa kafin yace"Hope dai za'a bani aronsu for just an hour?.."yana murmushi yace"of course..Allah ya kiyaye hanya"..Prof ya amsa da"Ameen"snn sukayi sallama Sa’eed ya shiga motanshi ya wuce suma suka shiga na Prof suka wuce.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
16
Shopping sosai Prof ya shiga yi musu Aysha tun tana cewa ya kyaleshi haka har ta hakura kawai ta zuba mishi ido...ta lura ba karamin money spender bane shi..baijin kashe kudi sam..yanda yake musu siyayya ko shekara guda zasuyi a school sai haka...Billy dama batayi mgn ba kallonshi kawai take...saida ya dauki duk wani abu da students kamar su suke bukata snn ya wuce counter...bayan yayi payment akai musu packaging wani messenger ya dauki kayan yabisu dashi mota...ya zubasu nan cikin booth suma suka shiga suka wuce...a hankali Aysha ta juya tana kallonshi tace"Babyy.."ya dora hannu kan lips dinshi yace"shushsh ba sai kince komai ba pls"...shirun tayi bata sake mgn ba kaman yanda ya bukata...saida ya tsaya Pizza Hut yayi musu takeaway snn suka wuce Hostel...a bakin gate dinsu yayi parking Billy ta bude mota ta fita bayan ta mishi godia...Aysha kuma sake juyawa tayi tana kallonshi da cutest eyes dinta cikin shagwa6an da yake mutuwar so tace"Baby u shouldn't have done this...i told u munada komai da komai fa"...kallonta yayi for like 5 mins kafin ya dauke kanshi yana sakin murmushi...this girl is damn cute..bai ta6a ganin wanda shagwa6a yakema kyau kaman ita ba..she is just different..sake turo baki tayi hadda bubbuga legs dinta a kasa tace"Baby manaa"...daria ya saki sosai har jikinshi na dan jijjigawa yana daga hannu yace"ohk am sorry...amma ke din ce bakiji baby girl...idan har am important to u zakiyi accepting kayan nan and azaki sake kokarin hanani siyan maki wani abu ba"...turo baki tayi tana kallonshi kaman zatasa kuka...kallonta kawai yake yanajin kamar yakai hannu yaja dan bakin da take turo mishi...tace"shikenan nima daga yanxu duk abunda na gani na siyan maka sai kayi accepting ka yadda?.."gyada kanshi yayi yace"na yadda"..nan da nan ta saki murmushi har dimples dinta suka lotsa...sun dan ta6a hira kadan kafin yayi mata sallama ya wuce ita kuma ta kwashi kayan da suka siyo ta shiga ciki...bata samu Billy a dakinsu ba dan haka tana ajiye kayan ta fita zuwa room 2b da ta jiyo hayaniyarsu a can...tana shiga wata daga cikinsu mai suna Rahma tace"yauwa ga Lamidon nan ma tazo"...karasawa tayi ciki ta zauna tana kallonsu tace"meya faru ake neman Lamido?.."Rahma ta sakw cewa"mgnr bikin Aneesa ne wlh...kinsan munyi mata alqawarin zamuyi selecting music mai dankaren dadi muyi training sbd muyi performing ranar dinner dinta?.."gyada kai Aysha ta shigayi tace"inaga shine dalilin da yasa take nemana...ko daxu naga missed calls dinta ina tareda Baby"...Rahma tace"yauwa to shine mukeso ki za6o mana latest music mai dadi snn ki koya mana rawan da zamuyi tunda dai kaf Hostel din nan ba wanda ta iya wani rawan kirki idan bake ba"...dan murmushi Aysha ta saki kafin tace"to ku da kuketa wnn lissafin Aneesan tace muku 'yan class dinsu baza suyi bane?..kunsan fa 'yan Nursing din nan da shegen iyayi"...wnn karon Billy ce tace"yo Lamido kamar bakisan 'yan class din nasu bane?..babu abinda zasu iya wlh shiyasa itama Aneesan ta nememu kuma bai kamata mu watsa mata qasa a ido ba...dukda ba department dinmu daya ba year dinmu daya and tanada kyakyawan relationship damu sbd haka ba wanda ya kamata ya fitar da ita kunya idan ba mu din ba..koya kukace Midwives?.."da sauri suka hada baki suna fadin"Zancenki dutse hajia Bilisu"..sauke ajiyar zuciya Aysha tayi tace"shikenan sai mu fara this weekend...amma wane time kuke ganin zamuyi selecting evening ko night"...Rahma tace"kam night ai sai yafi sugar Lamido..yanda zamusha sha'aninmu babu wani takura"...gaba daya sukayi na'am da wnn shawara dan haka suka tsaida mgn kan zasu ringa dance training dinsu every Saturday and sunday around karfe 8 na dare.
Tun daga wnn rana suka fara training dinsu kaman yanda suka tsara...every weekend suke taruwa suyi abunsu ba wanda ya sani...a haka suka cinye satin farko na clinical posting dinsu suka cinye na biyu...a cikin sati na uku ne za'ayi bikin and sun gama training dinsu tsaf daidai da anko duk cikinsu ba wadda batayi ba...duk tsawon wnn lokacin Aysha bata sake haduwa da Dr.Bobby ba a Hospital kuma yana shiga ward dinsu Allah ne kawai baisa sun sake haduwa ba shiyasa take cewa Allah ya amsa addu'anta dan koshi yasan yanda ta tsani ganinshi shiyasa suke samun sa6ani dashi.
Yau Saturday za'ayi dinner Aneesa gashi evening duty take kuma ta rasa wadda zata kar6an mata aikin zuwa gobe...jiyama Allah ne ya taimaketa wata daga cikin staff din dakin ta kar6i evening din tayi mata ita kuma tayi mata morning sbd event din jiya kamu ne so tana tashi daga Hospital din ta koma Hostel suka shirya suka tafi...event din yau kuma na dare ne gashi bata san wanda zai rike mata aikin ba...tun daxun take zaune gefen gadonta tana daure da towel sai tufka da warwara takeyi...tsoro takeji kar ta tafi biki wani matsala ya faru ayi blaming dinta...sai wata zuciyar tace mata tayi tafiyarta kawai ai bai zama lallai ita kadai take evening ba so dayar zata rike dakin...da wnn shawara na zuciyarta ta yanke hukuncin zuwa bikinta kawai dan Allah ya gani bazata iya hakura da zuwa dinner nan ba...yanda sukayi training idan bataje ta baje kolin rawan nan ba matsala za'a samu ta sani...Billy data fito daga wanka ta kalleta ganin tayi nisa cikin tunani tace"to ya muke ciki ne Lamido?..kin samu mai rike miki aikin?.."sauke ajiyar zuciya tayi a hankali tace"ashe bani kadai zanyi evening din bama..da akwai wata staff kuma nasan bazaki zuwa ba"...Billy da har ta fara shiryawa tace"har naji dadi wlh dan Allah ya sani idan bakije bikin nan ba bazamu ji dadinshi ba muma...yanxu ki karasa shiryawa kisa kayanki nasan wnn dan rainin wayon bestyn naki ya kusa zuwa...kuma dai kinsan make up da zuwa da wuri mukayi ba
Book Chapters
Chapter 12
Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59