gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 1 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://arewanovels.com ÿþKELTOUMA

1



Sumayyah AbdulQadir



07030137870 (whatsapp only)

takorikabara@gmail.com

GARGADI DA TUNASARWA

"Labarin dake cikin littafinnan da duk abinda ya kunsa kirkirarre ne, kuma kagagge. An rubuta domin fadakarwa da nishadantar da mai karatu. Ba a yi shi domin cin zarafin wani, ko wata ba, ko wata kasa ko wani jinsi ko yare na wata al umma ba, don haka idan kaji wani abu a cikin labarinnan; suna ko gari, ko sunan kabila ko wata kasa da yayi kama da naka to arashi ne kawai aka samu irinna fiction. Gabadaya sunayen jarumai, garuruwan cikin labarin da yanki da akayi amfani dasu duka bana kowa bane, kintace ne kawai da hasashe na marubuciyar, an sanya ne kawai domin kayata labarin da armasa shi."

"Ba a yarda wani ko wata, ko wata kungiya ko kafar yada labarai ta karanta shi a wata kafa ta sadarwarta ba tareda rubutaccen iznin marubuciyarshi ba."

"Yin hakan karya doka ne, kuma abinda zai janyo tuhuma daga dokar shari ah ta"

hakkin mallaka. Fatan alkhairi ma duk makaranta littatafan TAKORI.

-SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)

1/1/2026

SADAUKARWA

"LABARIN  KELTOUMA SADAUKARWA NE GA DUKKAN  YAN AREWACIN KASATA NIJERIYA, WADANDA SUKA SAMU KANSU DA YIN KAURA DON NEMAN MAFAKA GA RAYUWARSU (GUDUN HIJIRA) SANADIN IBTILA IN TA ADDANCI A KO INA SUKE A FADIN KASARMU MAI ALBARKA, NAJERIYA."

-SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)

1/1/2026

TAKORITES

"Kafin mu fara ina mai farin cikin tallata muku kayan abincin LAZEEZUN na Haj. Aishat Aliyu Sabuwa, Kaduna. Mai kamfanin Lazeezun Venture and Global Services. Khairan Lazeezun mai garin Danwaken Lazeezun mai dadi da gamsarwa, garin kunun Lazeezun mai gardi da dakakken Yajin Lazeezun mai dadin dandano."

"Kayan nan na LAZEEZUN ina baku tabbacin daban suke da duk wani kalar garin danwake ko garin kunu ko dakakken yajin da kika sani, ni din dai tested ce, kuma trusted ce akan kayan LAZEEZUN. Na ci na yaba nida iyalina shine nace bazan ci dadin nan nikadai ba tare da na tallata muku Khairun Lazeezun ba."

"Kayan danwaken Lazeezun da garin kunun Lazeezun da yajin Lazeezun suna nan suna ratsawa a wasu daga supermarkets din garuruwan Abuja, Kano, Maiduguri, Kaduna kai"

"har Janhuriyyar Nijar, a yanzu haka garin danwaken Lazeezun da garin kunun lazeezun da yajin lazeezun sun fara tsallakawa har ketare, sun isa UK, Dubai, Egypt, da Saudiyyah, kawai ki tuntubi Haj Aishat Aliyu a wannan lambar waya (08030802900) daga duk gari ko kasar da kike don dandana Lazeezun dinmu mai dadi."

Ban fada muku abinda ban ci naji

ba!!!

Madallah daku.

Takorinku.

SHIMFIDAR LABARIN

ZURI AR MARIGAYI GRAND KHADI



"uri ar Marigayi Alkalin Alkalan Tambuwal, wanda ake kira  Grand Khadi , wato Alkali Jalloh Ahmad,"

"wata fitacciyar zuri a ce sananniya, mashahuriya, kasaitacciya, kuma hamshakiyar zuri a mai fadi da girma a garin Sokoto-Birnin Shehu."

"Sau da dama in ana bada tarihin zuri ar Jalloh Ahmad, zaka ji ana buga babban misali da tsananin hadin kansu, son juna, da kaunar junansu, har ila yau, ana bada kwatance dasu da irin kyawun surar da Allah yayi musu mazansu da matansu."

"Allah ya albarkacesu da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsu. Alal misali, tun a zamanin da can, an san duk inda zuri a mai fadi da yado take (extended family), to dole ake samun hatsaniyar zaman tare na yau da gobe, da yawan sabani, kyashi, hassada, gutsuri  tsoma na  yan ubanci ko makamantansu a"

"tsakanin mambobin wannan family, matansu ko  ya yansu, ko faccaloli, to amma yawancin wadannan matsaloli babu su a zuri ar gidan Alkalin Alkalai."

"Anyi ittifakin cewa su zuri ar Jalloh sun baiwa irin wadannan kananan matsalolin baya, basa nuna  yan ubanci ga junansu, koda ace suna yi din, toh da hankali da tunani da ilmi suke yin nasu, wato bana kyashin juna ko hassada bane a ah, na rige-rigen samun cigaban rayuwa ne."

" In baka yi bani wuri in wuceka (a neman ilmi da neman na kai) shine abinda Jalloh suka sa a gaba. Zamantakewarsu ta yau da kullum mai ma ana ce kwarai da gaske, sannan abar sha awa da burge kowa da ya sansu ko yaji labarinsu."

Akwai fahimtar halin juna na hakika da kuma girmama juna tsakanin zuri ar Jalloh Ahmadu. Babba da yaro kowa ya rike matsayinsa.

"Duk da cewa  ya yan Grand Khadi, sun fito daga cikin iyaye mata daban  daban, wato gidane da aka fifita POLYGAMY, aka auri"

"mata har hudu rus! Aka kuma yi rayuwa tare, rayuwa irin ta ga baki ga hanci (tsakanin dakunan matan gidan na wannan na kallon na waccan, kitchen din gida gabadaya guda daya), kuma kowacce data zo ta haifi nata yaran gwargwado, a karkashin inuwar auren adalin miji daya tamkar da goma a gun matansa, mutum mai tawadi u da wanzar da adalci da kyautayi a tsakanin matansa."

Kokari Grand Khadi lullum shine ya tabbatar da farin ciki da hadin kai a tsakanin iyalinsa.

"Matan Grand Khadi Jalloh hudu babu wacce bai haihu da ita ba; uwargida itace Inna Jari wato (Jarin gida), Yaya Suwaiba ta biyu, sai Hajja Badejo, da ya auro daga Wurno, da amaryarsa Haj. Hadiza da kowa a gidan ke kira (Maman Nasiba)."

"Zaman lafiya da hadin kan da ake dashi a wannan family din, ta ko ina ka hanga ka duba sai kaga bazai rasa nasaba da kasancewar kusan duka iyalin Jalloh Ahmadu, ilmin addini ya wadacesu ba."

"Allah yayi ahalin Jalloh masana ilmin Al-qur ani ne, sannan mafi yawansu ta fannin"

abun duniya zamu iya cewa mawadata ne ko masu babban rufin asiri.

"Ba ga ilmin addinin kadai Jalloh suka yi shuhura ba, har da na zamanin, shi yasa ake zaune lafiya a wannan babban gida."

"Kowa ka gani a a zuri ar Jalloh yanada abin yinsa kwakkwara, kusan har ya zarta dan uwansa abun yi da rufin asiri, da wuya ka gane wanda yafi wani nasibi a cikinsu, don basa barin dayansu yayi kukan babu (ya nemi komai ya rasa), ba tareda sun yi gangami da hobbasa sunyi rige-rige wajen agaza masa ba."

"Kenan tunda abubuwan da ke haddasa fitina a yawancin (extended family) zuri ar Jalloh duk sun basu baya; kamar rashin abun duniya, da rashin taimakawa juna, rashin ilmin addini, rashin abinyi da sauransu sai ya zamana nasu nakasun shine  competition (gasa da juna), wanda ke faruwa a tsakanin  yammatan family din kadai, don samarin zurri ar duka masu dattaku ne da halin girma, (amma babu manyan matsaloli irinsu hassada ko kyashin juna)."

"Misali, a tsakanin  yammatan Jalloh family, kowacce naso ace tafi  yar uwarta iya ado na fita tsara, ko tana so ace tafi sauran iya"

"gayu da iya karkata daurin dankwali, da iya shiga (dressing) mai burgewa, ko son ace tafi sauran  yan uwanta yawan kayan kwalliya masu aji. Don kwalisa kam! Wannan kowa ya shaida a jinin  yammatan gidan Jalloh take."

"Iyayensu maza duka cikinsu daya. Wato Jarin gida ce ta haifi manyan ya yan Alkali Jalloh, wannan ya kara taimakawa wajen haduwar kansu, don kowanne shi ke da fada aji a gidansa, kuma abinda babba ya yanke dole na kasan su bi."

"Mai bin Jarin gida a matan gidan wato Hajiya Suwaiba, daga zuwanta ta fara da haihuwar mace, itace babba a  ya ya mata, wadda ita kadai tayo gadon Grand Khadi ta fannin profession; Alkaliya Shafa atu Jalloh kenan (Justice Shafa atu), da suke kira (Yaya  Yar Dada)."

"Inna Badejo kuma da aka auro a bayan Suwaiba tazo ta haifi auta a  ya ya maza, daya tamkar da dubu watau Baffa Attahiru."

"Haj. Hadiza wato Maman Nasiba itace uwa ga autar gidan gabadaya mai suna Nasiba Jalloh, tana aure a Mubi. Maman Nasiba itace amarya a cikin matan Grand Khadi Jalloh Ahmad."

**** **** ****

"Grand Khadi Ahmad Jalloh, ya rayu tsayin shekaru 77 a duniya, kafin Allah ya dauki ransa, don haka shi ya raini yaransa duka, suka taso a gabansa, yayi musu duk irin tarbiyyar da yake so su tashi da ita, wadda a halin yanzu ta zama abar kwatance take kuma baiwa kowa sha awa, har ake buga misali da ita ta fannin hadin kai da kaunar juna."

"To bayan rasuwar Grand Khadi, abubuwa sun cigaba da gudana babu dadi, don babu jimawa Jarin gida ma ta bishi daga  yar gajeruwar jinyar ciwonta na Asma."

"Hakika Jarin gida da Grand Khadi, an yi doguwar rayuwa mai albarka, an kuma bar zurri a mai nagarta, ilmi da cikar tarbiyyah, an bar baya mai kyau, da zuri a mai dada fadada da yaduwa kullum."

"Sauran matan Grand Khadi kuma da yake da sauran kuruciyarsu ya rasu, bayan gama takabarsu duk sai suka koma gaban iyayensu suka sake aure, a garuruwan da suka firfito mabambanta."

**** **** ****

"Tunaninshi ya cigaba da nausawa yana zurfafa akan zuri arshi da kakanninshi, a daidai lokacin da jirgin da suka shiga na (Air Mexico) shi da abokan aikinsa biyu ya fara kokarin motsawa don barin kasar ta Mexico."

"Wato tunda ya zauna a kujerarsa, aka ambaci cewa jirgi ga inda zai tashi dasu wato kasar shi ta gado  Nigeria , sai ya zama babu abinda yake shiga cikin ransa da kwakwalwarsa a lokacin sai tunanin asalinsa, with nostalgia kwarai yake tunanin. Ya shiga tuno tarihinsa dana ahalinsa baki daya (iyaye da kakanni). Wasu labaran ma na zuri arsu da suke shigowa cikin tunaninsa a yau, da yawa a bakin Abbih yake tsintarsu, don ba a haifeshi ba lokacin da wasu abubuwan da yawa suka faffaru."

"Iyalin Jalloh Ahmadu Tambuwal kenan nake baku labari! Banda kasancewarsu sanannen family a garin Sokoto, to masu dauke da Tutar Uthmaniyya ne, wadanda tarihinsu ya nuna Kakannin-kakannin Grand Khadi, suna cikin Birnin Shehu lokacin da aka kafa daular Uthmaniyya, kuma suna da alaqa ta jini sosai da  Sultanate of Sokoto ."

"Don haka zuri arsu ta Alkalin Alkalai Jalloh Ahmadu, wani family ne da a ko ina ake ganin kima da martabarsu a Sokoto da makwabtanta."

"Ba kuma don tarin arzikin su ba, ko don sun tara  ya ya da dukiyoyi sai don tsarkin nasabarsu, da girman matsayin asalinsu da ake gani, da tsarkin tushensu."

"Ta fannin sana a, yawancin iyayensu manyan  yan kasuwa ne, a fanni daban daban na kasuwanci."

"Kasancewarsu jinin sarakunan Musulunci, hakan bai hanasu yin karatun boko mai zurfi ba; manya da yaransu in ana kure ilmin boko to sun gama kureshi, ba don su dogara dashi ba, sai don amfaninsa na zahiri ga rayuwar yau, tunda sun fi baiwa kasuwanci muhimmanci."

"Allah ya albarkacesu da tarin zurri a na  ya ya maza da mata. Kusan kowa a cikin  ya yan Grand Khadi ya hayayyafa da yawa, don suma  ya yan na Grand Khadi duk sunyi gadon mahaifinsu wajen aure-aure, basa taba auren mace daya sai biyu ko uku ko hudu,"

"Polygamy (auren mace sama da daya) yana cikin tsarin rayuwarsu, wanda a cikinsa duk suka taso, aka kuma sansu akansa."

"Muhammad Jalloh, wanda ya kasance (Da na biyu) a gidan Grand Khadi, shine kawai ke auren mace daya tamkar rai! Wato Abbihnsa! Mahaifinsa duk a ya yan Jalloh ya fita daban; tun daga akidarsa, tunaninsa, da halinsa, duka sun fita zakka dana sauran  yan uwansa."

"Sabida shi tun asali Abbih wani irin dan boko ne, da sau tari shi da kansa yake tsokanar Abbih da cewa  Abbih bokonka yayi yawa ."

"Manyan  ya yan Grand Khadi maza sune mahaifinsa, Ambassador Muhammad Jalloh, wanda ya biyo Yaya Babba a haihuwa, wato shine Da na biyu a  ya yan marigayi Grand Khadi da Jarin gida."

"Babban gidan shine Alhaji AbdulQadir Jalloh Ahmad, wanda tsohon gogaggen  Oil Mogul ne (Yaya Babba kenan) kamar yadda kafatanin zuri ar ake kiranshi."

"Tun bayan rasuwar Grand Khadi, Yaya Babba, ya hada igiyar family dinnan a hannunsa ya rike da gaskiya da amana,"

"Sukuma kannen sai suke masa biyayya kamar mahaifinsu, sai abinda ya zartar kowa ke bi, sai abinda ya bada umarni za a aikata gabadaya."

"Abbihnsa nada kanne biyar; Abdulqayyum Jalloh, AbdulWahhab Jalloh, da Haj. Shafa atu Jalloh (Yaya  Yar Dada), Barrister Nasiba Jalloh (auta a mata) sai autansu a maza Quantity Surveyor ne (QS Attahiru Ahmad Jalloh) wanda yaci sunan Sarkin Musulmi Sultan Attahiru, suna ce mashi Baba Sultan."

"Dukkansu dinnan suna zaune da iyalansu cikin birnin Shehu, sai ko Nasiba dake aure a Mubi, in ka cire nasa mahaifin babu wanda ya tsallake ya bar gida kasar Nigeria, shima Abbih ya bar gida ne sanadin yanayin aiki irin na diplomasiyya."

"A takaice wannan shine tarihin Kakanninsa da iyayensa gabadaya. Tarihin da yake ta tilawa cikin kwakwalwarsa, tun shigarsa jirgi yau."

"Jirginsu ya fara kartar kasa zai bar Mexico, tsayin wannan lokacin ya duka yayi nisa a duniyar tuna zuri arsa da kewar iyayensa."

"Dalilin shigowar tunanin nan cikin kansa, bazai rasa nasaba da kasancewar inda ya taho din gida bane, Sokoton da ya jima bai ziyarta ba. Suna saka ran Insha Allahu nan da awanni goma sha biyu da  yan mintuna, zasu yi landing a garin Kano, inda daga can zasu sake hawo wani jirgin zuwa Sokoto."

**** **** ****

OFFICIAL SOJOURN

"Ya jima bai kara yin wata tafiya ta aiki wadda in yaje zai dade a tafiyar ba, tun bayan kammala wancan project din na baya inda suka kai tallafi ga mata da kananan yara bisa annobar yunwa data afka a kasar Tanzania."

Project din da saida suka share tsahon watanni uku suna aiwatar dashi ba tareda sun waiwayi gida ba.

"Sai a wannan shekarar, da kungiyarsu (UNICEF) suka kara ankara da hazikancinsa, da kuma irin jajircewarsa da gogewarsa akan ayyukan jin kai (Humanitarian Space), tun bayan nasarar da ya samu na kammala wancan project din da karin girma a Tanzania. Tofa shikenan tun daga wancan lokacin kungiyar tasu ta UNICEF suka sako shi a"

"gaba; ma ana kota ina wani aiki gwaggwaba (mai tsoka) dake bukatar kwarewa, jink an talakawa da sadaukar da kai yazo; a gaba- gaba suke sanyashi ya jagoranta."

"Shima da kansa ya gane UNICEF suna kara janshi a jiki sosai a shekarar nan, don a halin da ake ciki yanzu ya zama shine tauraron da ke haskawa a karbar projects; hazikin matashin ma aikacin da tauraronsa yafi na sauran matasan wajen haskawa a wannan shekarar. Ya zama wanda UNICEF suke ji dashi a cikin kaf! Matasan ma aikatansu."

"Sun jingina shi sosai a jikin manyan harkokinsu yanzu, suna jikashi yadda ya kamata da  projects masu tsoka, ya riga ya zama dan gaban goshin shuwagabanninsu."

"A kokarin (United Nations Children s Emergency Fund) da akafi sani da  UNICEF na samar da tallafin ilmi ga yaran da masifar ta addanci tayi musu sanadin rayukan iyayensu, wani ibtila I ne na rana daya, da yazo ya afkawa arewacin Najeriya wai shi (terrorism; Boko Haram, and Armed Banditry)."

"Babban abinda wannan ibtila I ya haifar, ya shafi rayuwar kananan yara da yawa a kasar Najeriya, sakamakon kashe iyayensu da ake tayi kamar kisan kiyashi a wasu kauyukan na Zamfara, dazuzzukan Borno, da wasu sassa daga biranen Arewa, kai wasu ma har gida ake zuwa akashe iyayensu a lokacin, a bar yaran suna GUDUN HIJIRA ba dare ba rana."

Ta sanadin hakan aka samu  Refugees

( yan gudun hijira).

"Cikin refugees dinnan har da irin wadannan yara kanana, aka barsu da rayuwa mummuna cikin maraici, jahilci, kunci, yunwa, da rashin kulawar kowa."

"Labarin halin da suke fuskanta yazo ga majalisar dinkin duniya (United Nations) cewa akwai yara kanana cikin  yan gudun hijira, suna cikin ragaita ta maraici da cututtuka a wasu yankuna ko sansani da ake kira (sansanin  yan gudun hijira), wadanda a turance ake kira (Internally Displaced People) ko a takaice (IDPs)."

"A nazarin hakan da UNICEF tayi ne tayi wannan

Please Login or Register in order to submit comment