You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
bayi yayi wanka snn ya fito ya shirya kanshi cikin wata armless shirt da wando three qtr snn ya nufi parlor...parlon Mummy ya samesu zaune gaba daya as aunty sumy na gida itama ranan bataje aiki ba Miemie ma bataje sch ba sbd fever data kwana dashi ita kuma ilham tun 1 aka tashesu...karasawa yayi ciki ya zauna da igbo ya gaida Mummy itama ta amsa da igbo snn tayi adding da"yau baka fita ne naga har yanxu baka shirya ba?.."dan ta6e baki yayi yace"i just don’t feel like going out..i think zamana zanyi a gida in huta"...Aunty Sumy tace"aikam bai kamata kaki zuwa ba Bobby..remember it’s a Festival week and abune wanda yake taking place once in a year sai nakega kaman bai dace kaki zuwa ba ko don sbd guests dinku"...Mummy ma na gyada kai tace"sumayya gaskia ta fada Bobby"..shiru yayi cikin ranshi yana ayyana bazaku gane bane...abun kaman hadin baki kawai sukaji sallamr Nur a parlon...Bobby ya kulle ido tareda fadin"the fool is here..nasan yanxu ko banida intention din fita saina fita ko don nacinshi"...daria Mummy sa aunty sumy suka saka jin abunda yace...Nur daya karaso ciki ya zauna ya shiga gaisawa dasu Mummy shima cikin igbo...aunty sumy tace"wlh har mantawa nake Nur yanajin igbo sbd bai cikayi ba unlike abokinshi da mgn daya biyu sai ansa igbo a ciki"...murmushi Nur yayi yana shafa kanshi yace"wlh ni kaina ina manta inajin yaren aunty...gaba daya hausawa sun janyeni"...daria suka sake yi Mummy tana ai dole hausawa su janyeshi tunda yake zaune a kano...bayan sun gama Nur ya juya yana kallon Bobby kafin yayi mgn Bobbyn ya mike yana cewa"ba saika 6ata bakinka ba nasan meya kawoka..ka bani just 5 mins zan shirya in fito"...daria gaba daya suka kara sawa Bobby ya wuce flat dinshi...aunty sumy tace"Nuru kai kadaine maganin Bobby gashi tun kafin kayi mgn an tafi shiryawa"...dariyan shima yasaka yace"kinsanshi baya son naci ai..ni kuma indai inason yayi abu bana barinshi har saina samu abunda nakeso"...bayan 5 mins ya fito a shirye kaman yanda ya fada...Nur na ganinshi ya mike yana sallama dasu Mummy Ilham tace"uncle bobby inaso inje plss"..kallonta bobby yayi sai kuma yace"no kiyi hakuri sai gobe kuje tareda su aunty kinji"..makale shoulder dinta tayi tana fadin"oh oh inaso inje yau"...kallonta kawai yakeyi totally speechless..shi ba son zuwan nan nasu yakeba wlh..ko gobe da aunty sumy tace zasuje suji lecture da za’ayi ba so yakeyi ba...Nur da yaga tana shirin sakin musu kuka yace"zamuje dake baby don’t cry"...nan da nan ta washe bakinta tana tsallen murna..."uncle Nur"..yaji Miemie ta kira sunanshi...a hankali ta juya yana kallonta sai yaga tayi narai narai tana kallonshi...murmushi ya saki dan ya gane mgn take mishi a haka..so take taje itama and tana tsoron furtawa sbd Oga Bobby kada ya hana...saida ya dan saci kallon Bobbyn snn ya dubeta yace"kema zakije kou?.."daga mishi kai tayi da sauri..yace"to je dauko mayafinki"..da sauri ta mike zuwa dakinta ta dakko veil da phone dinta ta fito...Bobby da haushi ya isheshi ya bude baki zai fara masifa Mummy tace"don’t say anything plss..kuje dasu su gani ai ba dadewa zaayi ba"..gum ya maida bakin nashi ya tsuke ba tareda ya fadi abunda yayi niyya ba...sallama sukayi musu suka fita Bobby ya shiga motanshi tareda driver da kuma ilham shi kuma Nur ya dauki Miemie a nashi motan suka tafi.
Tsaye take gaban mirror dinsu tanata kallon kanta kaman bata ta6a ganin mirror ba...straight gown ce a jikinta na wani lace mai kyau..dinkin yabi jikinta ya kwanta luf luf hakan kuma ya baiyanar da beautiful figure dinta...daurin dankwalinta Zara Buhari as usual gashinta ya leko ta karkashin daurin..gaba daya ranta ba dadi duk ma tasan ba jin dadin yau din zatayi ba sbd Bobby..duk ta tuna kashedin da yayi mata jiya na idan tayi wani abu zai hadata da daddy sai taji kaman tasa kuka wlh...yanxu haka yakeso taje tayi zaune a wurin tayita kallonsu knn ita bazatayi rawa ba...da yasan yanda take kaunar rawa da baiyi mata haka ba wlh..kawai rawan yakema bala’i jiya kaman zuwa tayi club ta kwana...Billy ta shigo dakin tana sanye cikin kayanta irin na Aysha sak har dinki da daurin dankwalinsu iri daya...batace mata komai ba ta karasa cikin dakin ta dauko veils dinsu da suke zube kan bed dinta ta hada da wayoyinsu snn taja hannun Aysha suka fita daga dakin...binta kawai takeyi har suka isa compound snn ta saketa ta mika mata veil da wayanta ba musu ta kar6a ta yafa itama Billy ta yafa nata snn tace"nasan in muka daka ta taki zamu iya kwana nan ciki baki gama kallon madubi ba..na fada maki idan kika kiyaye babu abunda ya isa ya maki amma har yanxun kinki kwantar da hankalinki”..juyawa Aysha tayi tana kallonta kaman zatasa kuka tace"yandu fisabilillahi saidai inje inyi zaune kaman gunki ni bazanyi abun arziki ba?..ai wnn rashin imani ne wlh"..ta karasa mgn hawaye na cikowa idonta...daria yaso kufcewa Billy amma ta gimtse suka fita daga wurin...inda Sa’eed ke tsaye suka nufa kafin su karaso ya bude musu mota Aysha ta shiga gaba Billy kuma baya snn shima ya shiga ya tayar da motar suka tafi...a hanya ya dubi bestyn tashi yaga fuskan nan cunkus sai ya kallo Billy ta mirror yace"waya ta6amin besty ta?.."daria Billy ta saki tace"akan mgnr jiya nefa"..dan murmushi shima ya saki yana kokarin controlling dariarshi yace"besty har yanxu mgnr rawan ne dai?.."a fusace ta juya tana kallonshi tace"malam ba ruwanka dani tunda biyewa Billy kake kunamin daria...kawai sai inje inyi zaune ni bazanyi rawa ba sbd rashin imani"...ta karasa mgn hawaye na sake ciko eyes dinta...wnn karon kasa 6oye dariar sukayi dan dagashi har Billyn basu san sanda ta fito ba...daria sukeyi sosai sai kace ta6a66u Aysha kuma ta shaqa iya shaqa kawai sai ta rufe fuska da hands dinta ta wani rushe da matsanancin kuka...ganin kukanda take sai darian ya sake zuwa musu aikam sukaita yinshi knr sabbin kamu saida sukayi me isarsu snn suka bari...Sa’eed ya dan juya yana kallonta with a little smile yace"besty dan Allah kiyi hakuri kinji..nifa bake nakewa daria ba"...yana rufe baki Billy ma tace"nima na ranste ba dake nake ba dan Allah ki bar kuka"...ai kaman ma sunce tacigaba don kara sautin kukan tayi hadda su buga kafafu a kasa ba shiri Sa’eed ya gangara gefen titi yayi parking...juyawa yayi yana kallonta ya wani marairaice yace"yanxu besty dan girman Allah bazakiyi shiru ba?..nace fa am sorry kuma da gaske ni ba dake nake ba"...banza tayi dashi tana cigaba da kukanta...yana mata ciwo idan ta tuna saidai kawai taje wurin a matsayin hoto bazatayi rawa ba...gashi ance hadda favorite mawaqinta aka dauko Ado Gwanja kuma ace bazatayi rawa ba ai wlh an cuceta...wayanta dake ajiye kan dashboard ne ya fara ringing Sa’eed yakai hannu ya dauka ganin yanda tayi banza da wayan...Baby boo ya gani kan screen din dan haka ya juya screen din yana nunawa Billy..da sauri tace"yauwa dauka kace masa yazo ya rarrashi kayarshi tunda mu taki ta sauraremu"...ba musu Sa’eed yayi sliding tareda sawa a speaker...on the other side Prof Ahmad yace"my baby girl"...hada ido Sa’eed sukayi da Billy suna kunshe daria kafin ya maze yana cewa"ahm ba ita bace sunana Sa’eed"...Prof yace"ai besty zaka cemin yanda zanfi ganewa"...Sa’eed ya kara sakin murmushi before yayi adding"besty ce dama tun daxu take kuka wlh kuma munyi iya bakin kokarinmu taki tayi shiru"...hankalinshi har ya fara tashi yace"wait voice dinta ne nakeji tana kuka yanxu?.."da sauri Sa’eed yace"itace wlh...mun rasa yanda zamuyi da ita"...Prof yace"bata waya muyi mgn"...ba musu Sa’eed ya ajiye wayan kan laps dinta...voice dinshi taji yana fadin"hello baby girl"...dan dakatar da kukan tayi tana goge tears dinta tace"umhum"..yace"why are u crying baby girl..waya ta6amin ke?.."saida ta sake goge tawagar hawaye da suka biyo fuskarta tace"ba komai"...yace"no ban yadda ba baby kodai inzo ne?.."girgiza kai tayi tace"aah.."yace"then promise me u will stop crying inba haka ba kuma am coming"...a hankali tace"I promise"...yace"yauwa my little baby girl i love u kinji?..and zanzo da daddare sakin fadamin wanda yasa babyna kuka"...kai take gyadawa kaman yana ganinta kafin tace"toh.."yace"ohk bye"...itama tace"bye.."snn ta ajiye wayar...Billy da Sa’eed hanci da baki suka saki suna kallon ikon Allah ganin har ta dea kukan kaman ba itane suke roki ta dena ba amma taki...bata kalli kowadaga cikinsu ba ta maida kanta jikin window...suma basuce mata komai ba as suna tsoron su sake mgn ta kuma langabe musu Sa’eed ya koma seat dinshi ya zauna snn tada motar suka karasa cikin makarantan.
Wucewa sukazo yi ta daidai inda suke tsaye da alama wani suke jira...Bobby rikeda hannun Ilham Miemie kuma na tsaye kusada Nur don ko kadan batason hada ido da Bobby data tabbatar haushinta yakeji for following them...Bilkisu da Sa’eed ne suka fara tahowa suna zuwa inda suke gaishesu snn suka wuce ita kuma tana baya dan cewa tayi bazata jera dasu ba...ganinshi tsaye a wurin ta sake dinke fuskanta tsaf tana cigaba da tafiya kaman batasan suna wajen ba...kafin ta wuce Nur ya kira sunanta"Lamido"...a hankali ta juya tana kallonshi with a little smile kan face dinta tace"Sir good afternoon"..yace"afternoon ya gajia"...murmushi kawai tayi batace komai ba...Miemie da a kallon farko taji ta burgeta sbd kyanta itama ta gaisheta..Aysha ta amsa ta murmushi tana mamkin inda provost ya samo yarinyar me kyau haka...so tayi ta wuce batareda ta gaishe da Bobby ba amma sai taga bai dace ba kuma yana iya hadata da daddy dan haka ta dan juya tana kallonshi a kaikaice fuskan nan ba fus tace"ina yini"...ko kallon inda take baiyi ba balle ya amsa mata...ita kuma jin yayi shiru ta daga ido sai taga wayanshi ma yake dannawa aikuwa ta daddage ta murguda masa baki sai kuma karaf a idanunshi...idanunta na sauka cikin nashi tayi kasa da nata da sauri...kallonta yayi for like 2 minutes snn ya dauke kai...ita kuma juyawa tayi zata tafi Ilham da har yanxu ke rikeda hannunshi tace"Ehihie Oma"...juyawa Bobby yayi yana kallonta da mamaki jin tayi mata igbo..kafin yayi mgn Aysha data juyo itama tana kallonta with smile tace"hey I don’t understand igbo...how are u"..ilham ta saki murmushi tace"am fine"...Aysha ta gyada kai dan yarinyar sosai ta burgeta sai ta ganta kaman Yusra don itama akwai surutu...tace"ya sunanki?.."da sauri ilham tace"sunana Nadia amma ilham ake cemin..mamana kuma sunanta Sumayya muna cemata aunty...wancan kuma sunan..."bata karasa ba Bobby ya toshe mata baki yana hararanta yace"and who asked u all these?.."turo baki tayi tace"Uncle Bobby let me finishi plss"...bai bari ta sake mgn ba ya kama hannunta suka bar wajen...Aysha ta bisu da kallo tana hararan bayanshi kaman idanun zasu fado...tsaki taja tacigaba da tafia itama...tana shiga inda hall din yake kafin ta karasa Bobby dake tsaye yana jiran shigowanta yace"come here"...juyawa tayi a tsorace tana kallonshi don batasan da mutum ba a wurin...ya wani hade rai yace"bazaki zoba?.."turo baki tayi ta wuce inda yake...tana karasawa ta rungume hanu tana ciccin magani and hakan bai dameshi ba ya nuna gashinta dake a waje fuska babu alamun wasa yace"maida wnn gashin da kika fito dashi"...dagowa tayi ta kalleshi hawaye har sun ciko idonta sbd haushi...har yanxu idan ta tuna batada daman yin rawa a wurin nan sai taji kaman ta shakeshi ya mutu...ganin yana mata wnn kallon da bata so takai hannu ta tura gashin nata ciki...ya bita da wani irin kallon kafin yace"now leave"...ba misu ta juya ta tafi daga wurin hawayen dake cikin idonta na gangarowa kasa...shima ya kama hannun ilham zasu shiga saiga Miemie da Nur sun shigo...Nur ya kalleshi da mamaki yace"wai dama baka shiga ba?..meka tsaya yi a nan toh?.."banza yayi dashi yaja ilham suka shiga ciki...shima shiga cikin sukayi yana mamakin abunda ya tsaidashi a waje bayan tun daxu ya shigo.
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
23
Suna nan zaune daya daga cikin mawaqan da sukazo ya fara performance dinshi...hajia Aysha na zaune tana kallo kaman tayi kuka...yana kammalawa favorite din nata ya shigo tareda ganguna da ‘yan rawarshi aikuwa gaba daya hall din ya rude da sowa da tafi...kaman yasan halinda take ciki saida ya samo favorite dinta a cikin waqoqinshi nashi ma snn akayi playing ya fara miming...nan take hall din ya sake rudewa da muryan mata duk suna bin waqar wasu kuma suna zuwa suna mishi liki...itadai tana daga gaba gaba tana kallonsu tanajin ciwon da bata isa ko dan liki taje tayi ba...tana kallon su Billy sukaje sukayi liki snn suka dan taka rawa suka fito...hawaye taji suna ciko mata ido kawai saita rufe fuska da hannayenta tana kokarin mayar da hawayen...Bobby da tun daxun hankalinshi ke kanta daga inda yake yana ganin yanda ta rufe fuska fuska ya wani ta6e baki cikin ranshi yace"ko kukan jini zakiyi bazakiyi rawa a wurin nan ba wlh"...ita kuwa bata ma san yanayi ba saida ta gama goge tears din snn ta bude fuska...daga karshe ma mikewa tayi ta fita a wurin don bataga amfanin zamanta ba...duk akan idon Bobby da kona one second bai dauke idonshi kanta ba sbd yasan tsaf zata iya fakar idonshi ta shige cikin ‘yan rawa idan taga baya kallonta...can waje ta fita ta samu wuri tayi zamanta tana jera masa Allah ya isa a cikin ranta kmr daga sama taji sallaman mutum a kanta..idonta ta lumshe tasan yanxu zuwa zaiyi ya kara mata kan abunda take ciki dan ko ba’a ba tasan shine...muryan kadai taji ta gane Sir Abdool ne...kallon yanda ta kulle idanu yake kafin a hankali yace"may i?.."kai ta gyada mishi ba tareda ta bude idon ba...zama yayi nan kusada ita yana sake kafa mata eyes dinshi yace"Lamido wai bakida tausayi dama?..ace duk tsahon lokacin nan inata faman baki hakuri amma kinki hakura"...bude idon tayi tana dan turo lips dinta tace"Sir nifa ba fushi nakeyi dakai ba"...tana rufe baki yace"idan ba fushi kikeyi dani ba meye wnn toh?..meyasa har yanxun bakya picking calls dina?.."dan juyawa tayi tana kallonshi tadan marairaice tace"da gaske ba fushi nakeyi ba"...yace"then fadamin idan sona ne bakyayi I won’t force you"...sake narkewa tayi tana dubanshi tace"inada wanda zan aura ne"...hannu yakai ya dafe chest dinshi tared runste ido yace"that hurts"...a hankali tace"am sorry"...bude idon yayi yana kakalo murmushi yace mata"as i have said I won’t force u to love me and congratulations to the lucky guy"...dan murmushi kawai tayi batace komai ba..she’s happy yayi understanding dinta...muryanshi taji yana cewa"but akwai alfarma da zan nema wurinki"...tana gyada kanta tace mishi"inaji"..yace"if I can’t be ur lover at least i will be glad to be ur friend"...bright smile ta saki tana dubanshi tace"then we’re friends"...murmushin shima ya saki yace"yes we’re friends..thanks for accepting my offer"...daria kawai takeyi tana kallonshi..taji dadin yanda ya fahimce ta har hakan yaso yawa ta manta baqin ciki hanata rawa da akayi...shima darian yakeyi yana kallonta deep down yanajin ciwon rashin samun soyayyanta amma ya ya ita tunda bata sonshi?..kaman ance ta daga ido sukayi ido hudu da Bobby daya wani hade rai yana binta da tsinannen kallon nan bata qauna...darian da takeyi ya tsaya cak itama ta hade rai tareda dauke idonta daga gareshi...shi kuma wucewa yayi zuwa office dinshi yanajin haushin yanda heart dinshi ke neman deceiving dinshi yana sashi jin abunda sam bai kamata ace yajishi akan jinin Fulani ba.
A takaice ranar haka aka tashi taron nan batayi rawa ba sbd tsoron kar ya fadawa daddy...haka suka koma hostel itada Billy tanata ciccin magani Billy batabi ta kanta ba ta shiga sabagar gabanta...sai dare da babynta yazo snn ta dan samu nutsuwa dan bai bar hostel dinba saida ya tabbata yayi flushing away wnn damuwan da take ciki.
The next day around 10 suka fita sbd da wuri ake fara lecture din...dress code dinsu na ranan white ne dan basuyi anko ba saidai ance everybody should wear white cloth...itada Billy black straight skirt suka saka da farar shirt sai farin kimono da suka dora akan kayan itama white da digi digon black a jiki suka yafa black veil...ita Billy tasa turban snn tayi veiling da mayafin while hajia indo batasa komai ba sai dan mayafin data yafa akanta...daidai sa bags da suka rike iri daya ne suma duk farare...suna shigowa cikin school kiran Husna ya shigo wayan Billy nan ta dubi Aysha da sauri tace"Lamido ina tunanin su Hamma fasun karaso kinga Husna na kirana"...Aysha tace"to mu karasa parking space muga ko suna can"..daga haka suka wuce zuwa parking lots din...tun daga nesa suka hango motanshi dan haka suka nufi inda take...Hamman nasu ya shiga binsu da kallo yana murmushi yace"lallai ashe gayunku kawai kukeyi a makarantan bamu saniba"..Aysha tace"kai Hamma meya wani gayu a nan"..yana kallon Billy yace"gayu ne mana..dan bakiga yanda kukayi kyau bane"...kafin Aysha tayi mgn Husna tace"Hamma mudai dan Allah mu karasa ciki kar a fara abun arzikin bamu shiga ba..nasan anjima nayi zaka fara cewa azo a tafi daddy yace kar ayi dare"...murmushi kawai yayi gamida girgiza kai snn suka dunguma zuwa hall din...da yake yau kusan kowa yana inviting family ko friends dinshi sai hall din ya cika yayi taf fiyeda sauran ranakun...wuri suka samu suka zazzauna daga gaba gaba yanda za’ayi komai akan idonsu snn suka cigaba da kwasan hira kaman sun shekara basu hadu ba...suna nan zaune gab da za’a fara Sa’eed shima ya shigo tareda lubna aikam suna ganinta suka mike zuwa inda take sukayi hugging dinta..shi kuma Sa’eed ya karas shna gaisawa da Hamma dasu Husna...bayan sun gama rungume rungumensu suka karasa suma suka zauna Lubna nata jadda musu sai sunzo kd bikinta nanda few weeks sukace zasuje inshaAllah...saida kowa ya gama shiga snn Proprietor,Provost da kuma manya manyan doctors da zasu gabatar da lecture suka fara shigowa...duk yawan jama’an dake wurin baisan meyasa idanunshi suka hango mishi ita zaune a tsakiyar wasu maza ba...ranshi yaji ya 6aci sosai yanxun duk space dake cikin hall din nan ta rasa inda zata zauna sai ta shiga cikin maza?..wai wace irin yarinyace ne wnn?..wane irin shegen rashin hankali gareta?..har suka isa high table da aka tanada dominsu suka zauna bai denajin ciwo ba...sai a lokacin Aunty Sumy dasu Miemie suka karaso...Nur ne ya amsa mike daga hannun mc yayi welcoming guests dinsu snn ya gabatar da sunan disease da za’ayi lecture a kanshi Sickle Cell Anaemia wanda akafi sani da Sickler...tafi wurin ya dauka kowa yana ganin dacewar gabatar da lecture akan Sickler sbd yanda masu ciwo irinshi suke facing challenges a rayuwarsu na yau da kullum...bayan hall din ya danyi tsit ya dora da fadin"and before i hand over the mike to our qualified doctor Olusola Bulus...i will like to invite Aisha Ahmad Lamido for a brief introduction of Sickle Cell Anaemia"...fuska daure Bobby ke kallon abokin nashi ko meye ma’anar hakan da yayi oho?..meye amfanin wani kiranta tayi bayani tunda ga doctor zaiyi lecture a barshi ya gabatar da abunshi mana...Aysha da taji sunanta unexpected kasa mikewa tayi daga inda take zaune...Hammanta ne ya sunkuya yayi mata mgn a kunnenta kan idon Bobby da idanunshi ke wurin...a hankali ta mike daga inda ta fito zuwa kan stage...tana isa ya ba ta mike dake hannunshi ta amsa ta fara da gaishe da manyan baqi da colleagues dinta dake wurin snn ta shiga yi musu brief introduction ko ince explanation na Sickle Cell Anaemi kaman yanda aka bukaceta...ta burge mutane da dama a wurin domin tun daga kan yanda take mgn with courage and confidence zaka san ba karamar mai kwanya bace...uwa uba kuma dressing dinta daya sake fito da ainihin kyawunta hatta yanda take mgn ma abun kallo ne...hall din yayi wani irin tsit ko tari babu sai sweek voice dinta dake tashi ta cikin speakers...bata shiga deep ba ta tsaya iya introduction kmr yanda akace tayi snn ta sake miqawa Nur mike din ta sauka daga wurin..tafi sosai aka shiga yi mata hatta doctors dake wurin saida suka jinjina mata dan tayi kokari sosai ba kadan ba...tana karasawa inda take Hammanta ya mika mata hannu suka tafa and again kan idanun Dr.Bobby da yabita da wani hadadden harara data sauka daga stage...kawai haushi yakeji and ya rasa dalili...gaba daya mutanen wurin ma haushinsu yaji yanaji for clapping mata da sukayi ballantana kuma Nur dashine wanda ya haddasa komai...aunty sumy dake zaune daga dan gaba itama kallonshi kawai take tana mamakin abunda aka mashi yake wnn cin kunu haka...ta lura ko noticing zuwansu ma baiyi ba hankalinshi na can wurinda batasan me yake kallo ba...text tayi typing a wayanta"what’s wrong?..why are u frowning ur face?.."ta tura mashi...wayan na aljihunshi yanajin shigowan text bai duba ba..ta sake tura mashi"Bobbyyyy"...zaro wayan yayi cikeda haushin damunshi da akeyi zaisa a flight mode idonshi ya sauka kan sunanshi data kira...sender ya duba yaga itace sai ya bude message din da sauri shi sam ya mance sunyi mgn daxu tace mishi suna hanya...yana gama karantawa ya daga kai yana duban wurin wai ko zai hangota amma bai ganta ba...text ne ya sake shigowa wayan ya duba sai yaga tace"ba ganinmu zakayi ba kawai ka bar frowning face dinka haka kar guest dinka suyi tunanin wani abu"...ajiyar zuciya ya sauke yana sake wurga idonshi still bai gansu ba dan haka yayi typing"ohk na dena"shima ya tura mata...yana gama tafiya ya maida wayan aljihu yana kokarin daidaita face dinshi kmr yanda tace kar guest dinshi suyi tunanin wani abu...doctor Olusola ne ya fara bayani kan yanda Sickler yake..yanda yara ke samu ta hanyar iyayensu and hanyoyin daya kamata abi don ganin sun zauna cikin koshin lafia...saida ya dauki more than one hour yana abu daya kafin ya gama...bayanshi wani doctor Solomon shima yayi bayani stigmatization da suke fuskanta a society da kuma hanyoyin daya kamata abi don kiyaye wnn stigmatization din and lastly doctor Nuruddeen wato Provost yayi bayani kan hanyoyin da za’abi wajen preventing haihuwan yara masu sickler snn idan an haifesun hanyoyin da za’ayi taking proper care of them tun daga neonatal stage zuwa child har zuwa adolescent...daga nan kuma ya sake mika godia wa duk wanda suka halarci taron a matsayinshi na Provost na FCNM tareda fatan komawa gida lafia...daga nan kuma sai aka hau raba drinks da snacks each table aka ajiye musu nasu snn aka faraci...bayan sun gama Provost ya sake amsan mike yace yanaso su zama ready for the Fun Walk don in the next 10 minutes zasu fita...haka kuwa akayi duk mutane suka fara mikewa suna fita daga hall din...Bobby ma ya taso daga inda yake zuwa inda ya hango su aunty sumy zaune...tun kafin ya karasa Ilham ta mike tana rungumoshi..shi kuma yajata suka karasa wurin yana kokarin dora smile kan face dinshi yace"wai yaushe kukazo?..kinsan banga shigownku ba?.."aunty sumy tace"dama ya zaayi kaga shigowanmu hankalinka na wani wajen..wai mema kake kallo ne kam?..and meya 6ata maka rai da kaketa cin magani haka?.."dan shafa kanshi yayi yace"bafa wanda ya 6atamin rai kawai zaman wajen ne ya isheni..kuma zakuyi walk din ne ko bazakuyi ba"..mikewa aunty sumy tayi hannunta rikeda bag dinta tace"rufamin asiri da wnn tafiyar Bobby..komawa gida zamuyi dama lecture mukazo ji kuma an gama so we are going back home"...gyada kanshi yayi cikin jin dadin tafiyar da zasuyi yace"gara ku koma ai dan wnn walk din wahalar banza ne kawai"..aunty sumy ta wuce suka fara tafia tace"wnn karon ma bazakaje ba knn?.."yace"haba!.Allah ya kiyaye ai bazan iya wnn wahalar ba"..murmushi kawai ta sakeyi batace komai ba...saida ya rakasu har mota yaga sun shiga sun fita daga makarantan snn ya juya zuwa office din Nur don yasan da yawa daga guest din da basu tafi ba suna can...snacks ya samu sunaci da drinks dinsu sunata kwasan hira kaman basu ba...daidai lokacin da ya shiga yaji Gabriel na fadin"ni wlh yarinyar nan cema ta burgeni gaba daya tunda na ganta naji na gagara sukuni...yaya ma sunanta kace?.."yayi referring tambayar to Nur dake sauraronshi yana daria yace"kai wnn yarinyar tafi karfink wlh..Lamido matar manya ce ba yara irinku ba"..daria suka saka Gabriel din na cewa kodai shima Nur sonta yake Nuru yace ai babu mamaki ma idan yana son nata...Bobby dake tsaye jikin kofa yana sauraran conversation din nasu kasa karasawa ciki yayi..haka nan yaji wani
Book Chapters
Chapter 18
Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59