gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 6 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aiki yake yi. Amma ina! Sai ji yayi Haladu na gyaran murya yana cewa.

" Yallabai, yanzu na hango ku wajen  yan dukununun jajayen matan sansanin nan, me suke ce maka an yi musu? Sarakan kukan tsiya? "

"Cikin rashin kulawa hade da mamakin hali irin nasa Yassar ya dago kai daga fuskar kwamfutarsa ya kalleshi, da idanun nan nasa masu kaifi darashin son wargi, tambayar da Haladu yazo da ita a ganinsa ya zama raini ga na gaba (insubordination) da shiga abinda bai shafeshi ba."

"Kawai sai Haladu ya ga Yassar yayi tsaki, ya girgiza kai, sannan ya hau typing a cikin system din dake gabansa, ba tareda ya tanka masa tambayarsa ba."

A daidai lokacin Yassar ya budo Shafin kundin adana sakonnin sirrikan rayuwarsa (diary) dake cikin system dinsa.

"Da farko kwanan wata Mr. Yassar ya fara sakawa a cikin shafin  diary din, inda ya rubuta& "

" 1st September& ranar daya ga watan tara a IDP Camp, Anka, Zamfara& . ."

"Kafin ya cigaba da rubutun, sai ya dan dakata, ganin har lokacin Haladu na tsaye bai tafi ba yana jiran amsar tseguminsa. Cikin"

"Sokoto accent dinsa, Mr. Yassar yace da Haladu ba tareda ya dubeshi ba."

 Su wa kuma aj- jajayen mata?

"Nan Malam Haladu ya zauna a kujerar dake fuskantar Mr. Yassar, ya hau fassara masa abinda yake nufi da  jajayen mata da ya ambata, yadda zai gane wadanda yake magana akansu, bayan sarai Yassar ya gane suwa yake nufi. Shima Haladun da irin tashi Bazamfariyar hausar, wadda in ya farata in har kai ba bazamfare bane ko kwararren Basakkwace da kyar zaka iya gane ta gabadaya, Haladu yace."

" Ranka shi dade, kaima ad-da ganinsu ka san irin bakin haurennan ne daga dazuzzukan Ifrikiyyah, wanda in za a yanaka ni bana ce ga kabilarsu ba ko yarensu, kyawun su yafi kama dana larabawan jeji kona Sahara, to yaya kakeso in ce maka sunansu yadda zaka gane in ba jajayen sansanin nan ba?"

"Dubesu dai su ba hausawa ba, su ba Fulani ba, su kuma ba Indiyawa ko Sudanai ba, basu kuma da kamanni da Tubawa/Abzinawa. Takamaimai baza a iya cewa ga daga inda suke ba, tsakanin kasashen"

"Afrika, musamman in kaji wannan yaren da suke yi a junansu."

"A hankali Mr. Yassar ya cira kansa yana kallon Haladu, ya dan saka biron hannunsa a bakinsa ya ciza kadan cikin mamakinsa, a ransa yace wasu mutanen dai akwai dorawa kai jidalin abinda bai shafesu ba, ko ina ruwansa da asalinsu ko inda suka fito? Idan ya sani din dame zai kare shi? Ko kuwa zai daukesu ya maida su ne?"

"A fili kuma yace yace masa  tunda ka dage lallai kana son jin tsegumin me suka ce min, to babu abinda suka ce min anyi musu, kawai naga yarinyar tana kuka ne da giramanta da komai."

"Tausayin uwar da yadda naga ta damu da kukan  yar tata, yasa na tambayeta ko kukan me  yarta take yi?"

"To ko amsa basu gama bani ba, nan na nemesu na rasa ."

"Haladu yace  ai kowa ya gane matar nan bata son laifin  yar kullutun uwar  yar nan tata, su bakin zuwa ne a wajennan, basu jima sosai da zuwa camp dinnan ba. amma kowa ya gama saninsu, sabida bambancin launin"

"fatarsu. Gabadaya in ka lura zaka ga a tsorace suke da kowa, basu da yarda da jama a, basa sakin jikinsu suyi rayuwa irinta sauran  yan gudun hijira, ita  yar ta kasa sabawa da zaman sansanin nan har yau sai kuka, taki sabo da mutanen wurin gabadaya."

"Ga dukkan alamu shagwababbiya ce ta kin karawa,  yar fari,  yar gata ko  yar auta a gun uwar, shagwabarta ce tasa na tsanesu wallahi."

Ko daga ina suke Allah masani. Yanzu har ya zamana uwar bata damuwa da yawan kukanta kamar farkon zuwansu nan da zaka ga in ta fara itama uwar sai ta dinga tayata suyi ta yi .

"Femi dake gefe yana aikinsa cikin wasu files, amma kunnensa na tare dasu, nan ya sako musu baki da cewa."

" Kun san me? Ni kuma burgeni sukayi, na yaba kwarai da nutsuwar uwar, kalleta a nitsenta tsaf, kamar ba wadda ke cikin walagigin rayuwa ba."

"Kalli yadda ta nutsu tana baiwa rigimammiyar  yarta baki cikin lalama, kulawa, tausasawa da juriyar uwa akan rigimar dan ta."

"Duk da ban jin yaren da takeyi, amma na karanceta akwai nutsuwa da addini kwarai, sannan da tawakkalin zaman wajennan tattare da ita."

"Sannan kaga bata je tana kokawa da maza don amsar tallafi ba (yadda matan wurinnan keyi), duk da  I am quite sure su basu samu komai ba, ba kuma zasu samu din ba ."

"Gabadaya surutansu daga Femi din har Haladu ya fara hawa masa kai, bai cika son ayi ta maganar mutum a bayan idonsa yana zaune yana ji ba."

"Sai kawai ya rufe system din gabansa ji kake bam!, ba kuma tareda ya tsaya kasheta ba, sannan ya mike cikin nutsuwa ya saka takalmansa ya bar musu wajen, uffan bai ce ba."

**** **** ****

"Koda ya koma hotel dinsu yau, sai da yayi waya da Ammih yaji lafiyarta, ya tambayi Abbih tace yana office bai dawo ba tukunna, ta tambayeshi komai lafiya ince ko? sabida a cewarta taji muryarsa wani iri kamar yana"

cikin damuwa.  I hope ka ci abincin rana dana dare Ibny?

"Murmushi Yassar yayi, cike da kaunar mahaifiyarsa, yace  komai lafiya Ammih sai kewarki, bana cin abinci da rana, saboda a lokacin ina aiki acan Anka, sai na dawo hotel nake saka order a kawomin dan  light dinner . Amma kwarai kullum da safe ina yin kyakkyawan breakfast mai nauyi kafin na fita."

"Litinin, Alhamis da Jumaah kuma kinsan azumi nake ."

"Yassar ya dan nisa, cikin nauyin baki dana zuciya, shi ya san baya iya boyewa Ammih komai nasa, ko abinda ke damunsa komai kankantarsa, amma yau ya kasa gaya mata abinda ya gani ya dameshi, ya wuni surr! Yana tunawa, suna raunana ilahirin kuzarin jikinsa. Wadannan idanun& wadannan jajayen jikakkun idanun masu kama da shatin kwan zabo& wadannan idanun sun kassara shi. Da Ammih ta matsa da son jin dalilin sauyawar muryarsa sai yace."

" Ammih yau din kawai ji nake jikina da zuciyata suna wani irin sauyawa. Tamkar wanda measles ke shigarsa. Ji na nake kamar ba ni ba, kamar sabon ni (new me), wato"

kamar an sake haifoni duniya. Ammih yau gabadaya na manta duk wani tension dina .

Ammih tace  toh fa! Idan kaji irin haka toh sauyin alkhairi ne ke tunkaroka. Yawaita karanta  hasbunallahu waniimal wakeel .

"Yassar yace  toh Ammih. Bari in yi waya a kawomin abincin kafin nayi wanka, dawowata hotel kenan daga can Anka ."

"Sannan ne sukayi sallama ya shiga wankan da tun dazu yake son shiga sakamakon zafin Zamfara dake uzzura masa. Yassar na cikin wanka a tsakiyar shower, yayinda ruwa mai dumi ke bi ta saman sumar kansa, jajayen matan, (ta bakin"

Haladu) suka sake fado masa a rai.

"Yana wanka yana tunanin fuskokin Uwa da  yar. Gasunan kamar an tsaga kara, saboda tsabar kamanninsu da juna."

"Surar yarinyar da mahaifiyarta ta kira da suna KELTOUMA ke sake gilma masa, kamar yadda ruwan ke bi yana wanke sumar kansa haka yake jin yana wanke masa kwakwalwa yana zuba masa sabon vibe na rayuwa wanda a baya bai taba experiencing ba, Keltouma ga haiba ga kyau kamar balarabiyar Hijaz, sannan ga kamala a kan"

"fukokinsu duka, mai nuni da cewa su din ba mutanen banza bane ba kuma wulakantattu ba, kaddarar rayuwa ce ta tafi karfinsu ta yi sanadin shigo dasu IDP Camp."

"At the same time yana tuna annakiyar dattinsu (dauda) data samu muhallin zama a farar fatar jikinsu da atamfar jikinsu, da kwantacciyar damuwa mara misaltuwa dake kwance a saman kyawawan fuskokinsu."

"Sunan da bai taba jin mai irinsa ba, ya sake yi masa dirar mikiya hadi da amsa- kuwwa cikin kunnuwansa;  KELTOUMAH!"

**** **** *****

"Daidai lokacin da ya fito wankan, hatta jijiyoyin jikinsa jinsu yake ba a yadda ya saba jinsu ba, sun yi relaxing sosai. Fatarsa tayi sumul da wankin data sha, jikinsa yayi tas, ya kara yin fresh, sai sheki fatarsa keyi kamar koyaushe ya fito wanka, a hannunsa karamin farin tawul ne, yayinda yake daure da faffadan a kugunsa, yana tsane kansa da tawul din yana kallon agogo duka a lokaci guda. Sai ga kiran Abbih ma ya shigo masa."

"Daidai da zuwan mai kawo masa abinci a bakin kofa, shi kuma yana kwankwasawa."

"Yassar ya fara da amsa kiran wayar mahaifinsa tukunna, da matukar ladabi irin nasa ga Abbih kamar yana gabansa, sannan ya nufi kofar ya bude aka shigo masa da abincin, kamar yadda ya saba gaida Abbih yau ma saida ya rankwafa kamar Abbih na wurin, yace cikin damuwa,"

 Abbih save this date for me kaima a

DIARY dinka& . 1/09 .

Abbih yace  me ya faru a yau 1/09?

"Nan yake labartawa Abbih,  jikina ne yake ta karbar wani sabon sauyi, yana kaiwa zuciyata ita kuma tana karba, wanda yake bani tabbacin rayuwata zata canza salo da taku daga yau ."

"Abbih yayi murmushi kafin yace  ina yiwa rayuwar nan ta tilon Da na Muhammad Yassar fatan nasara, da cikar kamalarsa cikin dan lokaci, addu ata shine yayi AURE kafin zagayowar ranar 1/09 ."

Yassar yayi  yar dariyar maganar Abbih

yace.

 Abbih nah kenan! .

Nan ya shiga labartawa Abbih yadda ya samu dangi a zuwansa Sokoto da wajen Baba Ado a Tambuwal.

"Sai Abbih yace  ina fatan kaga  yan uwanka mata na wajen Yaya babba? Yassar yace  eh na gansu Abbih  sai Abbih yace  duk sun girma ko? ( Ya yan Alhaji Abdulqadir Abbih ke nufi). Yassar abun ya bashi dariya yace  su wa kenan Abbih? Abbih yace  Sahlah da Shafa atu mana? Yassar yace  Toh Abbih ni ina idona ya kai kan girmansu, sun dai gaisheni na amsa, na basu tsarabarsu ."

"Abbih yace  dadina da kai rashin iya mu amalla da kanne, ai wato girman yaran nan harda na ban tsoro, kamar masu cin dusar kajin Agric ."

"(Girman jikin Yaya Babba duk  ya yansa suke debowa, sai ka gansu kamar sun fi shekarunsu mazansu da matansu)."

Yassar cikin subutar baki yace

 musamman wannan Sahlar .

"Sai Abbih ya samu gangara, ya kada kai ya hau cewa."

 Awo wollah. Kaga da kai wani dan kirki ne da zan iya ciwa alwashi bai sakani

"kaffara ba, ai da a cikinsu zaka zabo mana daya, ayi  yar gida kowa ya huta, Tuwo na maina, dakan daka shikar daka tankaden bakin gado, duk mu huta da tuzurancinka ."

Zancen zucin Abbih ya fito fili ba tareda ya sani ba. Sai ji yayi Yassar yana dariya wadda bata ko kai ga shiga cikin cikinsa ba. Yace.

" Abbih! Sau nawa zan gaya maka banida ra ayin auren zumunci? Ka manta da wannan tunanin, please Abbih nah."

"Ni dukkansu kannena nake ganinsu, wadannan yaran masu rawar kan tsiya Abbih masu kama da kajin gidan gona ina zan kaisu ribda-ribda dasu haka?"

"Sannan kaga raini zai gitta tsakanina dasu, raini irinna  yammatan family ga yayyensu maza, wanda ke zuwa sanadin auren zumunci."

"Saboda duk girman nan da suke bani zubewa kasa zaiyi warwas Abbih. Muddin suka ji irin maganar nan da kake yi akaina dasu. Please Abbih! Idan kanada wannan burinma ina rokonka ka cireshi a ranka, bana sha awar auren zumunci sam, balle aure- auren mata da yawa irin nasu Yaya babba."

"Abbih nafi son girmana ya cigaba da gudana a idon kannena! Sannan idan na tashi aure inyi zabinda bazan yi nadama acan gaba ba . Abbih cikin takaicinsa yace  wannan ra ayin naka ne kawai, gyambo sarkin son girma, auren zumunci ai ba zubda girma bane a idon kanne, karfafa zumunci ne, addini da al ada duk basu hana ba."

"Ai shikenan, ni bazan maka dole ba, ina nan ina zuba idon ganin matarka nan kurkusa, tunda baka son nawa  ya yan, dana dade ina yi maka sha awa."

"Ina zuba idon ganin surukar da zaka kawomin Yassar,  yar manyan mutane,  yar babban gida, wadda zata cika min gida da  ya yan da ni Allah bai bani da yawa ba, nan bada jimawa ba nake burin ganin iyalinka."

"Don wallahi Allah ne shaida ko ban fada ba, na gaji da zamanka haka, sannan tafiye- tafiyennan naka babu iyali yana matukar damuna ."

Abbih ya karasa cikin karayar murya mai nuna damuwar da yake ciki akan al amarinnan.

Yassar sai ya karyar da kai kasa sannan ya karyar da murya cikin ladabi da lallashi yace.

" Abbih! In dai don ni kake shiga damuwa akan ina tafiye-tafiye babu aure to ina rokonka ka daina, ka kurbi ruwan buta a kaina ka kwantar da hankalinka kaji, Insha Allah Dan ka Yassar yana cikin kariyar Ubangiji daga addu arku da bata yankewa a gareshi."

"Abbih Yassar baya wasa da ibadar azumin Litinin da Alhamis da kuka horeshi da ita, baya kai idonsa kan haramu din da zai hanashi sukuni, insha Allah Abbih inada kyakkyawan zato akan Yassar dinka, abinda kake gudu har abada bazai faru dashi ba."

Na yi maka alkawarin har in gama rayuwar samartakata bazan kusanci zina ba.

"Abbih ina ji a jikina lokacin da kake ta burin zuwansama ya kusa& . bada jimawa ba zaka tara jikokinnan a gabanka masu yawa Abbih, zan kawo maku kyakkyawar suruka kaida Ammih, yadda kuke ta damuna nan bada jimawa ba ."

"Ta cikin wayar Abbih yayi murmushi mai karfi da fidda sauti, har Yassar na iya jin sautin murmushin nasa, yace,"

" that s my my one and only Muhammadu Yassar! Allah ya cika wannan ji a jikin naka, ya zamo min goron sabuwar shekara, kuma absolute reality dinda zan dade inaw anna murmushin a kansa! ."

"Daga haka Abbih ya bar zancen aure, ya canza topic din hirarsu ta hanyar tambayarsa gameda aikin nasa, Yassar yayi ta fada masa irin cigaban da suketa aiwatarwa a aikin nasu."

**** **** ****

"Yau satin su Yassar uku kenan da zuwansu IDP Camp na garin Anka, a wata sassanyar Asabar din karshen mako, wadda ta kasance asabar din karshen wata, ma aikatan wajen basu cika zuwa ba, hantsi ya dubi ludayi a daidai lokacin da Mr. Yassar Jalloh, da colleague dinsa Engr. Femi Ogunbiyitan suka shigo IDP Camp, yau babu chauffer dinsu tare dasu, don tunda suka gane hanyar Anka suka dakatar dashi daga kawo su, su suke kawo kansu kullum ko Yassar ya tukasu ko Femi ya karbeshi, haka suka shararo farar motar nan"

"aguje kirar Hilux (4-wheels drive) mai dauke da tambarin UNICEF a jikinta, a sukwane yau suka shigo IDP Camp."

"A yau Yassar din ke jan motar da nishadi sosai a tattareda shi, Femi na daga gefensa na mai zaman banza, suna hirar yadda lokaci ke gangarawa da gudu, wai gashi har sun kwashi sati uku da fara project dinsu. So far, so good, Alhamdulillah! Komai na aikin nasu yana tafiya cikin nasara da kwarewarsu, kuma bisa workplan yadda aka tsaro musu tun farko daga hedkwata dinsu."

"Mr. Yassar, kamar ance ya daga kai ya dubi gabansa, nan ya hango uwar da  yar suna tafe, uwar nata sassarfa rike da hannun  yarta, ita kuma tana tafiyar hawainiya kamar bata so, wannan abu yana matukar bashi takaici, yadda uwar nan ta maida wannan gansamemiyar budurwa kamar  yar goye, ko ina zai gansu sai ya gansu uwar ta rike hannun abarta,  yar na tafiya kamar mai ciwon kafa, ko kuwa wadda kwai ya fashewa a ciki, ta cukuikuiye fuska da fushi da hawaye da bacin rai."

Ga dukkan alamu ofishin ma aikatan sansani suka nufa. Inda suma nan suka nufo shi da Femi.

"Shi ya rasa mai

Please Login or Register in order to submit comment