gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 10 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a banida lafiya, zai fi min sauki ."

"Femi yayita dariya kafin yace.  ina nan dai ina zuba ido! Don ko marasa lafiyan ma ai suna aure suna dan romanciyya da matan, amma banda kai ."

"Ya dafe murfin motar da Ogan nasa ke ciki yana masa murmushin shegantaka, yace  drive with care Boss."

"Karya nake ince jan mutunci da class, tsare mutuncin kai da halin girma irin naka baya burgeni! ."

"A haka Yassar ya bar Femi. Ya kama hanyar Tambuwal dauke da  Adhkaris Sabah a bakinsa, jefi-jefi yana tukinsa yana amsa wayoyi ta hanyar amfani da (earpods), yawancin wayoyin da Mr. Yassar yake amsawa daga hedkwata dinsu ne, wasu daga iyayensa dake kasar Mexico."

"Har ila yau, Family dinsu Yassar kasancewarsu mutane ne masu zumunci da hadin kai, hakan yasa in aka ji mutum shiru na wani dan lokaci sai an samu wanda ya neme"

"shi a waya don jin lafiyarsa kawai, shi kam Yassar abin ya hadu da farin jininsa a ko ina ba a cikin danginsu kadai ba, mutum ne mai matukar shiga rai, don haka ya zama mutum mai yawan ta ammali da amsa kiran wayar jama a data  yan uwa da iyaye a koda yaushe, ba daga danginsa ba, ba daga abokanan aikinsa ba, ba ga makotansa ba kowa kiran Muhammad Yassar yake don jin lafiyarsa a Zamfara, shiyasa kusan koyaushe baya zama shiru, sai in yaso yin wani muhimmin nazari ne ko hutawa ko aiki na nutsuwa yake kashe wayoyinsa gabadaya."

"Sokoto ya fara shiga bisa umarnin zuciyarsa na ya fara gamawa da Baffanninsa kafin ya wuce Tambuwal, don haka gidan Alhaji Abdulkadir Ahmad Jalloh Yassar ya fara nufa."

Tun a bakin gate maigadi ya gaya masa babu kowa a gidan sai Sahlah da masu aiki.

Har zai koma ya wuce gidan Yaya  yar Dada (Haj. Shafa atu) sai kuma ya fasa ya fito zuwa cikin gidan don yasan in Yaya Babba (Alhaji Abdulkadir) yaji ya zo har kofar gidan

ya juya ya tafi bai shiga ba Allah kadai zai raba su.

"Sahlah Abdukadir Jalloh, wadda kawayenta ke kira Sahlah Jalloh, kanwa take ga Yassar tunda kuwa  yan maza zar suke."

"Sahlah bata da tsayi cancan tanada kyau, kyau mai sanyi irin na jikokin Jalloh Ahmadu, wankan tarwada ce mai manyan idanu da yawan son ado da iya yanga."

"Ita kadai tayiwa Yayan nata kyakkyawar tarba ta hanyar kawo masa ruwa, spiced tea, da kuma lemon kwali, sannan tace da mai aikinsu a shiryo lunch a kawowa Yayansu na Mexico falon Daddynsu."

"Bai zauna a falon ba sai da ya shiga toilet ya dauro alwallah, yazo yayi sallar data riskeshi a hanya sannan ya zuba tea din yana sipping kadan-kadan, har yanzu ba kowanne abinci Yassar ke iya ci ba duk da fadan da Ammih tayi masa kafin tahowarsa sai abunda ba a rasa ba."

"Musamman da yake gashi yaga wannan din ma masu akin gidan ne sukayi, don ko daga yanayin  ya yan Yaya Babba ka san basu shiga aikin abincin gidansu."

"Sahlah ta zo ta gaisheshi bayan ta tabbatar ya kimtsa, karshen iya ado na  yammatan zamani to Sahlah Jalloh ce, a kasaicensa da yanayin fuskar da ya saba yiwa kannensa magana cikin rashin walwala Yassar yake tambayarta,"

 ke kadai ce a gidanne har yanzu?

"Nan take gaya masa ai ba yau jama ar gidanma zasu dawo ba, su Hajiyarta da Anti Amina kishiyarta sun je biki Birnin Kebbi, itama don tana da semester exams ne yasa bata bisu ba."

"Da ganin Sahlah kaga hadaddiyar ajebo, kuma  yammatan dake ji da kansu da ganiyar  yammatancinsu a level one din jami a (JJC) a Danfodio take karatu."

"Sahlah bata kai ga rufe bakinta ba daga bayanin da take yi masa, bayan ta zauna a kujerar dake fuskantar sa, kawai sai ga Yaya Babba wato mahaifinta Alhaji Abdulkadir yana saukowa daga matattakalar bene, daman falon data yima Yassar jagora zuwa can nasa ne da bakinsa na jiki."

Tun daga matattakalar benen farko idanun Yaya Babba suka sauka akansu. Wannan ganin da Alhaji Abdulkadir yayi

musu a yau suna magana a hankali da juna ya kayatar da idanunsa. Kuma nan da nan ya sake darsa masa abunda ya dade yana darsawa a ransa.

"A idon Yaya Babba, Yassar da Sahlah sai suka yi matukar dacewa da juna."

"Ya dade dama da sha awar hakan a ransa wato nagartaccen dan sa Yassar yaci tudu biyu a gareshi; ya cigaba da zama dansa, kuma ya zama surukinsa akan Sahlah ko kanwarta Shafa atu."

Allah shine shaida in Yaya Babba yanada wani babban buri a yanzu to wannan ne kawai.

"Don haka Alhajin ya kara fadada far arsa sosai, yace  Marhaban da Da na, welcome my Son, yanzu kake tafe? "

"Yassar ya safko da guiwoyinsa kasa daga kan kujera ya duka har kasa yana gayas da Babansa, sai Yaya Babba ya shafa kansa da hannunsa na dama."

"Yace  yaya aikin naku a Zamfara din? Yassar ya amsa masa da komai lafiya, ya shigo ne musamman don ya gayas dasu, sai kuma gashi ya doki gurbi su Hajiya duka bai samesu ba, shine ya tsaya don ya gaida shi ."

"Cike da farin ciki Alhaji Abdulkadir yace  madallah da Dana na kaina, ku cigaba da hirarku kaida kanwarka, ni fita zanyi."

"Ya harari inda Sahlah ke zaune yana cewa da ita  kiyi serving dinsa mana? Kin girka masa fulasai a gaba ko budewa bakiyi ba, kuma ki tabbatar yaci abincin sosai don na san shi da wasa da ciki ."

"Sahlah tace  Toh Abbah, amma ai shigowarsa kenan ."

"Ta mike a yangace zuwa gaban warmers din don cika umarnin mahaifinta Yassar din shima yayi fit! Ya mike, ya rufawa Baban nasu baya yana fadin."

" Abbah ai nima ba zama zanyi ba, naci abinci kafin na fito, a kan hanya nake, daga nan zan wuce Tambuwal ."

"Alhaji Abdulkadir ya dan dakata da tafiya, kafin yace  ma ake a Tambuwal din? Don shi sau tari ma mantawa yake da Baba Ado, dattijon kamar wani neglected ne a wurinsu, Yassar yace,"

" babu komai Abbah, zan gayar da Baba Ado ne ."

"Yaya Babba yace  au toh! Ya bar shigowa garin nan sam, tunda jimawa rabon da in ganshi, shiyasa na kan manta yana raye."

"Kasan shi sha anin tsufa, shi Baba Ado kowa yaje wajensa sai yayi ta korafin bama gaishe shi, shiyasa nagaji na rabu dashi don ni mutum ne marar jure korafi."

"Allah na tuba yadda sabgogin rayuwa suka taru suka yiwa dan adam yawa ina zan ke tuna wanda ke can kauye? Banda abun Baba Ado shi fa da kansa ya zabi zaman kauye, kuma na me zai damu mutane don basa zuwa? Alhalin idan yana son gidan zama anan yayi magana zamu bashi?"

"Yanzu kowa al amuran neman cigaban rayuwa dana sungullar iyali sun sha kansa, banda kai cikin yarannan babu mai jure zaryar hanyarnan da ko kwalta cikakkiya babu ."

"Yassar bai ce komai ba, don inda sabo ya saba da irin wadannan maganganun na borin kunya na Yaya babba, a duk lokacin da ya ambaci Baba Ado a gabansa, amma ko kadan baya jin dadin maganganun da Baban nasu yake yi akan Baba Ado da tushensu wanda shine kauyen da yake rainawa, Yassar yace a"

"ransa wasu abubuwan ai ba sai gwamnati ta yiwa kasar haihuwarka ba, kai a matsayinka na dan kasa nagari ya dace tunda kanada hali ka shimfida kwaltar a garin iyayenka da Kakanninka."

"Har aka budewa Yaya Babba jibgegiyar motarsa ya shige gidan baya, yana kara jan ra ayinsa kan ya koma cikin gida yayi zamansa Sahlah ta taya shi hira, sannan ya wuce inda ya nufa. Yassar yace  toh ."

"Amma Yaya Babba yana fita Yassar bai koma cikin gidan ba shima tasa motar ya shige yayi kyakkyawan reverse, ya fita daga gate din gidan Yaya Babba."

"Ganin zaiyi dare yasa ya hakura da zuwa gidajen sauran Baffaninsa yau, wato Uncle AbdulQayyum da Alhaji Abdulwahhab, ya ja tayoyin motarsa a sittin, bai kara tsayawa a ko ina ba daga gidan Yaya Babba ba sai a garinsu Tambuwal, kofar gidan Ksakansa Baba Ado."

"A zauren gidan Baba Adon ne zaune bisa tabarma karauni, akanta kuma farin buzunsa na da yake kai, yayi matashi da tum-tum, a soron gidan Baba Ado akwai allunan"

dalibansa da Gafakar Alqur ani mai rubutun warshu.

"A gabansa kwanon farau-farau ne cike da tsinkakken Koko, haka yake yi in zai sha koko sai ya kwara masa ruwa ya maidashi farau-farau."

"Kasancewar tun kafin Yassar ya iso Tambuwal sunyi waya da Baba Ado ya gaya masa cewa ya kusa, don haka tuni Baba Ado ya tanadar masa abinda yake so wato ya aika an sayo masa balangu mai zafi na babbar tukuba na naman rago, da sabuwar damammiyar fura da taji sabon nono kindirmo da zuma."

"Dattijon ya kamo hannun jikan nasa ya zaunar dashi a gefensa, yana cewa  zo zauna daga kuturina, dawo nan zauna daga gefena duk motsin da nayi in san kana gefena ."

"Yassar tun kafin ya zauna ya soma sakin mita irin ta yaran da suka san kakanninsu na ji da su, suna kuma jurema mita da korafin rigimarsu."

"Yace  ni dai gaskiya Baban Tambuwal ka daina yimin irin wannan kiran na afujajan, wanna in inada  bp ai sai kasa ya kara hawa, in kayi hakuri ai kasan nida kaina ba sai ka"

"kirani ba, idan a samu faraga zaka ganni ne da kafafuna."

"Amma baka san irin yawan ayyukan dake gabana ba a Camp, zaka ce lallai lallai in bar komai in taho a washegari? "

"Baba Ado cikin lallashi da karya murya yace  to ni ka san dalilin da yasa na kirawo ka din? Ka san muhimmancinsa? Kayi hakuri mana, ka zauna tukunna, ka sha furar dana tanadar maka ka koshi, don na tabbata baka ci abinci ba, daga sannan sai kaji dadin yimin mita ."

"Yassar yana zama Baba Ado ya miko masa karamar kwarya cike da koren magani, yace  shanye wannan maza ka shafe sauran a jikinka da fuskarka ka bani kwaryar ."

Yassar ya hau yamutsa fuska cikin kyankyami yana fadin  Baba & . Please& . Kayimin rai. Ina shanye wannan koren dattin ai sai buzuna .

 Ni kuma bazan sallameka ka koma Zamfara ba sai ka shanye dattin nawa tas.

"Tunda kazo kasar nan Yassar hankalina bai kwanta ba, nikadai nasan irin mafarke-mafarken dana ke tayi akanka ."

Abun ya baiwa Yassar dariya yace  to Baba Ado wannan maganin ne zai hanaka yin mafarki na? Ai don ka sakani da yawa a ranka ne shiyasa kake yin mafarkina. Amma Baba Ado ya dage sai ya sha maganinnan zai kyaleshi ya koma Zamfara.

"Yassar sai faman cakuda fuska da cije baki yake yin da kyama sosai yake kallon koren ruwan maganin fatau da Baba Ado ke ikirarin sai ya sha, yana kissima irin rudewar da cikinsa zai yi da zarar yayi kurba daya bama shanyewa ba."

Baba Ado ganin tashin hakalin da jikan nasa ya shiga akan shan ruwan maganin da ya bashi sai ya koma lallashi ta hanyar bubbuga kafadunsa. Ya karkatar da kai yana mai nuna damuwarsa sosai da son Yassar ya sha maganin.

"Yace  sunansa  ganyen magarya , hakukuwan asali ne da Annabi SAW yayi mana nuni da amfanin ganyayyakinsu, wajen tsarin jiki da neman waraka daga kowacce cuta, kariya daga sharrin mutum ko aljan da kuma sihiri."

"Ka sha ka shafe jikinka kaji Muhammadu Yassar, hankalina yaki"

kwanciya da yawan mafarkan dana ke tayi a kanka. Kasan dai bazan baka abinda zai cuceka ba.

"Wannan maganar ta karshe da Baba Ado yayi ne tasa Yassar jin wani iri a ransa, kuma a take ya karbi kokon ya kafa kai ya rufe ido, sannan yayi bisimillah ya shanye tas."

"Baba Ado cikin jin dadi yace,"

 to ko kai fa? Zaka ce na gaya maka ko bana raye.

Na baka maganin tsari. Wanda ba dai mutum ba ko aljan su yi rinjaye akanka sai ikon Allah; Buwaya gagara misali .

Daga nan suka cigaba da hirar su irin wadda suka saba amma koda wasa Yassar bai gayawa Baba Ado irin maganganun da Yaya Babba yayi akansa ba.

"Sai dare sosai ya shiga Gusau, gajiyar tuki da sanyin damuna kuma suka taru masa suka murkushe shi a kan gadon hotel, sallah kawai ya iya yi ta maghriba da isha da shafa i da wutrin da suka riskeshi akan hanya, sai yabi lafiyar gado ya dukunkune kansa yanata rawar dari."

"Zazzafan zazzabi yazo yace salamu alaykum ga Mr. Yassar, ya kan dade bai yi ko ciwon kai ba, amma idan ya fara ciwo baya sha ta dadi, yau da stress ya zo ya rafkeshi gabadaya ko wayoyinsa bai iya ya kashesu ba, a haka ya kwana cikin lallausar bargonsa, cikin azabar zazzabi da massasara yana ta rawar dari."

"A rayuwar Yassar bai taba sha awar yayi aure ba sai yau. Ganin ya kasa amfanawa kansa komai daga kwance. Yanada gatansa, amma gashi yau zai mutu a daki babu mataimaki. Ko babu komai yau da ace yana da aure matarshi zata miko masa kwayar magani da gorar ruwan da ya kasa ko mikewa ya baiwa kansa, gashinan ko motsi ya kasa, balle ya isa ga inda yake ajiye (first aid) dinsa."

"Haka ya kwana linkif cikin masassara da ciwon kai, har garin Allah ya waye akan kunnensa bai samu runtsawa ba."

"Sai wajen karfe shida na safe ne Yassar yaji dan karfi ya zo masa, ya lallaba ya shige bathroom yayi alwallah yazo yayi sallahr asubahi itama daga zaune. Sakamakon kafafunsa sun kasa daukar tsayuwarsa. Don"

"haka duk yadda yake da muhimman ayyuka ranar yau a camp, bai iya yabi Femi sun tafi office tare ba a wayewar garin, ta waya sukayi magana, da kyar yace da Femi yaje kawai yau baya jin dadi."

"Femi bai tafi ba sai da yazo kofar dakinsa yana kwankwasawa, da kyar ya mike ya saka bedshoe dinsa ya isa ga kofar ya budewa Femi."

"Kallo daya Femi yayi masa yace  this is serious Boss, kana bukatar ganin likita . Shine ya kira likita ya zo ya duba shi, har abinda yaki jini saida likita yayi masa watau allura."

"Likitan yace stress yake tarawa kansa, lallai ya huta da fita kona kwana uku ne."

Ya kuma bashi maganin da ya dace ya bashi. Femi ya taimaka masa da ruwa ya kora magungunan. Don haka yau Femi shikadai ya tafi Anka. Da alkawarin zai masa dukkan ayyukansa.

"A daddafe yayi kwana ukunnan a dakinsa bai fita ko reception ba, bai je ko ina ba bayan barandar shan iska ta kofar dakinsa, bai je wajen aikinsa ba ko bakin pool da yake yawan zuwa da daddare ya huta, yana daki daga toilet sai sallah, sai azkar a dan littafinsa"

"na Hisnul Muslim, sai tilawa sai gado, ko abinci yake so saidai yayi waya restaurant din hotel ma aikatan su kawo masa har kofar dakinsa."

A haka ya kwashe kwanaki hudu cikin halin jinya. Amma me? Yassar jinyar gangar jikinsa kawai yakeyi zuciyarsa tana like can a wani wuri daban bata tareda gangar jikinsa.

"Dalili kenan da harlokacin ko wayoyinsa ya kasa budewa yau kwana hudu, sai fama yake da kwakwalwarsa da zuciyarsa wajen fafutukar son gane ME YAKE KEWA ma ana (me yake missing daga kasan ruhi har zuciyarsa wanda ya mamaye ransa ya hana shi jin ciwon dake addabarsa sai wannan wawakekiyar kewar?"

"Bilhakki ji yake yana kewar ganin wani abu. Yana matukar kewar wani abu a ANKA bayan aikinsa, da abokan aikinsa su Femi da sauransu."

"Bai tashi gane me yake kewar ba sai a washegarin ranar wadda ta kasance Alhamis, ya samu shiryawa ya tafi IDP Camp, Femi ranar baya nan yaje ofishinsu na Bauchi kan wani (three day official assignment)."

"Kasancewar accommodation/ reservation din watannin da zasuyi gabadaya UNICEF ta kama musu da hotel din NAHUCE HOTEL, Zamfara, wanda ke tsakiyar birnin Gusau, hatta laundry na kayan sakawarsu yana cikin tanadin masaukinsu, hakan yasa baya bukatar zuwa ko ina bayan abinda ya kawo shi Gusau din. Amma Femi yawonsa yake sosai a cikin gari."

"Yana karya kan motarsa a titin da zai shigar dashi garin Anka, wani bakon tunani ya bakunceshi, yau sati daya kenan (kwana bakwai) cur! Rabonsa da ganin kyawawan idanun kuka na AKOKE& those teary eyes din na (Keltouma)."

Sai yayi murmushi ya saka hannu yana shafa sumar kansa.

"Ma aikatan camp din yau tsilli-tsilli ne suka zo, Haladu ma shugaban ma aikata bai zo ba, daga Barau mai goge ofisoshin da sharesu sai wata mace Regina, ita Regina ma aikaciyar wani NGO ce dabam, tazo yin research akan rubutun Ph.D da take yi akan  yan gudun hijira."

"Yana shiga office din Regina ce ta fara gaidashi, ya amsa yana kokarin karkade"

"mazauninsa da hankacinsa, duk da cewa

Please Login or Register in order to submit comment