You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
lokacin nasan akwai dalili..meke tafe dakai?.."kai tsaye daddy yace"akan batun auren yaran nan ne..kayi hakuri ba nufina inyi jayayya dakai ba amma wata mgn Alhaji Lukman Waziri yazomun da ita jiya wanda yasa nayi tunanin in sake kawota gabanka ko za'a samu maslaha"...kai Lamido ke gyadawa yace"ina sauraronka..wace mgn ce wnn?.."daddy yace"ina wnn yaro dan wajen Col Attahir marigayi?.."Lamido ya gyada kai alamar ya ganeshi..daddy yacigaba da cewa"shine wai ashe yake sonta..ya dade yana sonta fada ne baiyi ba sai yanxun..ranar da sukazo nan tareda waziri mgnr ce ta kawosu sai kuma suka ji cewa ka riga ka fidda mata miji..wnn dalilin nema yasashi rashin lafia har ya kwanta asibiti"..wani irin tsit Lamido yayi kmr baya dakin..tabbas biri yayi kama da mutum..shi kanshi yayi mamakin yanda yanayin yaron ya sauya lokaci guda..tausayinshi yaji ya kamashi meyasa Waziri bai sanar dashi ba?..ga kuma shi wancan yaron Najeeb ya zaiyi dashi?..bayan dogon tunani ya dawo da dubanshi ga daddy dake zaman jiran tsammani yace"shi kuma wancan yaron Najeeb ya zamuyi dashi"..da sauri daddy yace"saida na fara tuntu6arshi kafin na kawo mgnr gareka..ya kuma tabbatar mun da cewa akwai yarinyar da yakeso"...numfashi Lamido ya sauke kafin yace"idan Allah ya kaimu dare kazo mun da iyalan naka gaba daya"..cikeda farin ciki ganin ya kusa cin nasara yace"zan kawosu in Allah ya yadda..na barka lafia"...daga haka ya mike ya sake mashi sallama snn ya tafi...koda yaje gida ya sanar da Ammi yanda sukayi dashi ita kanta ba karamin farin ciki tayi ba..sai a lokacin ya samu yayi breakfast din da bai samu yayishi ba daxu.
A can Kano kuwa tunda suka koma Bobby bai sake walwala ba...shi ba mara lafia ba kuma shi ba lafiyayye ba gashi nan ne kawai..gaba daya duniar yake ganin tayi juyin waina dashi daga farin cikin da yake ciki kafin ya santa zuwa baqin cikin da yake ciku yanxu bayan sanin nata...bakin kokarinshi yakeyi wajen ganin bai bar ciwon da yakeji ya kwantar dashi ba amma ko Allah yasan ba karamin wahala yake ciki ba..rabonshi da samun isashshen bacci har ya manta...kullum idan ba sedative yasha ba bai iya yin baccin...yana zuwa hospital dinshi kullum saidai ba wani iya aikin yakeyi ba mostly idan yaje kwanciya yake shima yaji da kanshi...Mummy tayi fadan tayi nasiha tayi magiya kan ya dena dorawa kanshi damuwa amma kwata kwata ya kasa yakice abun a cikin ranshi...kawai imagining yake wai ga Aysha an daura mata aure da wani shikam yasan da kyar idan ba wnn ce ranarshi na karshe a dunia ba...shi kadai yasan halin da yake ciki sai kuma Nur daya fadama duk abunda ya faru...Nur yaji tausayinshi matuka sbd yasan yanda ya kwallafa rai a kan Lamido..ya kuma san irin son da yake mata ba gama garin so bane..so ne wanda zaiyi wahala ta samu maiyi mata irinshi a dunia indai ba iyayenta ba...so ne wanda idan ta kuskura ya su6uce mata to ta tafka babban asaran samun masoyi kamarshi...wnn dalilin yasa kusan kullum Nur na tare dashi tunda har yanxu students basu dawo hutu ba and suna dawowa clinical posting zasu wuce..shike kwantar mashi da hankali tareda assuring nashi cewa komai zaiyi daidai...jinshi kawai yake don yasan zaiyi wahala ace an fasa auren nata.
Yau da wuri ya dawo gida sbd ciwon kai da yake fama dashi...yayi nisa cikin tunani har bai lura dasu Mummy dake zaune a parlor ba kawai ya wuce flat dinshi...gaba daya suka bishi da kallo ganin har yanxu Bobby bazai dangana ya mika komai ga Allah ba...ko Sab da zai koma school wnn karon aunty sumy ce ta maidashi madadin shi da yake maidashi koda yaushe...gaba daya Mummy itama cikin tashin hankali take don ganinshi a wnn halin ba karamin daga hankalinta yake ba...mikewa tayi zuwa dakin nashi..yana zaune kan sofa ya zabga uban tagumi da hannayenshi har ta karaso ta zauna nan kusa dashi baisani ba saida takai hannu ta dafa shoulder dinshi ya dago da sauri yana kallonta...kallonshi takeyi itama kafin tace"so duk mgnn da nake fada maka baka dauka ba knn koh?.."ya wani kwabe fuska yana kallonta yace"Mummy to me nayi?.."tace"kaki ka mika lamuranka ga Allah mana..do u think wnn damuwan daka daurama kanka shi zaiyi sorting things out?..baka yadda da ikon ubangiji ba ne?.."hannayenta ya kama ya rike yana dubanta in a calm voice yace"na yadda da ikon Allah mana kawai zuciata ta kasa daukan rasata da nake shirinyi..inama kokari Mummy Allah kadai yasan halinda nake ciki..ciwo nakeji sosai a zuciata Mummy ban san me zanyi ya dena ba"..kama hannunshi tayi tana cigaba da kallonshi tace"na fada maka ka kwantar da hankalinka jikina yana bani cewa ita din matarka ce..idan Allah ya yadda kuma kai zaka aureta ba wani ba"..kallonta kawai yakeyi kmr bai gane me take fada ba..cikeda assurance ta sake cewa"yes..ina nan ina maka addu'a and bi'iznillah Allah bazaiki amsan addu'a na ba"..dan murmushi kawai ya saki without saying anything..gani yake Mummy na son kwantar mashi da hankali ne kawai amma taya al'amura zasu canxa bayan Lamido da kanshi yace ya tsayar mata da wanda zata aura...shidai fatanshi bai wuce Allah ya cire mashi ita daga zuciyarshi ba koya samu ya huta.
Zaune suke cikin parlon Lamido gaba dayansu kmr yanda ya bukata...Ammi,daddy sai Aysha da Najeeb..gaba daya suna zaune a kasa while Lamido da tun shigowarsu ya kasa cewa uffan yana zaune a usual seat dinshi...kawai tunanin ta inda ya kamata ya fara yake..kmr bazaiyi mgn ba sai can yace"Najeeb"..a hankali Najeeb da har yanxun kanshi ke kasa ya amsa mashi...Lamido ya gyara zama before saying"tambaya nake son maka kuma inaso ka bani amsa iyakar gaskiayarka"..a hankali ya daga kai tareda fadin"InshaAllah"...Lamido yace"shin akwai wadda kakeso kafin wnn mgnr ya 6ullo?.."shiru dakin ya dauka kowa na jiran yaji amsar da zai bada...ganin yanda yayi shiru kai a duke Lamido yace"ko bakaji abunda na fada bane?.."da kyar ya bude bakinshi yace"ina dashi"..Lamido yace"a ina take?.."shiru ya sakeyi ba mgn a fusace Lamido yace"idan ina maka mgn kanamun shiru zakasa in canxa ra'ayina wlh"..tun kafin ya rufe baki yace"kayi hakuri..a nan Bauchi take"..kallonshi duk sukeyi before Lamido ya sake cewa"Bauchi a ina?..bude baki fa zakayi kayi bayani don idan ba gamsuwa nayi da yarinyar ba bazaka aureta bane"..har yanxun shidai kanshi na kasa yace"sunanta Bilkisu Ibrahim Muqaddas..tare suke makaranta da Maama"...wani irin zare ido Lamido tayi kai kace wani mugun abu ya fada..lokaci guda fuskanta ya washe da murmushi cikin tsantsan farin cikin da taji ya diro mata all of a sudden tace"Hamma are u for real?..da gaske Billyna kakeso?.."dakatawa tayi da mgnr tareda matsawa kusa dashi sosai hadda su kama hannunshi tace"bani labari Hamma yaushe ka fara sonta?..ya akayi ma kana son Billy amma ban sani ba..Hamma dan Allah ka..."bata karasa ba Lamido ya daka mata wani tsawan da batasan sanda ta koma inda take ba da sauri tana rarraba ido..sam ta manta wai a gabanshi suke..farin ciki yasa ta manta da hakan jin wai Hamma da kanshi ne yakeson Billynta..knn hakan yana nufin tun tale tale yana son Billy basu sani ba..shin Billyn tasan yana sonta ta 6oye mata kmr yanda itama bata fada mata Proprietor na sonta ba ko kuwa itama bata san yana son nata ba..duk zaman wurin sai taji ya gundureta Allah Allah take su bar wurin ta samu ta kira Billy taji ya wnn batu yake...Lamido dai maida dubanshi ga Hamman yayi yana cewa"kace mene sunanta?.."a hankali ya sake cewa"Bilkisu Muqaddas"..Lamido yace"jikar Inuwa Muqaddas ce knn?.."kai ya gyada mishi..Lamido yace"to Alhamdulillah 'yar manyan Mutane ce ai..shi Alhaji Muqaddas din was a very goon friend of mine and zan tuntu6eshi da mgnr"..da sauri yace"ai bamu gama daidaitawa da ita ba"..yace"wnn duk ba matsala bane zanyi mgn dashi dai..Allah yasa albarka"..duk suka amsa da"Ameen"..daga nan kuma ya maida hankalinshi kan Hajia Indo mai gayya mai aiki..ta sake sinne kai tamkar tana gaban surkai dukda cikin ranta murna ce fal na jin wnn labarin na Hamma da kuma warware wnn auren da Lamido keson hadawa da akayi..she's super excited kawai sai murmusawa takeyi ita kadai kmr munafuka...ganin bata ma san kallonta yakeyi ba yace"Aisha.."da sauri ta dago tana kallonshi kmr mutumiyar kwarai..kofa ya nuna mata tareda fadin"kina iya tafia"..da sauri ta mike ta kama hanya zata fita tace"Nagode Allah ya saka da alkhairi"..Lamido baice mata komai ba har ta fita snn ya dawo da dubanshi ga Hamma yace"kaima kana iya tafia duk yanda mukayi da Muqaddas din zakaji"..kai a kasa shima ya mike tareda yi masa godia ya fita...ya rage daga daddy sai Ammi a parlon..Lamido na duban Ammi yace"Maimuna kin amince da mgnr dan wajen Attahir?.."kai a kasa tace"na amince..Allah yasa haka shi yafi alkhairi"..yace"to madallah zanyi mgn da wazirin anjima..ita kuma Aisha ina sane naki fada mata sbd nasan hauka zataimn..idan kunje sai ku mata bayani"..daria sosai mgnrshi ya basu haka suka mishi sallama suka fita suna sake darian mgnr daya fada...suna fita Lamido ya dauki wayanshi ya kira Waziri suka fara mgn.
dadi sosai daddy yaji da Allah ya sauya al'amura haka?..ya tabbata Attahir zai kasance miji na gari a gareta ko don son da akace yana mata.
Aysha na fitowa daga parlon ta shiga kiran number Billy bata dauka ba..sake dialing tayi tana tafiya tana fadin"Billy pick up the call mana..pick up pls"..har ya gama ringing dinshi Billy bata dauka ba ita kuma bata gaji da jera mata missed calls ba...Hamma Najeeb daya biyo bayanta da sauri ya karasa inda take kawai sai ji tayi ya fizge wayar daga hannunta yana kallonta...juyawa tayi tana dubanshi itama sai kuma ta saki murmushi tace"Hamma dan Allah mgnr daka fadama Lamido gaske ne?..da gaske Billyna kakeso?.."harara ya watsa mata mai kyau kafin yace"ban saniba..kiranta kikayi zaki fada mata kou?.."murmushi ta Kara saki tace"of course mana..so nake inji labarin komai in detail amma batayi picking call dina ba"..ta karasa mgn tana turo baki...hannu ya kai ya dan bugi bakin nata before saying"to ban aikeki kije ki fada mata ba dan itama ba sani tayi ba..idan kika barni da kaina zanje in sanar da ita when the right time comes"..kallonshi take tana murmushi sosai tace"to bazan fada mata ba Hamma..amma dan yaushe ka fara sonta?..does she loves u too?.."girgiza kai kawai yayi yana murmushi jin wai tambaya take if tana sonshi..sai kace ba yanxu yace mata bata ma san yana son nata ba shine take mishi wnn tambayan kmr ba itane ta dauke mishi wuta sbd ance zai aureta ba.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
46
Zaune suke office din Nur tun safe ya baro nashi office din yazo ya tasa shi a gaba shi baije yayi aikinshi ba kuma shima bai barshi yayi nashi aikin ba...kawai yazo ya mishi kwance a office kaman wani mara lafia...for the fifth time Nur ya sake cewa"kaga malam if zaman office din nawa ke maka dadi tell me insan inda dare yayi mun..haka nan kazo Kamin wani kwance office sai kace mara lafia"..banza Bobby yayi dashi kmr baiji abunda yace ba..Nur ya tsaya kallonshi cikeda takaicin wnn iskancin da yake mai...murmushin iskanci ya saki tareda fadin"dont worry nasan maganinka ai..da Lamido zanje in hadaka tunda yanxu naga duk dunia ba wanda kake jin mgnrshi kmr nata"..still Bobby banza yayi dashi idanunshi lumshe sai karkada legs dinshi yake..Nur ya mike tareda tattara papers daya baza kan desk dinshi ya dauki makulli da wayanshi snn ya kama hanya fita yana cewa"to in ka gama saika rufe office din..naga kaman kwana zakayi a ciki"..sai yanxu ya bude ido yana kallon Nur dake neman barin office din yace"wai meyasa bakada mutunci ne Nur..baka ga halinda nake ciki ba da zaka dameni da surutu?.."juyawa Nur yayi yana kada kanshi yace"nine ma Lamido da naki accepting soyayyarka zakazo har office dina ka faramun hayaniya..na tabbata ko ita da tayi turning dinka down bakayi mata irin wnn wulakancin ba sai ni daka gama rainama wayo..don't worry nasan maganinka"..dafe head dinshi yayi yanajin yanda wnn iskancin na Nur ke neman kara mashi tension kan wanda already yake ciki..wayanshi ne ya fara ringing ya dauka da sauri ganin Mummy ce yayi picking tareda kaiwa ears dinshi before yace"Mummy"..a daya 6angaren full of excitement Mummy tace"Bobby guess what?.."dan shiru yayi kmr me tunani kafin yace"Mummy kinsan am not a good guesser kawai ki fadamin"..murmushi ta kara saki before tace wani abu another kira ya sake shigowa wayanshi..dubawa yayi sai yaga Waziri dan haka da sauri yace"Mummy hang on for a minute plss..Waziri ke kira"..Mummy bata ce komai ba tayi hanging call dinta shi kuma yayi picking na waziri tareda fadin"Baffa barka da rana"...Nur da yaji ya ambaci waziri yayi saurin komawa cikin office din ya zauna nan kusa dashi ya tattara duk attension dinshi a kanshi yana son yaji me wazirin zaice?..cikeda farin ciki shima wazirin yace"barka dai Attahiru ya jiki ka?.."yace"na samu sauki"..waziri yace"to Alhamdulillahi haka akeso..Allah ya kara lafia"..Bobby ya amsa da"Ameen"..suka yi shiru na dan lokacin kafin waziri yace"wani albishir ne zanyi maka mai dadi wane tukuici zaka bani?.."dan murmushi Bobby ya saki jin abunda ya fada..to wane albishir ne wnn?..shifa gani yake a halin nan da yake ciki matukar ba cewa za'ayi an bashi auren Lamido ba ba wani albishir da za'ayi ya faranta mashi rai..kawai gani yake ba wani albishir ne da zai sashi farin ciki ba amma dukda haka bai gwale Kakanshi ba yace"duk abunda kakeso Baffah"..waziri yace"to an baka auren Aisha...yanxun nan muka yi Waya da Lamido yake sanar dani yanda akayi"...wani irin diff Bobby yayi kaman baiji abunda yace ba...meyasa waziri zaiyi playing mashi such an expensive joke?..why zaiyi wasa da zuciarshi akan lamari irin wnn..duk sai yaji ranshi ya 6aci yama rasa abunda zaice...jin yanda yayi shiru waziri yace"ko bakaji abunda na fada bane?.."a hankali ya kakalo murmushi tareda fadin"nasan da wasa kake Baffah"..da sauri Waziri yace"na ta6a maka wasa da irin wnn mgnr dama?.."shiru ya sake yi yana tunani lokacin daya wani bright smile yazo kan fuskanshi yana cewa"da..Allah da gaske kake Baffah?.."cikeda assurance Lamido ya sake fadin"da gaske nake wlh..yanxun Lamidon ya kirani muka yi mgn"...lumshe ido Bobby yayi ya bude yana jin wani irin sanyin dadi na cika zuciyarshi kawai sai ya shiga karanta duk abunda yazo bakinshi kmr wanda ya zauce...addu'a kawai yakeyi ba tareda ya bude ido ba kuma ba tareda ya ajiye wayan dake makale kunnenshi ba..banda murmushi ba abunda yake saki sai kuma bakinshi dake motsawa a hankali sbd addu'a da yake...Nur dake zaune yana kallonshi wnn smile da yake saki kadai ya isa ya fahimci dalilin hakan...lokacin daya ya bude idon nashi sbd mgnr waziri da yaji ya mike tsaye yana shafa gashin kanshi still bai dena murmushi ba yace " yanxu Baffa u mean ni zan aureta knn?..i can't believe this?.."murmushi waziri ya kara saki before saying"kai zaka aureta insha Allah sbd haka rashin lafia ya kare"..murmushi kawai yake saki yana gyada kai yama kasa bude baki yayi mgn...kawai mamakin yanda al'amari ya canxa yake..is this really happening ko kuma day dreaming yake?..a hankali ya zauna kan sofa dake nan kusa dashi bayan sunyi sallama da waziri ya sake lumshe ido yayi relaxing kan sofa din murya can kasa yace"i can't believe this?..Allah kasa ba mafarki nake ba"..Nur dake zaune yana kallonshi tasowa yayi daga inda yake ya karaso nan kusa dashi ya zauna yana dubanshi da murmushi shima yace"ba mafarki kake ba Dr Bobby..it's reality..Lamido dai ta kusa ta zama matarka congratulations to u"..tun kafin ya rufe baki Bobby yayi mishi wani runguma cikin excitement yace"i still can't believe this Nur..Anya ba mafarki nakeba?.."Nur yace"i told u ba mafarki kake ba da gaske ne..Allah ne ya amsa addu'anka"..dagowa yayi yana kallonshi har yanxu bakinshi kaman go at auduga yace"Allah Alhamdulillah..Alhamdulillah Rabbi am forever grateful"..yana gama fadan haka kuma ya mike tareda zura wayanshi a aljihunshi yace"lets get going I need to talk to Mummy about this"..Nur baice komai ya mike bayan ya day car key dinshi suka fita daga office din...Motan Nur suka shiga don dama da ita suka zo..kai tsaye ya kama hanyan gidansu kmr yanda Bobby yace..ko a hanya Bobby bai dena hamdala ba..kawai gani yake Allah yana matukar sonshi daya canxa mgnr aurenta a lokacin da ya gama giving up..gaskia ne da masu iya mgn suka ce duk wani tsananin yana tareda sauki kmr yanda duk mai hakuri yana tareda nasara...shidai yayi hakuri ya kuma fawwala Allah lamuranshi dai gashi ya kawo mashi canji a lokacin da bai ta6a tsammani ba..Lallai Allah abun godia...har suka isa gidansu bai dena godia wa wnn ni'ima ta ubangiji ba..gani yake an gama mashi komai a dunia saidai kuma yayi fatan gama wa lafia...ko parking Nur bai gama ba ya bude motar da sauri ya fita zuwa cikin gidan...Nur ya bishi da kallo yana girgiza kai yace"wa yaga ba sabon ba"..karasawa yayi ya gyara parking dinshi snn ya bude motar shima ya fita zuwa ciki...yana shiga yaci Karo da Mummy dake kokarin Shiga parlonta kawai sai ya rungumota ta baya yana cewa"Mummy I can't believe this..waziri yace wai ni zan aureta yanxu..am super excited Mummy Allah yasa ba mafarki nake ba"..juyawa Mummy tayi ta dagoshi daga jikinta tana kallonshi da murmushi a fuskanta itama tace"ba mafarki bane..duk wani da kaji a gaske yake faruwa ba mafarki ba..dama ba nace maka jikina na bani kai zaka aureta ba?.."da sauri ya shiga gyada kai kafin ya lumshe idanunshi ya sake rungume Mummy yace"Mummy nagode sosai..nagode da addu'arki gareni Allah ya saka da aljannah"...hannunshi Mummy ta kama suka karasa parlorn suka zauna tana dubanshi tace"Ameen..kaima Allah ya maka albarka..waziri yace mun gobe zasuje su samu Lamido tareda uncles dinka akan mgnr auren naku"..sake rungumeta Bobby yayi yama kasa cewa komai...Nur dake tsaye tun daxun yana kallonsu sai yanxu Mummy ta lura dashi tace"Nuru karaso ciki mana"..yana murmushi ya karasa cikin parlorn ya zauna yana gaishe da Mummy...kmr wanda ya tunada wani abu sukaga ya mike da sauri ya kama hanyar flat dinshi duk suka bishi da kallo suna daria..daidai lokacin Aunty Sumy ta shigo wayanta rike a hannunta tace"yanxun muka gama mgn da Aunty Munubiya tace tana nan zuwa gobe inshaAllah"..Mummy tace"to Allah kawota lafia".
Yana Shiga parlonshi ya zauna kan three seater tareda dialing number ta yana lumshe ido..har ya gama ringing bata dauka ba ya sake kira still no answer kawai sai ya ajiye wayar tareda mikewa ya shiga bedroom direct ya fada bathroom ya daura alwala ya fito ya shimfida carpet ya tayar da sallah don ya nuna godia wa ubangijinshi for such a blessing da yayi mashi na bashi auren Lamido...har azumi ya kamata yayi don nuna godiyarshi wa Allah...har dare ya tsala bai dena Kiran wayanta ba ita kuma bata dauka ba..ganin ba daga wa zatayi ba yayi sending mata"thank u..thanks for accepting me..I love you"..daga haka ya jiye wayar ya lumshe ido yana tuna duk moments da yayi spending da ita..kaman yayi tsuntsu yakai kanshi Gombe haka yakeji amma ba zaiyi wnn rashin kunyan ba matukar ba cewa akayi yazo ba..afterall saura baifi 4 days suyi resuming school ba so zai na samun daman ganinta duk time din da yaso..he prays Allah ya shirya mashi ita yasa bazata na aikata abubuwanda dole zaisa yayi mata masifa ba.
Gombe..
Tunda Lamido ta samu labarin yanda reshe ya juye da mujiya sai abun yazo mata a bazata sosai..wani irin sanyi taji jikinta yayi zuwa yanxun for sure tasan she does not hate him amma ya zatayi da Prof ne kam?..ba wai aurenta da Bobby ke 6ata mata rai ba..kawai yanda baby zai dauka kaman dama can yaudaranshi take shiyasa ta hanashi zuwa ga parents dinta da wuri..and shi kanshi proprietor nan ba sabawa tayi dashi ba..ita bata San ma ta ina zata fara zama da wnn mutumin as her hubby ba..tasan yana sonta da gaske amma har ga Allah itadai gani take kmr bayan auren zai sake rikidewa ya dawo asalin proprietor data sani a baya..gaba daya ranar yini tayi a daki tana faman kunchi ko abinci bataci ba kuma ba wanda yace mata don me...conference video call ta hada musu itada Billy da besty tana tuttura baki ta fada masu duk abunda ke faruwa ga mamakinta sai taga gaba daya sunyi farin ciki da mgnr don har lissafin biki suka fara kawai ta kashe wayarta tana huci..ita fa har yanxu bata ga ta inda ita da proprietor za’ace suyi aure ba..to ta inama za’a fara?..kawai gani take kmr abun ba mai yiwuwa bane..gashi tun jiya take kiran wayan Prof a kashe har zuwa yanxu kama a kashen yake ta rasa dalilinda yasashi kashe waya..so take ta sanar dashi an samu turn of events ya gwada turowa wai ko Lamido zai sauraresu amma bata samun wayan nashi..duk tabi ta zama wata iri ita ba mai lafia ba kuma ba mara lafia ba..tana gani tun daxun yake kiran wayanta taki dauka don batasan abunda zai fada mata ba kmr yanda itama batasan abunda zata fada mashi ba...kunayanshi ma taji tanaji wlh..tana nan kwance a daki har dare daddy ya turo Yusra ta kirata..ba musu ta mike tareda maida hulan kanta ta nufi parlon nashi..suna zaune tareda Ammi ta karasa ciki a nutse ta zauna a kasa..daddy yace"nasan kin samu labarin abunda ke faruwa wajen Amminki koh?.."ta daga kai alamar ta sani..daddy yacigaba"to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi mana biyayya a wnn auren..a yanda yaron ke sonki nasan kema bazaiyi taking naki long time kafin ki fara sonshi ba..kuma ban yadda ki mashi wani rashin kirki ba Aisha..inaso ki girmamashi kmr yanda kikeyi a baya snn kar in sakeji ance kin hadu da wnn mutumin ko waya ban amince kiyi dashi ba..idan Allah ya kaimu gobe zasuzo a tsaida ranar aurenku..Allah yasa haka shine alkhairi a tare daku Allah kuma ya maku albarka baki daya"..a hankali ta gyada kai idonta a kasa..saida ta tabbata ya gama snn tace"daddy dan Allah ina son zuwa Bauchi gidan aunty fiddausi"..daddy yace"ba wnn sunday zakuyi resuming school ba?.."a hankali tace"eh amma kafin sunday din zan dawo..ko kuma a daukemu daga can tareda Billy kawai mu wuce"..shiru daddy yayi kmr bazaiyi mgn ba sai can yace mata"shknn saiki shirya gobe da safe a kaiki..Allah maki albarka"..ta amsa da"Ameen daddy"..snn ta mike ta fita daga parlon..Ammi ta bita da kallo bayan fitar nata tace"ikon Allah..wai Aysha ce tayi wnn nustuwa haka sbd mgnr aure ya 6ullo..wonders shall never end"..ta karasa mgn tana daria yayinda daddy ke girgiza kai shima yana murmushi..shi kanshi yaga wnn canjin tattare da ita fatanshi dai Allah yasa auren nasu shine alkhairi a tareda kowannensu.
Washegari da safe ta shirya kmr yanda daddy yace driver dinsu ya dauketa zuwa Bauchi..tana zuwa gidan ta fashewa small mom dinta da kuka wai za’a mata auren dole..Aunty Fiddausi nata aikin rarrashinta tace"ni banga abun tada hankali anan ba Aysha bayan kowa ya shaida irin son da akace yana maki"..tun kafin ta rufe baki tace"Aunty inyamuri ne fa..kuma wlh bashida mutunci masifaffe ne na bugawa a jarida..shknn ni sai a hadani dashi salon yayitama mutum masifa komai fa shi abun fada ne a wurinshi"...daria aunty fiddausi ta kunshe kafin tace"to kiyi hakuri ni da kaina zanyi masa fada ya dena maki masifa gaskia..kuma shi da yake jikan waziri ta ina ya zama inyamuri kuma?.."da sauri tace"babarshi inyamura ce kuma shima yanayin inyamurancin..kawai sai in haifi ‘ya’ya a dinga koya musu igbo..wlh an cuceni"..daria sosai small mom dinta ke mata don ita bataga abun daga hankali a nan ba...idan ta fahimceta ba ma rashin auren wancan saurayin ne damuwarta ba kawai damuwarta an hadata dashi kuma wai masifaffe ne..ta lura iskanci ne kawai yasa take wnn abun amma ba kiyayya ba don bisa ga dukkan alamu itama tana sonshi kilan ganewa ne kawai batayi ba.
Sha biyu da wani abu tayi sallama da aunty fiddausi ta wuce gidansu Billy..ta iske Ummansu a parlor tareda sauran siblings din Billy maza..ta karasa ciki a hankali kaman wata mara lafia ta shiga gaisawa da Umma..Umma dake dubanta with smile tace"ashe kuma proprietor dinku zaki aura?..dazu Bilkisu ke fadamun..to Allah ya sanya alkhairi ya nuna mana lokacin Aysha Allah yasa albarka"...juyawa tayi tana kallon Billy kmr zata fashe da
Book Chapters
Chapter 38
Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59