gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 9 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dalilin da yasa kake kula sha anin matar nan, domin a iyaka sanina da kai, a dukkan shekarun da nayi tareda kai, ban taba ganin ka tsaya da"

"wata mace kuna hira ba, hana rantsuwa ince banda Mamanka ."

" Duk inda mace take uwar kowa ce Femi, uwar al umma ce data cancanci girmamawa daga kowa ."

Daidai lokacin da suka kawo bakin motarsu.

"Yassar ya bude motar a hankali ya shiga ya zauna sannan ya kunna, Femi ma ya zagaya ya fada gaban motar, har Yassar yayi reverse Femi baiyi shiru ba da zancen su Ummami, cewa yake,"

" wato Boss, inka san wani abu wai shi  real definition of beauty in dirt (kyau a cikin datti) to wadannan mutanen naka ne, na tabbata rashin wanka, rashin abinci, da rashin isashshen barci duk su suka taru suka maida su hakan, ba wani abu daban ba."

"Hellelujah wannan sarkin kukan taka mace ce har mace, idan da ace zata samu sabulun wanka na mata mai kyau da tsaftace fata, wannan farar fatar tata data yi duhu tsaf zata yi tas, barinma ace ta samu maclean mai karfi irin Longrich ko Beverlyhills ya ratsa siraran hakoran nan nata, bakin nan nata ya dauki fentin baki (wetlips) da turaren cikin"

"baki (mouthfresh) fuskar nan ta samu cream mai kyau, na rantse nan da wata uku komawa zata yi wata classy babe, ai wannan da kake gani ita ake kira  mace irin ta sakawa a gaban  Hilux dinka. Wadda zakaiyashiga ko ina da ita a matsayin macen aure. Look at beauty at its peak mallam! Kyau gashinan a sarari& har zuba yake& . ."

"Yassar bai san sanda ya kaiwa Femi duka a bayansa ba, Femi ya kauce ya daki iska, Femi don dariya kamar ya tuntsura. Yassar ya ja dogon tsakin da bai shirya ba ganin Femi ya fara sauka daga kan layi wato ya karkace daga kan profession dinsa da mission dinsa, ya fito da dara-daran idanunsa akan Femi yana cewa.  Ya isa haka Femi! Nasan kai dama mayen mata ne, amma a shawarce zai fi kyau ka tsaya akan abinda ya kawoka kadai, a IDP Camp kake kan aiki, ba a U.S club ba, ina ganin kame mutuncinka zai fi maka alkhairi a"

wurinnan .

Femi yace cikin gardama da jayayya da Boss dinsa.

" Shin Oga, an gaya maka kowa ma irinka ne? nidai gaskiya dan adam ne kuma jinsin namiji sannan inada feeling akan"

"fararen mata. Ta yaya zanga abu mai kyau da ya kayatar da zuciyata irin wannan yarinyar, amma in kasa cewa komai a kansa saboda nazo IDP Camp yin aikin NGO?"

"Ai ni banida wannan nunkufurcin. At least dai in yaba ban iya munafurci ba, koda ban taba musu  ya ba, ban kuma ce zan taya ba, kawai ina gaya maka abinda zuciyata ke fadamin akanta."

Ko kuwa a zatonka kowa ma marar lafiya ne kuma marar feeling irinka?

"Ka sani sarai ina son fararen mata, wadanda babu su a kabilar dana fito, ita kanta uwar ma in ka lura sosai zaka ga ba wani tsufa tayi ba, wahalar rayuwa ce kawai da  trauma din zaman wajennan suka taru suka tsofeta haka, amma gaskiya Allah yayi halitta a nan, ba ga  yar ba, ba ga uwar ba& . ."

"Ya juyo da sauri yana kallon bakin Femi dake masa wannan kalami, cikin mamakin rashin kunyarsa. Sai ya daure fuska ya harareshi, amma ya ko kasa tada injin motarsu, sabida mamakin abunda Femi ke furtawa a kansa. Femi bai yi shiru ba ya kara barota da zafi da cewa& ."

" Dubi dai yadda haskensu ya haske kowacce mace dake giftawa da sunan mace a filin sansanin nan, dubi yadda kyawunsu ya dallare kyawun kowacce mace dake giftawa a wajen nan da sunan mace."

"Duk da cewa cikin dauda suke, datti da rashin gyara amma dube su tamkar wasu taurari dake walainiya a tsakanin daruruwan taurari don haske, yarinyar sai ta zama tamkar mafi hasken cikin taurarin, wato tauraruwa Zahrah& .. ."

"Zuwa yanzu Mr. Yassar ya kai makura wajen fusata da rashin kamun kan Femi, a ganinsa wannan zubar da girma ne da rashin shin kamun kai Femi yake tayi ba komai ba, yace a matukar hassale."

" Femi& Please, Be yourself. Maintain"

the decorum of humanitarianism!!!

"Na rantse idan ka sake yimin maganarsu bazan daukeka a motar nan ba, saidai ka karasa Gusau da kafafunka, ko ka hau motar haya ka koma Hotel ."

"Femi nata dariyar mamakin rikicewar Ogansa akan  yan maganganunsa akan su Keltouma, wadanda shi yayisu ne kawai don tsokana da raha, amma yadda yaga Oga Yassar ya maida abun fada ya saka shi dariya matuka. Cikin afi da hurwar neman afuwa yace,"

" Tuba nake Sabbeni, na bari! "

**** **** *****

"Wani abu kuma da yazo ya rikirkita nutsuwarshi a jefa shi a damuwa ta babu gaira babu dalili shine yadda yake yawan tunawa da maganganun da abokin aikinsa Femi yayi masa akan Keltouma, gashi dai Femi yayi cikin raha da tsokana ne irin nasa, kuma tuni shi Femi ya manta anyi, amma me?"

"Shi maganganun sun tsaya masa a rai matuka gaya sun ki wucewa a cikin kwanyarsa. Haka kawai koyaushe ya kebe kansa don yin wanka ko barci ko wani aiki sai maganganun sun fado masa a rai, wato maganganun Femi akan Keltouma sai yake ta ganin cewa duka gaskiya ne, duk da cewa shi"

"Femi ya fada ne don ayi wasa da dariya irinta abokai samari  yan bana bakwai duk da ya san Mr. Yassar bai san wasa ba shi, babban abunda yafi sukurkuta nutsuwarshi da Femi yace wai ya lura baida lafiya tunda bashi da feelings akan mata."

"Sai yake tambayar kansa shin da gaske ne maganar Femi, cewa bashi da lafiya? Tunda shima kansa ya san bashi da feelings akan kowacce mace???"

"Ammih da kanta ta taba yi masa wannan zargin, ta tambayeshi ya fada mata gaskiya ko bashi da lafiyar maza ne duk matar da ta kawo masa komai haduwarta sai ya kauce yace baya so?"

"Bai manta amsar da ya baima Ammih a lokacin ba, cewa yayi,"

 nima ban sani ba Ammih! .

"Sannan a hankali sai ya dawo yake ta ganin gaskiya a sauran maganganun Femi, wadanda a baya ya kalla a matsayin shirme da Rashin kamun kai, cewa da Femi yayi wai; Akoken nan taka idan taji wanka da wanki, mace zata koma har mace (ta sakawa a gaban Elantra dinka ce)."

"To duka yanzu dai ya yarda da maganganun Femi, amma a ransa kadai, sai ya ga kamar maganganun Femi sun bude masa ido ne ga abunda shi sam bai ankara dashi ba sai yanzu da ya nutsu yaketa digesting dinsu, ya yarda Allah yayi halitta a tareda Keltouman Ummami, irin halittar da ba duka mata Allah yake yiwa ba."

"Haka kawai duk sanda ya tuno yawan koke-kokenta, da yawan share ido da take yi da bayan hannu, ko gefen dukunkunannen gyalenta, ko fyace hanci da take yi idan tana kukan da gyalenta, cikin yanayin shagwabarta ta halitta, duk sai ya samu kansa da daburcewa wani lokacin harda yin dan murmushi ba tareda ya san yayi ba, duk ya kasa sukuni da wani munafikin nishadi yake ziyartar zuciyar shi a duk lokacin da ya tuno fuskarta da jikakkun idanunta, domin kwarai kukan da shagwabar, da share idon, wani irin kyau suke yi mata matuka, su fiddo zahirin zallar kuruciyarta fili."

"A fili Yassar ya furta sunan da a yanzu zuciyarsa ke tunawa, sunan da ya dade da"

"yanka mata ragonsa, sunan da a ganinsa shi yafi dacewa da ita ba sunanta na yanka ba."

"Sunan da babu abunda yafi yawan tunawa yanzu, duk sanda ya kebe kansa don yayi barci ko wanka, ko wani muhimmin aiki sama da shi, tun daga ranar da ya saka mata sunan ba abinda zuciyarsa ke yawan tunawa sai shi, da shagwababbiyar kyakkyawar fuskarta, daga inda yake zaune a lokacin ya mika hannu yana shafo tarin lallausar sumar kansa ya damke daga sama har kasa, sannan ya yafito sunan da karamin sauti, daga can kasan makoshinsa yace."

 A-ko-ke! .

"Da haka tunanin sa ya cigaba da zurfi yana ninkaya da nisa akan  Akoke , yana darsa masa wani abu mai dadin da baya fasaltuwa a kasan ransa, wasu abubuwa da bai taba sanin zuciyarsa na kunshe dasu ba, sababbin feelings ne da bai taba ji akan mace ba, suketa narkewa kamar dalma a zuciyarsa, yana danganta duka maganganun da Femi yayi da karan kansa da Keltouma."

"Ya tambayi kansa to ko dai Femi yana nuna masa hanya ne kawai a fakaice? Tunda ya zama makaho bai san abinda ya dace ba? Yana ce masa ya gyara wannan yarinyar ya aureta mace ce har mace, da zai duk yiwa irin tarbiyyar da yakeso ta mike da ita ba tareda wani da namiji ya riga shi shiga rayuwarta ba? Femi yace Keltouma, (inka dauke annakiyar daudar da rashin wankanta) mace ce har mace data isa manyan maza kamarsa su aureta?"

"To amma saboda Allah meyasa sai ita? Zuciyarsa tayi masa adalci? Ace duk matan duniya da ya baro a gida da waje, ba wadda tunaninsa ya taba rayawa ta dace dashi da zama mata a gareshi sai wadda ke cikin dauda (datti),  yar gudun hijira da ko asalinta bai sani ba?"

"A hakan kuma gangar jikinsa na cigaba da karbar wani sabon sako game da ita, zuciyarsa kuma na azarbabin amshewa ba tareda ya sani ko ya ankare ba."

"Yau da Ammih tayi masa waya da daddare take gaya masa ga Ziyadah nan tazo Sokoto hutun summer, (ita Ziyadah family friends suke dasu, diyar abokin aikin Abbih ce"

"Amb. Mahmud Shinkafi), Ammih tace cikin kwantar da sauti saboda sanin hali."

" Ziyadah tace tana so zata kawo maka ziyara a garin da kake, ka bani adireshin wajen naku in bata. Duk da cewa ita a Sokoto ta sauka. Amma tace dani zata yi tattaki tazo har Gusau saboda ta ganka ."

"Yassar kamar zaiyi kuka ta wayar saboda atake yaji wani irin bacin rai yazo ya lullubeshi, kamar yau ne rana ta farko da Ammih ta fara jona masa mata, don yadda ya marairaicewa Ammih, harda cewa ya gaji da ture-turen  yammatan da take masa, har yanzu da baya gida ma baza a kyaleshi ba, har wajen aikinsa sai an biyoshi dasu sansanin  yan gudun hijira? "

Ammih tace  na bari .

"Ita Ammih a tunaninta ta haka ne zai ga wadda tayi masa a cikinsu har ya kyasa yace mata yaga matar aure, in yaso daga nan ita kuma sai tayi magana da yawunsa, don Ammih ta riga ta saka a ranta jan ajinsa da halinsa na son girma a idon mata shine bai barinsa iya kula  yammata da sunan neman"

"soyayya har yau, tunda dai ta tabbata lafiyarsa kalau."

"Shikuma ya san idonsa bana kallon  yammata bane a halin yanzu, na son ganin duk marassa galihun dake kasar nan, (musamman  yan gudun hijira) sun samu shelter daidai misali ne."

Idonsa bai iya kallon kowacce mace da soyayya da kauna ba bayan ita Ammih data sunkuya tayi yunkuri ta kawo shi duniya.

"Saboda idonsa baya kallon kowacce mace da wata manufa, balle ya kai ga developing feeling ko wani special interest akansu, yace."

 Ammih! Please in rokeki alfarma. Ki yiwa Allah kada ki aiko min kowa nan.

"Gashi ni ba a Gusau nake wuni bama, a wani surkukin local government dinsu ne wai shi  Anka ."

Barci ne kadai yake kaini Hotel dinmu a Gusau.

"Ammih a irin ayyukan dake gabana, bana bukatar ziyarar kowa nan kusa, don Allah Ammih kimin alfarma har na gama project dinnan na dawo gida, kada ki turomin kowa ."

"Ammih dai ba haka taso ba, amma jin ya bata ranshi sosai da albishirin zuwan Ziyadah data yi masa, yasa tace  tunda dai nace na bari sai ka bar rokona ko? Daga haka dole ta canza akalar hirar tasu da wata dabam, ta kyaleshi da zancen Ziyadah."

**** **** ****

"Da yammacin ranar wata Asabar ya samu kiran waya daga Baba Ado, akan hanyarsa ta komawa hotel dinsu."

Duk da cewa Baba Ado ya saba yana kiranshi a waya lokaci-lokaci tun daga lokacin da ya mallaka masa wayar hannu. Don kawai su gaisa suyi hira su tattauna rayuwa. Amma yau a muryar Baba Ado damuwa ce tsantsa.

"Dagawarsa keda wuya sai yaji Baba Ado yayi sansanyar ajiyar zuciya, kafin yace."

" Muhammadu Yassar, zaka iya zuwa Tambuwal gobe? "

Girgiza kai yayi yana ce da Kakan nasa cikin sigar wasa na Kaka da jika.

" Idan nazo me zaka bani? Nasan na sake nazo gidanka koren magani zaka kulleni a soro ka bani ba wani abu ba, ni kuma ka san ba son jike-jiken nan naka nakeyi ba. Amai yake saka ni, in kuma ba so kake in kwararo maka shi a kan buzun ka ba ."

Cike da kauna da lallashin jika Baba Ado yace  to me ac-ciki don kayi kumallo a shimfida ta? Ai ko a jikin malun-malum dina ne kayi amai babu komai .

"A karshe ya dage lallai Yassar ya zo, har yana ce masa da gaske maganin tsarin zan baka ka canka daidai, inma kayi amansa ai dole ya kasance wani kadan ya sulala ya shige cikin hanjinka ."

"Yassar ya dade da sanin rigimar Baba Ado akan bashi maganin gargajiya, amma yanzun tsaka da aiki suke, ta yaya zai ce lallai ya bar abinda yake ya kamo hanya a gobe haka kawai bai shirya ba yaje Tambuwal, ba kuma tareda wani kwakkwaran dalili ba, ya san kuma dole yayi dare a hanya, tunda dole yaje a ranar ya dawo a ranar, tunda litinin akwai aiki sosai a Camp."

"Kodayake dama jefi-jefi Baba Ado ya saba yi masa hakan tun zuwansa Najeriya, haka kawai sai yace dashi ya shigo Tambuwal don kawai ya bashi tofin addu a, ya kan ce baya jin dadin mafarkan da yakeyi akan jikan nasa YASSAR a dan tsakaninnan, don kusan kullum Baba Ado sai yayi mafarkinsa rike da jariri yanata kuka."

Wannan mafarkan ne suka sa hankalin Kakansa Baba Ado yaki kwanciya. Don a tunanin Baba Ado mayu ko miyagu ne ke son kama masa jika daga zuwansa aiki kasar Najeriya.

"Shikuwa a rayuwa me yake dashi da zai iya sakawa Yassar dimbin alherinsa da kulawarsa gareshi bayan tsayawa wajen ganin yayi masa addu a da neman masa tsarin jikinsa daga sharrin zamani dana miyagun mutane? Bai haifi Da a duniya ba, amma ya san Yassar jikansa ne, wanda Allah ya halitta daban cikin zuri ar dan uwansa Jalloh Ahmadu, domin ya zama inuwa kuma sanyin idaniya daya tal a gareshi."

"Ba yadda ya iya da rigimar Kakannasa Baba Ado, haka washegari Lahadi ya shirya ya"

"kama hanya shikadai a motarsu  Hilux don tafiya Tambuwal, amsa kiran Baba Ado."

Ba yadda Femi bai yi dashi ba kan yana son ya bishi ya raka shi daganan yaga garinsu na asali amma yaki.

"Yace shi baya son tafiya tare dashi a mota yana cikashi da surutan wofi, daga ranar da yayi masa magananganu akan su Keltouma Yassar yake avoiding hira dashi kuma yace ya daina yawo dashi ko ina har su koma U.S."

"Femi bai ji haushi ba saima dariya da yayi tayi, kafin ya kada kai ya buda hannuwa irinna ko a jikinsa, yace."

 Babu damuwa Boss. Ina nan dai ina zuba ido .

"Bai gane me Femi yake nufi da yana nan yana zuba ido ba, don haka yana kokarin shiga mota ya juyo ya dan dubi Femi din, yanayin fuskarsa na nuna rashin fahimta da neman karin bayani akan maganarsa, sai Femi yace."

" Eh mana, ina nan ina ta zuba idon ranar da wata mace zata kayatar da zuciyarka. Ko ka daina yimin kallon mayen mata, inata addu ar Allah ya kawo wadda zatayi min wuf! Da zuciyar nan taka Boss. Don from all indications Oga Yassar lafiya kalau yake."

"You are just choosy, ina nufin, nan kusa ba kowacce mace ke burge namiji irinka ba. zaka dade baka samu wadda tayi maka ba, amma idan ka samu din kafi kowa iya soyayya da mayatar son mace. Amma banda haka mata ai abokan rayuwa ne, duk wani jin dadi na rayuwa saida su, duk wata nutsuwar namiji duk ilminsa, kudinsa ko mulkinsa bata tafiya daidai sai da su a gefen hakarkarinasa, kai ne dai har yau baka dandana ni imominsu ba, balle kasan tarin alfanunsu."

"Idan kuma matar aure akayi maka a kauyen naku zaka je zance, shiyasa kaki yarda in bika, to ina nan dai ina zuba ido! ."

"Tsaki Yassar yayi, shirmen Femi yayi yawa, sannan ya shige motarsa ya kunna, yayi ribas, bai san yaushe Femi zai daina shirme akan mayatar mata ba, ya girma bai san ya girma ba, sannan ya sauke gilas ya dan zuro kansa waje, yace da Femi."

 Allah yayi maka maganin matsalar dake damunka Femi idan mai magantuwa ce.

Ace mutum bashida wata matsala kullum sai maganar MATA? Mata dai mata dai kawai Femi? Kuma haka kake tsammanin kowa ma irinka ne?

"A shekaruna na wuce a yimin auren kauyenmu, ko auren zumunci a garinmu yadda kake cewa. Ka cigaba da dauka na

Please Login or Register in order to submit comment