gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 13 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine kawai Ummami ta ce masa; ga asalinsu, wato dai suna da tsarkakakken asali da kyakkyawar nasaba ba tsintattun bisa titi bane."

"Hirarsu tayi nisa sosai yau, har bai san sanda ya fara bata labarin iyayensa da danginsa dake Sokoto ba, kai yau har labarin Babansa Ado, dattijo mai ran karfe da"

tsananin soyayya a gareshi saida ya baiwa Ummami.

"Daga yadda yake bada labarin kansa, Ummami taji a ranta Yassar dan manyan mutane ne, kuma dan babban gida na ilmin addini da boko, da uwa uba arziki da tarbiyyah. Kenan halin kwarai ba a kasa Muhammadu Yassar ya sunkuya ya dauka ba."

"Sanda itama ta shiga bashi nata labarin bata sani ba, labarin da ko Keltouma Ummami bata taba tunanin baiwa shi ba."

Ummami ta soma bashi tarihinsu da

cewa;

**** **** ****

ASALINMU!!!

" Kamar yadda na fada maka a baya sunana Nana Aicha. A gidan mu tun tasowata, kowa da  Aichata ya ke kirana."

Ni da mahaifin Keltouma asali da tushenmu daya wato mun fito daga kabila guda.

"Asalin kakanninmu tarihi ya nuna cewa su ake kira  Larabawan Sahara , ana kiran"

kabilarmu da kabilar  Tuareg . Yarenmu/harshenmu duka na  Tuareg dinne.

Iyayena dana mahaifinta sun fito ne daga wani surkukin jeji dake karkashin karshen yankin garin Arlit.

"Arlit kuma tana cikin wani yanki na kasar Nijar, amma kakannin mahaifiyata sun fito ne daga kasar Somalia."

"Sanin kowa ne Larabawan Sahara bama zama waje daya, muna ninkaya ne a cikin rairayi da hamada na saharar Africa daban daban, domin neman alkaryar da dabbobinmu zasu sake suyi kiwo, ko su samu ruwan sha da abinda zasu ci, amma mu kakanninmu tarihi ya nuna basu cika yin nisa a yawonsu ba, duk yawonsu baya wuce zagayen Saharar Arlit, da iyakar data raba kasar Nijar da Najeriya."

"Iyayena dana mahaifin Keltouma bayan kasancewar tushensu daya, addininsu ma daya ne wato addinin Islama, wanda shine addini mafi rinjaye daya mamaye Sub-Saharar Africa, musamman a kasashe irinsu Sudan, Misra, Chadi, Mali, Somalia, Mouritania da Algeria."

"Inada shekaru goma sha hudu aka wayi gari da karyewar tattalin arzikin kasa, wanda ya jefa al ummar kasarmu cikin halin wata irin fatara da yunwa mai tsanani, da rashin ayyukan yi ga matasa. Wannan matsi/talauci da yunwa wanda karyewar tattalin arziki ya kawo, yafi yawa a yankinmu na jejin Arlit."

"Hakan yasa wasu daga cikin matasan kasar da yawa suka zabi yin hijira (migration) don tsira da kuruciyarsu, da yadda zasu samu abinci da abun dogaro da kai da tallafawa dattijansu da karfinsu ya riga ya kare."

"Hakika yunwa tayi yunwa a wancan lokacin, don hatta rakumanmu komawa sukayi kashi da fata, ko ince kashi da rai. Suka koma babu kuzari da koshin lafiya a tare dasu, daga bisani aka wayi gari Rakumanmu suna kasa tafiya saboda yunwa da taci karfinsu, duk da juriyar halitta irin wanda aka san Rakumi dashi a wannan lokacin suma annobar yunwar ta shafesu."

"Monsour Salihou, na daya daga cikin matasan dake tashen kuruciya da samartaka a lokacin cikin kabilar  Tuareg ."

"Monsour saurayi ne mai zuciyar nema da kula da iyayensa, yana cikin matasan da ake ji dasu a kabilarmu ta  Tuareg ."

Monsour yana daga cikin mutanen da suka zabi yin hijira daga Arlit don neman abinci.

"A wani yammaci yazo ya samu mahaifinsa wanda dattijo ne sosai mai kusan shekaru tamanin, ana kiransa Modibbo Salihou, ya gaya masa shawarar da ya yanke ya kuma nemi yardarsa, albarkarsa da addu arsa kan yana son tafiya ci-rani."

"Modibbo Salihou yace da dansa Monsour  kaima ka san bazan hanaka ba, amma bisa sharadin na yi maka aure, in yaso sai ka tafi tare da matarka ko ina zaka je, har zuwa sanda zaka juyo gida ."

Monsour bai shirya aure a lokacin ba amma baida zabi banda amincewa da sharadin mahaifinsa don ya barshi ya shiga duniya ci-rani.

"Ba a kwana ba, a ranar saida Modibbo Salihou ya dangana da gidan mahaifina Malam Tajo, ya nema ma dansa Monsourou aurena a hannunsa."

"Nida Monsour makwabta ne, gida uku ne tsakanin gidan iyayena da nasa, a lokacin ina hannun kishiyar mahaifiyata Iya Tinau, mahaifiyata tun ina karama ta rasu ta barni a hannun Tinau har girmana."

"Mahaifina yanada  ya ya da yawa da Tinau, amma nikadai ya haifa tareda marigayiya uwargidansa wato mahaifiyata."

"Idan maganar kyau ake, ni Nana Aicha daban nake a  yammatan kabilar Tuareg gabadaya na dararma sauran tsararrakina, kyawuna har buga misali dashi ake a garinmu; sai kaji ana cewa (gata da kyawo kamar Aichata) haka nake tun ina karama da wani irin kyawun surah na halitta dana fuska da kowa ya ganni sai ya tanka."

"Sati bai kare ba saida aka daura aurena da Monsour akan sadakin Rakuma biyar, inda Monsour ya kasa samari bila adadin alfarmar ana girmama Modibbo Salihou a kabilar Tuareg gabadaya ba wanda yayi jayayya da dansa da yazo daga baya."

"Bayan aurenmu da sati biyu yace da mahaifinsa yana so zai tafi kamar yadda sukayi alkawari, Modibbo yace bai yarda ya barni a gida ba sai dai ya saka ni a gaba mu"

"tafi zuwa duk inda zashi, saboda yasan baida ranar dawowa sai ranar da Allah ya nufa. Monsour ya amince. Modibbo yayi mana addu a muka bi ayari."

**** **** ****

"Ayarin matafiyan nan sun fito ci rani daga saharar Arlit, ba tareda sanin inda suka nufa ba, kai ko inda zasu je basu sani ba, sun dai fito ne da niyyar sai inda mai ya kare musu, zaka yi mamaki in kaji cewa matafiyan dake cikin ayarin gabadaya basu mallaki komai a tare dasu da sunan guzuri ba, sai arzikin dogayen ramammun Rakumansu, wadanda sune kadai kadararsu sai dan ruwan shansu a battocinsu rataye a wuyansu."

"A haka suke tafe bisa Rakuman, idan sun gaji sai su sauka su cigaba da tafiya da kafa, suna jan ragamar Rakuman, har zuwa sanda suka fita daga saharar Arlit gabadaya."

"Nonon Rakuman da cukwi da ruwa shine kadai abincinmu, har muka yi nisa da Arlit muka cigaba da nausawa cikin Sahara."

"Koda aka zo boarder sai wasu daga cikin mutanen ayarin suka zabi rarrabuwa, suka watsu cikin kasashen Africa daban-daban,"

"inda mafi yawa suka nufi kasar Cameroon, wasu sukayi Ghana, wasu Benin Republic da Guinea Bissau, kalilan ne suka nufo kasar  Najeriya ciki harda Monsour dani iyalinsa."

**** ***** ****

Zan iya cewa bayan neman na kai harda rabon binne cibiyar Keltouma a kasar Najeriya ya fiddomu daga gida (Arlit).

Koda muka shigo kasar hausa mun fara tsintar kanmu a wani gari wai shi (Shinkafi) wanda ke karkashin jihar Zamfara.

"Yawanci mutanenmu na daji idan suka samu kansu a birni sun fi ganewa aikin gadi, amma Monsour zaciyarsa tafi gaban nan neman arziki ya fito na sosai, da niyyar duk ranar da Allah ya bashi dama zai ya je ya zo da Modibbo kasar Najeriya don mahaifiyarsa ta jima da rasuwa. Modibbo Salihou shikadai yake zaune a gidansa bayan tahowar Monsour, ya haifi wasu  ya yan bayan Monsour amma basuyi tsahon rai ba bakidaya."

Monsourou ya hadu da wani ubangida a garin Shinkafi wanda shi ya saka shi a harkar sana ar hako albarkatun kasa da akeyi a wasu sassa na dazuzzukan Zamfara.

"A lokacin da aka aurawa Monsour ni, ban fi shekaru goma sha biyar ba, Monsour ya sayar da rakuminsa yakama mana hayar karamin gida ya kuma shiga sana ar kodagon hako gwal a yankin Bukkuyum, ya kanyi kwanaki uku zuwa hudu bai zo gida ba suna can wajen sana arsu."

"A haka Allah ya albarkacemu da samun haihuwarta, a shekararmu ta kusan biyar da aure. Ta ko ina jaririya bata baro gida ba, tazo da kyawun ta na kabilar  Tuareg din asali wanda yafi gaban kwatance. Kai kace  yar tsanar robace irin mai motsinan don kyawun sura."

"Jaririya bata yi kama dani ba ko mahaifinta, saita tsallakemu ta dauko Kakarta ta wajen uba a komai, mai suna Iya Aaminata, zubin halittarta duk na kakarta ne bata baro komai nata ba. Tayi mana fintinkau a kyau, daga ni har mahaifinta."

Ranar kwana bakwai da haihuwar muka zaba mata suna KELTOUMAH.

Keltoumah suna ne na Kabilar Tuareg mai nufin  lumana ko  zaman lafiya (peace

/tranquility).

"Tun daga sanda aka haifeta mahaifinta ke nuna mata madaukakin gata na duniya iri- iri, kullum cikin dinka mata sabbin suttura yake, baya fita ya dawo hannu rabbana sai ya riko mata duk abinda take so na ci kona wasa, tanada shekaru biyar ya saka ta a makarantar allo a garin Shinkafi."

"A haka Keltouma take girma, cikin gatan uba, kauna mai tsanani, soyayya da kulawar mahaifinta."

"Tanada shekaru goma mahaifinta yayi sabon gida nasa na kansa a garin Zurmi, muka tattara muka koma karamar hukumar Zurmi daga garin Shinkafi, kasancewar Zurmi tafi masa kusa da wajen sana arsa a Bukkuyum."

"Keltouma tunda ta tasa tayi hankali saita amshe hidimar mahaifinta daga hannuna, ita ke kula da dawainiyar abincinsa idan yazo gari, bata wasa da cikinsa da kiyaye cimarsa ta masu lalurar ciwon suga."

"Dole na sakar mata girkin Babanta, haka sauran aikace-aikacen gida saboda in ni nayi ma cewa zai yi bai fita tas kamar na"

"Keltouma ba, duk da bata da zafin nama amma in ka barta a hankali zata yi girkinta cikin nutsuwa mai matukar gamsarwa."

"Keltouma tun tasowarta yarinya ce mai tsafta, tana kuma da yawan kyankyami a halittarta. Komai mahaifinta ya samo akanta yake karewa. Sannan in bata yarda da tsaftar abu ba bata ci sam. Ko taci zata amayo shi."

"Bazan iya kwatanta maka irin shakuwa da soyayyar dake tsakanin Keltouma da mahaifinta Monsour ba, yawun bakina ko tawadar alkalami yayi kadan ya bayyana ta, amma a takaice tafi shakuwa dashi fiyeda ni. Tun tana karama muka rasa Modibbo Salihou Allah bai cika burin Monsour na kawo shi Najeriya ya zauna kusa damu ba."

Kuma daga kanta ko batan wata ban sake samu ba ma ana bamu sake samun haihuwa ba.

A lokacin bazarar bara Keltouma nada shekaru goma sha biyar a duniya aka wayi gari da labarin barkewar rikicin ta addanci da bullowar  yan ta addar bindiga (bandits) a wasu sassa na garuruwa da kauyuka dake yankin jihar Zamfara.

"Ana kiransu  yan bindiga, wasu marassa imanin fulanin daji masu shiga kauyuka da muggan makamai su tsare hanyoyi suna yin ta addanci ga al ummar da basu ji ba basu gani ba."

"Gabadaya jihar Zamfara ta zama babu tsaro, kwanciyar hankali yayi karanci, ta addanci ya fara yawaita. Ya zama hanyoyin Zamfara basa biyuwa ta dadin rai, kananun hukumomi irinsu Shinkafi, Tsafe, Maru, Bakura da Maradun abun yafi shafarsu musamman kauyenmu na Zurmi."

**** **** ****

"Daga wannan bazan iya tuna komai na abubuwan da suka faru a lokacin ba, sakamakon halin tashin hankalin da muka samu kanmu rana daya, ko ince juyin rayuwa na farat daya."

"Munata jin wai-wai akan abubuwan dake faruwa a jihar, ashe al amarin na tafe kanmu bada bata lokaci ba."

Watarana Monsour ya kamo hanya zuwa Zurmi daga Bukkuyum. Ina madafi ina girki Keltouma na tsakar gida tana min tsintar shinkafa sai gawarsa da aka tsinta akan

"titi aka shigo mana da ita, wai  yan ta adda sun taresu a hanya sun kashe mutanen motar, sun yi garkuwa da wasu, gabadaya dai labari yazo mana cewa babu wanda ya tsira a cikin motar hayar."

"Akan idonta aka shigo da gawar mahaifinta jina-jina, bayan sun sassareshi a koina a jikinsa."

"Keltouma ta kasa manta wannan majigin da wannan ranar, har a cikin barcinta ganin wannan al amarin take yi yana gilma mata."

Bamu farfado daga wannan yanayin ba ba abu na biyu ya sake faruwa.

"Al amarin da tashin bomb ya fara, ya ritsa da kaso 80% na mutanen kauyen bayan kashe mahaifinta da akayi da kwanaki kalilan."

Bazan iya tantance ko firgici da dimuwa ne suka shafe min tunanina daga wancan lokacin ba.

Don bazan iya kara adar da me ya faru damu ba kuma.

"Ni dai na wayi gari na ganmu muna tafiya dauke da gammon kayanmu nida Keltouma don barin kauyenmu, cikin  yan"

"gudun hijirar dake barin Zurmi zuwa IDP Camp, sanadin barkewar rikicin ta addanci da tawayen  yan ta adda ta ko ina a kauyen, masifu suka barke ba ji ba gani a garin Zurmi. Sakamakon bamu da muhallin zama kuma, bayan  yan ta adda sun mamaye kauyenmu wato sun ci shi da yaki, sun kwace ragamar kauyen da mulkin gidajenmu"

gabadaya.

"Tun washegarin ranar da aka kwace garin Zurmi muke tafiya a kafa, tafiyar kwana daya da rabi cikin rana da yunwa da kishirwa mai tsanani, masu kuka nayi masu salati na yi yara da manya da dattijai, kafin muka wayi gari a inda gwamnati ta bamu mafaka (IDP Camp), cikin tagayyara da koke-koken kananan yara, muka shiga sansanin da akafi sani da  sansanin  yan gudun hijira ."

"Rahoton da kafafen yada labarai suka fitar a safiyar shine; A ranar 9/9 na shekarar da ake ciki, sunyi nasarar kwace kauyen karamar hukumar Zurmi, da sauran kauyuka dake makwabtaka dashi."

" Yan ta addan sun kashe na kashewa, sun nakasta mutane masu dimbin yawa,"

sannan suka kwashi ganimar dukiyar bayin Allah da basu ji ba basu gani ba.

"Don haka zan iya cewa Keltouma tayi doguwar rayuwa da mahaifinta tun daga haihuwarta har girmanta, sabo da soyayya irinna tsakanin Da da mahaifi mai girma ne a tsakaninsu. Duk wata kulawa da abokantaka ta kawaye da dangi ita ta samesu ne daga mahaifinta."

"Zan iya cewa mahaifinta shi ya raineta ba ni ba, ba don kuma bana taredasu ba a ah, Monsour shi ya zauna tare da ita ya saurari dukkan kalaman shirmen kuruciyarta da matsalolin yarintar yaro a lokacin da yafi so a saurareshi, har fiyeda ni uwar dana tsugunna na haifeta, wato ya kasance uban kwarai a gareta yana bata lokacinsa da kulawarsa fiyeda ni."

"Barci ne kadai yake rabasu itada Mahaifinta, in dai yana gari, shima din sai bayan fara balagarta. Don haka kallon (uwa, uba da dangi da aboki duka) Keltouma take yiwa mahaifinta ba kallon Uba kadai ba."

Na dade ban yarda da wannan al amarin ba cewa yanzu babu Monsour a tare damu! Monsour shine makwafin dangi da iyaye a

"gareni, ya rike amanata a bayan ran iyayenmu, shikadai nake dashi a duniya da zan kalla in tuna gida Arlit."

Don nima nawa mahaifin ya jima da kwantawa dama shiyasa daga ni har Keltouma mun kasance kullum a cikin dimuwa da firgicin rashin Monsour daga lokacin da abun ya faru har zuwa yau.

"Kalilan cikin jama ar kauyen, da muka samu tsira da rayuwarmu yawanci duk mata ne na cikin gida da kananan yara, mune muka wayi gari dauke da tsummokaranmu a kawunanmu, muka bi  yan gudun hijira wutsiya a zage, suttura a fatattake, kafa babu ko takalmi futu-futu muke tafe kamar an hakomu daga kabari don jar kasar data fitittike mu a kan hanyar zuwa sansanin gudun hijira."

"Zuciyar kowannenmu tayi duhu, rayuwa tayi kunci, har bansan yadda zan fassara halin da muka samu kanmu ciki nida Keltouma ba, ranar da muka wayi gari a IDP camp, gabadaya rayuwar tayi juyin waina da farin cikinmu rana daya ba tare da tsammani ba."

"Farin ciki yayi kaura daga zukatanmu, bakin ciki mara misaltuwa na kewar Monsour ya maye gurbinsa, tu daga wancan lokacin kuncin rayuwa ya kulla alaqa da zuciyar Keltouma."

"Ba Keltouma kadai ba da yawan yara an kashe iyayensu uwa da uba, wasu Kakanni, wasu  ya yansu da abokansu, da  yan uwa na jiki makusantansu."

"Munada yawan da bazai misaltu ba a wannan sansani, inda

Please Login or Register in order to submit comment