gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 3 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lele bane shi, wanda da wuya ace ga laifinsa, kasancewarsa tsoka daya a miya a gun Uwa da ubansa."

"Duk wani burin Abbih da Ammih toh ya kare akan walwalar dan su Yassar, farin cikinsa shine nasu."

"Sun kwashe sama da shekaru goma sha biyu a kasar Amurka, inda acan shi Yassar ya samu yayi karatun sakandire gabadaya a birnin Dallas (Texas), kasa ta karshe da suka dire da zama sanadin aikin Abbih a halin yanzu itace, Mexico."

"Lokacin dasu Abbih zasu koma Mexico, Abbih da Ammih sun bar tilon dansu Yassar ya shiga jami ar Texas, yayi karatun digirinsa"

"na farko kan (International Development), a digirinsa na biyu, sai ya zabi ya karanci abinda yafi so; (Humanitarianism and Disaster Management)."

"Abbih kullum yana kan jaddada masa ya rike zumunci da  yan uwansa na Sokoto, saboda shi baya samun lokacin danginsa sosai, Abbih ya taba ce masa  ko bayan ransa bai yarda ya nesanta kansa dasu ba, ko ya saba umarnin daya daga cikin Baffanninsa."

"Amma wani abun mamaki bai cika cewa ya kula da Kakansa Baba Ado ba, wanda shi a ganinsa ai Baba Ado shi yafi bukata da cancantar a kula dashi fiye dasu Alhaji Abdulqadir Jalloh (Yaya Babba), shi da bai da komai, a kauyensu can yake rayuwarsa shikadai a gidansa kamar maye, to babu Da babu jika, Baba Ado Allah bai taba bashi haihuwa ba har tsufansa."

"Baba Ado ciki daya ya fito da mahaifin su Abbih. Ko don wannan dalilin ya isa ace duka family din suna kula dashi da rayuwarsa amma ina! Grand Khadi ya rayu cikin zumunci da dan uwansa na kauye, tare da kyautata masa, amma bayan ransa kowa daga"

"cikin  ya yansa baya bashi muhimmanci, sabgar gabansu suke yi, basu cika tunawa ma da Baba Ado ba, in ka cire shi Yassar din. Da Allah ya sanyawa kauna da shakuwa da yawan tausayin Baba Ado."

"Kusan shikadai (Yassar) za a ce yana yawan saka shi a rai, yana kula da zumunci na tattaki dashi."

Ya sha tambayar kansa ko mai yasa su Abbih basu cika damuwa da kanin Babansu Ado bane?

"Yassar har baya son ya yardarwa kansa amsar dake yawan zuwar masa a matsayin amsa ga tambayar zuciyarsa, mai cewa,"

" Saboda shi Baba Ado talaka ne, kuma bai haihu a duniya ba! ."

**** **** ****

"Da alama tunanin da yake tayi dinnan tun tawarsu dadi yake yi masa, tunda kuwa iyayenshi da family dinshi ne kadai cikin tunanin nasa& ."

"Yassar bai san wata hatsaniyar rayuwa ba, bayan wannan da muka bayyana a sama. Zero tension mind gareshi."

"Tunanin dattijo Baba Ado da Baffanninsa da zai je ya tarar ya koma yi yanzu, hakan ya dan fara kawar da damuwarsa, ya fara saka masa zumudin son isa kasarshi Najeriya lafiya, ya je yaga Baba Ado, yanata mai addu ar ya tadda danginshi na gida kowa lafiya."

"Yanzu Jirgin ya fara karkatowa kasa- kasa, alamar yanaso zai sauka, bayan tafiyar awanni kusan goma a sararin samaniya ba tareda transit ba."

"Mr. Yassar na cewa a ransa& ko ba don sauran  yan uwansu ba, yana sauka a kasar Najeriya, idan ya huta kadan, yayi reporting a wurin da aka turo su aiki, zai wuce jiharsu Sokoto, amma ya yanke a ransa garin Kakanninsu wato karamar hukumar Tambuwal zai fara zuwa kafin ya shiga babban birni Sokoto."

"Ba don kowa zai fara shiga Tambuwal ba sai saboda yaga lafiyar Baba Ado, dattijon Kakansa da yake so matukar so, tamkar shine Grand Khadi. Ya sawa rasa sai ya fara gayar da Baba Ado kafin kowa, sai yaga lafiyarsa, sannan ne zai iya samun nutsuwar shiga"

Sokoto gun sauran Baffanni da Yakumbobinsa.

"In yaso daga nan sai ya dawo Zamfara din, ya maida hankali kacokam! Kan abinda ya kawo shi kasar Najeriya a wannan karon, wato IDP Camps Renovation Project din da kungiyarsu ta UNICEF ta turo shi."

"Daga nan sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi don ganin ya cimma kyakkyawar nasarar aikinnan, wajen tabbatar da samuwar ingantaccen ilmi, da kula da lafiyar kananan yaran dake cikin IDP Camps."

**** **** ****

Wani abu da zai baka mamaki. Duk cikin dangin Abbih ba wanda ransa yake so kamar neglected Baba Ado.

"Hakika tasu tazo daya, jininsa ya hadu dana dattijon ba tun yanzu ba, gashi dai mai karamin karfi a cikin iyayensu amma shine dattijon da akan manta dashi a dangi, sakamakon yana Tambuwal yaki yarda da zaman birni, kuma bai taba haihuwa ba balle in an ga  ya yansa a tuna shi."

"Abbih ya taba bashi labari cewa Baba Ado ya dade yana aure-aure a can baya, wai"

"don ya dace da samun haihuwa amma Allah baisa ya samu ba, shiyasa yake zaune shikadai yanzu a gidansa dake garin Tambuwal kamar baida kowa, sai yaran kauyen da ake kawo masa dalibtaka, da suka zame masa almajirai, kasancewarsa malamin Al qurani, yana koyar da yara kanana rubutun Al qur ani akan allo da karantar dasu kira ar  warshu . Wannan rayuwar kadaici da Rashin haihuwa ta Baba Ado shine abinda ya saka masa tausayi da kaunar Baba Adon a ransa."

"Matan garin Tambuwal ma yanzu sun daina yarda Baba Ado ya auresu, tun daga sanda aka gano matsalar rashin haihuwar daga gareshi take (Baba Adon), sakamakon yawan aure-aurensa. Ta karshe da ya aura ko shekara bata yarda ta rufa tare dashi ba ta fece."

"Allah ya dauki tausayin Baba Ado ya saka a zuciyar jikansa Yassar, bazai manta ba a sanda yana yaro kullum Baba Ado zai zo gidansu (kafin iyayensa su bar Skoto) sai ya kawo masa tsarabar kayan gona, ya kan kawo masa koren  Data, ko ya riko masa Yalon Bello."

"Ammih tayi ta mita kan ita dai ya daina cin Yalon Baba Ado da yawa haka, sakar masa ciki yakeyi, amma shi Yassar ba abinda yake doki irin zuwan Baba Ado gidansu, don ya san zai kawo masa Yalon Bello."

"Baba Ado ya taba ce masa Data na wanke dattin ciki, tun daga lokacin ya rike hakan a ransa, a ganinsa don yaci  Data ta wanke masa ciki yayi ta zagawa ai ba komai bane, karin lafiya ne. Ammih taki ganewa."

"Wannan ne musabbabin shakuwarsu da dattijon Kakan nasa, Baba Ado yana nuna kulawarsa gareshi yana yaro ta hanyar sauraron duk shirmen da yazo masa dashi na yarinta, da kuma jure yawan tambayoyinsa kamar dan jarida."

"Yassar mutum ne mai kwakwar tambaya sanda yana yaro, ko Ammi bata jure yawan tambayoyin Yassar, sai Baba Ado."

"Iyalin marigayi Grand Khadi, da dukkan zuri arsa sun mallaki manyan tanqara-tanqaran gidajen zamani a wurare daban-daban cikin birnin Shehu, amma banda Baba Ado."

"Baba Ado bai mallaki komai ba a rayuwarsa na dukiya sai tawadi u da yakanah, sai gidan da yake ciki a garin Tambuwal mai dakuna uku, sanannen malamin Al qurani ne a Tambuwal, wanda bai taba dogara ko jiran  ya yan dan uwan nasa su kawo masa komai ba, duk da wadatarsu."

"Watakila a dangi shi Yassar dinne kadai yake lura da cewa ba a kula da Baba Ado yadda ya kamata, hasali ma akan manta da shi a kauye, shikuma sam bai damu ba, rayuwarsa kawai yakeyi shikadai a inda yake, cikin ibadah, wadatar zuci da tsarkin addini."

"Abbih ne ma kadai in ya bushi iska yake dan masa ihsani, wanda bai taka kara ya karya ba, sabida Abbih sam baya kyauta mai yawa, shima daga shekara sai shekara wato idan ya zo hutunsa na karshen shekara gida Sokoto, ya kan dan shigo yayi masa ihsani, wanda baya taka kara balle ya karya."

"Yassar ya dade da gane cewa Abbihnsa bashi da mikakken hannu (yawan kyauta) saboda dadewarsa a diaspora yayi tasiri mai yawa a halayya da dabi unsa. Abbih akwai tattali (economizing), kai duk wasu halaye na"

bature masu kyau da akasinsu Abbih ya ara ya yafa.

"Yassar tun yana yaro akasin mahaifinsa ne ta fannin yawan kyauta da yawan mika alheri ga kowa nasa, hannunsa kullum a sake yake, a mike, musamman ga wanda ya lura mai karamin karfi ne kasa dashi, da duk masu bukatar taimako da suka bi ta hanyarsa."

"Amma akwai wani bad side a halayyar Mr. Yassar Jalloh, wanda ba kowa ya sani ba sai iyayensa, kamar yadda kowanne mutum yake tara bai cika goma ba, to shima Yassar mutum ne mai taurin kai, mai (kafiya), mai magana daya a mafi yawan lokuta."

"Mutum ne wanda baya juyuwa ta dadi, wato a takaice Yassar nada halin ra ayin rikau, baya taba barin abinda yasa kansa indai yayi daidai da ra ayinsa."

"Lallashi, fada, banbaki ko duka basa biyar dashi su hanashi yin abinda ransa yake so, tun yana yaro haka suke fama dashi, idan ya riga ya sakama ransa yana son yin abu, tofah sai yayi shi ruwa da iska hankalinsa ke kwanciya."

"A baya iyayensa na damuwa da wannan halin nasa, saboda dukkansu sun shaida"

"mutum ne shi mai wuyar sarrafuwa, shiyasa kawai komai Yassar ya kawo yace yana so basu cika jayayya dashi ba, in dai bashi da illah ta fuskar addini da lafiyarsa da martabarsu."

"The good side of him shine tsananin kirkinsa, da kyautatawa, gashi da son fita hakkin kowa nasa ta hanyar kyautata mu amala, kannensa na Sokoto da suke  yan maza zar da cousins duka, nephews da sauransu koyaushe cikin dokin zuwansa Sokoto suke."

"Ba ddon komai bas ai don saboda gwaggwabar tsarabar da yake riko musu duk zuwansa gida, baya fashin tsarabarsu baya mantawa, wadda in ka duba zaka ga kome zai kawo musu mai daraja ne da amfani, wanda zai dade yana amfanarsu musamman ta fuskar karatu, kamar wancan zuwan nasa (Apple Ipad/tablet) ya kawowa yara-yaran  yan sakandire, manyan kuma da  yammatan kowanne hadaddiyar kwamfutar bisa cinya (Laptops) kirar kamfanin ASUS samfurin jiya-jiya (new models), haka ya kawo musu su tsaraba da yazo Sokoto, kuma ba wanda ya mata a cikin kannensa maza da mata."

"Tun daga lokacin da Yassar ya gane nakasun Abbih, shi sai ya ninka kyautarsa ga  yan uwa, shiyasa a kullum yake kokarin zama makwafinsa a gun jama a da gurin danginsa wajen kyauta (duk da basa korafi akai). Misali idan biki ko suna ya tashi kowa zai bada gwaggwabar gudunmuwa da kowa a dangi sai ya jinjina wanda aka baiwa ya jima yana mora, amma banda Abbih."

"Yassar sai ya kasance akasinsa, ya taso da zuciyar son taimakon masu karamin karfi da danginsa, da son kyautata rayuwar kowa dake aiki a karkashinsa."

"Tun yana karami ya taso da halin kakansa marigayi Grand Khadi, wato tarbiyyar Alkalin Alkalai ta darajja dan adam mai karamin karfi, musamman marasa galihu, marayu da gajiyayyu."

"Ya kasance mai yawan tausaya ma marayu, ko dattijai marasa gatan  ya ya a girmansu, irin dai Kakansa Baba Ado Jalloh."

"Kenan tun Yassar yana karami ya taso da  humanitarianism dinsa a dabi a, ba wai a karatun aji kadai ya dauka ba."

"Saboda Yassar kusan yafi kowa sanin dadin gatan iyaye, shiyasa yake tausayawa marasa  ya ya da marayu marasa iyaye a raye."

"Watakila wadannan halayen nasa ne suka sa a shigarsa jami a, sai ya zabi mayar da kansa HUMANITARIAN ta fannin profession."

A kullum tunanin Yassar shine; shin ko yaya yara marasa gatan iyaye (wadanda iyayensu suka rasu suka barsu) suke iya rayuwar farin ciki bayan gushewar iyayensu daga doron kasa???

Ganin cewa shi da girmansa (at 33 years) iyayensa sune tsaye akan hidimarsa da tattalin al amuransa har gobe&

Ammih da Abbih sune farin cikinsa kuma masu kula dashi da gemunsa a kasan haba da komai. Kai har gobe Ammih ke kula da komai nasa including ci da sha& .

Sai yake yawan cewa a ransa&

"To wadanda basu da Ammih da Abbih fa, ta yaya suke tafiyar da rayuwarsu???"

"Abubuwa da yawa, har a wannan matakin, sai Ammih tasa ido a kansa ta tsaya ta kula dashi da lallashi sannan zai yi, misali ko akan shan magani, idan bashida lafiya, sai Ammih ta bashi da kanta da hannunta, ta kula da cin abincinsa bisa ka ida. Baka tashi ganin rudewar Ammih Tarha sai Yassar bashi da lafiya."

"Ita Ammih bata taba duba cewa wai yazu ya girma. Kullum kallonshi take a bashi da maraba da jaririnnan nata (Ibny) na shekaru talatin da uku na can baya, wanda take goyawa da majanyi kullum ta manne a bayanta."

"Inda aka yi sa a shine duk dangin nasu wato zuri ar Alkali Jalloh Ahmadu, babu mai jiran Abbih yazo ya bashi wani abu. Sau tari ko ya bada gudunmuwa, ko bai bada ba basu noticing. Allah ya azurtasu ya yalwata arzikinsu. In ka cire Baba Ado mai karancin samu."

"Wanda shima in aka yi duba na tsanaki ga tasa kadaitacciyar rayuwar, tofa cikin rufin asirin Allah yake rayuwarsa a inda yake zaune. Ba rashin ci, ba rashin sha kona suttura."

"Saidai kawai ace kalar rayuwarshi da ta iyalin dan uwansa marigayi Alkalin Alkalan Tambuwal Jalloh, ta sha bambam."

"Rayuwar Baba Ado, gabadaya rayuwa ce ta gudun duniya, ba ruwanshi da kyale- kyalen zamani da neman tara duniya, komaiya samu shi da amajiransa yake ci, ba ruwasa da son jin dadin duniya, yafi maida hankali ga malantarsa da aikin gonarsa."

**** **** ****

"Jirginsu yaci gaba da saukowa kasa- kasa daga cikin hazon samaniyar Subhana, ya gama shigowa yankin Ifrikiyya, dauke da Mr. Yassar Muhammad Jalloh, wanda har zuwa lokacin yake lumshe da idanunsa, yana tunanin rayuwarsa data iyayensa gabadaya, sana ta kanin Kakansa Baba Ado, a haka har suka sauka a garin Kano, inda basu bata lokaci sosai ba suka bi connecting flight zuwa garin Sokoto."

"Mr. Yassar Muhammad Ahmad Jalloh, kamar yadda yake rubuce a jikin fasfo dinsa,"

"ya sauka a kasarshi ta gado cikin wannan daren mai lullube da bakin hadari, ba jimawa da saukarsu a filin jirgin saman Sokoto aka tsuge da ruwan sama, ruwa ake kamar da bakin kwarya."

"Hakika garin Zamfarar Najeriya na daya daga cikin kananan jihohin arewacin Najeriya da yake matukar so, saboda tana makwabtaka da jihar iyayensa. Suna kuma amfani da kusan dialect guda. Don haka yana son birnin Zamfara sosai a ransa, kamar ko kwatankwacin yadda yake son jihar Sokoto."

Don haka da bisimillah sosai a bakinsa da addu ar neman nasarar abinda ya kawo shi yake shigowa cikin garin na Zamfara.

"Daga saukarsu  chauffer din dake jiran isowarsu tuntuni, ya daukosu a bayan motar UNICEF wata sullubebiyar farr Hilux mai dauke da tambarin UNICEF, kai tsaye ya wuce dasu babban birnin Zamfara, wato Gusau."

"Da shigarsu Gusau ya wuto dasu masaukinsu, inda aka tanadar musu masauki a shahararren hotel dinnan (Nahuche Hotel),"

dake da muhalli anan a tsakiyar Gusau din Zamfara.

"Sai a washegari ne bayan sun yi barcin gajiya sun more sun huce gajiya, sunyi wanka, suka sauko kasan hotel din sukayi karin kumallo a dakin cin abincin hotel din, daga nan basu koma daki ba, direban da aka tanadar musu don zirga-zirgarsu a Zamfara (chauffer) dinsu na jiya mai suna Kamilu, ya wuce dasu garin Anka, shi da Femi da Mrs. Sylvanus, Yassar ne a gefen direba, wato mazaunin gaban motar, yayinda Femi da Ngozi suke hakimce a gidan bayan Hilux din."

A yau Mr. Yassar sanye yake da shadda Sheraton kalar  sea green da aka yiwa dinkin zamani na mazan Arewa  yan hutu.

"Rabonshi da irin wannan shigar ta al ada irin haka, cikin Caftan na shadda da hula cikin kamala har ya manta, ba kuma karamin kyau shigar tayi masa ba, ta maidashi cikakken Ba-Afirkensa, har Femi saida ya kasa shiru da ganin haduwar kyan da Ogan nasa yayi, da yadda dressing din ya fiddo"

"kamalarsa, ilhamarsa da kwarjininsa. Femi saida ta kai shi ga tankawa inda yace."

" wato daidai ne da ake cewa kowa ya bar gida-gida ya barshi, na kuma yarda (No place like home)! ."

"Sai Yassar ya

Please Login or Register in order to submit comment