You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
gidan daddy ya mikama Ammi makullin motar ba musu ta kar6a ta bude musu ya shiga front seat Aysha kuma ta shiga baya sai ita Ammin ta shiga driver seat..dama haka yake bai cika daukan driver zuwa gidan Lamido ha sai dai idan daga can zai wuce aiki bazai dawo ta gidan ba..itama Ammi duj zataje da kanta take driving kanta tareda yaran...motar shiru har suka isa gidan Lamido ba wanda yayi mgn cikinsu...a tare suka bude mota suja fito snn suka nufi entrance din gidan...daddy ne yayi sallama Lamido ya bashi izinin shiga snn suka shiga makeken parlon nashi...as usual yana zaune kan kujera yana kallonsu har suka karaso duk suka zauna a kasa snn suka fara gaisheshi..amsawa yayi cikin dattako da kamala irin nashi kafin yayi shiru yana kallonsu kmr bazaiyi mgn ba sai can kuma yace"Maimuna mgn ce nakesonyi dake"..kai a kasa Ammi tace"ina sauraronka Baffah"..yace"ina fatan Ahmad ya sanar dake yanda mukay dashi jiya"..kai ta daga tareda fadin"ya sanar dani"..Lamido yace"MashaAllahu...yanxu meye shawaranki akai?.."da sauri tace"ai ni banida wani shawara face bin umarninka Baffah..duk hukuncin daka yanke daidai ne Allah yasa haka shi yafi alkhairi"..cikin murmushin jin dadin kalamanta yace"to Madallah Maimuna Allah ya maki albarka"..ta amsa da"Ameen Ameen"..shiru dakin ya sakeyi kafin Lamido ya tsayar da idonshi kan Aysha da taji wani hadadden tashin hankali ya risketa yanxun nan..haka nan jikinta ya bata wnn kiran na Lamido bana lafia bane..gashi sai wani mgn sukeyi a kunshe ta kasa gane me suke cewa...ganin yanda duk tabi tayi tsuru tsuru tana rarraba ido Lamido ya saki murmushi wai tunma kafin taji mgnr da zai fada nata knn..dama yasan zaisha rikici ba dan karami ba da yarinyar nan amma saidai ko mutuwa zatayi bazai canxa mgnrshi ba..cikin muryar daya kusa sata fitsari yace"Aisha"..a firgice ta dago kai tana kallonshi har hawaye sun fara ciko idanunta..Lamido bai damu da hawayen nata ba yacigaba da mgn"kin turo mahaifinki jiya akan mgnr wanda kikeso koh?.."da sauri ta gyada mishi kai kmr mara hankali..Lamido yace"Alhamdulillah to inaso ki sanar dashi cewa ni Lamido na dade dayi maki miji"..wani irin zare idanu tayi tana kallonshi kmr bata gane me yace ba...ganin haka Lamido ya sake daure fuska yanda bata isa ta kawo mashi wargi ba yace"kinji abunda na fada ko in sake maimaitawa?.."nan take ta dawo daga suman zaunen da tayi hawaye suka shiga sauko kan fuskanta tace"na..ji"..yace"MashaAllah saiki kirashi ki fada mashi"..sake gyada mashi kai tayi hawaye na sake tururuwar zubowa fuskanta...har wani sarawa taji kanta nayi sbd tsabar tashin hankali..tunda take zata iya ranstuwa bata ta6a tsintar kanta cikin tsananin tashin hankali irin wnn ba..me Lamido yake nufi da yayi mata miji ne wai?..yanxu yana nufin bazata auri baby ba?..kuma waye shi wnn mijin da yayi mata?..lokaci daya ta kasa daurewa ta saki wani irin kuka tareda dora hannunta a kai kmr wanda uwa da ubanta suka mutu..shknn tasan ta riga ta gama yawo domin Lamido bazai ta6a canxa mgnrshi ba..abune wanda tasan ya zamar mata dole ta auri za6in da yayi mata amma shin waye wnn za6in nashi?..meyasa tun tuni bai ta6a furta yayi mata miji ba sai yanxu?..meyasa saida ta kawo wanda takeso Lamido zaiyi mata haka?..kuka takeyi wiwi tamkar wanda ta rasa iyayenta..Lamido sai yayi relaxing kan kujeran da yake yana kallon yanda take kuka kmr ranta zai fita..ganin haka daddy ya daka mata tsawa yana cewa"Aysha bakida hankali ne zaki tasa mu gaba kina mana kuka haka?..so kike ki nuna ba'a isa dake bane ko yaya?.."da sauri ta hau girgiza kai har yanxu hawaye basu dena ambaliya kan fuskanta ba ko mgn ta kasayi.
Jama’a wa kuke ganin Lamido ya za6a a matsayin mijinda zata aura..Bobby ne?..ko kuma wani ne daban?..🙄
Rano✨
Wnn littafin na kudi ne ban yadda wani ko wata ya fitarmin dashi ba...masu buqatan siya zasu tura 300 zuwa 2208991344 Aisha Ahmad Tijjani Zenith Bank...sai a tura evidence of payment via 07063800556.
43
Kuka takeyi sosai cikin tsananin tashin hankali da rashin sanin tudun dafawa...yanxu wnn mgnr na Lamido na nufin auren dole za'ayi mata knn?..yanxu suna suna nufin ta rabu da baby knn?..innalillahi wa inna ilaihi rajiun...bude baki daddy ya sakeyi da nufin yayi mata masifa sai Lamido ya daga masa hannu alamar he shouldn't say a word..ba musu yaja bakinshi ya rufe yana kallonta..Ammi dama tana zaune ko kai bata dago ba balle tayi mgn...kallonta Lamido yayi fuska a daure ya sake kiran sunanta...ta dago tana kallonshi hawaye nata sintiri kan cheeks dinta...murya a dake yace"anyi maki wani abun ne kikema mutane kuka?.."shiru tayi kai a kasa..a fusace Lamido yace"ba mgn nake maki bane?.."girgiza kai ra shigayi da sauri tana runtse idanunta...yace"to kan wane dalili zaki zauna kina mana kuka?..ko kinga abokin wasanki a nan wurin,?.."nan ma kai ta sake girgiza alamar babu..yace"then wipe off those tears tun kafin raina ya 6aci..kika bari na sakejin kukanki kuma zakiga matakin da zan dauka"..tsit tayi tana toshe baki da hannayenta...shi kuma ya zuba mata ido har saida ta goge hawayen tas snn ya juya yana duban daddy yace"Ina Najeeb yake?.."kai a kasa daddy yace"yaje wajen aiki"..Lamido baiyi mgn ba sai wayarshi daya dauka nan kusa dashi yayi dialing number Najeeb..yana fara ringing Hamma Najeeb ya dauka da fadin"barka da safiya"..Lamido yace"barka dai..kana ina yanxu?.."Najeeb yace"ban dade da shigowa office ba"..yace"to ka dauki excuse ka dawo gida inason ganinka yanxun nan"..da sauri yace"Baffa lafia kuwa?.."katse wayarshi Lamido yayi bayan yace"ka hanzarta ba zaman jiranka zamuyi a nan ba"..su daddy dai na zaune sunajin me yake cewa amma ba wanda yace uffan...zaman kurame suka shigayi a parlon har Najeeb ya karaso...waje Lamido ya nuna mashi kusada Aysha ya zauna snn ya sake daure fuska yanda zai dauki mgnr da zai fada da muhimmanci kafin ya nuna Aysha da hannunshi yace"fadamun ya kake da wnn yarinyar?.."kallonta Hamma ya juya yayi snn ya dawo da kallonshi ga Lamido cikeda mamakin tambayar...cikin tsawa Lamido yace"bada kai nake mgn bane?.."da sauri yayi kasa da kanshi kafin yace"qanwata ce ita"..Lamido ya sake cewa"qanwarka kawai?.."juyawa Hamma ya sakeyi ya kalli su daddy snn ya kuna juyowa ga Lamido yaga yanda ya tsareshi da ido sai yace"kuma tanada sunan Mamana"..duk yanda Lamido yakai da daurw fuska saida mgnr nan ya bashi daria..wai tana sunan mamanshi..amma wnn yaro Najeeb ba dan karamin soko bane...hatta su daddy saida mgnr ya basu daria kuma duk basu kawo komai a ransu ba saida Lamido yace"to itace wadda na za6a maka matsayin matar da zaka aura kamar yanda kaima kaine na za6a mata matsayin mijinda zata aura"..wani irin diff dakin yayi kmr anyi ruwan sama an dauke...daddy da Ammi syka shiga kallon kallo dan ba wanda tunaninshi yazo nan wurin...Aysha kuwa wani irin darammm taji gabanta ya fadi ta shiga zare ido kmr wata zakanya ta juya tana kallon Hamman da shima idanunshi ke kanta yana zare ido...relaxing Lamido yayi yana kallon yanda suke kallon kallo a tsakaninsu..daga reaction dinsu ya fahimci mgnr a bazata yazo musu...har yanxu kuma parlon tsit an rasa mai kwarin guiwar da zai fara mgn cikinsu...baki Aysha ta bude zata sake rushewa da kuka Lamido ya daka mata wani tsawan da batasan sanda ta kankame Najeeb dake zaune kusada ita ba...ba shiri ta hadiye kukan tsaf tana cigaba sauke numfashi gamida rarraba ido kmr shege a rabon gado...wani shiru dakin ya sake dauka kafin Lamido ya juya yana fuskantar su daddy yace"Ahmad ko baku fahimci mgnr dana fada bane?.."daddy ta hadiye wani yawu daga bakinshi kafin cikin karfin hali yace"mun fahimta Baffa..kuma munyi na'am da haka ubangiji ya sanya alkhairi a ciki"...kasaitaccen smile Lamido ya saki ya dubi Ammi ita yace"kema kin amince Maimuna?.."har yanxu kanta na kasa tace"na amince..Allah ya tabbatar da alkhairi"..wanu murmushin Lamido ya kara saki kafin yace"Allah ya maku albarka"..suka amsa da Ameen snn ya sake juyawa ga iyayen gayyar wato Lamido da Hammanta...idanunshi ya tsayar kan Najeeb da yake ganin komai dake faruwa kmr a faraki yace"daga yau inaso ka fara daukanta matsayin matar da zaka aura ba wai qanwa ko mai sunan Mamanka ba..kema kuma ki tabbata kin bashi wnn matsayin don ko mutuwa daya daga cikinku yayi sai an daura wnn auren..kuje na sallameku"...mikewa Hamma yayi da kyar ya juya zai fita daga parlon Lamido yace"dawo ka tafi da ita"..ba musu ya dawo tareda durkusawa ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye snn ya shiga janta kmr mara lafia suka fita daga parlon...juyawa yayi wajen su daddy yace"kuma kuna iya tafia Allah ya maku albarka"..bayan sun amsa da Ameen duk suka mike suka sake mishi sallama zasu fita Lamido yace"Ahmad ka tabbata ka fada masu suyi kokari su fahimci junansu kafin ta gama makaranta don wnn aure ko mutuwa nay banaso a fasa yinshi"...gyada kai daddy yayi before"zanyi kokari in Allah ya yarda..mun barka lafia"..daga haka ya juya yabi bayan Ammi suja fita daga parlon...basu samu su Aysha nan compound ba hakan ya nuna musu cewa kilan sun wuce gida dan haka shima ya bude nashi motar suka shiga wnn karon da kanshi ya jata suka bar gidan...a hanya Ammi tayi tsit ta kurawa waje daya ido tana tunani...gangarawa gefen titi yayi yai parking tareda jama hannunta ya rike cikin nashi...ta juyo da sauri tana kallonshi sai kuma ta sakar mashi smile dinta me kyau...kallonta yakeyi da damuwa yace"kiyi hakuri Maimunatu"..Ammi ta dan wara ido tana dubanshi tace"hakurin me kuma?.."yace"nasan bai zama lallai kiso wnn hadin nasu ba amma inaso kisan babu yanda zamuyi da Lamido tunda ya riga ya furta"..hannunshi itama ta rike tana sakin murmushi tace"ko kusa bana kin auren Aysha da Najeeb wlh..kawai mgnr ne yazomin a bazata kasan ban ta6a kawo a raina wai shine mijinda ya za6a mata ba...Najeeb yaron kirki ne mu muka raineshi sbd haka babu wanda ya dace da auren Aysha idan bashi ba..nasan zai riketa da kyau kuma zai iya bida ita a hankali sbd rashin jinta"...ajiyar zuciya daddy ya sauke yana kallonta da murmushi..gaskia Maimunatu matar arziki ce...da wnn maganganun nata sai yaji duk kokwanton da yake akan batun ya gushe..tabbas shi kanshi yasan Najeeb yaro ne mai hankali kuma bayada wani mugun hali da za'a hanashi aure sbd shi..dadin dadawa kuma danshi ne domin shi ya rikesh tun yana dan karami kuma kmr yanda ta fada zai iya da Aysha sosai sbd ya riga dama yasan halinta ciki da bai so basu da damuwar komai...tayar da motar yayi suka karasa gida kowa ranshi fess dan Allah ya gani sunyi na'am da wnn za6in na Lamido...a parlor suka iske Najeeb din zaune ya buga uban tagumi ga kukan Aysha daya karade dakin gaba daya...yana jin shigowarsu ya mike da sauri ya isa garesu yana cewa"dan Allah daddy babu yanda za'ayima Lamido ya janye mgnr auren nan?.."kallonsh duk su biyun sukeyi kafin su hada baki wajen cewa"baka sonta ne?.."wani irin kunya yaji ya rufeshi dajin tambayan nasu...shaf ya manta fa iyayenta ne and suna iya jin babu dadi idan ya nuna bai sonta..amma shi harga Allah ba kinta yake ba kawai abun ne yazo mishi unexpected sai kuma wnn uban kukan da take sai kace ance za'a aura mata dodo...girgiza kai ya shiga yi da sauri yana nuna kofar dakinsu yace"kawai..banaso ayi mata dole ne..rufe kanta tayi fa a daki taketa kuka daddy kada wani abun ya sameta"..kama hannunshi daddy yayi suka karasa cikin parlor suka zauna snn yace mishi"indai don wnn ne ka kwantar da hankalinka ai ka riga kasan yanda take dama..wnn kukan koma waye akace zan za6a mata sai tayishi so wnn kar ya dameka ko kadan..kawai kacigaba da addu'a"..kai kawai ya iya gyadawa cikin ranshi yana jinjina kalar darun da za'ay da ita don yasan dole ne sai tayishi wlh...mikewa yayi bayan yayi musu sallama ya koma wurin aikinshi yayinda Ammi ma ta shiga kitchen shi kuma daddy yai zaune a parlon yana sakawa da kwancewa..fatanshi kawai Allah ya daidata al'amura kada azo ana samun matsala...Aysha kuwa tana daki tanata rizgar kuka ba wanda yabi ta kanta don a cewarsu idan ta gaji dan kanta zata dena kuma zata bude kofa ta fito ko don yunwar cikinta
kuwa.
A hankali ya bude idonshi daga nannauyan baccin daya daukeshi as a result of drugs dinshi da yasha..duba yakai ga agogon dakin yaga it's almost five dan haka ya sauka daga gadon da sauri ya fada bathroom yayi alwala ta fito snn ya tada sallah yana jin haushin rashin tashinshi da sukayi har time din sallah ya wuce...yana idar da sallah Sab ya shigo dakin yana dubanshi yace"waziri yace wai ya jikinka?.."mikewa yayi daga inda yayi sallahn yace"da sauki..muje"..tare suka fita zuwa parlon waziri shi da Sab din...yana ganinshi ya saku murmushi tareda furta"jiki yayi kyau knn?.."murmushi shima Bobbyn ya sakar mishi har suka karasa ciki..nan kusada wazirin ya zauna yana dubanshi da murmushi..so yake ya tambayi ko sunyi mgn da Lamidon amma baisan ta yaya ba...bayan waziri ya sallami baqin dake tare dashi ya shiga duban Bobby fuska da murmurshi sosai yace"zaka iya rakani wani waje yanxu?.."a hankali Bobby ya daga mishi kai alaman zai iya..waziri ya maida dubanshi ga Khalid dake zaune parlon shima yace"kaje kace a fitomin da mota"..ba musu khalid ya juya ya fita shi kuma waziri ya mike tsaye tareda kama hannun Sab yace"kaima muje kayi mana rakiya mai sunana"..a tare suka fita duk su ukun zuwa motarshi da har an fito da ita...makullin motar ta kar6a daga hannun driver dinshi ya mukawa Sab yace yayi driving dinsu...ba musu Sab ya amsa key din dukda cewa baisan kan garin sosai ba...ya bude driver seat ya shiga su kuma suka shiga baya snn ya tada motar suka fita daga gidan...saida suka hau babban titi Waziri yace"zaka iya gane Gra?.."a hankali Sab yace"da kyar zan gane gaskia"..gyada kai waziri yayi yace"to muje zanyi directing dinka"..haka kuwa Sab yaja motar suna tafe yana nuna mishi hanya har suka shigo Gra...suprise yakeso yaima Bobby shiyasa bai sanar mishi inda zasuje ba..yaso ace yareda uncles dinsu sukazo amma bazai iya jira har su dawo daga aiyukansu ba shiyasa yaga gwara ya fara zuwa shi kadai suyi mgn gemu da gemu da Lamido inyaso daga baya sai su sake dawowa tareda 'yan uwan mahaifinshi don kawo dukiyar aure...waziri nacigaba da nuna ma Sab hanya har suka iso Lamido's Palace...wani irin bugu zuciyar Bobby yayi da yaga an rubuta The Lamido's 6aro 6aro a can saman gate din estate din...duk fadin Gombe kuma yasan Lamido ne kadai mutuminda yayi suna da sunan sosai dan haka ba tareda wani tantama ba brain dinshi ya fada mashi cewa wnn estate dinsu Lamido ne...lumshe ido yayi tareda jingina da kujera knn hakan na nufin Waziri zuwa yayi suyi mgn da Lamido?..wani irin faduwa gabanshi ya sakeyi daya tuna cewa fa tayi bata sonshi..yanxu idan sukaje ta sake tozartashi tace bata sonshi fa?..hankalinshi yaji ya tashi har wani zufa ya faraji na ba gaira babu dalili amma yayi kokari bai bari waziri ya fahimta ba har aka bude musu gate suka shiga ciki...tafia sukayi ba wani mai nisa da yawa ba suka karaso gidan Lamido...daga nan waje Sab yayi parking motar snn duk suka bude suka fito...suka sanya waziri a tsakiya suka shiga cikin gidan...daidai entrance suka hadu da wani brother din daddy ya fito daga parlon Lamido yana ganin Waziri yayi saurin dunkule hannu tareda risinawa yana fadin"Allah ya taimaki Waziri...barka da zuwa"..Waziri ya amsa da"barka dai Mahmoud..ya iyali?.."Mahmoud Lamido yace"suna lafia lau Waziri..a fito lafia"..Waziri ya gyada mishi kai yana murmushi..sai a snn Bobby da Sab suka gaishe da mutumin snn sukabi bayan Waziri zuwa cikin parlon...Lamido na ganinsu ya fadada murmushin fuskanshi yace"Waziri ne a tafe?.."Waziri daya karasa ciki ya zauna kan one of kujerun dake parlon yace"wlh nine Lamido"..Lamido yace"to barka da isowa"..Waziri yace"yauwa..ga jikokinka nan na kawo makasu har gida"...kallonsu Bobby Lamido yayi yana cigaba da murmushi yace"yaran Attahiru koh?.."Waziri ya gyada mash kai shima yana murmushi...Bobby ne ya fara gaisheshi kai a kasa sai Sab shima ya gaisheshi...bayan gaisuwa Waziri yace"jiya na kira wayarka ai"..Lamido yace"na gani wlh..lokacin ne ina tareda Ahmad kan batun auren 'yarsa daya taso shiyasa banga kiran naka bama sai daga baya"..waziri na gyada kai yace"ikon Allah watace zatayi aure cikin yaran nashi?.."Lamido yace"babbar ce wai ta turo a sanar dani wani dake neman aurenta yanaso ya turo shine nace ta dakatar dashi dan na riga nayi mata miji tun tuni"...wani irin faduwa gaban Bobby yayi kirjinshi sai up and down yake fatanshi bai wuce Allah yasa ba akanta ake mgn ba...shi kanshi waziri zuwa yanxu gaban nashi faduwa yake yace"wacce daga cikin yaran wai?.."kai tsaye Lamido yace"Aisha mana..ina wnn yaro Najeeb?.."Waziri yace"dan wajen marigayi Auwal koh?.."Lamido yace"yauwa to shine wanda na za6a a matsayin mijin nata..kasan ubanta shi ya rike Najeeb din kuma nasan ba wanda zai iya zama da ita sai shi shiyasa na tarasu na fada musu ko bayan raina ban yadda a fasa wnn auren ba"...wani irin tari ne ya sarke Bobby kaman wanda ya kware da wani abun...hankalinshi yakai kololuwar tashi har wani zufa ya faraji all of a sudden ga kuma coughing da taketa faman yi non stop..nan take hankalin Waziri ya tashi shima..Sab ya rikoshi yana yana shafa bayanshi amma kmr tunzurashi suke don cough din sai karuwa ma da yayi...da sauri Waziri ya mike yana duban Sab hankali a tashe yace"kamoshi muje asibiti"...Lamido ya mike shima yana dubansu yace"ina zuwa"..daga haka ya shiga wani corridor dake nan cikin parlon..bayan few minutes ya fito rikeda goran zamzam da akayima addu'a a hannunshi..yana karasowa ya bude tareda kafa goran a bakinshi nan da nan kuwa ya shiga shan ruwan kaman an aikoshi...saida tasha almost half snn ya cire baki tareda yin kasa da ido yana sauke numfashi...hawaye ne sosai suke cikowa idonshi amma bayason su zubo...bayason ko waziri yaga wnn tears din sbd ya gaji da zubar da hawaye a gabansu...zuciyarshi wani irin rauni tayi mashi wanda bata ta6ayi masa irinshi ba...kokari yake sosai na ganin ya 6oye abunda yakeji amma abun yaci tura sbd bashi keda control din kanshi ba...runtse ido yayi yana maimaita innalillahi a cikin zuciyarshi har yanxu kuma bai denajin hadadden zufa na lullu6eshi ba...kallonshi Lamido yake cikeda mamaki yace"meya sameshi ne haka?.."Waziri ne yayi karfin halin cewa"dama baida lafia don daxun aka sallamoshi daga asibiti..ina ganin zamu tafi kawai a sake maidashi can"...da sauri Lamido yace"a maidashi gaskia don wnn tarin nashi bana lafia bane..Allah ya baka lafia Attahiru"..ya karasa mgnr referring to Bobby dake dafe da chest dinshi da hannu daya dai kuma daya hannun ya dafe head dinshi da yaketa jujjuyashi from side to side...Sab har ya fara hawaye shima a haka ya kamashi zuwa inda yayi parking mota..bude baya yayi ya sashi ciki snn yayi saurin zagawa zuwa driver seat Waziri kuma ya shiga baya suka tafi...kai tsaye asibitin da suka baro daxu ya shiga nuna masa suka maidashi.
Aysha kuwa yini tayi daki tana kuka ba wanda yabi ta kanta saida su Husna suka dawo..sune sukaita tambayanta meya faru amma ta kasa ko bude baki balle tayi musu bayani...ganin abun nata bana kare bana kare bane gashi har dare zaiyi bata fito taci abinci ba daddy dake parlonshi ya kira Ammi yace mata"Maimunatu je ku duba yarinyar can don Allah..wnn kukan da take ai saiya haifar mata da ciwon kai"..ajiyar zucia Ammi ta sauke Allah ya sani itama tun daxu takejin kmr taje ta rarrashi kayarta amma sbd kara irin nasu na fulani kasa zuwa tayi...yanxu kuma da daddy yayi mgn da kanshi ko musu batayi mashi ba ta kama hanyar dakin nasu...su Husna na zaune sun sanyata tsakiya tana fada musu cewa Lamido ne yace zai hadata da Hamma Najeeb aure..Husna da bataga wani abun tayar da hankali a mgnr ba tace"to Adda wnn ne abun kuka kuma?..Hamman da kinfi kowa sanin halinshi ne kike kuka sbd zaki aureshi?..ai murna ya kamata kiyi ma"..Husna na rufe baki Ammi data shigo dakin tace"Husna kuje parlor ku jiramu zamuyi mgn"..ba musu Husna ta kama hannun Yusra suka fita...suna fita Ammi ta zauna nan kusada ita tareda kama hannunta ta rike kafin tace"ki tsayar da kukan nan mgn zamuyi"..ba musu takai hannu tana share hawayenta...Ammi na dubanta da kyau tace"bakya son Najeeb din ne?.."da sauri ta shiga gyada mata kai alamar eh..janyota Ammi tayi ta rungume a jikinta tana shafa bayanta tace"to ki dena kukan nan indai baso kike kisama kanki ciwon kai ba..so nake ki kwantar da hankalinki zamuyita addu'a inshaAllah idan ba alkhairi bane Lamido da kanshi zaice ya janye mgnr"..luf Aysha tayi jikin mahaifiyar tata tana sauke numfashi..wato dai duk dunia babu inda ake samun irin wnn nustuwan sai wurin uwa...hankalinta taji ya dan kwanta unlike daxun da take ganin duk tashin hankalin dunia a kanta ya kare...kawai har yanxu ta kasa picturing itada Hamma matsayin mata da miji...jin yanda tayi tsit Ammi ta dagota daga jikinta tana sake rike hannunta tace"kinji abunda na fada maki koh?.."gyada kai tayi a hankali Ammi tace" yauwa kuma banaso shima Najeeb din kice zaki nuna masa wani abu..kucigaba da mu'amalarku kmr da inshaAllah indai ba alkhairi bazaki aureshi ba"..sake gyafa kanta tayi tana fatan Allah yasa ba alkhairi din...mikewa Ammi tayi itama ta mikar da ita tsaye tana cewa"muje to kici abinci..haka nan yau duk kinbi kin dorama kanki damuwa ko abincin bakici ba"...daga haka Ammi ta shiga janta suka fita daga dakin..Lamido dai mamaki fal cikin zuciyarta na ganin yanda Ammi take lalla6ata yau..anya kuwa ba kofar rago ake shirya mata ba?..tasan dai yanda Ammi take da zafi zaiyi wahala tazo ta rarrasheta haka kawai...sai kuma wata zuciyar tace mata kilan sbd tasan ba'a kyauta mata bane shiyasa take haka...ko su Husna dake zaune parlor abun ya basu mamaki ganin Ammi rikeda hannun Addarsu har dinning...ba wai Ammi bata sonta bane no kawai dai basu cika jituwa bane sbd halayen Ayshan da kusan gaba daya basu mata ba..ga kuma kasancewarta 'yar fari shiyasa abun ya hade mata biyu amma yau ga Ammi rikeda hannun 'yarta sai sukay kaman wasu qawaye...daddy daya fito don tafia masjid ya hangosu a dinning Ammi na kokarin serving dinta sai ya saki murmushi hade da girgiza kai snn ya fita daga gidan...Maimunatu sarkin kara yau an ajiye karar a gefe knn...yaji dadin yanda yaga Ayshan har ta dan sauko shiyasa akace dai duk fadin dunia mutum baida wanda ya wuce mahaifiyarshi...babu wanda zai soka kaman ita haka kuma babu wanda zai ji tausayinka ya kuma damu da damuwarka kamar mahaifiyarka...itace zata soka kilan fiyema da yanda kake son kanka..(Rabbi ya sakawa iyayenmu da alkhairi ya basu aljannah).🙏🏻
Saida Ammi ta tabbata taci abincin da yawa snn tace taje tayo alwala ta sameta dakinta...ba musu ta wuce dakinsu tayi alwalan snn ta fito..su Husna suma duk alwalan sukayi snn suka wuce bedroom din Ammi kamar yanda tace musu su sameta a can...a tare sukayi sallahn nasu gaba daya bayan sun idar Ammi tace duk su sa 'yar uwarsu a addu'a idan akwai alkhairi tsakaninta da Najeeb Allah ya tabbatar idan kuma babu Allah ya kawo mafita..Aysha dai sam ba wnn addu'an takeso ayi ba tafiso kawai suce Allah ya kawo hanyarda fasa auren inyaso sai kowa Allah ya hadashi da alkhairin nashi a gaba...zata iya hakura da auren baby amma bazata iya auren Hamma da take mishi kallon dan uwanta da syka fito ciki daya ba.
Washegari ta tashi da dan dama dama don batayi kuka ba kwata kwata saidai yawan tunani...tun jiya taje tunanin yanyar da zatabi wajen sanar da Prof halinda ake ciki amma ta kasa...hakan yasan ta sanar da Ammi ita kuma tace idan daddy ya dawo fada mashi sai ya kirashi da kanshi yayi mashi bayani sbd kada ma yayi zaton ko yaudaranshi zatayi...da wnn shawara na Ammi ta dan samu nustuwa amma dukda haka tana tunanin halinda bawan Allahn nan zai shiga duk ya samu labari...daddy na dawowa Ammi ta fada mishi yanda sukayi yace ta kawo numbershi ya kira da kanshi suyi mgn..ba musu ta bashi number nashi snn ta zauna nan parlon daddy ya kira number...yana dagawa daddy yace shine mahaifin Aysha sai kuma ya dora da fadin yanda sukayi da Lamido kan batun zuwa neman aurenta da yace zaiyi...hankalinshi ya rashi sosai wanda hatta daddy saida yaji tausayinshi...ya kwantar mashi da hankali
Book Chapters
Chapter 36
Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59