gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 4 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan juyo daga kan wayarsa, yayi ma abokin aikinnasa dake bayan mota kallo na tsanaki cikin alamu na nuna rashin fahimtar inda zancensa ya dosa."

Femi ya kara gyara bayaninsa da cewa.

" Yanzu saboda Allah Boss, kanada irin wadannan hadaddun Decent Agbada (kayan al ada) amma ka zauna kake fama da makure wuya (tsuke wuya da necktie), da aikin zanzarewa cikin wando kamar wani tsuntsu wai shi Jemage? ."

"Kin cewa Femi komai yayi, don inda sabo ya saba da shakiyancinsa. Ya juya ya maida fuskarsa kan wayarsa."

"Ngozi ma da bata cika saka musu baki ba musamman inda Oga Yassar ake hirar, yau saida ta sako musu baki da cewa."

" he s right Sir, you are looking different today! ."

"Kasancewarsa wankan tarwada mai hasken kala, gashinan fes dashi don tsabta, kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba shi, ba karamin kwanciya shaddar tayi a lallausar fatar jikinsa ba. A kansa bakar hular yayin samari ce wai ita  Tonak . Hannunsa na hagu kuwa daure yake da bakin agogo hannun maza na  Movado ."

"Yassar Jalloh, saurayi ne dogo kyakkyawa, wanda ya mallaki kyakkyawar sura ta asalin  yan Africa, surar da farat daya kwarjininta da cikar zatinta zai sa ta saye zuciyarka a kansa."

"Gashi da mikakken hanci siriri, da wasu irin lumsassun idanu kamar misalin na mai jin barci."

"A yawancin lokuta idanunsa kamar wani maganadisu ne (magnet) da zasu motsa zuciyar mai kallonsu, hard ai idan macece, nan da na zasu hargitsa tunanin duk mace data yi kuskuren ko gangancin kallon tsakiyarsu, zuwa wani tunanin na daban mara tushe."

"Yanayin kallon dake cikin halittar kwayar idanunsa, shi yafi komai sayo masa"

kauna da soyayya a zuciyar wanda duk wanda yayi kuskuren hada idanu dashi.

"Yassar mutum ne daya da daya ko a cikin  yan gayun maza, gashi da tsaftar bugawa a misali, ya iya sanya sutturar da zata dace dashi da kowanne yanayi; a koyaushe zaka ganshi tsaf-tsaf, dressing dinsa mai tafiya da yanayi ne, da al adar wajen da yake ciki a lokacin."

"Abin nufi, Yassar yana kwalliyarsa ne dai-dai da yadda zaka ga ta dace da al adar mutanen wajen da yake, ko kuma yanayin da ake ciki."

"Kai tsaye idan kayi arba da Yassar Jalloh, zaka kira shi gogaggen Bafillacen dan boko, wanda ya samu horo cikin ilmummukan zamani daban-daban, tun daga kananan shekaru na kuruciya."

"Kamar yadda muka ji a baya mahaifiyarsa Hajiya Tarha daga wani babban gari a jihar Sokoto wai shi Dogon Daji aka auroma Abbih ita, tun auren saurayi da budurwa."

"Tarha tun zamaninta kyakkyawar mace ce, bafullatana, kamar ta hada iri da larabawa, hakan take har tsufanta, bazaka taba iya gane"

"shekarunta ba, sabida Abbih yana kula da ita matuka gaya. Inda mai cin kudin Abbih a duniya, to Ammih da Ibnynta ne."

"Har suka shigo garin Anka Femi da Ngozi ne kadai ke tattaunawa a tsakaninsu, suna magana ne akan yadda zasu tsara shige da ficensu kullum daga Gusau zuwa Anka, da sauran wuraren aikinsu da shakatawarsu."

"Tafiya dodar! Ta awanni biyu kwarara daga Gusau ce ta kawosu garin Anka, inda acan zasu yi aikin project dinsu."

"Yassar dake gidan gaban mota amsa wayoyinsa kawai yake yi, cikin kan wayoyinsa guda biyu, anata tambayar saukarsa lafiya, daga gida ne, daga hedkwatarsu ne, daga Sokoto ne, kai har Uncle dinsa QS (Baba Sultan) saida ya kirashi don jin yadda ya sauka a Gusau (Attahiru autansu Abbih)."

"Ammih kuwa saida yayi da gaske ya samu ya katse wayarsu, lokacin da suka doso gate din shiga IDP camp din."

"Domin Ammih data fara koro masa labari, duk abubuwan da suka faru a gida bayan tahowarsa saida ta kwashe ta soma"

"labarta masa, kai Ammih da Ibny sai Allah! Don har da labarin magenta da take kiwo mai suna (Saghirah) ta haifi  ya yan maguna goma sha biyu jiya saida ta bashi. Tace gasunan sun lullube Saghira sunata sha nonon uwar gwanin bann sha awa, sunata kewarka."

Kamar haka nakeso ka cika min gida da

 ya ya nima .

"Shi dai murmushi yake, daga baya ya zarce da dariya, wai harda maguna a kewarsa. Yanata dariya yace."

 Ammih Ho! Ammih sarkin labari&  .

"A dai-dai lokacin suka iso gate din shiga IDP Camp, dole yayi mata sallama. Yace in ya koma hotel zuwa dare zai sake kiranta ta karasa masa labarin Magenta Saghirah da yaranta."

**** **** ****



"IDP CAMP, ANKA"

"tsarin aikinsu kullum a Camp din zasu dinga wuni, don tabbatar da cewa project dinsu ya tafi daidai da yadda"

aka tsara musu aiwatar dashi a workplan

dinsu.

"Target dinsu shine samar da ilmi ga kananan yara  yan gudun hijira a inda suke zaune, ilmi mai kyau kamar na kowa, ta hanyar gina musu makarantu a inda suke, da kawo masu tallafin kula da lafiyarsu, ta hanyar gina musu dakin shan magani, domin taimakawa walwala da lafiyar kananan yaran cikinsu, kamar yadda muka bayyana a baya."

"Mr. Yassar, rana ta farko da aka zagaya da shi cikin idp camp din Anka, for site seeing, saida ya zagaya toilet a office dinsu yayi ta kwaranya amai, sabida kazantar da ya gani ake zaune cikinta ta isa a bada labari, abun na kazanta saidai ace ba a magana, har tuntube yayi da busashshen kashi. Tashin hankalin da yasa shi zagayawa bayi a guje yayi ta kelaya amai kamar zai amayar da  ya yan hanjinsa."

"To bayan ya fito daga toilet dinne yana wanke fuskarsa da hannayensa a  sink na cikin office din da aka tanadar musu, idanunsa sun kada, sunyi jajir, sabida aman da ya kwarara yasa duk ya jigata ya gaabaita."

"Yana dagowa yayi arba da wani daga cikin ma aikacin wajen mai suna Haladu, yanata kyalkyala masa dariya, don kallon wani"

" ajebo yake yiwa Mr. Yassar, banda haka su ai sun saba ganin kazantar data fi haka a wurinnan, har haihuwa ake a gabansu, su sa a kwashe kazantar, sai yake bashi labarin irin yadda rayuwar IDP camp din take a takaice, yace."

" Ai baka ga komai ba Oga Yassar, tukunnah ma, somin tabi wai kwarto ya taya Karuwa."

"Mutanen nan in anyi duba da halin da suke ciki abun tausayi ne matuka, banda ku, UNICEF, da sauran kungiyoyin sa-kai na kasashen waje (international NGOs), irinsu UNDP, babu wanda ya damu dasu balle asan halin da suke ciki ayi tunanin tallafawa rayuwarsu."

Mu da muke nan tare dasu mu muka san irin kazantacciyar rayuwar da suke yi a camp dinnan.

"Ko ka san cewa  Banditry is the major calamity da yafi yawa anan Zamfara, kuma duk shine sanadin zuwan mafi yawansu nan helter-skelter (wutsiya a zage), don ta sanadinsa ne mutanenmu ke zama displaced,"

"su rasa ina zasu saka kansu? Kuma ina zasu je su zauna lafiya?? Hence, internally displaced."

"Zama suke anan suna rayuwa kamar wasu dabbobi fa, asali shi wannan camp dinma public school ce aka mayar musu da ita camp, in ka lura zaka ga azuzuwa ne aka mayar  tents , a cikin azuzuwannan suke kwana suke wuni, zaka iya ganin family kamar guda biyar (a kowanne miji da mata fiye da daya, da yara shida ko biyar), amma duk anan suke kwana anan suke saduwar aure, ga yara, in wani bai farka ba wani zai iya farkawa."

"Kaga kenan duk wani rashin tarbiyyah ya kare a wajennan, sabida iyayen babu sirri, babu tarbiyyar badawa, wato mai kwabawar shima baida kwaba."

Baka tashi ganin danniya da mugunta daga camp leaders mace ko namiji sai NGOs sun kawo tallafi.

"To muma muna aikin ne kawai sabida muna dan samun na amfani, amma ba don isar albashin mu ba& . ."

"Tsaf Haladu ya kwancema Mr. Yassar yanayin rayuwar IDPs. Ga kwartanci ga neman yara kanana mata, yaran ma da yawa sun saba da maza. Su suke kai kansu. Zaka ga"

Uwa ce da kanta zata tura  yarta wajen mazan don su samu dan abun amfani.

"Zuciyar Mr. Yassar ta karye, ta kara da rugujewa, ta motsu iya motsuwa& . Hirar sam ba dadi take yima Yassar ba, sai faman cije lebe yake tayi yana yamutsa fuska, kamar zaiyi kuka, sabida abun yana taba zuciyarsa tsantsa. Humanity dinsa na halitta ya fara motsawa a cikin kirjinsa."

"Ta yadda da yanada yadda zaiyi, ko da ace shi wani shugaban kasa ne ko gwamnan jiha, da daga yau zai zama babu sauran  yan gudun hijira a sansaninnan, daga rana irin ta yau& "

"Domin duk zai yi musu gata, ya sada su da danginsu, in basu da dangi, ya zama uwa da ubansu a matsayinsa na shugaba, da da hali, da ya dawo musu da iyayensu da  yan uwansu da aka karkashe musu ba laifin tsaye babu na zaune."

"Kamar ya roki Haladu yayi masa shiru haka da bashi labarin, ya rabu da shi haka da wadannnan zafafan labaran na IDPs masu kona zuciyar duk mai Imani."

"Ya zama ya gundura, wato baya ko son jin karashen labarin, sabida babu abinda ke"

"daga hankalin Yassar a duniya irin yaji labarin ana kwartanci da kananan yara, duk wani nau in (child abuse) yana daga hankalisa balle iri wannan, zuciyarsa mai tsananin rauni ce akan zalinci ga marassa galihu, ko rashin tausayi a garesu, musamman yara mata!"

"Kenan rashin gatan muhalli shine yasa suka koma wannan kaskantacciyar rayuwar mai kama data zamanin cinikin bayi, ko kuwa zamanin jahiliyya period."

Don haka da tunanin wadannan al umma Mr. Yassar ya kwana a ransa yau. Har mafarkin  yan gudun hijira saida yayi. Daga bisani hakura yayi dan barci.

"Da Assalatun fari ya tashi, yayi nafila ya roki Ubangiji nasara akan nasarar abinda ya kawo shi, ya kuma rokama duk wani (displaced person) a kasar Nigeria Allah ya bashi mafita ta alkhairi, ya raba shi da rayuwar kaskanci ta IDP camp, ya sadashi da gatansa idan da rabo."

**** **** ****

"Washegari da safe ya kama Asabar ce, Yassar bazai shiga Camp ba, don haka kai"

tsaye ya kama hanyar Sokoto shikadai a motar ofishinsu farar Hilux dinnan tun daga Zamfara.

A Tambuwal ya fara tsayawa gun Baba Ado. Zo kiga min bakin Baba Ado kamar zai tsage don murnar ganin jikan nasa a bazata.

"Sun karasa wunin sur tare, suna diban hirar yaushe gamo, irinta Kaka da jikan da suka fahimci juna."

"Baba Ado ya sayo masa lafiyayyen balangu da fura mai sanyi data ji danyen kindirmo, Yassar ya ci, ya sha, ya gyatse, shi kuma da zai tafi ya aje masa kudade masu dama na abincin da zai jima baiyi awo ba, kamar dai yadda ya saba masa a kowanne zuwa nasa wajensa."

"Wannan karon Yassar harda lafiyayyar wayar hannu ya hada ma Baba Ado, don ya dinga jin lafiyarsa akai akai daga duk inda yake."

"Sai washegari lahadi da sassafe ya karasa cikin Sokoto, gidan Babansa Alhaji Abdulqadir ya fara halarta, nan kannensa da matan Alhajin su uku suka yi masa"

"kyakkyawar tarba, kannen suka yanyameshi suna  oyoyo! Yayan Mexico! ."

"Yassar mutum ne ma farin jini ba a cikin danginsa kadai ba, har a cikin al umma sabida ilhamominsa masu yawa ne. Haka yabi kannen ubansa daya bayan daya har gidajensu, mazansu da matansu ya gaishesu, yayi musu ihsanin da ya saba, ya isar da sakon Abbih da Ammih ga kowa. Kuma bai kwana ba, a ranar ya kukkuta ya samu ya koma Gusau."

**** **** ****

THE BEGINNING& ..



"itinin, babbar ranar aiki ce ga duk wani ma aikaci, ba ga na gwamnati kadai ba, harga su na NGOs. Kowanne ma aikaci"

"ka duba ranar Litinin zaka ga ya fito ne akan lokaci, cike da himma da kuzari, a kokarin cimma abinda aka sa a gaba."

"Wajen misalin karfe goma na safe. Su Yassar na ofishin da aka basu cikin IDP Camp, aka kuma shirya musu shi da kyau da kujeru da teburansu uku, ga (Air Condition) mai aiki da solar inverter, kai komai na bukatar"

ma aikaci dan gata an tanadar musu yada zasuji dadin gudanar da aikinsu ba tangarda.

"Gabadayansu sun nutsu suna shigar da tsare-tsaren gabatar da aiki ta hanyar rubuce- rubuce cikin systems din dake gabansu, shi da Femi tebur din su nakallon na juna, a gabansu gorar ruwan roba ce mai sanyi ta Aquafina, sai rabar ni imar sanyin firji take fiddawa, kasancewar an wayi gari cikin zafin shigowar damuna yasa duk da sun kuna na urar sanyaya daki, to sun bude duka tagogin ofishin, suna aikin suna hira jefi-jefi shi da Femi."

Yayinda Ngozi tana daga gegensu bisa nata tuburin tana nata aikin daga gefensu.

"Daidai wannan lokacin suka ji dirin isowar wasu manya-manyan motocin Akori  kura, irin motocin dake kawo tallafi, wadanda da alama sun zo ne daga gwamnatin  yan siyasa ba daga kungiyoyin NGO suke ba. Sun gane hakan ne ta hanyar rubutun dake jikin motocin, mai dauke da tambarin gwamnatin wata jiha daga Arewacin Najeriya."

"Nan daga inda suke zaune, ta tagar ofishinsu, suna iya hangen har can tsakiyar Camp din, da duk abinda ke wakana, nan suka"

"ga idp s din suna gudun yada kanin wani, don su samu su hau layi ayi musu register su samu karbar abubuwan tallafin da aka kawo."

"Camp leader mace da camp leader namiji kuwa sai zuba iko suke da wulakanci, don a hannunsu za a damka komai in an gama yiwa kowa rajista."

"Ga al ada ta camp leaders kuwa in aka zo rabon tallafi, sai wadanda ke yi musu biyayya ko na hannun damansu kadai suke ganin damar baiwa."

"Watakila hakan ne yasa itada Mamanta suka ja gefe guda suka rakube, suka zubawa sarautar Allah ido. Idonsu kyam! A kan motar kayan. Don ba tun yau ba basu cika samun komai ba in an zo rabon tallafi, saboda rashin kuzarinsu da rashin namiji tareda su a sansanin da zai iya yi musu kokawar samu."

Da kuma uwa-uba wariyar launin fata da ake yawan nuna musu. Saboda fatar jikinsu data bambanta data sauran  yan gudun hijira.

Kana ganinsu kasan ba asalin hausawa bane. Sannan basu da kuzari da karfin halin iya mu amalla da kowa a wajen. Balle a samu

"wani ya ja su a jiki, kullum a salafce zaka gansu idanu zuru-zuru mai fallasa yunwar dake cikinsu, basu da karsashi ko kadan kamar sauran IDP s din, ga yunwa ta samu muhallin zama sosai a kasusuwan dogon wuyansu da dan siririn jikinsu, kwayar idanunsu kuwa babu komai sai ramar ido, ta zuzzurma ciki don galabaita, don ba kullum suke sa ar samun abincin da zasu ci sau daya a rana ba wanda ake rabawa a IDP camp din."

"Mr. Yassar da Femi, suka saki aikin da suke yi suna kallon irin gumurzun da akeyi na saka karfi wajen karbar tallafin, wannan shine karo na farko da suka ga yadda rabon tallafin ke kasancewa, kamar wasu almajirai haka suke dafifin karbar sadaqa, kowa an masa packaging na  yan abubuwan amfani irinsu sabulun wanka dana wanki da suke kira (hygiene kits), mai karfi ya samu, ko wanda keda uwa a bakin murhu."

"Daga bisani ma barin abinda suke yi gabadaya suka yi shida Femi, suka shiga takowa suka nufo harabar wajen rabon don baiwa idonsu abinci, suna kallon komai da yadda akeyi suna tattaunawa a tsakaninsu"

(with concern) irin na ma aikatan jin kai da suka san muhimmancin aikinsu na humanitarianism.

"Yassar da Femi, suna magana ne kan yadda zasu canza tsarin wannan mugunta da danniya da akeyi a camp, wajen karbar  hygiene kits , don kiri-kiri sai wanda camp leaders suka ga dama suke baiwa, inda sukayi shawarar zasu rubuta sakon email na gaggawa zuwa hedkwata dinsu, su bada report akan wannan danniyar da suka ga masu karfin wajen nayi wa  yan uwansu  yan gudun hijira don a yiwa tufkar hanci.  & When destinty calls& ! Hakan ya dace da sunan abunda ya faru a daidai wannan lokacin, da Mr. Yassar ya samu kansa da juya idanunsa accidentally zuwa bayansa."

"Wasu mata ya gani a tsugunne a takure a wurin da suke tsaye, farare ne sal guda biyu, babba da yarinya, kansu a duke, sun takure manne da jikin junansu, kamar Uwa da  ya, kamar kuma Yaya da kanwarta."

"Babban abinda yasa shi kallonsu da mamaki shine su basu je sunyi kokawar samun rijista ba, balle suyi kokarin karbar (hygiene kits) din da ake rarrabawa."

"Sannan su basu koma wajen kwanansu ba, suna dai takure a gefe, uwar na kallon kokawar da akeyi tsakanin maza da mata wajen amsar  Hygiene Kits , yarinyar kuma tana rabza kuka wiwi da hawaye Sharaf - sharaf, bako ruwanta da wasu

Please Login or Register in order to submit comment