gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 2 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yunkurin don tallafa musu, da"

hadin guiwar Babban Bankin Duniya (World Bank).

"Me kake zato idan aka bar yaran nan suka girma a haka cikin jahilci, cututtuka da rashin tallafin kowa?"

"Idan babu jin kai ko tausayi daga gwamnati, ya kamata ace akwai hakan daga kungiyoyin sa-kai na ciki dana waje (local and international NGOs), babu abinci, ba ilmi, babu koshin lafiya, babu tallafi daga kowa, ga babu ran iyaye?!"

"Sune irin matasan da idan aka barsu suka girma a haka, suke zama mugaye, marasa Imani, marasa tausayin kowa (heartless), sune irin matasan da a halin yanzu suka addabi al umma da dukiyoyinsu a kan hanya da cikin gidajensu, sabida a ganinsu suma ba a tausaya musu ba, babu wanda yaji kansu a lokacin da suke bukatar tallafi don gina rayuwarsu, babu wanda yaji tausayinsu ya sakasu a makaranta, ko ya basu magani in suna cikin ciwo, a lokacin da suke bukatar suma a tausaya musu, a kyautata rayuwarsu ta hanyar basu ilmi da kulawa da kariya irinna kowa."

"A binciken UNICEF ta gano cewa refugees an barsu suna rayuwa kara zube, sannan kananan yaran cikinsu ba cikakkar lafiya, saboda basa samun kariya (rigakafi na kananan cututtukan yara), balle ayi maganar sauran bukatu na rayuwar yau da kullum."

"UNICEF suna da labarin cewa; yaran dake rayuwa a can wata rayuwa suke a wulakance a sansanin  yan gudun hijira, wanda shine abinda yaja hankalin UNICEF ta kawowa rayuwarsu tallafin gaggawa."

"Daya daga cikin kyawawan manufofin kungiyar UNICEF sun hada da; tabbatar da yara marasa gata sun samu ingantaccen ilmi kamar suna gaban iyayensu, da cikakkiyar lafiya ta hanyar rigakafi. A bisa wadannan kyawawan manufofin ne, UNICEF, (karkashin majalisar dinkin duniya) suka kirkiri wannan (6-months IDP Renovation Project), wanda shine aka turosu suyi a Nigeria inda zasu fara da jihar Zamfara, inda abun yafi tsanani, shida wasu mutum biyu dake aiki a kasanshi daga HQ dinsu; Femi Ogunbiyitan, da"

abokiyar aikinsu mace mai suna Mrs. Ngozi Sylvanus.

Project din ya kunshi; gina kananun makarantun firamare dana karamar sakandire a duka sansanin  yan gudun hijira na jihar Zamfara da kewayenta.

"Sannan zasu samar da dispensaries, dakunan shan magani dana ganin likita kai har da dakunan kwanciyar asibiti don marasa lafiya. Su kuma tabbatar da an zuba magungunan da suka dace a wadace, an zuba likitoci da ma aikatan jinya, zasu yi aiki kai da kai bisa yarjewar ma aikatar ilmi da ma aikatar lafiya na jihar Zamfara, don aiwatar da duka wadannan kyawawan manufofi na UNICEF ga refugees."

"Kafin wa adin watanni shidda dinnan kacal da aka deba musu ya cika, ana fatan su kammala duka wadannan ayyukan kafin cikar, ko cikin wa adin, refugees su fara karatu da shan magani a cikinsu. Suma rayuwarsu ta kyautata, su samu sauki ta wadannan fannonin, watau fannin ilmi da kiwon lafiya."

**** **** ****

"Ya nisa a hankali, daidai sanda tunaninsa ya zo nan. Sai lokacin ya ankara da Femi dake gefensa yanata zuba masa hira, amma sam hankalinsa baya tareda Femi. Gashi dai yana jinsa, amma sam bai wani fahimtar zancensa."

"Don haka nema dazu da ake ta kakabin bada umarni ga fasinjojin kan su daura  belt lokacin tashin jirgin ya cika, yanzu zai bar kasa& . zuwa sararin samaniya& . Shi Mr. Yassar Jalloh, har a lokacin bai ko motsa ba, balle yayi tunanin  fastening nashi belt din, sakamakon yayi nisa a tunanin asalinsa da iyayensa daya baro a gida yau, kaunar iyayensa da kewarsu cike fal da zuciyarsa."

"Har Femi (sarkin kankanba) yadda Mr. Yassar ke yawan kiransa, cikin harshensa na hausa/Fulani, ba tareda ko sau daya Femi ya san ma anar kalmar  kankanbar ba, ya ankara da cewa Ogansa bai daura  belt dinsa ba."

"Ai kuwa nan yayi kankanbar tasa, ta hanyar zuro hannu ta bayan Yassar ya hau daura mishi belt, ba tareda wani bayani ba ko son katse masa dogon tunanin sa, wanda hakan yasa dole Mr. Yassar ya dawo daga"

 nostalgic thoughts dinsa. Ya dawo duniyar dake gabansa.

"A hankali kyakkyawar fatar bakinsa wadda ke zagaye da lallausar gashin baki, baki sidik, irin gashin bakinnan da ya zagayo har kasan haba daga saman lebe na zaratan matasa dake cikin lokacin samartakarsu, wanda ake kira  quarter million ta motsa kadan, cikin motsi mai nuna mai nuna furta kalmar godiya."

"Jirginsu ya hau hazo sosai, yana tafiya dodar, a lokacin nan Yassar ya jingina bayansa sosai a jikin kujerar zamansa, yasa hannunsa na dama ya tallafe kansa. Sai ya samu kansa da kara komawa cikin tunani, saidai wannan karon tunanin irin sallamar da sukayi yau shi da iyayensa ne wadanda yake kira  Abbih da  Ammih ; wato mahaifiyarsa Hajiya Tarha da mahaifinsa Amb. Muhammad Jalloh Ahmad."

"Kwarai ya damu da yadda damuwarsu da tafiyar nan tasa ta fito fili, kamar ba gida zai je ba, har sun kasa boye damuwarsu"

"wannan karon, damuwa da kewar dansu ta nuna sosai akan dattijan fuskokinsu."

"Zaka iya karantar hakan tsantsa daga kalaman bakinsu, dama cikin kwayoyin idanunsu. Karara Ammih da Abbih suka nuna masa basa son wannan tafiyar tasa, sabida jimawar da zata daukeshi har fiyeda ta baya, da kuma yanayin wajen da zaya je aikin, ba irin na baya bane."

Kamar Ammih da Abbih sunada masaniyar cewa tafiyace da zata juya rayuwarsa ta jirkitata upside down.

"Duk da kasancewar ba wannan ne karo na farko da ya fara balaguron aiki irin wannan ba, saidai wannan shine karo na farko da zai yi irinsa a kasarsu ta haihuwa Najeriya da babu kwanciyar hankali a cikinta a lokacin."

"Duk da kasancewarshi dan Nigeria gaba da baya, amma ya kan jima bai zo kasar ba, kuma in zai je kusan da yawo kawai yake zuwanta, a dalilin yanayin aikin mahaifinsa; tun haihuwarsa Abbih da Ammih suke yawo dashi a hannunsu da kafadunsu a fadin sassan duniya."

"Daga baya shima da ya kawo karfi, ya gama karatunsa na jami a, sai ya fara kalar nasa aikin, sai ya zamanto shima nasa harkallar ayyukan mai yawan tafiye-tafiye ne, lungu da sako na kasashen Afrika masu tasowa (developing countries) babu inda UNICEF basa tura shi."

Wannan ya kara sa Yassar yin nesa da kasar haihuwarshi sosai. Duk da kasancewarshi jika na musamman da ake ji dashi cikin zuri ar Grand Khadi Jalloh Ahmadu.

"Shima ya san hakika iyayensa zasuyi kewarsa bama irin Ammihnsa, ba sai wani ya fada cewa Ammih zatayi kewa ba, Mamanshi da bata hada kaunarsa data kowa da komai, wadda ya tabbata in banda neman abinci ya zamarwa dan adam dole, musamman Da namiji, ko gefenta Ammih bazata so ya dinga gusawa ba."

Inda kuwa shi mace ne ba namiji ba da wuya idan Ammih zata barshi ya tafi gidan miji ya barta.

Sanin kowa ne dama akan sha aninsa Ammih bata fulako (duk da cewa bafulatanar

"ce) amma akansa Ammih bata kara, bata iya alkunyar nan nasu na gado ga dan fari ba."

"A matsayinta na bafullatanar garin Dogon daji gaba da baya, in dai a kansa ne, Ammih (Haj. Tarha) ajiye fulatancinta take a gefe, don sau tari zaka ji tana cewa kawayenta cikin raha in sunce bata musu kara a kansa, sabida  Ibny din da take kiransa a gaban kowa, sai tace  ai daga shi babu wani, shine na fari shine kuma auta ."

"Hakika akwai shakuwa tsakanin kowadanne iyaye da Dan da suka haifa, amma shi tashi shakuwar da Ammih da Abbih??? Umhm, wata irin shakuwa ce ta musamman, data isa a bada labari, don ba duk Da da iyaye keda irinta ba."

"Hakan kuma baisa sun bar tarbiyyarsa ta gurbata ba, iyayensa suna janshi a jiki suna kuma nuna masa kauna a zahiri tun yana yaro. Wannan ya biyo bayan kasancewar shi kadai Allah ya basu a matsayin kwansu a duniya."

"Amb. Muhammad da Haj. Tarha a kafatanin rayuwarsu basu samu haihuwa ba bayan tashi, har gashi shekarun girma sun cimmasu, tuni Ammih ta wuce menopause, ba tareda sun samu karin zuri a ba, shima kuma"

"ya kai munzalin da za a kira shi cikakken matashi yanzu, ko kuwa cikakken mutum dan (mid-thirties)."

"Don haka ba sai an fada ko an kwatanta ba yasan shima zai yi kewar wadannan dattijan nasa, da kuma uwa uba girkin Ammih, wanda kafin fara aikinsa da"

"`UNICEF , baya iya cin kowanne girki ta dadin rai in ba nata ba."

"Shiyasa kwata-kwata baya son yin tafiyar da zata daukeshi koda sati biyu ne ba tareda Ammih ba, balle akai wata guda, ina kuma ga azo ga batun watanni irin wadannan! Kwarai yana wahala sosai wajen cin duk abincin da ba na Ammih Tarha ba."

"Ya kasance Da daya kwal daya taso a gaban iyayensa, bai san babu ba, bai taba cewa yana son kaza ba a nemo masa ba, tunda ba kani ba kanwa, ba Yaya namiji ko Yaya mace, don haka duk wani gata na duniya Yassar ya ganshi tun daga kuruciyarsa, ko mu ce Yassar Jalloh dan gata ne nna karshe, yana kuma kan ganin gatan har gobe a gun iyayensa da dangin mahaifinsa."

"Saboda duk abinda iyayensa suka samo a kansa yake karewa, shi daya dinnan tal! Da suka mallaka, shi yassa ya taso a mutum asalin dan hutu, wanda bai san wani abu wai shi rashi ko wahalar rayuwa ba."

Yazo kuma ya samu aiki gwaggwaba daidai da zabinsa akan profession dinsa (humanitarian space) amma cikin rashin sa a sai ya zamanto a nesa da inda iyayensa suke zaune ya samu aikin nasa.

"To amma da yake aikin zabin ransa ne, kuma yanada passion akan duk wani humanitarian abu, dole kan ba yadda zaiyi, ya yarda ya tafi United States, birnin New York, inda acan Headquater din UNICEF yake, ya bar Ammih da Abbih a kasar Mexico."

"Daga lokacin sai cin abincinsa ya koma maleji, mafi aksari kayan marmari acan inda ya samu kansa."

"Yassar bai san ya sayi abinci a restaurant ko ya girka da kansa ba, tsabar sangartashi da Ammih tayi da dadadan girke- girkenta na zamani dana gargajiya. Kai ko ruwan zafi Yassar yana ganin wahalar dafawa da kansa, saboda hatta shayi Ammih ke dafa masa da kanta. Don haka a dalilin rashin"

Ammih kusa dashi dole hakan tasa ya koma cin (canned food) da fruits a can inda ya koma.

"A wannan sallamar tasu da Ammih ta ce masa ya kamata zuwa yanzu ya koyi cin kowanne irin abinci ya samu, koda na sayarwa ne, tace ya daina cin kayan gwangwanin nan, saboda tattalin lafiya, tace ko don saboda an tabbatar da suna da illa sosai ga lafiya, kuma ya rage dogara da ita akan abinci, sannan cikin murmushinta mai sanyaya masa rai tace."

" Ibny , (sunan da Ammih tafi jin dadin kiransa dashi)  & .watarana kuma aure zaka yi, mu raba gida kwata-kwata, nida kai zai zama sai da Ziyara."

"Lokaci yayi daya kamata kayi aure haka Ibny, idan kayi aure dole ka koma cin na iyalinka, ba yadda za ayi in dauwama ina baka abinci."

"In babu aure akwai mutuwa, gara ka koya tun yanzu, kana jina ko Ibny? Kasa a ranka tun yanzu kwanonka zai fita daga hannun Ammih, daga ranar da aka shafa maka Fatiha, ko ranar da muka wayi gari babu ran Ammih! ."

Sannan tace.

" Ibny, duk inda kaje ka kula da sallah cikin kowanne hali kake, nasan kana kula da ita, amma ka kara akan yadda kake yi."

Sabida ita sallah kariya ce daga aikata duk wata nau in alfasha da aikin munkari.

"A karshen sallamarsu Ammih ta kara jaddada masa nasihohinta, tace ya kula da nafilfilin cika Mizani; sallar walha (salatul Dhuha), Raka atainil fajr, da shaf I da wutri, a bayan kowacce sallahr farillah."

Kalamanta na karshe gareshi da zai

taho.

" Ka kula da kanka, ka kular min da"

kanka da cikinka Ibny! .

" Kullum irin kalar nasihohin Ammih kenan, idan ya gaya mata zaiyi balaguron aiki, tuni ya dade da haddace nasihohin Ammih."

"A yadda Ammih ta damu da tafiyar tasa sai kayi tsammanin shi din wani karamin yaro ne da bazai iya kula da kansa ba, ba cikakken matashi mai cikakkun hakoran girma 32 ba."

Ita Ammi damuwarta akan tafiyar itace kasancewar inda zai je din sunada tabbacin

"babu kwanciyar hankali, sannan kauye ne inda babu mai kula dashi, shi kuma bazai tsaya ya kula da cikinsa ba, sai dai yayi ta cikawa kansa aiki, wanda yafi karfin gejin daukar dawainiyar kwakwalwar mutum daya."

"Kowa dake tare dashi ya yarda Mr. Yassar workaholic ne, ya riga ya sabarwa kansa da rashin hutu akan aiki, kamar yadda yake a dabi arsa (goal-oriented person) ne;"

"Ammih tace ita dai damuwarta tafi yawa akan abincin da zai dinga ci, kwarai ta sanshi sarai akan abinci indai abincin ba nata bane, shiyasa da yace watanni har shidda rus! Zaiyi a wannan tafiyar Ammih ta shiga dimbin damuwa sosai."

"Duka wadannan tunaninnikan suna kara masa kewar Ammih, har yaji kamar ya fasa tafiyar, ya hakura da project din da aikin gabadaya ya koma gida."

"Don haka jikinsa duka ba lakka sam, nan ya koma ya sake kwantar da kai a wuyan kujerarsa ya lumshe idanunsa, har Femi ya gama daura mashi belt ba tareda ya kulashi ba, amma yana jinsa, yana kuma kallonsa, da Femi ya gaji da yi masa hira baya kulashi"

"shima sai ya kama bakinsa, wato yayi shiru, don Yassar bai tsinka masa surutunsa ko daya ba. Wannan halin shirun idan Ogansu Mr. Yassar ya shigeshi, to yafi so a kyaleshi ne, Ogansa nada yawan shariya, sau da dama ana yi masa magana zaiyi kamar ba dashi ake ba, abokan aikinsa su Femi da su Atiku sun riga sun saba da hakan ha rya zamanto basa damuwa."

"Daga bisani Yassar sai barci mai nauyi ya daukeshi. Ita dama Ngozi tun shigowarsu jirgin magazine din gabanta ta dauka take dubawa, don Mr. Yassar ba abokin hirarta bane saboda yanayinsa na rashin walwala da rashin sakin fuska ga kowa."

"Har cikin barcinsa haka yayi ta jin kewar baro iyayensa da yayi, tana kara ninkuwa a kasan ransa, duk da irin dokin zuwa Nigeria da yaketa yi a baya."

"Bai tara sani da kaddara ba. Amma ji yake a jikinsa tamkar idan yaje Najeriya wannan karon wani abu mai karfi zai rikeshi, ya zamar masa Katanga da iyayensa, ya hana shi dawowa gabansu, kai ji yake kamar bazai dawo ya taddasu a raye ba."

**** **** ****

"Wani abu dake dada burge Abbihnsa da halin dan nasa shine; in ka cire kafiya akan ra ayinsa, to Yassar mutum ne mai matukar kirkin gaske wanda yawan sabgoginsa basa hanashi kula da zumuncin  yan uwansa."

"Mr. Yassar tun da ya taso ya taso da son danginsa/ yan uwan mahaifinsa dana mahaifiyarsa gabadaya, wadda asalinta  yar garin Dogon Daji ce, daga can Grand Khadi ya aika aurowa Abbih ita."

Kusan zai iya cewa Yassar har ya fishi kokarin kula da zumuncin da ya rataya a wuyansa shi Abbih din.

"A baya kusan duk bayan watanni uku zaka ga Yassar yana kan hanyar zuwa Sokoto, baya gajiya da zaryar zuwa gayar da Baffanninsa da Goggonninsa da kannensa maza da mata dake can."

"Kasancewar Abbinsa  Diplomat ne da ake yawan canzawa  posting zuwa kasashen daban-daban, shi yasa bai cika zuwa gida ba shi, sai shekara-shekara."

"A karshen kowacce shekara Abbih ya kan zo gida yayi hutun karshen shekara (annual leave) da iyalinsa, a lokacin azumi da"

"sallah karama, tareda  yan uwansa a gida Sokoto (Birnin Shehu) cikin family house dinsu."

"A tasowarsa Yassar ya ga an canza musu kasashen zama dai-dai sun kai bakwai, Ammih daga kansa bata kara ko batan wata ba, shima Yassar din da kyar da taimakon Allah dana likitoci da yawon asibitoci da barar da dukiya wajen dabarun asibiti suka samu haihuwarsa, bayan kwashe shekarunsu bakwai da aure itada Abbih, shiyasa ba karamin dan

Please Login or Register in order to submit comment