gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 5 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maza dake wucewa ko su Yassar dake tsaye a gefensu suna kallonsu."

"Yassar da Femi duka sun tattara hankalinsu yanzu a kansu. Suna jin yadda Uwar ta fara rarrashinta, har muryarta ta fara dishewa don tsabar lallashin  yar, amma yarinyar nan ta nuna bata jin lallashin da uwar ke mata sam don taki daina kukan."

"Tayi banza ma da uwar taki ko kallonta, zuwa yanzu kukan nata ya koma sheshsheka da ajiyar zuciya."

Iska ta zuqo ma kunnen Mr. Yassar maganganun yarinyar ga uwarta cikin dakushewar muryar kuka& .

Shima da kansa ya shaida a mafi yawan lokuta yana da ji mai karfi ba tun yau ba. Watakila shiyasa har ya iya jiyo me yarinyar ke fadi ma uwarta cikin halin kuka.

" Ummami yau zamu tafi daga nan ko, Ummami ba sai gobe ba ko? "

"Uwar tace  Oh ni, na dauka mun gama wannan maganar tuntuni Keltouma?"""

"""Ni dai Ummami ki yarda mu fita titi ko bara ce muyi, yafi zaman wajen nan tunda kinga ba abinci muke samu ba, in mukayi bara zamu samu kudin mota mu bar garin nan."

"Ummami yunwa ta isheni Ummami, cikina dunkulewa yake yi, hanjina zai tsinke Ummami, don Allah ki yarda mu tafi, rabona da abinci kinga yau kwana biyu, kada muma azo a kashemu anan, ko yunwa ta hallaka mu& .."

Ummami mu tafi daga nan& don Allah

Ummami! .

"Sai yaji uwar ta canza harshe, ko don kar su ji me suke cewa ne oho! Magana take cikin wani yare irin wanda bai taba ji ana yi a duniya ba, abunda ya iya ji kawai a ciki shine cewa da uwar tayi."

" Keltouma am& .! . Sai ta cigaba da magana cikin yaren. Bai kuma san me take cewa ba cikin harshen da take yiwa diyarta, shi ba larabciba shi ba fullata ba, amma ga dukkan alamu rarrashin  yar tata dai take yi cikin harshensu, da lafazi mai dadi da sanyayawa rigimammen yaro irinna Uwa, tana"

"shafa kanta tareda jijjiga kafadarta don tayi shiru duk da girmanta, abun gwanin ban tausayi sannan soyayyar uwar ga diyarta akwai ban sha awa."

"Yassar bai san meyasa ya tafi sosai cikin kallonsu da sauraronsu ba, yayi nisa da sha awar halin kulawa da wannan nitsatsiyar Uwar ke nunawa diyarta. Farare ne sal, su ba fulani ba su ba larabawan kauye ba."

"Amma a hakan farin nasu ya hadu da dauda (datti) duk sun yi duhu sun koma zuwa brown, kamar an shafa musu jar kasa, saboda rashin wanka da rashin ganin ruwa& ."

"Yanata kallonsu bai sani ba ashe daga bayansa Femi yanata yi masa magana cewa ya wuce su tafi, har ya kai ga kada masa yatsun shi a gaban idonsa suka bada sauti  das! . Don ya dawo da hankalin Ogansa gareshi, saboda ya lura Yassar baya tare dashi sam yana ga wadannan mutanen na gefensu, sai Femi ya dafa kafadarsa daga bayansa yana cewa."

" Boss, me kake kallo ne haka? ."

"Sai shima Femi idonsa ya fada kan fuskar fararen matan guda biyu dake tsugunnemanna jikin juna daya na kuka, ya"

gane abinda ya dauke masa hankalin Oga kenan kukan da yarinyar keta yi.

"Femi yace a ransa hankalin Boss na kan yagalgalallun matan nan, masu kama da tsada, saboda gasu jawur dasu, amma ba tsafta. Uwa da  yar ta, ko Yaya da kanwarta ne Allah masani, fatarsu har ta dafe don dauda kamar an shafa musu shuni sabida rashin wanka da rashin wanki."

Femi yace.

" Ha an!, Boss, wadannan watermelon (kankana) sarakan ruwan hawayen kake kallo halan?"

"Ai tun zuwanmu na lura dasu basu da aiki sai kuka, kullum zaka gansu cikin kuka kamar an tsaga kankana, in daya bata yi, zaka samu daya na yi daya na rarrashinta ."

"Yassar bai saurari Femi ba, kawai ya hau takawa zuwa inda suke, kwarai yake son sanin kukan me yarinyar nan take yi haka, da girmanta da komai, ba wai kankanuwar yarinya bace ko yarinyar goye."

"A dai-dai gabansu kadan Yassar ya ja birki ya tsaya, gani yayi yarinyar ta zame kasa gabadaya gaban mahaifiyar tana cigaba da"

"kuka harda shura kafa tana bori irinna kananan yara, abun ya koma sakarci zai ce ko rashin kwaba? Yana jin yadda take cigaba da rokon Maman cikin kuka kan ita dai su tafi titi, suyi bara zasu samu abinci, su bar wurinnan ita bata son zaman wajen& .. zasu samu kudin mota su tafi garinsu idan sunyi bara."

"Uwar kuma nata yi mata yare da lallashi, amma wannan karon da alama ta fara gajiya da rigimar  yar tata, ta fara hadawa da fada-fada, ta hanyar daga murya data soma yi ya gane fada takeyi mata yanzu, ba a dai gane me take ce mata, don cikin yarensu ne take fadan."

"Sai ya samu kansa da yi musu sallama, cikin ladabi yake kallon Maman. Uwar, wadda yaji yariyar ta kira da wani suna wai UMMAMI ta amsa sallamarsa, ba tareda ta dago kai ta dubeshi ba."

"Yassar ya dan russuna (ya rage tsaho) a gaban uwar, amma guiwarsa bata kai ga taba kasa ba, alamu na girmamawa ga wanda ya girmeka, yace."

" Iya sannu koh? Sannu da rigimar ta! . Ta amsa da cewa  yawwa Dan nan, ai inda"

"sabo na rigada na saba da koke-koken banza na KELTOUMA! ,"

 To Iya me ke damunta haka? Ko bata da lafiya ne?

" Ina mai tabbatar maka lafiyarta kalau, damuwa ta sakawa ranta ."

" To Iya a kaita asibiti mana su duba ta da kyau? Shikansa kuka wani zubin yana iya zama ciwo ba a sani ba, ko ayi kokari ayi mata maganin damuwarta ."

"Yassar ya fada bayan yayi musu kallon tsaf, idonsa akan yarinyar da tayi jajawur don kuka tayi dirshan a kasa gaban uwarta, muryarta kamar ta gyare don zaki da iya rera kuka irin mai daga hankalin duk wanda ya ji shi balle  Uwa-mahaifiya ."

" Kayyasa! Lafiyarta kalau nace maka, rigima ce kawai irin tata, ta babu gaira babu dalili, tunda na gaya mata abunda take so bazata samu a halin yanzu ba, sai ta koyi hakuri da tawakkali, kamar kowa dake wajennan ."

"Daga haka, uwar rasa me zata kara ce masa tayi, shima kuma haka."

"Saboda Allah shine shaida; tana bara bakinta don kara cewa wani abu, itama kukan"

"ne zai kwace mata, a rasa mai rarrashin wani, cikinsu itada 'yarta, saboda damuwar da  yarta ke ciki akan bata son zaman wajennan kwarai tana huda zuciyarta."

"Yarinyar kuwa zuwan Yassar gabansu sai ya zama kamar an kara tunzura kukanta, kamar wadda aka shuna mata kashin awaki a hanci don ta kara tunzura. She really needs a listening ear, tana so uwarta ta saurareta ne, ta gane damuwarta ba lallashi take so ba; action take so a dauka akan bukatarta."

"Kukan yarinyar da rashin jin lallashinta ya fara bashi takaici, maimakon tausayinta da ya darsu masa a rai da farko."

"Sai lokacin ya kalleta ta gefen idonsa, mamaki ya kama shi ganin cewa ta kai munzalin da za a kirata 'budurwa' saboda ga kirjinta nan cike da dukiyar Fulani ya tasa sosai ya cika fam, amma take kukan sakarci irin haka, ya sake bude idanunsa waje yana dubanta da mamaki, sai taga tamkar Mr. Yassar harararta yake yi."

"Don haka ba shiri ta juya musu baya, ta ja gyalenta ta rufe rabin fuskarta, ba tareda ta bari sun hada ido da Mr. Yassar ba."

Yassar yace calmly.

" Tashi mana daga cikin kasa? Ki kyale Iya da kukan nan naki haka, you aren't a kid. (Ke ba karamar yarinya bace) ."

"Ganin yarinyar bata motsa ba, Yassar yaji ya fara harzuka da miskilancinta, yace  na tabbata kina ji na, you aren t a deaf, to ina rokonki alfarmar ki tashi daga cikin kasar nan haka, kuma ki bar kukannan, tun kafin ki kaini gejin da raina zaiyi bacin da zamu zo mu saba hali ni da ke."

"Sentence dinshi na karshe ko kusa bata iya fassara shi a cikin kwakwalwarta ba, hausar tayi mata tsauri, kasancewarsu ba hausawa ba. yace  ko baki ganin duk kin bata jikinki da jar kasa? Kina shagwaba haka mara kan gado kamar wata yarinyar goye."

"Alhalin kowa ya dubeki ya san gansamemiyar budurwa ce, wadda ta isa ajiye nata  ya yan a gabanta, amma ba kya ko jin kunyar bara baki kina kuka a bainar nasi? ."

"Sautin muryarsa mai zurfi, da wani irin taushin amo take fita tiryan-tiryan daga makogaronsa, cikin basakkwaciyar hausarshi da bata fita da sauri, amon muryarsa na nuna bada umarni ga sakaltaccen yaro. Kusan zurfin muryarshi da taushinta shi yafi komai"

"dukan dodon kunnenta, har saida jikinta ya dauki rawa bata sani ba, kwarjinin dake cikin muryarsa duk ya dabarbartar da ita, kasancewar Yassar nada  masculine voice ."

"Muryarsa ta mazan Sokoto ce, ga zurfi, ga amo, mai fita da karfin sauti, kuma at the same time, muryar Yassar mai tausasa zuciya ce, mai cike da izzar mazantaka."

"Ala tilas ta maida sautin kukan nata cikin kirjinta, tana hadidiyeshi ta karfi, saboda ga dukkan alamu kiris mutumin nan yake jira ya hambareta, ba don kaifin idon mahaifiyarta ba, tana so kukan ya tsaya a kan dole, sabida mutuminnan da baya lallashi sai fada da bada umarni."

"Amma sheshshekar kukan nata wadda ke fita daga kasan zuciyarta taki tsagaita mata, duk da ta hadiye kukan gabadayansa."

"Ramammun idanunta masu cike da hawaye kadai sun gama fadin halin kuncin da zuciyarta ke ciki, amma duk da haka Yassar ji yake yafi jin tausayin Uwar, fiyeda ita, domin dukkan kulawarta da hankalinta ta tattarasu akan damuwar  yar tata."

"Shi da kansa yasan fadan karfin hali yake mata, amma yana yawan fada a ransa cewa; tabbas duk wanda yake rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira (IDP Camp) dole a mafiyyawan lokuta yayita kuka har ya godema Allah!"

Ba don komai ba sai domin rashin gatan da walagigin rayuwar da suke ciki ya isa! Duk yadda yake jin zai iya fasalta yadda ya riski muni da kaskancin rayuwar IDP camp ya zarce yadda harshensa ko biron mai rubutu zai iya fasaltashi.

"Wannan tunanin ne yasa yaga dole a yiwa yarinyar nan uzuri, wanda da farko ya gaza yi mata, don bai ga dalilinta na yawan kuka tana daga hankalin uwarta ba, ya dawo ya dan sassauta murya a gareta, ganin ta yi shiru yanzu ta daina kukan, amma duk da haka cikin tsuke fuska da hade gira yake cewa."

" Ke kuwa KHULTHUM me kikeso, kike yima Mamanki kukan daga hankali haka, fada min yanzu, ko menene insa tayi miki?? "

Sai a lokacin yarinyar wadda mahaifiyar ta ta kira da suna KELTOUMA ta

"dago jajayen idanunta da sukayi luhu-luhu don kuka, suka kuma kada sukayi jajir don zubar hawaye, sukayi nasha-nasha cikin maikon hawaye, ta saukesu a hankali cikin kwayar idon Mr. Yassar M. Jalloh. Jin wani suna da ya kirata dashi wanda ba nata ba..."

"Shi dai Yassar ya san, tun daga wannan dakikar ne& kaddarar da ya dade yana tsammanin zuwanta ta fara, kuma kaddarar da yake ta ji a jikinsa a tahowarsa Nigeria wannan karon, kaddarar data gayyaceshi gabagadi, ya rufta zuwa ga begen wata zuciya ma abociyar jin kadaici, da tarin kalubale na kuncin rayuwa dana kuruciya."

"Ita wannan zuciyar mai tsananin rauni ce, da yawan kukan neman a saurareta& . Kwarai kaddara ta gayyaceshi yau& . The destiny that invites him to fall for the lonely, challenging, youngish, crying and craving weak soul& "

"Daga wannan ranar, daga wadannan awannin, daga wadannan mintocin na wannan dakikar shi ya san rayuwarsa bata kara komawa (zero tension) dinta yadda take a baya ba."

"Yassar cigaba da kallon inda take durkushe yayi, babu ko kiftawa, wani abu da ya faru unexpectedly kuma unintentionally a lokacin shine haduwar kwayar idanunsu."

"A rayuwarsa bai taba jin irin abinda yaji saukarsa a zuciyarsa yau ba, wani miracle ne mai kama da sukar allura mai tsini da kaifi, al amari daya huda zuciyarsa daga haduwar idanunsu da yarinyar dake durkushe gabansa, wanda yafi gaban ya iya fassara shi, sabida bai taba jinsa akan kowa ba."

"Idanunta masu cike da hawaye suka shige linkif! Cikin nasa, abun daya haifar da tsayawar motsin jijiyoyin jikin Mr. Yassar na wucin gadi. Zanen idanunta mai matukar daukar hankali ne sabida kyan tsarinsu, tamkar shatin zanen kwan Zabo."

"Ya kasance tun fil azal shi ba gwanin kallon mata bane, kallo irin wanda ya wuce ka idar shari ah tun daga yarintarsa har a girmansa baya kallon mace cikin ido ko mahaifiyarsa. Watakila saboda yau yayi wannan kuskuren na kallon Keltouma cikin idanunta shine dalilin da yasa yaji abinda yake ji din, tunda kuwa a zahiri har tsakiyar"

"kwayar idonta ya kalla na  yan dakikai bada niyya ba, sai don ya gargadeta akan ta daina kuka."

"Shiru tayi masa, don wani abu a halayyarta shine itama gwanar iya kyaliya/shariya ce, wato miskila ce ta gaske, musamman idan bata sanka ba, da wuya ta kula ka, ko ta saki jiki da kai, kuma dai bata da amsar da zata bashi a yanzu, tunda bata sanshi ba, bata taba ganinsa a camp din ba sai yau, kuma bai yi kama da ma aikatan IDP irinsu Haladu ba."

"Shi wannan duk da duhun fatarsa sumul yake, tamkar an baro shi daga cikin kwai don sheki da tsabta, gashinan dai kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba fatar jikinsa. A ranta take fadin me take so kuwa?"

"Banda Ummami ta amince su bar wajennan? Ita ko karkashin gada ne su koma da bara zaifi bata farin ciki, fiyeda rayuwar sansanin gudun hijira."

To amma wa zata gayawa ya saurara har ya fahimceta? Tunda uwar data haifeta ma tace rigima ce kawai take yi?

"Ko tanada amsar bashi a wannan lokacin bazata bashi ba, saboda halinta na"

"rashin sabo da mutane, in kaji fitar sautinta to tabbata uwarta kadai take yiwa magana, kukan da takeyi yaki tsayawa balle kirjinta ya rage hawa da saukar da yakeyi na sheshsheka, kallon da Mr. Yassar yake kora mata na gargadi yasa kukan ya sake tunkudowa daga makogaronta har ya rinjayi duk wani kokarinta na son dakatar dashi."

"Ganin halin da kulasu din da mutumin yayi ya kara jefa  yarta sai Uwar ta mike zuruf, kafin tace dashi cikin hausarta da bata cika fita da kwarewa sosai ba."

" Kayi hankuri ka ji Da na? Ka barni nikadai na iya da rikicin KELTOUMA. Kyaleta tayi ta yi tunda bata gajiya. Rikicinta ba mai karewa bane, na riga na saba da koke- kokenta na babu gaira babu dalili."

"Abinda takeso kuma ba zata sameshi nan kusa ba, saboda bazan tafi bara titi da diyar da Monsouru ya barmin amana ba, gara mu zauna anan cikin kulawar gwamnati, har illa masha Allahu."

"Yassar zai kara magana kenan ya ga ba amfanin ya kara ce musu komai, sakamakon"

"bugun kirjinsa har yanzu ya ki daidaita, ya kasa komawa normal tun daga haduwar idonsa dana yarinyar da aka kira Keltouma, kuma ya rasa kalmar sake hadawa a bakinsa, saboda abinda ya fahimta shine uwar bata son a tsawatarwa  yarta akan kukan ko kadan, nan da nan zata amshe mutum da bada uzuri, amma lallai kukanta harda na rashin kwaba da sakalci."

"Yassar na kallo matar ta kama hannun  yarta, ta mikar da ita tsaye, ta hau karkade mata jar kasar data shafa a kayan jikinta da hannayenta na Uwa mai kulawa."

"Kafin yace meye wannan kuma sun bace ma ganinsa, kamar walkiya haka ya nemesu ya rasa a gun, suka barshi a wurin tsaye kamar sabon gunki, suka shige suka kutsa cikin dafifin masu kokawar amsar (hygiene kits). Ba kuma don su yi kokari su samu su karba ba, a'ah, sai don su bacewa idanun  bakon fuskar nan, ga dukkan alamu daga uwar har  yar, duk a tsorace suke da zaman wurin, kai har ma da mutanen wurin bakidaya."

"Juya bayansa dinnan da zaiyi don komawa office, hannayensa duka biyu zube"

"cikin aljihun kaftaninsa, sai yayi ido hudu da Femi da har lokacin yake tsaye bayansa. Gabadaya ya manta tare suke da Femi."

"Nan Femi ya kyalkyace da dariya, bai ce masa komai ba, Yassar yaja tsaki don dariyar Femi taki karewa, ya wuce ta gabansa yayi gaba. Femi yabi bayan sa da sauri suka jera, suna komawa office dinsu."

"Bayan sun shiga ofis sun zauna. A lokacin Haladu ya zo inda yake zaune, Yassar yana kokarin bude system dinsa a kokarinsa na son kawar da tunanin matan nan da ya addabeshi Haladu yazo ya tsaya a gaban kujerar dake fuskantarsa.  Fadi ba a tambayeka ba , sunan da Yassar ya dade da sanya masa kenan wato Haladu. Ya sani sarai Haladu ya zo ne kawai don ya cikashi da labarunsa, da ba sai ka tambayeshi ba, ya hana shi yin aikin dake gabansa. Ya fahimci Haladu irin mutanennan ne masu surutun da ya wuce kima da yawan son jin tsegumi da kawo shi."

Ilai kuwa Haladu na isowa bayan sun gaisa a maimakon ya juya ya kyaleshi ko don ganin

Please Login or Register in order to submit comment