gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 11 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an goge masa ko ina tas, ya ajiye brief case dinsa da wasu files a muhallin da yake ajiyesu, sai ya juya ya fito zuwa barandar ofishinsu."

"Mr. Yassar yayi tsaye kawai a kofar ofishin ma aikata, hannayensa duka biyu zube cikin aljihun kaftan dinsa, kamar yana nazarin wani abu, yana walainiya da dara-daran idanunsa, kamar mai tsimayen bullowar rana da wata."

"Barau ya gama aikinsa yazo zai wuce inda suke kwana, nan ya tadda shi a haka, yace."

" Yallabai ba dai har zaka fita ba? Yassar yace ba tareda ya dube shi ba,  a ah, ba fita zanyi ba, zan dan zaga ajujuwan can da aka kammala ginawa ne, kafin na hada report dina na yau  ayyah, to Allah yasa kada ka hadu da wannan  yar anacen, matarnan mai nacin son ganinka, yau kwana uku kenan tana faman yi mana zarya aka, wai tana nemanka."

Kuma daga dukkan alamu cikin tashin hankali take neman naka .

"Yassar ya juyo yana kallon Barau da alamar tambaya, don bai fahimci zancen nasa"

"ina ya dosa ba, Barau ya gane karin bayani Ogan yake bukata, sai yace."

" Eh, ai wato daga yadda take fasaltamin na gane kai take nufi. Da wata kwamacalar hausarta kamar yare, wallahi sau biyu ina korarta a office dinnan amma gobe sai ta sake dawowa tana rokona ina kake."

Da alama tana cikin matsalar data ke ganin babu wanda zai saurareta ya kuma taimaka mata cikinmu idan ba kai ba.

"Don jiya data ishemu da zarya, abokinka Bayarbe yace ta fada masa ko neman me take yi maka, yace mata baka da lafiya bazaka zo ba amma matar nan taki fada, ta juya ta tafi ta barmu tana kuka ."

"Zuwa yanzu Yassar ya baiwa Barau dukkan hankalinsa, ya shiga tashin hankalin da fuskarsa bata nuna hakan ba, yace da Barau  ta yaya ka tabbatar da cewa ni take nema? Barau yayi dariya yace  to naji tana cewa  don Allah ku kaini wajen Oganku, ina nufin dogon cikinku, mai dogon hancinnan wanda duk ya fiku kirki ."

"A zahiri, Yallabai kai kadai ka siffantu da wadannan siffofin a wajennan yanzu."

"Sannan kai kadai kake kula sha aninsu. Ko ni da nake lebura a wajennan na shaida kafi kowa kirki da yawan taimako a cikin ma aikatan wajennan da sauran ire-iren ku dake zuwa aikin jin kai wajennan, ga ka kuma da dogon hancin da gaske take tubarkallah kamar yadda ta fasalta hanci kam akwai shi masha Allah harda na kyautarwa ."

"Yassar ya dubeshi da hanzari, kallon da ake kira (kallon ya isheni haka) da kyawawan idanunsa masu kama dana basarake, jin Barau ya saki layi yana magana muhimmiya kuma ya koma shirme, shi a wurinsa kallon ya dakata haka kawai yayi masa, amma sai Barau yaga tamkar Mr. Yassar ya harareshi."

Ya russunar da kansa yana fadin  tuba nake Yallabai! Na janye maganar wasa daga cikin kalamaina .

"Yassar yace  jeka nemota, ka kirawomin ita ."

"Da Barau ya wuce cikin sansanin, Mr. Yassar sai ya tsaya standstill a jikin barandar ofishin nasu, harde da dogayen hannayensa a kirji, yana nazarin wani abu a ransa& ."

 Me yayi missing a tsayin absence dinsa cikin halin jinya?

 Me yayi missing da yake ta jin idanunsa na kewar ganin wani abu?

"Ya gane cewa tunda ya shigo camp yau, idanunsa ba abunda sukeyi sai marari da kulafucin son ganin giftawar farar fatarta.. mai haske idanun kowane dan adam da yayi arangama da ita& tamkar tauraruwa Zahrah a cikin taurari ta bakin Femi."

"Lokacin da Barau ya fara yi masa maganar Ummami na nemansa ruwa a jallo, zuciyarsa harbawa ta shiga yi, anan ya ankare da cewa su yayi ta kewa a cikin halin jinyarsa& har yake jin tamkar ya baro wata muhimmiyar ajiyarsa a can cikin IDP camp a garin Anka& ."

"Sai ga Ummami ta biyo bayan Barau sun taho, yau tafiya take faram-faram bazar-bazar cikin sauri kamar zata tashi sama, ko kamar zata kifa don azamar tarar da Mr. Yassar. Amma ba tareda tilon  yar tata ba."

"Sauri take tayi ta taddashi kada a kara ce mata baya nan, ba a san yaushe zai dawo ba,"

tana da yaqinin shikadai ne zai taimaka mata a wurinnan a halin yanzu.

"Yassar tun daga nesa ya karanto damuwa da tashin hankalin dake kwance akan kyakkyawar fuskarta, wadda ta danyi haske yanzu a dalilin tana ganin sabulun wanka, Yassar yayi silar da suke samun yin wanka yanzu koda ba kullum ba suna yi, hakan yasa ta danyi haske jazur da ita abinki da farin mutum."

"Tana isowa gabansa ta zube tana maida numfashi, kamar wadda ta ci uban gudu, ko kamar wadda (at long last) ta ke jin ta iso gaban  savior dinta, a ranta tana cewa  the only shoulder to lie on that she have in this camp Mr. Yassar ne."

"Cikin haki, bayan ta zube a gabansa take magana, cikin sarewa da fidda rai da rayuwar  yarta."

" Kai kadai nagani mai idon Rahma da tausayi garemu a sansaninnan, kuma kai kadai ka taba taimaka mana ba tareda ka damu da korafinmu da aibantamu da aketa yi a idonka ba."

"Hatta a kwayar idanunka na fahimci kai mai kyautayi ne da zuciyar Imani, mai son taimakon mara gata ne."

"To yanzunma bata canza zani ba taimakonka nazo nema; ka taimaka mini Dan nan, diyata Keltouma ce babu lafiya."

"Yassar yaji wata mumunar faduwar gaba, murya na karkarwa yace,  don Allah Ummana ki tashi daga kasa, ni dan ki ne, ki daina durkusa min, me ya sameta haka? "

"Ummami ta gaya masa cewa  yau kwananta uku tana amai me jini a ciki, wani lokacin har da guda-guda, babu wanda ya kallemu a sansaninnan, balle wani ya nuna yasan halin da muke ciki."

Ina tsoron kada itama na rasata& ina tsoron rasata kamar yadda na rasa mahaifinta& &  .

"Ta saka fuskarta a tafukanta ta fashe da kuka tana fadin  ka taimaka min Dan nan, yadda Allah ya taimakeka, ita kadai ta ragemin da nake gani inji dadi yanzu a duniya! ."

"Yassar yace  to ki tashi daga wannan kwanciyar a gabana, ai bai kamata kina"

"durkusa min ba, in dai kin yarda cewa ni Danki ne ."

"Amma ta kasa tashi, sai kara jujjuya kai take tana rokonsa  ka taimaka min kada in rasa KELTOUMA& . Bamu da kowa a sansaninnan sai Allah sai kai, da zuciyata ta amince min cewa mai kirki ne kuma mai son taimakon bayin Allah ne, koda baka furta ba na fahimci kana tausayinmu."

"Duka sansaninnan kowa na jin dadin rayuwarsa banda mu, ban san maiyasa muka zama saniyar ware ba, ko saboda yarenmu ya banbanta da nasu, ko kuma don kalar fatar mu ba irin tasu bace?"

Mutanen Najeriya ashe mutanene masu kabilanci. A yau ina nadamar shigowarmu kasar Najeriya& .. .

Sai Yassar ya katseta cikin kwantar da hankali da cewa.

 ba wai duka  yan kasar nan muka taru muka zama daya ba akan dabi armu ga bakin haure.

"Akwai masu tunanin cewa addinin Allah (Islam) ya hada mu, sannan  yan adamtaka wato kasancewarmu duka jinsin  yan Adam"

"shima ya hada mu ,ba tareda banbance yare, addini ko kabila ba daga cikinmu ba ."

"Ko Ummami bata fada ba kasan taji dadin kalamanshi baka da zuci. Barin da yace a daukota aje asibiti. Har kana iya karantar ajiyar zuciyar samun sassauci akan farar fuskarta, da share hawaye data yi cikin samun relief."

Yassar yace  Barau!

Barau dake gefe yana sauraronsu yace

 na am Yallabai

 Jeka kirawo min women s camp leader .

Barau Ya juya cikin sansanin. Ba jimawa suka dawo tareda wata tikekiyar mace kamar Basamudiya don girman jiki. Tana isowa ganin Ummami sai ta hade fuska tana fadin.

 Au! Karata kika kawo kenan? Don na dauki Omonki guda daya da sabulun wanki rabi?

" Ni nace a kira ki inji Mr. Yassar cikin hade fuska sosai. Sai ta nutsu ta maida hankalinta gareshi. Mr. Yassar yace  ki taimaka mata kusa yarinyarta a bayan motata, muje likita ya dubata ."

"Camp leader tace  toh ranka shi dade, ai matar nan ce akwai ban haushi, ta fiye shiru- shiru na munafurci da nunkufurci ita a dole ba a sonta, shiyasa bana shiga sha aninta, ban haushinta yanada yawa kamar a kanta a ka fara zaman Sansanin Gudun Hijira."

"Ita kuma  yar tata kamar diyar gwal, haka take lallabata kamar ita kadai ce  ya a wurinnan, sai kukan banza da wofi kamar wadda ake yankar naman jikinta ."

"Ta fadi hakan cikin kunkuni da mita, da alama mutum ce mai mitar tsiya kuma ta dade tana jin haushinsu."

"Yassar ya kara hade giran sama dana kasa. Don haka camp leader da rawar jiki tayi shiru haka, ta bi bayan Ummami zuwa ajin da suke kwana, da taimakonta aka saka Keltouma a motar Yassar don kuwa goyota tayi gabadaya a bayanta kamar ta goya karamin yaro, Camp leader kakkarfar macece samun irinta cikin mata sai daidaiku, ta shiga gefen Keltouma bisa umarnin Mr. Yassar, sai ya umarci Ummami ita kuma data shiga gaban motar."

"Wani Asibiti mai zaman kansa Yassar ya kai su anan cikin Anka, nan da nan likitoci"

"suka karbeta, wuni guda an kasa gano hakikanin me ke damun Keltouma har saida aka kira CMD na asibitin bakidaya."

"Da kansa yayi nasa gwaje-gwajen, likitoci da Nasis suka maida hankali wajen diyar Ummami sosai albarkacin Mr. Yassar da ya bude bakin aljihu kota ina don a kula da ita, ta sha ruwa wajen leda uku kafinma ta fara dawowa hayyacinta. Awanni uku da zuwansu Keltouma ta samu barci akan gadon asibitin."

"Wannan uzurin ne ya rikeshi a camp yau, don saida ya tabbatar Keltouma ta bude ido bayan ta tashi daga barcin data samu, ta fara shaida wadanda ke kanta ta hanyar ambatar sunan mahaifiyarta, sannan yace ma Ummami zai tafi masaukinsa, sai gobe in sha Allah idan ya shigo camp zai biyo zo ya ga jikin nata a kuma karbi sakamakon gwaje-gwajen da aka yi mata."

"Yassar ya cikama Nurses on duty ido sosai, shiyasa suka rika kula da  yar Ummami, camp leader ya barwa kudi ko zasu bukaci wani abu, bayan ya je ya lafto musu abinci a restaurant din asibitin, da sayayyar abubuwan amfani a wani supermarket dake like da asibitin."

Wannan girmamawa da tagomashin alherin da Yassar ya yiwa Camp leader ta hanyar damka mata kudi a hannunta yace ta kula dasu shi yasa ta koma kula dasu Ummami da rawar jikinta. Amma bayan tafiyarsa kudin ta soke a jikinta bata saya masu komai ba.

"A matukar gajiye ya koma Gusau yau, sallar maghriba da isha kadai yayi ya bi lafiyar gado."

"Daren yau duk juyin da yayi da tunani da damuwar Keltouma na kwance gadon asibiti yake yinsa& . Har ya soma tuhumar kansa kan cewa damuwarshi kan sha aninsu yayi yawa, tausayinsa da yawan kulawarsa a kansu ya wuce kimar da zai iya bada hujja."

Bai san dalili ba kawai jinsu yake tamkar barin jikinsa.

A duniya Yassar ya san bai taba damuwa da wani bare da saka shi a rai irin yadda ya damu dasu Keltouma ba.

"A duk sanda ya tuno idanunta dake cike da hawayen shagwabar nan sai ya ji matsananciyar faduwar gaba, da wani nishadi mai sanyi a ransa, shagwabarta da (delicate nature) dinta su suka sa yake yawan tunata,"

"sukayi dalilin da ya sakata sosai a ransa, alhalin yasan shi baya shiri da shagwababben yaro."

"Ya sha gayawa kansa ita kam Akoke shagwabar ta karbeta, idan akwai wanda shagwaba take yiwa kyau a duniya to Keltouma  yar Ummami ce."

"Ummami, tanada wata kebantacciyar baiwa akan kaunar  yarta, wadda ba duk iyaye mata keda su akan  ya yansu na fari ba, wadannan dalilan suka sa yake ganin girmanta take kuma burgeshi."

"Ya taso a extended family din da aka fi favoring haihuwar  ya ya maza, ake gasar haihuwarsu a tsakanin (iyayensu mata), don sun fi yi musu dadin competition a tsakanin kishiyoyi da faccaloli, ita kuwa wannan Ummami madaukakin son da takewa  yarta ta fari kuma mace, sai kayi tsammanin bata san wani abu wai shi haihuwar da namiji ba a duniya."

"Kasa jiran Femi ya gama shiryawa yayi, a washegari kenan, ko karin kumallo bai tsaya yayi yadda ya saba ba, Allah kadai yasan irin wahalallen barcin da Mr. Yassar yayi a daren"

yau saboda zullumin result (sakamakon gwaje- gwajen da aka yiwa Keltouma).

Don haka shikadai ya kama hanya da sanyin safiya yayi tafiyarsa Anka bai jira Femi ba.

"Office dinsu ya fara zuwa amma bai iya kulla komai ba, hankalinsa yana kan lafiyar Keltouma, duk tarin ayyukan dake gabansa haka ya tsallakesu don hankalinsa gabadaya yana can asibiti, ya adana system dinsa da sauran tarkacensa dake cikin brief case a muhallinsu na kodayaushe, sannan suka gaisa da Haladu da Regina, wadanda suma yau duk sunyi sammakon zuwa, sai yace ma Haladu zai je ya dawo koda Mrs. Sylvanus tazo yace tayi masa aikin da ya bar mata."

"Ya iso asibitin wajejen karfe goma na safe nan ya samu babban likitan ya iso, shi da ma aikatan jinya duk akan Keltouma suna bata taimakon gaggawa, jikin nata ya rikice gabadaya, Ummami tana gefe tana sallar walha, tana addu ar nemawa diyarta sauki."

"Likitan dama isowarshi yake jira, yana zuwa ko gaisawa likita bai bari sun gama yi ba ya ce su biyo shi zuwa ofishinsa shi da mahaifiyarta, don tace dashi ko menene likitan"

ke son gaya mata ya bari sai wanda ya kawosu ya zo sannan ya gaya masu tare.

"Yassar da Ummami a gaban bahaushen likitan. Yassar ya zauna a kujerar dake fuskantar likita, Ummami ta zauna a kujerar dake kallon wadda Yassar ya zauna, Likita ya bashi hannu suka gaisa, sannan ya warware takardun sakamakon yana nuna musu komai cikin takarda da kwamfuta yana hadawa da bayani yadda dukkansu zasu gane, na sakamakon binciken da suka yi akan aman jini da Keltouma keyi."

"Sun hada hankulansu sun bashi suna saurare, Ummami dai ita ta haifi Keltouma amma kirjinta baya dagawa da sauka kamar yadda na Mr. Yassar keyi, a lokacin da likitan ya kammala yi musu bayanin abunda ke tareda  yar Ummami."

 Gastric Ulcer .

 Tsananin yunwa ce da stress na damuwa suka jawo mata .

"Yassar yaji wani irin ba dadi a zuciyarsa, yayi shiru ya kasa magana, ita kuwa Ummami zuruu tayi da ido, hannayenta na"

zube kan teburin likita. Don Batasan meye ma anar Gastric Ulcer din ba.

"Lokacin da likita ya fadi makudan kudaden da treatment da jinyar zasu lashe, Ummami sai ta fashe da kuka wiwi."

"Likita da Yassar suka rasa yadda zasuyi su lallasheta, tace  likita ku barni inyi kukana, shine kadai abinda zan iya, ni bani da ko sisi."

Ita kenan na mallaka a duniya na baro kowa nawa banida halin komawa.

Ina zan nemo wadannan kudaden daka ambata don nemawa Keltouma lafiya?

"Ba zan daina kukan rashin mahaifinta ba, har duniya ta nade tunda a rashinsa ne rayuwa take ta fallasa mu."

"Sai yanzu ne nake da tabbacin mune  yan gudun hijira, mun rasa bango abun jinginarmu, har yunwa na neman hallakamin  ya, abunda kafi karfi ace yau yafi karfinka (abinci) bamu da sauran gata sai na Allah nida diyata Keltouma tunda babu Monsour babu mai maida mu gida& ."

"Mu ba komai bane face  yan gudun hijira, bamuda inda zamu samu wannan kudin, na dade ina rokon Allah kan har in gama rayuwata ta duniya kada ya salladamin"

"yin bara, kamar yadda Keltouma ta zabar mana . Sai kuka."

"Yassar ya ji wani sabon tausayin Ummami ya dada kamashi, soyayyar da take yiwa  yarta mai girma ce. Itada Ammihnsa Haj. Tarha bai san wa yafi wani soyayyar  ya ya ba, zuciyarsa tayi nauyi ainun da kukan da Ummami keta yi, sai ya katseta da cewa."

" Ummami ki nutsu, kada damuwa tasa ki raunana imaninki mana, Allah na sane dake."

"Sanda Allah ya tashi baki ita, baki san zai baki ita din ba, ki tuna Allah shine gatan bawa ba iyaye ba, ba kuma ya barin wani don wani ya rayu ko yaji dadi idan wa adin wancan din ya cika."

"Abinda likita keso daga gareki shine, ki kwantar da hankalinki yadda zaiji dadin gudanar da aikinsa na nema mata lafiya ."

Sai Ummami ta share hawayenta da habar zaninta tace  ta ina hankalina zai kwanta banida kudin da likita ya ambata?

"Yassar yace cikin bata rai  ki kwantar da hankalinki abunda likita ke bukata daga gareki kenan, babu wanda yace ki kawo kudi! ."

"Zuwa yanzu ta fara samun relief, sai zufa (jibi/gumi) da take sharewa

Please Login or Register in order to submit comment