gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 15 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wace rana Keltoumah ta bude baki tana magana sosai, irin yadda shi bai san ma tana iyawa ba, bai taba ganin tayi doguwar magana ta sentence biyu ba. Ga sautin muryarta mai dadin sauraro yana fita rai-rai-rai dan siriri dashi kamar ana busa sarewa a kunnen mai sauraro."

"Bai gama fita daga wannan  shock din ba, na kalmar fadowar kwarto da ta fito daga bakinta, yaji ta shiga zayyano yanayin rayuwar takura, matsi da danniya da wulakanci da suke ciki a IDP Camp dalla- dalla. Duk da cewa Yassar ya ga wasu abubuwan da idanunsa, kuma Haladu ya taba labarta masa wasu daga ciki da bai kai ga gani da idanunsa ba, bai ji mummunan labari daya daga hankalinsa irin na yau ba, data ce kullum Ummami bata barci sai gadinta, cikin fargabar fadowar kwarto kansu cikin dare suke kwana su kuma wayi gari."

"Ta shiga zayyano masa irin yadda suke rayuwa a Camp cikin wahala, ukuba da kyara da tsangwamar abokan zama, kawai don su kyawawa ne, da siririyar muryarta mai ban tausayi ta cigaba da farke masa irin kaffa-"

"kaffan da Ummami ke yi da ita, don kada a cutar da mutuncinta cikin dare, ko bayan gida zata sai Ummami ta rakata, shiyasa kowa ya tsanesu musamman mazan wajen, a karshe tace  kullum Ummami tana son yin barci amma bata yi, saidai ta dan yi a zaune da Asubahi in ta idar da sallar asubah, ba tareda tasan lokacin da ya dauketa kadan ba ."

"Jikin Mr. Yassar gabadaya sai yayi mugun la asar. Idanunsa sun kada sun kankance da wani sabon So da kaunar Keltouma, ga tausayin soyayya mai tsanani da yazo ya lullube shi. Heart dinsa na bugawa fat- fat cike da fargabar abinda zai iya fito daga bakinsa..."

Amma a wannan lokacin komai ya kwace masa. Ma ana bashi ke baiwa zuciyarsa umarnin d yake so ba a ah zuciyar ce da kanta ke jan ragamar kalaman dake son fitowa daga bakinsa& .

"Mr. Yassar ya dubi Ummami dake gefensu a zaune tana tahiyar idar da sallahr walha, tunda Ketouma ta soma magana ba kakkautawa ta tada sallar walha ta rabu dasu. Tana sallamewa Ketouma na gamawa. Sai"

"kawai taga Mr. Yassar ya matso gabanta ya durkusa akan gwiwoyinsa, kamar zai shige cikinta don girmamawa, kamar ya samu kansa gaban Ammihnsa Tarha yana so zai farke mata damuwar ransa."

"Ya bude bakinsa da kyar kamar mai ciwon hakori ko wanda kuraje suka makalewa makogaro, yake ce da Ummami cikin inda- inda da rashin daidaito na fitar sauti;"

" Ummami ki aura min KHALTHOUM mana, tunda kinga bata son zaman IDP Camp, idan mutum ya furta da baki da zuciyarsa baya son abu, idan da hali ka nesantashi dashi kafin ya zame masa ciwon damuwa."

"In yaso maimakon zaman Camp tana kuka kullum, sai tayi zaman aure irinna kowacce mace, na ibadar bautar Allah."

"Sannan nayi amfani da damar na sakata a makaranta, tayi karatun addini dana zamani, yadda Ni (dana ke fatan zama miji a gareta), dake mahaifiyarta, da  ya yanta masu zuwa a gaba, da al ummar duniya bakidaya watarana zamuyi alfahari da ita ."

"Ya maida kallonsa ga Keltouma wadda ta gama daskarewa daga zaune, ko numfashi ta kasa ja cikin huhunta saboda kidima. Yace."

"Khulthoum ki amince ki aureni, nikuma na rabaki da zaman IDP Camp har abada!!!"

"Nayi alkawarin killace ki a dakin aurena, muyi zama na soyayyah da amana, mu yi ibadahr aure na har abada tare, kiyi ta haifa min  ya ya Khulthoum, ina tayaki raino da tarbiyyarsu, masu irin halin Ummami, kuma masu kama dake, amma ba masu irin halin KUKANKI ba ."

"Ba Ummami kadai ce ta kusan sakin fitsari daga inda take zaune ba, hatta Keltouma din zumbur! Tayi ta mike tsaye, tana zazzare ido kamar marar gaskiya. Kasancewar ba amsarsu yake son ji a take a lokacin ba, yana kawowa nan da maganarsa sai ya mike tsaye, bai ko kalli idanun Keltoumah dake jujjjuyawa ba cikin kaduwa ya juya ya fice daga dakin."

"Saida ya kai bakin kofa sannan ya dan dakata yana ce dasu, su tashi su dauki abinda zasu dauka zai mayar dasu Camp yadda ya"

"dauko su don zuwa asibiti, don a lokacin yana sauri ne zai karasa Sokoto amsa kiran Babansa babba, Alhaji Abdulkadir Jalloh Ahmad."

**** **** ****

-TAKORINKU 23/3/2026

"Karshen littafi na daya kenan, wanda shine shimfidar LABARIN KELTOUMAH."

"Mu biyo Keltoumah da Mr. Yassar M. Jalloh, don jin amsar da zai samu daga bakin KELTOUMAH, da mahaifiyarta UMMAMI."

"Shin ko Mr. Yassar Jalloh zai cikawa Ummami burinta, na komar da ita cikin ahalinta dake yawo a Sahara daban-daban???"

"Shin ko Mr. Yassar zai samu cikar burinsa, na hada rayuwa ta har abada da AKOKE???"

Yanzu ne zamu fara shiga ainahin gundarin gwagwarmayar rayuwar KELTOUMAH (Khulthoum Mansour). Zamu

"cigaba da karanta labarin marainiya Keltoumah nida ku, muji wata irin SADAUKARWA dake cikin SO na hakikah."

"Littafi na biyu, na uku dana hudu na sayarwa ne. Zasu zo muku a manhajojin TELEGRAM da AREWAPEN. Ku tuntubeni a 07030137870 don a yi tafiyar rayuwar KELTOUMAH  yar UMMAMI tare daku."

Taku a kullum;

Sumayyah Abdulkadir (Takori)

TAKORITES

"A karshen littafi na Daya ina mai farin cikin Kara tallata muku kayan abincin LAZEEZUN na Haj. Aishat Aliyu Sabuwa, Kaduna. Mai kamfanin Lazeezun Venture and Global Services. Khairan Lazeezun mai garin Danwaken Lazeezun mai dadi da gamsarwa, garin"

kunun Lazeezun mai gardi da dakakken Yajin Lazeezun mai dadin dandano.

"Kayan nan na LAZEEZUN ina baku tabbacin daban suke da duk wani kalar garin danwake ko garin kunu ko dakakken yajin da kika sani, ni din dai tested ce, kuma trusted ce akan kayan LAZEEZUN. Na ci na yaba nida iyalina shine nace bazan ci dadin nan nikadai ba tare da na tallata muku Khairun Lazeezun ba."

"Kayan danwaken Lazeezun da garin kunun Lazeezun da yajin Lazeezun suna nan suna ratsawa a wasu daga supermarkets din garuruwan Abuja, Kano, Maiduguri, Kaduna kai har Janhuriyyar Nijar, a yanzu haka garin danwaken Lazeezun da garin kunun lazeezun da yajin lazeezun sun fara tsallakawa har ketare, sun isa UK, Dubai, Egypt, da Saudiyyah, kawai ki tuntubi Haj Aishat Aliyu a wannan lambar waya (08030802900) daga duk gari ko kasar da kike don dandana Lazeezun dinmu mai dadi."

ba!!!

Ban fada muku abinda ban ci naji

Madallah daku.

Takorinku.


Downloaded From https://arewanovels.com


Please Login or Register in order to submit comment