gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 12 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a goshinta, tace  likita duk abinda zakuyi in dai zaisa Keltouma ta cigaba da takawa a doron kasa cikin koshin lafiya, na amince dashi kuma na kwantar da hankalina ."

"Likita da Yassar suka mike tsaye a tare suna murmushi, likita yace  sai kiyi tayi mata addu a Allah ya bata lafiya mai dorewa a treatment dinda zamuyi mata ."

Ummami bata da masaniyar wa ya biya makudan kudin asibitin da ake kula da lafiyar Keltouma.

Tun daga ranar da aka fara magance matsalar tata Ummami ko likita da camp leader mai tayasu jinya basu kara ganin Mr. Yassar ba.

"Wata irin extra kulawa Keltouma ke samu a asibitin kudin, magunguna da allurai masu tsada, sai bayan ta fara samuwa wato da kwana uku da tafiyar Mr. Yassar daga asibitin ne likitan da ya jagoranci kula da Keltouma yake gaya mata  ai wanda ya kawo ku dinnan shine yake biyan kudin komai da kansa, ba asibitin bane suka dauki nauyi kamar yadda"

kike zato. Mu wannan asibitin na kudi ne ba na gwamnati bane.

A zaton Ummami da farko likitan ne ya dubi Allah ya tausayawa  yar marainiyarta yayi mata ceton rai a kyauta.

"Daga lokacinnan Ummami bata kara ganin Mr. Yassar ba, basu kara ganin ko inuwarsa a asibitin ba, har bayan kwana bakwai da zuwansu. Sai abinci da abin sha lafiyayye mai rai da lafiya da ya biya asibitin suke basu kullum akan kari suna ci suna kara murmurewa, kumatu na kara yin jajir."

"Da maraicen ranar Asabar Ummami na baiwa Keltouma Ayaba da gwanda a baki tana sha, Ummami na cewa Camp leader."

" toh nikam inata addu a Allah yasa dai lafiya Malam Yassar yake, kinga har yau shiru, bai kara waiwayowa ba, ina addu ar Allah ya dada hada fuskokinmu dashi koda sau daya ne don in gode masa ."

"Camp leader tace  ai can sansani ma bana ganinsa kwana biyu baya zuwa, sai dayan abokinsa Bayeraben da daya macen kabila, ta"

tambayi Ummami ko sun san shi a wani waje ne kafin zuwansu sansani?

Tana mamakin yadda ya damu dasu. Kuma kowa ya shaida su kadai yake kulawa a sansanin  yan gudun hijira.

"Ummami tace  ko daya, kawai haduwar jini ne, ko ince yana cikin na Allah wadanda akace irinsu basa karewa a duniya& . ."

"Ummami bata kai ga rufe bakinta ba sai ga sallamar Mr. Yassar a kunnensu, yana tsaye bakin kofar shigowa dakin dauke da murmushi a tattausan bakinsa, tsaf kalaman Ummami na karshe suka shige kunnuwansa, yana sanye cikin makubar shaddah  getzner babbar, kansa babu hula, kwarjininsa da cikar zatinsa gabadaya ya cika idanun duk wanda ke dakin, sannan hancin kowa ya karbi bakuncin kamshin turarensa na  Bakkarat Rouge ."

"Ummami ta wangale baki kamar bazata kara rufewa ba, ta kuma amsa sallamarsa da doki da farin ciki, shikuma yana shigowa yace  Ummami kin yi kiba kinyi kyau Masha Allah . Idanunta ko ba a fada ba cike suke da"

"kewar ganinsa, at the same time cike da damuwarta na rashin ganinsa for a long time suke."

"Kallo daya tayi masa ta hango adadin ramewar da yayi cikin  yan kwanakin data yi bata ganshi ba, ko Keltouma dake kwance akan gadon asibiti rai a hannun Allah batayi ramar da Mr. Yassar yayi ba."

"A rashin sanin Ummami, jinin jikinsa"

aka kwashe ake karawa Keltouma& .

"Bayan ya bada jinin nasa ya koma gida kuma shima tasa jinyar ta sameshi, jikinsa ya rikice da damuwa da ciwon zuciyar da bai san dalilinsa ba. Shi dai kawai ya san yana fatan Keltouma ta mike, ta kuma rayu, rayuwa mai tsayi, don ya san hatsarin  gastric ulcer shine ciwon da ya kashe wani abokinsa Salah farat daya."

"Ummami ta rasa ina zata ajiyeshi don kewa da farin cikin ganinsa. Shikuma kallon gadon da Keltouma ke kwance yake satar yi, Karin jini dana ruwa ake mata, baya ko tantama jininsa ne yake ta sauka dis-dis yana shiga jikinta, don yace kada asaka mata jinin"

"sayarwa, a gwada nasa in yayi daidai a debi ko leda nawa ne."

"Tsigar jikinsa saida ta tashi yarrr! A lokacin da idanunsa suka sauka akan Keltouma, don farar shimi ce kawai a jikinta yau, kanta babu ko kallabi, duk da gashin a cukurkude yake ba wanki ba taza ba gyara, amma baki ne sidik sassalka, Ummami na kokarin bashi kujera duk ta cika shi da hira tana ce dashi."

" Da ace zan iya, da nayi fushi da kai Malam Yassar, yau kwana na takwas kenan da ban sakaka a idanuna ba, ban kuma san inda zan nemoka ba."

Ni ba abun in shiga gari in bada cigiya ince ko an gano min Da na Yassar dan aljannah?

"Sosai ta bashi dariya har saida ya fadada murmushinsa, tace  wallahi babu abinda ban kiyasta ba a raina na yadda zanyi na nemoka a jihar Zamfara da kewaye, idan da baka dawo yau ba nayi niyyar shiga lungu da sako na garinnan in yi ta cigiyar Dan Ummami ."

"Dan murmushin da yake yi ya zarce zuwa dariya. Yassar yayi dariya ya sake yi, sannan ya duka kansa har kasan guiwarsa"

"saura kadan ya kai kasa yana gaisheta, da muryar lallashi da amsar laifi yace,"

" tuba nake Ummaminmu, nima nayi fama da  yar masassara ne, bata gama sakina ba har yanzu, karfin hali nayi yanzunma na fito saboda in duba ku."

"Ko ranar da muka zo nan ban jima da tashi daga masassarar ba dama, ina komawa gida ta dawo min sabuwa, amma Alhamdulillah naji sauki sosai yau, kuma ko kafin naje camp, nan na fara isowa wajenku don nayi kewar ganinki nima ba kadan ba ."

"Ummami taji dadin maganarsa sosai, ta tausaya masa, tace  kace Da kwance uwa kwance akayi kenan kai da kanwar taka ."

"Sai kuma tayi murmushin tsokana ta ce,"

 ni kadai kayi kewar gani Malam Yassar? Banda kanwar taka sarkin kuka? .

"Wannan karon bai iya ya hadiye faduwar gabansa ba, wanda ya maye gurbinsa a fuskarsa da dan siririn murmushi."

"Sannu a hankali ya daga kai ya dubi Keltouma din, wadda ke barcinta sadidan"

"akan gadon jinyar marasa lafiya, sai lokacin Ummami ta ankara da babu cikakiyar suttura a jikin Keltouma, tayi hanzarin janyo blanket ta rufe mata jikinta gabadaya, sai fuskarta sumul dake barci tana sauke numfashi cikin koshin lafiya."

"Shaf! Ummami ta manta shimi ce a jikin Keltoumah, saida taga Mr. Yassar ya kai idonsa kanta a sace, sannan tamkar magnet ya damke idanun nasa ya rike su a kanta ya kasa daukesu, sakamakon cewa yau ya ganta ne a (zahirin Keltoumah), ya ga abinda bai taba gani a tareda mace ba, sannan da idanun Rahma da jin kan marar lafiya ya kalleta bada irin  annoying look din da yafi yi mata a baya ba."

"Rana ta farko da ya samu kansa da yi mata kallon tsanaki, kallo na nutsuwa, na lumana da kwanciyar hankali, ya kuma yi sa ar ganinta tsurarta in her natural being, ba tare da tana kuka ko fushi ko fyatar hanci ba, sannan tsaf cikin tsafta tayi fresh da ita babu ko kyallin hawaye a idonta, don kullum sai nos ta mata wanka da tawul, ga cima ta samu tsayin dan lokaci mai kara lafiya. Shi da kansa"

ya fada a ransa  AKOKE KYAKKYAWA CE in ka cire shagwabarta .

"Ta yi wani irin fari sosai ta murje kamar balarabiya, fatarta tayi santsi ta koma kamar ta jariri sabon haihuwa, hancinta ya fito sarari dan sirit dashi, don kullum sai an mata wanka safe da yamma yanzu, don haka duk wannan annakiyar dattin ya tafi daga jikin Keltouma da Innarta yau babu shi."

"Wani irin sardidin hanci mikakke Allah ya halicci Keltouma dashi tamkar ita ta saita ma kanta shi ta ajiyeshi tsakanin idanunta, bakinta dan tsurut dashi ruwan hoda (pinkish), kallonsa kadai idan yana motsi ko kuka abun sha awa ne ga Da namiji, tana kwance rigingine da karin ruwa dana jini duka a hannunta, suna shiga jikinta dis-dis a hankali."

"Tunanin cewa  Jininsa ne wannan! ya haifar da wani ignition a zuciyarsa. Yadda ya kwashe jinin jikinsa ya bata, shi kansa yayi mamakin kansa, lokacin da likita yace za a sayi jini sosai a kara mata ya samu bakinsa na subucewa cikin fadin."

" ku gwada nawa, in yayi daidai a diba, kada asa mata jinin kowa sai nawa, bana son na sayarwa ."

"Tabbas bakinsa ya ambaci  Jinina! ba tareda ya san ya fada ba, maganar zuci ce ta fito fili har Ummami taso taji ta, wadda tasa Ummami din juyowa. Tace dashi."

" ehen? Maganar jini naji kake yi ne Da na? Ai tun zuwan mu suke kara mata jinin nan, ta zubar da jini da yawa daga cikin cikinta. "

"Yassar ya dawo daga tunanin da ya tafi kuma nan da nan ya ankara da subutar bakinsa, yayi hanzarin gyara maganarsa da cewa."

" Ummami! Cewa nayi naga jinin ya kusa karewa, bari na kira Nos suzo su cire mata ."

"Bayan yayi magana da Nos din dake waje kan tazo ta cirewa Keltouma karin jinin da ya kare, Nos din take gaya masa babban likita na kiranshi a ofishinsa."

"Yassar yaje ya sameshi suka yi musabiha yadda suka saba, nan Doctor Kazim yace  ga jikin Keltouma yayi kyau cikin dan"

"lokaci Alhamdulillah har fiyeda zatona, an godewa Allah an kuma godewa mutanen kwarai irinka."

"Keltouma ta samu sauki kamar bata yi ciwo ba, amma akwai yuwuwar ciwon nan ya kara dawowa idan ta koma zama da yunwa da damuwa irin baya."

"Mahaifiyarta ta gaya min cewa kai ba Dan ta bane, nayi mamaki kwarai da tace aiki kawai kazo yi a sansaninsu na  yan gudun hijira, kayi ra ayin ka taimakesu a lokacin da kowa baya ta tasu. I m extremely impressed!"

"Ina fatan kana cin duk abubuwan da na lissafa maka, domin samun karin wadatar jini da karfi a jikin ka? "

"Yace  kada ka damu likita insha Allah I will be fine, will take care of myself, my only concern is Ummami to be happy, and Keltouma to stay healthy (Insha Allah zan ji sauki, zan kula da kaina, damuwata shine Ummami ta kasance cikin farin ciki, Keltouma kuma ta samu koshin lafiya)."

"Likita na dariya yace  Malam Yassar kodai? Kodayake bari in bar kaza cikin gashinta, in aka dafata da kayan kamshi tayi kamshi sai kowa yaji ."

"Yassar bai wani gane zaurancen da likita Kazim yayi masa ba, yayi dan murmushi kawai ya mike yana barin ofishin, ba tareda yace da likitan komai ba."

Don har ga Allah bai fahimci cewa magana mai harshen Damo likita Kazim yayi masa ba.

***** ***** *****

"A kwana goma da akayi ana jinyar Keltouma a asibiti, shi da uwar Keltouma sun kara shakuwa, sun saki jiki da juna sosai saboda ita kanta Ummami bata fi gejin shekaru arba in da yan kai a duniya ba. Don haka ake mata kallon Yayar Yassar a idanun ma aikatan asibitin."

"Kullum ya fito aiki sai ya fara zuwa ya kashe lokaci mai yawa a clinic dinnan tareda Ummami, sun zama tamkar Yaya da kaninta, Akoke sarkin kuka kuwa, ai yanzu shiru kake ji, kamar ba ita ba, sautinta ya daina fita da"

"sunan kuka, bata umh bata umh umh don ko hira suke bata saka musu baki, zaka samu kodai tana barci, ko tana kallon shirye-shiryen da ake yi a talbijin din dake kafe a bangon dake fuskantar gadonta a tashar fina finai da raye-raye, duniya sabuwa! Bata komai sai aikin ci da sha tasa a gaba, tana maida komada daga tsohuwar yunwa, da kwanciya a katifar gadon asibiti mai laushi wadda rabonta da kwanciya akan irinta tun mahaifinta na raye, sai ko idan Nosis sun shigo sun tasheta zaune don ta sha magungunanta kota karbi allura."

"Ya daina kiranta  Iya tunda jimawa sai  Ummami , wato yadda yaji  yarta na kiranta, wannan shi yafi komai dadi ga Ummami saboda a yadda ta fahimta Mr. Yassar mutum ne mai saukin kai da girmama na gaba dashi."

"Haka zai zo tun safe ya zauna har sai hantsi ya dubi ludayi suna hira shi da Yayarsa, yayinda Keltouma koma musu take tamkar kurma, tayi bakam da ita, in dai Yassar yana wuri tofa dif! Take komawa a wurin har sai ya tashi, bata kallonsu bata shiga hirarsu, kuka kuwa ta jima da manta yadda ake yinsa."

"Wato dai a takaice ya gama gane Keltouma; damuwa da zaman IDP Camp, da rashin son zaman wajen shine sanadiyyar kasancewarta a halin kuncin data kasance a baya ba rashin mahaifinta kadai ba."

Don haka duk lokacin da suka hada ido itada Yassar sai ya faki idon Ummami ya galla mata harara. Amma bata ko kallon inda yake balle tasan yana yi. Aikin banza yakeyi wai harara a duhu.

"A baya ya dauka kuka halittar Keltouma ne, domin mawuyaci ka ganta bata kuka. Ya taba cewa a ransa."

" Da ace ana tara ruwan hawaye, da an tara rijiya guda da hawayen Keltouma."

"Komai suke bukata kuwa saidai wani ya tadda wani, Mr. Yassar M. Jalloh, ya tsaya masu. Akan abinci ne, abubuwan sha ne masu kara lafiya da kuzari, magunguna da kayan masarufi na bukatar dan adam yau da gobe ne duk basu rasa ko daya ba. Tuni suka murje suka wartsake daga komadewar da suka yi da dauda da datti, suka zama  yan gayu a gadon asibiti."

"Hatta Camp leader bata son ace za a sallamosu, don kullum sai ta zo, har tayi"

"guzurin abinda suka rarrage ta tafi dashi camp, mutunci sosai take musu yanzu."

"A halittar Yassar shi ba mutum ne mai shiru-shiru ba, sannan shi ba mutum ne mai yawan surutu ba, baida kwaramniya ko kadan, adadin surutunsa yanada alaqa da yadda zuciyarsa ta karbeka, ma ana; idan Yassar yana sonka zai saki jiki da kai, idan zuciyarsa tayi na am da kai to sannan ne zaka ga hirarsa da raharsa har sai ka godewa Allah. To hakan ce ta kasance tsakaninsa da Ummami, wadda a yau da hira tayi hira tsakaninsu take gaya masa sunanta na asali"

shine  Nana Aicha .

Keltouma ce ta saka mata suna  Ummami tun tana karama ma ana (Ummanta) kuma sunan sai ya bita a bakin kowa nasu.

"A wannan zaman jinyar na Keltouma Yassar ya saba da Ummami sosai, ya shiga jikinta yadda ba a zato, ya yi matukar shiga ran Ummami da kirkinsa da kyautayi da alkhairansa, (in cash and in kind) Yassar yi musu alkhairi yake, yadda yake kula da sha aninsu ko mahaifiyarsa da kanwarsa ne"

"sai hakan, ya kyautata musu a wannan jinyar iyakar kyautatawa."

"Zama yake zaman Rakuma a gaban Ummami, yi yake kamar yana gaban Yayarsa, suyi ta hira yana yi yana gyara mata bahaguwar hausarta, amma zaka yi mamaki matuka idan ka kalli Keltouma a irin wannan lokacin da Mr. Yassar ke tare dasu!"

Annabi SAW yayi gaskiya da yace zuciya na son mai kyautata mata!!!

"Keltouma duk da halinta na miskilanci da shiru-shiru ta dade tana tarawa tana debewa gameda Mr. Yassar a ranta, akan tarin abubuwan kyautatawa da alkhairai da Mr. Yassar ke yi musu, ko mahaukaci yasan mai kyautata masa, har ya zamanto a dan tsukin, daga can wani sako na kasan ranta taji tana son ta ganshi ya shigo, kunnenta na mararin son yaji (masculine soft voice) dinsa na sauka a gangar dodon kunnenta, yana gayar da Ummami ne ko yana mata hirar abokinsa Femi mai kankanbar tsiya. Wani  pleasant feeling Keltouma ke ji a kasan ruhinta a duk lokacin da taji sallamar Mr. Yassar a dakin jinyarta."

"A wani maraice, Yassar da Ummami suna hira Mr. Yassar yace,"

 nikam Ummami meye babban burinki na rayuwa a yanzu?

"Babu dogon nazari, babu wani dogon tunani ko bata lokaci Ummami tace dashi cikin murya mai ban tausayi."

" Babban burina a rayuwata yanzu shine komawa kasata ta gado, cikin ahali,  yan uwa da dangina in akwai saura a raye."

Rabona da gida da kowa nawa tun auren da mahaifina yayi min da Baban Keltouma a shekarunmu na kuruciya.

A yanzu kuwa na tasar ma shekaru talatin da takwas zuwa da tara. Yanzu ban sani ba ko akwai sauran dangi na da suka rage a raye ko babu?

Shi kam Baffana na dade da samun labarin rasuwarsa tun wani zuwa gida na karshe da Baban Keltouma yayi lokacin da yana raye.

"Tace  aure ne ya fiddo ni daga gaban iyayena, ban kara ko ganin kowa nawa ba har yau, iyayena duk sun rasu ban je ba, saboda kullum nace da Monsour ina son zuwa gida in zai je zan bishi baya yarda, don gani yakke idan najje bazan yarda na dawo tareda shi ba."

Yau gashi babu Monsour a duniya ban san ta yaya zanyi na koma kasa ta ba don mu akan Rakuma muka shigo kasar Haussa .

Yassar da saurin baki ya tambayi Ummami ko yaya sunan kasar data fito din?

"Ya zama  very intrigued! Ga son jin labarinta, saboda a wannan dan tsukin komai ya kwace daga mulkinsa da ikonsa, zuciyarsa ta fara gama kumbiya-kumbiyarta, ta yarda tana cikin soyayyah mai dumbin yawa a inda bai dace ba."

"Fatansa a yanzu

Please Login or Register in order to submit comment