gtag('config', 'G-VDLWYD7FHB'); Reading KELTOUMA Tafiyar Kaddara By takori kabara Chapter 7 | ArewaNovels
ArewaNovels

Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa mahaifiyar yarinyarnan da  yarta ke samun daukan attention dinsa a duk lokacin da ya gansu sai ya dakatar da duk abinda yakeyi ya tattara hankalinsa a kansu, duk sanda ya gasu sai hankalinsa ya dauku garesu. Toh yanzunma hakan ce ta faru, sun sa hakalinshi ya tafi garesu gabadaya."

Saura kadan Mr. Yassar ya kwashe kafafunsu da hancin motarsa saboda yadda suka tsallako ba tareda duba tahowar motar dake gabansu ba.

"Kuka na hawaye ba sauti yarinyar keyi yau ma, tana tafe tana share ido da hanci da gefen gyalenta, gyalen ma wani dukun-dukun dashi, hannnunta cikin na mahaifiyarta kamar dai  yar shekara biyar din da za a tsallakar titi."

"Har ransa yaji faduwar gaba lokacin da ya kusa kwashesu da hancin motarsa, sabida tafiyar hawainiyar da yarinyar keyi akan hanyar data tabbata mota na wucewa, da taimakon Ubangiji ya samu ya kauce musu, ya ga ya dace daga yau ya sakama yarinyar nan"

sunan da ya dace da  habit dinta na koke- koke. Tuni zuciyarsa ta dade da ambatarta da suna Akoke .

"Wannan shine ganinsa na uku kenan dasu, kuma kullum ya gansu da hawaye shabe- shabe yake ganinta, idanunta a jike kamar  yar yaye, uwarta na faman lallashinta kamar ta hadiye abarta don so, kauna, tattali, tausayi da kulawa."

"Alal hakikah haushi sosai yarinyar ta koma baiwa Mr. Yassar yanzu, saboda ya tabbata tana azabtar da uwarta da kukan nan nata, wanda a ganinsa na shagwaba ne kawai, kamar a kanta aka fara zaman sansanin  yan gudun hijira?"

"Ko ina ka duba akwai yara  yammata sa anninta, amma su babu abinda ya damesu, sabgogin gabansu kawai suke yi a cikin camp wasu har da hira da samarinsu hankalinsu a kwance, suyi nan suyi can kamar suna gidan iyayensu, har wajen samari  yammatan ke zuwa ana barin rashin tarbiyyah, sai ita indararo sarkin kuka da aukin kwararar da hawaye."

"Daga cikin motarsu yake zaune, bayan yayi parking a inda ya dace, ya kashe injin"

"motar, yana kallon yadda yarinyar ta tsaya a bakin kofar shiga ofishinsu ta lafe, ta noke a jikin kofa wato taki shiga, sai uwar ta yi mata wata magana cikin yarensu, sannan uwar ta shige cikin ofishin ta barta a bakin kofa."

"A tare shi da Femi suka fito daga motarsu, suka rurrufe kofofinta duk a tare, sannan cike da aji (class) na kasaitattun samarin dake ji da lokacinsu da tashen ilmin bokonsu, suka soma takawa cikin kyakkyawar shiga ta kamala, da wani irin takun tafiya na aji da kasaita daga Mr. Yassar Jalloh, suma kuma kai tsaye ofis dinsu wanda ke cikin ofishin ma aikata suka nufa."

"A bakin kofar shiga yarinyar na nan tsugunne akan kafafunta inda uwar ta barta, tana hadiyar rai gami da sauke ajiyar zuciya mai nauyi, alamar taci kukan har ta gode Allah."

"Kukan ya tsaya don kansa yanzu, tana goge hawaye da dukunkunannen yalolon gyalenta da ya sha datti ya koshi mai kama da abun tatar koko, kallo daya zaka yi mata ka gane tana cikin damuwa mai tsanani musamman na rashin tsaftar da take ciki."

"Hakika rashin wanka ukuba ne, sannan wata izaya ne da yafi komai azabtar da zuciyarta. Kuma babban abinda ke takura rayuwarta da kara saka mata kin zaman IDP Camp."

"Wata irin rudewa ce ta sameta a lokaci guda, data dago jan idonta don kallo masu tahowa, cikin kuskure idanun suka fada cikin na ingarman matashin dake tahowa, wannan shine karo na uku da suka hada ido accidentally, daga inda take tsugunne tana iya hango harara mai dauke da gargadi (warning look) da Mr. Yassar ke zabgo mata tun daga nesa."

"Tayi maza ta sunkuyar da kanta. Yana zuwa gabanta yayi kamar zai wuce, har ya wuceta da taku daya, biyu ko me ya tuna? Sai sai ya dan dakata, har Femi yazo ta gabanshi ya shigeshi ya shiga ofis, shikuma sai ya dawo da baya, ya kalleta a kankance da ido, kana yayi kasa da murya yadda ita kadai zata iya jinsa yace."

" Hello, crying Angel! Ina rokonki don Allah ki rage kuka!!!"

Idan damuwa ce dake kuma kinaso Allah ya musanya miki damuwar nan da

"madawwamin farin ciki, toh kuka da zubda hawaye ba sune maslaha ba ."

"Ta sunkuyar da kai daga barin kallonsa, a take jikinta yayi sanyi, ya kuma soma daukar rawa, sakamakon wani azababben kallo na kasan ido Yassar Jalloh yake kara kora mata daga tsakiyar lumsassun idanunsa. Kukanta in one way or another, bai san dalili ba; hurting din feeling dinsa yakeyi."

" Idan kika yi saken da nayi miki gani na hudu da hawaye ko kaka a idonki, na rantse sai na kabari ya fiki jin dadi a wurina."

"In fact sai kin gane Camp ba lahira bane, ba kuma karshen rayuwar diya mace bane."

" IDP Camp life , ba komai bane face jarrabawa daga Allah, domin ya jarrabi imanin wasu kalilan cikin bayinsa."

"Wawuya kawai marar tawakkali, shagwababbiya, mara tausayin mahaifiyarta ."

"Jajayen idanunta ta zazzaro waje tana masa kallon tsoro, hadi da mamakin kausasan kalamansa gareta."

"Yassar bai tsaya ba yayi tsaki ya wuce zuwa cikin ofis dinsu, yanata kara sakin tsuka kasa-kasa, kamar wanda yaci tsaka."

 I hate to see this tears .

"Ofishin ma aikatan IDP camp na Anka, wani babban aji ne shima aka mayar ofis, akwai kujeru da tebura da tsirarun ma aikata suna ta kai kawo a cikinsa. Kasancewar asabar ce da yawan ma aikata suna gida basu zo ba."

"Nasu Yassar ma karamin ofis ne guda can cikin babban ofis din ma aikata aka gyare musu shi tsaf, ya sha windows da net, da solar inverter."

"Uwar bata ga tahowarsu ba shi da Femi ta bayanta, ta shige ofishin, Femi ne ya fara rufa mata baya kafin Yassar ya shigo daga karshe."

"Uwar sanye take da zanin wata kodaddiyar atamfa koriya fatau, da wata jar bulawus yagalgalalliya a jikinta, ragga ne sosai (tsumma) don kuwa sun mutu, tayi lullubi da zanin atamfar har kanta."

"Gaban Haladu ta russuna ba tareda la akari da cewa zata girme masa ba, tana ce masa cikin muryar roko mai ban tausayi."

" Dan nan ka taimakawa diyata da kayan mata (audugar mata) da anka raba jiya, mu bamu samu ba (hygiene kit) ."

"Haladu ya kalleta a lalace, sannan cike da raini da tsana ta babu gaira babu dalili yace."

" Shin wa kika baiwa ajiyar audugar matan da anka raba jiyan accikinmu, da yanzu zakki zo karbar ajjiyarki? "

"Ya fada yana zazzare mata ido kamar sa arshi ko kanwarshi da bazamfariyar hausarshi, matar kamar zata yi kuka tace  ka dubi Allah nace ka taimaka mata, wallahi diyata bata iya amfani da&  ta kasa cigaba, don da kunya tace diyarta bata iya amfani da tsumma ba wajen yin kunzugu."

Amma yaya zata yi da diyarta sarkin taurin kai da shagwaba?

"Tayi-tayi da ita ta saka tsumma tace ita Allahnbur saidai audugar mata, har ta kawo tsohon tarihi ta tunawa uwarta, ita Babanta ya hanata amfani da tsumma a yayin kunzugu."

"Inda ta cewa uwar cikin kuka,  kin manta watarana ina ciwon mara, muka je asibiti da Babana, inaji likita na gayama Babana cewa al ada zan fara yi, ya bashi shawara kan ya dinga sayamin audugar mata duk wata, saboda shi tsumma likita yace ana"

daukan cututtuka wajen amfani dashi idan ba ayi taka-tsan-tsan ba wajen tare al ada.

Tun daga lokacin Baba yayi alkawarin sayamin auduga duk wata. Don yau kinga babu idon Baba sai kice in tare da tsumma? Nidai Ummami bazan saka tsumma ba .

"Ta kara luguiguita zuciyar uwar da cewa  nasan da Babana yanada rai ko kobon shi na karshe kenan a aljihunsa, sai ya san yadda yayi ya sayo mun audugar mata . Tasaka mata kuka sosai cikin shagwaba da jin maraicin mahaifinta."

"Koda ma can tunda Allah yasa ta haifeta a duniya, diyarta KELTOUMA, ta kasance yarinya mai yawan gwalangwaso (fi ili/taste) da matukar kiyaye tsaftar jikinta, data abinda zata ci ko duk abinda zata yi amfani dashi, don dai rayuwa tayi gwatson mage dasu ne, a sanadin ibtila in nan na ta addanci, da ina za a ga Keltoumanta haka; dukun-dukun  cidin- cidin da dauda/datti? Keltouma da ke wanka kusan sau uku a rana saboda yawan gwalangwasonta da fi ilin tsabta?"

Ummami ta tabbata wannan na daga cikin abubuwan da ke kara ma diyar tata

"trauma na kuncin zuciya, in ta duba kanta a mudubin motar wajen taga yadda suka koma kamar majanunai, ko masu cutar kanjamau itada Ummami, cikin dan lokaci da rashin Monsourou, wannan tunanin kadai yana sawa Keltouma tayi ta kuka ba kakkautawa har sai wani lokacin ta shide."

"Ya zamana yanzu Ummami ta fara gajiya da lallashin da take yawan yiwa Keltouma, saidai ta zuba mata ido cikin alhini a duk lokacin data soma koke-kokenta."

"Yau da suka wayi gari taga bakon wata ya zowa Keltouma, kememe taki yarda da yin amfani da tsumma, sai tace gara ita tazo da kanta ta rokar mata alfarmar audugar, in yaso su Haladu suyi mata wulakancin da suka ga dama duk zata shanye, in dai a karshe zasu bayar da  hygiene kit dinnan ga diyarta."

Ta gwammace Haladu ya yi mata Rashin kunyar akan dai ta turo Keltouma gaban idon wadannan fikakkun samarin marassa kirki da basa ganin kan kowa dake sansanin da gashi rokon audugar mata.

"Dole ta kiyaye martabar diyarta daga kurayen mazan da suka cika IDP Camp, suna"

"lalata mutuncin kananan yaran mutane, masu kwabawa yaran wato iyayensu suma watsatstsun ne basu da mafadi. Ya rabbi ka raba duk musulmi da zaman sansanin gudun hijira (inji Ummami)."

"Ganin ta cigaba da tsayuwa bata tafi ba, tana jiran lallai ya bayar sai Haladu ya mike a hassale ya soma sababi, yana nuna mata hanyar fita da dan alinsa, fadi yake cikin daga murya."

" ku wato mutanen nan na gama ganeku, girman kanku bai barinku yin fafutuka da kokawar amsar tallafi kamar sauran mutanen wurinnan, sabida kuna jin kanku mai kama da fantekar jeren mata."

"Saidai bayan an gama rabo ki boye  yar ki a bakin kofa, kizo ki damu mutane da rokon a bata kaza a bata kaza ko, haka fa kuka yi min watan da ya gabata. To an hana ta din, baza a bata din ba, ko ince na karfi ne kuzo ku kwata, sakarkaru kawai."

"Ko kuma in kun matsu, to ki aiko yarinyar da kanta wurina can anjima idan gari yayi duhu ta amsa, bayan  hygiene kits biyar har kudin kashewa zan bata& &  ."

"Da alama Haladu bai san da shigowar mutum ta bayansa ba, yayi nisa a zazzaga rashin mutuncinsa, rashin tausayi da rashin tarbiyya tsantsa ga rayuwar bayin Allah, don cigaba yayi da cewa."

" Yarinyar taki dako kirgen dangi babu a jikinta, sai dan banzan tsayi kamar falwaya, da wani kanta kamar ciyawar Doki, ita kike faman boyewa maza ko?!"

"Yo Allah na tuba ni Haladu, ko ina bin mata a sansanin nan, ai bazan bi wadanda basa wanka ba& & . ."

"Zuwa yanzu hawayen takaici ya zuboma matar da jin irin kalaman tozarcin da Haladu yake fadi akan diyarta. Zuciyar Mr. Yassar dake tsaye daga bayan Haladu yana saurare ta shiga wani irin tafarfasa. Duk da cewa tuni yanada labarin ana yin badala da  yammata da yara mata a IDP Camp, bai taba katarin gani da idonsa ko ji da kunnensa ba sai yau (tayin kwartanci a fakaice), kwartancin ma na wulakanci. Yassar yayi gyaran murya, nan Haladu ya juyo da sauri, suka hada ido."

"Haladu ganin fuskar Oga Yassar yayi ta hade tayi murtuk, ta murtuke kamar hadarin da ya nausa yayi gabas, tayi kamar launin"

"toka-toka, ba abinda ya tsana a duniya irin rashin tausayi ga mata, da rashin sanin ciwon kai ga da namiji."

"Wani zazzafan mugun kallo Yassar yake yi ma Haladu, hakan yasa hanjin Haladu ya hautsina saboda tsorata da yayi da zafin kallon da Yassar ke masa."

"Amma sabanin tunaninsa Yassar bai ce masa komai ba, sai ma dauke idonsa da yayi daga kan Haladun, ya tako kadan ya wuce ta gaban Haladu, sannan ya maida hankalinsa kacokam gun matar, wadda har zuwa lokacin take tsaye a gun, tana matse ido da tsane hawaye, da Sokoto accent dinsa Mr. Yassar ya karasa gabanta ya tambayeta."

" Iya, yaya dai? Meke faruwa haka a wurinnan? Wa ya saka ki kuka? "

"Ta juya kawai don barin wurin, hawaye na disar mata dis-dis! Daga idonta zuwa kan yatsar kafarta. Kamar bazata amsa masa ba shima, amma abu daya yasa ta daga ido ta dan dubeshi; intonation din cikin muryarsa."

"Sakamakon shi a cikin tashi muryar akwai maturity (akwai sanin ciwon kai), akwai"

tarin girmamawa da alamun tausayawa a gareta.

"Sannan har ila yau, muryarsa dauke take da nagarta da girmama na gaba, sannan akwai wata ilhama a tareda duk wani tashin amon muryarsa, mai nuna shi din daga babban gida na tarbiyyah ya fito."

"Yayi mata maganar ne cikin girmamawa da matukar ladabi, tamkar mai magana da mahaifiyarsa."

"Ba kamar Haladu ba, wanda ke magana da ita gatsau, cike da raini, izgili da wulakanci a gareta, babu albarka da tausayi ko kankani a cikin zancensa, tamkar zai kai mata mahangurba."

"Hakika ranta yayi mugun baci da kalaman Haladu, amma bata tanka ba, a ranta tana so ta gane ko me Haladu yake nufi data tura masa diyarta amsar hygiene kit idan gari yayi duhu, rashin albarkar data ke gudunma  yarta a sansanin nan?."

"Ai ko zasu mutu babu kayan amfani, jini kuma zaiyi ta malala a tsanin kafafun Keltouma saboda rahin auduga, bazata sake zuwa ofishin nan neman taimakon kowa ba."

Bazata yi saken da mutuncin  yarta zai wulakanta a wurin kurayen lalatattun mazan dake wurinnan ba marassa tsoron Allah.

"Ta kwana da sanin abubuwan da ke wakana a camp din, don a fili akeyi ba wai boyewa ake yi ba, wanda shi ya maida ita (over-protective) akan diyarta& & ."

"Ita ba irin wadannan lalatattun iyayen sansanin nan bace, masu sarayar da mutuncin  ya yansu don a basu sabulu ko audugar mata. Koda zasuyi yawo tsirara itada  yarta, yunwa kuma ta kashesu a sansanin  yan gudun hijira zata kula da mutuncin  yarta fiyeda"

komai.

"Ummami ba tun yau ba ta gama lura da cewa Haladu ya tsanesu, ba laifin tsaye babu na zaune, koko tace ya tsani ya bude ido yaga gilmawarsu a camp dinnan. Maganarsa ta yau akan Keltouma ce tafi komai bakanta zuciyarta, saboda Keltouma itace kadai abinda ta mallaka a duniya ahalin yanzu."

 Nace what s happening? (Me ke faruwa) me take so?

Yassar ya dan daga murya yana tambaya kamar a fusace. Ganin ta kasa

"amsashi sai ya mayar da akalar tambayar tashi ga Haladu da turanci a matukar fusace. Haladu ya hadiye tsoronsa, ya mayar masa da martanin abinda ya kawota, ya kara da cewa,"

 sanda ake registar rabon kayan suna ina? Suna tsaye a wajen suna kallo fa.

"Sai daga baya zaka gansu sun zo sun ishi mutane da  yar murya, kullum haka suke yi itada  yar ta."

"Sai su dinga ware kansu, kamar su suka fi kowa, ga  yar tata kamar wata diyar gwal da bata shiga ko ina da kanta, saidai ta aiko uwarta, ita tana makure a gefe tana shagwaba, wallahi shine abinda yake bani haushi dasu Oga ."

"Yassar ya juya zuwa kofar shigowa da hanzari ya dubi yarinyar, still tana can durkushe a inda ya barta, tayi maza ta sunkuyar da kai don tsoron sake kallon idanunsa take ji sosai."

"Haushinta ya kara kama shi, he was like  ta raina uwarta, banda haka ta yaya Uwa zata zama  yar aiken diyarta, banda sangarta da rashin hankali irin nata? "

"Wannan yarinyar da kanwarsa ce da suka fito gida daya, yau Allah kadai zai"

"rabasu, sangartarta da shagwabarta sunyi yawan dake bukatar tsawatarwa daga babba, wato tana bukatar kamar wani dan uwa namiji ya dinga yi ma jan ido bayan Innarta, wanda zai daidaita mata sahu ta san ta girma."

Don daga dukkan alamu bata san darajar uwa ba. Batasan Annabi ya faku ba. Balle uwa-tagari mai attributes din kwarai irin tata.

"Shi fa duk inda UWA mace take wani matsayi mai girma na dabam yake bata, fiye da kowa da komai, sabida son da yakeyi ma Ammihnsa."

"To babu dangin Iya balle na Baba, kuma dai ba abinda ya zo yi kasar Najeriya ba kenan, wato shiga rayuwar wasu 'yan gudun hijira. A ah, yazo ne takanas domin inganta rayuwar kananan yaransu."

"Ya lura matar nama  yar ta wani irin gangariyar SO. In yace so, to zallar so da kauna yake nufi na Uwa-mahaifiya ga abinda ta haifa, irin son da wasu iyayen ke yima  ya yansu wanda har ya zarta kima, son da ya wuce ace ana yima  ya ya masu shekarun balaga irin shekarunta,"

 Ko ina ubanta& ?

"Mr. Yassar yana wannan tunanin bai samu amsa ba yaji Haladu na cewa cikin tsawa  Du Allah Malama ki bace mana da gani anan, in taga dama ta zauna haka ba kunzugun ."

"Matar na jin haka ta taka da sauri ta fice da sassarfa. Ga dukkan mamakin Haladu da Femi, sai suka ga Mr. Yassar ya cira kafa yabi bayanta da azama shima, yana mai cewa."

 Don Allah Iya& ki dakata.. .

"A bakin kofa

Please Login or Register in order to submit comment